Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

Shi kuwa Habu harya fara taku daga wurin da yake yana mai yin gaba, sai kuma yaja ya tsaya lokaci d'aya, yana mai sake juyowa b'arin da Yarima Asad yake.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Shin wai me ma yasa da zaka koma ne Bro?"

Tambayar tazowa Yarima Asad a bazata.
Hakanne yasa ya d'ago k'wayoyin idanuwansa da sauri, yana mai zubasu akan fuskar Habu.
Kana daga bisani ya d'an bud'e baki cikin daburcewar magana, yana mai fad'in.

"Dama...da..y.Yake jiya bayan mun koma gida na nemi wani muhimmin abuna na rasa ne...to shine wai da nake tsammanin ko a wurin da muka...zaz..zauna jiya na yadda shi, to bayan kuma na riga nazo, sai naga ai bani da tabbacin idan na shiga cikin na duba ma zan same sa, tunda dama zargi ne nake ba tabbatarwa ba, shiyasa kawai na yanke hukuncin juyawa na koma."

Ya k'arasa maganar yana mai sauke numfashi, tare da saurin kawar da idanuwansa daga kan fuskar Habu, yana mai sauke wasu irin ajiyar zuciya.
Domin ko gani yake tamkar Habun zai gano gaskiyar abun da ya kawo sa gidan nasu idan ya cigaba da kallon sa.

Ko kad'an baiyi tinanin zai iya shirga irin wannan k'aryar ba, sai gashi kuma tazo cikin k'wak'walwarsa ba tare da ya shirya ba, hakanne yasa sa sake lumshe idanuwansa, yana mai godiya ga Allah da yasamu abun fad'e cikin sauk'i.

Shi ko Habu harga Allah ya yadda da abun da Yarima Asad ya fad'a masan.
Hakan ne yasa sa bud'e baki yana mai cewa.

"Amma kuma shine da zaka juya ba tare da ko nema na kayi ba, ashe dama babu amana kenan, tunda har zaka iya zuwa k'ofar gidan mu ka juya ka tafi ba tare da ko nema na kayi ba, bayan kuma kasan ko a waya ne idan ka kira ni zan futo.
Kuma ma ai zata iya yuwuwa anan d'in ka yarda abun naka, dan haka bara yanzu naje na kawo maka fura in yaso bayan kasha sai muje mu duba ko.
Amma fa kasani wallahi banji dad'in yadda kaso tafiya ba tare daka shigo ba ko kad'an."

Ya k'arasa maganar yana mai shirin juyawa ya tafi.

"Sorry Bro, ban san me zance bane idan na k'araso shiyasa har na yanke hukuncin juyawa na tafin, amma kayi hak'uri, hakan bazata sake faruwa ba daga yau in sha Allah."

Yarima Asad ya samu kansa da bawa Habu hak'uri, duk da kasancewar sa mutum da baya bada hak'uri koda kuwa shine yayi maka laifi, amma sai gashi yau Habu ya ciri tuta, badan komai ba kuma yayi hakan sai dan tsananin mutuncin Habu da girman sa da yake gani acikin idanuwansa tun daga jiya had'uwar su ta farko, wanda ya rasa dalilin da yasa yake jin hakan a gare sa.

"Ba komai Aboki ya huce, yanzu dai kad'an jirani anan bara naje na kawo maka abinci ko."

Da sauri Yarima Asad yace.
"Da kabar abincin nan ma Bro, saboda wallahi a k'oshe nake ni, kuma ma kaga sauri nake yi ai."

Ya fad'i hakan saboda yadda yaji gaba d'aya ya gaji da zaman cikin d'akin, bashi da wani buri a yanzu face ya gansu sunje cikin lambun nan, ko Allah zai sa ya sake arba da kyakkyawar fuskar ta.

"Wannan ne kuma baka isaba wallahi, yau sai kaci abincin gidan mu, domin kuwa dama munyi alk'awari daku akan duk ranar da kuka dawo sai kunsha fura tun da jiya baku shata ba."

Habu ya fad'a yana mai cigaba da tafiyar sa, ba tare da ya tsaya bi takan Yarima Asad ba.

Hakan da Yarima Asad yaji ne ya sanya sa lumshe idanuwansa, kana ya d'an jingina jikin sa da kujerar yana mai d'aga kansa sama.
Yayinda har lokacin yake jin zuciyar sa na cigaba da yin bugu da matuk'ar sauri.

Baifi minti goma Habu ya d'auka da futar sa ba, sai gashi nan ya dawo hannun sa rik'e da wani k'atoton tray'n silver mai tsananin kyau.
Yayinda saman tiren kuma yake jere da kayan abinci kala-kala akan sa.

"Dining za akai maka ko kuma anan zakaci?"

Cewar Habu a lokacin da ya k'araso gaban Yarima Asad da yake lumshe da idanuwansa har lokacin.

"Ajiye anan d'in kawai."

Ya fad'a yana mai d'agowa daga kishingid'en da yake tare da bud'e idanuwansa.

"Ok to a sakko k'asa ko."

Cewar Habu yana mai ajiye tray'n a k'asan had'ad'd'en capet d'in da yake malale a tsakiyar falon.

Ba tare da ya sake cewa komai ba ya sauko k'asan, yana mai tank'washe k'afafuwansa a gaban tray d'in.

Wani had'ad'd'en akushi'n da yake rufe da murfinsa ne ajiye akan tray d'in, a gefen sa kuwa wata azababbiyar k'warya ce mai tsananin ado a jikin ta da aka rufe ta da faifan kaba, yayinda daga saman faifan kabar kuma aka kife ludayin duma akan sa.
Sai a gefen k'waryar kuma wani had'ad'd'en kwandon kaba ne da yake cike mak'il dasu ayaba, lemo, inibi, tufa, tare da yankakkiyar jar kankana akansa.

A hankali Ya d'aga zara-zaran yatsun hannunsa da suke d'auke da kwantaccen gashi akan su, yana mai d'orasu akan murfin akushin nan, kana ya d'an zame sa yana mai ajiye sa a gefe.

Da sauri ya lumshe idanuwansa, saboda wani irin daddad'an k'amshi da yaji ya daki hancinsa.
Lokaci d'aya yaji yawun sa ya tsinke, duk da kasancewar sa mutum wanda bai saba cin abinci ako wane wuri ba, amma kallo d'aya kawai yayiwa farfesun naman ragon da yayi matuk'ar dawuwa yana futar da tururi da k'amshi ya burge sa.

"Malam ka fara da fura kawai, dan a gaskiya yau baka isa kace zaka tafiba ba tare da kasha fura ba, dan haka fara da ita karma cikin ka ya cika ba tare da kasha ta ba."

Cewar Habu cikin barkwanci sa, yana mai kai hannunsa zuwa kan faifan kabar nan da yake kife akan k'waryar ya janye sa.

Da sauri Yarima Asad ya sake had'iyar yawu, saboda yadda idanuwansa sukayi masa tozali da damammiyar furar da ta kasance fara k'al cike da kusan k'waryar nan.
Babu abun da take futarwa sai k'yallin nono, da alamun dai gaba d'aya furar da aka sanya aciki bata da yawa, kusan duka nonon ne.

Lokaci d'aya yaji wata irin yunwa ta taso masa, wato dai tun yunwar jiya da take k'unshe a cikin sa ta sanadin abincin da bai samu yaci ba itace ta motso yanzu.

A hankali ya mik'a hannunsa yana mai d'aukar ludayin dumar nan da shi.
Kana ya sanya sa a cikin kakkaurar furar yana mai d'an jujjuyata, tukun ya d'ebo kusan rabin ludayin yana mai d'orasa akan lab'b'ansa.

Da sauri ya sake lumshe idanuwansa a lokacin da d'an-d'anon furar ya sauka akan harshen sa, ga wani irin ni'imtaccen sanyi wanda baiyi yawa ba, kana kuma shi baiyi kad'an ba da ya kasance a cikin ta, wato dai d'an dai-dai dai-dai kenan.
Zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai tab'a shan fura mai dad'in wannan ba.
Hak'ik'a yau d'in ya tabbatar da yazo hurin masu abun, wato kenan da duk wacce yake sha a gida ba fura bace yanzu ne yake shan asalin fura.

Ji yake tamkar kunnen sa zai tsinke tsabar dad'i, tini yaji damuwar dake dank'are a cikin ransa ta d'an ragu, saboda sanyin furar da ke sanyaya masa zuciyarsa.

Sai da yasha ta sosai, tukun ya ajiye ludayin yana mai mayar da murfin kabar nan ya rufe k'waryar.
Kana ya d'auki fuck d'in da yake ajiye akan trya d'in, yana mai sanya sa a cikin akushin nan na naman rago.

Zallar tsoka da romo ne kawai a ciki mai tsananin laushi, domin kuwa gaba d'aya sai da aka zare k'asusuwan dake jikin naman tukun akayi farfesun, dama kuma haka sukeyi ako da yaushe, farfesun tsoka daban kana na k'ashi ma daban.
Cako 'yar madai-daiciyar tsoka yayi da fuck d'in, yana mai kaita cikin bakin sa.
Bai san lokacin da ya sake lumshe idanuwansa ba yana mai d'an jin-jina kai a hankali.

"Ashe dama Fulani ma sun iya girki irin haka."
Ya fad'a acikin ransa yana mai tauna tsokar bakin sa a hankali.
Yayinda yake jin dad'in ta na ratsa har cikin k'wak'walwarsa.

Bai wani ci naman da yawa ba ya ajiye fuck spoon d'in a gefe, yana mai rufe akushin, saboda furar da ya riga ya d'irka a farko.
Kana ya d'auki ruwan da Habu ya tsiyaya masa a kofi mara sanyi yana mai shanye sa shima.

Tukun ya d'an janye jikin sa daga gaban kayan abincin yana mai jingina da kujera.

"To ya kaji dawuwar tamu mu Fulani."
Cewar Habu yana mai d'an had'a kwanikan wuri d'aya.

"Masha Allah."
Yarima Asad ya fad'a yana mai jifan sa da murmushi.

"To kaga yanzu zamu iya tafiya duban abun ko."
Habu ya fad'a yana mai mik'ewa tsaye.

Jinjina kai shima Yarima Asad yayi yana mai mik'ewa tsayen ba tare da yace komai ba.
Tukun suka jera shi da Habu suna masu kama hanyar waje.
Yayinda Yarima Asad kuma yake fatan Allah ya had'asa da ita a wurin, koda kuwa bazai samu damar yi mata magana ba ya samu kawai ya kalle ta, ya san zaiji dad'i a ransa.

Suna shirin shiga cikin tamfatsetsen had'ad'd'en lambun nan nasu mai cike da abubuwan ban sha'awa a cikin sa wayar Habu ta d'auki ringing.
Hakan ne yasa sa dakatawa daga tafiyar da yake, wanda hakan ya sanya Yarima Asad tsayawa dole shima, yana mai sanya hannu a cikin aljihun wandon sa ya zaro wayar tasa.

Sunan da yayi saving d'in number babban yayansu da shi yaga ya futo akan screen d'in wayar.
Hakan ne yasa sa amsa wayar da sauri, yana mai kaita kan kunnensa.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.
"Asallamu alaikum Hamma na."
Tukun yayi shiru da alamun yana sauraron abun da yayan nasa ke fad'e ne.
Kana daga bisani kuma ya bud'e baki cikin sauri yana mai fad'in.
"Eh ina nan.
Tom shikenan gani nan zuwa yanzun."
Ya fad'a yana mai janye wayar daga kan kunensa.
Kana ya juyo b'arin da Yarima Asad yake yana mai fad'in.

"Wallah Hamma Jauro ne wai ke nema na yanzu zan d'an yi masa wani aiki, amma idan ba damuwa mai zai hana kazo mutafi tare, na san ba jimawa zanyi ba, in yaso idan mun gama sai mu dawo mu duba ko."

Habu ya fad'a yana mai kallon Yarima Asad.

"A'a, ina ganin kawai kaje, ni kuma sai na k'arasa ciki na duba abun tun da kaga har mun k'araso, in yaso kazo ka same ni anan cikin in kagama."

Cewar Yarima Asad yana mai kallon Habu.

"Tom shikenan hakan ma yayi, ka.jirani a cikin yanzu nima na san zan dawo."

Habun ya fad'a yana mai juyawa ya tafi da sauri.

"Tom shikenan sai ka dawo."
Cewar Yarima Asad yana mai fara d'aga k'afafuwansa ya doshi cikin lambun shima.

Tun daga bakin wurin ya fara waige-waige, yana mai fatan tozali da ita, amma sai dai har ya k'arasa zuwa wurin da suka zauna jiya baiga ko mai kama da ita ba.
Hakan ne yasa sa jin duk babu dad'i a ransa.

Har yanzu wanan shimfid'ar da suka zauna jiya akanta tana nan shimfid'e a wurin, sai dai kuma yau ko kallon ta baiyi ba ya huce zuwa gaban wata had'ad'd'iyar kujerar gini da take kafe a cikin k'asa yana mai zama.
Kana ya lumshe idanuwansa yana mai jin yadda zuciyar sa take wani irin bugu.

Sosai yake jin ciwon rashin ganin ta da baiyi ba a cikin ransa, domin ko yana da abubuwan yi da yawa ya barsu ya tawo nan d'in, gashi kuma da alamun har ya tafi bazai samu abun da yazo nema ba, sa'ar sa d'aya ma da Allah ya kawo Habu kafun ya tafi, da ko nan d'in ma bazai samu damar shigowa ba, duk da dai a yanzun ma yana jin ina ma ace baizo wurin ba, tunda gashi nan babu ko mai kama da ita, gashi shi kuma bazai tab'a iyayiwa Habu maganar ta ba, to yama ce masa me.

Ya jima lumshe da idanuwansa yana mai jin d'aci a ransa, kana daga bisani ya bud'e su yana mai sauke su akan had'ad'd'un furannin da suka yiwa lambun k'awanya kala-kala.

Sosai wurin yayi matuk'ar birge sa tun a jiya da suka shigo cikin sa, domin ko a rayuwar sa yana matuk'ar son wuri irin wannan, wato wurin da babu hayani sai kukan tsuntsaye da k'amshin furanni, tare da sassanyar iska kawai da zata na futa a cikin sa.

Zugum yayi a wuri d'aya, yana mai hurga idanuwansa a wurare daban-daban lokaci bayan lokaci.
Kafin daga bisani kuma ya mik'e tsaye, yana mai juyawa bayan sa yakai idanuwansa zuwa wata doguwar hanya da ya hange ta zagaye da dogayen bishiyu, ta yadda har wurin ya zamto tamkar lungu.

A hankali, kana kuma cikin sanyin jiki ya fara d'aga k'afafuwansa yana mai dosar hanyar, domin kuwa haka nan kawai yaji yana sha'awar yawatawa acikin wurin, kana kuma ga sautin kukan tsuntsayen da yake ji yana futowa daga cikin hanyar da sukayi matuk'ar d'aukar hankalin sa.
A rayuwarsa yana matuk'ar san tsuntsaye, domin ko bai k'i ba ya yini zaune a gaban su yana kallon su ko da daga nesa ne kuwa, saboda ba k'aramun nishad'i ganin su yake sanya masa a cikin ransa ba.

Cikin sanyi ya cigaba da dosar hanyar har ya k'arasa bakin ta.

Sosai wurin yayi matuk'ar birge sa fiye da ko ina.
Saboda yadda ya hangi hanyar doguwa da ita sosai, ga kuma wasu irin korayen ciyayi da suke zagaye da ita masu matuk'ar kyau da k'amshi, kana kuma ga dogayen bishiyun da sukayi mata k'awanya.
Hakan yasa ya danna kansa cikin ta yana mai jin wani irin shauk'i na d'ibar sa, ta yadda har ya fara jin rad'ad'in da zuciyar sa ke yi masa na rashin ganin abun da yazo nema na kaucewa.

Tafe yake kansa durk'ushe a k'asa har yay nisa sosai daga bakin hanyar.
Yayinda yake jin kukan tsuntsayen nan na sake kusanci da wurin da yake tunkarar.

Kamar ance d'ago kanka ka kalli gaban ka, ya samu kansa da d'ago kan nasa yana mai jefa idanuwansa akan hanyar da yake bi.

Take kuwa yayi suman tsaye a wurin da yake, zuciyar sa na wani irin bugu da matuk'ar k'arfi, ta yadda har yake jin tamkar zata hudo k'irjin sa ta futo waje.
Su kuwa idanuwansa cak ya tsayar da su akan Gimbiya Haddiyal da ya hangota tana tun karo wurin da yake kanta durk'ushe a k'asa itama.

Wani irin yanayi yaji yana lullub'e gaba d'aya ilahirin jiki da zuciyar sa.
Yayinda bugun zuciyar sa kuma ke k'aruwa sosai da sosai.
Gaba d'aya kasa ko da motsi yayi a wurin da yake a tsaye, tamkar yadda ya kasa janye idanuwansa daga kanta.

Ganinta yake tamkar ba ita bace wacce ya gani jiya, domin kuwa ba k'aramun mugun firgitaccen kyau yaga ta k'arayi masa ba fiye da jiya, hakan yasa yaji gaba d'aya yanayin sa na sauyawa.

A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa ko kad'an bata san da kafuwar sa a wurin ba, asalima gaba d'aya hankalinta ba a wurin yake ba.
Domin kuwa tun daga jiya har kawo yau bata sake yin murmushi ba, asalima ita kanta futowar bata dad'e da yinta ba, itama kuma tazo ne wurin tsuntsayenta ta basu labarin mutane biyun da ta had'u da su, wa'yan da take jin tsanar su sama da ta komai da kowa a duniya, saboda yadda taga suna shirin gina mata katanga a tsakanin ta da Gid'ad'on ta, wato Yarima Asad da kuma Jauron Yamma.

Gaba d'aya yinin jiya batayi sa a dad'i ba, asalima koda ta kwanta bacci gaba d'aya k'in d'aukar ta yayi, babu abun da ya tsaya mata arai face had'uwar su da Yarima Asad, tana mai jin hutar tsanar sa na k'ara ruruwa a cikin zuciyar ta.
Ba ita bacci ya d'auka ba har sai misalin k'arfe biyu na dare.
Haka kuma baccin na d'aukar ta ta fara mafarkin Gid'ad'on ta, sai dai kuma jiya bada murmushi ta tarbe sa ba, ta je masa ne da kuka, tana mai cewa ya gaggauta bayyana gare ta a zahiri, tun kafin magautansu su samu damar yin nasara a gare su, domin kuwa a kullum abubuwa marasa dad'i na sake faruwa ne.
Sai dai kuma har tayi ta gama baice mata komai ba tamkar kullum, sai kawai murmushin da yake aikin aiko mata da shi.
Hakanne yasa yau tana tashi daga bacci ko karyawa bata iya tsayawa tayi ba tayi wanka ta shirya, kana ta tawo wurin tsuntsayenta ta sanar musu da halin da take ciki.
Tukun a k'arshe bayan tagama fad'a musu ta taso ta tawo domin ta koma d'akin ta, wanda kuma yayi dai-dai da tawowar Asad cikin wurin badan yana tsammanin zai ganta aciki ba kuwa.

Sanye take da normal kayan fulani farare kar masu adon ja da bluen zare a jikin su, wato dai irin na kowa bana sarauta ba a jikin ta.

Babu wata kwalliya a fuskar ta sai kwalli kawai da ta zizara sa a cikin idanuwanta, su kuwa pink lips d'inta babu abun da suke faman futarwa sai shek'in maik'o, duk da ba wani abu ta shafa akan su ba, yayinda gashin kanta kuma ya kasance a tsafe kwance luf-luf abayan ta gwanin ban sha'awa.
Sai k'afarta kuma da take sanye da wani takalmin roba mai matuk'ar kyau mara tudu.
Amma a hakan ba k'aramun kyau tayi ba, domin ko ko za'a tara matan da sukayi kwalliya kafun a samu wacce ta d'auko hanyar kamo ta a kyau sai an yara, saboda ita nata kyawun daga Allah ne.

A duk d'aga k'afar da takeyi tana k'arayo kusanci da shi haka yake jin bugun zuciyar sa na k'ara k'aruwa.
Yayinda har lokacin kuma idanuwansa suke kafe akanta, yana mai kallon yadda iska ke d'an kad'a kayan jikin ta, ga kuma wasu daga cikin silin gashin kanta da suke tashi d'an sama, kana daga k'arshen sa yana juyawa ta yadda har yake haurowa kan cikinta, saboda sassanyar iskar dake kad'awa a cikin wurin.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal kanta durk'ushe a k'asa ta cigaba da tunkaro wurin.

Jin da tayi bugun zuciyar ta na sauyawa ne, ga kuma alamun idanuwa da taji suna yawo akan ta ne, ya sanya ta d'ago kanta tana mai sauke dara-daran fararen idanuwanta masu d'auke da blue black d'in k'waya a cikin na Yarima Asad.

Take kuwa a wurin ta k'ame k'am, ba tare da ta iya cigaba da d'aga k'afafuwan nata ba, yayinda lokaci guda kuma duka yanayin ta ya sauya, ta yadda har launin idanuwanta suka fara canzawa.

Kallon-kallo suka fara jifan junansu da shi daga wurin da ko wannen su yake a tsaye.
Yayinda zuciyoyin su kuma suke wani irin bugu tamkar zasu hudo k'irjinsu su futo waje.

Shi kuwa Yarima Asad wani irin azababben kyau yake gani a jikin yarinyar, hak'ik'a jiya baiga komai bama ashe agunta, domin ko yanzu har wani irin maik'o yake gani kwance a cikin idanuwanta, tamkar wacce ta zuba musu mai.
Lokaci d'aya yaji tsigar jikin sa na wani irin mimmik'ewa, ta yadda har ya fara manta asalin wurin da yake, babu abun da yake gani face ita ako ina nasa.

"Subahanallah! Oh my God!"

Ya fad'a a k'asan lips d'insa ba tare da yasan ya fad'i hakan ba, yana mai cigaba da kallon ta.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal babu abun da take ji sai hutar tsanar sa da take k'ara ruruwa a cikin zuciyar ta.
Wato yau ma kenan wannan d'an iskan mutumin ya sake dawowa cikin gidan su da irin shigar sa ta jiya kenan.
Ta fad'i haka acikin ranta tana mai son ta janye idanuwanta daga cikin nasa, amma gaba d'aya taji ta kasa yin hakan.
Wanda hakan kuma ba k'aramun sake k'ona mata rai yayi ba.

"Shin me yake nufi da ni ce shima?"

Ta sake fad'ar haka acikin zuciyarta, tana mai jin yadda k'irjin ta ke cigaba da bugun tara-tara.

"Gid'od'o am! Gid'ad'o am!!"

Ta fad'a a cikin zuciyarta tana mai rumtse idanuwanta da matuk'ar k'arfi, saboda jin da tayi ta kasa janye su daga cikin na wannan d'an iskan mutumin da yake tsaye a gaban ta.
Take kuwa k'wak'walwarta ta hasko mata fuskar Gid'ad'on ta yana mai jifan ta da kyakkyawan murmushinsa da yake sake tafiya da ita ako da yaushe.
Kafin daga bisani kuma ta bud'e idanuwanta tana mai juyar da kanta gefe.
Kana ta d'an d'aga lab'b'anta tana mai fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakin ta.
Tukun ta d'an kauce daga saitin Yarima Asad, tana mai cigaba da tafiyarta kanta d'age a sama.
Yayinda shi kuma har lokacin yake k'ame a wurin da yake, idanuwansa k'ur akan ta ba tare da ya iya kaucewa ba.

Tamkar bata san da wanzuwar sa a wurin ba tazo ta saitin sa tana shirin hucewa, ba tare da ko kallon inda yake tayi ba.
Hakan da Yarima Asad ya gani ne ya sanya sa lumshe idanuwansa da sauri, kana ya bud'e su yana mai sake zuba su akanta.
Ganin da yayi tana shirin yi masa nisa ne, ya sanya sa mik'a zara-zaran yatsun hannunsa dasauri yana mai cafko nata da su.

Lokaci d'aya sukaji wani irin mugun shok a jikin su, wanda har yayi sanadiyyar amsawar kowace jijiya dake a cikin jikin su, amma duk da haka Yarima Asad bai saki hannun nata ba, saima sake damk'esa da yayi a cikin nasa, yana mai zuba k'wayoyin idanuwansa akan bayanta, tare da sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya.

Yayinda ita kuma Gimbiya Haddiyal ta tsaya cak a wurin da take, tana mai jin wani irin mugun bak'in ciki tare da tsanar sa na yiwa jiki da zuciyar ta bargo.

Da matuk'ar k'arfi ta rumtse idanuwanta, saboda jin yadda ya fara d'an murza tafin hannunta a cikin nasa da tayi.
Lokaci d'aya jikin ta ya d'auki wata irin kyarma, yayinda take jin zuciyar ta na wani irin turiri tamkar zata k'one dan bak'in ciki.
Kafin daga bisani kuma ta bud'e idanuwan nata da gaba d'aya suka juye daga fari zuwa ja, kana ta fara juyawa ahankali-ahankali zuwa b'arin da yake, har ta sauke rinannun idanuwanta a cikin nasa, tana mai jifan sa da wani irin mugun kallo.

Da sauri Yarima Asad ya saki hannunta da yake sark'e a cikin nasa, saboda yadda ya hango asalin wutar tsanar sa a cikin idanuwanta.
Sai dai kuma har lokacin bai iya janye nasa idanuwan daga cikin nata ba, yayinda yake jin zuciyar sa na cigaba da bugawa da matuk'ar k'arfi.

Yayinda ita kuma Gimbiya Haddiyal ta janye idanuwanta daga kansa a hankali, kana ta fara d'aga k'afafuwanta tana mai yin gaba.

Taku d'aya, biyu, ukku tayi kome ta tuna kuma ta tsaya cak a wurin da take, ba tare da tayi gaba ba.
Kana daga bisani ta juyo gaba d'ayan ta b'arin da Yarima Asad yake, tana mai sake zuba idanuwanta a cikin nasa.
Tukun daga bisani ta fara d'ago k'afafuwanta tana mai matsowa zuwa wurin da yake.

Shi kuwa Yarima Asad da sauri ya lumshe idanuwansa, yana mai jin yadda yanayin sa ke k'ara sauyawa, sabo da ganin ta da yayi ta tunkaro sa.

Sai da har tazo dab da shi, ta yadda baifi tazarar taku biyu ya rage a tsakanin su ba tukun taja ta tsaya cak.
Kana ta bud'e bakin ta tana mai fesar da wata irin zazzafar iska daga cikin sa, ta yadda har ta sanya Yarima Asad bud'e idanuwansa akanta, saboda yadda ta daki fuskarsa.
Kana ta d'aga lab'b'anta cikin kakkausar muryar ta da take cike da b'acin rai, tare da gargad'i, tana mai fad'in. "K.............✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*06*



"Kai waye? Me kake tak'ama da shi, da har kake gigin had'a k'azamin jikin ka da nawa?
Shin in tambaye ka man.
A ina kaga tambarin dake nuni da cewar jikin na kowa ne, da har kake gigin kusanta kanka da shi?"

Ta fad'a tana mai sakin wani irn huci, idanuwanta k'ur a cikin nasa.
Yayinda shi kuma Yarima Asad yayi suman tsaye a wurin da yake, yana mai kafeta da lumsassun fararen idanuwansa da gaba d'aya suka fara sauya launi, saboda zafafan kalamanta da suke dukan dodon kunnuwansa.
Babu abun da yafi tsaya masa a rai tare da k'ona masa zuciya, face k'azantar da yaji ta danganta sa da ita.

Shin ashe dama wannan ranar zatazo, ranar da har mace zata iya tsayawa a gaban sa tana jifan sa da mugayen kalamai dan kawai ya d'an rik'e hannunta, macen ma kuma wacce bata kai ba, mace bagidajiya wacce ko sutura bata sani ba sai tasu ta gargajiya, macen da kallo d'aya ya mata ya fahimci batai nisa a cikin ilimin boko ba.
Shi da mata masu aji, kyawu, kud'i da ilimi suke mararin samun ko da kallo ne daga gare sa amma

Please Login or Register in order to submit comment