Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani irin k'arfi zuciyarsa ta harba, ta yadda har bai san lokacin da ya rumtse idanuwansa da k'arfi ba.
Ba kuma shi ya iya bud'e suba har sai da ya jiyo muryar Habu suna gaisawa da Al'amin.

Bud'e murfin gidan baya yayi yana mai zama a ciki tare da rifosa.

"Sannu d'an uwa fatan mun sameku lafiya."
Cewar Yarima Asad yana mai juyawa ya mik'awa Habu hannu.

"Lafiya k'alau wallahi d'an uwa ya hanya."
Habu ya fad'a yana mai basa hannu suka cafke.
Tukun ya d'ora da fad'in.

"Shine kuma kawai sai na nemeka na rasa a waccan ranar, tafiya babu sallama kasa gaba d'aya hankalina ya tashi."

"Murmushin yak'e Yarima Asad yayi yana mai d'an sosa k'eyarsa, tare da cewa.
"Ba zaka gane bane Bro."

"Tom ai shikenan yanzu sai muje daga ciki ko."
Habun ya fad'a yana mai sakin murmushi shima.
Yayinda shi kuma Yarima Asad yayiwa motarsa key, suna masu nufar cikin masarautar.


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFU CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Gaba d'aya yinin yau cir kusan a tsaye Gimbiya Tasmir tayisa, tana mai tinani tare da zagayen d'aki ba tare da ta iya ko sanya abinci a cikinta ba.
Tun bayan tafiyar Hadima Fulaika da kuma Shairama ta kasa samun nutsuwar zuciya, domin kuwa wani irin mugun son had'uwa da Bir ne taji ya mamaye ilahirin zuciya da ruhinta.
Babu yadda batayi ba dan taji ta dena jin hakan, amma gaba d'aya abun ya citira, hakanne ya sanyata yanke hukuncin bin shawarar amintattun nata da suka bata a yau ba sai gobe ba, gudun kar ta zauna tayiwa kanta illa, domin kuwa zuwa yanzu ita kanta ta tabbatarwa kanta da cewar ta kamu da son Bir, soyayya mai tsanani ma kuwa.
So irin wanda take jin muddin babu shi itama babu ita, wato dai bazata iya rayuwa ba ba tare da shi ba, saboda yadda son sa ke k'ara dabai-baye zuciyarta a duk bayan giftawar sakan bayan sakan tun bayan tafiyar Shairama.

Yanzu haka zaune take a gaban dressing mirrow tana shafa hoda akan fuskarta.

Kwalli ta d'auko bayan ta gama shafa hodar ta zizarasa acikin fararen idanuwanta, tukun ta d'auki man leb'e tana mai shafasa akan jajayen kyawawan lab'b'an ta.
Kana ta mik'e tsaye tana mai nufar gaban wardrobe d'in ta.
Gaba d'aya tana komai ne cikin sanyi, domin kuwa bata san irin kallon da zai mata ba bayan ta gama shaida masa abun da take da niyyar yi.

Wata blue'n doguwar riga mai azabar kyau da adon duwatsu a jikinta ta sanya a jikin ta.
Tukun ta juya tana mai tafiya wurin da takalmanta suke ta d'auki wani plat, shima blue color mai d'auke da adon gashi a jikin sa ta sanya su.
Tukun ta k'ara komawa gaban madubi, tana mai d'aukar turare mai sanyin k'amshi ta feshe ilahirin jikin ta da shi.
Kana ta juya tana mai nufar wata hanya da zata futar da ita bayan gidan su ba tare da tabi ta babban falo ba, domin kuwa ko kad'an bata fatan wani ya ganta, ballantana har ya tambayeta wurin da zata da yammar nan.

Tafe take jiki a sab'ule tana mai tinanin yadda zatayi ta had'u da shi, domin kuwa bata son kowa ya fahimci abun da yake damunta, ban da haka da sanyawa zatayi a kira mata shi kai tsaye, to sai dai kuma yin hakan tana jin tamkar zai iya sanyawa mutane su fara tinanin wani abun.
Hakan yasa ta doshi hanyar wurin data san sunyi waccan had'uwar ta k'arshe da shi, tana mai fatan Ubangiji yasa ta gansa anan d'in, domin kuwa ji take tamkar bazata kwana da rai ba muddin bata samu ta futar da abun da ke cikinta ba a garesa.
Sosai take muradin arba da kyakkyawar fuskarsa, tare da sassanyan murmushin sa, domin kuwa tun a waccan ranar da yayi mata shi a lokacin da zai tafi ya tsaya mata acikin rai.
Hak'ik'a shi d'in mai kyau ne ajin farko, wanda bata tab'a sanin da hakan ba sai a waccan ranar, ta yadda har yanzu take ganin tamkar babu wanda ya kaisa kyawu a duk fad'in duniyar nan.

Tinane-tinanen da take ne ya sanya ko kad'an ba taga nisan wurin ba, duk da kasancewarsa mai nisan kuwa tsakanin sa da b'angaren su har ta iso.
Hakanne ya sanya ta fara waige-waige a cikin filin, domin taga ta inda zata hangosa, sai dai kuma har ta d'auki tsayin mintina biyar tana faman kalle-kalle bataga ko gilmawar dabba ba balle kuma mutum.
Sosai kuwa taji zuciyarta tai mata ba dad'i, ta yadda har take jin tamkar ta d'ora hannu aka taita tsala uban kuka, ko ta rage jin takaicin rashin ganinsa da batayi ba acikin ranta

Da farko k'in tafiya tayi tana mai samun jikin wata bishiya ta jingina da ita, domin kuwa tana zaton zai iya zuwa wurin ako da yaushe, amma a k'arshe kuma data ga har ta shafe sama da mintina talatin a wurin babu shi babu alamunsa, ga kuma gari daya fara duhu alamun dare ya sanyo kai, ya sanya ta hak'ura tana mai fara d'aga k'afafuwanta cikin tsantsar bak'in ciki da takaici ta doshi hanyar data futo.

Tana shirin barin cikin wurin gaba d'aya taji zuciyarta tayi wani irin harbawa da matuk'ar k'arfi.
Hakanne ya sanyata tsayawa cak a wurin da take, tana mai rumtse idanuwanta da k'arfi.
Kana daga bisani ta bud'e su tana mai fesar da iska, tare da fara juyawa zuwa bayanta.

Karaf kuwa idanuwansu suka sark'e cikin na juna.
Wasu irin tagwayen ajiyar zuciya ta fara saukewa, tana mai jin wani irin farinciki na lullub'e ilahirin jiki da zuciyarta.
Wani irin mugun kyau taga yayi mata acikin idanuwanta, duk da kuwa ba kwalliyace ke d'auke a jikin sa ba.
Sanye yake da farin wargegen farin wando a jikin sa ba riga.
Yayinda hannunsa daya yake rik'e da wani d'an k'armin buhu, sai kwari da gwafarsa da kuma take mak'ale a hammatarsa, da alamun dai daga farauta ya dawo.

A hankali ta fara d'aga k'afafuwanta tana mai nufar wurin da yake, ba tare da ta iya janye idanuwanta ba daga cikin nasa.
Yayinda zuciyarta kuma ke cigaba da harbawa da tsananin karfi, tana mai bada wani irin sauti dip-dip-dip.

Shi kuwa Bir ko kad'an baiyi tsammanin ganinta a wurin ba, sai dai kuma da b'ullowarsa wurin yaji zuciyarsa tayi wata irin harbawa, hakanne ya sanya sa d'aga kansa yana mai kai idanuwansa zuwa kan hanyar, wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da itama Gimbiya Tasmir ta juyo, gaba d'aya idanuwansu suka sark'e cikin na juna.
Sosai kuwa yaji wani irin farinciki mara misaltuwa yayiwa zuciyarsa k'awanya.
Sai dai kuma ko kad'an bai bari ya bayyana akan fuskarsa ba, saboda rashin sanin abun da ya kawo ta wurin da bai yi ba.

Ba ita ta tsaya ba har sai da ta k'arasa dab da shi.
Tukun taja ta tsaya cak suna masu lumshe idanuwansu a lokaci guda.
Yayinda zuciyoyinsu kuma suka cigaba da harbawa a tare.
Lokaci d'aya Gimbiya Tasmir taji duk abubuwan da suka faru a tsakaninta da shi sun dawo mata a cikin rai.
Take kuwa taji wani irin nauyinsa tare da kunyarsa sun lullub'e zuciya da ruhinta, ta yadda har tak'asa bud'e k'wayoyin idanuwanta data lumshe, ballantana har ta sanar masa da abun da tazo da niyyar sanar masan.
Domin kuwa bata son da wani ido zata kallesa ta furta masa abun da yake a cikin zuciyarta ba, bayan duk irin hulak'antasan da tayi a baya.

Shi kuwa Bir a hankali, kana kuma cikin sanyi ya wara idanuwansa akan kyakkyawar fuskarta.
K'ur ya kafe fuskarta da idanuwa, yana mai yaba kyawun hallitarta a zuciyar sa.
Hak'ik'a Gimbiya nada kyawu, irin kyawun da kafun asamu mai irin sa sai an bincika acikin mata.

Komai nata yayi, tamkar ita ta zauna ta tsara kanta.

Wani irin shauk'i yaji yana lullub'e ilahirin jiki da zuciyarsa, ta yadda har yake jin gaba d'aya yanayin sa na sauyawa, yayinda tsigar jikin sa kuma take d'an mimmik'ewa.

A hankali ya fara rak'wafawa, yana mai rage tsayinsa, ya dawo da shi dai-dai saitinta.
Tukun ya fara matsar da fuskarsa zuwa dab da tata, yana mai jin wani irin abu na fuzgarsa zuwa kan kyawawan jajayen lips d'in ta, da suke futar da k'yallin man leb'en data shafa musu.
Da sauri Gimbiya Tasmir tayi wani irin bud'e idanuwanta, saboda jin saukar numfashinsa da tayi akan fuskarta.
Ai ko take idanuwansa da nata suka sark'e a cikin na juna, yana mai dab da had'e tsinin hancinsa da nata.
Ganin hakan da Gimbiya Tasmir tayi ne, ya sanya ta jin tsigar jikin ta na bada wani irin yass!
Tukun ta mayar da idanuwanta tana mai sake kullesu da k'arfi, jikin ta na d'an rawa, ba tare da tayi k'ok'arin hanasa abun da taga yana shirin aikatawa ba.
Shi kuwa Bir hakan daya gani ne, ya sanya sa y................


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*13*



Ya saki wani irin murmushin da bai san lokacin daya tawo masa bama.
Kana daga bisani ya janye fuskarsa daga saitin tata yana mai mik'ewa tsaye, tare da zuba idanuwansa akan fuskarta har lokacin yana sakin murmushi, yace.

"Kai ashe 'Yammatan tawa dai matsoraciyace ban sani ba."

Wata irin kunya ce wacce bata san tana da ita ba ko kad'an a rayuwa taji tai mata saukar ungulu da jin furucin da yayi.
Yayinda a k'asan zuciyarta kuma take jin wani irin nishad'i irin wanda bata tab'a sanin da shi ba a rayuwa yana taso mata.

A hankali, kana kuma cikin sanyi ta bud'e idanuwan nata, tana mai d'ora su akan kyakkyawar fuskarsa.

Ido hud'u suka sakeyi da shi, yana jifan ta da kyakkayawn murmushinsa da yake matuk'ar birgeta.
Kafin daga bisani kuma ta sunkuyar da kan nata k'asa, tana mai fesar da numfashi.
Saboda haka nan kawai yau taji bazata iya jurar kallon cikin k'wayar idanuwansa ba, tamkar yadda ta saba a koda yaushe.
Ita da kanta mamakin yadda ba taji haushin abun da yayi mata ba a yanzu take yi a cikin ranta, asalima sai wani irin nishad'i ne taji ya lullub'e ta.

Shi kuwa Bir ganin hakan da yayi ne ya sanya lumshe idanuwansa, tukun daga bisani ya sake bud'e su akan fuskarta da take duk'e a k'asa, tana wasa da 'yan yastun hannunta yana mai fesar da iska.

Jin da yayi har yanzu tak'i tace komai ne, ga kuma alamun ta daya gani tamkar tana son yin magana, ya sanya sa k'ara gyara tsayuwarsa, yana mai k'ara fuskantarta.
Tukun ya bud'e baki cikin wani irin sauti mai tsananin taushi, yana mai fad'in.

"Da alamu dai Gimbiyar tawa ta fahimci abun da na dad'e ina muradin ta fahimta yanzu."

Ya k'arasa maganar yana mai d'an sake matsowa kusa da wurin da take.

Lumshe idanuwa Gimbiya Tasmir tayi, tana mai jin saukar furucinsa a cikin kunnuwanta tamkar sautin busar sarewa.
Amma sai dai kuma gaba d'aya nauyinsa da take ji ya hanata ta d'ago ta kallesa, ballantana kuma har ta furta masa abun da tazo da niyyar ta fad'an.

Fahimtar hakan da Bir yayi ne ya sanya sa sake bud'e baki, yana mai fad'in.

"Alamu da yawa sun nuna kina son fad'ar wani abu, amma kuma kina jin nauyin furtasa.
Ina so ki sani, Bir bai tab'a rik'onki a cikin zuciyarsa ba, ban tab'a d'aukar abun da kike yi mun ba a matsayin zalinci, asalima sai farinciki da yake sanyani, wanda hakan kuma shi ne ya sanya a kowane lokaci nake kai kaina wurin da kike, duk da sanin irin abun da zan had'u da shi da nayi.
Ban tab'a jin haushinki ba, asalima kome kikayi birgeni kikeyi, saboda ina miki sone irin wanda bazai misaltu ba, ita kuma zuciya ako da yaushe bata tab'a ganin laifin wanda take bege.
Ki cire nauyi, ki ajiye kunya a gefe, ki fad'i duk wani abun da yake a cikin ranki, domin kuwa Bir Jarumin iya naki ne."

Ya k'arasa maganar da busa mata iskar bakinsa akan fuskarta.
Yayinda ita kuma ta sake lumshe idanuwanta, tana mai jin wani irin farinciki mara misaltuwa na lullub'e zuciya da ruhinta, gaba d'aya bak'in cikin da yake dank'are a cikin zuciyarta na yayewa.

A hankali ta bud'e baki cikin sanyi murya ba tare da ta d'ago ta kallesa ba, tana mai fad'in.

"Kayi hak'uri."

"Hak'uri kuma, da aka yi me kenan?"
Shima Bir ya fad'a yana kallon zara-zaran yatsun hannuwanta da take wasa da su.

"Da abubuwan da suka faru a baya, hak'ik'a a yanzu na fahimci abun da kafad'a mun, zuciya ta aminta da cewar kai d'inne ita, wato idan babu kai, tabbas komai yana iya faruwa da ita."

Tayi furucin cikin wata irin murya, wacce ko kad'an Bir bai san tana da kalarta ba.

Wani irin farincikine yaji ya lullub'e ilahirin zuwaciya da ruhin sa, jin abun yake tamkar al'mara, jinsa yake tamkar *MU'UJIZA!* wai yau shi Bir ne Gimbiya Tasmir dako ganinsa bata son tayi, take tsaye a gabansa tana fad'a masa kalaman da suka kasance masu daraja da tsada a matsayinsa na k'ask'antaccen bawanta.
Hakan ko shine ya sanya sa bud'e baki cikin wani irin sauti mai matuk'ar sanyi da saukar da kasala, yana mai fad'in.

"Shin me kike nufi da hakan, kina nufin kice mun kema kina sona, kina sona tamkar yadda nake sanki, kin yadda kiyi rayuwa da k'ask'antaccen Bawan ki a matsayin masoyinki na har abada?"

Ya watso mata tambayar yana mai sake zuba idanuwansa a cikin nata.

Lumshe idanuwa Gimbiya Tasmir tayi, tana mai jin yadda zuciyarta ke cigaba da harbawa, kafin daga bisani kuma ta jin-jina masa kai alamar eh, ba tare data iya d'ago kai ta kallesa ba.
Hakan da Bir ya ganine ya sanya sa fad'in.

"Ki d'ago idanuwanki ki kalle ni, dago idanuwanki ki zubasu acikin nawa tamkar yadda kika sabayi abaya, d'ago idanunki ki bud'e bakinki ki amsa mun tambayata.
Shin da gaske ne kin zab'i k'ask'antaccen Bawanki amatsayin abokin rayuwa?"

Lumshe idanuwa Gimbiya Tasmir tayi tana mai jin tsigar jikinta na cigaba da tashi, kafin daga bisani kuma ta bud'e su tana mai d'ago kanta ta sanya idanuwanta cikin nasa tamkar yadda ya buk'ata, tukun ta d'aga lab'b'anta a hankali, tana mai fad'in.

"Kai ba k'ask'antacce bane ba, mutum ne tamkar kowa, mutum mai daraja da k'ima a idanuwana da cikin zuciyata.
Kai d'in ka zamto mutum na dabanne a wurina, kai d'in ka kasance gwarzo kuma Jarumi a wurina.
Kai ne mutum na farko da kafara b'atamun rai a duniya, kai ne mutum na farko daka fara sanya ni yawan magana a duniya, kai ne mutum na farko da ka iya kallon cikin idanuwana kayi mun magana ba tare da tsoro ko fargaba ba a cikin Bayi, kana kuma kaine mutum na farko da ka fara sanyani zubar da hawaye.
Hak'ik'a naci wuya, nayi kuka, na kasa bacci da cin abinci duk a silar ka, gashi kuma yanzu ina jinka tamkar yadda nake jin raina a zuciyata.
Hak'ik'a ina sonka, sanka so mai tsananin Jarumi!"

Ta k'arasa maganar cikin wani irin sauti, tana mai durk'usar da kanta k'asa.
Yayinda Bir kuma yaji wani irin farinciki irin wanda bai tab'a tsintar kansa ba a rayuwa.
Hak'ik'a yau ya yadda shi d'in mai sa'a ne tamkar yadda Iya tasha fad'a masa.
Wai yau shi Bir ne Gimbiya Tasmir ta kira da Jaruminta, tabbas yana jin al'amrin tamkar a mafarki.
Hakanne yasa sa d'ago tafin hannunsa yana mai kaisa kan idanuwansa ya murza su.
Kana ya sake bud'e su akan fuskar Gimbiya Tasmir yana mai fad'in.

"Shin mafarki nake ko ko zahiri ne, hak'ik'a idan mafarki ne ina fatan na dawwama a cikinsa har k'arshen rayuwata ba tare dana farka ba."

Ya fad'a cikin wani irin yanayi yana mai murza lallausar sumar kansa da yastun sa.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir murmushin da bata san lokacin daya tawo mata ba ta saki, tana mai kallon sa, saboda yadda taga yana ta faman muzurai.
Tabbas Bir ya had'u iyakar had'uwa, ya had'a duk wani abu da mace take burin namiji ya kasance da shi a ajikin sa.
Hakan data ganine ya sanya ta sake d'aga k'afafuwanta tana mai matsawa kusa da shi.
Tukun ta d'aga tafukan hannayenta tana mai shafar gefen fuskarta da su.
Kana ta bud'e baki tana mai cewa.

"Ba mafarki kake ba a zahiri ne, hak'ik'a Iya batayi laifi ba data kira ka da Jarumi, domin kuwa bayan jarumi kai d'in Gwarzo ne ma.
Ina sonka da zuciya d'aya Jarumi, fatana shine kasoni karka hulak'anta ni, kar kuma kadinga tunawa da abubuwan da nayi maka abaya har gaban abada."

Wani irin matsanancin farincikine ya lullub'e ilahirin jiki da zuciyar Bir, ta yadda har bai san lokacin daya fara d'aga k'afafuwansa ba, yana mai k'ara kusanta kansa da ita, sai ganin sa kawai da yayi tsaye a gabanta.
Yayinda idanuwansa kuma suka kasance k'ur akan fuskar ta.

Itama Gimbiya Tasmir idanuwanta ta zuba masa tana mai kallon cikin idanuwansa.
Kusancin da sukayi da junan su sosai ne ya sanya musu jin sauyin yanayi gaba d'ayan su.
Yayinda zuciyoyin su kuma suka kasance suna bugawa a tare.
Cikin wani irin yanayi na shauk'in da suke jin yana d'ibar su, Bir ya fara durk'usar da kansa a hankali, yana mai kai fuskarsa saitin tata.

Ido cikon ido suka cigaba da kallon junan su, yayinda tsigar jikinsu kuma gaba d'aya take mik'ewa.
A hankali Bir ya k'ara matsar da fuskarsa zuwa gaban tata, ta yadda har tsinin hancinta da nasa suka had'e wuri d'aya.
'Dan jujjuya fuska Bir ya farayi yana mai goga tsinin hancinsa akan nata.

Da sauri Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwanta, saboda ganin da tayi yana shirin had'e lab'b'an sa da nata, wanda hakan ya sanya taji wata irin kunya ta lullub'e ta.

A hankali Bir ya zaro harshensa, yana mai d'orasa akan lips d'in Gimbiya, ya fara d'an gogasa.
Wani irin yanayi gaba d'ayan su suka tsinci kansu a ciki irin wanda basu taba jinsa ba.
Kafin daga bisani kuma jikin Gimbiya Tasmir ya d'auki karkarwa, ta yadda har ta fara shirin fad'uwa a k'asa.

Ganin hakan da Bir yayi ne, ya sanyasa d'ora hannunsa d'aya akan k'ugunta yana mai dafe sa, kana ya sanya d'ayan kuma akan gadon bayanta ta k'ark'ashin mayawaicin gashin kanta daya zubo.
Tukun a hankali ya k'ara janyota zuwa cikin jikin sa, yana mai janye fuskarsa daga kan tata.

Ba zato ba tsammani kuwa Gimbiya Tasmir taji ta kwance akan faffad'an k'irjin sa.
Yayinda shi kuma ya d'auke hannunsa da yake akan k'ugunta, yana mai had'esa da na bayanta, yayi mata rumfa a cikin k'irjin nasa.

Lokaci d'aya kuwa suka fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya.
Yayinda Gimbiya Tasmir kuma ta sake kwanciya a jikin sa, tana mai jin yadda d'umin fatarta ke ratsa cikin jikin ta.
Sake mayar da idanuwanta tayi ta lumshe, tana mai cigaba da sauke numfashi, ji take inama ace su dawamma a haka.
Hak'ik'a da taso ta cutar da kanta da kanta ba tare data sani ba, domin kuwa yanzu a 'yar tsayuwar da sukayi, ta gama tabbatarwa da kanta cewar bazata tab'a iya rayuwa ba muddin babu shi a duniyarta.

Sun jima a haka, kafin daga bisani kuma Bir ya sanya hannuwansa biyo yana mai cirota daga cikin jikinsa, saboda ganin yadda gari yayi duhu sosai ba tare da sun sani ba.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir a hankali ta bud'e idanuwanta tana mai sauke numfarfashi, kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci yadda jikin ta yake a sanyaye, yayinda idanuwanta kuma suka kasance akan fuskar Bir.

A hankali Bir ya kawo yatsar sa yana mai lakutar hancinta da ita, kana ya bud'e bakinsa cikin wata irin murya mai tattare da tarin shauk'i a cikinta, yana mai fad'in.

"Ya da kallo haka 'Yammatan Bir."

Murmushi ne ya sub'uce mata, ta yadda har sai da dimple d'in ta ya lob'a, tukun ta sauke kanta k'asa tama mai wasa da yatsun hannunta.

Shi kuwa Bir idanuwansa ya d'aga sama, yana mai kallon yadda duk taurari suka bayyana, kana daga bisani ya sauke su yana mai fad'in.

"Ya kamata mutafi yanzu in rakaki hanya, kinga dare yayi ko."
Ya fad'a yana mai kallon ta.

Lokaci d'aya kuwa yanayin fuskarta ya sauya, walwalar da take akanta ta d'an ragu, domin kuwa ji take ba tak'i su dawwama a haka ba yadda suke, gaba d'aya tama manta da yau itace ranar su ta farko a tare.
Lura da hakan da Bir yayine ya sanyasa sakin murmushi, yana mai kai hannunsa ya rik'o nata hannun da shi, tukun suka fara tafiya a tare ba tare da yace mata komai ba.


Sai da har yakai ta kusa da b'angarensu, ta b'angaren wurin da k'ofar nan ta baya take, wacce ta futo ta ita, tukun Bir yaja ya tsaya a wurin, yana mai kallon cikin idanuwanta, tamkar yadda itama take kallon na-sa.
Kafin daga bisani kuma ya rage tsayin sa, yana mai had'e fuskarsa da tata.

Wata irin sumba ya sakar mata akan jajayen lab'b'an ta, tukun ya d'ago yana mai sakar mata murmushi.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ki kwana lafiya sarauniyar kyawawa, kiyi bacci mai dad'i, mai cike da mafarkan Jaruminki, ban da tinanin da kika san zai wahalar min da zuciyarki Gimbiyata."

Ya k'arasa maganar yana mai yi mata bye-bye, tare da juyawa ya tafi fuskarsa d'auke da murmushi.

Da idanu Gimbiya Tasmir tabi bayan sa, tana mai jin wata irin kewarsa na lullub'e ta, tamkar ada tare suke da shi ako da yaushe.
Ba ita ta iya janye idanuwanta daga kansa ba har sai da ta dena hangensa.
Tukun ta fesar da wata irin sassanyar iska, tana mai sakin murmushin da bata san lokacin daya tawo mata ba.
Yayinda idanuwanta kuma suke cigaba da hasko mata fuskarsa a lokacin da ya sumbaceta kafin ya tafi.

Cikin kasalar da salonsa ya saukar mata a jiki ta juya a hankali tana mai nufar d'akin ta zuciyar ta fes, ta yadda har take jin tamkar ba ita bace ta gama kuka tare da jin zafin zuciya ba a d'azu da safe.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*

Kai tsaye Al'amin ya doshi wannan lambun da Habu ya sauke su a ranar da sukazo siyan shanu.
Hakan da Habu ya ganine ya sanya sa fad'in.

"A'a Malam ina kuma kake shirin kaimu ne wai?"

"Kasan Allah, yau ba zaka kaimu ka kume mu acikin d'akin ka ba, bayan kuma ga wurin da ke sanyaya zuciya can mun san da shi, dan haka can zamuje kamar yadda ka kaimu a ranar farko."

Al'amin ya fad'a yana mai hararar Habu ta cikin glass d'in da yake haska masa kujerar baya.

"Ashe dai ba iya d'an uwa bane masifaffan da kace, masifaffun kuna da yawa dai, idan ba haka ba kuma daga 'yar magana sai dogon sharhi, to ni ajiye ni anan malam zan huce cikin gida, inyaso na biyoku can d'in daga baya."

Cewar Habu yana mai hararar Al'amin shima.

"Anji d'in ba komai."

Al'amin ya fad'a yana mai tsayawa a wurin, tukun Habu ya bud'e murfin motar yana mai fucewa tare da fad'in.

"Tom sai na k'asaro ko."

"Okay muna jira fa kasani ko."

Al'amin ya fad'a yana mai cigaba da tunkarar lambun da yayi matuk'ar birge sa tun a zuwan su na farko.
Shi kuwa Yarima Asad lumshe idanuwansa yayi, yana mai jin yadda zuciyarsa ke harbawa da sauri da sauri.

A bakin lambun Al'amin ya tsayar da motar, kasancewar babu hanyar shiga da mota cikinsa, domin kuwa 'yar k'aramar k'oface aka yanka ajikin wayar da tayi masa k'awanya, wacce ta itan ce kuma mutane suke shiga ciki.

Bud'e murafan motocin sukayi suna masu futowa waje.

Da k'arfi Yarima Asad ya rumtse idanuwansa, saboda jin da yayi zuciyarsa tayi wata irin muguwar harbawa fiye da da.

"Muje ko."

Yaji Al'amin na fad'a, hakanne ya sanyasa bud'e idanuwan nasa, yana mai fara d'aga kafafuwansa cikin sanyin jiki, suka doshi k'ofar.

Cak Yarima Asad ya tsaya yana mai jin bugun zuciyarsa na k'aruwa, saboda idanuwansa da suka hango masa matashin saurayin da zaiyi sa'a da shi kishingid'e akan tum-tum, jikin sa sanye da kayan sarauta irin na Fulani.

A kuma dai-dai lokacin shima Jauron Yamma da yake jiran isowar Gimbiya Haddiyal idanuwansa suka sauka akan fuskar Yarima Asad.

Take kuwa zuciyoyinsu suka buga a tare da matuk'ar k'arfi.
Kana ko wanne ya kafe d'an uwansa da kallo, suna masu jin wani irin abu na tsarga musu a zuciyoyin su mara dad'i.

Lokaci d'aya gaba d'aya d'an guntun annurin fuskar su ya d'auke, ba tare da su kansu sun san dalilin daya sanya su jin hakan ba.

Ganin da Al'amin yayi Yarima Asad ya tsaya ne, ya sanya juyawa baya kasancewar shi har ya huce sa yana mai fad'in.

"Ya dai d'an Uwa, lafiya ka tsaya anan ne kuma?"

Ganin da Al'amin yayi ko kallon sa Asad baiyi ba, ya sanya sa kai idanuwansa zuwa wurin da yaga Yarima Asad d'in na kallo.
Aiko shima yana kai idanuwan nasa hurin suka sauka akan

Please Login or Register in order to submit comment