Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wandinan jieans.
Sai white t.shir mai tsananin kyau da aka rubuta HAPPY BIRTHDAY PRINCE ASAD.
Da gwaro-gwaron rubutu a bayanta, daga gabanta kuwa Cutcee by Billy Abubakar Sardauna.
Aka rubuta sa da k'ananan bak'i, kana kuma 'yan k'anana da rubutun ya k'ara k'ayata rigar.
Sai facing cap itama daga gabanta an buga Happy birthday Prince Asad, yayinda a gefe wuri d'aya kuma akasa Cutcee Mrs Asad Billy Sardauna.
Kasancewar takalman k'afarsu suma bak'ak'ene kuma duk iri d'aya, shiyasa shigar tasu tayi masifar kyau, sannan kuma suma sukayi matuk'ar kyau.
Kallo d'aya zaka musu kasan nera ta jik'asu gaba d'ayansu, sabo da fatarsu da ta nuna hakan.

Ita kuwa Billy Zaune take akan kujera, wata matashiyar budurwa na tsala mata make up mai tsananin kyau akan fuska.
Sasai tayi masifar kyau yadda kasan aljana acikin kwalliyar tata.
Tukun bayan angama ta d'auki rapper ta dubu d'aya har guda biyu ta damk'awa mai kwalliyar, wato dubu d'ari biyu kenan.

Cikin matuk'ar farinciki mai kwalliyar tasa hannu ta amsa tana ami fad'in.
"Allah ya nuna mana ranar bikin nan akusa."
Kana tayi gaba abunta ranta wasai.
Ita kuwa Billy mik'ewa tsaye tayi, tana mai zuwa ta fara sanya kayanta data zaro.

Blue crazy jeans d'in da yayi matuk'ar kama jikinta tamkar da shi aka halliceta ta tsanya.
Kasancewar a yage yake daga kan cinyarta, shiyasa kuma fararen cinyoyinta suka bayyana ake ganin su.
Yayinda tsayinsa kuma ya tsaya mata a iyakar k'auri.
Daga k'asansa kuwa wata 'yar bezace a jikinsa.
Atak'aice dai iyakar had'uwa wandon ya had'u.
Wata mayyar had'ad'd'iyar red white t.shir mai tsananin kyau da uban adon bluen duwatsu daga gabanta ta sanya a jikinta.

Yayinda daga bayan rigar kuma aka rubuta Mrs Prince Asad a jikinta.
Tsayawa fad'ar irin kyawun da Billy tayima a yau b'ata lokacine, domin kuwa iyakar had'uwa ta had'u, cikin shigarta ta data bayyana hallitar jikinta tas.

'Yar k'aramr jar jaka mai bluen ado a jikinta tare da wani irin mahukacin hill shoe na mahad'in jakar ta sanya a k'afarta.
Kana kuma ba tare data d'aura d'ankwali ba ko kuma tasa hula akanta ta d'auki key d'in motarta, suna masu fucewa daga cikin d'akin ita da k'awayenta.
Yayinda hannuwan k'awayen nata kuma suke rik'e da gift d'in data tanadarwa Yarima Asad su.
Suna tafiya suna fasa mata kai tare da kod'a irin kyawun da tayi, ahaka har suka k'arasa cikin wata azababbiyar k'atuwar mota.
Tukun suka mata key suna masu fucewa daga cikin gidan.

Acan b'angarensu Yarima Asad kuwa, tsaye yake agaban wardrobe d'insa, yana mai duba kayan daya kamata ya sanya.
Yayinda Al'amin kuma yake zaune agefe cikin shiga irin wacce k'awayen Billy sukayi.
Wato bak'in wando jieans tare da farar t.shir, da kuma facing cap da suke d'auke da rubutu ajikin su.
Kuma gaba d'aya Billy ce tayi ordasu, kana ta rabawa mutanenta, sannan ta bawa Al'amin har kusan set hamsin tace ya bawa duk wa'yan da za su zo wurin su sanya.

Shi kuwa Yarima Asad bluen crazy jiean mai tsananin kyau da mutuk'ar tsada ya zaro daga ciki.
Kana ya d'auko white t.shit long slive mai tsananin haske da santsi.

Cikin k'ank'anin lokaci ya gama shiryawa, sabo da yadda Al'amin keta faman azal-zalarsa akan suyi sauri.
Blue boot mai mugun kyau ya sanya a k'afarsa.
Kana yabi ko ina na jikinsa da had'ad'd'en turarensa mai sanyin k'amshi da tsayawa a zuciya.
Tukun a k'arshe ya d'ora wata bule d'in had'ad'd'iyar jaket mai jikin jiens asaman farar rigar.
Ya subahanallah, irin fad'ar kyawun da Yariam Asad yayi a yau d'in b'ata lokacine.
Domin kuwa sumar kansa ma kawai da ta had'e da kwantaccen sajensa da suke futar da k'yalli ma kad'ai abun kallo ne.
Wani irin aski ne da aka kwashe gefe da gefe tare da tsaga akansa, ya masa kyau iyakar kyawu.

A tare suka jera shida Al'amin suna masu fucewa daga cikin d'akin.

Acan Asadullah Palace kuwa sosai wurin ya tsaru yayi kuma matuk'ar had'uwa.
Wani irin cool music ne mai sanyin dad'i yake tashi a cikin wurin.
Yayinda jama'a kuma 'yan gayu suke zazzaune akan kujeru, kusan gaba d'ayansu sanye da irin shigar da k'awayen Billy sukayi mazansu da matansu.

Yayinda 'yammatan cikin masarautar wasai kuma suke sanye da wata had'ad'd'iyar atamfa super holand d'inkin dogayen riguna fitet a jikinsu, kasancewar su haka sukace ba zasu sa kayan Billy ba, suma nasu ankon zasuyi.
Wannan dalilin ya sanya ankon ya rabu kala biyu a wurin, dana atamfa da kuma na k'ananan kaya.
Amma gaba d'aya maza da sauran mata abokansu Yarima Asad duk kayan Billy suka sanya.

Koda su Billy suka k'araso wurin sosai aka dinga binta da idanuwa duk inda ta gifta.
Direct ta hucewarta zuwa cikin d'an plat d'in nan na Yarima Asad.
Yayinda k'awayenta kuma suka samu wuri suka zauna anan filin.
Wanda shigarta ta kuma ba k'aramun k'onawa su fa'iza da sauran duk masoyansa na cikin masarauta rai yayi ba, ta yadda har sukejin tamkar suje su futo da ita suyi mara d'an iskan duka a gaban jama'a.
Gaba d'ayan su suma akwai abubuwan da suka tanada wa'yan da sukesa ran zasu samu nasarar janyo hankalin Yarima Asad zuwa garesu da su.

Sosai fa wuri ya had'u, kusan kowa ya zauna yanzu zuwan Yarima Asad kawai ake jira.

Misalin k'arfe hud'u da minti goma shabiyar dai-dai motarsu Yarima Asad da Al'amin ke tuk'ota ta danno kanta cikin wurin.
Take kuwa gaba d'aya idanuwa sukayo kansu, kowa burinsa yaga futowarsu.

Al'amin ne ya fara futowa, kafin daga bisani kuma Yarima Asad ya zuro k'afafuwansa waje.
Kana daga baya ya sanyo duka gangar jikin nasa waje.

Take kuwa wurin ya d'auki sowa da tafi da matuk'ar k'arfi.
Yayinda MC kuma ya kashe kid'an dake tashi yana mai fad'in.

"Masha Allah! Ga mai gayya mai aiki nan wanda kowa ke zaman jiran isowarsa ya k'araso yanzu, dan haka ina son abasa hannu guys."

Yayi maganar cikin harshen turanci.
Take kuwa kakejin raf-raf-raf na tashi a wurin.
Yayinda shi kuma Yarima Asad da Al'amin suka huce zuwa wurin.
Direct ya doshi wurin da aka tanadar masa dan zama, daya futa daban da sauran.
Yana tafiya yana mai d'agawa jama'ar da sukazo wurin hannu tare da sakin murmushi.
Lokacin da idanuwansa suka sauka akansu Suhaib abokansu na dubai kuwa, kasa hucewa mazaunin nasa yayi, sai da har ya k'arasa wurin da suke suka gaisa cikin tsantsar farinciki.
Kana ya dawo yana mai hucewa mazauninsa.
Tukun mc ya k'ara d'aukar mic d'in yana mai fad'in.

"To masha Allah ga dai Prince Asad nan ya k'araso, dan haka yanzu muna buk'atar ganin Mrs Prince Asad a wurin nan, ta k'araso a yanka cake.
Wato, Billy Abubakar Sardauna!"

Wuuuuuuu!!!

Wurin gaba d'aya ya d'auki sowa da tafi cikin matuk'ar farinciki.
Yayinda su Baby, Fa'iza da kuma sauran makusantan Asad duk suma suka mik'e suna masu tafiya wurin da kujerarsa take.

Ita kuwa Billiy jin abunda Mc ke fad'e daga cikin falon da take a zaune, ya sanya ta mik'ewa tsaye cikin tsantsar farinciki.
Kana ta d'auki wasu irin had'ad'd'un kwalayen da suke cike da gift d'in ban mamakin data siyo zata bawa Asad a cikinsu.
Sannan ta fara takawa cikin wani irin taku tana mai fucewa daga wurin.

Shi kuwa Mc kasancewar sun riga sun gama tattaunawa da Billy, shiyasa tana futowa ya canza sauti, yana mai sanya wakar Complete me ta Simi.

Habawa take gaba d'aya idanuwan jama'ar dake wurin ya dawo kan Billy, data futo cikin wani irin taku tana mai dosowa wurin.
Yayinda kid'an da aka sanya kuma yayi matuk'ar hawa da yanayin wurin.
Shi kansa Yarima Asad idanuwa ya zuba mata yana kallonta, wanda hakan kuma ya sanya Billy da take kallon cikin k'wayar idanuwansa ranta yayi matuk'ar haske.

Cikin wani irin sanyin dad'i mai ratsa zuciya muryar mawak'iyar take tashi.
Yayinda idanuwan Yarima Asad kuma har yanzu suke akan Billy da ke tunkarosa, yana mai jin tamkar itace ke fad'en baitikan da mawak'iyar take fad'i, barin ma da aka zo wurin da take cewa.

_No one complet me! No one complete me more than you!
If i no get you._
_It's like the sun without the light_
_It's like the moon without night_
_Cause i need you in my life ohohooo._
_If i no get you... It's like the faith without believe, like a heart without beat_
_What a heart without a beat?_

Sosai Billy taji wani irin mugun shauk'i tare da farinciki na d'ibarta.
Shi kuwa Yarima Asad tamkar ance ya d'aga kansa ya kalli hanyar shigowa, ya samu kansa da d'aga kannasa tare da kai idanuwansa kan hanyar.

Zumbur kuwa ya mik'e tsaye daga zaunen da yake, zuciyarsa na wani irin harbawa da matuk'ar k'arfi.
Kana ya rumtse idanuwansa da k'arfi, jikin sa na d'aukar kyarma.
Yayinda zuciyarsa kuma yake jin tamkar zata fad'o k'asa d'an tsananin bugun da take, sabo da h..............✍
*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*18*



Hangowar shigowar Gimbiya Haddiyal cikin wurin da yayi, fuskarta d'auke da tsantsar murmushi.
Yayinda idanuwanta kuma suka kasance akan ruwan swiming pool d'in nan tana kallonsa, da alamun dai shine yaja hankalinta daga shigowarta cikin wurin, duba da yadda gaba d'aya ta bada nutsuwarta a wurin tana ta sakin murmushin da ya kusa zautar da Yarima Asad daga tsayen da yake.
Yayinda daga bayanta kuma Habu ne sanye da k'ananan kaya a jikinsa, shi kuma idanuwansa akan Al'amin.
Ita kuwa sanye take da wasu blue d'in kayan fulani masu matuk'ar kyau.
Yayinda kanta kuma yake yafe da blue d'in mayafi mai girma na mahad'in kayan, kasancewar kuma mayafin ya d'an zame baya, shiyasa lallausan bak'in gashin kanta ya bayyana, atak'aice dai lifayace ajikinta amma ta kayan fulani.
K'afafuwanta kuwa sanye suke da wani bluen d'in takalmi mara tudu mai adon gashi a jikinsa.
Iyakar had'uwa ta had'u cikin shigar blue d'in da tayi, domin kuwa ba k'aramun haskawa farar fatarta tayi a cikin kayan ba.

Cikin tsantsar kad'uwa, had'i da zallar mamaki Yarima Asad ya cigaba da kallonta.
Kafin daga bisani kuma yakai dubansa wurin da yaga tana kallo, domin yaga abun da yake sata murmushin da takeyi.
Bai tab'a sanin tana murmushi ba sai yau daya gani, sabo da aduk had'uwarsa da ita shi ranta ab'ace yake ganinta.
Babu abun da yake face mamakin ganinta a wurin, sabo da shi dai yasani babu tayyada za'ayi a irin k'iyayyar da take nuna masa ta yadda tazo wani birthday paty'nsa ba.
Hakanne kuma a zahirima, domin kuwa Al'amin ne ya kira Habu ya sanar masa da birthday d'in, kana ya nemi alfarmar idan ba damuwa ya lallab'i Haddiyal su tawo tare.
Shi kuwa Habu sanin da yayi na babu tayyada za'ayi Haddiyal ta yadda ta biyosa, ko wane irin lallab'i zaiyi mata kuwa, shi yasa tun a shekaran jiya yace mata tashirya yau zasuje Jahar Wasai yawon sallah.
Ai kuwa cikin tsantsar farinciki mara misaltuwa ta amice masa har tana had'awa da godiya, kana ta tafi da sauri taje ta tambayo Lamid'o, kuma cikin sa'a batare da b'ata lokaciba a take a wurin yace ya batta su tafi.

Hakan yasa suka doko sammako tun safe. Misalin k'arfe shad'aya na rana kuma suka sauka acikin d'aya daga cikin gidajen Lamid'o da suke anan cikin garin wasai.
Kana anayin sallahr la'asar Habu yace mata ta shirya yanzu zasu tafi wurin.
Ai kuwa ba tare da b'ata lokaci ba ta shirya d'in.
Ba kuma tayi wata kwalliya ba akan fuskarta, sai hoda da man leb'e kawai data shafa akan pink lips d'inta.
Tukun suka tawo nan d'in, kuma tundaga bakin get ta gane cewar wurin shak'atawa ne sukazo.
Kana kuma tana shigowa fulawoyin da suke a wurin tare da kukan tsuntsayen da taji yana tashi suka d'auki hankalinta, tayyada har batasan lokacin data fara sakin murmushi ba, domin kuwa ita aduniya babu abun da tafiso sama da irin wannan yanayin.

Lura da Billy tayi hankalin Asad ya bar wurin ta gaba d'aya. Ga kuma mik'ewar da taga yayi a zabure.
Hakan ya sanyata d'an juyawa baya, kamar yadda sauran jama'ar da suke kallonsa ma suka juya, domin suga abun da ke faruwa daya ja hankalinsa haka.

Karaf kuwa idanuwanta dama duk na sauran mutanen suka sauka akan kyakkyawar budurwar da suka gani tamkar balarabiya, cikin shigar kayan fulani ta d'an juyar da fuskarta gefe tana sakin murmushi, ta yadda har fararen hak'waranta tare da dimple d'inta suka bayyana.

Wani irin abu Billy taji ya caki k'awon zuciyarta, lokaci d'aya taji kanta yayi wata irin sarawa, kana idanuwanta kuma suka fara ganin Haddiyal biji-biji.
Ga wata irin muguwar tsanarta da taji ta lullub'eta, sabo da fahimtar da tayi na ita Yarima Asad yake kallo.

Lokaci d'aya tinanin-nika kala daban-daban suka fara fad'owa cikin ranta.

A fannin su Fa'iza kuwa, suma itan suke kallo, suna masu mamakin abunda ya sanyata take ta sakin murmushi.

A b'angaren Al'amin kuwa da sauri ya mik'e tsaye yana mai yin hurin Habu, cikin tsantsar farinciki.

Speaker da MC ya hurace ta sanya gaba d'aya mutanen suka mayar da hankulansu garesa.
Tukun shi kuma ya bud'e baki yana mai fad'in.

"To masha Allah ga Mrs Prince Asad nan ta k'araso, dan haka yanzu zasu yanka cake, kafin daga baya abada gift."

Raff! Rafff!! Rafffff!!!
Kakejin k'arar tafi da k'arfi.

Hakan da Billy tajine, ya sanyata janye idanuwanta daga kan Haddiyal, tana mai cigeba da tafiya, sai dai kuma gaba d'aya walwalar da take akan fuskarta da yanzu ta d'auke d'ip, sabo da ganin da tayi na har yanzu shi Yarima Asad bai janye idanuwansa daga wurin ba, asalima ko alamar janyewar baiyi ba, duk da cake d'in da mc yace zasu yanka kuwa.

A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa kwata-kwata bata lura da abun da yake faruwa a wurin ba, sabo da yadda hankalinta ya tafi can wata duniyar. Sai da har sautin mc ya daki kunnuwanta, tukun ta janye idanuwanta daga kan ruwan, tana mai kaisu b'arin da tajiyo sautin ya futo.

Cak kuwa ta tsaya a wurin da take, lokaci d'aya annurin kan fuskarta ya d'auke tas, sabo da ido hud'un da sukayi da Yarima Asad.

Da k'arfi zuciyarsu tayi wata irin harbawa alokaci guda, kana suka cigaba da kallon junansu ido cikin ido.
Kafin daga bisani kuma Haddiyal ta janye nata daga cikin nasa a hankali, tukun ta saukesu a wurin da mutane suke, tana mai fara kai dubanra inda da zata hango Habu, domin taje ta samesa taji dalilin daya sa ya kawota wannan wurin, bayan kuma ba haka sukai dashi ba.
Hak'ik'a da tasan wannan wurinne zasu zo, da babu abunda zai sanya ta biyosa.

Sosai takejin zuciyarta na k'una da tafarfasa, sabo da wanda ta gani.
Hakan yasa idanuwanta suna sauka akan Habu ta fara d'aga k'afafuwanta fuskar nan ta a mugun had'e, tana mai yin wurin da suke, domin taje tace masa ya tawo su tafi.

Shi kuwa Yarima Asad ganin da yayi ta k'arayo ciki duk da idanuwan da suka had'a, ya sanya sa fesar da wani zazzafan numfashi.
Kana kuma ya janye idanuwansa daga kanta, sabo da jin da yayi har Billy da duka sauran wa'yanda zasu yanka cake sun k'araso wurin.
Sai dai kuma ko minti d'aya bai iyayi ba da janye idanuwansa daga kanta ya sake mayar dasu, sabo da ganin da jin da yake na tamkar inya d'auke idanuwan nasa daga kanta zai nemeta ya rasane.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal tsaf tana jin idanuwansa suna yawo akanta, sai dai kuma ko kad'an bata k'ara gigin d'ago kai ta kallesa ba har ta k'arasa wurin da Habu da Al'amin suke a zaune.

Tsaye tayi akansu tana mai sakin huci.
Jin hakan da Habu yayine ya sanya sa d'ago kansa, yana mai watsa idanuwansa akanta.
Ganin da yayi gaba d'aya launinsu ya fara sauyawa ne, ga wani irin matsanancin b'acin rai da yake kwance a cikinsu, yasa tun kafin ta kaiga yin magana yayi sauri d'ago hannunsa yana mai kamo tsintsiyar hannunta da shi.
Kana ya bud'e baki cikin sanyin murya yana mai cewa.

"Yi hak'uri ki zauna k'anwata, minti biyar ma yayi yawa ina masa Allah ya sanya alkhairi zamu tafi."

Taune leb'enta tayi na k'asa da k'arfi, tana mai jin wani irin mugun bak'in ciki na k'ara turnuk'eta, kana daga bisani kuma ta zauna ba tare data gaida ko Al'amin ba.

Cikin b'acin rai Billy ta k'arasa jikin Asad har tana d'an manne masa ta tsaya.
Yayinda suma sauran 'yan uwansa suka matso duk kusa da shi.

Ganin da sukayi har lokacin kwata-kwata hankalinsa baya wurinne, ya sanya Baby ta d'auko sabuwar huk'ar da take ajiye a gefe tana ta faman k'yalli.
Kana ta kamo tafin hannunsa tana mai damk'a masa ita aciki.
Jin alamun da yayi ana k'wak'uba masa abu a hannunsa ne, ya sanya sa janye idanuwansa daga kan Haddiyal da yaga ta zauna, yana mai kaisu kan tafin hanun nasa.

"Yanzu za'a yanka cake, dan Allah Yaya ka nutsu a yanka kaji."

Baby da taso ta gane ko wacece wadda yake kallon ta rad'a masa haka ahankali, tana mai kallonsa.
Bai iya cemata komai ba, sai numfashi kawai daya fesar.
Kana ya rik'e huk'ar a hannunsa da kyau.
Tukun ya d'agota yana mai kaita wurin k'atoton cake d'in da yayi matuk'ar had'uwa ya tsaya.
Kana Billy da gaba d'aya ranta ya gama dagulewa, farincikin da take ciki ya kau, tayi saurin d'ora nata tafin hannun akan nasa kafin wata ta d'ora, tukun suma su Baby gaba d'ayan su suka d'ad'd'ora akan nata.
Kana ya sake mayar da idanuwansa wurin da Haddiyal take yana mai cigaba da kallonta, sabo da ji yake tamkar zata gudune idan baya ganinta.

Shi kuwa MC ganin hakan da yayine ya sanya sa bud'e baki yana mai fad'in.
"1, 2, 3, Gooo!"
Amma sai dai me, amai-makon Yarima Asad yayi k'asa da hannunsa sai sukaga ko motsasa ma baiyi ba, ballantana kuma yayi k'ok'arin yankawa, sabo da shi kwata-kwata ma hankalinsa baya wurin, shiyasa har baiji lokacin da MC ke irgen ba.

Sosai kuwa hakan ya k'ara matuk'ar b'ata ran Billy, tayadda har bata san lokacin data d'aga idanuwanta ba tana mai hurgawa Haddiyal wata muguwar hararar da bata san tanayi ba ita.
Kafin daga bisani kuma ta danna hannun Yarima Asad da nata hannun da yake asaman nasa zuwa kan cake d'in.
Hakan da yajine ya sanyasa yin k'asa da hannun nasa ba tare daya kalli abun da sukeyi ba.

"Huuuuuuuuuu!"
'Daukacin jama'ar da suke a wurin suka sanya ihu tare da sakin tafi, alokacin da huk'ar taje k'asan cake d'in.
Tukun MC ya saki wak'ar Happy birthday.

Da sauri mutane suka fara mimmik'ewa tsaye suna masu d'aukar su hotuna.

Ita kuwa Billy ganin da tayi Yarima Asad yak'i janye hannunsa daga kan huk'ar ne, duk da yadda su duka suka d'auke nasu daga kan nasan, ya sanya ta d'aukar wata 'yar k'aramar huk'a, domin ta fara aiwatar da abun da tayi niyyar yi.

A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa, sosai taji idanuwansa da suke akanta sunyi bala'in takura mata.
Hakanne ya sanya ta mik'ewa tsaye da sauri tana mai juyawa zata tafi.

A kuma lokacin itama Billy ta yanko wani b'ari daga jikin cake d'in, tana mai sanya yatsunta ta d'aukosa da hannunta, tana mai kawosa saitin bakin Yarima Asad.

Take kuwa wuri ya k'ara d'aukar sowa da tafi, sai dai kuma masu ihun ko rufe bakinsu basu kaiga yiba, gaba d'ayansu sukayi shiru tsit suna masu futo da idanuwa waje.
Sabo da yadda sukaga Yarima Asad yayi saurin damk'ar hannun Billy da nasa hannun adai-dai lokacin data kawosa saitin bakinsa.
Kana kuma ba tare daya kalleta ba ya yarfar da hannunta k'asa, ta yadda gaba d'aya cake d'in da yake a cikin sa ya zube a k'asa.
Tukun ya fara k'ok'arin futa daga tsakan-kanin wurin hankalinsa a tashe, sabo da ganin da Yayi Gimbiya Haddiyal na shirin tafiya.

Gaba d'aya shiru wurin ya d'auka ana mai binsu da idanu, yayinda kowane mutum yake cikin tsantsar mamakin hulak'ancin da sukaga yayiwa Billy.
Ita kuwa Billy wani irin muguwar tafarfasa taji zuciyarta nayi mata da abun da yayi matan.
Hakanne ya sanyata yin sauri tana mai rigasa fucewa daga cikin wurin a zafafe, tare da nufar wurin da Gimbiya Haddiyal take.
Wato dama ashe sabo da wannan bagidajiyar yarinyar Prince yake hulak'anta ta.
Tabbas kuwa yau za'ayita ta k'are, domin kuwa sai ta koya mata hankali, ta bata kunya abainar jama'a, sabo da ko gobe ance ta k'ara kulasa bazata k'ara ba, domin kuwa ba taga da abunda ta fita ba.

"Hey stupid Vilager dakata anan!"

Muryar Billy ta daki kunnuwan Gimbiya Haddiyal cikin amon sauti adai-dai lokacin data fara tafiya.

Tsit kuwa kake jin wurin ya d'auka tamkar ba a tab'a hallitaba a cikinsa, yayinda idanuwan mutane wurin kuma gaba d'aya suka koma kan Haddiyal da Billy da take tunkarar wurinta cikin b'acinrai.

Cak Yarima Asad ya tsaya a wurin da yake jikinsa na rawa, sabo da abun da yaji Billy na cewa.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal duk da yadda sautin ya daki kunnuwanta, amma bata tsaya da tafiyar da take ba, asalima ko juyawa batayi ba, sabo da bata tabbatar da cewar da ita take ba.

"Dake nake bafullatanar k'auye, nace ki dakata anan ko."
Billy ta sake fad'e cikin amo, sabo da ganin da tayi Gimbiya Haddiyal bata tsaya ba.

Cak kuwa Gimbiya Haddiyal ta tsaya a wurin da take, sabo da fahimtar da tayi na tabbas da ita wacce take magana take.
Kafin daga bisani kuma ta juyo b'arin da take tana mai watsa dara-daran fararen idanuwanta acikin na Billy.

Cak itama Billy ta tsaya a wurin da take ba tare da ta cigaba da tafiya ba, ba dan komai ba kuwa sai sabo da yadda tayi matuk'ar firgita da kyawun Haddiyal.

Ashe da ba sosai ta gantaba daga nesan da take ba kenan, lokaci d'aya taji ta raina nata kyawun da take tak'ama da shi gaba d'aya.
Sai dai kuma wannan bashine zai hanata tayi mata gargad'i akan Prince d'inta ba.
Hakan yasa ta bud'e baki bayan ta watsa idanuwanta acikin na Gimbiya Haddiyal, tana mai fad'in.

"Ina son ki bud'e kunnuwanki da kyau ki saurareni, sannan kuma kiyi amfani da abun da zan fad'amiki ta lalama.
Ma'ana dai Asad nawane, mallakina ne, nice matarsa sabo da nice wacce iyayensa suka san da ita
Hakan yasa nake jan kunnenki akan ki futa daga harkarsa, ko da wasa karki k'ara kuskuren kusanta kanki da shi, sabo da shi d'in ba tsararki bane, ba kalarki bane, ya huce ajinki.
Idan kuma har bakiji abun da na fad'a miki ba, to kisani tabbas zan tabbatar miki da ramin kura ba hurin wasan makawo bane.
In banda ma abunki, dan Allah ki dubi kanki, sannan kuma ki dubesa, ki fad'amun ta ina kuka dace?"

Billy ta k'arasa maganar tana mai d'an girgiza jiki, kana kuma cikin sauti.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal ko kusa ko kad'an kalamanta basuyi mata zafi ba, asalima sai kallon cikin idanuwanta data sakeyi, kana ta saki murmushin gefen bakin da har yasanya kumatunta lob'awa.
Tukun daga bisani ta janye idanuwanta daga kanta tana mai juyawa ta fara tafiya.

"Ke d'in wacece, da har ina magana zaki juya ki tafi ba tare da nace ki tafi ba? Ke kinsan koni wacece kuwa?"

Billy ta fad'a cikin matsanancin b'acinran da murmushin Haddiyal ya sakar mata tana mai sakin huci.

Cak Gimbiya Haddiyal ta tsaya a wurin da take ba tare data k'ara ko d'aga k'afarta ba.
Kana daga bisani ta juyo da kanta tana mai watsa idanuwanta a cikin tsakiyar na Billy.
Tukun ta bud'e baki cikin sassanyar muryarta mai matuk'ar dad'i da sauti, kana kuma da d'an amo, tana mai fad'in.

"Wacece ke kuwa bayan karuwa!"

Ta fad'a cikin wani irin sauti tana mai cigaba da kallon tsakiyar idanuwan Billy.
Yayinda ita kuma Billy taji saukar sunan karuwar data dangantata da shi acikin kunnuwanta tamkar saukar ruwan dalma, ta yadda har idanuwanta suka kad'a sukai jajajir lokaci guda.

Hakanne ya sanyata d'aga tafin hannunta cikin zafin rai, tana mai yin kan fusakar Haddiyal da shi tare da fad'in.
"Keeeee!"
Amma sai taji caraf an damk'i hannun nata da matuk'ar k'arfi, alokacin da yake gab da isa kan fuskar Haddiyal dako motsi bata canzaba daga yadda take balle ta tsorata.

Hakan da tajine ya sanyata d'ago kanta domin taga wanda ya tareta daga aikata abun da tayi shirin aikatawa.

Idanuwa Hud'u sukayi da Yarima Asad, da yayiwa hannun nata wata irin damk'a da k'arfi.
Yayinda idanuwansa kuma sukayi wani irin ja, yana mai sakin huci tamkar zaki.

Kallon cikin idanuwan Billy yayi, kana ya yarfar da hannun nata a k'asa da k'arfi, yana mai bud'e baki cikin amo yace.

"K'arya tayi ba karuwar bace ke?"

Da k'arfi Billy ta rumtse idanuwanta, sabo da jin kalamin daya jefeta da shi jikinta na d'aukar rawa.
Yayinda gaba d'aya jama'ar wurin kuma suka mik'e tsaye a firgice suna kallonsu, sabo da babu wanda kalamin Asad bai girgiza ba a wurin, dan kuwa shi MC ma gaba d'aya mick d'in hannunsa ya saki a k'asa, kasancewar kuma dama tunda Billy ta futa daga wurin ya kashe kid'a, shiyasa wurin ya kara d'aukar shiru.
Tukun shi kuma

Please Login or Register in order to submit comment