Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tab'e fuska tare da fad'in.

"Ba zan sha ba Mamyna na k'oshi."

"A'a Zakina daurewa zakayi dole kasha, saboda zai taimaka maka wurin rage rad'ad'in ciwon."

Ta k'arasa maganar tana mai sake d'ora masa cup d'in a baki.

Rumtse idanuwansa yayi yana mai bud'e baki ya fara sha, sai dai kuma kwata-kwata baya jin dad'in bakinsa, a haka dai harya shanye, tukun ya janye bakinsa daga kan cup d'in.

Hakan da Babban Yaya ya ganine ya sanyasa matsowa wurin, yana mai basa maganunuwan daya b'allo.

Karba yayi yana mai watsasu a ciki baki.
Kana shi kuma Babban Yaya ya d'ora masa jarkar ruwa akan baki ya shanyesu.
Tukun ya fara shirin kwnaciya, amma sai Mai Martaba ya hanasa yana mai matsowa ya zauna a gefensa.
Kana ya zaro wani mai a cikin 'yar roba daga cikin aljihunsa, da alamun dai dama ya tanade sa ne saboda yau d'in, saboda ba'a tab'a amfani dashi bama.
Tukun ya lakatosa yana mai murzasa a cikin tafin hannunsa.
Kana ya fara shafe bayan Yarima Asad dashi har zuwa kan cikinsa da k'irjinsa da bulalan suka tab'a.

Da k'arfi kuwa ya rumtse idanuwansa yana mai fad'in.

"Ashsssss...da..dyyyyy!!!"

Yayi furucin a wani irin sakalce, yana mai shash-sheka fuska tamkar zai fashe da kuka.
Wanda hakan kuma ya sanya Babban Yaya fashewa da dariya ba tare daya shiryaba, yana mai fad'in.

"Kaji d'an kan uba, wato bakayi kukan bulalai ba sai kukan shafa magani, saboda kasan anan lallab'aka zasuyi ko, raggon maza kawai."

"Mamayna kin ganshi ko."

Cewar Yarima Asad a wani irin shagwab'e k'walla na tsiyayo masa da gaske.

Da sauri kuwa Mamy ta juya wurin da Babban Yaya yake zaune tana mai sakar masa dundu a baya, tare da fad'in.

"Rabu dashi Zakina, duk matasan gidannan babu Jarumi irinka, harshi d'in kafisa."

"Wayyo Dady Mamy zata b'allamaka bayan d'anka."

Babban Yaya ya fad'a shima a shagwab'e tamkar zaiyi kuka.

Yayinda Mai Martaba kuma daya gama shafawa Yarima Asad man yace.

"Ni idan ma nazo har k'afafunka zan karye, tunda har kake tab'amun Babana."

Ya k'arasa maganar yana mai kwantar da Yarima Asad rubda ciki ba tare daya cire ko towel d'in jikinsa ba, tukun ya janyo k'aton eskimo ya rufesa dashi.
Wanda hakan kuma ya sanya jikinsa ya dena rawar da yakeyi.
Kana kuma cikin d'an k'an-k'anin lokaci bacci ya d'aukesa.
Hakanne yasa suka mik'e gaba d'ayansu suna masu fucewa daga cikin d'akin, suka barshi yayi baccin kafun lokacin sallahr magariba yayi.


*BABBAN ZAURE LOCUS.*

Wata irin matsananciyar soyayya Abdulmajid (Bir) yake nunawa Gimbiya ita, gaba d'aya tun adaren jiya da Yarima Asad ya tafi yake jin zuciyarsa tayi sakayau, gaba d'aya damuwar da yake a ciki a 'yan kwanakinnan duka ta b'ace, sai wata irin azababbiyar soyayyar Gimbiya da yake ji tana cigaba da fuzgarsa.
Yayinda a fanninta itama tayi yinin yau d'in cikin matsanancin farinciki da walwala, irin wanda tunda tazo gidan bata tab'a yinsa ba, domin kuwa ada duk bata yadda da gaske yake ya fasa zuwanba, sai a yau d'in da taga kwata-kwata baima futaba, sai aikin manne mata da yake tayi, domin kuwa ko kiching data shiga zasuyi aiki tare da Ummi shima zuwa yayi ya zauna, ak'arshe dai har sai da Ummi ta gaji ta korasa tukun ya futa ya koma wurin Kaka.

Sosai suka maida hankali wurin koyar karatun alk'urani tare da bak'ake, kuma Alhamdulillah suna fahimta sosai, tare da saurin d'aukewa duk da dai ba wani da yawa ake yi musu ba.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir tini ta fara sanya hijabai da mayafai da sukaje ita da Matar Sheikh Ahmad suka siyo.

Yanzu haka zaune suke a cikin falo suna kallon wani indian seris firm, gaba d'ayansu harda Abba Sheikh Ahmad ya shigo ciki bakinsa d'auke da sallama.

Amsa masa sukayi, tukun ya k'araso ciki yana mai samun wuri ya zauna, kana ya gaishe da iyayensa harma da Kaka da tunda ya shigo take jifansa da harara, wato dai tana son ta takalosa ya kuma kulata tace masa mara kunya, wanda hakan kuma daya lurane ya sanya yak'i kulata, sai gaisuwar dasu Bir, Auta da kuma Gimbiya suke masa daya amsa.
Kana bayan sun gama duk gaisawar yayi gyaran murya, yana mai gyara zamansa ya fuskanci Iyayensu.

Hakan da sukaji ne ya sanyasu d'agowa suna masu d'ora idanuwansu akan fuskarsa.
Yayinda shi kuma ya karyar da murya, yana mai bud'e baki cikin tsananin ladabi yace.

"Dama akan batun da'awar da nace maka muna shirin zuwane, to a shekaranjiya da muka sake zama dasu Mai Martaba ya amice mana, sannan kuma ya bada gudummawa sosai, hakan yasa muka yanke jibi a matsayin ranar da zamuje Jahar Kagul cikin masarautar Fuld'e, domin anusar dasu girman zunubin da suke aikatawa, to bayan an gama tattaunawarne kuma sai aka bijiro da batun zuwa K'asar Malin, Cikin BAK'AR MASARAUTA, to shine a k'arshe mai martaba ya buk'aci gobe muje tare da shi Abdulmajid wurinsa."

Ya k'arasa maganar yana mai kallon Umminsa dan yaji abun da zatace, amma sai kuma yaji daga ita har Abba sunce Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a yasa adace."

"Amin Amin." Gaba d'ayansu suka amsa da haka, Yayinda wani irin matsanancin farinciki kuma ya lullub'e zuciyar Bir, saboda sanin da yayi na muddin akaje za'a jiyo masa labarin halin da Iyarsa take.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir kanta ta durk'usar k'asa, tana mai jin tamkar tace musu su hak'ura kar suje, saboda tsoron abunda zai faru idan sunje d'in da takeyi, domin kuwa ita tasan halin ahalinta kwata-kwata, babu wani abu mai suna imani ko tausayi a tare dasu duka, sai dai kuma duk da haka wani b'angare na zuciyarta na fatan Allah yasa adace.

Haka dai suka cigaba da tattaunawa gaba d'ayansu suna masu fatan Allah yasa adece, tukun da dare ya farayi misalin k'arfe tara kowa ya tashi ya tafi d'akinsa.

Washegari.

Misalin k'arfe tara na safe suka futo cikin shirinsu na tafiya Fada.
Sanye Bir yake da wani farin tattausan yadi sabo fidigl da yayi bala'in yi masa kyau, yana futar da k'yalli.
Yayinda kansa kuma yake d'auke da bak'ar hula, takalman k'afafuwansa suma bak'ak'e, sai kuma tsintsiyar hannunsa da take d'aure da bak'in agogon fata da yayi bala'in k'ara haska fatarsa.
Iyakar kyau yayisa cikin shigar manyan kayan, sai dai kuma duk da haka har yau bai gama sabawa dasu ba, domin kuwa sai yayta jin tamkar suna tsinkulinsa.

Shi kuwa Sheikh Ahmad sanye yake da milk d'in shadda da tayi matuk'ar yi masa kyau.
Haka suka futo a jere gwanin sha'awa dasu, suna masu bud'e mota suka shiga.
Tukun mai gadi ya bud'e musu get Sheikh Ahmad ya taketa suna masu fucewa daga cikin gidan.

K'arfe tara da kusan arba'in suka isa cikin Masarautar Wasai.
Kai tsaye sukayi Fada, saboda dama anan d'in sukayi zasu had'u yau da misalin k'arfe goma na safe dai-dai, tare da duk sauran malaman da za'ayi tafiyar dasu.

Cikin tsananin girmamawa da mutuntawa jama'ar Fada suka tarbesu.

Gaba d'aya basu hannu Sheikh Ahmad yayi sukayi musabaha, wanda hakan da Bir ya ganine kuma ya sanyasa shima matsawa yana mai mik'a musu nasa hannun suka gaisa, tukun ya koma kusa da yayansa ya zauna, yayinda su kuma jama'ar wurin suketa aikin binsa da kallo, saboda duk sunji labarinsa wurin Sheikh Ahmad a wanan zaman da akayi.

Acan b'angarensu Yarima Asad kuwa sosai yaji dad'in magun-gunan da ake basa tun jiya, domin kuwa yau sakayau yaji ya tashi, gaba d'aya rad'ad'in da jikinsa yake yi ya kau, sai d'an abun da ba'a rasaba.

Zaune suke a cikin d'akin gefen gado, futowarsa daga wanka kenan Al'amin yana shafa masa man da Mai Martaba ya shafa masa jiya a tsakiyar bayansa.
Yayinda Babban Yaya daya shigo yanzu kuma yake zaune akan kujera yana kallonsu.
Tukun daga bisani ya sauke idanuwansa akan agogon da yake d'aure a hannunsa.
Kana ya mik'e tsaye da sauri, saboda ganin da yayi gomar harta kusa, duka baifi minti biyar ya rage ba.

Har ya fara tafiya sai kuma ya juyo yana mai kallon Yarima Asad tare da fad'in.

"Gafa sabon abokinku can yazo, kuma ku shirya anjima Malam zaizo ya fara koya muku karatun da na fad'a muku, kafun kuma ka gama warkewa ku dinga zuwa da kanku can wurin da yake."

"Wane Abokin namu kuma?"
Al'amin ya fad'a yana kallonsa.

"Wanda yaje har gidansu yayi masa rashin mutunci mana"
Cewar Babban Yaya yana mai hurgawa Yarima Asad harara.
Yayinda shikuma ya d'ago kansa da sauri yana mai watsa idanuwansa akan fuskarsa, saboda abun da yaji ya fad'a.
Kana daga bisani kuma ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Yana ina Yaya, dan Allah kace masa yazo ya dubani, ko kuma kayi mun magana kafin ya tafi ni sai naje wurinsa ina son nayi masa godiyane."

"Kai kuma d'inne yau kake fad'in zakayiwa wani godiya da kanka Asad?"

Babban Yaya ya fad'a cikin matsanancin mamaki.

Shi kuwa Yarima Asad lumshe ido kawai yayi yana mai jinjina masa kai.
Yayinda Al'amin kuma ya bud'e baki cikin dariya yana mai fad'in.

"Ai yanzu ba wancan Asad d'in daka sani bane na baya Yayanmu, wannan wani dabanne da soyayya ta sanyasa kusan haukacewa."

Da sauri yaja baya, saboda dukan da Yarima Asad ya kawo masa yana mai tuntsirewa da dariya.
Shi kuwa Babban Yaya murmushi yayi yana mai fad'in.

"To masha Allah, a gaskiya dole ma muyiwa Gimbiya Babbar tarba, tare da tanadin tukuici aduk ranar data zo ko dan canza mana Asad d'in mu da tayi."

Ya k'arasa maganr cikin matsanancin farinciki yana mai jutawa ya tafi.


Yana shiga cikin Fada ya huce wurinsu Sheikh Ahmad yana mai mik'a masa hannu suka gaggaisa, tukun ya koma gefen Bir yana mai dafa kafad'arsa tare da fad'in.

"Masha Allah K'anina, ina maka murna da dawowa cikin ahalinka."

"Nagode."
Bir ya fad'a yana mai durk'usar da kai k'asa.

A kuma dai-dai lokacin Mai Martaba ya shigo cikin Fada.
Da sauri kuwa Fadawansa suka mimmik'e tsaye, suna masu yi masa katanga ya zamto babu mai ganinsa hatta dasu d'in kuwa, kana suna faman aikin yi masa kirarin zama da sukeyi harya zauna akan kujerarsa.
Kana suma suka ja baya suna masu zama.
Tukun aka fara gaisawa a mutunce dashi.
Bayan an gama gaisawar ne kuma ya kalli Bir alokacin da yake gaishesa yana mai fad'in.

"Matsonan tawo kusa dani ka zauna d'ana."

Kai durk'ushe a k'asa kuwa Bir ya mik'e tsaye daga wurin da yake, yana mai tawowa kusa da kujerar Mai Martaba ya zauna.

Shi kuwa Mai Martaba cikin matsananciyar soyayyar Yaron da yaji tana lullub'esa lokaci guda, ya kife tafin hannunsa akan lalallausar sumar kansa, bayan ya zare masa hula da d'ayan hannun.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Allah ya albarkaci rayuwarka, ya kareka daga sharrin mak'iya da mahassada, ya nisanceka daga aikata sab'onsa. Hak'ik'a ina maka murnar saduwa da iyayenka da 'yan uwanka 'Dana. Kuma daga yanzu ina son ka d'aukeni tamkar uba a wurinka nima, duk abunda kake buk'ata kazo ka sameni ka fad'a mun kaji ko."

Ya k'arasa maganar yana mai mayar masa da hular kansa, gaba d'aya tausayin yaron ya mamaye masa zuciya.
Shi kuwa Bir a hankali ya d'aga masa kai ba tare da yace komai ba, sai wata irin matsananciyar soyayyar dattijon da yaji ta lullub'e zuciyarsa.
Kana kuma mamakin ganin yadda ya zauna akusa da Sarki harya tab'asa ya lullub'esa, saboda su dai a inda ya baro ko hanya baka isa ka had'a da 'Dan Sarki bama ballantana kuma Uban.
Tukun daga bisani ya fara shirin tashi ya koma wurin da yake, amma sai yaji Mai Martaba ya rik'o hannunsa yana mai fad'in.

"Yi zamanka anan kaji ko."

Komawa yayi ya zauna d'in yana mai tank'washe k'afafuwnasa.
Yayinda shi kuma Mai Martaba yayi gyaran murya.
Wanda hakan kuma da sukajine ya sanyasu nutsuwa gaba d'ayansu.
Kana Waziri da yake zaune a gefe yayi bismillah yana mai gabatar da abunda ya tarasu a wurin, tukun akace Sheikh Ahmad ya bud'e wuri da addu'a.
Sannan kuma bayan an gama aka fara tattauna yadda tafiyar zata kasance.

Yayinda ake tambayar Bir kuma yadda yanayin mutanen Bak'ar Masarauta suke yana mai basu amsa.

Gaba d'aya shiru wurin ya d'auka, kowa da abun da yake sak'awa a cikin zuciyarsa, saboda yadda mutanen Bak'ar Masarauta suke da sukaji a bakin Bir.
Kafin daga bisani kuma Mai Martaba da kansa yayi gyaran murya.
Kana ya bud'e baki cikin dakakkiyar muryarsa yana mai fad'in.

"Duk da munji yadda jama'ar suke, hakan ba zaisa mu fasa abunda mukayi niyyaba, amma sai dai kuma shirin namu zai canzane akan na baya yanzu, wato amai-makon mutura iya Malamai to yanzu zamu had'ane harda mayak'an mu na Masarauta, kuma zasu tafi da kayan yak'i, saboda gudun ta kwana, ma'ana dai dan kariya tunda bamu san irin tarbar da zasuyi manaba, domin kuwa ko addini ya hallata hakan, dan haka nake son na sanar muku da duk wanda yasan zaije to yasa aransa zai tafi Jahadine, wato zai tafi yiwa musulunci hidima, kuma idan ya tafi babu tabbacin zai dawo gida, tamkar yadda magabatanmu sukayi a lokutansu."

Shi kuma Abdulmajid zamu tafi da shine domin ya zamto mana jagoran tafiya, saboda shine kad'ai yasan hanyoyi daya kamata mubi. Sannan kuma nima harda ni a cikin mutanen da zasuyi tafiyar."

Da sauri gaba d'aya jama'ar wurin suka kallesa, saboda jin abunda ya fad'a.
Hakan da ya ganine ya sanyasa girgiza musu kai alamun tabbatarwa, kana kuma ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Tabbas dani za'ayi tafiyar, saboda bai kamata ace a matsayina na shugaba ba na turaku ni kuma na zauna da lafiyata, sannan kuma ko bayan hakama nima ina son ladan.".

" Allahu Akbar!"

Gaba d'aya jama'ar cikin falon suka d'auki kabbara.
Saboda gamsuwa da kowa yayi da hukuncin da aka yanke.
Kana a k'arshe aka tsayar da ranar da za'a tafi, wato nan da kwana goma masu zuwa dai-dai kenan, sannan kuma Mai Martaba ya bada umarnin aje a fara futo da kayan yak'i.

Shi kuwa Bir jin da yayi hardashi a cikin tafiyarne, ya sanyasa jin wani irin matsanancin farinciki ya lullub'esa, saboda yadda ya fara hango kansa a gaban Iyarsa zaune suna hira, hak'ik'a shi d'in zai iya cewa yafi kowa farinciki da tafiyar, domin kuwa kwata-kwata bai kawo kansa mutuwa bama shi.

Shi kuwa Sheikh Ahmad jin da yayi harda Bir za'ayi tafiyarne, ya sanya yaji jikinsa yayi d'an sanyi, saboda ya sani ba lallai bane a yadda Ummi take zumud'in dawowarsa ta barsa ya k'ara komawa k'asar nan.

Haka dai suka gama tattaunawa, tukun ak'arshe duka Malaman suka mik'e harsu bakwai domin su tafi.

A jere Babban Yaya da Sheikh Ahmad harma da Bir da Mai Martaba yayi masa mahaukatan kyaututtuka, har da su ta doki tare da alkyabbu da yasa Babban Yaya ya d'auko masa idan sun futa.

"Yawwa k'anina, Abokinka fa yace nace maka dan Allah kazo ka dubasa bazai iya zuwa bane da yazo kun gaisa."
Cewar Babban Yaya yana mai kallon Bir.

Shi kuwa Bir da bai gane kowa yake nufi ba d'ago kansa yayi yana mai kallonsa ba tare da yace komaiba.
Hakan da Babban Yaya ya ganine kuma ya sanyasa fad'in.

"Asad mana, daka hak'ura ka sadaukar masa da budurwarka."

Babban Yaya ya fad'a yana dariya.

Dariya shima Bir yayi yana mai sunkuyar da kai k'asa, saboda gane ko waye da yayi, kana daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Dama ai tasace."

Shi kuwa Sheikh Ahmad kallon Babban Yaya yayi yana mai fad'in.

"Wai har anyi shad'inne?"

"Anyi mana tunjiya, gashi can yana ta zuba raggonta."

Cewar Babban Yaya yana dariya.

Shi kuwa Sheikh Ahmad ido ya zaro yana mai cewa.
"Amma ai ya haye ko?"

"Ya haye dak'yar, dan kuwa da an k'ara biyar a gaba k'ilama sai dai a d'aukesa.

"Ka jika sai kace kai iyawar zakayi, to muje tare nima na dubasa."

Cewar Sheikh Ahmad yana sakin murmushi.
Tukun suka jera suna masu dosar part d'in Mamy.

B'angarenta suka fara zuwa suka gaisheta, yayinda tai ta sanyawa Bir albarka tana mai kuma yiwa Sheikh Ahmad godiya na karatun da yaranta zasu na d'auka a wurinsa, dama wanda su kansu suke sauraro a gidan tv da redio.
Tukun a k'arshe da suka tashi tafiya tace su sanarwa da Ummin tasu tana nan zuwa har gida tayi mata murna.
Sannan suka fuce suna masu tafiya d'akin su Asad.

Babban Yayane ya fara shiga, tukun Sheikh Ahmad ya rufa masa baya, kana a k'arshe Bir shima ya shigo.

Da sauri Asad da Al'amin da suke zaune aken kujera Al'amin na basa labarin free weeding pics d'in Billy yana tab'e baki, shi kuma suka juyo suna masu sauke idanuwansu akansu.
Sanye Yarima Asad yake da three quater a jikinsa tare da wata 'yar k'aramar rigar net mara hannu a jikinsa.

"Sannunku da zuwa."
Al'amin da Yarima Asad suka fad'a fuskarsu d'auke da murmushi.
Kana Asad ya sake juyawa b'arin da Bir yake yana mai kallonsa, tare da sakar masa murmushi, tukun ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Tawo nan kazauna d'an uwa."
Ya k'arasa maganar yana mai yi masa nuni da kujerar da take facing d'in wacce suke zaune akai.

Murmushi shima Bir ya sakar masa yana mai k'arsowa wurin da suke ya basu hannu, tukun ya zauna akan kujerar yana mai fad'in.

"To ya d'an soyayya, ya kuma akaji da tsamin jiki."

Yayi maganar cikin barkwancinsa daya saba da shi. Wanda hakan kuma ya sanyasu kwashewa da dariya gaba d'ayansu harda su Babban Yaya.
Tukun Al'amin da Yarima Asad suka gaishe da Sheikh Ahmad.
Kana bayan sun gama gaisawa ya kalli Asad yana mai fad'in.

"Ya jikin naka to."

"Jiki da sauk'i."
Cewar Asad, tukun shi kuma Sheikh Ahmad ya kalli Bir yana mai fad'in.

"To taso muhuce ko."

"Dan Allah Yayanmu kabar mana shi, idan yaso da yamma sai na kawosa har gida."

Cewar Al'amin da sauri yana mai karyar da wuya ya kalli Sheikh Ahmad.
Da sauri shima Yarima Asad yace.

"Dan Allah ai Aboki zaka zauna ko?"
Ya k'arasa maganar yana mai kallon Bir.

"Ka barshi anan d'in kawai, inyaso da yamman idan ya rakosa har dai baka komai sai ka had'asu kayi musu k'arin karatun, domin kuwa ka gansu nan duk fankuna ne daga karatun sallah babu abunda suka iya."

Cewar Babban Yaya yana dariya.
Yayinda Yarima Asad da Al'amin kuma suka turb'une fuska.

Shi kuwa Sheikh Ahmad dariya yayi yana mai fad'in.

"A'a fa Ciroma karkayiwa k'annena sharri banaso."

"Sharri ko gaskiya, ai gasunan sai kun had'e tukunna zakace na fad'ama."

Ya sake fad'e yana dariya, saboda yadda yaga sunata b'ata rai.

"To naji muje, Jaririn Ummi ni na huce sai mun had'u a gidan ko."

Cewar Sheikh Ahmad suna masu juyawa suka futa da Babban Yaya.

Shi kuwa Yarima Asad gwalalo idanuwa yayi yana mai kallon Bir tare da fad'in.

"Wai kai nan a sangamemen gardin nan naka ake cewa Jariri, kuma ko kunya bakaji?"

"To ai Jaririnne, idan kuma ka musa ka bari muje mu tambayi Ummina zata fad'a maka."

Bir ya fad'a yana mai jifan Asad da hararar wasa tamkar dama can sun saba da juna.
Dariya kuwa suka kwashe da ita duka.
Tukun Asad ya gyara zamansa yana mai kallon Bir, kana daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Nagode! Nagode sosai Aboki da sadaukarwarka gareni, hak'ik'a ka taimakeni, banda haka da yanzu k'ila kaine ka shanye bulalun nan bani ba."

Murmushi Bir yayi yana mai kallon Yarima Asad, kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kai Malam nifa babu sadaukarwar da nayi maka, saboda dama can bayi nake ba ina da tawa Gimbiyar, kawai dai yadda kayine ya sanya nace ni kuma sai na nuna maka bana tsoron barazana, sai kuma gashi daga baya kazo ka lashe amanka da kanka."

Bir ya fad'a yana mai kallon Asad tare da sakin dariya sosai.

Shi kuwa Al'amin cikin dariyar da yake ya kalli Yarima Asad yana mai fad'in.

"Sai kaga ashe shi d'in k'aramin mara kunya ne dai ko."

Da sauri kuwa Yarima Asad ya kaimasa duka yana mai fad'in.

"Magulmaci naga har wani dad'i kakeji bak'in mugu, to barama kaji ni yanzu akan Gimbiyata bank'i ace mun har sakarai ba muddin zan sameta."

"Tabbas kuwa na yadda, tunda gashi nan harka iya tsayawa wani k'ato ya dakeka akanta."

Al'amin ya fad'a still yana dariya.

Shi kuwa Yarima Asad cikin wani irin yanayi ya lumshe idanuwansa, kana kuma daga bisani ya bud'esu yana mai fesar da iska.
Sannan yace.

"Kun san Allah, ji nake tamkar aduk duniya babu wani namijin da yake yiwa budurwarsa ko matarsa irin son da nakeyi mata."

"Kai gaye dakata, dan ni wallahi ban yadda kana mata irin son da nake yiwa tawa Gimbiyar ba."

Cewar Bir da sauri yana mai girgizawa Asad kai.

"Tunda kasameta abati ba tare da kaci nad'a ba dama ai dole kace haka."

Yarima Asad ya fad'a yana mai tab'e baki.

Hakan kuma shine ya sanya Bir kwashewa da dariya, yana mai fad'in.

"Kai yanzu dan 'yar bulala talatin d'in da aka sauke maka akanta shine har kake tinanin kayi wata bajinta, to ka bud'e kunnuwanka kaji irin bak'ar azabar da nasha kafun na samu Gimbiya ta fara ko kallona ma, kai kafun ma nan ku fara k'iyasto yadda soyayya zata yiwu tsakanin Bawa da 'Yar Sarki."

Shiru gaba d'ayansu sukayi suna masu zubawa Bir idanuwa.
Hakan da ya ganine shima ya sanyasa gyara zamansa, tukun ya fara zayyano musu tarihin tasa soyayyar tun daga ranar daya fara d'ora idanuwansa akan Gimbiya Tasmir har zuwa gudowarsu.

"Cab', kace kai da tini ka shanye bulalun tunda an riga da ansaba dama. A lallaine Allah na gode maka dana sauke girman kai naje na bada hak'uri."

Cewar Yarima Asad yana mai jinjina kai tare da kallon Bir.

Shi kuwa Al'amin cewa yayi.
"A gaskiya na jinjina maka Aboki.

Murmushi kawai Bir yayi ba tare da yace komai ba.
Yayinda shi kuma Asad ya mik'e tsaye yana mai fad'in.

"An kira sallah muje muyi alwala sai muhuce masallaci ko."

Ya k'arasa maganar yana mai shigewa bathroom.

Haka dai suka yini hira, tukun bayan sallah'r la'asar suka had'awa Bir shatara ta arzik'i, tundaga kan sutura, alkyabbu, har dasu dokin da Mai Martaba ya basa, sai dai kuma shi dokin anan ciki suka barshi iyakaci kawai yaje ya hau ya d'anasa, tukun suka shige motar Al'amin shi kuma Yarima Asad ya koma gida suka tafi.

Kusan a lokaci d'aya suka koma gidan tare da sheikh Ahmad, domin kuwa yana shiga ciki ko rufe get d'in ba'a yiba shima Al'amin ya ddano hancin motarsa zuwa ciki.

Hakanne yasa suka had'u su duka ukkun suna masu shigewa cikin gidan.

Zaune suka samu Ummi da Kaka acikin falon.

Kai tsaye Bir ya huce jikin Ummi yana mai kwanciya akai.
Kana ya bud'e baki cikin yin k'asa da murya yana mai fad'in.

"Ina Gimbiyata Ummina, naga ban gantaba?"

"Kai kai Jaririna kai kullum rashin kunyarka k'aruwa takeyi."

Cewar Ummi tana mai dungure masa hanci.

Da sauri kuwa ya b'oye fuskarsa a cikin jikinta yana mai sakin dariya.
Yayinda itama d'in ta saki murmushi tana mai amsa gaisuwa da Al'amin yake mata cikin tsananin sakin fuska.

Sheikh Ahmad ma barka da gida yayi mata yana mai gabatar da Al'amin a wurinta, tare da sanar da ita a wurinsu Jaririnta ya huni ma ai.

"Masha Allah, kace Jaririna yayi Abokai, to ya gidan dasu Mamanku da kuma mai jikin?"

"Da sauki mai jiki, suma kuma duk suna gaisheku."
Al'amin ya fad'a fuska asake.

A kuma lokacin Gimbiya Tasmir da take sanye da riga da siket na sabuwar a tamfar da suka anso daga wurin d'inki ita da Matar Sheikh Ahmad ta futo daga cikin d'aki

"Sannu da dawowa Yayanmu."

Ta fad'a tana mai zama a kusa da Ummi, ya zamto sun sata a tsakiya ita da Bir.

"Yawwa k'anwata ya gida?"

Cewar Sheikh Ahmad yana mai mik'ewa ya fuce zuwa nasa part d'in.

Shi kuwa Bir a hankali ya zura hannunsa ta bayan Ummi yana mai muntsino fatar bayan Gimbiya dashi.

Da sauri kuwa ta kallosa tana mai kwad'a masa harara tare da shassheke fuska tamkar zata fashe da kuka.

Gwalo yayi mata yana sakin dariya, kana daga bisani ya bud'e baki acan k'asan mak'oshi yana mai fad'in.

"Kinga Abokina nan munzo tare."

"Hummm! Allah ya shirya dai."
Kaka da taga yadda yake rad'a mata magana ta fad'a tana mai tab'e baki.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir da sauri ta juya wurin da Al'amin yake tana mai gaishesa.

Amsa mata gaisuwar shima yayi yana mai tsokanarta da yau saurayinta ya cikasu da labarinta. Yayinda a k'asan zuciyarsa kuma yake yabawa da kyawun da Allah yayita da shi.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir murmushi tayi ba tare da tace komaiba.

Haka dai sukaita hira har zuwa lokacin da aka kira sallahr magariba, tukun sukayi al'wala suna masu had'uwa da Babban Yaya, Auta harma da Abba da yadawo yanzu suka huce masallaci.

Ana idar da sallah kuwa bayan sun gama adduoinsu Sheikh Ahmad ya fara koyawa Bir da Al'amin karatu.
A haka har aka kira sallar isha'i, tukun bayan sun dawo Al'amin yace zai huce shi.
Amma gaba d'aya Bir ya hanasa tafiya, sai da har sukaci abincin dare, tukun ya rakasa har bakin motarsa, kana bayan yaga tafiyarsa duka ya juyo ya dawo cikin gidan.

Zaune ya samu Sheikh Ahmad a gaban Abba da Ummi yana kora musu bayanin yadda sukayi a zaman nasu na yau.

Ai kuwa Ummi tana jin ance tare dashi da kuma Bir za'a tafi, ta fara girgiza kai cikin matsanancin tashin hankali da firgici.
Wanda hakan kuma da Sheikh Ahmad harma da Bir

Please Login or Register in order to submit comment