Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

suka gansu da shi.
Ga kuma irin shigar da take sanye ajikin Gimbiya Haddiyal, sabo da sudai har dai ba inyamurai ba basu saba ganin mace budurwa na yawo babu ko d'an kwali akanta ba.
Hakan yasa suka fara tinanin kosuwaye sud'in to ba 'yan k'asar nan bane ba, yayinda wasu kuma suka fara fad'in larabawa ne, sabo da mayawaicin bak'in gashin Gimbiya Tasmir da suka gani ya sauko har kusan k'ugunta.

Da sauri ta rik'e hannun Bir tana mai mannewa ajikin sa, tare da durk'usar da kanta k'asa jikinta na 'yar rawa.
Hakan da Bir yajine ya sanyasa fesar da iska.
Kana ya d'an durk'usar da kansa k'asa, yana mai kawo bakinsa saitin kunnenta, tukun yayi mata rad'a da cewar.

"Ki bari na d'auki jakar mutafi ko, babu abunda zasuyi mana kinji."

Ya fad'a asanyaye shima tamkar maijin tsoron, sabo da yadda yake jin zuciyarsa na cigaba da bugawa da k'arfi.

'Dada masa kai tayi a hankali tana mai d'an matsawa, amma sai dai kuma duk da haka bata saki yatsunsa ba data rik'e su.
Wanda hakan kuma shi ya k'ara janyo hankulan jama'a kansu, sabo da su dai hausawa da kunya mace da namiji suyita nanik'ewa junansu akan titi, koda mata da mijine kuwa.

"Gimbiyata rigima ko."
Ya fad'a yana mai d'an sakar mata murmushi.
Kana ya durk'usa yana mai shitin d'aukar jakun-kunan nasu, amma sai yaji wani al'amaji agefensa yana mai fad'in.

"Ina za'a kaine Alhaji?"

"Yawwa yaro d'aukar mun wannan."

Bir ya fad'a yana mai nuna masa ta kayansu, kana shi kuma ya d'auki ta kud'in ya rik'e a hannu, wanda hakan da yayin kuma shi ya sake bawa Gimbiya Tasmir damar samun rik'e hannun nasa, tare da k'ara shigewa cikin jikinsa sosai.
Tukun suka fara d'aga k'afafuwanu a tare, suna masu ratsa cikin mutanen domin subar tashar.

Yuuuuu!
Haka ake binsu da idanu harda masu waigensu.
Ba kuma komaine yake ta janyo hakan ba, sai rashin d'ankwalin da yake akan Gimbiya, sai zallar doguwa rigar jikinta da takalmi kawai, ga kuma shi kansa kyawunsu da yake k'ara fuzgar mutanen wurin.
Kana kuma da yadda suke tafiya ammane da juna, tana k'ara cukwikwiyesa, kai kace wani zai k'wacesa idan ta sake sa.

Ahaka sukai ta ratsa jama'a duk inda suka huce sai an kallesu, domin kuwa masu tafiya ma har d'an tsayawa wasu sukeyi, su kuwa masu sana'a gaba d'aya sakin abun da sukeyi sukai, suna masu binsu da idanu, wanda hakan kuma ya sanya gaba d'aya sukaji sunyi matuk'ar takura, sabo da sudai basuga abun kallo ajikin su ba da ake musu wannan mayen kallon, ahaka har suka fuce daga cikin tashar gaba d'aya.

Tsaye sukai abakin titi ba tare da sun k'ara takuba.

Ahankali kana kuma cikin sanyi Gimbiya Tsmir ta bud'e baki tana mai fad'in.
"To yanzu ya zamuyi Jarumi?"

Fesar da iska Bir yayi, tare da lumshe dara-daran idanuwansa.
Kana daga bisani ya bud'esu akan fuskarta, tukun ya bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Tinanin da nake kanyi kenan."

Tukun yayi shiru yana mai jaye idanuwansa daga cikin nata, ya mayar dasu kan titin yana mai kallon wurare.

Cak ya tsaya da idanuwansa akan wani tank'asheshen store da yake cike da kayan abinci tundaga waje har zuwa cikinsa.
Tukun daga bisani ya janye idanuwansa daga kansa yana mai fesar da iska.
Kana ya sake kallon Gimbiya yana mai cewa.

"Kinga tawo muje wancan babban shagon, in yaso sai mu tambayi mutumin ko yasan wurin da ake siyar da gidaje."

Jinjina masa kai tayi ba tare da tace komai ba, tukun ta janye idanuwanta daga cikin nasa.
Kana suka fara d'aga k'afafuwansu suna masu dosar tank'asheshen shagon da yake kallonsu, yayinda shi kuma Al'majirin da yake rik'e da jakarsu yake biye da su.

Wata irin matsananciyar harbawa zuciyar Bir tayi da azabar k'arfi, adai-dai lokacin daya d'ora k'afarsa d'aya akan tiles d'in da yake abakin k'ofar shiga store d'in.
Kafin daga bisani kuma jikinsa ya d'auki 'yar kyarma, yana mai zaro idanuwansa waje, sabo da k............✍

tashe, suna masu yowa kanta.

"Na shiga ukku na lalace, wayyo Dady wayyo Momy mutuwa zanyi Prince ya cuceni."

Ta fad'a da wani irin k'araji tana mai cizge ribom d'in kanta tare da warwatsa gashin kanta, bayan ta zube gwiwoyinta ak'asa.

"Innalillahi wa'inailahir raji'un, meya farune me Prince d'in yayi miki? Dauhgter! Daughter!!!"

Daga Momyn nata har Dadyn ta suka fad'a a matuk'ar rud'e suna masu rige-rigen kamata.

Wayyo Allah na zuciyata bugawa zatayi, Prince ya cuceni ya hulak:antani wayyo Momy mutuwa zanyi!"

Ta sake fad'e tana mai sake zubewa ak'asa tare da dukan lallausan capet d'in cikin d'akin da hannunta.

Hakan da mai Girma Gwamna ya ganine ya sanya sa shirin fucewa waje, hankali abala'in tashe da niyyar yaje yasa ajiyo masa labarin abunda Asad yayiwa 'yarsa, sabo da ganin da sukayi tak'i fad'a musu.
Akuma lokacin ne suma su Zee suka shigo cikin falon.

Hakan yasasa dakawa a wurin yana mai fad'in.

"Me Asad yayiwa Bilkisu ne? Ku fad'a mun mai yayi mata yauma?"

Zee ce ta bud'e baki tana mai fara zanyo masa duk abun da ya faru, har karuwar daya kirata da shi kuwa.
Kana ita kuma d'ayar ta zaro wayarta tana mai kunna datar ta ta huce IG direct, sannan ta nunowa Dadyn Billy fuskar wayar tana mai fad'in.

"Kaga fa irin cin mutuncin da yay mata Dady, yanzu gashinan har jama'a sun samu gaba d'aya labarin da ake a kowace kafar sadarwa yau kenan.

Tunda Zee ta fara karanto musu abunda ya faru gaba d'aya daga shi har Momyn Billy sukayi suman tsaye, suna masu binta da idanuwa tare da saurarenta, kana kuma bayan ta gama suka d'ora da kallon videon da d'ayar ta hasko musu.

"Yanzu ni wannan Yaron zai hulak'anta haka, kamarni za'aciwa mutunci aduniya, hak'ik'a ba iya ke kad'ai yayiwa ba, koma nace ni yaron nan yaciwa mutunci bake ba, dan haka bance ko wayarsa ki kira ba daga yau, gobe zamuje har gaban iyayensa ayi komai ya huce."
Cewar mai girma Gwamna ransa a mugun b'ace yana mai kama hanyar waje ya fuce da matuk'ar sauri.
Hak'ik'a tunda yake a rayuwarsa bai tab'a jin ransa ya b'aci ba irin yau, sabo da ba k'armun hulak'antasa Asad yayiba, domin kuwa ya riga daya sani wannan abun har siyasarsa sai ya shafa, wai kamar shi 'yarsa ta cikinsa aka samu wani ya hulak'anta, har kuma ya kirata da karuwa acikin jama'a.
Tabbas da ace Asad ba d'an wani bane shima, da daga yau bazai k'ara ko shurawa ba a duniya, bayan haka kuma da abun ya shafi karankaf danginsa.
Sai dai a yanzun ma baya tinanin zai iya hak'ura, bari dai kawai goben tayi suje wurin Iyayensa, sai suji irin matakin da zasuce zasu d'auka.

Ya raya haka acikin ransa yana mai zaro wayarsa domin ya kira abokinsa Alhaji saleh, da sukaje tare da shi a wancan karan.

*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Cikin tsantsar tashin hankali Sarki Barbaru ya k'arasa bakin k'ofar d'akin Gimbiya, yana mai bugata tare da fad'in.

"'Ya! 'Ya!! 'Ya!!!"
Yake fad'i da wani irin k'arfi, yana mai cigaba da buga k'ofar, sabo da jin da yayi shiru bata bud'e ba.

Da gudu matansa suka k'araso cikin falon hankulansu a tsantsar tashe, sabo da sautin bugun k'ofar da sukajiyo da k'arfi.

Shi kuwa Sarki Barbaru jin da yayi shiru har sama da minti biyar yana bugun k'ofar tare da kiran sunanta ba tare data bud'e ba, ya sanya barin jikin k'ofar yana mai komawa wurin window tare da sanya hannunsa ya turasa da k'arfi.

"K'asss! Kakejin k'arar karyewa sakatar jikin windown, yana mai matsawa gefe.
Kana Sarki Barbaru ya k'ara zuwa kansa yana mai waige-waige tare da kiran sunanta.
Kafin daga bisani kuma ya koma yayi tsit yana mai zare idanuwa, tare da wuwwurgasu cikin d'akin, sabo da yadda yaga ko k'yallinta bai hangoba, saima wasu daga cikin kayanta daya gani zube ak'asa.

"Ina Gimbiya ta shiga ne yau?"

Ya fad'a yana mai juyawa ya kalli matansa.

"Tana ciki ai gaba d'aya yau bama ta futo waje ba."

"Gimbiya Salwa ta fad'a da sauritana mai jin yadda k'irjinta ke wani irin bugu da tsantsar k'arfi.

"Me kike nufi da bata futoba, bayan kuma gashinan babu ita acikin d'akin?"

Ya k'arasa maganar da k'arfi yana mai juyawa da matuk'ar sauri ya doshi waje, domin yaje ya shiga ciki ta hanyar baya ya dubata sosai.
Da gudu suma matansa gaba d'aya biyun harma da sauran 'Ya'yansa sukabi bayansa hankulansu atsantsar tashe.

Suna futowa wajen suka had'e da jama'ar da suka tawo tare harda Boka mai hutar kasko.
Kana gaba d'ayansu suka had'u suna masu hucewa baya.
A kuma lokacin su Gimbiya Salwa da Haiwai sukaji labarin kashe dakarun bakin k'ofa da akace Shairama tayi, wanda hakan kuma ya sanya su sake matuk'ar rud'ewa suma.

Tundaga nesa suka hangi k'ofar abud'e, hakanne ya sanya Sarki Barbaru ya k'ara saurinsa tamkar ya kifa ak'asa.
Yayinda ita kuma Gimbiya Salwa take had'awa harda d'an gudunta, gaba d'ayanta a tsantsar rud'e.

Gaba d'ayansu suka danna kansu zuwa cikin d'akin alokaci d'aya, sai dai kuma abunda suka ganine ya sanya su tsaywa cak a wurin da suke, suna masu baza idanuwa a kowace kusurwa ta d'akin, zuciyarsu na tsananta bugu.
Sabo da ganin da sukayi na babu Gimbiya babu alamunta kuma.

Kafin daga bisani kuma Mahaifiyarta ta zura aguje tana mai bankad'a k'ofar bathroom tare da danna kanta ciki.

"Tasmir! Tasmir!! Tasmir!!! Kina inane ki futo mana, 'Yata wai ina kika shiga ne."

Ta fad'a cikin wani irin k'araji, tana mai fara zagaye acikin tank'ashe-shen bathroom d'in
Kafin daga bisani kuma ta zura aguje tana mai fucewa, hawaye na b'allewa daga cikin idanuwanta ta.

"Batanan wallahi, batanan na duba banga Gimbiya ba ku taimakeni ku nemomun ita. "

Ta fad'a a wani irin firgice tana mai sakin wani irin kuka da matuk'ar k'arfi, domin kuwa haka kawai jikinta ya bata ba lafiyaba tun da taji abunda akace Shairam tayi.

Shi kuwa Sarki Barbaru a wani irin haukace ya juya b'arin da Boka mai hutar kasko, yake yana mai fad'in.

"Kanaji ko, kanji ko Boka mai hutar kasko, kana jin abunda take cewa wai bataga 'Yata ba. Na rok'eka kayi maza kai binciko mun inda ta tafi."

Sarki Barbaru ya fad'a a haukace yana mai riga Boka mai hutar kasko fucewa.

Hakan yasa shima Boka mai hutar kasko rufa masa baya suka tafi domin aje ayi bincike
Yayinda suma gaba d'aya sauran Jam'ar harma da wa'yan da basu san da abun ba da sukaji suka had'u suka tafi zuwa d'akin Boka mai hutar kasko.
Ita kuwa Gimbiya Salwa banda aikin gurshk'en kuka babu abun da takeyi, a haka har suka k'arasa bakin k'ofar d'akin.

Boka mai hutar kasko ne ya fara shiga ciki, tukun Sarki Barbaru yabi bayansa, kana su Gimbiya Salwa ma da duk sauran 'Ya'yan sa suka danna kansu ciki.
Yayinda su kuma sauran jama'ar tasu sukayi tsaye cirko-cirko abakin k'ofar, hankulansu a tsantsar tashe.

Aciki kuwa basu tsaya ba har sai da suka dangana da da wurin da kayan aikin Boka mai hutar kasko suke.

K'ullukan tsummokarnsa da layoyinsa ya d'auko.
Kana yasa kaskon huta a gaba, su kuma su Sarki Barbaru suka
tsaye daga gefe suna kallonsa.

Cikin sauri ya fara kwance k'ullikan tsummokaran, kana ya mik'e tsaye bayan ya dunk'ule wasu layoyin acikin tafin hannunsa, tukun ya fara zuba abubuwan acikin hutar dake ci yana mai yin wasu irin surutai tare da rumtse ido.

Ya d'auki dan tsayin lokaci yana yi, kafun daga bisani kuma ya tsaya yana mai bud'e idanuwan nasa.
Koriya shar yaga hutar ta dawo daga jar da take.
Hakan yasa sa sake matsawa jikin kaskon, yana mai kai idanuwansa cikin tsakiyar hutar.

Da sauri, kana kuma cikin tsantsar firgici, rud'u, had'i da tashin hankali ya d'ago idanuwansa, yana mai watsasu akan fuskar Sarki Barbaru, jikinsa na kyarma!

K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI.*

K'arfe shad'aya da rabi na safe dai-dai motarsu ta tsaya acikin tashar da take a tsakiyar cikin garin Wasai.

Cikin farinciki mutanen cikin motar suka fara furfutowa.
Yayinda Gimbiya Tasmir da Bir kuma sukayi shiru suna masu kallon junansu.
Hakanan kawai sukaji gaba d'aya jikinsu yayi sanyi, sabo da rashin ta inda zasu fara yanzu idan sun sauka da basu sani ba.

Ganin da Bir yayi gaba d'aya mutanen cikin motar sun fuce, sai sukad'ai ne kawai sukai saura, ya sanyasa yunk'urawa shima yana mai fad'in.

"Mu futa ko Gimbiyata."

'Daga masa kai kawai ta iyayi ba tare da tace komai ba, domin kuwa haka kawai takejin tamkar ta fashe da kuka, ga wani irin abu da taji ya tokare mata ak'irji.
Yayinda cikin zuciyarta kuma take cike da tinanin halin da ahalinta suke aciki yanzu.

Bir ne ya fara fucewa, tukun itama ta biyo bayansa.
Dasauri ya lumshe idanuwansa, yana mai jin zuciyarsa na wani irin harbawa da tsananin k'arfi.
Sabo da yadda iskar garin ta daki gangar jikinsa a lokacin daya futo.
Cikin sanyi jikin daya ziyarce su gaba d'aya daga shi har ita, suka fara d'aga kai suna masu kallon yadda wurin yake
Kasancewar kuma ranar yau d'in da zafinta ta bud'e, shiyasa gumi ya fara tsattsafo musu ajiki, domin kuwa ko ba rana ma dolene suji zafin garin, duba da irin yanayin wurin da suka baro.

"Yawwa Malam ga jakun-kunan ku ko."
Drivern motarsu ya fad'a yana mai nuna musu su ak'asa.

Hakan yasa Bir yin wurin jakun-kunan asanyaye yana mai sanya hannu ya d'aukosu.

Ita kuwa Gimbuya Tasmir da sauri ta matso jikinsa, tana mai d'an nanik'e masa, sabo da yadda taga idanuwan kusan duka jama'ar dake wurin ya dawo kansu.
Shiyasa gaba d'aya taji tsoronsu ya lullub'eta, domin kuwa sai take zaton kamar sun take wata dokarce shiyasa har ake kallonsu haka.

Su kuwa mutanen dake kallonsu, ba komai bane ya janyo hankulansu zuwa garesu sai tsananin kyawun da suka gansu da shi.
Ga kuma irin shigar da take sanye ajikin Gimbiya Haddiyal, sabo da sudai har dai ba inyamurai ba basu saba ganin mace budurwa na yawo babu ko d'an kwali akanta ba.
Hakan yasa suka fara tinanin kosuwaye sud'in to ba 'yan k'asar nan bane ba, yayinda wasu kuma suka fara fad'in larabawa ne, sabo da mayawaicin bak'in gashin Gimbiya Tasmir da suka gani ya sauko har kusan k'ugunta.

Da sauri ta rik'e hannun Bir tana mai mannewa ajikin sa, tare da durk'usar da kanta k'asa jikinta na 'yar rawa.
Hakan da Bir yajine ya sanyasa fesar da iska.
Kana ya d'an durk'usar da kansa k'asa, yana mai kawo bakinsa saitin kunnenta, tukun yayi mata rad'a da cewar.

"Ki bari na d'auki jakar mutafi ko, babu abunda zasuyi mana kinji."

Ya fad'a asanyaye shima tamkar maijin tsoron, sabo da yadda yake jin zuciyarsa na cigaba da bugawa da k'arfi.

'Dada masa kai tayi a hankali tana mai d'an matsawa, amma sai dai kuma duk da haka bata saki yatsunsa ba data rik'e su.
Wanda hakan kuma shi ya k'ara janyo hankulan jama'a kansu, sabo da su dai hausawa da kunya mace da namiji suyita nanik'ewa junansu akan titi, koda mata da mijine kuwa.

"Gimbiyata rigima ko."
Ya fad'a yana mai d'an sakar mata murmushi.
Kana ya durk'usa yana mai shitin d'aukar jakun-kunan nasu, amma sai yaji wani al'amaji agefensa yana mai fad'in.

"Ina za'a kaine Alhaji?"

"Yawwa yaro d'aukar mun wannan."

Bir ya fad'a yana mai nuna masa ta kayansu, kana shi kuma ya d'auki ta kud'in ya rik'e a hannu, wanda hakan da yayin kuma shi ya sake bawa Gimbiya Tasmir damar samun rik'e hannun nasa, tare da k'ara shigewa cikin jikinsa sosai.
Tukun suka fara d'aga k'afafuwanu a tare, suna masu ratsa cikin mutanen domin subar tashar.

Yuuuuu!
Haka ake binsu da idanu harda masu waigensu.
Ba kuma komaine yake ta janyo hakan ba, sai rashin d'ankwalin da yake akan Gimbiya, sai zallar doguwa rigar jikinta da takalmi kawai, ga kuma shi kansa kyawunsu da yake k'ara fuzgar mutanen wurin.
Kana kuma da yadda suke tafiya ammane da juna, tana k'ara cukwikwiyesa, kai kace wani zai k'wacesa idan ta sake sa.

Ahaka sukai ta ratsa jama'a duk inda suka huce sai an kallesu, domin kuwa masu tafiya ma har d'an tsayawa wasu sukeyi, su kuwa masu sana'a gaba d'aya sakin abun da sukeyi sukai, suna masu binsu da idanu, wanda hakan kuma ya sanya gaba d'aya sukaji sunyi matuk'ar takura, sabo da sudai basuga abun kallo ajikin su ba da ake musu wannan mayen kallon, ahaka har suka fuce daga cikin tashar gaba d'aya.

Tsaye sukai abakin titi ba tare da sun k'ara takuba.

Ahankali kana kuma cikin sanyi Gimbiya Tsmir ta bud'e baki tana mai fad'in.
"To yanzu ya zamuyi Jarumi?"

Fesar da iska Bir yayi, tare da lumshe dara-daran idanuwansa.
Kana daga bisani ya bud'esu akan fuskarta, tukun ya bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Tinanin da nake kanyi kenan."

Tukun yayi shiru yana mai jaye idanuwansa daga cikin nata, ya mayar dasu kan titin yana mai kallon wurare.

Cak ya tsaya da idanuwansa akan wani tank'asheshen store da yake cike da kayan abinci tundaga waje har zuwa cikinsa.
Tukun daga bisani ya janye idanuwansa daga kansa yana mai fesar da iska.
Kana ya sake kallon Gimbiya yana mai cewa.

"Kinga tawo muje wancan babban shagon, in yaso sai mu tambayi mutumin ko yasan wurin da ake siyar da gidaje."

Jinjina masa kai tayi ba tare da tace komai ba, tukun ta janye idanuwanta daga cikin nasa.
Kana suka fara d'aga k'afafuwansu suna masu dosar tank'asheshen shagon da yake kallonsu, yayinda shi kuma Al'majirin da yake rik'e da jakarsu yake biye da su.

Wata irin matsananciyar harbawa zuciyar Bir tayi da azabar k'arfi, adai-dai lokacin daya d'ora k'afarsa d'aya akan tiles d'in da yake abakin k'ofar shiga store d'in.
Kafin daga bisani kuma jikinsa ya d'auki 'yar kyarma, yana mai zaro idanuwansa waje, sabo da k............✍

*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_

UMAR FARUQ*D*

*20*

Kansa da yay wata irin sarawa, wanda har hakan ya sanyasa d'an cije leb'ensa da k'arfi, tare da rumtse idanuwansa.
Kana daga bisani ya bud'esu yana mai jin yadda bugun zuciyarsa ke k'ara tsananta
Tukun ya k'arasa tura kansa cikin store d'in Gimbiya Tasmir na manne dashi, yayinda shi kuma Al'majirin nan ke biye dasu abaya.
Akuma dai-dai lokacin shima Sheikh Ahmad daya gama biyan kud'in siyayyar da yayi ya juyo da niyyar futowa.

Dam! Dam!! Dam!!!
Zuciyoyinsu sukayi wata irin mahukaciyar bugawa alokaci d'aya, idanuwansu na sark'ewa a cikin na juna.
Ita kanta Gimbiya Tasmir da sauri ta d'an janye jikinta daga jikin Bir, tana mai mik'ewa tsaye tare da zaro manyan idanuwanta ta zubasu akan fuskar Sheikh Ahmad, sabo da tsananin kamar da taga yanayi da Jaruminta.

Shi kuwa Sheikh Ahmad da Bir kafe junansu sukayi da idanu, ba tare da wani ya iya ko da k'wak'k'waran motsi daga yadda yake ba, yayinda zuciyoyinsu kuma suka cigaba da bugu da tsananin k'arfi a tare.
Gaba d'ayansu suna masu jn wani irin yanayi na huda k'ashi da tsokar su yana kwaciya a cikin jininsu.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir a hankali ta janye idanuwanta daga kan fuskar Sheikh Ahmad, tana mai mayar dasu kan fuskar Bir ta kallesa, kana kuma ta sake mayar dasu zuwa kan fuskar Sheikh Ahmad, gaba d'aya mamakin irin kamar da tagani a tare da su tayi matuk'ar girgizata.

Shi kuwa Sheikh Ahmad gaba d'aya ji yayi ya rasa kuzarinsa, sabo da ganin matshin yaron da yayi, wanda ko kad'an basa da maraba da Umminsa.
Hak'ik'a da ace macece kuma babba kamar Umminsa, da babu abun da zai hanasa ya dage yace itace ya gani.

Sun jima suna kallon juna ba tare da wani ya iya ko da kwakkwaran motsi a cikinsu ba, kafin daga bisani kuma Sheikh Ahmd ya janye idanuwansa daga kan fuskar Bir, yana mai fesar da iska.
Kana ya d'an juya bayansa jiki asanyaye yana mai fad'in.

"Yawwa kasa su kawo mun kayan cikin mota."

Ya fad'awa mai shagon, kana ya juyo ba kuma tare daya sake d'aga kai ya kalli Bir ba yace masa.
"Sannu ko."

Tukun ya fara d'aga k'afa jiki asanyaye yana mai nufar hanyar waje.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir tini ta k'ara sandarewa a wurin, sabo da yadda taji hatta da muryarsu sak iri d'aya data jaruminta.

Da k'arfi ta rumtse idanuwanta, sabo da yadda taji k'wak'walwarta na wani irin juyawa, kana tinanin-nika barkatai na fad'owa cikinta.

Shi kuwa Bir har Sheikh Ahmad ya huce ta gefensa bai iya d'aga ko lab'b'ansa ba, ballantana kuma ya iya amsa sannun da yayi masa, sabo da yadda yaji gaba d'aya komai na jikinsa yayi nauyi, sabo da kawai ganin bawan Allah'n da yayi, sai dai kuma ko kad'an cikin wani ikon Allah bai kawowa kansa cewar ko d'an uwansa bane ba.

"Me kuke sone Yallab'ai."

Muryar me siyar da kayan ta daki dodon kunnuwansu daga shi har Gimbiya Tasmir, wanda hakan ya sanya su dawowa cikin hayyacinsu gaba d'aya.
Tukun Bir ya bud'e baki a wani irin fuzge, yana mai fad'in.

"Gida!"

Cak Sheikh Ahmad daya zura k'afarsa d'aya waje yana shirin futa ya tsaya a bakin k'ofar, sabo da muryar da yaji mai kama da tasa zam yana fad'in wai Gida zai siya anan d'in, wanda kuma ya tabbatar da cewa wanan matshin yaron daya ganine yayi maganr, duk da dai baiga lokacin da yayin ba ma, sabo da babu wani a cikin shagon bayanshi da kuma masu siyar da kayan, sai su d'in da suka shigo yanzu, shiyasa yasan shi d'in.

Shi kuwa mai shagon cikin tsantsar mamki ya bud'e baki bayan ya wurgawa Bir wani irin kallo mai kama dana anya ko kana cikin hankalinka, yana mai fad'in.

"Gida kuma? Anan d'in?"

Rumtse ido Bir yayi da k'arfi, sabo da yadda yake jin zuciyarsa na cigaba da harbawa da k'arfi, kana yana mai jin wani irin abu na fuzgarsa dan gane da mutumin daya bar gabansa, wanda har hakan ya sanyasa cewa gida ba tare daya shirya fad'in hakan ba.
Kana daga bisani ya bud'esu yana mai fad'in.

"Bak'ine mu a garin, shine muke son samun gidan zama zamu siya ne, kuma bamu san ta inda zamu fara ba."

Da sauri Sheikh Ahmad ya juyo gaba d'ayansa, yana mai sake zuba idanuwansa akan bayan Bir da yaji yace bak'ine su.
Lokaci d'aya kuma wani tinani ya fad'o masa, tare da wata dabara.
Hakanne ya sanya sa komawa ciki jiki asanyaye.

Shi kuwa mai shagon jin da yayi Bir yace masa bak'ine su, kuma siya suke son yi, ya sanyasa d'an washe baki, sabo da yasan dolene ma ya samu dasu ba k'aramun samuba, kafin daga bisani kuma ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Ah barkanku da zuwa bak'i, gida kuwa kun samesa kun ga..."

"Afwan mai shago fa dan Allah."
Sheik Ahmda ya katsesa da fad'in haka ba tare daya bari yakai k'arshen maganar da yakewa su Bir ba.
Tukun ya juya yana mai mik'awa Bir hannu tare da fad'in.

"Ni sunana Sheikh Ahmad. Nace mai zai hana ku biyoni na kaiku wani gidana ku gani ko zai muku, tunda naji gidan kuke nema?"

Da sauri Bir ya d'aga kai yana kallonsa, ba tare daya iya mik'a masa hannun ba, sabo da abun da yaji ya fad'a.
Yayinda shi kuma mai shagon nan harma da sauran yaran shagon suka saki baki suna masu zuba idanuwansu akansu, gaba d'aya mamaki ya gama kashesu, sabo da tsananin kamar da suka gani a tattare dasu, wacce da su duk basu lura dasu ba sai yanzu.

Shi kuwa Sheikh Ahmad ganin da yayi yaron ya kasa cewa komai, sai kallonsa kawai da yake yi, ya sanya sa girgiza masa kai tare da fad'in. "Muje ko."

Ya k'arasa maganar yana mai janye hannunsa da ya mik'a masa suyi musabaha, tare da dafa kafad'arsa.

Da sauri Bir ya lumshe idanuwansa, sabo da saukar hannun bawan Allah'n da yaji akan kafad'arsa, wanda hakan yasa yaji tamkar har zuciyarsa ya tab'a.
Tukun daga bisani ya fesar da iska, yana mai jinjinawa Shiekh Ahmad kai.
Kana ya juya wurin Gimbiya yana mai fad'in.

"Mu bisa ko Gimbiyata?"

Jinjna masa kai kawai itama ta iyayi ba tare da tace komai ba.
Tukun Sheikh Ahmad ya k'ara sakin murmushi, sabo da yadda yaga kamar gaba d'ayansu a tsorace suke, gashi kuma ma dai daga ganinsu zaka san amarya da angone su d'in, saboda yadda sukayi matuk'ar dacewa da juna, sai dai kuma sosai mamakin ganin macen a haka babu ko d'an kwali a jikinta ballantana kuma lullub'i ya rufesa, da kuma ya tina sunce su bak'ine, sai yayi tinanin maybe haka su al'adarsu take a k'asarsu.
Tukun ya sake damk'o tafin hannun Bir yana mai rumtsesa a cikin nasa.
Kana ya fara yin gaba wanda hakan ya sanya dole suka rufa masa baya suma.

Suna gab da futa ya juyo yana mai kallon mai shagon tare da fad'in
"To sai da anjimanku ko."

Jinjina masa kai kawai mai shagon ya iyayi, sabo da tsananin mamakin da yake aciki.
Yayinda acikin zuciyarsa kuma yake fad'in.

"Amma wannan babban Mamalin d'an hulak'ancine ashe dama, in banda rainin hankali taya

Please Login or Register in order to submit comment