Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskarsa kika sakeyi kafun nabar wurin nan, saina saki kin gane baki da wayo.
Domin kuwa Gid'ad'o nawane ni kad'ai. Na rantse da girman Allah babu wata mace data isa ta rab'esa bayan ni, nice na dace dashi, kuma nice tasa dani zaiyi rayu...

"Idan har kika k'ara kuskuren barin bakinki ya k'ara furta kalmar Jarumina naki ne, ina mai tabbatar miki da sai nasa almakashi na datse harshenki.
Domin kuwa Jarumi nawa ne kad'ai, ni yasa ni, kana kuma ni kad'aice mallakinsa."

Gimbiya Tasmir ta katse Gimbiya Haddiyal da fad'in haka cikin wara irin gigitacciyar tsawa mai tsananin firgitarwa.
Wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da Ummi, Kaka, Iman, matar Sheikh Ahmad, tare da sauran ma'aikatan gidan suka k'araso wurin.

Sosai hankalinsu yayi matuk'ar tashi, saboda furucin da sukaji kyawawan 'yammatan sunayi gaba d'ayansu, babu alamun rahama akan fuskokinsu.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal wata irin tafarfasa da k'una taji zuciyarta nayi, saboda furucin da Gimbiya Tasmir ta sakeyi.
Hakanne yasata juyawa b'arin da Bir yake tana mai kai idanuwanta kansa.
Kana ta bud'e baki cikin wani irin sauti tana mai fad'in.

"Wacece ita a wurinka? Ina son ka bud'e bakinka a yanzu ka fad'a mata ko ni d'in wacece a gareka.
Nice nan Haddiyal d'inka d'iyar Sarkin Fuld'e, masoyiyarka wacce muke rayuwa tare da kai aduk daren duniya cikin mafarki.
Shekaru da dama na d'auka ina binciken wurin da kake, amma ban ganosa ba sai jiya.
Dan haka wallahi idan duk mutanen duniya zasu taru, basu isa su rabani da kai ba, sannan kuma babu wata d'iya macen data isa ta rab'eka muddin ba itace ta kaw..."

"Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Idan har kika cigaba da danganta Jarumina da naki zanyi miki babbar illa kafun kibar gidan nan, domin kuwa Bir na wane ni kad'ai.
Na bar kowa na bar komai nawa dominsa, dan haka kuma zan iya aikata komai akansa! Wannan gargad'ine nayi miki, idan har kinji to kin tsira, idan kuma bakijiba to tabbas zan miki ta yadda zakiji. Domin kuwa akan Jarumi zan iya aikata komaiii...!!!"

Gimbiya Tasmir ta fad'a cikin wani irin k'araji da hargowa, gaba d'aya launinta na sauyawa.
Wanda hakan da Ummi ta ganine kuma ya sanyata d'ora hannu aka cikin matsanancin tashin hankali da firgici, tana mai fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Meye hakan yake shirin faruwa a gidana?"

Yayinda Iman da matar Sheikh Ahamd kuwa tuni suka fashe da kuka, saboda firgitar da sukayi da ganin yadda Gimbiyoyin biyu suke sakin wani irin huci, tare da furta kalmomi masu muni ga junansu.

Ita kuwa Kaka wata irin shewa ta kwashe da ita, tana mai fad'in.

"Masha Allahu, ke ko d'iyar Fillo daga ina haka kikazo kiyimun maganin kafurar nan?
Kai koma dai daga ina kike ni wannan bai dameni ba tunda har naji kema son Jikana kikeyi, dan haka na rantse da Allah kece zaki auresa, dama bason kafurar nan nake tare dashi ba.
Yo me ma za'ayi da jinin kafurai, bayan ga Musulma kuma 'yar uwarmu 'yar Fulani, tabbas kwantar da hankalinki Yarinya Biro naki ne. Ke kuma me idon mayu da kike wani wuro hanci kina kumbura, to kisani ko fashewa zakiyi wallahi bazan guji jinin fuld'e ba naso bare, baren ma kuma tsatson masu fitsari a tsaye ba tsarki."

Kaka ta k'arasa maganar tana mai matsawa kusa da Gimbiya Tasmir ta dunguri kanta, tukun taja baya tana mai zuwa ta shafi gefen fuskar Gimbiya Haddiyal tare da sakar mata murmushi.

Shi kuwa Bir gaba d'aya kasa motsi yayi a wurin da yake, banda aikin binsu da idanu babu abun da yake iyayi.
Sosai ya fahimci abun da magan-ganun kyakkyawar bafullatanar da yaji tace 'yar Sarkin Fulanice ita suke nufi.
So yake ya tashi ya janye Gimbiya daga wurin, amma gaba d'aya yaji ya kasa yin hakan kwata-kwata, asalima sai zuciyarsa ke raya masa cewar muddin yayi hakan tamkar ya hulak'anta ita wannan yarinyarce da take fad'in ta dad'e tana dakon sonsa suna a had'uwa a mafarkinta.
Wani irin abu yakeji dan gane da bafullatanar na lullub'esa, ta yadda har ya kasa janye k'wayoyin idanuwansa daga kan fuskarta.

Jin furucin da Gimbiya Tasmir tayi ne ya sanya Gimbiya Haddiyal taji zuciyarta ta k'ara dugunzuma.
Lokaci d'aya taji tsanarta ta lullub'e gaba d'aya zuciya da ruhinta.
Hakan yasa itama ta bud'e baki tana mai cewa.

"A duk duniya, banga 'ya macen data isa ta shiga tsakanina da Gid'ad'o am ba, domin kuwa ina yi masa sone irin son..."

"Dan girman Allah Baiwar Allah kiyi hak'uri mana, shin ke d'in wacece ma da zakizo kinemu tayar mana da hankali?"

Ummi ta katse mata maganar da take da fad'in haka, tana mai dafa kafad'arta cikin matsanancin firgici.
Yayinda idanuwanta kuma suke zubar da k'wallar tashin hankali.

Hakan da Gimbiya Haddiyal tajine ya sanyata jin zuciyarta tayi rauni.
Lokaci d'aya kuwa sai ga ruwan hawaye nan sun b'alle daga cikin idanuwanta da tsananin gudu, kana ta juya b'arin da Ummi take tana mai watsa idanuwanta akan fuskarta.
Tukun ta bud'e baki cikin kuka tana mai fad'in.

"Ke d'in nasan Mahaifiyarsace, dan haka zan baki amsar tambayarki yanzu.
Ni d'in masoyiyarsace, nasosa tun kafin insan meye so, na sosa tun ina da k'arancin shekaru har nazo na girma. A duk daren duniya da mafarkinsa nake kwana, haka idan gari yawaye da zarar na lumshe idanuwana shi nake gani. Nayi bincike iyakar bincike domin na gano inda yake, amma ban gano ba, nayi kuka tamkar hawayena zasu k'afe ta silar sonsa, gaba d'aya jama'ar masarautarmu suna mun kallon wacce Aljanu suka shafa ta sanadinsa, ciki kuwa harda Iyayena. Samari da dama 'ya'yan Sarakai da Attajirai sunzo wurina da sunan soyayya, amma sai dai kuma ko darajar kallo basa samu daga gareni, ballantana kuma na kulasu, duk saboda ina ganin tamkar idan nayi hakan ban masa adalciba, kana kuma naci amanarsa, saboda baya a kusa. Amma shi kuma kinga abun da yayi mun Mama, kinga sakayyar da yayi mun akan soyyar da nake masa, amai-makon ace yau d'in dana ganosa nazo na tararar dashi d'inma yana jirana, amma sai na samu akasin hakan, asalima bai sanniba har da wata macen yake tare a gefensa.
Zuciyata na zafi Mama, zuciyata tana rad'ad'i Mama, kuma wallahi tallahi idan kikace bazaki bani shiba bugawa zatayi! Zan mutune gaba d'aya in bar duniyar da soyayyarsa a zuciyata, saboda inayi masa sone irin son da babu maiyi masa makamancinsa aduniya, ina sonsa irin....

"K'arya kike! K'arya kike mak'aryaciya!! Kuma idan har kikai kuskuren k'ara mai-maita abun da kika fad'a a wurinnan, zan illatakine yanzu a take, saboda Bir na wane ni kad'ai."

Gimbiya Tamsir ta fad'a da wani irin k'araji, jikinta na d'aukar wata irin matsananciyar kyarma.

"Kafin ki illatani ni zan fara illataki, sabo da alk'awarine na d'aukarwa kaina na cewar ba zan tab'a barin wata mace ta rab'i Gid'ad'o am ba, idan kuma har nasame sa da ita, to tabbas daga ranar zasu rabene rabuwa ta har abada."

Cewar Gimbiya Haddiyal a wani irin haukace, tana mai d'ago sandar tsafinta da wani irin sauri adai-dai lokacin da itama Gimbiya Tasmir ta zaro takobinta da take acikin aljihun rigarta, suna masu d'agosu atare suka nuna junansu da su.
Tukun suka bud'e baki cikin wani irin k'araji da hargowa, suna masu rumtse idanuwansu, ita Gimbiya Tamsir na fad'in.

"Shairamaaaaaa!!!"

Yayinda Gimbiya Haddiyal kuma tace.

"Zaibaaaaaaaa!!!"

Take kuwa dank'areriyar macijiyar nan ta bayyana asama tana mai karkad'a harshenta tare da tunkarar kan Gimbiya Haddiyal gadan-gadan. Sai dai kuma kafun ta kaiga isa wurinta saiga wasu irin malam bud'amana littafinan sun futo a cunkushe masu matuk'ar yawa bakyan gani daga jikin tsinin sandar Gimbiya Haddiyal, suna masu yin kan macijiyarnan.
Hakan kuwa shi yasa sukaci karo da junansu.
Take kuwa daga macijiyar har malam bud'emana littafin suka zube a k'asa wanwar.
Ganin hakan da Gimbiya Haddiyal tayine ya sanyata sake d'ago sandarta cikin zafin nama, tana mai k'ara nuna Gimbiya Tasmir da ita tare da sake fadin.

"Zaibaaaaa!"

Take kuwa wasu malam bud'a mana littafin suka sake bayyana a cunkushe suna masu tafiya saitin idanuwan Gimbiya Tasmir aguje.

Cikin wani irin zafin nama Gimbiya Tasmir ta durk'usa k'asa, wanda hakan kuma ya sanya malam bud'amana littafin suka huce suna masu tarwatsewa ba tare da sun caki idanuwanta ba tamkar yadda Gimbiya Haddiyal taso.
Tukun tana tashi d'agowa itama ta sake fad'in "Shairama." Tana mai nuna saitin k'awon zuciyar Gimbiya Haddiyal da takobin.

Aikuwa da wani irin gudu macijiyar ta mik'e tana mai lauyewa asama tare da yin saitin k'awon zuciyarta ta.

Cikin wani irin zafin nama Gimbiya Haddiyal ta kife ak'asa wanwar ribda ciki, hakan yasa macijiyar wucewa tana mai fad'uwa ak'asa itama.

Yayinda Ummi kuma hankalinta idan yayi dubu sai da duka ya tashi, sabo da abun da ta gani yana faruwa acikin gidanta.
Gaba d'ayanta ta rud'e ta firgice ta gigice, jikinta na wata irin karkarwa.

Matar Sheikh Ahmad da Iman kuwa curewa sukai a wuri d'aya, suna masi sakin wani irin gigitaccen kuka na firgici da tashin hankali.

Yayinda Kaka kuna ta saki fitsari a zaninta, saboda ganin macijiyar da tayi, kafin daga bisani kuma wani irin zawo tamkar ruwa ya fara tsiyayowa a jikinta.

Shi kuwa mai gadi da sauran 'yan aikin gidan gaba d'ayansu rud'ewa sukayi, jikinsu na wata irin kyarma.

Yayinda Buba da yake acan waje kuma tare da drivern motar suka shigo cikin gidan aguje, saboda sautin hayaniyar da sukeji.

Shi kuwa Bir motsawa baiyi ba daga yadda yake, saboda shi irin wa'yannan abubuwan ba bak'in gani bane a wurinsa, shiyasa basu firgitasa ba.

Cikin zafin nama suka sake mik'ewa tsaye a tare, suna masu sakin wani irin huci tamkar namun dajin da sukaga nama.
Kana suka k'ara d'aga abubuwansu a tare kowacce na kallon 'yar uwarta.
Tukun Gimbiya Tasmir ta bud'e baki cikin wata irin murya mai matuk'ar amo, tana mai fad'in.

"Har abada Jarumi nawane ni kad'ai, bazan tab'a barin wata d'iya mace ta rab'esa ba muddin zuciya na bugu a k'rjina, saboda Bir nawane ni kad'ai kowama ya sa..."

"Zakuwa zuciyarki ta dena bugawa daga yanzu, saboda har abada Gid'ad'o am nawane ni kad'ai.
Kuma nayi rantsuwa da Ubangijin Nagge da Shalle saina kassara duk wata mace dana gani akusa da shi."

Itama Gimbiya Haddiyal ta fad'a cikin wata irin murya mai tsantsar firgitarwa.

Tukun a tare a kuma alokaci guda suka sake nuna junansu da mugayen abubuwansu, suna masu kiran Shairama da Zaiba!

Take kuwa macijiyar nan ta bayyana cikin wata irin kala, ga kuma wani irin girma data k'ara tana mai tafiya a guje zuwa kan Haddiya.
Hakan data ganine ya sanyata sanya sandarta ta maketa cikin zadin nama.

Taga-taga Macijiyar tayi baya zata fad'i, wanda hakan kuma da Gimbiya Tasmir ta ganine ya sanyata yin k'asa da takobinta da matuk'ar k'arfi, tana mai nuna k'afafun Gimbiya Haddiyal da ita.

Yayinda Ita kuma Gimbiya Haddiyal ta k'ara harar idanuwanta da wa'yannan malam bud'amana littafin da basu da kyan gani ko kad'an, sabo da curewar da sukayi a wuri d'aya.

Lura da Bir yayi na dagaske so suke suyiwa junansu lahanine, ya sanya mik'ewa tsaye a matuk'ar figice, kana kuma cikin sauri yana mai buga musu wata gigitacci'yar tsawar data sanya ko ina na cikin gidan amsawa, yana mai fad'in.

"Bazaku dena ba! Me kukeyi hakane!!"

Sai dai amma ko d'ar baiga sunyi ba ballantana suyi shrin dena abun da sukeyi, asalima sai k'ara zafi da fad'an nasu yake tsananin sakeyi, gaba d'ayansu jikinsu na wtaa irin rawa, yayinda launikan idanuwansu kuma suka sauya daga farare suna masu komawa tamkar garwashi.

Hakan daya ganine ya sanyasa yin wurin da Gimbiya Tamsir take cikin sauri da niyyar ya rik'eta, sai dai kuma tana lura da shi tayi saurin nunasa da takobinta.

Fattt!
Kakejin k'arar fad'uwarsa a k'asa bayan yayi baya.
Wanda hakan kuma ta faru akan idanun Gimbkya Haddiyal.
Ai kuwa take ta sake jin zuciyarta ta k'arayin bak'ik'k'irin, tsanar Gimbiya Tamsir na sake cakarta.

Ai kuwa cikin zafin naman da yafi duk na baya ta buga wani irin tsalle tana mai nuna tsakiyar kan Gimbiya Tasmir dai-dai saitin k'wak'walwarta da Sandar nan.
Sai dai kuma tini Gimbiya Tasmir ta lura da ita, hakan yasa kuwa tayi wani irin baya tana mai bank'arewa, kana ta d'ago cikin wani irin salo tana mai canza wuri tare da sake nuna Gimbiya Haddiyal da takobinta.

Ita kuwa Ummi sosai tak'ara firgita, tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, banda zagaye acikin compuond d'in babu abun da take iyayi, domin kuwa tayi musu magana daga wurin da take a tsaye sai dai ko alamun sunjita ma bata gani ba a tare da su.

Kaka kuwa zuwa yanzu ko motsi bata iyayi daga zaunen da take a jikin bango, yayinda acikin zuciyarta kuma take fad'in har abada bazata sake ko kallon fuskar Gimbiya Tasmir ba, ballantana ta zageta tunda dai ta gane Aljanace ita d'in ba mutumba.

Ita kuwa Iman ganin da tayi sunk'i denawane, saima gaba da abun ke k'arawa, gashi an yadda Bir ak'asa, ya sanyata b'anb'are jikinta daga cikin na matar Sheikh Ahmad tana mai rugawa a guje ta tafi cikin gidan.

Bata tsaya a ko ina ba sai acikin d'akin Ummi.
Tukun ta mik'a hannunta da da yake wata irin bala'in karkarwa tana mai d'aukar wayar Ummi.
Kana ta kamo number Sheikh Ahmad tana mai doka masa kira.

Ab'angaren Sheikh Ahmad kuwa alokacin yana tsakiyar yiwa d'alibai lecture ne yaji vibrating d'in wayarsa ajikinsa.
Har zaik'i d'auka da farko sai kuma ya zura hannu ya zarota acikin aljihunsa, alokacin tana gab da tsinkewa.
Ganin da yayi Ummice ke kiransa ya sanya sa d'aga wayar da sauri yana mai mannata akan kunnensa.

Ita kuwa Iman jin da tayi ya d'aga ne ya sanyata bud'e baki cikin matsanancin kuka, tana mai fad'in.

"Munshiga ukku Auncle, dan Allah kayi sauri kazo zasu kashe kansu katawo katawo yanzu."

"Me kikace Iman? Su wayene zasu kashe kansu? Ina Ummita? Meya sameta ne?"

Ya jero mata tambayoyin a jere, kana kuma acikin tsananin firgici jikinsa na d'aukar kyarma.
Sai dai kuma d'ip yaji ta kashe wayar ba tare data basa amsa ba.
Hakanne kuwa ya sanya sa d'aukar sistem d'insa cikin matsanancin sauri yana mai fucewa daga cikin lecture hall d'in, ba tare dako sallama yayiwa d'aliban nasaba, wanda hakan da suka ganine kuma ya sanya su sukayi matuk'ar firgita suma, domin kuwa duk a tinaninsu Ummin da sukaji ya ambaceta ta mutu.

Shi kuwa Sheikh Ahmad da gudu-gudu ya k'arasa wurin da motarsa take yana mai bud'eta.
Hulla computer d'insa yayi a gidan baya yana mai zama tare dayi mata key.
Kana yajata a wani irin haukace yana mai d'aukar hanyar get tamkar zai tashi sama.
Wanda hakan kuma ya janyo hankulan mutane da dama kansa, gaba d'ayansu suma suka firgita, sabo da fahimtar da sukayi na ba lafiyaba.

Cikin mintinan da basu huce ashirin ba ya k'arasa cikin unguwartasu da bata da yawan jama'a acikinta.

Tundaga nesa ya fara sakin horn, kwata-kwata shi ko lurama baiyiba da motar da take fake a gefen gidan nasu.
Ganin da yayi babu alamun za'a bud'e masa get d'inne, ya sanya bud'e murfin motar yana mai bugosa tare da zurawa aguje ya tura 'yar k'aramar k'ofar da take ajikin get d'in.

Tsaye yayi k'am abakin k'ofar jikinsa na d'aukar kyarma, sabo da abun da idanuwansa suke gane masa yana faruwa acikin gidan nasu.

Su kuwa Gimbiyoyin tini zuwa yanzu sun galabaita gaba d'ayansu su biyun, ta yadda har suke tangad'i gumi na yanko musu ajiki tamkar zasu fad'i ak'asa, sai dai kuma duk da haka basu da alamun zasu tsaya daga azababben fad'an nasu da sukeyi mai tsananin firigtarwa.
Yayinda har yanzu kuma babu wacce ta samu galaba akan 'yar uwarta, wato dai sunyi rashin sa'a k'arfinsu yazo d'aya.

Cikin tsantsar firgici da tashin hankali Sheikh Ahamd ya tunkari wurin da suke gadan-gasan, bakinsa d'auke da addu'oi.

Ba tare da jin wani tsoro ko fargaba ba ya shiga tsakiyarsu, yana mai buga masu wata gigitacci'yar tsawa.
Take kuwa a wurin gaba d'ayansu suka zube ak'asa, suna masu yadda abubuwan hannunsu.
Tukun macijiyar da malam bud'amana littafin suka b'ace b'at.
Yayinda su kuma suke ta sakin numfarfashi, suna masu jifan junansu da muguwar hararar, ko wacce tana jin tamkar ta tashi taje ta shak'i wuyan 'yar uwarta har sai taga ta dena numfashi tukun ta barta.


*JAHAR KAGUL.*

K'arfe d'aya na rana dai-dai tayiwa su Yarima Asad abakin masarautar fuld'e.
Al'amin ne ya zaro wayarsa yana mai nemo number Habu ya doka masa kira.

Tana fara shiga kuwa Habu ya d'auka, alokacin kuma yana zaune acikin d'akin Gimbiya Kab'el mahaifiyarsu ne, suna tattaunawa akan Haddiyal na labarin da sukaji na cewar Gid'ad'onta ya bayyana, harma ta tafi wurinsa da asuba ba tare da sun saniba.

"Hello 'Dan uwa har kun k'arasone?"
Cewar Habu yana mai mik'ewa tsaye.

"Eh mun k'araso gama anan waje ma kai muke jira."

"Amma ai da kun shigo duka kawai ko."
Habu ya fad'a yana mai fara tafiya.

"To mudai gamu anan muna jiranka, kayi maza ka k'araso dan Allah."
Cewar Al'amin yana mai katse kiran.
Tukun ya juya b'arin da Yarima Asad yake yana mai fad'in.

"Kasa a ranka in sha Allah zuwan sa'a yau mukayi, kacire duk wata fargabar da take a zuciyarka.

"Uhm!"
Kawai Asad ya iya fad'e, sabo da shi kad'ai yasan yadda yakejin zuciyarsa na lugude a halin yanzu, yanajin tamkar idan yauma ta mai-maita irin kalamanta na baya, to bazai iya d'aga k'afarsa daga wurinba ba tare da zuciyarsa ta buga ba.

Cikin k'ank'anin lokaci Habu ya k'araso wurin da suke jiki asanyaye.
Hakan da Al'amin ya lura dashine, yasa bayan sun gaisa ya d'ora da fad'in.

"Amma lafiya kuwa kake d'an uwa, na ganka gaba d'aya ba irin yadda na saba ganinka ba?"

Nannauyan numfashi ya fesar, yana mai lumshe idanuwansa.
Kana daga bisani ya bud'esu yana mai fad'in.

"Dolene kaganni haka d'an uwa, saboda gaku dai kud'in kunzo ita kuma wacce kukazo domin tan bata nan."

Dasauri Yarima Asad ya juya baya yana mai kai idanuwansa kan fuskar Yarima Asad, yana mai fad'in.

"Kamarya bata nan, to ina ta tafine kuma?"

Ya k'arasa maganar a asanyaye, damuwa na bayyana akan fuskarsa.

"Abun ba dad'i wallahi, gaba d'aya yarinyar mu kanmu mun rasa gane kanta, atak'aice dai wai ta tafine wurin wani yaro da take mafarkinsa tsawon shekara da shekaru, wanda ta dalilinsane ya sanya bata tab'a yadda wata maganar arzik'i ta had'ata da wani saurayiba. Shi kuma yaron tunda suke basu tab'a had'uwa dashi ba sai a mafarki da take ganinsa, to shine jiya garin bincikenta ta gano inda yake, hakan yasa yau tunda asuba ta tafi ba tare data sanarwa kowa ba, sai da gari ya waye mukejin labarin wai d'an jahar wasai ne ma."

Habu ya k'arasa maganar cikin sanyi.
Yayinda Al'amin kuma yayi shiru yana mai jinjina girman Al'amarin acikin ransa.

Shi kuwa Asad suman zaune yayi a wurin da yake, yana mai jin saukar kalaman Habu acikin kunnuwansa tamkar zubar ruwan dalma a zuciyarsa.

Da k'arfi ya rumtse idanuwansa jikinsa na d'aukar kyarma.
Lokaci d'aya yaji tsanar mutumin da bai sansa ba tayi wani irin lullub'e zuciya da b'argonsa.
Hak'ik'a ko waye shi d'in zai bincikosa, sannan kuma ya gargad'esa akan ya futa daga harkar Matarsa, idan kuma haryak'i ji, to fa tabbas zai d'auki hukuncin da ba zai yiwa ko dad'i ba akansa, domin kuwa ba zai tab'a iya jurar rasata ba acikin rayuwarsa, kana kuma bazai iya aurenta zuciyarta na cike da k'aunar waninsa ba.

Ya raya haka acikin ransa yana mai sanya hannu ya bige hular dake sanya akansa ta fad'a k'asa.

Taune leb'ensa na k'asa yayi da tsananin k'arfi tamkar zai hudasa, yayinda jijiyoin tsakar kansa kuma suka futo suna masu yin rad'a-rad'a akan goshinsa.
Kana daga bisani kuma ya bud'a idanuwansa da lokaci d'aya suka kad'a sukai jajahur tamkar gauta.
Tukun ya bud'e baki cikin wata irin murya yana mai fad'in...........✍




*SHARHI NAKE SON GANI MAI SUNAN SHARHI HAKAN SHI ZAI SA KUGA NEXT PAGE A KAN LOKACI. 😀😀*



SHARE PLS.


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*24*



"Mu koma ko Al'amin."
Ya fad'a murya asanyaye.
"Kamarya ku koma kuma, ai yau kun shigo ciki dai ku gaisa da Baffa da Daddenmu ko?"
Habu yace da sauri yana mai kallonsa.
Wanda hakan da Al'amin yajine kuma ya sanyasa fad'in.
"Kuma hakane d'an uwa, muje inyaso bayan mun gaisa saimu huce."
Ya k'asara maganar yana mai yiwa motar key.
Tukun suka fara tafiya suna 'yar hira da shi da Habu.
Yayinda Yarima Asad kuma ya jingina da kujera yana mai rumtse idanuwansa da k'arfi.
Ko kad'an baiso Habu yace su shiga ciki ba, domin kuwa burinsa a yanzu shine ya gansa a cikin Jajar Wasai, ko ya samu ya had'a kan mutanen da zasuyi masa gadin Haddiyal, saboda ya gano inda wanda take kira da Gid'ad'onta yake, domin yaga da abunda yafisa da shi da har takasa sonsa.

Fada suka fara hucewa.
Sosai kuwa Lamid'o ya sakarmusu fuska suka gaisa cikin mutuntawa tare da jama'ar fada, domin kuwa tsaf ya ganesu tun kafin Habu ma yace masa 'yan masarautar wasai ne da sukazo kwanaki.
Kana a k'arshe kuma sukayi sallama suna masu tashi suka tawo b'angren Mahaifiyarsu Habu.

Cikin sakin fuska da mutuntawa ta tarbesu, tukun tasa aka kawo musu fura mai sanyi tare da kayan itatuwa.
Gaba d'ayansu k'in cin komai sukai, saboda wata irin kunyarta da sukaji sunaji, barin ma Asad da ko ido ya kasa d'agowa ya kalleta.
Itama d'in a fanninta ba wani iya kallonsa tayiba a mtsayinsa na sirikinta da Habu ya bata labarinsa, su kuwa dama fulani har dai kunyace a wurinsu ta taru ta k'are kowa ya sani.
Amma da taga da gaske baza suci komai bane ya sanyata bud'e baki tana mai ce musu suci abinci mana, nan d'in ma ai duk gidane.

"A'a Dada ak'oshe mukene wallahi."
Yarima Asad da gaba d'aya ya k'agara su tashi su tafi ya fad'i haka da sauri, gudun kar Al'amin ya amsa da tom.

Jin hakan da Habu yayine ya sanyasa fad'in.

"Barsu Dadde bara muje d'akina saci acan, maybe suna jin kunyarkine anan d'in."

Yayi maganar cikin raha, wanda hakan kuma da Yarima Asad yajine ya sanyasa mik'ewa tsaye da sauri, yana mai d'an k'ara durk'usawa yace.

"To Dadde mu mun huce."
Ganin hakan da Al'amin da Habu sukayi ne ya sanya su mik'ewa suma.
Kana suka sakeyi mata sallama tana mai fad'in su gaida mata Umminsu, kana sukayi gaba.

"Yawwa mu huce can d'in ko."
Habu ya fad'a yana mai nuna hanyar d'akinsa.

"A'a d'an uwa hucewa kawai zamuyi, saboda ko da munje can d'in ma babu abunda zan iyaci wallahi."

Yarima Asad ya fad'a da sauri yana mai fara tafiya wurin da motarsu take.
Hakan da Al'amin yajine ya sanyasa bin bayansa, tukun shima Habu ya biyo bayansu, a haka dai sukayi sallama da juna suna masu tafiya gaba d'aya rai ba dad'i.
Yayinda zuwa yanzu kuma Yarima Asad yake jin ciwon da kansa ya fara yimasa na matuk'ar tsananta.


*JAHAR WASAI, BABBAN ZAURE LOCUS.*

Cikin tsananin aljabi, tare da tsoro Sheikh Ahmad ya durk'usa k'asa jiki asanyaye yana mai d'aukar sandar da tokobin ya rik'esu a hannunsa.
Yayinda su kuma suka rumtse idanuwansu da matuk'ar k'arfi, suna masu fesar da numfarfashi.

Ita kuwa Ummi har yanzu bataji nutsuwarta ta dawo ba, sai dai kuma kaso hamsin ya ragu na firgicin da takeji cikin d'ari daga zuciyarta.
Yayinda Iman da Matar Sheikh Ahmad kuma suka zuba masa ido suna masu kallon sandar da takobin daya rik'o.
Kaka kuwa da sauri ta rarrafa k'udaje na binta ta kama hanyar falo a haka.

Yayinda Ubangayyar Bir kuma ya koma kan kujerar daya tashi yana mai binsu da idanuwa, gaba d'ayama shiya rasa abun da zaiyi.

A hankali Sheikh Ahmad ya bud'e baki bayan ya kalli Gimbiya Haddiyal cikin taushin murya, yana mai fad'in.

"Daga ina kikene k'anwata? Wurin wa kuma kikazo anan d'in."

Wasu sababbin hawayen ne suka sake futowa daga cikin idanuwanta, kana daga bisani ta durk'usar da kanta k'asa tana mai jin yadda zuciyarta ke sake zafi.
Tukun ta bud'e baki cikin muryarta mai had'e da kuka tana mai fad'in.

"Diyar Lamid'on Fuld'ece ni, na tawo ne daga cikin masarautar mu da take a jahar kagul, sunana kuma Gimbiya Haddiyyal, na kuma zo nan d'in ne dominsa."

"Wake nan? Waye ne kikazo wurin nasa?"

"Gid'ad'o am, amma sai nayi mugun gani a tare dashi, bayan kuma dogon lokacin dana d'auka ina zaman jiransa."

Tayi maganar tana mai d'ago jik'ak'k'un idanuwanta da suke cike da soyayyar Bir a cikin su ta kallesa tare da nunasa, kana daga bisani kuma ta mayar da kan nata k'asa tana mai sake rumtse idanuwanta da matuk'ar k'arfi.

Shi kuwa Sheikh Ahmad sosai kalamanta sukayi matuk'ar basa mamaki, hakanne ya sanyasa bud'e baki yana mai fad'in.

"Amma dama kin sansane shi d'in?"

Sake rumtse idanuwanta tayi da matuk'ar k'arfi.
Kana ta bud'e baki jikinta na rawa, ta fara basa irin labarin data bawa Ummi.
Wanda hakan kuma ya sanya jikin

Please Login or Register in order to submit comment