Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cigaba da bugawa.
Kana a hankali, sannan kuma cikin sanyi yace.

"Wa'alaikumu salam, d'an uwa gani fa a k'ofar gida na iso."

Ya k'arasa maganar yana mai d'an rumtse idanuwansa, tare d'a taune leb'ensa, domin kuwa baisan abun da zai cewa Habu ba akan sake dawowa gidan nasu da yayi.

"Shin da gaske kake ko da wasa dan Allah d'an uwa, domin ko kaga har ka sanyani na mik'e daga zaunen da nake."

Ya sake jiyo Habu na fad'in haka cikin tsananin murna.
Hakanne yasa ya bud'e idanuwan nasa daya rumtsesu, yana mai fesar da iska.
Kana yace.
"Da gaske nake d'an uwa, ina bakin get ka futo ka shigar dani."

"Tom shikenan bani minti biyar kawai, in sha Allah yanzu zaka ganni a gaban ka."

Ya ji Habu ya fad'a yana mai yanke kiran.
Hakanne ya sanya sa janye wayar daga kan kunnensa, yana mai a jiyeta a gefe wurin mai zaman banza, kana ya mayar da jikinsa jikin kujerar yana mai kishingid'a ya lumshe idanuwansa, tare da mamakin kansa na yadda harya iya kiran Habu ya shaida masa cewar ya dawo.
A yanzu kuma babu abun da yake tinani sai hanyar da zai bi ya sadu da farincikin ransa.
Yayinda b'angare d'aya na zuciyarsa ke fad'a masa cewar kawai ya sanarwa Habu da abun da yake faruwa, k'ila ma harya taimakesa wurin shawo masa kanta, tun da dai mutum ne shi d'in mai kirki.

Ita kuwa ta d'ayan b'angaren ce masa tayi, kul Asad, kar ka kuskura ka fara gigin zubar da mutuncinka ako ina, ka bar abun kawai ya tsaya a iyakar wanda kayi a wurinta, dan ko idan yak'i goya maka baya, ko kuma yak'i taimakonka bayan ka riga ka gama basa labarin kayi yaya, kaga shi kenan daga ranar zai raina ka shima.

Sosai ya jinjin kansa, yana mai aminta da shawarar zuciyarsa ta k'arshen, wato dai ya yadda da cewar Habu zai iya raina sa idan yaji labarin, wanda shi kuma ba zai tab'a so hakan ya faru ba.

Acan b'angaren Habu kuwa cikin sauri ya mik'e daga kan kujerar da yake a cikin tafkeken falonsu yana mai yowa waje.

Ko kad'an bai kawo komai ba a ransa da jin dawowar Yarima Asad gidan nasu.
Hakan yasa cikin tsananin farinciki ya tunkari get d'in gidan nasu.

Yana gab da k'arasawa k'ofar wayarsa da take rik'e a hannunsa ta d'auki ruri.
Hakanne yasa sa d'an dakatawa daga saurin da yake, yana mai kai idanuwansa kanta.
Sunan Al'amin d'in da ya gani yana yawo b'aro-b'aro akan screen d'in wayar tasa ne, ya sanya tsayawa cak, yana mai picking d'in kiran.

"To sarkin wutar ciki ganinan na kusa k'arasowa get d'in fa.
Kace dai wannan karan kaga dama ka biyo d'an uwa, domin kuwa nasan ba kai ne zakace yazo ku tawo ba sai da shi ya janyo ka, saboda ya fika kirki dama."

Habu ya fad'i haka daga d'aga wayar ba tare da ya bari Al'amin yayi magana ba.

Acan kuwa b'angaren Al'amin nannauyan numfashi ya fesar, saboda jin da yayi zatonsa akan Asad ya tabbatta, wato dai nan d'in ya tawo yanzuma kuma ya k'araso.
Tukun ya bud'e baki bayan ya gama jin surutun Al'amin yana mai fad'in.

"To ai dama dole ne ka yabesa, tun da yana son 'yar gidanku ba."

"Kamar ya kenan Al'amin, wata 'yar gidan namu ce kuma Asad yake so, shin haka kukai da shi ne dama?"

Habu ya fad'a cikin tsantsar mamaki, yana mai jiran yaji abun da Al'amin zai ce.

"Tabbas kuwa d'an uwa, yanzu haka ma shine dalilin da yasa na kira ka, saboda ina son kai taimaki d'an uwana ko zai koma sukuni tamkar yadda yake a baya, domin kuwa ba tare da shi muka tawo ba, asalima bai sanar dani zai zoba tamkar yadda yayi a waccan zuwa."

Al'amin ya fad'a cikin sanyi, kana ba tare da ya tsaya jiran abun da habu zai ce ba ya d'ora da basa labarin duk abun da ke faruwa, tun daga ranar da sukayi zuwansu na farko Gimbiya Haddiyal ta kifawa Yarima Asad madara a jiki, har kawo yau daya dawo bai b'oye masa komai ba.

Ai kuwa da sauri, kana kuma cikin tsantsar mamaki Habu yace.

"Kana nufin kace mun dama Haddiyal ce ta zuba masa madara a jiki, amma kuma yace mun ba ita bace ba."

"Tabbas kuwa, yayi hakanne kuma duk dan karkace zaka hukunta ta, domin kuwa tun a kallon farko da yayi mata gaba d'aya tinaninsa da komai nasa ya koma kanta, dan haka nake rok'onka akan ka taimake mu dan Allah Habu, wallahi d'an uwana yana cikin damuwa."

"Kar kadamu Al'amin, in sha Allah zanyi iyakar bakin k'ok'ari na, domin kuwa nima d'an uwan Asad ne, dan haka bazan so na gansa cikin damuwa ba.
Sai dai kuma abun da nake son ka sani shine, koda Haddiyal na sonsa dole akwai bugun shad'i da akeyi kafun ta zamto tasa, saboda a tabbatar da jarumtarsa, sannan kuma haka idan ma ita d'in bata sonsa iyayen mune ke sonsa, shima bugun shad'ine zai basa ita idan ya haye."

Cewar Habu jiki a sanyaye shima.
Shiru Al'amin yayi da jin batun, yana mai tinanin shin anya kuwa Asad zai iya aminta wani gardi can yay ta zanesa akan za'a basa yarinya, kana kuma a hakan ma bayan an zanesa babu tabbacin shi d'inne zai mallaketa.
Tabbas da kamar wuya Asad ya amince da hakan, domin kuwa asanin da yayi masa ko k'waro ya tsani ya tab'a fatarsa a rayuwa.
Hakanne yasasa bud'e baki cikin sanyi, yana mai fad'in.

"Tom shikenan Habu mun gode, yanzu dai dan Allah duk yadda za'ayi kasan yadda kayi ka had'asa da ita kafin ya tafi.

"Tom shi ke nan, yanzu dai bara naje na shigo da shi yana can waje yana jira na, kar kadamu kaji."

Cewar Habu yana mai yanke kiran.
Kana ya cigaba da tafiya zuciyar sa cike da mamamkin zurfinciki irin na Yarima Asad.

Yana futa wajen kuwa ya hango had'ad'd'iyar motarsa da take ta faman k'yalli kafe a wuri d'aya.
Hakanne yasasa tunkarar ta kai tsaye.

A cikin motar kuwa har kawo yanzu Yarima Asad lumshe yake da idanuwansa, yana mai tinanin yadda rayuwa ta canza masa.
Shi Asad da ake bi yana d'auke kai tare da sakin tsaki, yau shine yake bi ko darajar kallo baya samu.

A haka Habu ya k'araso jikin motar har ya k'wank'wasa masa glass bai jisa ba, sai da har ya bud'e motar ya shigo kasancewar babu lock a jikinta, sannan yasan da zuwan nasa.

Hakanne yasa sa d'ago kansa, yana mai sauke idanuwansa akan fuskar Habu da shima yake kallonsa, ba tare da yace komai ba.
Kana ya d'an k'ak'alo murmushin yak'e ya yafa akan fuskarsa yana mai fad'in.

"Ashe ka k'araso d'an uwa, sai kuma kaji yauma na sake dawowa ko?"

Ya k'arasa maganar cikin sanyi, yana mai tinanin abun da zaice masa a gaba, wanda ba zai sa Habun yayi wani tinani daban akan dawowar tasa ba.
Amma sai kuma yaga ya saki murmushi yana mai fad'in.

"To ai ba abun mamaki bane dan na ganka yau, kuma ko da gobe ma zanganka ai ba zanyi mamaki ba, saboda nan d'in ma ai gidanku ne ko?"

Wata irin fad'uwar gaba ce ta ziyarci Yarima Asad, saboda jin abun da Habu ya fad'a, yayinda tsoron kar dai ace Habu ya gano abun da ke kawosa ya lullub'esa, ta yadda har ya gagara b'oyuwa akan fuskarsa.
Tukun ya bud'e baki cikin rawar murya, yana mai fad'in.

"Eh...eh..."

"Kaga d'an uwa yanzu dai tayar mana mota mu shige ciki, yau har wurin Lamid'o da Dadden mu sai na kaika kun gaisa da su."

Habu ya fad'a masa haka cikin raha, saboda ganin da yayi duk ya rikice lokaci guda.
Yayinda Yarima Asad kuma ya fesar da nannauyan numfashi, yana mai lumshe idanuwansa tare da bud'e su, tukun yayiwa motar key ba tare da yace komai ba, yana mai nufar cikin masarautar.

Ba su tsaya a ko ina ba sai a bakin part d'in su Habu.
Tukun suka bud'e murafan motocin suna masu futowa waje.
Sosai Habu ya jinjina kyawu da iya d'aukar wankan Yarima Asad a cikin ransa a lokacin daya futo waje dukansa.
Hak'ik'a gayen yayi kyau, kuma ya had'u iyakar had'uwa.
Tabbas zai so k'anwarsa ta aure sa, domin ko ba k'aramun dacewa yaga sunyi ba fiye da yadda yaga dacewarta da Jauron Yamma.
Kuma dama can shi Jauron Yamma ba abokinsa bane ba, shi ya sa yaji yafi son ace Yarima Asad ne ya sameta, sai dai kuma shi kansa a yanzu ya gane ba lallai bane wannan had'ad'd'an gayen ya iya jure bulalun shad'i a jikin sa.
Saboda kallo d'aya mutum zai masa ya gane shi d'in d'an madarane lamba d'aya.

Haka yay ta tinane-tinane a cikin ransa, a haka har suka k'arasa zuwa cikin d'an madai-daicin falonsa mai kyan fasali da tsari, da yaji kayan ado na fulani a jikin bangonsa.

"Bismillah zauna ko d'an uwa."
Habu ya fad'a yana mai yiwa Yarima Asad nuni da kujerar da take a gabansa.

Murmushi Yarima Asad yayi masa ba tare da yace komai ba, yana mai zama akan kujerar.
Kana ya fara tinanin yadda zaiyi ya samu had'uwa da ita kafin ya bar gidan.

Shi kuwa Habu cikin sauri ya kawo masa ruwan jarka, yana mai tsiyaya masa shi a cikin wani had'ad'd'en kofin silver.
Sannan ya basa shi bayan ya rik'esa a hannunsa, kana ya juya da sauri yana mai fad'in.

"Please ka d'an jira ni yanzu zan je na dawo."

Ya k'arasa maganar yana mai fucewa daga cikin d'akin ba tare da ya tsaya jin ta bakin Yarima Asad ba.

Shi kuwa Yarima Asad ruwan yasha, kana ya ajiye cup d'in a k'asa, yana mai mayar da kansa jikin kujerar tare da lumshe idanuwansa.

A b'angaren Habu kuwa ko da ya futa bai tsaya ako ina ba sai a bakin k'ofar d'akin Gimbiya Haddiyal.

Hannunsa ya d'ora akan k'ofar, yana mai sanya yatsunsa ya k'wank'wasa ta.
Tukun yaja ya tsaya a gefe, yana mai jiran abasa izinin shiga.

Wata matashiyar budurwace da take sanya da kayan hadimai tazo ta bud'e k'ofar.

Da sauri ta d'urkusar k'asa tana mai fad'in.

"Barka da futowa."

Jin-jina mata kai Habu yayi ba tare da yace komai ba, yana mai sanya kansa zuwa cikin d'akin.

Zaune ya hango ta gaban mirrow ana gyara mata gashin kanta.
Yayinda jikinta kuma yake sanye da blue d'in kayan fulani da sukayi matuk'ar yi mata kyau.

Da sauri 'Yarmmatan da suke mata gyaran kan suka durk'usa k'asa suna masu mik'a gaisuwarsu wurin Habu.
Jin-jina musu kai kawai suma yayi, tukun suka mik'e da sauri bayan sun ajiye cumb d'in da suka gyara mata kan da shi, suna masu fucewa daga cikin d'akin.
Kasancewar sun riga da sun gama dama.
Yayinda ita kuma Gimbiya Haddiyal ta juya b'arin da take fuskarta d'auke da murmushi, tana mai fad'in.

"Barka da zuwa Hamma na."

Jinjina mata kai Habu yayi yana mai zama akan had'ad'd'iyar kujerar k'arfen da take a cikin d'akin.
Tukun ya fuskanci Gimbiya Haddiyal da itama ta k'araso ta zauna akan gadonta.
Kana ya bud'e baki cikin taushin murya, yana mai fad'in.

"Kina ganin zako mu samu madara a yanzu?"

"A'a gaskiya a yanzu babu, saboda an riga an futar da duk wacce aka tatsa a yau da safe."

Ta fad'a cikin nutsuwa, tana mai had'awa da girgiza masa kai.

"Kash, amma ba hakan naso ba, but abun da za'ayi yanzu shine, kitashi kije ki samo mana fura da nono, idan an dama sai ki kaiwa bak'ona ita d'aki na, ni yanzu zan k'arasa wurin Hamma Jauro ne.
So idan kinje sai ki gaishesa amutunce please kinji k'anwata."

Ya k'arasa maganar yana mai mik'ewa tsaye.

Ko kad'an bata kawo komai a ranta ba itama ta mik'e, tana mai rufa masa baya, domin taje ta aiwatar da abun da ya sanya tan.

Ba tare da ta tsaya neman wanda zaiyi mata aikin ba ta huce kiching d'in su na nan cikin bababn falonsu.

Zagaye bangon kiching d'in yake da kanta ta ko wane b'angare.
Yayinda daga kan kantocin kuma aka jere wasu irin k'warare tare da luwadun duma masu uban ado a jikin su.
Daga k'asa kuwa sababbin randina ne masu sha ajiye akan d'an gurbin k'asar da aka yi musu.

Direct ta huce gaban wasu had'd'd'un k'warare, tana mai sa hannu ta d'auko guda d'aya.
Kana ta d'auki ludayin duma d'aya tare da sabon faifan kaba.

Wucewa tayi da su zuwa gaban sink d'in da yake a cikin kiching d'in, tana mai kunna ruwa ta d'auraye k'waryar da ludayin tas.
Sannan ta koma bakin randar nan bayan ta yarfe k'waryar, tana mai bud'e ta.

Cike take dank'am da kindirmon nono fari kar da shi gwanin ban sha'awa.

Hannunta ta sanya a ciki tana mai d'ebo nonon da kofi ta zubasa a cikin k'waryar.
Sai da ta zuba sa da yawa, kana ta sake bud'e wata tunkuyar silva da take a gefen wannan k'atuwar randar.

Ita kuma cike take da 'yan mulmulen furar da take ta tashin k'amshi.

Guda biyar ta d'iba tana mai sanya su a cikin k'waryar, kana ta a jiye furar akan table d'in da yake acikin kiching d'in, tana mai bud'e wata kula ta d'ebi sugar dai dai wanda tasan zaiyiwa furar a ciki ta zubasa.
Tukun ta fara damata cikin k'warewa, wanda hakan ya sanya har ta gama ko kad'an bata tab'a jikinta ba.

Ruwa mai sanyi ta d'an d'ebo kad'an ta zubasa a cikin furar, saboda kaurin da taga tayi sosai.
Kana ta sake juyata ta had'e da ruwan.
Tukun ta sanya murfin kabar ta rufe k'waryar tare da d'aukar ludayin dumar ta d'orasa a saman murfin.
Sannan ta d'ago ta tana mai rik'eta a hannunta tayi gaba.

Acan b'angaren Yarima Asad kuwa har yanzu lumshe yake da idanuwansa, yana mai faman aikin tunaninta.

Ba zato ba tsammani kuwa yaji sautin muryar da ko daga bacci ya tashi ba zai gaza shaida mai ita ba, wadda tun daga lokacin da ya jita sau d'aya tazauna daram acikin k'wak'walwarsa.
Hakanne ya sanyasa mik'ewa daga kishingid'en da yake a jikin kujerar firgigit, yana mai bud'e idanuwansa.
Yayinda zuciyarsa kuma ta fara wani irin harbawa da bud'ewa da matuk'ar k'arfi.

So yake ya d'aga lab'b'ansa ya amsa sallamar da tayo, amma yaji gaba d'aya ya kasa yin hakan, saboda yadda bakin sa yay masa wani irin nauyi.
Yayinda har lokacin kuma idanuwansa suke kafe akan k'ofar shigowa d'akin.

Jin sautin muryarta da ya sakeyi tana mai k'ara doko wata sabuwar sallamar ne, ya sanya sa d'aga jajayen lab'b'ansa da sauri, yana mai amsa mata da wani irin sauti tamkar wanda aka fuzgo maganar daga cikin bakinsa.

A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa har ta fara shirin juyawa ta koma, saboda duk a tinaninta ko sun tafine, sai kuma kawai ta jiyo sautin amsawar da akayi.
Hakan yasa ta kama labulen k'ofar hankali kwance, tana mai turesa tare da kai k'afafuwanta zuwa cikinsa.
Sai dai kuma tana shigar tayi wani irin k'amewa a wurin da take, jikinta na d'aukar rawa, yayinda zuciyarta kuma tayi wani irin matsanancin harbawa, wanda rabon da taji makamancinta tun a waccan ranar da suka had'u, saboda yadda idanuwanta suka afka cikin tsakiyar na Yarima Asad daga shigowarta ta.

Cikin wani irin yanayi suka cigaba da jifan junan su da kallo.
Yayinda ko wanne yake jin zuciyarsa tamkar zata futo waje, saboda bugun da takeyi.
Sosai Yarima Asad yaji wata irin fargaba ta lullub'e sa, kana kuma tinanin abun da ya kawota cikin d'akin yanzu ya lullub'e zucyarsa.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal wani irin matsanancin b'acinrai ne taji ya caki k'awon zuciyarta.
Tabbas da tasan wannan mutuminne bak'on na Hamma Habun nata da babu abun da zai sanya ta yadda tayi aikin daya satan, ko da kuwa hakan zai zamto sanadin b'atawarta da shi, in yaso daga baya sa shirya.

A hankali ta janye idanuwanta daga cikin nasa, tana mai shirin juyawa ta fuce daga cikin d'akin.
Da sauri kuma taja ta tsaya, saboda tino wanda ya aiko ta wurin sa da tayi, gashi kuma ya had'ata har da Allah akan idan taje tayiwa bak'onsa tarbar mutunci.

Hakan da tina ne ya sanya ta juyawa cikin sanyi, tana mai nufar wurin da Yarima Asad yake a zaune kanta durk'ushe a k'asa, domin kuwa ko tanawa kowa rashin mutunci a cikin mutane bai kamata tayiwa Hamma Habu'nta ba, domin kuwa zata iya cewa a duk cikin yayyin ta babu mai mata soyayyar da shi d'in yake mata.
Haka kuma babu wanda ta shak'u da shi kamar shi.

Shi kuwa Yarima Asad har yanzu bai iya janye k'wayoyin idanuwansa daga kanta ba, domin kuwa ba k'aramun tsananin kyau yaga ta yi masa ba a cikin shigarta ta yau.
Hak'ik'a yau ya k'ara tabbatar da ita d'in mai kyau ce.
Da sauri ya sake wara idanuwansa akan gadon bayanta, alokacin data durk'usa tana shirin a jiye k'waryar furar a gaban sa, saboda yadda yaga bak'in gashin da ya faro tun daga gaban goshinta ya sauko har zuwa kan gadon bayanta.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal sosai taji ta k'agara tabar cikin d'akin, saboda ita a halin yanzu ko inuwarsa bata son ta rab'i kusa da wurin da take ballantana kuma shi.
Hakanne yasa tana gama a jiye furar ta mik'e tsaye da sauri, tana mai juyawa da niyyar ta koma.

Amma sai dai kuma d'aga k'afarta d'aya ke da wuya, ta jiyo sautin muryar sa cikin wani irin sanyi, yana mai fad'in.

"Ji mana!"

Take kuwa taji wani irin mugun bak'in ciki ya k'ara turnuk'eta, wato dai shi wannan mutumin ba zai fasa shiga harkarta ba kenan.
Ba zai rabu da ita ba ya dena kula ta, duk da yadda ta nuna masa rashin son hakan daga garesa, abun takaici da k'arin ban haushin ma shine, ako da yaushe idan zaiyi magana yana yinta ne cikin isa da gadara, wanda kuma bai san ita a duk duniya ba idan aka cire iyayenta da Gid'ad'on ta babu wani mahaluk'i da take ganin ya kai yayi mata magana da isa, har kuma ta tsaya ta sauraresa, domin kuwa ko yayyinta basu tab'a yi mata hakan ba.
Hakanne yasa ba tare da ta juyo ba ta cigaba da d'aga k'afafuwanta tana mai cigaba da tafiyarta.

Ganin hakan da Yarima Asad yayi ne, ya sanya rumtse idanuwansa da matuk'ar k'arfi, yana mai jin wani irin mugun bak'inciki na cakar zuciyarsa.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e su akan bayanta gaba d'aya har sun fara sauya launi.

Ganin da yayi har ta kusa isa bakin k'ofa ne, gashi kuma idan ya tafi bai fad'a mata abun da yazo da niyyar fad'en ba bai san yadda zaiyi ba, ya sanyasa bud'e murya cikin sauri yana mai fad'in.

"Dan darajar Iyayenki karki k'arasa bakin k'ofa, ba tare da kin saurari abun da zan fad'a miki ba."

Cak kuwa Gimbiya Tasmir ta tsaya a wurin da take tana mai rumtse idanuwanta, domin ko ba karamar daraja iyayenta suke da ita ba a wurinta.

"Minti biyar ma yayi yawa Please!"

Ta sake jiyo sautin muryarsa yana mai fad'in hakan.
Hakanne ya sanyata juyowa b'arin da yake, tana mai juyar da kanta gefe ba tare da ta yadda ta kallesa ba, domin kuwa ko kad'an bata buk'atar sake ganin fuskarsa ma kwata-kwata.

Shi kuwa Yarima Asad da k'arfi ya rumtse idanuwansa, yana mai jin wani irin takaici a ransa.
Wai yau shi Asad ne yake had'a yarinya da Allah da iyayenta, domin kawai ta tsaya ta sauraresa.
Hak'ik'a duniya tai masa gwatson mage.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e idanuwan nasa yana mai diresu akanta.
Tukun ya mik'e tsaye gudun kar lokacin da ya rok'etan su cika tak'i saurarensa, yana mai fara d'aga k'afafuwansa ya doshi wurin da take, cikin takunsa wanda shi kad'ai ke nuni da ko shi d'in wane ne ba sai an fad'a ba.

Yayinda yake jin bugun zuciyarsa kuma na k'aruwa tamkar k'irjin sa zai tsage.

Sai da yaje har dab da ita tukun yaja ya tsaya.
Kana ya zuba idanuwansa akan kyakkyawar fuskarta da take matuk'ar fuzgarsa, yana mai fesar da iska.
Kana daga bisani ya d'aga lab'b'an sa cikin taushin murya, yana mai fad'in.

"Sunana Ahmad Abdallah Ahmad.
Amma ahalina suna kirana da Asad, Mamy na kuma na kira na da Zaki, Yayinda abokanai na kuma suke kira na da Prince.
Mahifina shine Sarkin Jahar Wasai, wato Lamid'on Jahar mu.
Na taso cikin gata, tun da nake a rayuwa ban tab'a neman abu na rasa ba, komai na zuwar mun tun kafin na buk'ace sa.
Nayi rayuwa a k'asashen turawa da na larabawa, naga jama'a iri-iri a cikin duniya, naga kyawawan mata k'abilu daban-daban, masu aji, kud'i da gata.
Amma a hakan bantab'a ganin wacce ta birgeni ba cikinsu, duk da yadda suke k'ok'arin kusanto kansu da ni ako da yasuhe kuwa.
Sai dai kuma kin san me?

Ya fad'a yana kallonta, yayinda ita kuma har lokacin kanta yake juye a gefe tana sauraran labarin nasa, wanda har yanzu ta kasa gane fa'idar da labarin zai mata da yake fad'a matan.
Jira take kawai mintinan daya d'iba su cika ta k'arawarta gaba, domin kuwa idanuwanta suna akan agogon bangon da yake a cikin d'akin ne.

'Dan rumtse idanuwa Yarima Asad yayi, yana mai jin nauyin abun da yake shirin fad'a mata.
Kana daga bisani ya bud'e su, yana mai d'orawa da fad'in.

"Had'uwar k'wayoyin idanuwa na da naki a karon farko, komai nawa ya canza, bugun zuciyata ya sauya, tinani na ya dawo kanki.
Rayuwa ta bud'e mini sabon shafi, wanda ko a mafarki ban tab'a tinanin zuwansa gare ni ba.
Nayi duk iya k'ok'arin da zanyi wurin ganin na ya kice abun da nake ji akan ki, amma gaba d'aya abun ya citura, ta yadda har a k'arshe na gane zuciyata ta ka...

Yayi wani irin datse hak'oransa da k'arfi yana mai rumtse idanuwansa, saboda jin abun da yake shirin fad'en da yayi banbarakwai a garesa, yayinda jijiyoyin kansa kuma suka futo sukai rad'a-rad'a akan goshinsa, zuciyarsa kuwa wani irin harbawa take tamkar zata hudo k'irjin sa ta futo waje.
Sosai lab'b'ban sa suke wata irin karkarwa.
Yayinda har lokacin kuma hak'waransa suke a had'e wuri d'aya, yana mai jin tsoron abun da rabasun zai janyo masa.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal ganin da tayi har lokacin data d'ibar masan ya cika ba tare da yakai k'arshen bayanin iskar sa da yake yi ba ne, ya sanya ta juyawa a hankali, ba tare da ko farcen k'afarsa ta kalla ba tana shirin tafiyar ta.

Da sauri, kana kuma cikin rawar jiki da bugun zuciya Yarima Asad ya wara hak'waransa, saboda ganin ta da yayi ta juya zata ta tafi.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e bakinsa cikin rarrabewar magana, yana mai fad'in.

"Ma'ana dai.
IN.A...SA..N..KI!!!"




*WAYYO PRINCE ASAD YA KWAFSA MANA GIRMA YA FA'DI YAU 🙉🙉🙉 😭😭*


*COMMENT KO EMOJI NA MURMUSHI GA DUK WANDA PAGE ƊIN YAU YAYI MASA DAƊI NAKE BUƘATAR GANI FAN'S PLS*


*HAR YANZU FA BA MUYI KOMAI BA NA DAGA CIKIN CAKWAKIYAR DAKE TATTARE A WANNAN ƘAYATACCEN LABARIN NA BAƘAR MASARAUTA.*

*TABBAS IDAN NAGA ZAZZAFAN SHARHI ZAKU SAMU WANI A GOBE, AKASIN HAKA KUMA ZAI SA KUJI SHIRU HAR ZUWA RANAR MONDAY*


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*11*



Cikin matsanancin firgici, tashin hankali, had'i da rud'un da kalaminsa suka saukar mata ta juyo garesa a wani irin firgice, tana mai watsa k'wayoyin idanuwanta da suka koma jajajir a cikin nasa.
Yayinda jikin ta kuma ya d'auki wata irin karkarwa, irin wadda tun da take a rayuwarta bai tab'a yi ba.

Shi kuwa Yarima Asad cikin sanyi ya lumshe idanuwansa, yana mai sake bud'e su a cikin nata.
Kana ya k'ara d'aga lab'b'an sa yana mai fad'in.

"Hak'ik'a ina sonki da zuciya d'aya."

Da wani irin sauri Gimbiya Haddiyal ta fara girgiza masa kai, tana mai ja da baya daga wurin da take.
Iyakar kid'imewa ta kid'ime, ta rud'e, domin kuwa ko kad'an batayi tinanin abun da zai futo daga bakinsa ba kenan.

Ganin da Yarima Asad yayi tana shirin fucewa daga cikin d'akin ba tare da ta basa amsa bane, ya sanyasa matsawa wurin da take da sauri, shima yana girgiza mata kansa.
Kana ya sake bud'e baki cikin wata irin raunanniyar murya, yana mai fad'in.

"Dan Allah karki tafi ki barni.
Ke kad'ai ce macen da idanuwana basa gajiya da ganinta, ke kad'ai ce macen da kunnuwana suke muradin jin sautin muryarta ako da yaushe, kana kuma ke ce kad'ai macen da zuciyata ta fara k'aunarta.
Akan ki na fara furta wannan kalmar, hak'ik'a ina sonki so mai tsana..."

"Ya isa! Ya isa!! Ya isa na gaji da sauraran kalaman ka da suke shirin tarwatsa mun k'wak'walwa."

Ta fad'a da wani irin k'araji, tana mai sanya yatsun hannuwanta biyu ta toshe kunnuwanta dasu.

Yayinda shi kuma Yarima Asad yayi suman tsaye a wurin da yake cikin matsanancin firgici, idanuwansa akan fuskarta.

Wata irin zazzafar iska ta fesar daga cikin bakinta,

Please Login or Register in order to submit comment