Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuma key d'in motarsa ya d'auka, yana mai hucewa gaban dressing mirrow.

Tsaye yayi a gabansa yana mai kallon kansa acikin sa.
Kafin daga bisani kuma murmushi ya d'an sub'uce masa ta gefen baki, saboda yadda shi kansa ya koka da kalar kyawun da yayi yau d'in.

Hak'ik'a shi d'in mai kyau ne lamba d'aya shima ya sani.
Tukun ya juya yana mai fesar da iska, tare da fatan Allah yasa itama taga kyawun nasa tamkar yadda ya gani idan yaje.


"Masha Allah ashe haka Zaki'n nawa yake da tsananin kyawu dama."

Yarima Asad yaji muryar Mamy'nsa cikin raha tana mai fad'in haka a lokacin da ya b'ullo cikin falonsu.
Hakanne yasa sa yowa wurin da take yana shash-shake fuskarsa tamkar zai fashe da kuka yace.

"Kenan da bama kisan ina da kyau d'in ba sai yau."

Ya k'arasa maganar cikin turo baki tamkar yayayyen yaro, yana mai zama a kusa da ita tare da d'ora kansa akan kafad'arta.

"In jiwa yace maka hakan, ni kuwa na san Zakina na da kyawu tun a daren dana haifesa."
Ta k'arasa maganar tana mai shafa kansa.
Kana kuma ta d'ora da fad'in.
"To yanzu kuma ina zuwa ne Zaki na?
Da alamun dai yau ka ware kenan."

Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi, yana mai jin yadda zuciyarsa ke bugu da k'arfi.
Kana daga bisani ya janye kansa daga kan kafad'ar Mamy'n tasa, tare da d'ago idanuwansa ya bud'e su akan fuskarta.
Tukun ya d'auki hannunsa ya kai kan k'eyarsa yana mai sosawa, tare da d'an yamutsa fuska.
Kana yace.

"Zani d'an wani wurine kimun addu'ar samun nasara Mamy na."
Ya k'arasa maganar a sanyaye.

Murmushine ya bayyana akan fuskar Fulani.
Saboda fahimtar inda yaron nata yake nufin zashi da tayi, duba da irin sigar da taga ya mata magana da ita.
Sai dai kuma ita duk a tinaninta wai ko zai futa ne nemo wadda za'a had'a ayi auren kamar yadda suka shawarcesa da yin hakan.
Hakanne yasa ba tare da ta tsaya tambayarsa wurin da zashi ba ta dafa kansa tana mai fad'in.

"Allah ubangi ya kai mun kai lafiya ya kuma dawo mun da kai lafiya.
Rabbi ya baka abun da ka futa nema muddin ya zamto alkhairi ne albarkacin fiyayyen halitta.
Ubangiji ya shirya mun kai ya tsareku daga sharrin mutum da Aljan.
Tashi kaje Allah ya bada sa'a yasa kayi nasara."

Ta k'arasa maganar da sakin murmushi, tana mai zame tafin hannunta da yake a tsakiyar kansa.

Sosai Yarima Asad yaji mugun dad'in addu'ar da Mamy'n tasa tayi masa.
Hakanne yasa sa fad'in.
"Amin Amin Mamy na."
Tukun ya mik'e yana mai fara tafiya.

"Ina fatan dai kayi azkarul sabah ko?"

Ya sake jiyo sautin muryar Mamy'n tasa a lokacin da yake shirin futa daga cikin d'akin tana fad'in haka.

Hakanne yasasa juyowa b'arin da take yana mai jinjna mata kai, ba tare da yace komai ba.
Tukun ya juya yana mai fucewa daga cikin falon.

Direct ya doshi inda jerin motocinsa suke, yana mai shiga cikin wata farar benz da take ta faman k'yalli da d'aukar ido, da alamun dai kamar sabuwace ma, duba da yadda su kansu tayoyinta suke k'yalli.
Tukun ya bud'eta yana mai shiga ya zauna a cikinta tare da rufota yayi mata key.
Kana ya take ta a guje tamkar zai tashi sama, yana mai fucewa daga cikin part d'in su ya doshi hanyar da zata kai sa waje.

Sosai yayi gudu bana wasa ba akan kwalta.
Hakanne ya sa yana zuwa gaban masarautar fuld'e shabiyu da rabi dai-dai na cika.

Sai a lokacinne kuma yaji wani irin tsoron abun da zai tarar a wurinta ya sake lullub'esa.
Ta yadda har ya ji zuciyarsa na wani irin bugu da tsananin k'arfi, tamkar zata hudo k'irjinsa ta futo waje.

Tsaye yayi daga d'an nesa da ga gaban get d'in masarautar, yana mai tinanin yadda zai yi.

Gumi ke d'an tsats-tsafo masa akan goshinsa tsabar tashin hankalin da yake a cikinsa.
Kafin daga bisani kuma ya juya b'arin da wayarsa take, yana mai kai hannunsa kanta ya d'auko ta.
Tukun ya shiga cikin contact's d'in sa, yana mai fara nemo number Habu, saboda shawarar da zuciyarsa ta basa na ya kira sa yace masa yana waje da ya bi.

A hankali, kana kuma cikin sanyi tamkar mai tsoron wayar ya karata akan kunnensa, bayan yayi dialing number Habu d'in.

Da k'arfi ya rumtse idanuwansa yana mai jin k'irjin sa na wani irin bugu da tsananin k'arfi, a dai-dai lokacin da sautin shigar wayar ya fara dukan kunnensa.
Kafin daga bisani kuma ya fara k'ok'arin janye wayar daga kan kunnensa, domin ya yanke kiran, amma sai dai kuma bai kaiga kashewarba muryar Habu ta daki dodon kunnensa, yana mai fad'in.

"Assalamu alaikum 'Dan uwa!"


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA*

Tun daga waccan ranar har kawo yau Bir bai sake had'uwa da Gimbiya Tasmir ba.
Sosai ya koma wal'walarsa, yana k'ok'ari wurin ganin ya yakice soyayyar Gimbiya Tasmir a zuciyarsa.
Kuma Alhamdulillah tinaninta ya ragu sosai a cikin zuciyar tasa.
Tini gaba d'aya ciwukansa suka k'arasa warkewa tas, tamkar bai tab'a yinsu ba ma.
Domin kuwa har maganin goge tabo sai da Iya ta basa ya dinga shafasa.

Yanzu haka zaune yake a gefen Iya k'ark'ashin inuwar wata bishiya, ya d'ora kansa akan cinyarta.
Yayinda idanuwansa kuma suka kasance a lumshe tamkar mai yin bacci, sai dai kuma a zahirin gaskiya ba baccin yake ba, tinanin mahaifansa na asali da ko fuskarsu bai tab'a sani ba yake yi.
Yayinda Iya kuma take ta aikin shafa lallausar sumar kansa.

A hankali ya bud'e kyawawan idanuwan nasa.
Kana ya d'an ture hannun Iya da yake akansa da nasa hannun, yana mai mik'ewa zaune.

"Ya dai Jarumi na, ko ka gaji da kwanciyar ne?"

Iya ta fad'a cikin taushin murya, tana mai kallonsa.

Fesar da iska Bir yayi, kana ya d'an lumshe idanuwansa yana mai sake bud'e su.
Tukun ya jin'jinawa Iya kansa, yana mai had'awa da fad'in.

"Eh Iya ta zan d'an je daji ne, kin san mun kwana biyu rabon mu da muci nama ko?"
Ya k'arasa maganar da sakar mata murmushi.

Murmushin itama Iya ta sakar masa tana mai fad'in.

"Tabbas kuwa Jarumi na, rabon mu da cin nama tun kafin ka kwanta ciwo."

"To kuwa ki shirya yimana daddad'ar dawuwarki, yanzu zanje na dawo."

Ya k'arasa maganar yana mai mik'ewa taye.

"Tom shi ke nan Jarumina a dawo lafiya."
Cewar Iya itama tana mai mik'ewa tsaye.
Yayinda shi kuma Bir ya huce cikin d'akin su kai tsaye daga nan wurin.

Bai wani jima aciki ba sai gashi nan ya futo hannunsa rik'e da kwari da gwafar sa.
Kana ya doshi hanyar da yasan zata kaisa wurin da zai samo abun da ya futo nema cikin sauk'i.

Acan b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa rabonta da futa tun ranar bikin godiya ga abun bauta Gargabilu.
Yayinda har yau kuma tinanin Bir yak'i b'acewa daga cikin ranta kwata-kwata, asalima zuwa yanzu har ya zame mata jiki, ta saba da shi a koda yaushe.

Haka kawai yau tun da ta tashi da safe taji tana sha'awar futa waje ta zagaya cikin gidan nasu, tamkar yadda ta saba yin hakan a wasu lokutan dama.

Wannan dalilinne ya sanya yau ta kira 'yammatan da suke yi mata gyaran kai suka gyra mata shi.
Tukun suka had'a mata ruwan wanka a cikin bayin dake cikin d'akin nata.
Sannan ta tashi tana mai hucewa ciki.

Ba laifi ta d'an jima a cikin bayin kafun ta futo.
A lokacin kuma tini har 'yammatan nan sun gama gyara mata d'akin tsaf, yana ta tashin k'amshin turare.

Kai tsaye ta huce gaban dressing mirrow'nta, tana mai janyo tattausar kujerar da take a jiye a gefensa ta zauna a kai.
Kana ta fara matsar mai a hankali, tana mai shafe lallausar fatar jikinta da take ta faman k'yalli da shi.

Sai da har ta gama shafa man tas, tukun tabi jikin nata da ruwan humrori masu sanyin k'amshi.
Kana ta juya b'arin da 'Yammatan Bayin nan suke tana mai kallonsu, sannan ta d'auke idanuwanta.
Hakan da suka ganine ya sanya su tawowa da sauri zuwa wurin da take.
Kana suka huce gaban mirrow'n suna masu d'auko duk wani abu da suka san zasu buk'ata wurin yi mata kwalliyar.
Sannan suka fara mata cikin tsantsar k'warewa da kuma sauri.
Kasancewar sanin da sukayi na Gimbiya Tasmir ta tsani abu lak'ai-lak'ai a rayuwarta, yanzu nan sai ta sa a hukunta mutum akan hakan.

Cikin dak'ik'un da basu zarce goma shabiyar ba gaba d'aya suka gama tsantsara mata kwalliyar data zamto mara hargitsi akan kyakkyawar fuskarta.
Tukun suka sake d'aukar cumb suna masu k'ara taje tattausan gashin kanta da tsayinsa ya sauka har gadon bayanta.
Kana a k'arshe bayan sun gama ta sallamesu ta hanyar d'aga musu hannu da tayi.
Kana itama ta mik'e tsaye tana mai nufar gaban had'ad'd'iyar wardrob d'in ta.

Doguwar riga maroon color data kasance fitet mai hannun best ta zaro a cikin kayan nata.
Tukun ta zuge zip d'in bayanta tana tana mai sanyata a jikinta, bayan ta fara sanya under wears a k'asa.

Sosai rigar tayi matuk'ar kamata yadda kasan a jikinta aka d'inkata.
Ta yadda har hakan ya bayyana kyakkyawar surar da Allah ya k'era mata.
Yayinda daga k'arshen rigar kuma ta baya ta kwanta a k'asa sosai.
Plat d'in takalmi'n da ya kasance maroon color ta d'auko, tana mai sanya kyawawan k'afafuwanta acikin sa.
Kana ta juya cikin takunta da shi kad'ai abun kallone, tana mai nufar hanyar da zata futar da ita waje.
Yayinda doguwar rigar jikinta kuma ke shararar k'asa.
Tayi kyau iyakar kyau tamkar ita tayi kanta.

Tana futa waje gaba d'aya dakarunta da ako da yaushe suke kasancewa a bakin k'ofar b'angarensu suka zube a k'asa wanwar suna masu mik'o gaisuwa.
Ko kad'an bata tsaya bi takansu ba, asalima bata nuna tasan da wanzuwar suba a wurin tayi wucewar ta gaba.

Hakan da suka ganine ya sanya su mik'ewa tsaye da sauri, suna masu shirin mara mata baya.
Amma sai dai kuma ko taku biyu ba suyi ba ko wanne ya k'ame a wurin da yake.
Saboda hannun da Gimbiya Tasmir ta d'aga musu alamun bata buk'atar rakiyar tasu yau kenan.

Bata tsaya ba har sai da ta isa gaban wani d'irkeken lafiyayyen farin doki.

Cikin k'warewa da sabo da hawansu da tayi tun tana 'yar k'aramarta ta d'an buga tsalle kad'an, tana mai hayewa saman dokin.
Kana ta rik'e linzaminsa tana mai d'an haurinsa a hankali da dunduniyar k'afarta.
Take kuwa dokin ya zabura a guje, yana mai kama hanyar da ta d'orasa a kanta.


Acan b'angaren Bir kuwa cikin nishad'i yake tunkarar wurin da yake tsammanin zai samu abun da ya futo nema.
Sosai yaje jin dad'in yanayin garin a yau.
Saboda yadda wata irin sassanyar iska mai tsananin dad'i take kad'awa tana dukan jikinsa da ya kasance ko riga babu akansa.

Tafe yake yana lumshe idanuwansa hankalinsa kwance, yayinda kwari da gwafarsa kuma take rataye a kafad'arsa.

Lokaci d'aya ya tsaya cak a wurin da yake, yana mai d'an sake rumtse idanuwansa da k'arfi yanzu.
Saboda jin da yayi bugun zuciyarsa na sauyawa, wato dai gudunta ya k'aru sosai da sosai fiye da na baya.
Wanda hakan kuma ya sanyasa fahimtar dalilin sauyawar, wato dai yana kusa da Gimbiya Tasmir kenan.
Ai kuwa da sauri ya bud'e idanuwan nasa, yana mai juyawa ya canza hanyar da yake kanbi, saboda duk a tinaninsa tanan b'arin take, domin kuwa shi a yanzu baya fatan abun da zai sake had'asa da ita, ballantana ma har ta tayar masa da tsohon mikin da ya samu ya fara warkewa.

A bangaren Gimbiya Tasmir itama haka taji sauyawar bugun zuciyarta lokaci guda, wanda hakan kuma ya sanyata lumshe idanuwanta, tana mai d'an damk'e linzamin dokin ya rage gudun da yake yi.
Ba dan komai ba kuwa tayi hakan, sai dan fahimtar dalilin da ya sanya bugun zuciyarta ta sauyawa da tayi.

A hankali ta wara idanuwan nata da launinsu ya d'an fara sauyawa, tana mai jin duk ba dad'i a ranta, domin kuwa har ga Allah ita dai tana matuk'ar jin takaicin fad'uwar gaban da ganin Bawan ke sanya ta yi.
Yayinda har lokacin kuma dokin ta ke cigaba da tafiyarsa.

Da matuk'ar k'arfi ta damk'i linzamin dokin nata tana mai tsayar da shi.
Saboda jin da tayi gabanta ya k'ara yin wata irin muguwar fad'uwa.
Kafin daga bisani kuma ta d'aga idanuwanta tana mai kaisu zuwa kan hanyar da take kan bi.

Take kuwa idanuwansu suka sark'e cikin na juna daga can nesan da ta hangosa.

Kallon-kallo suka fara aikawa junansu da shi.
Ita daga saman doki, yayinda shi kuma yake a k'asa a kan k'afafuwansa.
Wasu irin abubuwa suke gani suna futa daga cikin idanuwansu suna jonewa wuri d'aya aduk lokaci guda.
Yayinda bugun zuciyarsu kuma ya sake tsananta, ta yadda har suke jin tamkar zasu hudo k'irjinsu su futo waje.

Cikin wani irin yanayi na b'acin ran da ya riski Gimbiya Tasmir yanzu ta janye idanuwanta daga cikin na Bir da matuk'ar sauri, tana mai sauka daga kan dokin nata.

Ganin hakan da Bir yayi ne, ya sanyasa juyawa da sauri, yana mai shirin tafiya, domin ya cikawa Iyarsa Al'kawarin da ya d'aukar mata.
Amma sai dai kuma ko taku ukku cikakku baiyi ba, ya ji sautin muryar Gimbiya Tasmir ta daki dodon kunnuwansa, tana mai fad'in.

"Dakata anan wurin!"

Cak kuwa ya tsaya a wurin ba tare da ya iya juyowa ba.
So yake ya d'aga k'afafuwansa yayi gaba tun kafin ta k'araso inda yake, amma gaba d'aya yaji ya k'asa yin hakan.
Domin kuwa ba k'aramun shigarsa sautin muryarta yayi ba.
Yayinda har lokacin kuma zuciyoyinsu ke cigaba da bugun da suke daya zarce k'ima.

Da d'an k'arfi ya rumtse idanuwansa, saboda jin motsinta da yayi a bayansa gab da shi.
Yayinda ita kuma take cigaba da tun karosa fuskar nan tata a matuk'ar d'aure.

Ba ita ta tsaya ba har sai da ta zagayo b'arin da Bir yake fuskanta, wato dai ta tsaya daga gabansa ya zamto suna facing d'in juna, kana kuma dab da shi tana mai zuba idanuwanta akan fuskarsa.
Jin alamun tsayuwarta a gabansa da yayi ne, ya sanya sa fara bud'e idanuwansa a hankali, har ya bud'e su duka a cikin tsakiyar nata.

A hankali Gimbiya Tasmir ta d'an d'aga jajayen lab'b'an ta, tana mai fesar da iska.
Kana ta lumshe idanuwanta tare da sake bud'e su akan fuskar Bir da yake aikin kallonta.
Tukun ta fara magana cikin wani irin yanayi, wanda shi baza a kirasa dana fad'a ba, kana kuma baza ace na lalama ba, tana mai fad'in.

"Ina son kasani, ban tsayar da kai ba anan wurin domin na kalli cikin idanuwanka, sannan kuma ban tsayar da kai ba da niyyar nasa a hukuntaka.
Na tsayar da kai ne kawai domin na sake yi maka tambayar da ka gagara bani amsar ta a karo na k'arshe kenan, wanda kuma idan har yauma ta kasance tamkar wa'yancan shud'ad'd'un ranakun, to ina mai tabbatar maka da ni kaina ban san irin hukuncin da zan d'auka akanka ba.
Dan haka amsar tambayata nake buk'ata a karo na k'arshe daga bakinka.
Shin meye dalilin da yasanya gabana yake fad'uwa a duk lokacin da mukayi kusanci da kai?"

Ta k'arasa furucin cikin wata irin murya, tana mai kafesa da idanuwanta.

A hankali Bir ya lumshe idanuwansa, yana mai jin yadda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da tsananin k'arfi.
Kafin daga bisani kuma ya sake bud'e su a cikin tsakiyar na Gimbiya Tasmir.
Kana ya d'an ja numfashi yana mai fesar da shi a hankali.
Sannan ya bud'e baki cikin wata irin murya mai tsananin taushi.
Yana mai fad'in.

"Hak'ik'a a yau d'in kinyi futowar sa'a Gimbiya.
Domin kuwa Bir zai baki amsar tambayarki, duk da baisan a yadda zaki d'auketa ba, sai dai kuma ba lallai bane ta zamto mai dad'i a gareki, amma tun da ke d'in ce kika buk'aci ji da kanki, to ki sani nima zan fad'a miki.
Kafin nan kuma ina son ki sani bawai zanyi hakan bane domin tsoron hukuncinki, ba kuma zanyi bane saboda gudun b'acin ranki, haka kuma ba zanyi bane dan hakan ya sanyaya miki rai ba, domin kuwa asalima sai dai ta k'ara hargitsa miki k'wak'walwarki ne.
Zan fad'a ne kawai domin farincikin Iyata.
Dan haka ina son kisa a ranki a yau a kuma yanzu, zaki samu amsar tambayar da kika dad'e kina tsumayen jinta daga bakin Bir, duk da dai ba lallai bane ta zamto mai dad'i agare ki ba."

Yayi maganar cikin jarumta da dakewar zuciya, idanuwansa akanta babu alamun tsoro a tattare da shi.
Kana ya juya baya, yana mai d'an d'aga k'afafuwansa yayi taku d'aya biyu ukku, tukun ya sake juyowa b'arin da take yana mai dawowa ya tsaya dab da ita.
Kana ya jefa idanuwansa a cikin nata bayan ya d'an rank'wafo da wuyan sa saitin fuskarta.
Yayinda ita d'in ma take kallon tsakiyar idanuwansa.
Tukun ya sake bud'e bakinsa yana mai fad'in.

"Amsar tambayar ki itace.
Zuciyarki ta kamu da son k'ask'antaccen Bawanki mara galihu, soyayya mai tsanani wadda ke kanki baki san lokacin da kika afka cikinta ba.
Ma'ana dai kina jin fad'uwar gaba ne a duk lokacin da kuka had'u da Bir ba dan ya aikata wani abun akanki ba.
Sai ta dalilin matsananciyar soyayyarsa da tayiwa zuciyar ki kamun kazar kuku.
Idan kuma har baki aminta da zancen na ba, kina iya zuwa ki samu malaman soyayya, domin suyi miki k'arin fashin bak'i akan alamar da tak....

"Kaiiiiiiiiiiiii!!!"

Gimbiya Tasmir ta fad'a da wani irin k'araji, cikin tsantsar firgici, tashin hankali, rud'u, had'i da zafin rai, tana mai d'ago tafin hannunta ta kawosa saitin kumatun Bir da niyyar ta yarfa masa mari.
Amma sai dai kuma hannun nata na zuwa dab da fuskar tasa ya k'ame k'am, ba tare daya k'arasa kai ba tamkar wanda aka tsayar da shi.
Sai wata irin azababbiyar karkarwa da yake tamkar zai tsinke.
Yayinda idanuwanta kuma sukayi wani irin mahaukacin rinewa da ja, suna masu furfutowa waje.
Kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu tsananin gudu da ciwo suka b'alle daga cikinsu suna masu wanke kwalliyar fuskarta.

Shi kuwa Bir a hankali ya lumshe idanuwansa, yana mai sakin wani irin murmushin gefen baki, tare da jiran yaji saukar marin akan fuskarsa................✍




*INA MAI SHAWARTAR DUK WANI MEMEBER NA CIKIN GROUPS DIN BAKAR MASARAUTA FANS DA SUKA SAN BASA COMMENT SU FARA DAGA YAU ZUWA JIBI, MUDDIN SUNA SON SU CIGABA DA ZAMA ACIKIN GROUP DINA, SABODA SHARARAR DA ZANYI A CIKINSA, KUMA A WANNAN KARAN BABU WATA KO WANI DA BAYAN NA CIRESA ZAI BIYONI PC YANA BANI HAKURI AKAN NA MAI DASA KUMA NA MAHAR DASHI DIN.*

*GA WAYAN DA BASA CIKI KUMA.SUNA SON SHIGA SAI SUYI MUN MAGANA TA WHATSAPP NUMBER TA KAMAR HAKA, 08038135929. WAYAN DA SUKA IYA COMMENT DA SHARHI KAWAI NAKE BUKATA, IDAN KUMA MUTUM BAI IYABA TO TABBAS KO NA SASA ZAN KUMA CIRESA, SABODA NA DENA SAKIN LINK DIN GROUP DINA YANZU.*




BY
_UMAR FARUQ_


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*10*



Jin shirun da yayi har kusan bayan mintina ukku ba tare da ta maresanba ne ya sanyasa bud'e idanuwansa a hankali akan fuskarta.
Kana ya d'an juyar da su zuwa gefen da tafin hannunta yake a tsaye har yanzu yana faman karkarwa, wato dai kusa da fuskarsa.

A hankali ya janye idanuwan nasa daga kan tafin hannun nata, yana mai jan numfashi ya fesar da shi.
Kana ya sake hulla k'wayoyin idanuwansa a cikin tsakiyar nata da suke zubar da ruwan hawaye tamkar an bud'e famfo.
Tukun ya d'an tura lowar lips d'in sa cikin baki yana mai tsotsarsu.
Kafin daga bisani kuma ya bar tsotar leb'en, yana mai bud'e baki cikin taushin murya, kana kuma acan k'asan mak'oshi yace.

"Me ya dakatar dake daga yin abun da zuciyarki ta umurceki kiyi? Me ya dakatar dake daga yin abun da kikasan zai rage miki rad'ad'i da k'una a zuciya?
Ga fuskata ki mareni, ki mareni Gimbiya, ki dakeni, ki had'a harda bulala, muddin hakan zai rage miki rad'ad'i da k'unar da kikeji a cikin ranki.
Nace ki mare ni ko kya samu salamar rumtsawa a daren yau.
Domin kuwa ni kai na nasan da ciwo abun, da ciwo-ciwo ma mai tsanani, ace Uwargijiya ta kamu da son k'ask'antaccen Bawanta.
Wannan dalilin shine ya sanya ki kaga ako da yaushe ina k'in baki amsar tambayar taki, saboda ada na barki ne har zuwa lokacin da zaki fahimta da kanki.
Amma ke kuma kika k'i gane hakan, kika d'auki abun tamkar raini, bacin kuma bakinsan fad'ar itace ta zamto mafi munin girman raini a gareki ba.

Ya k'arasa maganar da d'an sakar mata murmushi, yana kallon cikin idanuwanta babu alamun tsoro tattare da shi, asalima wani irin mugun shauk'i yake ji yana d'ibarsa.
Kana ya sake d'aga jajayen tausasan lab'b'ansa, yana mai d'orawa da fad'in.

"Sai dai kuma abun da baki sani ba shi ne, ba wai ke kad'ai kike jin yadda kike ji ba aduk lokacin da zaki ganni, ba ke kad'ai gabanki ke fad'uwa ba idan hanya ta had'amu.
Nima duka ina jin irin yanayin da kike ji a kaina, amma da yake ni kinga babbane, shiyasa ko kad'an ban tab'a jin haushinki ba.
Wato dai atak'aice k'ask'antaccen Bawan ki ma yana sanki, soyayya mai tsananin ma kuwa!"

Ya k'arasa furucin da lumshe idanuwansa, yana mai jin yadda zuciyarsa take yin wani irin sanyi, saboda futar da abun da yadad'e zaune a cikinta daya samu yayi yanzu.
Kana daga bisani ya sake bud'e idanuwansa akan firgitacciyar fuskar Gimbiya Tasmir da har yanzu ruwan hawaye ke zuba akanta.
Jikinta na karkarwa.
Tukun ya sakar mata wani irin murmushin gefen baki, yana mai juyawa ya tafi abunsa, ba tare da ya tsaya jiran jin ta bakinta ba.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir da k'arfi ta dunk'ule tafin hannunta da har yanzu yake a d'age a saitin inda fuskar Bir take kafun ya tafi, tana mai yarfar da shi a k'asa da matuk'ar k'arfi.

Sosai gaba d'aya ilahirin jikinta ke wata irin karkarwa tamkar wacce aka sanya a cikin ruwan k'ank'anra.
Yayinda gumi kuma ke tsats-tsafo mata ta kowace kafar gashi dake jikinta.

Iyakar rud'u, tashin hankali, had'i da firgici yau ta shigesa da kalaman Bawan nata, irin wanda bata tab'a shigar ko da makamancinsa ba a duniya.
Ta rasa dalilin daya hana hannunta kasa k'arasawa kan fuskarsa a lokacin da ta d'agasa da niyyar ta wankesa da azababben mari.
Ta rasa dalilin da ya sanya tabarsa har ya tafi ba tare da tayi masa wata illar ba, duk da tana da abubuwan da zata illatasan a tare da ita cikin sauk'i.
Ta rasa dalilin daya sata kasa ko da bud'e baki ta zagesa a yau d'in, duk da yadda ranta yakai k'ololuwa wurin b'aci da abun da ya sanar matan.
Ta rasa dalilin da ya sanyasa fad'in haka ba tare da tsoro ko shakkar abun da zatayi masa ba.
Hak'ik'a yayi gaskiya da yace ta maresan ko hakan zai rage mafa rad'ad'i da k'unar da take ji acikin ranta, domin kuwa ita kanta tasan da ta maresan zata d'an ji dama a ruhinta, amma sai dai kuma ko kad'an bata san abun da yasa ta kasa marin nasa ba.

To idan ya zamto da gaske duk maganganun sa suke ya zakiyi kenan?
Zuciyarta ta raya mata hakan.
Da sauri ta girgiza kanta tana mai bud'e baki tace.

"Inaaa, Ubangiji ya rufamun asuri, ni Gimbiya Tasmir ba zan tab'a riskar wannan bak'in lokacin ba, lokacin da za'ace zuciyata ta kamu da son Bawa.
Habawa k'aryane wallahi!"

Ta k'arasa furucin da wani irin k'araji, tana mai juyawa a haukace tayi wurin dokinta.
Cikin zafin nama ta haye samansa tana mai damk'ar linzaminsa.
Tukun ya d'iba aguje suna masu komawa wurin da suka futo.
Wato gida kenan, domin ko gaba d'aya ji tayi ba zata iya k'arasawa wurin da ta futo zuwanba, asalima babu abun da take buk'ata a yanzu face ta ganta a cikin d'akinta ta rufesa ita kad'ai, ko ta samu tayi tinanin abun da zatayiwa Bawan can akan kalamin rashin d'a'ar daya furta gareta.
Hak'ik:a tana jin duk duniya babu wani mahaluk'i da ya tab'a cutarta irin sa da ya had'a kansa da ita, a matsayinsa na bawanta.

Ko iya k'arasawa wurin da dokunan ta suke ba tayi ba ta sauka daga kansa, tana mai bin k'ofar da take a baya wacce zatayi saurin sadata da d'akinta, ba tare da wani ya ganta ba ta shige cikin gidan, har lokacin kuma tana tsiyayar da ruwan hawaye daga cikin idanuwanta.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR KAGUL.*

Da k'arfi Yarima Asad ya rumtse idanuwansa, saboda jin saukar muryar Habu a cikin kunnuwansa.
Ji yake inama bai kirasan ba, domin ko bai san ta yadda zaiyi masa bayanin da zai fahimta ba.

Sake jiyo sautin muryar Habu da yayi a cikin wayar yana mai fad'in.

"Hello! Hello!! 'Dan uwa kana jina ne."
Ya sanyasa wara idanuwansa, yana mai jin yadda zuciyarsa ke

Please Login or Register in order to submit comment