Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin gida ma za'a yisa wurine aka samu aka tsarasa.
Yayinda daga shi kuma za'a kai amare gidajensu a yau d'in.

Misalin k'arfe bakwai na dare gaba ki d'ayansu suka gama shiryawa.
Sanye Amaren suke da wani d'an ubansu less mai azabar taushi da kyawu milk color a jikinsu.
Yayinda daga saman less d'in kuma aka rufa musu wasu irin had'd'un alkyabbu masu tsananin kayu da tsada ruwan k'wai.
Suma haka a b'angaren Angwaye sanye suke da milk d'in shadda getzner, tare da milk d'in hula da cover shoe d'in k'afafuwansu.
Sai Alkyabba ruwan k'wai na maza masu azabar kyau.
Iyakar kyawu sunyisa fiye da duk kyawun da sukayi da rana ma.
A haka suke tawowa ko wanne hannunsa rik'e dana Amaryarsa anayi musu video.
Gaban wasu d'irka d'irkan fararen dokuna kar suka tsaya.
Tukun Yarima Asad ya sakarwa Gimbiya Haddiyal ta hau kai.
Kana shima ya hawo yana mai zama a bayanta tare da manne mata sosai, wanda hakan kuma yasa suka jisu a cikin wani irin yanayi gaba d'ayansu.
A hankali ya mik'a hannunsa yana mai kife tafinsa akan lallausar cinyarta. Yayinda d'ayan hannun kuma ya rik'e linzamin dokin da shi.

A b'angaren Bir da Gimbiya Tasmir suma d'ayan dokin suka hau.
Tukun suka fara tafiya a hankali ana haskesu da camerori, yayinda bud'a kuma da kad'e kad'e gaba d'aya suka cika wurin.

A haka har suka k'arasa filin bikin.
Kasancewar kuma kusan kowa yazo su kad'ai d'inne dama ake jira, shiyasa gaba d'aya idanuwa ya dawo kansu da suka k'araso d'in.

Tini Al'amin da Amaryarsa da aka riga aka kawota suke zaune akan kujerarsu, suma d'in da irin shigar su Bir a jikinsu.
Yayinda Iyaye matan wurin kuma gaba d'aya harsu Ummi da Iyayen Gimbiya Tasmir dana Haddiyal suke sanye da wani azababben less mai tsananin tsada blue color a jikinsu.
Kansu kuwa d'aure yake da gwaggwaron da yayi bala'in yi musu kyau.
Atak'aice dai sosai wurin yayi matuk'ar d'inkewa da Iyaye mata, domin kuwa hatta dasu Jakadiya da kuma su Gimbiya Huwaila da Amina duk suna wurin.

A jere a hakan kuma hannuwansu sark'e a cikin na juna suke dosar wurin da kujerunsu suke.
Suna k'arasawa gaban kujerun Bir da Gimbiya Haddiyal suka zauna akan tasu, yana mai wani manne mata.
Yayinda Gimbiya Haddiyal kuma taji kanta yayi wata irin azababbiyar sarawa adai-dai lokacin da idanuwanta suka sauka akan kujerar.

Kafe kujerar tayi da idanunta da suka fara sauya launi, jikinta na d'an fara 'yar karkarwa.
Hakan da Yarima Asad yajine ya sanya d'ago kai da sauri yana kallonta.

"Ya akaine mu zauna ko."

Ya fad'a a wani irin sanyaye yana mai murza tafin hannunta da yake acikin nasa a hankali.

K'ala batace masa ba sai kawai kallonsa da tayi tare da girgiza masa kai.
Amma sai dai kuma ganin da yayi kowa ya zauna su kad'ai ake jirane, ya sanyasa dafa kafad'unta yana mai zaunar da ita.
Kana shima d'in ya zauna akai.

Da azabar k'arfi kuma ya rumtse idanuwansa jikinsa na d'aukar kyarma, saboda yadda yaji wasu irin abubuwa tamkar allurai sun caki gaba d'aya ilahirin jikinsa, ga wani irin azababben rad'ad'i da azabar zafin da yaji yana bai-baye jikinsa tamkar wanda yake a gaban wuta.

Lokaci d'aya kuma jikinsa ya d'auki wata irin azababbar kar-kar-kar! Yayinda tinaninsa kuma tini ya fara gushewa, idanuwansa kuma tini suka koma tamkar garwashi.

Jin da yayi tamkar an sake cako masa abu ta k'asansa ne, ya sanyasa mik'ewa a wani irin firgice, kana kuma a haukace yana mai buga wani azababben ihu mai firgitarwa da rud'arwar daya hargitsa gaba d'aya ilahirin al'ummar da suke a cikin filin.
Kafin daga bisani kuma ya kama alkyabbar jikinsa yana mai mata wata irin ketawa, tare da k'ara sakin wani azababben ihun, tukun ya fara shirin zurawa a guje, amma sai kuma ya kife a k'asa yana mai fad'uwa wanwar babu alamun numfashi tattare da shi!

Take kuwa jikin Gimbiya Haddiyal ya k'ara tsananta rawar da yake yi.
Yayinda gaba d'aya jama'ar cikin filin kuma sukayo wurin cikin azababben tashin hankali da firgici.
Amma kuma gannin da sukayi Gimbiya Haddiyal ta saki wata irin azababbiyar k'ara mai tsananin firgitarwane, ya sanya jama'a da yawa jikinsu d'aukar karkarwa.
Tukun daga bisani kuma tayi wani irin kukan kura a haukace tana mai yin.............✍




*UMAR DAYYAN* 😀


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*32*



Kan Jakadiya da taga tana shirin barin filin tamkar yadda Gimbiya Huwaila ta barsa aguje.
Hakan kuwa shine ya sanya hankalin mutane komawa kanta aka bita ana shirin kamota, saboda kowa a azatonsa guduwa zatayi, amma sai kuma sukaga ta damk'i wuyan Jakadiya da masifar k'arfi tana mai fara hujijjigata, tare da rufeta da wani irin azababben duka tanayi tana sakin k'ara mai tsananin firgitarwa.

Cikin matsanancin tashin hankali tare da azabar firgici Gimbiya Fulani da take kuka kashirb'an ta kira mai martaba a waya tasanar da shi.
Yayinda Yayar Yarima Asad mai biwa Baban Yaya ita kuma ta kira wayar Babban Yaya tana mai sanar dashi abunda ke faruwa hankali a tashe.
Kasancewar kuma a lokacin suna tare da Sheikh Ahmad ne, saboda haka sukace su zasu raka k'annen nasu maza wuraren Amarensu, shiyasa yana yanke wayar ya sanar masa, ai kuwa cikin zafin nama da azabar tsoro suka mik'e suna masu dosar wurin bikin.
Wanda zuwan nasu kuma yayi dai-dai da lokacin da Mai Martaba da kuma jama'ar da suke tare a lokacin suka k'araso.

Da matuk'ar sauri, kana kuma cikin matsanancin firgici sukayi kan Haddiyal da sukaga tana wani irin hujijjiga Jakadiya, tana k'ara tare da dukanta.
Yayinda gaba d'aya matan wurin kuma suketa k'ok'arin k'watarta amma gaba d'aya sun kasa.

Ita kuwa Jakadiya tini idanuwanta sukayo waje, yayinda matsanancin tsoro da tashin hankali kuma suka dabai-bayeta.
Kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci ba k'aramun laushi tayi ba, domin kuwa zuwa yanzu ko numfashi sai da k'yar take iya fesar dashi.

Da sauri mutane suka fara bud'awa su mai martaba wuri da sukayi kan Gimbiya Haddiyal.

Habu ne ya fara k'ok'arin b'anb'are Jakadiya, amma gaba d'aya ya kasa, domin kuwa ba k'aramun rik'o Haddiyal tayi mata ba tana wasu irin magan-ganu da bakowa ke fahimtarsu ba.
Hakan da Mai Martaba yajine kuma ya sanyasa cewa kowa yayi shiru.
Wanda yin shirun nasu ne kuma yasa muryar Gimbiya Haddiyal ta bayyana rad'au, tana mai fad'in.

"Munafuka annamimiya muguwa azzaluma, wallahi yau saina kasheki tunda har kuke neman ganin bayan rayuwar Mijina, me Mijina yayi muku da kuka takura masa kuka addabi rayuwarsa kuka hanasa sukuni tun yana d'an k'arami?"

Take kowa na wurin ya zaro ido suna masu kallon Gimbiya Haddiyal cikin matsanancin firgici.
Yayinda ita kuma ta sake shak'ar wuyan Jakadiya tana mai juyawa ta kalli Mai Martaba da jajayen idanuwanta, tukun ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Kasheta zanyi tun kafin ta kashe mun Mijina, domin kuwa tun yana yaro suka hanasa jin dad'i, suka rabasa da farin cikinsa, suka sa mutane suke zaginsa tare da aibatasa, amma ahakan ma bai isaba yanzu haukatar dashi suke so suyi, itace da hannunta ta zuba garin maganin akan kujerar da zai zauna kafun muzo nina sani, a kuma tafi bakin fada dai dai kusa da dakali a hak'o k'asa nan ma akwai mugun abun masu abu a wurin, duk da wannan ba wa'yannan tsinannun ne sukayisa ba, bayan shi kuma aje a tone k'asar da take a bakin k'ofar shiga b'angaren Mamynsa nan ma akwai sabon aikinsu da sukayi wanda harya riga ya tsallakesa."

"Ayirrryirrriiiii!!!!"
Hadima Larai ta saki wata mahaukacir bud'a tare da tafa hannu, tana mai matsowa gaban Jakadiya.
Yayinda d'aukacin Jamar da suke a wurin kuma suka dawo da dubansu gareta cikin matsanancin mamaki mai tafe da firgici, domin kuwa da yawa daga cikin mutanen wurin ma sun zata haukacewar itama tayi.
Amma sai kuma sukaji sautin muryarta a nutse tana mai fad'in.

"Shi dama ramin k'arya ai k'urarrene, yau gashi ke dai k'arshen naku yazo Munafukar Jakadiya maha'inciya.
Ya Mai Martaba, duk abunda wannan Yarinyar take fad'e akan Jakadiya gaskiyane, domin kuwa nida kunnena naji suna tattauna yadda zasuyi su zuba magani a cikin ruwan maganin Yarima idan an masa bugun shad'i, shi kuma maganin nasu amaimakon bulalun su warke zasu sake bud'ewa ne suna komawa tamkar k'una, daga nan kuma har ak'arshe ya zama kuturu gaba d'ayansa. Wannan dalilin shine ya sanya kaga na kifar da wancan maganin alokacin da zata kawosa, kuma nayi shiru da bakina ne ban fad'a ba saboda rashin shaidar da zan nuna, domin kuwa hausawa sukace idan baka iya kama b'arawo ba to shi zai kamaka, dan haka nake bada shawara akan abi ta maganar yarinyar nan aje a gwada tono wurin da tace anyi binne anan d'in."

Ta k'arasa maganar tana mai jifan Jakadiya da ta gama tabbatarwa kanta da tata tak'are yau wata muguwar harara.
Yayinda Mai Martaba kuma da duk wani mutum da yake wurin sukayi bala'in girgiza da jin abunda Hadima Larai ta fad'a.
Hakan yasa wasu daga cikin Fadawan Sarki suka tafi a guje ba tare da sun tsaya jiran a basu umarni ba zuwa wurin da Haddiyal tace sunyi binnen acan.

Ita kuwa Mamy sosai take kuka idanuwanta na zubar k'walla, yayinda Sheikh Ahmad Babban Yaya kuma sukayi wurin Yarima Asad da yake sheme a k'asa tamkar gawa, suna masu yi masa addu'o.

Su kuwa Fadawan nan rabuwa sukayi, wasunsu suka tafi bakin fada suna masu zuwa suka fara hak'o k'asar wurin, yayinda wasun su kuma suka tafi bakin get d'in b'angaren Mamy suma suka fara hak'osa.
Su mutanen bakin Fada sai da sukayi rami mai zurfi, tukun sukaga wata tukunyar k'asa a cikinsa, yayinda cikin tukunyar k'asar kuma take k'unshe da wani bak'in k'yalle.

Ai kuwa cikin zafin nama ba tare da sunji tsoron komai ba d'aya daga cikinsu yasa hannu yana mai zaro tukunyar, tukun suka juya cikin sauri tare da matsanancin mamaki suna masu komawa wurin bikin da ita.
Su kuwa masu hak'o na b'angaren Mamy, kasancewarsa sabone shiyasa ko kad'an basuci wata wahalar hak'an ba, suka tarar da wasu irin manya-manyan layoyi tare da mushen bak'in bunsuru a cikin ramin.
Sosai sukayi bala'in firgita da ganin hakan, sai dai kuma a haka sukai mazantaka d'aya daga cikinsu ya zura hannu ciki yana mai zaro abubuwan.
Wanda futowar su waje kuma yayi dai-dai da lokacin da Gimbiya Huwaila ta saki wata masifaffiyar k'ara acikin part d'inta.
Tukun ta d'iba aguje tana mai fucewa daga ciki ta doshi wurin da ake biki, tana mai fad'in.

"Wayyooo Allah na nashiga ukku na sun hak'e ramin bayan kuma boka yace duk randa aka hak'osa to ranar zata kasance ranar mutuwata ko kuma ta haukana. Shikenan na riga dana sani na haukace Jakadiya kin cuceni kinyi a idon Jama'a sun ganki."

Ta k'arasa cikin filin a wani irin bala'in haukace, wanda zuwan nata kuma yayi dai-dai da lokacin da suma fadawan da sukayo hak'an gaba d'ayansu suka dawo.

Cikin tsananin firgici da tashin hankali gaba d'aya ilahirin jama'ar wurin hankalinsu ya koma kan Gimbiya Huwaila da take tonawa kanta asirin mugayen abubuwan da tayi.
Bata tsaya ko ina ba har sai da taje tsakiyar filin kusa da Gimbiya Haddiyal da take rik'e da Jakadiya har yanzu.
Tukun taja ta tsaya tana mai kafe Jakadiya da tayi bala'in galabaita da ido, kana kuma take jin inama ace Allah ya d'auki ranta a yanzu a wurinnan ko zata huta da tashin hankalin daya risketa.
Tukun daga bisani ta kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya, tana mai nuna Jakadiya da hannu.
Kana ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Shegiya Jakadiya Munafuka anji jiki, ji yadda tayi wuk'i wuk'i da ido a hannun jikarta.
Hhhhhhhhhhh!!! To duk wace ta jamana bala'in idan bake ba, sai da fa nace miki karki bari kowa ya ganki amma kika bari, to ai ga k'arshenki nan garin san kud'in masifa da gidaje da dokuna jikarki tana hujijjigaki kamar ta samu tsuntsu."

Ta k'arashe maganar tana mai k'ara kwashewa da dariya.
Tukun daga bisani kuma ta juyo b'angaren da Mai Martaba yake a wani irin haukace, tana mai cire d'an kwalin kanta tayi wurgi dashi, kana kuma ta fashe da wani azababben kuka tana mai bud'e baki tace.

"Tun daga ranar da Fulani ta haifo d'a Namiji nake son ganin bayansa, saboda sanin da nayi na zai iya zama magaji watarana, amma sai kuma hakan yak'i yuwuwa har tazo ta k'ara haifo wani ba tare da ko b'arin d'a namiji ni na tab'ayi ba, bayan kuma tazo gidanne abayan-bayana. Wannan dalilin ya sanya naji na tsani yaron sama da tsanar da nayiwa yayansa, saboda shi d'in ya zamto mai farn jinin mutane, sannan kuma Ubansa ya fifitasa sama da duk sauran 'ya'yansa ciki kuwa harda manyan 'ya'yana. Babu kalar Asirin da bamuyi ba tun daga cikinsa, saboda kar a haifesa amma abun baici ba, duk da haka ni kuma nak'i hak'ura, saboda ina ganin wataran nima zan haifo d'a Namiji."

Kwashewa ta sakeyi da wata jahilar dariya tana mai rik'e ciki, yayinda gaba d'aya jama'ar wurin kuma sukai suman tsaye, saboda yadda kalaminta suka girgiza zukatansu.
Tukun ta d'ago tana mai fad'in.

"Kun san me ya faru, to bara kuji na fad'a muku, daga baya dai aikin mu yaci, wato a lokacin da aka haifo waccan Babyn ni kuma na koma wurin Boka, shine fa ya had'a mun wani magani yace asanyasa a cikin rawanin da yaron zaisa yayi hawa, to da zarar ya tab'a fatar kansa zaiji tamkar ana cinna masa huta acikin jikinsa ne, lokaci d'aya kuma zai hargitse ya firgice, tukun bayan wani d'an lokacin gaba d'ayansa zai haukace. To shine fa tsinanniyar Jakadiyarnan tace zata iya aikin, kuma tayi sa'a tasamu damar yin komai, sai dai kuma abun haushin shine a lokacin sai kawai yayi ciwo, amma bai haukace ba ko daga baya.
Wallahi na tsani Fulani na kuma tsani 'Ya'Yanta maza gabaki d'ayansu.
Bayan wa'yancan aikin kuma haka muka cigaba dayi amma sukak'i su mutu, kuma basu haukace ba, shine fa dana koma wurin Boka na fad'a masa an kifar da maganin baiyi wanka dashi ba yace akwai aikin da za'ayi masa na k'arshe, wanda muddin ankiyaye zai haukace hauka kuma ta har abada, to daya bani abubuwan da za'a bunne ya tsallaka sai na bawa matsiyaciyar matalauciyar munafukar Jakadiyar nan, ita kuma saita sanya cikin dare aka binnesu a jiya, to wanda kuma akace za'a bad'a masa ya zauna akai, shine yanzu bayan angama shirya wuri tazo ta zuba akai ba tare da kowa ya luraba, ashe kuma wawiyar batasaniba an luran tunda gashi nan na haukace yanzu, wayyo Allah Jakadiya kinyiwa kanki garin son kud'inki na masifa har bakyaso ayi miki kishiya wurin yin mugun abu, sai gashi kuma yau 'Yar k'aramar yarinya mai kama da Babyn roba ta tona miki asiri. Hhhhhhhhh Allah ya k'ara naji dad'ina wallahi, dan haka sai da anjimanku na gama fad'ar komai na futa Jakadiya aci duka lafiya Allah yasa ma ki mutu kowa ya huta da munafurci."

Ta k'arasa maganar tana mai sake kwashewa da wata jahilar dariyar, kana ta ruga a guje tana mai sake dosar wurin data futo.

"Allah yaisa ban yafe miki ba, na sakeki na sakeki Huwaila saki Ukku!!! Bana kuma fatan ko alahira na sake ganin fuskarki."
Mai Martaba ya fad'a cikin wani irin yanayi, gabaki d'aya idanuwansa sun kad'a sunyi jajahur tamkar garwashi.
Banda girgiza kai babu abunda yake iyayi, domin kuwa shi kad'ai yasan irin rad'ad'in da yake jin zuciyarsa nayi masa.

Ita kuwa Gimbiya Fulani da duk sauran 'yan uwan Asad kuka suke sosai abun gwanin ban tausayi, yayinda Babban Yaya kuma yaketa sharce k'walla.
A kuma wannan lokacinne suma wa'yanda suka hak'o abubuwan suka kawosu suna masu fad'in inda suka ciro kowanne.
Hakan da Gimbiya Haddiyal ta ganine ya sanyata yin wurgi da Jakadiya da matuk'ar k'arfi ta kife a k'asa bata iya ko d'aga yatsarta.
Tukun ta fara tunkaro wurin abubuwan cikin wata irin tafiya wacce take kama data 'yan maye zam.
Sai dai tazo har kusa da abubuwan, sannan taja tsaya tana mai binsu da idanuwa.
Kafin daga bisani kuma ta bud'e baki cikin wata irin murya mai amo, tana mai fad'in.

"Wannan na bakin Fadar shi kuma d'an uwanka ne najiki yayisa Mai Martaba, wanda ta dalilin hakanne kuma ya sanya Yarima ya dena shiga fada, sannan kuma ya tsani duk wani abu daya danganci sarauta, kana kuma ya tsani manyan kaya ya koma mutumin banza mai son mata, tare da rashin girmama manya, saboda sanin da yayi na hardai yana ahakan to fa bazai tab'a gadar sarauta ba har abada. Sai dai kuma bazan fad'a muku kowaye ba, saboda da karta silata a samu rabuwar zumunci, saboda shima a yanzu haka naga nadama dank'are a cikin zuciyar...."

Maganarta ta yanke saboda fad'uwar da tayi ak'asa tana mai lumshe idanuwanta tamkar mai yin bacci.

A hankali kuma Wambai ya zame jikinsa daga cikin mutane ba tare daya bari kowa ya luraba, yana mai dosar b'angarensu.
Wasu irin hawaye ke zuba daga cikin idanuwansa hankalinsa gaba d'aya a bala'in tashe, yayinda matsanancin tsoro kuma yayiwa zuciyarsa k'awanya.

Da sauri Matarsa da take gyara yafin gyalen kafad'arta tana shirin fucewa da niyyar ta tafi wurin mother's nigt d'in, saboda bata san abunda yake faruwaba ta silar rashin shiryawar da batayi ba da wuri, taja baya tana mai zaro idanuwa, saboda yadda taga yana kuka bilhak'i yayi cikin d'akinsa.
A guje kuwa ta bisa zuwa ciki itama hankali a masifar tashe.

"Baban Zarah me yake faruwane naganka haka?"
Ta fad'a a lokacin data k'arasa kusa dashi cikin matsanancin firgici.

"Babu abunda ma be faruba Umman Zarah. Domin kuwa na cutar da d'an uwana tare da iyalansa, saboda kwad'ayin mulkin duniya cutarwa mai tsanani, nayi abubuwa da yawa ciki kuwa harda su bunna-bunne abakin Fada saboda kar yaronnan ya dena shiga, intaka'ice miki zance dai nine nan na zama silar daya sanya ya juye daga d'an hausawa zuwa na turawa, saboda nasan muddin yana a hakan babu wanda zai tab'a basa sarauta.
Ashe duk ban saniba kaina nake cutarwa bashi ba, hak'ik'a a hud'ubar da Sheikh Ahmad yayi yau akan Shugabanci na firgita sosai, kuma naji na dena sha'awarsa, hakan yasa na yini tinanin yadda za'ayi na tone abubuwan da na aikata ba tare da kowa ya sani ba, sai kuma yanzu gashi komai ya futo fili matar yaron da kanta ta fad'a, duk da dai ni ta rufamun asiri, amma fa haukacewar Huwaila da naga tayi ba k'aramun razanani tayi ba, Hak'ik'a na tuba Allah na tuba ka yafemun."
Ya k'arasa maganar cikin matsanancin kuka.
Yayinda Itama matar tasa tini hawaye suka jik'a mata fuska tana mai binsa da wani irin kallo.

Acan b'angaren Gimbiya Amina kuwa cikin matuk'ar firgici ta koma b'angarenta, bata tsaya ako ina ba har sai da ta isa cikin bedroom d'inta.
Kana ta dafe k'irjinta da hannu tana mai fad'in.
"Yau naga bala'i ni Amina, Allah nagode maka daka rufamun asiri ka kuma sanya na dena abubuwan da nakeyi tun baya, k'ila da tini yanzu tare dani da ita zamu haukace mu fallasa asirin kanmu cikin bainar jama'a.

Acan filin biki kuwa cikin matsanancin firgci da tashin hankali Babban Yaya yake d'an girgiza kafad'ar Yarima Asad.
Yayinda Sheikh Ahmad kuma yake d'an bubbuga kumatunsa yana mai kiran sunansa.
A hankali kuwa ya fara bud'e idanuwan nasa, sai dai kuma nauyi da azababben ciwon da yaji kansa yana yine ya sanyasa mayar da idanuwan ya rufe yana mai sakin numfarfashi.

"Asad! Asad!! Asad!!!"
Cewar Sheikh Ahmad yana mai cigaba da d'an dukan kumatunsa.
Shi kuwa Yarima Asad da yake jin muryarsa a sama a hankali ya mik'a hannunsa yana mai rik'o tsintsiyar hannun Sheikh Ahmad dashi.

"Tashi zaune kaji."
Cewar Sheikh Ahmad yana mai d'agosa zaune.
Da k'arfi Yarima Asad ya cije leb'ensa, saboda tsananin ciwon da yake ji kansa yanayi masa.
Wanda hakan kuma da Sheikh Ahmad ya ganine ya sanyasa barinsa a wurin Babban Yaya dasu Bir da duk suka zagayesa cikin matsanancin tashin hankali, yana mai komawa wurin Gimbiya Haddiyal da take kwance a k'asa tamkar mai bacci.

"Ina ganin a kaita cikin gida zaifi a dubata acan d'in."
Cewar Sheikh Ahmad yana mai kallonsu.

Da sauri kuwa Habu ya nad'e hannun rigarsa yana mai sunkuyawa ya sab'eta.
Yayinda Mai Martaba kuma da gaba d'aya ya kasa Magana tun d'azu, sai kallon Jakadiya da yaketa aikin yi ya bud'e baki yanzu yana mai fad'in.

"Ku d'auki wannan munafukar maciya amana ku kaita cikin kurkuku."
Tukun ya juya yana mai bin zugar mutanensu zuwa b'angaren Gimbiya Fulani da yaga andosa da Haddiyal.

Su kuwa Fadawansa cikin b'acin rai wani ya k'arasa wurin da Jakadiya take yana mai damk'o hannunta ya fara janta a k'asa.
Yayinda sauran kuma suketa tsine mata ahaka har suka isa cikin kurkukun Masarautar ko motsin kirki bata iyayi, saboda tsananin jigatuwar da tayi.

Acan falon Gimbiya Fulani kuwa ruwa Sheikh Ahmad yasa aka kawo masa a kofi.
Tukun yayi addu'oi a cikinsu na tsawon mintina kusan bakwai, kana ya d'ago kansa yana mai tsiyaya ruwan acikin tafin hannunsa ya yarfawa Gimbiya Haddiyal shi akan fuska.
Take kuwa taja wata doguwar ajiyar zuciya tana mai yamutsa fuska.
Hakan daya ganine ya sanyasa k'ara yarfa mata yana mai fad'in.

"Su wayene ku?"

"Haddiyal ce nice nan."

Ta fad'a cikin wata irin murya irin ta 'yan maye ba tare data bud'e idanuwanta ba.

Hakan da Sheikh Ahmad yajine yasa ya cewa Habu ya d'ago masa da kanta, kana kuma ya juyo masa da kunnenta saitin bakinsa.
Haka kuwa yayin, tukun shi kuma ya fara rero wasu daga cikin ayoyin alqu'ani cikin zazzak'ar muryarsa daya san tana bawa Aljanu wahala.

Ai kuwa batare da yayi nisaba ta bud'e baki da sauri, tana mai sakin wani irin numfarfashi tace.

"Katsaya! Katsaya!! Zan fad'a maka ko wacece ni."

"To wacece ke d'in? Me kuma kikeyi ajikin Baiwar Allah? Me yasa kike cutar da ita."

Cewar Sheikh Ahmad yana mai kallon fuskar Haddiyal data bud'e ido tana mai sunkuyar da kai k'asa.
Yayinda Iyayen Gimbiya Haddiyal kuwa mamaki yayi matuk'ar kashesu da ransu, saboda su dai tunda suke da 'yar tasu basu tab'a sanin tana da Aljanu ba sai zargin da akeyi ada akan haukar son mutumin mafarkinta da tayi, saboda basu tab'a tashi ba.

Ita kuwa Aljanar da take jikin Gimbiya Haddial cikin sauke numfashi ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Sunana Habiba, kuma ni ba muguwa bace ba, asalima ban tab'a cutar da Haddiyal ba, birgenin da takeyi ne kawai ya sanya nake sonta."

"Yanzu me kikayi mata inba cutarwar ba, kinsa yarinya ta fad'i acikin jama'a kowa yanayi mata kallon mahaukaciya, kuma bayan hakama a ina kika tab'a jin ance Aljani ya zauna ajikin mutum?"

"Wallahi ban kasance d'aya daga cikin Jinnu masu cutarwaba Ya Sheikh, asalima ko a yanzu na bayyana saboda dole, domin kuwa naga zai cutune kuma nasan cutuwarsa zata shafi Haddiyal shiyasa. Tun a ranar da aka haifeta a wurin da Kakarta take bata tsafi babu kaya a jikinta naga tayi mun kuma na fara bibiyarta, amma har kawo yau ban tab'ayi mata wata cutarwaba."

"Duk da haka bamason taimakon naki mungode da wannan ma da kikayi ya isa haka, dan haka ina mai umartarki daki futa daga jikinta yanzu ki koma daji kan bishiyu ki cigaba da rayuwarki acan, saboda Allah bai halliceta ba domin zaman Aljanu ko Aljana ba a jikinta, idan kuma har kikayi mun gardama to tabbas zan wahalar dake ne sosai."

"Bama za'azo ga wannan fagen ba Ya Sheikh, dan haka ni na tafi..."
Ta k'arasa maganar tana mai yin wasu k'wararan atishawa har guda ukku.
Tukun Haddiyal ta bud'e idanuwanta da take jin sun mata bala'in nauyi, tana mai fara bin mutanen wurin da ido.

"Haddiyal!"
Sheikh Ahmad ya kira sunanta yana kallonta.
"Na'am!"
Ta fad'a a sanyaye tana mai durk'usar da kai k'asa, mamaki da tambayoyin dalilin dayasa ta ganta a haka cike fal zuciyarta.

"Inane yake miki ciwo yanzu kuma?"

"Babu ko ina, sai kawai jikina da nake jinsa ba k'wari sosai."

"To masha Allah zuwa anjima zakiji k'warin jikin shima."
Cewar Sheikh Ahmad yana mai juyawa ya fara yin addu'oi acikin k'aton farin sabon botikin da yasa aka kawo masa cike da ruwa.

Shi kuwa Mai Martaba hakan daya ganine ya sanyasa mik'ewa daga kusa da Asad da yake zaune idanuwansa alumshe, saboda yadda yake jin har yanzu kansa nayi masa ciwo.
Yana mai fad'in.
"To Masha Allah, tunda duk sun tashi ina ganin yanzu sai kuje kuyi sallah a kuma shirya akai ko wace Amarya d'akinta."

Da sauri Gimbiya Fulani ta d'ago tana kallonsa tare da fad'in.
"Amma harda marasa lafiyan suma yau zasu tare?"

"To meye amfanin zaman nasu anan d'in, tunda jikin nasu da sauk'i, kawai a shiryasu akai ko wacce gidanta."

"Tom shikenan bara mu tashi."
Gimbiya Fulani ta

Please Login or Register in order to submit comment