Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni.
Dan haka alfarma d'aya nake son kayimun yanzu a rayuwa."

Iya ta katse Bir da haka tana mai kallonsa ido cikin ido.

Da sauri kuwa shima ya bud'e bakinsa yana mai fad'in.

"Me kike so inyi Iyata, ina saurarenki ki fad'i kome nene kinfi k'arfin alfarma a wurina, duk wuyarsa kuwa na miki alk'awarin yi miki shi."

"Ka dena kukan nan da kakeyi, wannan itace kawai alfarmar da nake buk'ata daga gareka, domin ko kukan da kakeyi shine zai sanya hankalina ya rink'a tashi, ta yadda har zan rasa nutsuwata, amma muddin ka kwantar da hankalinka, kasani ko baka kusa dani raina zaiyi haske."

Da sauri Bir ya d'ago tafin hannuwansa duka biyu yana mai fara sharce hawayen da suke kwance akan fuskarsa.
Tukun bayan ya gama goge nasa ya mayar da hannuwan nasa kan fuskar Iya yana mai goge mata itama, tare da fad'in.

"To kema ki dena kukan kinji Iyata."

Murmushi Iyar ta sakar masa duk dan hankalinsa ya kwanta.
Kana daga bisani ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Yanzu ya kukayi da ita Gimbiyar ne?"

"Tun a daren jiya ta futo da kayanta k'ofar d'akinta ta baya, harma da duka dukiyar, tukun ni kuma na d'aukesu na kaisu wurin dana san babu wanda hankalinsa zai kai wurin.
Sai kuma sitirar sawa data bani wacce zan sanya adaren yau idan zamu tafi, ita kuma gata nan a wurina.
Sannan kuma munyi da ita zamu had'une a wurin da nayi ajiyar kayan alokacin da sawu zai d'auke.
Wato dai cikin tsakar dare."

Ya k'arasa maganar asanyaye.
Ita kuwa Iya murmushin k'arfin hali ta saki, tukun tace.

"To Ubangiji ya bamu sa'a, yanzu bara na wuce na tafi wurin aikina, inyaso ma had'u da daren idan kun fito."

Ta k'arasa maganar da mik'ewa tsaye, tana mai zuwa ta bud'e k'ofar d'akin sannan ta fuce.

Acan b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa zaune take a gaban mahaifiyarta tayi zugum a wuri d'aya, gaba d'aya jikinta a mugun sanyaye.
Har yanzu bata bar fargabar tafiyar da suke shirin yiba, haka kuma har yanzu zuciyarta bata fasa gargad'inta akan abunda take shirin aikatawar ba.
Sai dai kuma masu iya magana kance wanda yayi nisa baya jin kira, to hakan take a gareta itama, domin kuwa tayi nisan da bazata tab'a jin kiraba a soyayyar Bir.

Gyara zama mahaifiyarta tayi tana mai fuskantarta sosai.
Kana daga bisani ta bud'e baki tana mai fad'in.
"Kina da damuwa sosai a cikin ranki 'yata, kuma ba tun yau na lura da hakanba, duk da alamu sun nuna kina b'oye mun.
Shin me yake damunki ne 'yata? Me yake faruwa, wanene yayi miki laifi, ko kuwa dai har yanzu akan batun Bawan da aka hanaki hukuntawa ne?"

Durk'usar da kai Gimbiya Tasmir tayi, tana mai k'ok'arin mayar da hawayen da suke shirin gangarowa waje daga cikin idanuwanta.
Hak'ik'a tana matuk'ar son ahalinta so mai tsananin, sai dai kuma ya zatayi, dolene ta tafi ta barsu muddin tana son rayuwarta tai tsawo, sabo da ta sani muddin akace babu Bir acikin rayuwarta to itama fa babu ita, idan kuma ta zauna a cikin nasu tasan dole sai hakan ta faru.
Hakan yasa ta k'ara durk'usar da kanta k'asa.
Kana ta bud'e baki cikin sanyi tana mai fad'in.

"Babu komai, ni ba abun da yake damuna."

Shiru mahaifiyarta tayi ba tare da tace mata komai ba, sai idanu data k'ara zuba mata tana nazartarta.
Tukun daga bisani kuma tace.

"Tom shikenan na hak'ura, amma bawai dan na yadda da batunki ba 'yata."

"Zan shiga ciki Fulaika zatamun gyran kai."
Gimbiya Tasmir ta fad'i haka tana mai mik'ewa tsaye, sabo da lura da tayi na idan ta cigaba da zama a wurin tsaf asirinta zai iya tonuwa, ta sanadin kukan da yake shirin kufce mata.
"Tom shikenan sai kin futo."
Mahaifiyarta ta fad'a alokacin tini ma har tayi gaba ita da sauri.
Da idanu ta bita tana mai k'ara tabbatarwa kanta da 'yarta ta na tare da damuwa, amma zata barta zuwa na d'an wani lokaci, tana da tabbacin ita da kanta zatazo ta bayyana mata abunda ke cikin ranta.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir tana shigewa cikin d'akinta ta gark'amawa k'ofar key, sabo da bata fatan wani ya shigo a halin yanzu, ballantana kuma har ya lura da shirin da take.
Tukun ta manne ajikin k'ofar tana mai silalewa a k'asa ta durk'ushe, tare da sakin wani irin azababben kuka mai sosa zuciya.
Shin meysa so zai mata haka?
Wai yau ita Tasmir ce take had'a kayanta da niyyar guduwa tabar gaban iyayenta da tunda take a rayuwa basu tab'a nisanta da junaba.
Hak'ik'a so bai mata adalciba ko kusa ko kad'an.
Ta raya haka acikin ranta tana mai cigba da sakin kukanta tamkar ranta zai futa.
Ba ita ta tsagaita da kukan da takeyi d'in ba har sai da taji kanta ya fara sarawa, tukun ta rarrafa daga durk'ushen da take tana mai nufar bakin gadonta.
Kana ta kwanta luf akai, tana mai jin zuciyarta na zafi.

Misalin k'arfe biyu na dare dai-dai.
Gimbiya Tasmir ce tsaye a tsakiyar d'akinta, tana mai sanya wata doguwar had'ad'd'iyar bak'ar riga ajikin ta.
Farar jaket ta d'auko ta d'ora asaman rigar mai kauri, sabo da sanyin da akeyi.
Kana ta sanya bak'in takalmi mara tudu a k'afarta.
Tukun ta huce gaban wata 'yar k'aramar durowa mai tsananin kyau da take acikin d'akin nata.

Gaba d'aya tana komai ne cikin sauri tamkar zata tashi sama.

Bud'e 'yar durowar da take a gefen gadonta tayi.
Take kuwa wasu irin dank'ara-dank'aran sarak'unan gwala-gwalai suka bayyana acikin ta.

Sark'ar k'afa ta d'auka tana mai k'arata akan wacce take a k'afarta.
Tukun ta sanya d'ayar a wuya tare da 'yan kunnayenta, harma da zobuna.
Kana su kuma ragowar ta d'ebesu ta zuba acikin aljihun rigar sanyin jikinta, sannan ta zuge zip d'in aljihun.
Bud'e wardrobe d'inta tayi tana mai zaro takobinta aciki.
Kana ta juya cikin sauri, tana mai dosar wurin k'ofar nan batare data rufe mayawaicin bak'in gashin kantaba.

A hankali ta murd'a handle d'in k'ofar tana mai bud'eta, kana ta zura kanta waje tana mai dube-dube daga nan cikin d'akin da take.
Ganin da tayi babu alamun ko inuwar mutum a wurin, ya sanyata futowa gaba d'aya daga cikik d'akin.
Tukun ta mik'i hanyar da zata kaita wurin da sukayi zasu had'u da Bir cikin sauri.
Tana gab da barin sashin nasu ta tsaya cak a wurin da take, tana mai juyo da kanta ta watsa idanuwanta akan ginin gidan nasu a hankali.
Take kuwa wasu irin hawaye masu tsananin gudu suka b'alle daga cikin idanuwan nata, suna dira akan kuncinta.
Ta d'auki tsayin mintuna biyu tana kallon gidan nasu.
Kana ta janye kan nata tana mai cigaba da tafiya cikin sauri.

Sosai Gidan yayi tsit gaba da'ya, yadda kasan ba'a tab'a hallita a cikinsa ba.
Babu abunda takeji yana tashi sai kukan tsuntsaye kawai.
Yayinda wata irin sassanyar iska mai matuk'ar sanyi kuma take kad'awa ako ina tana dukan jikinta.

Tun daga nesa ta hango alamun mutane har biyu ajikin bishiyar nan.
Hakanne yasata fahimtar Iya tayo masa rakiya kenan.

A b'angaren su Bir kuwa, suma zuwansu kenan wurin shi da Iya data kasa rik'e k'wallarta zuwa yanzu.
Wasu irin d'irka-d'irkan jakun-kuna ne har guda biyu ajiye a gaban su.
Yayinda shi kuma Bir yake sanye da bak'in wandon na jeans, tare da farar shirt da sukayi matuk'ar amsar jikinsa sukai masa mugun kyawu.
Shi kansa ya yaba da kyawun da kayan sukayi ajikin sa, amma abunka da wanda bai saba ba, sai yake jin gaba d'aya sunyi mugun takura masa, ta yada har yake jin tamkar suna tsikarinsa ma.

"Barka da futowa Gimbiya."
Iya ta fad'a asanyaye a lokacin da Gimbiya Tasmir ta k'araso wurin da suke.

Jinina kai kawai Gimbiya tayi ba tare da ta iya amsawa ba, sabo da yadda take jin zuciyarta na k'arayin rauni.
Yayinda shi kuma Bir ya kafeta da idanuwansa yana kallonta tamkar ya samu tv.

"Mu tafi ko Jarumi."
Ta fad'a asanyaye tana mai kallonsa itama.
Rumtse idanuwan nasa yayi da k'arfi.
Kafin daga bisani kuma ya bud'esu yana mai juyawa wurin da Iya take yay mata wata mahukaciyar runguma.

Sharrr sharrr sharrr.
Haka hawaye suka fara kwaranya daga cikin idanuwansu tamkar anbud'e famfo.
Cikin tsananin kukan da Iya take ta d'ago tafin hannunta da yake wata uwar karkarwa, tana mai kifesa a tsakiyar kan Bir.
Kana ta fara shafa gashin kansa tana mai fad'in.

"Na rungumeka tunda jinin haihuwa a jikinka, nayi maka hidima irin hidimar da uwa kewa d'anta, na soka tamkar yadda nake son rayuwata.
Ashe irin wannan ranar zatazo garemu, ranar da zamu rabe tamkar yadda muka had'u sama taka Jarumina."

Ta k'arasa maganar tana mai sakar masa wasu irin sumbata akan fuskarsa ta ko ina.
Wanda hakan da Bir yaji ne kuma ya sanya zuciyarsa ta k'ara matuk'ar rauni, ta yadda hawayensa suka cigaba da futowa tamkar ana hankad'o su.

Itama Gimbiya Tasmir tini ruwan hawayen suka damal-male mata fuska, domin kuwa ba k'aramun tausayinsu taji ya lullub'eta ba.
Tabbas a yanzu ta k'ara tabbatarwa kanta da so mugun abune, so mugun iccene mai matuk'ar dafi, ta yadda har dai tsautsayi ya sanya mutum cin karo da shi, to shikenan kuma tasa ta k'are.

Sun d'auki tsayin mintina biyar a haka.
Tukun iya ta b'anb'are Bir ajikin ta dak'yar da d'an k'arfinta da yayi saura.
Kana ta bud'e baki cikin rawar murya tana mai fad'in.

"Kuyi maza ku tafi, sabo da baku da cikakken lokaci, ina muku fatan alkhairi tare da nasara acikin sabuwar rayuwar da zaku fara.
Ubangiji yaji k'anku ya had'a kanku, ya kuma sadaka da iyayenka Jarumina."

Ta fad'a tana mi shirin juyawa ta tafi.
Hakan da Bir ya ganine ya sanyasa zube gwiwoyinsa a k'asa yana mai sake fashewa da kuka.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir da sauri tayi wurin Iya, tana mai rungumeta ta baya.
Kana ta bud'e baki cikin matsanancin kuka tana mai fad'in.

"Ko wata irin barazana zasuyi miki, karkiyi gigin nuna musu cewar kin san da tafiyar mu, hakan kawai shine zai zamto miki tsira, domin kuwa idan sukai-sukai sukaji baki fad'a ba, dole su hak'ura su rabu dake a matsayin baki saniba kema.
Amma kuma muddin kika fad'a, to ina da tabbacin ko dak'ik'a d'aya ba zaki k'araba a duniya."

Jinjina kai Iya tayi ba tare da tace komaiba.
Yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir ta saketa tana mai dawowa baya.
Shi kuwa Bir cikin matsanancin kukan da yake yi ya bud'e baki, yana mai fad'in.

"Ina sonki Iyata, ina mugun k'aunarki Iyata, ban tab'a tinanin zuwan wannan ranar ba cikin rayuwata.
Ranar da zan nisanta dake.
Amma inaso kisa a ranki, ko badad'e ko bajima wataran zan dawo domin na tafi dake kema, muddin da sauran rai a gangar jikinmu."

"Nima ina sonka Jarumina.
Dan haka kuyi maza ku tafi.
Kai Jarumi ka rik'e Gimbiya amana, ka kula da ita da rayuwarta, ka zamto mata uwa, uba da danginta da tayi nesa dasu ta dalilinka.
Domin ko ita mace mai raunice akan namiji ako da yaushe, wato dai a yanzu kaine zaka zama jagoranku ba itaba.
Dan haka kuje nima na tafi, Ubangiji ya sadamu da Alkhairansa."

Ta k'arasa magaanar tana mai tafiya da sauri, ba tare da ta tsaya jin ta bakinsu ba, sabo da lura da tayi na muddin batayi hakan ba, to fa ba zasu tafi ba, gashi kuma lokaci na k'ara tafiya.

"Muyi sauri mu tafi lokaci na huce mana Jarumi."

Gimbiya Tasmir ta fad'a tana mai zuwa gaban jakar d'aya ta fara k'ok'arin d'aukarta.
Ganin hakan da Bir yayine, ya sanya mik'ewa tsaye yana mai zuwa ya amshi jakar tare da girgiza mata kai.
Tukun ya d'auki d'ayar wacce ta kasance cike da kud'i a cikinta.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir ganin hakan da tayi ne ya sanyata zare takobinta daga cikin d'an gidanta.
Kana ta nuna gefe guda da ita, tana mai fad'in.
"Shairamaaa!"
Wal! Macijiyar ta bayyana tana kallonta, tare da karkad'a harshe.
Yayinda shi kuma Bir yake tsaye a gabansu rik'e da jakun-kunan nan yana kallon Macijiyar shima.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir cikin sanyayyar muryarta da bata futa sosai sabo da kuka, ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Temakonki nake nema Shairama, kamar yadda aka had'ani dake domin ki taimakeni.
Zamu tafi sabuwar duniya ta daban, wacce ba tamuba, ba tare kuma da sanin wani ba Shairama, dan haka nake son ki sharemana hanya, ta yadda zamu ji dad'in binta ba tare da tangard'a ba."

Ta k'arasa maganar tana mai mayar da takobinta cikin gidanta.

Ita kuwa Shairama wani irin juyi tayi tana lank'washewa tare da karkad'a jiki.
Kafin daga bisani kuma ta fara tafiya daga kwancen da take tana mai bi ta saman duwarwatsu da sauri.
Ganin hakan da sukayi ne yasanya su bin bayanta cikin sauri suma.

Ta gefen filin biki suka huce, kuma sun hangi mutane na dasa wutar girki a wurin, amma kasancewar gaba d'aya ma'aikatan hankalinsu ba anan yake ba, shiyasa har suka bar area babu wanda ya kula dasu.

Cak suka tsaya a wurin da suke har shairama, badan komai ba kuwa sai sabo dakarun da suka hango rik'e da mahaukatan bulalansu, da kuma makamansu abakin get d'in futa daga cikin Bak'ar Masarauta.

A hankali Gimbiya Tasmir da Bir suka juyo da kansu suna masu kallon juna.
Yayinda Bir yake jin zuciyarsa tamkar zata faso k'irjinsa ta futo waje tsabar tsoro, sabo da shi dai ya sani muddin aka kamasu, to fa matsalar akansa zata k'are duka.

Ita kuwa Shairama wani irin juyi tayi a wurin da take, tana mai tashi sama tamkar tsuntsuwa.
Hakan da suka ganine ya sanyasu binta da idanu.
Yayinda ita kuma ta fara tafiya asama tana mai nufar bakin get d'in nan.
Ganin hakan da sukayi ne ya sanya su fara d'aga k'afafuwansu, suna masu dosar hanyar suma.

Ita kuwa Shairama tana k'arasawa saman kan wanda yake a farko, ta saresa a gefen wuyansa.
Take kuwa ya saki wata irin mahaukaciyar k'ara a wurin, yana mai zubewa a k'asa wanwar.
Jin hakan da 'yan uwansa na wurin sukayi ne, ya sanya su saurin firgita, suna masu kawo idanuwansu kansu Bir da suke tawowa wurin.
Sai dai kuma suma d'in cikin lokacin da bai wuce dak'ik'a biyu ba gaba d'aya Shairma ta saresu a wurare daban-daban suka zube ak'asa wanwar.
Tukun tayi gaba tana mai fucewa daga cikin get d'in, suma su Bir suka rufa mata baya cikin tsantsar sauri.

Ta cikin bishiyu da duwar-watsu suka dinga ratsawa suna tafiya da matuk'ar sauri.

Sai da har sukayi nisa da get d'in Bak'ar Masauta, sannan Shairama ta tsaya a wuri d'aya tana mai k'in cigaba da tafiya.
Kafin daga bisani kuma ta b'ace b'at.
Hakan da Gimbiya ta ganine ya sanyata fahimtar cewa Shiarma ta gama aikinta na yanzu.
Ai kuwa da sauri ta juya tana mai kallon Bir.
Kana ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Yanzu Shairma ta gama nata aikin, dan haka sai mu hanzarta mubar wurinnan tun kafin su farga."

"To ya kuma zamuyi nan, bayan kinsan babu jiragen k'asa da k'asa a ruwan gabas."

Bir ya fad'a sabo da ganin da yayi Gimbiya Tasmir ta d'auki wata hanyar daban.

"Ba zamu tab'a tafiya K'asar Hausa ba daga nan, sabo da idan mukayi hakan asirin mu zaiyi saurin tonuwa, ta yadda har za a iya biyo sahunmu kuma acimmana, kuma ko bayan haka ba lallaine mu samu jirgin da zai tashiba acikin daren nan.
Amma idan muka fara zuwa Jahar Markuz, hakan shi zai sanya su rasa gane inda mukayi, daga jahar markuz kuma sai muhau jirgin k'asar hausa anan, sabo da su dama jiragen dake zuwa jahar markuz cikin dare suke tashi."

Ta fad'a tana mai cigaba da tafiya.
Hakan yasa shima Bir yabi bayanta da tsananin sauri, hannunsa rik'e da jakun-kunansu suna masu ratsa dogayen bishiyu da duwarwatsu.

Gaba d'aya ko tsoron dare basayi kwata-kwata, burinsu kawai su gansu sun bar Jahar Karfuz gaba d'aya.

Sunyi doguwar tafiya, domin kuwa ita Gimbiya Tasmir har ta fara jigata ma.
Tukun suka b'ulla bakin tafkeken ruwan da wasu irin had'ad'd'un jiragen ruwa masu rufi sukai masa k'awanya a gefe.
Yayinda gaba d'aya wurin kuma ya kasance haske tarwai tamkar rana.
Ga kuma jama'a nan masu zuwa da wa'yan da suke a wurin, wasu rik'e da jakun-kunan su matafiya kenan, wasu kuma sun kasa kayayyakin sana'oinsu yadda kasan rana.
Wato dai tashar jiragen ruwace sukazo.

"Ruman! Markuz! Kuzo ku shiga nan."
Sukaji muryar wani mutumi yana fad'e tare da nuna jiragen da suke a kusa da shi.

Ai kuwa cikin sauri suka k'arasa wurin da yake.

"Ina zuwane?"
Ya fad'a yana kallonsu.
"Jahar Markuz."
Bir da bai gajiba kwata-kwata da tafiyar da sukayi ya fad'a, yana mai tallabo Gimbiya Tamsir jikinsa.

"To ku shiga nan ya cika kenan, dama kujerar mutum biyu sukayi saura."

Da sauri kuwa suka lumshe idanuwansu atare, suna masu sauke ajiyar zuciya.
Sabo da jin abun da mutumin ya fad'a da sukayi.
Kafin daga bisani kuma Gimbiya Tasmir ta fara hucewa ciki, tana mai zama akan kujerar da take a kusa da window.
Kana shima Bir yabi bayanta hannuwansa rik'e da jakun-kunansu.
A kujerar da take a kusa da ita ya zauna bayan ya dire jakun-kunan a k'asa.
Tukun aka saita komai, sannan matuk'an jirgin suka fara sarrafasa acikin ruwan suna masu d'aukar hanyarsu.

Da k'arfi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwanta, sabo da yadda taji zuciyarta tayi wani irin bugu da tsananin k'arfi adai-dai lokacin da jirgin ya fara motsi.
Tukun daga bisani kuma ta bud'esu tana mai kai dubanta waje ta cikin windown, ta farayiwa k'asar iyaye da kakkaninta, tushenta kallon bankwana hawaye na tsinkewa daga cikin idanuwanta.
Yayinda shi kuma jirgin ya fara nutsawa akan hanyarsa.
Wani irin abu taji ya tsaya mata a k'irji.
Hakan yasa ta d'ago tafin hannunta tana mai dafe k'irjin nata da shi.
Kana ta fara girgiza kanta, tana mai cigaba da kallon hanya, hawaye na cigaba da ambaliya daga cikin idanuwanta.
Shin ya iyayenta zasuyi idan sun tashi basu ganta ba, wane hali mahaifiyarta zata shiga.
Shin anya kuwa tayi musu adalici, sannan kuma tayiwa kanta adalci .
Ta raya haka a cikin ranta tana mai sake fashewa da kuka.

Jin hakan da Bir yayine ya sanya sa mik'a hannunsa yana mai janyota zuwa cikin jikinsa.
Shima d'in kuma dai hawayen na futa daga cikin idanuwansa.

Da sauri ta k'ank'amesa tana mai kifa kanta a k'irjinsa, wani irin kuka na k'ara k'wace mata.
Yayinda shi kuma ya d'ago tafin hannusa a hankali, yana kifesa akan lallausar bak'ar sumar kanta ya fara shafata ahankali, tare da d'an bubbuga bayanta da d'ayan hannun nasa.

Cikin zubar hawaye ta ciro kanta daga cikin k'irjinsa tana mai watsa idanuwanta acikin nasa.
Kana ta bud'e baki cikin wata irin murya, tana mai fad'in.

"Nayi komai sabo da sonka, na sadaukar da kowa nawa da komai nawa duk dominka, bani da kowa bani da komai sai kai yanzu a duniya.
Dan haka nake rok'onka akan kaji tausayina, ka rik'eni amana, karka juyamun baya kamun butulci ko ba yanzu ba, domin kuwa na riga dana sani muddin hakan ta kasance mutuwa zanyi, mutuwa zanyi cikin nadamar abun da na aika..."

Kuka yaci k'arfinta ta kasa k'arasa furucin.
Hakan da Bir yajine ya sanyasa durk'uso da kansa zuwa kan tata fuskar yana mai saurin had'e bakinsu huri d'aya.
Tukun ya watsa k'wayoyin idanuwansa da suke jik'e da ruwan hawaye cikin nata.
Kana ahankali, sanan kuma cikin wani irin salo ya fara tsotsar jajayen lips d'inta, yana mai cigaba da kallon idanuwanta .

Ita kuwa Gimbiya Tasmir tina a wurin da suke da tayi ne ya sanyata zame nata bakin a hankali daga cikin nasa.
Kana ta koma kan kujerarta ta zauna, tana mai d'ora kanta a kafad'arsa ta cigaba da tsiyayar hawayenta.
Yayinda jirginnan kuma yake ta tsala uban gudunsa acikin ruwa.

Misalin k'arfe biyar na asuba suka isa Jahar Markuz, wato dai tafiyar awa biyu da rabice ta kawosu nan d'in daga Jahar Karfuz.

Furfutowa suka farayi bayan kowa ya biya kud'in jirginsa.
Cikin ikon Allah tun kafin su Bir su futo daga cikin jirgin sukaji muryar wani daga cikin masu loda mutane yana fad'in.

"K'asar Hausa! K'asar Hausa!! K'asar Hausa mutum hud'u kawai sukai saura jirgi ya tashi."

Ai kuwa cikin sauri Bir yayi gaba rik'e da jakun-kunansu a hannunsu.
Itama Gimbiya Tasmir da matuk'ar sauri ta fuce daga cikin jirgin, suna masu yin wurin Jirgin K'asar Hausa da sukaji ana fad'e.

Zuwan nasu gaban jirgin kuwa yayi dai-dai da lokacin da wa'yan can cikon mutum biyun mace da namiji suka k'araso gaban jirgin suma.
Hakanne yasa suna zama aciki gaba d'aya kujerun suka cika taf.
Tukun aka shirya, direbobin kuma suka gyara zamansu suna masu fara sarrafa jirgin nasu zuwa cikin ruwa.

Zazzafan nunfashi daga Bir har Gimbiya Tasmir suka fesar alokacin da jirgin ya fara nutsawa hanya.
Sabo da tabbatarwa kansu da sukayi da sun riga sun tsira kenan.
Yayinda BIr kuma tinanin halin da Iya zata shiga ya sake lullub'esa yanzu.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Sosai 'Yammata da samarin cikin masarautar Wasai suke shirin zuwa wurin birthday d'in Yarima Asad da za'ayi party'n acikin Asadullah Palace, da misalin k'arfe hud'u na yamma, kamar yadda akayi na wancan shekarar data huce aciki.
Kasancewar kuma party'n Asadullah Palace iyakar na 'ya'yane, shiyasa gaba d'aya manyan gidan babu wanda yake tashi ma.
Yayinda a wurin uban gayyar kuma gaba d'ayama ya manta da cewar yau ne birthday d'in nasa, har sai lokacin daya dawo daga sallahr asuba yaga Mamynsa tsaye abakin k'ofar shigowa.
Yana shigowa kuwa ta dafa kansa tana mai sanya masa albarka, tare da fatan Allah ya k'aro masa shekaru masu albarka a gaba, ya kuma shiryasa ya basa abunda yake nema na alkhairi acikin sabuwar shekararsa data shigo.
Tukun yama tuna da cewar yaune zagayowar ranar haihuwarsa, sabo da dama ita Gimbiya Fulani haka takeyiwa duka 'ya'yanta, babu ruwanta da wani birthday party, tunda tasan hakan ba abu bane mai kyau, kasancewarta mace mai rik'o da addini.
Kana ta bud'e wata had'ad'd'iyar choculate tana mai sanya masa ita abakinsa.

Da sauri ya lumshe idanuwansa yana mai taune choculate d'in a hankali, yayinda acikin zuciyarsa kuma yake fatan Allah ya karb'i addu'oin da Mamy'n tasa tayi masa, sabo da yaji har fatan samun Hadiyyal d'insa tai masa.

Yana cikin wannan yanayin yaji ana fesa masa abu a jikinsa mai d'an damshi tare da tsananin k'amshi.
Hakanne ya sanyasa bud'e idanuwansa da sauri.

"Happy birthday to you!!! "

Baby ta fad'a alokacin da ya bud'e idanuwan nasa tana mai cigaba da fesa masa wasu irin had'ad'd'un fulawoyin da suke da tsananin k'amshi tare da danshi ajikin su akan fuskarsa.

Hakan ya sanya Yarima Asad sakin murmushin daya manta rabon da yayi irinsa.
Kana ya bud'e baki cikin sanyin murya yana mai fad'in.
"Thank you our Baby."
Tukun ya rab'a ta gefenta ya huce yana mai nufar d'akinsa.

Misalin k'arfe tara da rabi na safe yana kwance acikin d'aki kan gado ya kafe sili da idanuwa Al'amin ya shigo ciki, yana mai zama a gefensa.

A hankali ya d'an juyo da idanuwansa b'arin da Al'amin yake, yana mai fad'in.
"To yane Aboki?"

Fesar da iska Al'amin yayi yana mai lumshe idanuwansa.
Kana daga bisani ya bud'esu yana mai fad'in.

"Tashi zakayi mutafi wurin gyaran kai."

"Kamarya gyaran kai kuma, ni nace maka kaina na buk'atar gyarane?"
Yarima Asad ya fad'a asanyaye yana kallonsa.

"A'a bakace mun ba, kamawa kawai yayi kayin.
Sabo da taron da muke da shi ayau d'in."

"Wane kuma taro kenan Aboki?"
Yarima Asad ya k'ara fad'e yana mai mik'ewa zaune.

"Dallacan karka rainamun hankali mana, kafa sani sarai akwai birthday party da yamma, amma kake fad'in haka."

"Kashhh, in banda abunka Al'amin ni wane birthday party zani, bayan kuma kasan halin damuwar da nake a ciki."

"Kai kuwa ya kamata kaje Aboki, sabo da hakan shi zai sanyaka kaji kaso da yawa daga ciki na damuwarka ya tafi, kuma ma bai kamata ace sabo da haka ta faruba ka dinga cutar da kanka ako da yaushe.
Dan haka dan girman Allah karkace bazaka ba, sabo da mun riga da mun gama shirya komai, kuma nayi inviting d'in duk mutanen da suka kamata suzo.
Domin kuwa yanzu hakama mutanen mu na Dubai da other's Country duk suna hanya, wasu kuma suna hotel ma acan suka kwana sun iso tun jiya."

"Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi, yana mai fesar da iska, sabo da shi dai harga Allah a wannan karan baiso yin partyn ba.
Sabo da bashi da kwanciyar hankalin da zaiyi yadda yakeso a wurin.
Amma sai dai kuma bazai iya bad'awa Al'amin k'asa a ido ba ya basa kunya, tunda har gyayya yayo musu.

Hakanne ya sanyasa mik'ewa tsaye, yana mai fad'in.
"To muje ko."

Mik'ewa shima Al'amin d'in yayi suka kama hanyar waje, domin su tafi wurin askin.

Acan gidan Gwamna wurin Billy kuwa, sosai take shiri bana wasa ba.
Tini Zee ta k'araso tare da wasu k'awayenta guda biyu data gayyatosu zuwa wurin.

Zaune suke a cikin d'akinta kan wata mayyar kujeru suna hira.

Yayinda ita kuma Billy take tsaye a gaban wardrobe d'inta tana mai zaro kayan da zata sanya yau d'in.
Wani irin kitson atach ne akanta, brown color shuku masu matuk'ar girma da kyawu, da tsayinsa ya kusa zuwa kan k'aurinta.
Yayinda hannuwanta da k'afafuwanta kuma suke d'auke da wani irin bak'i da jan lalle da yayi bala'in yin kyau.

Sosai jikinta yake futar da k'yalli tare haske, atak'aice dai tayi kyau ba kad'an ba, da alamun dai har gyaran jiki tayi.

Misalin k'erfe biyu da rabi gaba d'aya k'awayenta suka gama shiryawa, cikin wasu had'd'un bak'ak'en

Please Login or Register in order to submit comment