Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa tambayoyin ajere kana kuma a firgice tamkar yadda Al'amin ya rud'e da jin furucin abokin nasa, tana mai k'arasawa zuwa wurin da suke tare da kife tafin hannunta akan fuskarsa, Amma sai kuma ta janyesa da sauri, saboda wani irin azababben zafin da taji ya daki hannun nata.

"Ummi kayan nan ne zasu k'onani, gaba d'aya zafi nakeji sosai."
Asad ya sake fad'e a rikice kuma da sauri, gumi na cigaba da yanko masa ta tsakar kansa zuwa kan goshinsa.

"Amma kayi addu'a kuwa kafun kasa su Zakina."
Fulani ta fad'a a rikice tana mai fara bud'e murfin jarkar hannunta.
Shiru Asad yayi ba tare daya iya cewa komai ba, Wanda hakan kuma shine ya sanyata gano amasar tambayarta garesa, wato aa baiyiba kenan.

Ba tare da ta k'ara ce masa komai ba ta dire bakinta akan bakin jarkar, tana mai fara karanto addu'oin kariyar Allah har na tsawo wasu mintina.
Tukun daga bisani ta janye kanta tana mai mik'awa Asad ruwan tare da fad'in.

"Yi maza kasha wannan."

Da sauri kuwa ya manna bakin jarkar akan tausasan lab'b'ansa da suka k'ara ja dan azaba, yana mai lumshe ido alokacin guda, tare da sakin wasu irin gaurayen a jiyar zuciya, saboda yadda yaji shigar ruwan cikinsa tamkar saurkar ruwan kank'ara, kafin daga bisani kuma sanyin ya fara ratsa ilahirin jikinsa, yana mai jin zafin na kaucewa gaba d'aya.

Bashi kuwa ya iya janye bakinsa daga kan jarkar ba har sai da yaji ruwan dake cikinta ya dena hucewa zuwa mak'oshinsa, tukun ya saketa a k'asa ta fad'i, yana mai fesar numfarfashi tare da jin kaso tamanin cikin d'ari na azababben zafin da yakeji a jikinsa ya tafi, ta yadda har gumin dake yanko masa da kuma tsananin ciwon da kansa keyi shima ya kau.

"Ya jikin naka yanzu."

"Alhmadulillah Mamy, yanzu bana jin zafin irin na d'azu."

Ya fad'a yana mai sake lumshe idanuwa.
"To kaga amfanin addu'a ai kenan ko, dan haka yanzu ina jinku kuyi azkar kafun ku huce."

Da Tom suka amsa mata, suna masu had'a baki a tare sukai tamkar yadda ta sabar musu a baya, tukun a k'arshe ta bisu da ruwan addu'oin tare da fatan alkhairi, sannan sukayi sallama suna masu fucewa daga cikin falon tare da dosar wurin da motarsu take.
Yau Al'amin ne ya zauna a mazaunin driver, yayinda Asad kuma yake a gefensa a haka suka tafi, yana mai jin fargabar rashin sanin tarbar da zata yi masa a yau na lullub'esa.



*BABBAN ZAURE LOCUS.*

Yau gaba d'aya a halin da ke cikin gidansu Sheikh Ahmad sunyi kwanan farinciki irin Wanda suka manta rabon su da suyi kamarsa, musammamn ma Ummi da Abba ta dalilin dawowar Bir garesu.

A b'angaren Gimbiya Tasmir kuwa jiya ta Jima batai bacci ba, saboda tinanin nata ahalin da ta baro ba tare data san halin da suke ciki ba yanzu.
Tukun a k'arshe bacci b'arawo ya saceta, hakan kuwa shine ya sanya yau bata farka da wuriba har Sai misalin k'arfe bakwai na safe.

A hankali take d'an motsa jikinta, kafin daga k'arshe kuma ta bud'e idanuwanta akan Iman data juyawa b'arin da take baya, zaune akan sallahya tana karatun alqur'ani.
Shiru tayi ba tare da ta iya cewa komai ba, sai aikin kallon bayan Iman da take tana mai sauraron abunda take fad'e, wanda ko kusa ko kad'an bata san ko meye shi d'in ba, sai dai kuma duk da hakan ba k'aramun dad'i taji yayi mata ba a kunnuwanta, kana kuma ga wata irin nutsuwa ta musamman da taji tana saukar mata a ilahirin jikinta.

Tamkar ance Iman ta juyo zuwa kan gadon ta tsayar da karatun da take tana Mai juyowa ta kallota, hakan kuwa shine ya sanya idanuwansa had'ewa cikin na juna.

"Barka da tashi Auntyna, fatan kin tashi lafiya."

Ta fad'a cikin tsananin far'ah, tana mai rufe qur'anin hannunta.
Hakan da Gimbiya Tasmir tajine, ya sanyata ture tattausan bargon da yake rufe a jikinta, tare da mik'ewa zaune daga kwancen da take.
Kana ta bud'e baki tana Mai fad'in.
"Lafiya k'alau, fatan kema kin tashi lafiya."
"Alhmadulillah Aunty na."
Ta fad'a tana mai juyawa ta doshi hanyar bathroom, bayan ta a jiye qur'anin a ma'ajiyarsa.

Ba wani dogon lokaci ta dauka a cikiba sai gatanan ta futo tana mai fad'in.

"Yawwa Aunty ga ruwan wanka can na had'a miki, da duk ma wani abun buk'ata kije kiyi, kafin nan ni kuma na gama gyaran d'akin."

Da Tom kawai ta amsa mata, tana mai sauka daga kan gadon tare da yin hanyar bayin.
Yayinda ita kuma ta fara gyara bedsheet d'in da yake akan bed d'in cikin sauri.

Acan b'angaren Bir kuwa Shima ba shine ya tashi ba har sai misalin k'arfe bakwai da rabi, kasancewar jiya sosai suka Dad'e suna hira shi da Auta kafun suyi bacci, gaba d'aya kuma rabin hirar labarin Iyane yake bawa Auta.

Bud'e idanuwansa yayi dai dai da lokacin da shi kuma Auta ya rufe al'qur'aninsa, hakanne ya sanya Bir sauke wata k'ak'k'arfar a jiyar zuciya, yana mai bin k'uranin harma da Auta da kallo daga kwancen da yake.

"Ina kwana Yayana, Ashe ka tashi."
Cewar Auta cikin far'a, a lokacin daya juyo b'arin da Bir yake.

Lumshe idanuwa Bir yayi, yana mai jinjina masa kai ba tare da yace komai ba, kana daga bisani kuma ya bud'e idanuwansa akan fuskarsa tare da fad'in.

"Kaima harka tashi kenan."

"Eh aini tun asuba na tashi mukaje masallaci ma."

Jinjina kai Bir yayi ba tare da yace komai ba.
Yayinda Auta kuma ya d'ora da fad'in.
"Akwai ruwan wanka na had'a maka aciki da duk wani abun buk'ata na ajema, katashi kaje kayi su Ummi na can na jiran futowarmu."

Sake jinjina masa kai yayi yana mai mik'ewa zaune tare da zuro k'afufuwansa k'asa, tukun daga bisani ya mik'e yana mai juyawa yayi hanyar bathroom d'in.
Yana dab da k'arasawa bakin k'ofar ya juyo yana mai fad'in.

"Gimbiya Bata zo ba?"

"Ina d'in zatazo?"
Cewar Auta da sauri cikin zaro idanuwa waje yana kallon Yayan nasa.

"Nan tazo ta ganni mana."
Bir ya fad'a hankali kwance, shima yana kallon K'anin nasa.

"A'a Yayana, ai mu anan ba'a irin haka, addinin mu bai yadda budurwa tazo d'akin saurayinta ba."

"Kamarya?"

"Ina nufin yanzu Gimbiya ba zata na zuwa d'akinka ba."

Auta ya fad'a a tsanake yana kallon Yayan nasa.
Yayinda shi kuma Bir ya tab'e baki yana kallon Auta, kafin daga bisani kuma ya juya yana mai cigaba da tafiyarsa, tare da fad'in.

"Ku wa'yannan Iyayin naku yayi yawa da yawa, komai ba ayi babu kyau babu kyau."

Da sauri Auta ya gumtse dariyar da taciyosa, saboda jin yadda Bir yayi furucin da alamun dai gaba d'aya abubuwan da aka ce masa ba ayi tun jiya sun fara bashi haushi.
Yayinda shi kuma ya shige cikin bayin yana cigaba da mitarsa.



Baifi minti talatin ta d'auka a cikin bayin ba sai gata nan ta futo k'irjinta d'aure da towel, ruwa na diga a jikinta, a lokacin kuma tini Iman ta gama gyaran d'akin fes.
Hakanne yasa tana ganin ta futo tace.

"Yawwa Auntyna tawo gaban madubi ki zauna, yau nice zan tsara miki kwalliya dan Allah."

Murmushi kawai Gimbiya Tasmir tayi mata ba tare da tace komai ba, sai tafiya da tayi zuwa kan kujerar tamkar yadda Iman d'in ta buk'ata.
Mai ta fara shafe jikinta da shi.
Kana Iman ta matso kusa da ita tana mai fara tsara mata sassanyar kwalliyar da tayi bala'in yi mata kyau da amsarta.
Ba wani ado mai yawa ta cika mata ba, asalima girace kawai ta zana mata, sai wani irin had'ad'd'en man leb'e data shafa mata akan jajayen lips d'inta, sai kuma powder a fuskarta, Amma duk da haka ba k'aramun bala'in kyau tayi ba.

"Masha Allah, gaskiya Aunty na ke d'in mai kyauce wallahi."
Cewar Iman a lokacin data fara taje mayawaiciyar bak'ar tattausar sumar Gimbiya Tasmir.
Yayinda ita kuma ta saki murmushi tana mai fad'in.

"To ai ban kaiki ba fa, Amma kiketa wannan abu haka tun jiya."

"Wane ni wane 'yan kashina, sai dai kuma idan zagina kikeson yine shiyasa zakice haka."
Cewar Iman a lokacin da take tsaga tsakiyar gashin nata.
Kana a k'arshe gaba d'aya ta watsa sa zuwa gadon bayanta ta yadda har ya kusa zuwa k'ugunta, ba tare data tufke mata shi ba.

"Masha Allah, wayyo Auntyna dan Allah kalli kanki a madubi, nasan yau dole Auncle ya rud'e."

Iman ta fad'a tana mai ja baya, kasancewar ta gama yi mata duk abun da ya dace.

Kyakkyawan murmushi Gimbiya Tasmir ta saki, tana mai kallon kanta a madubin tare da jinjina irin kyawun da tayi a yau d'in cikin ranta ita da kanta.
Tukun a k'arshe ta mik'e daga zaunen da take, tana mai yin gaban wadrobe.

Wata azababbiyar bak'ar doguwar riga mai tsananin kyau da d'aukar hankali ta sanya a jikinta, kana ta d'auki wata had'ad'd'iyar mayyar sark'a mai adon duwatsu kalar na jikin rigar ta d'aurata akanta, ta yadda adon duwatsun suka kasance sun zauna akan goshinta.
Yayinda tsintsiyar hannunta da kuma 'yatsunta suke ta futar da k'yallin zobunan gwalagwalen da suke mak'ale a kansu.

Da sauri Iman ta matso zuwa kusa da wurin da take, tana mai d'aukar d'an k'aramin gyalen rigar ta yafa mata shi aka, tukun ta d'an zamosa ya dawo dai dai rabin kanta, ta yadda gaba d'aya sumar kannata ta bayanna a fili gwanin ban sha'awa.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir takobinta ta d'auka ba tare da Iman ta lura da itaba ma, tana mai zurata a cikin wani aljihu da yake daga gaban rigar, wanda ba kowane ke lura da shi bama har dai bawai kasan a kwaisa ba.
Tukun ta rufawa Iman baya suna masu kama hanyar waje.

Sallamar da Iman tayi itace ta janyo hankulan gaba d'aya mutanen dake cikin falon, zaune a k'asan capet suna masu juyowa garesu har da Sheikh Ahmad kuwa.

Bir ma tuni ya shirya cikin shigar riga da wando na jiens, da sukayi bala'in yi masa kyau, yana manne a jikin Ummi tana shafa kansa tamkar wani d'an goye, wato dai atak'aice tun daga jiya har kawo yau ya k:wacewa Auta fadarsa.

Gaba d'ayansu Babu Wanda bai furta Masha Allah ba, saboda ganin irin kyawun da Gimbiya harma Iman sukayi, Sai Kaka kawai da take aikin tab'e baki tana jifan Gimbiya da mugun kallo a wani irin shek'ek'e.

Shi kuwa Bir cikin sauri ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kai gaskiya Gimbiyata kinyi kyau sosai, tawo nan kusa da ni ga wuri ki zauna kinji."

Da sauri gaba d'ayan su suka mayar da idanuwansu kansa, suna kallonsa hatta da Abba kuwa fuskokinsu d'auke da murmushi.
Yayinda Ummi kuwa ta dungure masa goshi tana mai fad'in."

"Naga dai alamun wannan Jaririn nawa kwata kwata baka data ido, ko 'yar kara ma baka iyaba akan Gimbiyar nan taka kai, to ba zata zo nan d'in ba."

Da sauri kuwa ya sanya tafukan hannayensa yana mai rufe fuskarsa alamun yaji kunya kenan wai."
Yayinda mutanen cikin falon kuma gaba d'ayansu suka sanya masa dariya.

Su kuwa su Gimbiya suna k'arasowa wurin suka zauna kanta durk'ushe a k'asa tana mai fad'in.
"Ina kwananku."
Ta fara da gaishe da Abba duk suna amsawa, a haka hartazo kan Kaka.
Amma a mai makon ta amsa tamkar yadda kowa yayi, sai ji sukai tace.

"To da bankwana ba har kya ganni, aikin banza aikin hofi kawai. Yo ni har an isa ayi mun wani salon gulma da kilibibine da har zaija hankalina zuwa ga wanda ya bawa gabas baya!"

Tsit kakejin falon yayi kowa najin ba dad'i da furucin da Kaka tayin.
Yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir ta d'ago idanuwanta tana mai satar kallon Kaka, tukun ta mayar dasu k'asa tana mai mamakin abun da ta tsarewa tsohuwar nan data adabbeta, sai dai kuma yau ko kad'an ba taji haushin kalamanta ba, domin kuwa harta fara sabawa ma.
Hakan yasa ta raya a ranta cewar.
"Lallaine tsohuwa bakisan wacece Tasmir ba, amma nasan ta inda zan b'ullo miki, tabbas zanyi maganinki cikin ruwan sanyi..............✍️




COMMENTS ND SHARE PLS.


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*23*



"Tawo nan ki zauna kusa dani kinji d'iyar albarka."
Ummi ta fad'a tana mai matsa mata gefenta, tare da jin ba dad'i a ranta da furucin da Kaka tayi.

Ita kuwa Gimbiya ahankali ta taso tana mai zuwa ta zauna a jikin Ummi.
Wanda hakan da Kaka ta ganine kuma ya sanyata tab'e baki, tana mai fad'in.

"Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, shi mutum dama idan akace bashi da zuciya ai sai dai hak'uri. Wai harda su 'yar albarka, ko ina albarkar take a tare da kafura."
Ta k'arasa maganar tana mai sake tab'e baki.

Shi kuwa Bir a hankali ya d'ago kansa yana mai watsa idanuwansa a cikin na Kakar tasa, gaba d'aya walwalar fuskarsa na d'aukewa.
Kana ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Naga alamun dai tsowuwar nan bason zamana kike acikin gidan nan ba. Haba dan Allah me tayi miki ne? Idan ma kuma dan ba addinin ku d'aya bane nima ai ba addinina d'aya dake ba."

"A'a Jikana me yayi zafi haka kuma, har kake fad'in banason zamanka a cikin gida, ni wallahi ba haka bane ba, kuma tunda baka so zan dena daga yanzu."

Kaka ta fad'a da sauri, tana mai kama bakinta da hannu.
Yayinda su kuma su Sheikh Ahamd duk sukai shiru ba tare da wani yace komai ba.
Shi kuwa Bir idanuwansa ya lumshe, sabo da jin abun da ta fad'a.
Harga Allah tun kallon farko da yayiwa tsowuwar yaji ta shiga ransa, saboda ganinta da yayi kusan tsufansu d'aya da Iyarsa, amma sai dai kuma abun da takeyiwa Gimbiyarsa yasa yaji ta fara bashi haushi.

"Yawwa kunga muci abinci rana tanayi ko."
Cewar Abba, tukun Iman ta fara saving d'in kowa tana mai tura masa gabansa.
Haka sukaci abincin sunayi suna d'an barkwancinsu abun gwanin ban sha'awa.
Yayinda Bir kuma yake ta basu labarin Iyarsa. A haka har suka gama tas.
Kana Iman da Gimbiya Tasmir suka d'auke kwanikan suna masu kaisu kiching.
Shi kuwa Sheikh Ahmad mik'ewa tsaye yayi yana mai fad'in shi ya huce makaranta.

Da Allah ya kiyaye hanya suka rakasa.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir suna shiga cikin kiching d'in taga wani window.
Hakanne yasa tana ajiye kwanikan ta huce gabansa tana mai lek'awa.

Had'ad'd'en d'an k'aramin garden ne mai cike da shuke-shuken furanni kala-kala gwanin ban sha'awa da shi.
Take kuwa taji wurin yayi matuk'ar birgeta, kasancewar ita dama ko da tana gida bata da wurin zama muddin zara futo waje wanda ya huce garden.
Hakanne yasa da sauri ta juya tana mai cewa.

"Kinga 'Yar uwa inace hanyar da zata kaini wurin nan."

"Laa ai Aunty kina futa daga kiching ma ga wata k'ofa nan a kusa data kiching d'in, tanan ma idan kika bi ciki zata kaiki, zakuma ki iya zagayawa ta waje duka."

"A'a bara nabi tanan cikin ma kawai."
Cewar Gimbiya Tasmir tana mai fucewa, ba tare data jira jin abunda Iman zata sake fad'a ba.

Tana kuwa futa ta d'ora yatsunta akan handle d'in k'ofar, tana mai murd'asa.
Take kuwa ta bud'e, hakan yasa ta danna kanta zuwa ciki fuskarta d'auke da tsantsar annuri.

Shi kuwa Bir ganin da yayi Abba ma ya tafine, ya sanyasa kallon Ummi yana mai cewa.
"Ummi zanje waje."

"To Yarona amma fa karka huce bakin get, tunda kaga basanin wani wuri kayiba."

"Tom Ummina bazan huce ba."
Ya fad'a yana mai mik'ewa yayi wajen.
Yayinda ita kuma ta tashi tana mai hayewa sama zuciyarta cike fal da farinciki.

Shi kuwa Bir yana futa compound d'in kai tsaye ya huce wurin wasu had'd'd'un kujerun silver daya gani, yana mai zama akan su.
Kana ya lula duniyar tinanin halin da Iyarsa take a ciki yanzu.


Acan b'angaren su Gimbiya Haddiyal kuwa, k'arfe tara da rabi suka iso cikin garin wasai.
Hakanne yasa tayi sauri ta durk'usa tana mai d'ago randarta ta d'orata akan cinyarta.
Kana ta d'ago jarkar nan tata tana mai bud'e murfinta ta tsiyaya yalon ruwan aciki, tukun ta d'ebi iccinan da zatayi amfani da su ta zubasu a cikin randar, sannan ta dunk'ule layunta a cikin tafin hannunta tare da rumtse idanuwanta, tana mai fara fad'in.

"Zaiba! Zaiba!! Zaiba!!!"
Tukun ta bud'e idanuwan nata.

Sosai ruwan ya dawo fari kar kuwa, tukun sai ga hanya nan ta fara bud'ewa, yana mai nuna musu inda zasubi tamkar a tv haka take gani.

Hakanne yasa ta jan dogon numfsahi tana mai fesarwa, kana ta saki murmushi afili, tana mai bud'e baki cikin tsananin farinciki tacewa drivern.

"Kaga wannan hanyar zaka bi."
Kasancewar hanyar data nuna masa tini ruwanta ya nuno mata ita.

Haka sukai ta tafiya tana mai fad'in hanyar da zasu bi har suka shigo cikin unguwar Babban Zaure.

Cikin tsananin farinciki Gimbiya Tasmir ta fara sakin murmushi, tana mai kallon unguwar data kasance tasu Gid'ad'on ta yau gata a cikinta.

A dai-dai lokacin da suka zo gifta gidansu Sheikh Ahmad taga hoton gidan ya tsaya cak a cikin ruwan.
Kana daga bisani kuma gaba d'aya ya d'auke duka ruwan na dawowa kalarsa.
Hakan yasata bud'e baki cikin sauri tana mai fad'in.

"Yawwa tsaya anan gamu munzo."

Ta k'arasa maganar tana mai d'auke randar daga kan cinyarta ta ajiyesa a k'asa.
A kuma lokacin Buba daya riga ya futo daga cikin motar ya k'araso wurin yana mai bud'e mata k'ofa.

Kyawawan fararen k'afafuwanta ta fara zurowa waje, kafin daga bisani kuma ta sako duka gangar jikinta.

Lumshe idanuwanta tayi, tana mai jin wani irin farinciki mara misaltuwa na lullub'eta, kana daga bisani ta bud'esu akan get d'in gidan su Sheikh Ahmad.

Wani irin kyakkyawan murmushine ya sub'uce mata, ta yadda har sai da dimple d'in ta suka bayyana.
Kana ta durk'usa tana mai zura hannunta a cikin motar ta d'auko sandar tsafinta.
Sannan ta kauce daga jikin k'ofar Buba ya rufeta.
Tukun ta kallesa tana mai fad'in.
"Ka jirani anan, ni yanzu zan shiga ciki wurin Gid'ad'o am."

Jinjina mata kai Buba yayi yana mai had'awa da fad'in.
"Afuto lafiya gatan Shalle."

Murmushi kawai ta saki, tana mai dosar get d'in gadan-gadan.

Cak ta tsaya adai-dai lokacin data d'ora hannunta akan k'ofar tana shirin turata, saboda yadda taji zuciyarta tayi wani irin harbawa da azabar k'arfi.
Hakan yasata rumtse idanuwanta da k'arfi tana mai bud'e su.
Kana ta tura k'ofar tana mai danna kanta zuwa ciki.

Ido hud'u sukayi da Bir da yake zaune akan kujerun da suke kallo get d'in.
Wanda hakan kuma ya sanya Gimbiya Haddiyal jin zuciyarta tayi wata irin harbawa, kana daga bisani kuma saiga hawaye nan sun tuttud'o daga cikin idanuwanta, sai dai kuma basu kaiga futowa waje ba.

A hankali ta fara girgiza kanta tana mai sakin wani irin murmushin farinciki, saboda ganin Gid'ad'o am d'inta da tayi a zahiri yau ba a mafarkin data saba ganinsa ba.

Shi kuwa mai gadi da sauri ya k'araso wurin da take yana mai fad'in.

"Sannu da zuwa Hajiya, lafiya wakike nema ne."

Inda yake bata d'aga kai ta kallaba, asalima ko jinsa batayi ba, sai ma k'afafuwana data fara d'agawa tana mai dosar inda Bir yake, har lokacin kuma bata janye idanuwanta daga cikin nasa ba, tamkar yadda shima ya kasa janye nasa daga cikin nata, kana kuma murmushin dake akan fuskarta bai d'auke ba.
Shi kuwa Bir tunda ya d'ora k'wayar idanuwansa a cikin nata yaji tamkar mayen k'arfene ya rik'e idanuwansa a cikin natan.
Sosai kyawun yarinyar yayi bala'in tafiya da shi duk da bai santaba, asalima bai tab'a ganinta ba sai ayanzu, amma kuma ya rasa dalilin dayasa ya kasa janye idanuwansa daga cikin nata har ta k'araso wurin.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal tana zuwa dab da shi taja ta tsaya tana mai lumshe idanuwanta.
Take kuwa hawayen da suke kwance a cikinsu suka samu damar silalowa aguje zuwa kan kuncinta.
Kana daga bisani ta bud'e su akan fuskar Bir, tana mai bud'e baki cikin tsananin farinciki tace.

"Ashe da rabon zamu gana a zahiri, ashe dama zan sanyaka acikin idanuwana gani gaka Gid'ad'o am.
Hak'ik'a na wahala iyakar wahala a soyayyarka, nayi kuka iyakar kuka tamkar hawayena zasu k'afe ta dalilinka, a kullum banda wani buri wanda ya huce ace na gano inda kake, a kullum ina kwanciyane da tinaninka, sannan kuma na tashi da tinaninka, wanda haka yasa wasu ke mun kallon wacce ta samu tab'in hankali, yayinda wasu kuma suke tinanin Aljanine ya aureni.
Anyi mun magani, anyi mun fad'a, amma duk basuyi aiki ba.
Shin kasan kome yasa hakan? Saboda nina san kai d'in mutum ne, jikina bai tab'a bani cewar kai Aljan bane, zuciyata bata tab'a rayamun cewar bazamu had'u a zahiri wataran ba. Ina sonka Gid'ad'o am, na fara sonka tun kafin na gama sanin kaina, ina fatan kaima d'in kayi farinciki da zuwana ko?"
Ta k'arasa maganar cikin kuka da dariya tamkar wata mara hankali.
Yayinda shi kuma Bir yayi suman zaune a wurin da yake, ba tare daya iya ko d'aga hannunsa ba, sai kawai idanuwansa da har yanzu suke akan fuskarta, yana mai jin kalaman da suke futowa daga cikin bakinta, wa'yanda kuma sukayi matuk'ar rud'asa, kana kuma suka sanya bugun zuciyarsa tsananta.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir da take zaune a cikin garden d'in nan tana mai tinanin gida, lokaci d'aya taji zuciyarta tayi wata irin mahaukacin bugu da tsananin k'arfi.
Wanda hakan kuma ya sanyata mik'ewa tsaye firgigit daga zaunen da take zuwa tsaye.
Kana tayi hanyar waje da bala'in sauri, sannan kuma cikin matuk'ar firgici, saboda haka kawai taji zuciyarta na raya mata cewar Bir d'inta ba k'alau yake ba.

Amai-makon tabi ta hanyar data biyo ta shigo wurin, sai kawai tabi ta babbar hanya, wacce zata sadata da compound ba tare data lura da nan d'in ma ta biyo ba.

Zuro kanta wajen yayi dai-dai da lokacin da zuciyarta tayi wani irin tsananin harbawa da matuk'ar k'arfi, wanda har hakan kuma ya sanyata rumtse idanuwanta.
Tukun daga bisani ta bud'e su, wanda kuma cikin rashin sa'a sai suka sauka akan kyakkyawar budurwar data gani tsaye a gaban Bir d'inta da yake zaune, tana mai jifansa da wani irin murmushi tare da kallo, irin wanda kallo d'aya mutum zai mata ya gane ko wane kalar murmushine.
Take kuwa jikinta ya d'auki wata irin karkarwa da tsuma.
Hankalinta gaba d'aya yakai k'ololuwa wurin tashi, matsanancinyar fargabar rashin sanin ko wacace itan suka lullub'e zuciya da ruhinta.
Wani irin mugun kishi taji na taso mata tun daga k'asan zuciyarta, saboda yadda taga tana cigaba da murmushi tare da jifansa da wani irin kallo.
Lokaci d'aya launin idanuwanta gaba d'aya suka fara sauyawa, kafin daga bisani kuma ta fara d'aga k'afafuwanta ba tare da tana ganin ko cikakken gabanta ba ta doshi wurin da suke gadan-gadan.

Ba zato ba tsammani kawai sukaji sautin dirar siririyar muryarta da take cike da fushi a cikin kunnuwansu, tana mai fad'in.

"Ya akai ne? Meke faruwa ne Jarumina.?"

Tamkar saukar aradu aka haka Gimbiya Haddiyal taji dirar muryarta a cikin dodon kunnuwanta.
Yayinda Bir kuma ya d'ago kansa da matuk'ar sauri, yana mai watsa idanuwansa akan fuskarta.
Ita kuwa Gimbiya Haddiyal cikin wani irin yanayi ta d'ago kanta, tana mai watsa idanuwanta akan fuskar Gimbiya Tasmir.

A lokaci d'aya zuciyoyinsu sukayi wata irin matsananciyar harba.
Kafin daga bisani kuma suka kafe junansu da ido, ko wacce kyawun 'yar uwarta na firgita ta, yayinda matsanancin b'acin rai kuma yake bayyana akan fuskokinsu.
Shi kuwa Bir a hankali ya janye idanuwansa daga kan fuskar Gimbiya Tasmir, yana mai mayar da su kan fuskar Haddiyal.
So yake ya gano wacce tafi wata kyau acikin su, amma gaba d'aya abun ya gagara.

Kafe junansu sukayi da ido, ko wacce tana jin yadda zuciyarta ke bugu da tsananin k'arfi.
Kafin daga bisani kuma Gimbiya Haddiyal ta bud'e baki cikin wata irin kausashash-shiyar murya, tana mai fad'in.

"Wacece ke d'in?"

Shiru Gimbiya Tasmir tayi tamkar ba zata ce mata komai ba, sai kallonta kawai data cigaba dayi zuciyarta na zafi, kana daga bisani kuma ta bud'e baki cikin muryarta da take futar da amon sauti, tana fad'in.

"Matarsace, masoyiyarsa, kuma rabin rayuwar...."

"Keeeeeeee!!!"

Haddiyal ta buga mata wata irin gigitacciyar tsawa da fad'in haka, wacce ta sanya har su Ummi da suke a fallo tare da Kaka da kuma Iman jin sautinta.
Yayinda zuciyarta kuma ke wani irin bugu da tsananin k'arfi, gaba d'aya lokaci guda launin idanuwanta suka sauya daga fari zuwa jajajir.

Shi kuwa Bir kafeta yayi da idanu, yana mai kallon ikon Allah, ba tare daya iya cewa komai ba.
Yayinda Gimbiya Tasmir kuma ta sake gyara tsayuwarta a wurin, tana mai cigaba da jifanta da wani matsiyacin kallo, gaba d'aya idanuwanta itama sun koma jajaye.

Me gadi kuwa da yake zaune akan bencinsa a wani irin firgice ya mik'e tsaye, saboda razanar da yayi da ihun da Gimbiya Haddiyal tayi.

Cikin zafin rai da tafasar zuciya tare da jin tsanar Gimbiya Tasmir a cikin zuciyarta ta bud'e baki tana mai d'orawa da fad'in.

"Kinyi na farko kinyi na k'arshe, ina mai tabbatar miki da ko kallon

Please Login or Register in order to submit comment