Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da har abada bazai manta ta ba akan abun da yayi mata, sai dai kuma ina, bazata iya hakan ba, saba da tsananin girmama junansu da suka taso da shi.
Ita kad'aice Innawuro ta raina ta, amma bayan haka kowa na jin tsorn yayansa a gidan nasu.

"Garinmu zantafi Hama, bazan iya k'wana a cikin garin nan ba."

Ta fad'a tana mai juyar da kanta gefe, ba tare data bari sun had'a ido ba.

"Kamarya gida kuma yanzu da yamma Haddiyal, to idan mun tafi yanzuma mu isa a wane lokaci kenan?"

Habu ya fad'a yana mai kallonfa.

"Zuciyata zafi take, bazan iya zama garin dana san ya kasance garinsu ba."
Ta fad'a tana mai sake taune leb'e.
Shi kuwa Habu sosai ya girgiza da jin kalamanta, wato kenan tsanar da takemasa har takai wacce bama zata iya zama a garin daya kasance garinsu ba.

Hakanne ya sanya sa sake bud'e baki yana mai fad'in.

"Yanzu dai bazamu tafi gida ba Haddiyal, dan haka ki tawo mu huce can, inyaso goben sai mutafi da sassafe."

Yayi maganar ba wasa, yana mai sakin hannunta yayi gaba zuwa wurin motar da suiazo acikinta, wacce ta kasance tasa.
Hakan da tajine ya sanyata juyawa tana mai bin bayansa, gaba d'aya zuciyarta a dagule.

A haka suka tafi ba tare da wani na cewa wani komai ba,, har suka isa d'an madai-daicin kyakkywan gidan su.

Gagaba d'aya walwalarta b'acewa tayi tas.
Ta yadda hatta da abinci bata iya cinsa ba, sai salllahrta kawai data samu ta dungura, tamkar yadda ta saba akoda yaushe, tukun ta sanya kayan bacci ajikinta tana mai kwanciya atsakiyar k'aton gadon da yake acikin d'akin nata, tare da jan bargo ta rufe jikinta.
Ko minti goma batayi ba da kwanciyar bacci b'arawo yayi gaba da ita da k'arfinsa.

Cikin wani kyakkywan lambu mai cike da duwarwatsu tare da wasu irin had'ad'd'un furanni masu tsanannin k'amshi ta tsinci kanta.
Sanye take da kayan fulani ba ko takalmi a k'afarta, tana ta faman juyi awurin tare da sake baza kunnuwnata.
Tana mai neman ta wurin da sautin daddad'ar busar sarewar da taji yana tashi yana dukan kunnenta yake futowa, wanda rabonta da taji irinsa tun a farko fara ganin Gid'ad'on ta acikin mafarki, alokacin yana zuwar mata sanye da kayan sarauta ajikin sa.

Sosai take juyi a filin daya kasance cike da iska mai sanyin dad'i ta ko ina.
Yayinda wasu irin fararen ruwa sukayiwa lambun k'awanya.

So take ta gane ta inda sautin yake futawa, amma gaba d'aya ta kasa, sabo da yadda ko ina na cikin wurin ya d'auka da shi.

Tana nan tsaye a wurin kuwa saiga kyawawan tsuntsaye nan har guda biyu, mace da namji sun sauka a gabanta.

Take kuwa ta saki murmushi cikin tsananin jin dad'i, sabo da da fahimtar da tayi na sunzo su nuna mata hanyane.

Su kuwa tsuntsayen da sauri suka k'ara tashi, suna masu fara shawagi a saitin fuskarta.
Kana daga bisani suka fara tafiya, itama ta rufa musu baya fuskarta d'auke da murmushi.

Basu tsaya ba har sai da suka isa bayan wani tafkeken dutse.
Hakanne ya sanya ta k'arasawa wurin itama.
Da sauri kuwa ta tsaya abayan mutumin data gani sanye da kayan sarauta ajikinsa ya juya baya yana kakkon dutsen.
Kana kuma yana aikin busa sarewar da dad'inta ke ratsa har cikin k'wak'walwarta.
Wato dai Gid'ad'onta yazo mata a irin yanayin daya fara zuwar mata, kafin daga baya kuma ya canza shiga.
Kasancewar kuma a wancan lokacin bai tab'a juyowa ta kalesa ba, sai dai taga jikinsa ta baya, shiyasa yanzu ta gyara tsayuwarta tana mai fad'in.

"Me yasa zaka juya mun baya, bayan kuma kasan ganin fuskarka shinafi muradi sama da komai a rayuwa."

Ta k'arasa furucin tana mai fesar da iska.
Dakatawa da busa sarewar da yake yi yayi shima, kafin daga bisani kuma ya saketa a k'asa ta sulale ta fad'i.
Tukun ya fara juyo gangar jikinsa ahankali zuwa wurin da take, har ya gama juyowa duka.

Cikin wani irin yanayi na tsantsar firgici, rud'utare da tashin hankali ta d'aga yatsar hannunta tana mai nunasa jikinta na d'aukar kyarma.

Shi kuwa Yarima Asad sosai idanuwansa suke zubar da k'walla, ta yadda har gaba d'aya fuskar sa ta jik'e sharkaf.
Kana daga bisani ya bud'e baki cikin kuka yana mai fad'in.

"Bashine Gid'ad'onki ba, nine nan masoyinki na asali, ni kika fara sani bashi ba, dan Allah karki barni Gimbiyata, kizo gareni duk abunda kike buk'ata zan miki shi a rayuwa"

Ya k'arasa maganar cikin matsanancin kuka yana kallonta.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal da gaba d'aya ta rud'e ta firgice da ganinsa, bata san lokacin da ta fara ja da baya ba tana girgiza masa kanta.

Ganin da tayi yana biyota tare da mik'o mata hannunsa yana kuka ne, ya sanya ta juyawa tana mai kwasa aguje, amma shima sai ya biyota da gudu yana kiran sunanta tare da fad'in karta tafi ta barsa shine masoyinta na asali.

Firgigit kuwa ta farka daga baccin tana mai sakin haki, tamkar wacce tayi gudun gaske.
Ga wani irin uban gumi da ya jik'ata yay mata sharkaf.

Girgiza kanta ta farayi tana mai zuro k'afafuwanta k'asa.

Gaba d'aya kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci yadda hankalinta yake a tashe.
Kafin daga bisani kuma ta fara zagaye falon, hawaye na kwaranya daga cikin idanuwanta, sabo da yadda k'wak'walwarta ke sake tariyo mata mafarkin tamkar yanzu abun ke kan faruwa.

Ji tayi gaba d'aya ta k'agara safiya tayi, sabo sa su tafi kota samu taje gida tayi bincike akan Gid'ad'onta, domin kuwa ba k'aramun firgitata mafarkin nan yayi ba.
Atak'aice dai yau kwanan tsaye tayi, har sai da aka fara kiraye-kirayen sallah a massalatai, tukun ta fad'a bathroom da sauri dan tayi wanka.

Misalin k'arfe shida na safiya ta gama shiryawa tsaf cikin wata black arabian gown.
Tukun ta tafi d'akin Habu tana mai k'wank'wasa masa.
Sosai mamakin ganinta a shirye ya lullub'esa alokacin daya bud'e d'akin.
Yayinda ita kuma ta turb'une fuska sabo da ganin da tayi da alamun yanzu ya tashima.
Tukun ta juya baya ba tare da tace masa komai ba bayan gaishesa da tayi.

Hakan da Habu ya ganine ya sanya sa sakin murmushi, tukun ya koma ciki shima.

Misalin k'arfe bakwai da rabi dai-dai suka haye kan kwalta, Habu yana mai daya sanin tawowa da Haddiyal.


****
A wani irn haukace Al'amin ke tuk'in motar akan titi, sabo da yadda yaga Asad na hawaye da gasken-gaske tare da dafe k'irjinsa.
Atak'aice dai yau shine ya dawo Asad d'in.
Hakan yasa kuwa cikin k'ank'anin lokaci suka k'arasa cikin masarautar wasai.

Kai tsaye Al'amin ya doshi part d'in su Asad da motar.
Suna zuwa ko parking d'in arzik'i Asad bai bari Al'amin ya gama yi ba ya bud'e murfin motar yana mi fucewa.
Tukun ya doshi k'ofar da zata sadasa da falonsu cikin sassarfa, har lokacin idanunsa na d'igar k'walla.
Kai tsaye ya doshi corridor'n da d'akin sa yake ba tare daya tsaya bi takan jama'ar daya huce acikin falon ba.
Yana shiga cikin d'akin nasa ya bugo k'ofar da k'arfi.
Kana ya zube akan kujerar da take akusa da shi, yana mai sanya hannunsa ya wargaza sumar kansa.
Kana ya dafe goshinsa da hannu d'aya, hawaye na cigaba da tsiyayo masa acikin idanu.
Shin me kuma zaiyi yanzu tsosa bayan duk abun da yayi?
Shin meye ai'bunsa? Da me wancan d'in yafisa da har take fad'in shi bai kai mutumin da zataso ba?

Sosai yake jin zuciyarsa na zafi tamkar ana cinna mata huta. Ga kuma wani irin matsanancin ciwon kai dayaji ya kawo masa ziyara lokaci guda.

Shi kuwa Al'amin koda ya futo daga cikin motar, amai-makon ya biyo bayan Asad sai kawai ya doshi part d'in Babban Yaya kai tsaye, domin yaje ya shaida masa abunda ke faruwa, sabo da ayi mai yuwuwa tun kafin damuwa ta sawa Asad wani ciwon.
Sabo da ba k'aramun firgita yayiba da yadda yaga Asad na kuka tare da dafe k'rji.
Domin kuwa shi kansa bazai taba iya tuna rabon da yaga hawaye a idanuwan Asad ba sai yau.

Zaune ya samu Babban Yaya akan kujera yana danna wayarsa.
Hakanne yasa sa k'arawa kusa dashi ya zauna, yana mai fad'in.

"Barka da hutawa Yayanmu."

"Yawwa Al'amin har kun dawo daga wurin party ne, ina shi Asad d'in yake ne?"
Babban Yaya ya fad'a yana mai janye idanuwansa daga kan wayarsa.

"Akwai matsala Yaya, dan Allah kayi wani abu akan Aboki, gaba d'aya nafara tsorafa da lamarinsa."
Al'amin ya fad'a muryarsa na rawa.
Shi kuwa Babban Yaya cikin tsantsar tashin hankali yace.

"Innalillahi wa'innailaihr raji'un, me yake faruwa ne, yana inane yanzu."

"Ya huce d'akinsa."

Cewar Al'amin, kana ya d'ora da basa labarin duk abun da ya faru, tundaga farko har zuwa k'arshe.
Shiru Babban Yaya yayi yana mai buga tagumi.
Tukun daga bisani ya d'ago yana mai cewa.

"Yanzu kaje ka lallashesa, in sha Allah idan na futo zan shiga wurin nasa, kuma zanje mu sake yin magana da Dady."

"Tom." Al'amin ya fad'a yana mai mik'ewa jiki asanyaye yayi waje.

Cikin k'ank'anin lokaci gaba d'aya labarin abun daya faru a wurin birthday d'in Asad ya cika gari, domin kuwa tini wa'yanda suka d'auka suka watsa sa a social media, tundaga kan facebook, instagram, twitter, whatsApp harma da youtube.
Kasancewarsu fitattu dagashi har Billy, domin kuwa gaba d'ayansu babu wanda IG basuyi veripying d'in sa ba, kasancewarsu na 'ya'yan manya masu tashe da masoya kuma.

Saosai kuwa abun yayi matuk'ar jan hankalin jama'a, gaba d'aya akaita d'orawa a status kowa da irin abun da yake fad'e akansu su duka ukkun.

Anan cikin Masaratar Wasai ma kuwa, tini labarin ya zagaye ko ina, hatta da kunnen hadimansu kuwa.
Yayinda wasu suka tausaya masa, wasu kuma irin magautansu abun yayi musu mugun dad'i, tayadda har sukai fatan Allah yasanya hakan ya zama sanadin bugawar zuciyarsa tamkar yadda sukaji yana fad'awa Haddiyal acikin Videon da suka kalla.

Ab'angaren su Huwaila kuwa sosai hakan yayi mata dad'i itama, sabo da tana ganin wannan d'in tamkar wata damace tazo mata wacce zata samu damar cika burinta na shekara da shekaru akansa.

Washegari misalin k'arfe tara na safe Babban Yaya ya turo kansa cikin falon Asad.

Kwance ya hangesa akan kujera ringin-gine idanuwansa na kallon rufin d'akin.
Domin kuwa kwata-kwata ko sallamar da Babban Yaya yayi baiji ba, sabo da yadda yayi nisa aduniyar tinani, ballantana kuma har ya amsa masa.
Hakan yasa Babban Yaya ya shigo yana mai yowa wurin da yake.
Tukun ya zauna akujerar da take akusa dashi, yana mai kallon yadda gaba d'aya ya rame tamkar wanda yayi doguwar jinya.
Kafin daga bisani kuma ya mik'a hannunsa asanyaye yana mai d'an bubbuga k'afafuwansa Asad, tare da fad'in.

"Tashi ta zauna zamuyi magana kaji."

Firgigit kuwa ya bud'e idanuwansa, yana mai kawosu kan Baban Yaya.
Kana daga bisani ya mik'e zaune yana mai fad'in.

"Barka da Safiya Yayana, amma fa banji ko motsin shigowarka ba."
Yayi maganar asanyaye yana mai kallon sa.

Shiru Babban Yaya yayi ba tare daya iya amsa gaisuwar tasa ba, sai kawai kallonsa da yake yi, wanda hakan kuma ya sanya shi Asad yayi k'asa da nasa idanun.
Kana daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Tayaya zakaji motsin shigowata, bayan ka d'orawa kanka damuwa akan abun da bai kai yakawo ba."

Da sauri Asad ya d'ago kansa yana mai sake kallon Yayan nasa, sabo da jin da yay yace wai abunda bai kai ya kawo ba.

Shi kuwa Babban Yaya ganin kallon da Yarima Asad d'in yayi masane, ya sanyasa d'orawa da fad'in.

"Bazan b'oye maka ba k'anina, hak'ik'a nayi mamakin jin abunda akace ka aikata.
Shin wayace maka ta haka ake samun mace idan bata sanka?
Shin kasan yadda abun da ka aikata ya baza duniya kuwa, yanzu gaba d'aya ko ina kaje a social media zancenka ake..."

"Yaya wannan ni duk bai dameni ba, burina kawai bai huce naga na mallaki Haddiyal ba, kuma wallah zan iyayin har abun da yafi haka muddin zata amshi soyayya ta."

Asad ya fad'a murya na rawa, yana mai kallon yayan nasa.

"Ai kuwa ina mai tabbatar maka da cewar bazata tab'a sonka ba, muddin irin shashancin da kayi jiya zaka cigaba dayi."

"To ya zanyi, me zanyi ta soni Yayana?"

Asad ya fad'a da sauri yana mai rik'o hannun Babban Yaya da nasa.

"Wane abune kasan tafiso a rayuwa, mai tafi k'auna, sannan kuma mai tafi k'i, kai d'in mene yafi bata haushi a tattare da kai kuma?"

Babban Yaya ya jero masa tambayoyin yana mai kallon fuskarsa.

Yayinda shi kuma ya rumtse ido yana mai tafiya duniyar tinani.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.
"Shi tafi so sama da komai a rayuwarta tace, abun da kuma tafi k'i nine, sannan kuma tace ta tsani sitirar da nake sawa wai ta 'yan iskace."

"To shi d'in kasan dalilin dayasa tafi sonsa sama da kowa?"

"A'a."

"Sabo da yana mata abunda take sone, sannan kuma yana yin shiga irin wacce take birgeta.
To idan hakane kaima mai zai hana ka fara sanya irin kayan da take so d'in.

"Kamarya kenan Yaya?"
Yarima Asad ya fad'a cikin wani irin yanayi, yana mai kallon Yayan nasa.
Shi kuwa Babban Yaya zama ya gyara akan kujerar, yana mai ganin hakan ma tamkar damace Allah ya turo musu wacce zasu samu su sauya Asad ya dena abun da yake yi da basu kamata ba.
Hakan yasa ya d'ora da fad'in.

"Kamar yadda kaji na fad'a maka, ma'ana dai kaima ka sanya manyan kayan, kaya na mutunci kaje wurinta, ni kuma ina mai tabbatar maka da ko yayene ne zata tsaya ta saurareka aranar, wato dai su kayan zasu ja hankalinta tunda irin shigar da take so kenan."

"Inaaa Yaya gaskiya ni bazansa manyana kayaba, haba ai zafima sai ya illatani."

"To ai kuwa baka shirya samunta ba, dan haka ni sakar mun hannuwa ina da abunyi."

Babban Yaya ya fad'a da d'an k'arfi, yana mai funcike hannuwansa daga cikin na Yarima Asad ya fara shirin mik'ewa ya tafi.
Hakan da Yarima Asad yaji ne ya sanya sa yin sauri yace.

"A'a Yaya, dan Allah ka zauna karka tafi, na yadda zan sa har dai hakan zaisa ta soni.".

"In sha Allah zata soka ma muddin zakayi hakan, sabo da ita mace ana jan hankalinta ne ta hanyar kyautatawa, yin abun da aka san yana birgeta, tare kuma da nisantar abubuwan da bata so, hakan shi zai sanya har mutum ya fara birgeta, bawai duk irin yadda kai kakeyi ba, dan haka duk ranar da zaka koma kayi shigar manyan kaya, ni nasan idan ka dawo zaka bani labari."

Ya k'arasa maganar yana mai juyawa ya tafi.
Shi kuwa Yarima Asad lumshe idanuwansa yayi, yana mai tinanin ta yadda za'ayi ya iya sanya manyan kaya, sabo da shi dai ban san kome yasa ba haka nan ya wayi gari yaji aduk duniya babu kayan daya tsana sama da irinsu, kwata-kwata basa birgesa ko kad'an, asalima idan ya sasu ji yake tamkar ya lullub'a manyan barguna a jikinsa.

Shi kuwa Babban Yaya koda ya futa daga wurinsa, kai tsaye part d'in mai martaba ya tafi, domin yaje su tattauna akan batun zuwa nemarwa Asad auren yarinyar, sabo da bazasu iya jurar ganinsa acikin halin da yake cikiba.

***
Da gudu Billy ta fuce daga cikin motar tun kafin Zee ta gama dai-daita parking, tana mai rugawa aguje zuwa cikin gidan nasu cikin matsanancin kuka.

Zumbur Dady'n ta da kuma Momyn ta da suke zaune acikin falon suka mik'e tsaye hankalinsu abala'in tashe, suna masu yowa kanta.

"Na shiga ukku na lalace, wayyo Dady wayyo Momy mutuwa zanyi Prince ya cuceni."

Ta fad'a da wani irin k'araji tana mai cizge ribom d'in kanta tare da warwatsa gashin kanta, bayan ta zube gwiwoyinta ak'asa.

"Innalillahi wa'inailahir raji'un, meya farune me Prince d'in yayi miki? Dauhgter! Daughter!!!"

Daga Momyn nata har Dadyn ta suka fad'a a matuk'ar rud'e suna masu rige-rigen kamata.

Wayyo Allah na zuciyata bugawa zatayi, Prince ya cuceni ya hulak:antani wayyo Momy mutuwa zanyi!"

Ta sake fad'e tana mai sake zubewa ak'asa tare da dukan lallausan capet d'in cikin d'akin da hannunta.

Hakan da mai Girma Gwamna ya ganine ya sanya sa shirin fucewa waje, hankali abala'in tashe da niyyar yaje yasa ajiyo masa labarin abunda Asad yayiwa 'yarsa, sabo da ganin da sukayi tak'i fad'a musu.
Akuma lokacin ne suma su Zee suka shigo cikin falon.

Hakan yasasa dakawa a wurin yana mai fad'in.

"Me Asad yayiwa Bilkisu ne? Ku fad'a mun mai yayi mata yauma?"

Zee ce ta bud'e baki tana mai fara zanyo masa duk abun da ya faru, har karuwar daya kirata da shi kuwa.
Kana ita kuma d'ayar ta zaro wayarta tana mai kunna datar ta ta huce IG direct, sannan ta nunowa Dadyn Billy fuskar wayar tana mai fad'in.

"Kaga fa irin cin mutuncin da yay mata Dady, yanzu gashinan har jama'a sun samu gaba d'aya labarin da ake a kowace kafar sadarwa yau kenan.

Tunda Zee ta fara karanto musu abunda ya faru gaba d'aya daga shi har Momyn Billy sukayi suman tsaye, suna masu binta da idanuwa tare da saurarenta, kana kuma bayan ta gama suka d'ora da kallon videon da d'ayar ta hasko musu.

"Yanzu ni wannan Yaron zai hulak'anta haka, kamarni za'aciwa mutunci aduniya, hak'ik'a ba iya ke kad'ai yayiwa ba, koma nace ni yaron nan yaciwa mutunci bake ba, dan haka bance ko wayarsa ki kira ba daga yau, gobe zamuje har gaban iyayensa ayi komai ya huce."
Cewar mai girma Gwamna ransa a mugun b'ace yana mai kama hanyar waje ya fuce da matuk'ar sauri.
Hak'ik'a tunda yake a rayuwarsa bai tab'a jin ransa ya b'aci ba irin yau, sabo da ba k'armun hulak'antasa Asad yayiba, domin kuwa ya riga daya sani wannan abun har siyasarsa sai ya shafa, wai kamar shi 'yarsa ta cikinsa aka samu wani ya hulak'anta, har kuma ya kirata da karuwa acikin jama'a.
Tabbas da ace Asad ba d'an wani bane shima, da daga yau bazai k'ara ko shurawa ba a duniya, bayan haka kuma da abun ya shafi karankaf danginsa.
Sai dai a yanzun ma baya tinanin zai iya hak'ura, bari dai kawai goben tayi suje wurin Iyayensa, sai suji irin matakin da zasuce zasu d'auka.

Ya raya haka acikin ransa yana mai zaro wayarsa domin ya kira abokinsa Alhaji saleh, da sukaje tare da shi a wancan karan.


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Cikin tsantsar tashin hankali Sarki Barbaru ya k'arasa bakin k'ofar d'akin Gimbiya, yana mai bugata tare da fad'in.

"'Ya! 'Ya!! 'Ya!!!"
Yake fad'i da wani irin k'arfi, yana mai cigaba da buga k'ofar, sabo da jin da yayi shiru bata bud'e ba.

Da gudu matansa suka k'araso cikin falon hankulansu a tsantsar tashe, sabo da sautin bugun k'ofar da sukajiyo da k'arfi.

Shi kuwa Sarki Barbaru jin da yayi shiru har sama da minti biyar yana bugun k'ofar tare da kiran sunanta ba tare data bud'e ba, ya sanya barin jikin k'ofar yana mai komawa wurin window tare da sanya hannunsa ya turasa da k'arfi.

"K'asss! Kakejin k'arar karyewa sakatar jikin windown, yana mai matsawa gefe.
Kana Sarki Barbaru ya k'ara zuwa kansa yana mai waige-waige tare da kiran sunanta.
Kafin daga bisani kuma ya koma yayi tsit yana mai zare idanuwa, tare da wuwwurgasu cikin d'akin, sabo da yadda yaga ko k'yallinta bai hangoba, saima wasu daga cikin kayanta daya gani zube ak'asa.

"Ina Gimbiya ta shiga ne yau?"

Ya fad'a yana mai juyawa ya kalli matansa.

"Tana ciki ai gaba d'aya yau bama ta futo waje ba."

"Gimbiya Salwa ta fad'a da sauritana mai jin yadda k'irjinta ke wani irin bugu da tsantsar k'arfi.

"Me kike nufi da bata futoba, bayan kuma gashinan babu ita acikin d'akin?"

Ya k'arasa maganar da k'arfi yana mai juyawa da matuk'ar sauri ya doshi waje, domin yaje ya shiga ciki ta hanyar baya ya dubata sosai.
Da gudu suma matansa gaba d'aya biyun harma da sauran 'Ya'yansa sukabi bayansa hankulansu atsantsar tashe.

Suna futowa wajen suka had'e da jama'ar da suka tawo tare harda Boka mai hutar kasko.
Kana gaba d'ayansu suka had'u suna masu hucewa baya.
A kuma lokacin su Gimbiya Salwa da Haiwai sukaji labarin kashe dakarun bakin k'ofa da akace Shairama tayi, wanda hakan kuma ya sanya su sake matuk'ar rud'ewa suma.

Tundaga nesa suka hangi k'ofar abud'e, hakanne ya sanya Sarki Barbaru ya k'ara saurinsa tamkar ya kifa ak'asa.
Yayinda ita kuma Gimbiya Salwa take had'awa harda d'an gudunta, gaba d'ayanta a tsantsar rud'e.

Gaba d'ayansu suka danna kansu zuwa cikin d'akin alokaci d'aya, sai dai kuma abunda suka ganine ya sanya su tsaywa cak a wurin da suke, suna masu baza idanuwa a kowace kusurwa ta d'akin, zuciyarsu na tsananta bugu.
Sabo da ganin da sukayi na babu Gimbiya babu alamunta kuma.

Kafin daga bisani kuma Mahaifiyarta ta zura aguje tana mai bankad'a k'ofar bathroom tare da danna kanta ciki.

"Tasmir! Tasmir!! Tasmir!!! Kina inane ki futo mana, 'Yata wai ina kika shiga ne."

Ta fad'a cikin wani irin k'araji, tana mai fara zagaye acikin tank'ashe-shen bathroom d'in
Kafin daga bisani kuma ta zura aguje tana mai fucewa, hawaye na b'allewa daga cikin idanuwanta ta.

"Batanan wallahi, batanan na duba banga Gimbiya ba ku taimakeni ku nemomun ita. "

Ta fad'a a wani irin firgice tana mai sakin wani irin kuka da matuk'ar k'arfi, domin kuwa haka kawai jikinta ya bata ba lafiyaba tun da taji abunda akace Shairam tayi.

Shi kuwa Sarki Barbaru a wani irin haukace ya juya b'arin da Boka mai hutar kasko, yake yana mai fad'in.

"Kanaji ko, kanji ko Boka mai hutar kasko, kana jin abunda take cewa wai bataga 'Yata ba. Na rok'eka kayi maza kai binciko mun inda ta tafi."

Sarki Barbaru ya fad'a a haukace yana mai riga Boka mai hutar kasko fucewa.

Hakan yasa shima Boka mai hutar kasko rufa masa baya suka tafi domin aje ayi bincike
Yayinda suma gaba d'aya sauran Jam'ar harma da wa'yan da basu san da abun ba da sukaji suka had'u suka tafi zuwa d'akin Boka mai hutar kasko.
Ita kuwa Gimbiya Salwa banda aikin gurshk'en kuka babu abun da takeyi, a haka har suka k'arasa bakin k'ofar d'akin.

Boka mai hutar kasko ne ya fara shiga ciki, tukun Sarki Barbaru yabi bayansa, kana su Gimbiya Salwa ma da duk sauran 'Ya'yan sa suka danna kansu ciki.
Yayinda su kuma sauran jama'ar tasu sukayi tsaye cirko-cirko abakin k'ofar, hankulansu a tsantsar tashe.

Aciki kuwa basu tsaya ba har sai da suka dangana da da wurin da kayan aikin Boka mai hutar kasko suke.

K'ullukan tsummokarnsa da layoyinsa ya d'auko.
Kana yasa kaskon huta a gaba, su kuma su Sarki Barbaru suka
tsaye daga gefe suna kallonsa.

Cikin sauri ya fara kwance k'ullikan tsummokaran, kana ya mik'e tsaye bayan ya dunk'ule wasu layoyin acikin tafin hannunsa, tukun ya fara zuba abubuwan acikin hutar dake ci yana mai yin wasu irin surutai tare da rumtse ido.

Ya d'auki dan tsayin lokaci yana yi, kafun daga bisani kuma ya tsaya yana mai bud'e idanuwan nasa.
Koriya shar yaga hutar ta dawo daga jar da take.
Hakan yasa sa sake matsawa jikin kaskon, yana mai kai idanuwansa cikin tsakiyar hutar.

Da sauri, kana kuma cikin tsantsar firgici, rud'u, had'i da tashin hankali ya d'ago idanuwansa, yana mai watsasu akan fuskar Sarki Barbaru, jikinsa na kyarma!


K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI.*

K'arfe shad'aya da rabi na safe dai-dai motarsu ta tsaya acikin tashar da take a tsakiyar cikin garin Wasai.

Cikin farinciki mutanen cikin motar suka fara furfutowa.
Yayinda Gimbiya Tasmir da Bir kuma sukayi shiru suna masu kallon junansu.
Hakanan kawai sukaji gaba d'aya jikinsu yayi sanyi, sabo da rashin ta inda zasu fara yanzu idan sun sauka da basu sani ba.

Ganin da Bir yayi gaba d'aya mutanen cikin motar sun fuce, sai sukad'ai ne kawai sukai saura, ya sanyasa yunk'urawa shima yana mai fad'in.

"Mu futa ko Gimbiyata."

'Daga masa kai kawai ta iyayi ba tare da tace komai ba, domin kuwa haka kawai takejin tamkar ta fashe da kuka, ga wani irin abu da taji ya tokare mata ak'irji.
Yayinda cikin zuciyarta kuma take cike da tinanin halin da ahalinta suke aciki yanzu.

Bir ne ya fara fucewa, tukun itama ta biyo bayansa.
Dasauri ya lumshe idanuwansa, yana mai jin zuciyarsa na wani irin harbawa da tsananin k'arfi.
Sabo da yadda iskar garin ta daki gangar jikinsa a lokacin daya futo.
Cikin sanyi jikin daya ziyarce su gaba d'aya daga shi har ita, suka fara d'aga kai suna masu kallon yadda wurin yake
Kasancewar kuma ranar yau d'in da zafinta ta bud'e, shiyasa gumi ya fara tsattsafo musu ajiki, domin kuwa ko ba rana ma dolene suji zafin garin, duba da irin yanayin wurin da suka baro.

"Yawwa Malam ga jakun-kunan ku ko."
Drivern motarsu ya fad'a yana mai nuna musu su ak'asa.

Hakan yasa Bir yin wurin jakun-kunan asanyaye yana mai sanya hannu ya d'aukosu.

Ita kuwa Gimbuya Tasmir da sauri ta matso jikinsa, tana mai d'an nanik'e masa, sabo da yadda taga idanuwan kusan duka jama'ar dake wurin ya dawo kansu.
Shiyasa gaba d'aya taji tsoronsu ya lullub'eta, domin kuwa sai take zaton kamar sun take wata dokarce shiyasa har ake kallonsu haka.

Su kuwa mutanen dake kallonsu, ba komai bane ya janyo hankulansu zuwa garesu sai tsananin kyawun da

Please Login or Register in order to submit comment