Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi d'in baya yinka.
Bai tab'a sanin haka 'yammatan da suke hauka akansa sukeji ba sai yanzu da abun yazo kansa.
Bai tab'a sanin haka duniya take yiwa wa'yan da suke so ba'a sonsu k'unci ba sai a yanzu.

Ko a mafarki koda wasa bai tab'a tinanin zai tab'a kamuwa da son wata hallita ba a duniya, ba tab'a tinanin irin wanan yanayin zai riskesa ba.

A kullum da mafarkinta yake fara baccinsa, da kuma shi yake k'ark'are sa kala-kala.
Kai a yanzu har takai ta kawo ma ko rumtse idanuwansa idan yayi ita yake gani.
Yayinda har kawo yau kuma kalaman ta gaba d'aya suka kasa barin cikin k'wak'walwarsa, domin kuwa kullum jin su yake tamkar a lokacin take kan furta masa su ma.
Wanda hakan kuma shike k'ara tayar masa da hankali, saboda shi so yake ya mance da ita har a bada a cikin rayuwarsa, saboda ya riga da ya k'udurtawa ransa cewar ko da zai mutu akan santa sai dai ya mutu, amma har abada bazai k'ara komawa garinsu bama gaba d'aya.

Babu juyin duniyar da Al'amin baiyi ba harma da Fulani da kuma Babban Yaya akan ya fad'a musu damuwarsa amma gaba d'aya yak'i ya.
Domin kuwa yana ganin ai abun kunya ne a garesa aji labarin cewar ya kamu da son wata 'ya mace a zuciyarsa, kuma ita bata son sa a matsayinsa na Prince Asad.

Hakan yasa Babban Yaya yaje ya samu Mai Martaba yana rok'onsa akan su rabu da Asad akan batun auren da ake son ayi masa, gudun kar ta sanadin hakan ya kamu da wani ciwon, domin kuwa gaba d'aya a tinaninsu hakanne ya sanya sa cikin damuwar da suka gansa ta kwana biyu aciki, idan aka cire Al'amin kawai da yasan gaskiya.

Amma sai Mai Martaba ya nuna masa cewar babu wannan batun, zuwa yanzu shima yaci ace ya fara magana zance d'aya, wato idan ya furta ya zauna a yadda yace a matsayinsu na manyan mutane.

Hakanne yasa mai martaba ya tako da kansa har zuwa d'akin Asad a daren jiya ya lallashesa tare da kwantar masa da hankali, da fad'a masa cewar hakan duk ba wani abu bane mai wahala, kawai k'udirtawa zaiyi a ransa cewa zai iya yin hakan, to tini zai ga komai ya huce.
Da tom kawai Yarima Asad ya bisa, saboda baya son kowa ya fahimci halin da yake ciki na zahiri, ya fuson suje a tinanin hakanne.

A b'angaren Billy kuwa, sosai ta haukace da kiran wayar Yarima Asad da kuma yini a cikin Palace d'insa, amma har kawo yau bai d'aga wayar ba, kana kuma bai je ba.
Kai a k'arshe ma sai jin wayar tasa tayi gaba d'aya a kashe, wanda kuma har kawo yanzu ma da take kan hanyarta ta zuwa Palace ta kira wayar tasa, amma still akace mata swicth off.

Sosai kuwa damuwa tayi mata yawa.
Yayinda Al'amin kuma yake ta aikin kwantar mata da hankali yana rarrashinta, saboda yadda ta addabesa da kira shima.
Tukun a jiya da daddare domin ta barsa ya sarara yayi mata k'arya da cewar takwantar da hankalinta, yau zai sanya Asad yazo Palace, inyaso sai suyi maganar baki da baki ma anan.
To hakan yasa ta hak'ura da kiran Al'amin d'in tun jiya, kana kuma yau ta shiryo da wuri ta tawo Palace d'in.

A b'angaren Al'amin kuwa sosai damuwa shima tayi masa yawa, gaba d'aya ya rasa sukuni, saboda ganin yada abokinsa ya koma.

A yanzu haka tafe yake a hanyarsa ta zuwa d'akin Yarima Asad d'in, domin ya lallashesa yau su futa waje suje ko palace ne, ko hakan ya rage masa damuwar da yake a cikinta.

Da sallama d'auke a bakinsa ya tura kansa zuwa cikin d'akin.
Kwance ya hango Al'amin akan doguwar kujera kansa d'age a sama, yayinda idanuwansa kuma suke a lumshe tamkar mai yin bacci, amma sai dai azahirin gaskiya kuma ba baccin yake ba, kawai ya rufe sune domin yaga fuskar da ta zamto masa masifa a rayuwarsa yanzu, ko ya d'an samu sukunin kewarta da yake ji tattare da shi.

Can k'asan mak'oshi ya amsawa Al'amin sallamar da yayo masa.
Hakanne yasa Al'amin kwata-kwata baiji amsawar da yayin ba.
Sai dai kuma ko kad'an bai damu da rashin amsawar tasa ba, saboda babu wani sabon abu acikin hallayar Asad da bai saba da shi ba.
Kana kuma tun da ya shigo ya fahimci idanuwansa biyu, saboda hango fatar idanuwan nasa da yayi tana motsawa.

Sanye yake da wando three quarter a jikinsa tare da shirt tamkar ko da yaushe.
Tun da yayi wanka bayan ya d'an samu yasha ruwan copy ya kwanta akan kujerar, har yanzu bai iya tashi daga kanta ba kuma.

K'arasawa Al'amin yayi zuwa kan kujerar da take facing d'in wacce Asad d'in yake kwance akan ta ya zauna shima.
Kana ya bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Bai kamata ace ka zauna kana shirin durk'usar da rayuwarka ba, a matsayinka na yaro matashi, akan d'an wani abu da bai kai ya kawo ba.
Ka sani Asad na dad'e da sanin abun da ke damunka, duk da dai har yau kai ka gaza bud'e baki ka fad'a mun.
Dan haka ni shawarar da zan baka a matsayina na d'an uwanka kuma amininka da baka da kamar shi a yanzu ita ce.
Ka cire girman kai ka yadda duk wasu burikanka na baya, kana ka manta da ko kai waye da irin furucin da kakeyi ake kuma yi akan ka.
Kamanta ka fuskanci abun da zuciyarka ke so da gasken-gaske tun kafin kazo kana nadama daga baya.
Wato ina nufin ka aje girman kan da yake d'awainiya da kai, ka fuskanci abun da zuciyarka ke so, sanan kuma kayi yak'i wurin nemansa, ma'ana ka tub'e kashiga fagen fafatawa wurin ganin ka samu muradin ranka.
Hakan kawai zakayi ka zamto real namiji gaye, amma muddin kak'i kuwa, to ina mai tabbatar maka da zakayi nadama ne wataran, domin kuwa ba zaka tab'a iya cire soyayyarta ba acikin ranka, tun da har ka kawo yau baka iya cire ta ba bayan duk hul...."

"Stop Al'amin! Stop it ya isheka hakan!!"

"Asad ya fad'a a wani irin hargitse cikin matsananciyar tsawa, yana mai mik'ewa zaune daga kwancen da yake, tare da kafe Al'amin da idanuwansa.
Wanda har hakan yayi sanadiyyar yankewar maganar da Al'amin yake yi tun kafin ya dira aya.
Ba dan komai ba kuma yayi masa hakan sai saboda jin da yayi yana masa fatan cewar bazai tab'a iya cire sonta ba a ransa, wanda hakan ya sanya yaji tamkar shi d'in mak'iyinsa ne ba masoyi ba.
Kana daga bisani kuma ya mik'e tsaye cikin sauri, yana mai juyawa ya kama hanyar bedroom d'in sa.

Da sauri shima Al'amin ya mik'e tsaye yana mai sa hannu ya cafko yatsun hannun Yarima Asad da nasan.
Wanda hakan ya sanya Yarima Asad tsayawa cak ba tare da ya iya juyowa ba.

Yayinda shi kuma Al'amin ya bud'e baki cikin sanyi, yana mai cewa.

"Kayi hak'uri d'an uwa, ka sani ban fad'i hakan ba domin na b'ata maka rai, nayi ne kawai saboda ganin da nake tamkar haka zai sa ka dawo cikin walwalarka ta baya, amma tun da har hakan ya b'ata maka rai kayi hak'uri, in sha Allah nima bazan k'ara mai maita irin wannan kalamin ba a gareka."

Da sauri Yarima Asad ya lumshe idanuwansa, yana mai jin gaba d'aya bai kyautawa Al'amin ba da abun da yayi masan, domin kuwa ko banza mai sanka ne kawai ke damuwa da halin da kake ciki, hakanne ya sanya ya juyowa b'arin da Al'amin yake cikin sanyi, yana mai fad'in.

"Shikenan kayi hak'uri kaima kaji."

Ya k'arasa maganar yana mai juyawa ya koma wurin da ya tashi.

"To ai ni dama kasan bana iya fushi da kai d'an uwa, dan haka yanzu abun da zai faru shi ne, ba zama zakayi ba zuwa nayi ka taso mu d'an futa musha iska yau, ko hakan zai rage maka rad'ad'in damuwar da kake ji a ranka.

Murmushin yak'e Yarima Asad yayi yana mai kallon Al'amin, saboda sanin da yayi na babu abun da zai ragu a yada yake jin dan ya futa, sai dai kuma baik'i ta tasan ba zai bisa, saboda dama shima tini ya gaji da zama da kwanciyar da yake ta faman yi a cikin d'aki tsawon kwana biyu kenan.

Hakanne yasa sa fad'in.

"Tom shikenan d'an uwa."

Jin hakan da Al'amin yayi ne ya sanya sa tashi yaje wurin da Asad yake ajiye key's d'in motocinsa ya d'auki d'aya.
Yayinda shi kuma Asad d'in ya mik'e tsaye bayan ya d'auki wayarsa akan center table d'in da yake a cikin d'akin.
Tukun suka futa a tare suna masu hucewa zuwa compound d'in gidan direct.

Al'amin ne ya shiga mazaunin driver, yayinda shi kuma Asad ya zauna a wurin mai zaman banza, yana mai jingina kansa da kujerar tare da lumshe idanuwansa.
Tukun Al'amin yayiwa motar key, bayan ya d'an sakar musu cool music a cikinta yana mai dosar hanyar get.

Ba su tsaya ako ina ba har sai da suka isa bakin had'ad'd'en get d'in Asadullah Palace.
Kana Al'amin ya d'an taka birki yana mai sakin horn.

Da sauri kuwa mai gadin wurin ya tawo, yana mai bud'e musu get d'in.
Kana ya danna hancin motar zuwa cikin wurin.

Tini idanuwan jama'ar da suke a cikin wurin kuwa ya dawo kansu gaba d'aya, saboda sanin wa'yan da suke a cikin motar da sukayi.
Yayinda 'yammata kuma suka fara mimmik'ewa tsaye, suna masu fara zagayawa a cikin wurin, cikin wani irin taku na d'aukar hankali.
Sai dai kuma ko kad'an wanda suke yi dan shi d'in baima san suna yi ba, saboda idanuwansa da suke a lumshe har lokacin.

Yayinda Al'amin kuma ya doshi wancan get d'in wanda ya kasance b'angaren Asad kad'ai kai tsaye.

Da sauri get man d'in wurin ya mik'e tsaye, yana mai sa hannu ya tura get d'in, kasancewar yana daga wajene dama.
Wanda hakan kuma ya sanya Billy da take zaune akan wannan kujerun idanuwanta akan get d'in tun lokacin da tazo, mik'ewa tsaye da sauri, tana mai sakin murmushi.
Kafin daga bisani kuma ta fara d'aga k'afafuwanta tana mai dosar bakin get d'in da sauri.
A kuma lokacin Al'amin ya danno hancin motar zuwa cikin wurin.

Suna k'arasawa parkin space Billy ma na k'arasowa wurin, sai dai kuma yanzu cike zuciyarta take da fargabar kalar tarbar da Yarima Asad d'in zai yi mata.

Jin da Yarima Asad yayi motar ta tsaya ne, ya sanya sa bud'e idanuwansa yana mai d'agowa daga kwancen da yake.
Kana ya mik'a hannunsa zuwa kan murfin motar, yana mai bud'esa tare da zura k'afafuwansa waje.

Yayinda Al'amin kuma har ya riga ya fuce duka.

Ita kuwa Billy tsaye take ta b'angaren da Asad yake idanuwanta k'ur akan k'ofar.
Hakan ko yasa yana gama futowa daga cikin motar idanuwansa da nata suka sark'e wuri d'aya.

Lokaci d'aya kuwa yaji wani irin b'acin rai mara misaltuwa ya tsaya masa a mak'oshi, ga wata irin mahaukaciyar tsanarta da yaji ta caki k'awon zuciyarsa.
Hak'ik'a da yasan zai zo ya same ta anan d'in, da babu abun da zai futo da shi daga cikin gida.
Ganin da yayi kallon nata tamakar yana cigaba da tafarfasa zuciyarsa ne, ya sanya sa janye idanuwansa daga kanta.
Kana ya fara d'aga k'afafuwansa yana mai rab'awa ta gefenta zai huce.
Amma sai kawai yaji an cafki yatsun hannunsa da k'arfi.
Take kuwa yaji wani irin mugun tuk'ik'in bak'in ciki ya k'ara turnuk'esa, ta yadda har bai san lokacin da ya juyo b'arin da take ba a mugun fusace, yana mai wu...........✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*09*



_NAKU NE WANNAN PAGE DIN MASU COMMENT DA SHARHI, HAK'IK'A SHARHINKU NA JIYA YAYI MATUK'AR BIRGENI, HAKAN YASA NA BAKU KYAUTAR WANNAN PAGE 'DIN KUYI YADDA KUKASO DA SHI, SANNAN KUMA A CIGABA DA GASHI WASA YANZU AKA FARASA. 😁_




Wurga mata wani irin mugun kallo.
Yayinda yake jin zuciyarsa na cigaba da turiri kamar zata babbake.
Tsanar Billy na k'ara taso masa tana lullub'e ilahirin jiki da zuciyarsa.

Lokaci d'aya yaji gaba d'aya haushin da yake ji ya dawo kanta, ta yadda har yake jin tamkar ta sanadinta ne ya shiga halin da yake a ciki yanzu.
Kafin daga bisani kuma ya funcike hannunsa da matuk'ar k'arfi, yana mai sakin wata uwar k'wafa yayi gaba.

Ganin hakan da Billy tayi ne ya sanya ta shan gaban sa da matuk'ar sauri, jikinta na wata irin karkarwa.
Gaba d'aya hankalinta idan yayi dubu sai da duka ya tashi.
Matsanancin tsoro da fargabar abun da yake nufi da yadda ya mata suka yiwa zuciyarta k'awanya.

Da matuk'ar sauri ta had'e tafukan hannayenta wuri d'aya, bayan tatsaya a gabansa tana mai jefa k'wayoyin idanuwanta a cikin nasa.
Kana ta fara murza tafukan hannayenta tana mai girgiza masa kai, kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu tsananin gudu suka b'alle daga cikin idanuwanta.

Ganin da tayi ya janye idanuwansa daga cikin nata yana shirin rab'awa ta gefen ta ya huce ne, ya sanya ta sake saurin matsawa gaban sa.
Kana ta bud'e baki cikin kuka, tana mai fad'in.

"Kar kayi mun haka Prince!
Sanin kanka ne ina sonka ina mugun k'aunarka, dan girman Allah na rok'ek'a da sunayen Allah kar kanemi ka kassara rayuwata.
Domin ko idan ka k'ini mutuwa zanyi Prince, mutuwa zanyi, mutuwa zanyi wallahi."

Ta k'arasa maganar cikin wani irin matsanancin kuka bilhak'k'i jikinta na karkarwa.

Da k'arfi Yarima Asad ya rumtse idanuwansa, yana mai danna lower lips d'in sa cikin bakinsa ya cijesa.
Yayinda Al'amin kuma ya koma jikin mota ya jin gina da ita, yana mai jin tausayin Billy na lullub'e sa lokaci guda.

Shi kuwa Yarima Asad cikin wani irin yanayi ya bud'e idanuwansa da suka sake rikid'ewa da ja akan fuskar Billy.
Kana ya fesar da wata irin zazzafar iska.
Tukun ya d'aga lab'b'an sa cikin kaushi, yana mai cewa.

"Kin san da bakya son rayuwarki ta kassara amma me yasa ni kuma kike son ki kassara tawa rayuwar?
Sanin kanki ne ni da bakina ban tab'a furta kalmar so a gareki ba, amma me yasa kikayi mun abun da kikayi mun?
Shin kinsan irin matsalar da hakan ya jefe zuciyata kuwa?"

Ya wasto mata tambayar cikin kakkausar muryarsa, yana mai kafeta da jajayen idanuwansa.
Yayinda ita kuma har lokacin take faman girgiza masa kai, hawaye na cigaba da tsiyaya daga cikin idanuwanta.
Kafin daga bisani kuma ta sake bud'e baki cikin kuka, tana mai fad'in.

"Ka sani nayi duk abun da nayi ne acikin mayen giyar sonka da take aikin bugar da k'wak'walwata a kowane lokaci.
Ka sani nayi hakanne saboda tsananin san da nake maka.
Nayi hakanne ba da nufin in cutar da kai ba.
Nayi ne saboda in samu damar mallakarka har abada, nayi ba dan nasan ranka zai b'aci ba irin haka.
Amma wallahi tallahi ina k'aunar ka Prince, idan kace zaka barni zuciyata bugawa zatay..."

"Ni kuma bana sanki Billy.
Bana sanki! Bana sanki!! Bana sanki!!!
Kuma babu ranar da zata zo wacce zan tashi da sanki a zuciyata.
Dan haka ina mai shawartarki akan ki gaggauta zuwa ki warware abun da kika had'a.
Idan kuma har kink'i ji, to ki sani ko da anyi abun ba zaki tab'a ganin d'igon murmushi akan fuskar Asad ba.
Ba zaki tab'a kasancewa a gefena ba.
Ba zan tab'a rab'ar jikin ki ba har abadan-abada, saboda na tsaneki a halin yanzu, ta yadda har nake jin ina ma ace ina da damar mai da baya gaba, da babu abun da zai sa nayi a acceptin d'in ki cikin rayuwata!"

Ya k'arasa maganar yana mai rab'awa ta gefenta ya huce cikin tsantsar zafin rai, yana mai dosar building d'in nan na cikin wurin.

Da matuk'ar sauri Billy ta durk'ushe a k'asa, tana mai d'ora hannuwanta biyu a tsakiyarka tare da fashewa da wani irin gigitaccen kuka, idanuwanta akan bayan Yarima Asad da yake tafiya da wani irin sauri tamkar zai tashi sama.

"Wallahi idan ka barni mutuwa zanyi Asad, dan girman iyayenka na rok'eka kayi hak'uri."

Muryar Billy ta daki dodon kunnuwan Asad a lokacin da ya d'ora yatsun hannunsa akan handle d'in k'ofar gidan.

Cak kuwa ya tsaya a wurin da yake ba tare da ya juyo ba yana mai rumtse idanuwansa.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e su yana mai fara juyo da kansa a hankali zuwa gareta, har ya sauke k'wayoyin idanuwansa a cikin nata.
Kana ya bud'e baki yana mai cewa.

"Ok, so kike in raya taki rayuwar ni kuma in kashe tawa da kaina ko?

Ya fad'a mata haka cikin sigar tambaya idanuwansa a cikin nata.
Kana kuma ba tare da ya tsaya jin amsar da zata basa ba ya d'ora da girgiza kansa, yana mai fad'in.

"Lalalaaa! That is impossible!"

Ya k'arasa maganar yana mai juyawa ya bud'e k'ofar tare da danna kansa cikin falon.
Yayinda ita kuma Billy ta sake b'are baki ta yadda har mai gadi yake jiyo ta tana mai fad'in.

"Asad! Asad!! Asad Kar kamun haka zuciyata zata fa..sh..e!"

Ta k'arasa maganar da k'yar, kuka na k'ara kufce mata.
Kafin daga bisani kuma ta mik'e tsaye tana mai nufar hanyar gidan gadan-gadan itama.

Ganin hakan da Al'amin yayine ya sanya sa yin sauri ya shiga gabanta.
Tukun ya fara girgiza mata kai yana mai fad'in.

"A'a Billy kiyi hak'uri kar kice zaki bishi ciki, saboda kin gani dai yanzu ransa a b'ace yake, dan haka idan kika shiga komai ma yana iyayi miki.
So kiyi hak'uri ki shiga motarki yanzu ki tafi gida, ina mai tabbatar miki da zai huce daga baya.
Yanzu duk yana cikin jin zafin abunne shiyasa har ya fad'a miki hakan."

Shiru Billy tayi tana mai kallon Al'amin, kana daga bisani kuma ta lumshe jik'ak'k'un idanuwanta tana mai jin-jina masa kai, alamun gamsuwa da batun nasa kenan.
Sannan ta juya cikin sanyi ba tare da tace komai ba, sai hawayen da suke cigaba da tsiyaya daga cikin idanuwanta, tana mai nufar wurin da mayyar motar ta take.

Shi kuwa Al'amin cikin sanyin jiki shima yabi bayan Yarima Asad zuwa cikin building d'in nasa.

Sosai Billy take jin ba dad'i a cikin ranta.
Hakane ya sanya gaba d'aya take tuk'in motar a hankali tamkar bazata tafi ba.

"To wai akan me ma zaki damu kanki har ki nemi illata rayuwarki, akan abun da kika riga kika san kin mallakesa?
Shin ko kuwa kin manta maganar ki har ta je gaban iyayensa, dan haka kawai ki rabu da shi ki kwantar da hankalinki, ko da bai so ki ba a yanzu dole ne bayan auren ya so ki tun da cikin gida d'aya zaku zauna, kai a k'arshe ma har ma ki juyasa, domin kuwa kin mallaki duk wani abu da ake buk'ata a jikin mace."

Zuciyarta ta raya mata hakan.
Aiko take a wurin ta shiga jinjina kanta, wani irin murmushin farinciki na sub'uce mata.
Kana ta bud'e baki tana mai cewa.

"Tabbas kuwa hakan da nayi shine dai-dai, dan haka wallahi sai ka zama nawa Yarima Asad.
Duk kayi abun da zakayi ka gama iyakar na yanzu ne kafun ka shigo hannuna nima."

Ta k'arasa maganar da d'an cije leb'enta na k'asa, tana mai hasasho lokacin a zuciyarta.
Tukun daga bisani ta take motarta tana mai dosar hanyar gidansu cikin tsananin gudu.

*BAYAN SATI 'DAYA*

Sosai rayuwa tayiwa Yarima Asad zafi.
Zuwa yanzu tini ya tabbatarwa kansa da cewar bazai tab'a iya cire soyayyarta ba a cikin zuciyarsa duk fad'e ne kawai yake yi.
Ta yadda har yake jin ba zai iya rayuwa adoron duniya ba muddin a kace babu ita a cikin rayuwarsa.

Zuwa yanzu shi kansa ba zai tab'a iya misalta adadin yawan son da yake yi mata ba, ko da kuwa za'a d'ora bindiga akansa ace idan bai fad'a ba za'a kashe sa.

Sosai duk wani makusancinsa ya shiga damuwa da ganin halin da ya koma, sai dai kuma har kawo yau yak'i ya yadda ya furtawa kowa abun da ke damunsa.
Domin ko duk a tinaninsa da zai iya yakice soyayyar ta a zuciyarsa, sai kuma a yanzu ya tabbatar da hakan ba abu bane mai yuwuwa.

A daddafe ya kawo har yau ba tare da ya sake sanyata a cikin idanuwansa ba a zahiri,
Amma kuma a duk daren duniya da mafarkinta yake kwana a cikin ransa.
Hakan yasa tun a daren jiya ya k'udirtawa ransa cewar zai koma masarautar fuld'e a yau ya ganta, ko Allah zai sa yaji sauk'in rad'ad'i da k'unar da yake ji a ransa.

Bai tab'a sanin haka so yake da zafi ba sai yanzu.
Yayinda itama Billy har yau bata fasa kiran wayarsa ba, tamkar yadda shima bai d'aga nata kiran ba.

Yayi nadamar yiwa Babban Yaya biyayya a lokacin da ya takura masa sai ya bisa masarautar fuld'e siyo shanu sama da sau dubu a zuciyarsa.
Ji yake ina ma ace baya na dawowa, tabbas ko da babu abun da zai sanyasa ya yadda ya bisa garin.
Sai dai ko kashe sa zaiyi idan bai je ba d'in ya kashe sa.

Shi kansa tausayin kansa yake ji a halin yanzu, domin ko bai tab'a tinanin shima babu zuciya a k'irjinsa ba kamar yadda yasha nanatawa 'yammatan da suke nuna suna sonsa wannan kalmar ba sai yanzu.
Hak'ik'a shima ya fahimci ba shi da wannan zuciyar ashe, domin kuwa ayadda Haddiyal ta hulak'antasa bai tab'a tinanin zai sake marmarin bin ko hanyar garinsu ba, sai gashi kuma shiryawa ma yake yi da zummar zai tafi can d'in cikin gidan su wajenta ma kuwa.

Tsaye yake a gaban dressing mirrow jikin sa a matuk'ar sanyaye, yana mai shafa mai akan fatarsa.

Sosai ya d'an fad'a a kwana taran da ya d'auka cikin tinani da damuwa.
A hankali ya mik'a hannunsa zuwa kan cumb d'in sa ya d'aukosa, bayan ya tsiyayawa lallausar bak'ar sumar kan sa mai ya fara taje ta.
So yake yau yayi kwalliyar da ya dad'e baiyi irinta ba, ko Allah zai sa idan ta gansa a haka itama taji wani abu dangane da abun da yake ji akanta.

Sai da har ya tabbatar da kannasa ya gyaru yayi bala'in kyau yana futar da shek'i, tukun ya d'auki body spray mai tsananin k'amshi, yana mai fara feshe jikinsa lungu da sak'o da shi.
Kana ya ajiyesa a gefe, yana mai kai hannunsa zuwa kan hair performe d'in sa ya d'auko sa ya feshe sumar kan nasa da shi shima.
Kana ya juya yana mai barin gaban mirrow'n ya doshi gaban wardrobe d'in sa daga shi sai d'an guntun wando a jikin sa.

Tsaye yayi a gaban sababbin kayansa yana mai binsu da idanuwa d'aya bayan d'aya.
Ya jima yana kallon su kafin idanuwansa su sauka akan wata mayyar suite da ya siyota a dubai mai tsananin kyau da tsada.
Domin kuwa adadin kud'in ta yakai kusan dubu d'ari a kud'in su na K'asar Hausa.

Hakanan kawai yaji ya dace ya sata, saboda sanin da yayi na shigar tana masa bala'in kyau, duk da kasancewar shi d'in ba ma'abocin sanyata bane ba, saboda nauyin da take da d'an shi.
Shi kuma a rayuwarsa gaba d'aya ya tsani sanya kaya masu nauyi, shi yasa ma yak'i jinin tufafinmu na hausawa.
Itama d'in zai sata ne yau d'in saboda jin da yayi wancan karan ta kushe shigar da yaje da ita, har da danganta ta da ta 'yan iska.
Wannan dalilinne yasa zai sanya masu arzik'i yau, gudun kar ta sake dizgasa.

Brow'n color ce amma irin tirarrar nan.
Sababbin iner wear's ya fara sanyawa a jikinsa.
Kana ya ware dogon wandon suite d'in yana mai zura kafar sa d'aya a ciki.
Tukun ya sanya d'ayar ma.
Kana ya d'auki 'yar farar shirt d'in ciki itama ya wareta yana mai sanyata a jikinsa bayan ya bud'e mab'allanta.

Stocking d'in rigar yayi a cikin wandon.
Tukun yabi saman wandon da wata had'ad'd'iyar brown belt yana mai d'aure k'ugunsa da ita.
Kana ya b'alle mab'allayan rigar.
Sannan ya d'auki turaren da ya zaro a cikin wata 'yar drawer da take a kusa da shi, ya feshe gaba d'aya jikinsa da shi.

Tukun ya d'aura agogon fatarsa shima brown color akan hannunsa.
Sannan ya d'auki necktiead ya sanya, yana mai gyara zamansa akan wuyansa.
Kana ya d'auko uwar gayyar wadda take masa nauyi a jiki, duk da dai ba wani nauyi ne da ita ba, dan dai kawai ya saba da sa 'yan k'ananan kaya ne, shi ya sa yake jin haka, yana mai d'orata asaman itama, bayan ya sanya brown falmaran d'in a farko.

Bai b'alle mab'allayanta ba, wanda hakan ya sanya ake ganin falmaran d'in cikin tare da farar shirt d'in.

Sosai yayi wani irin mugun kyau mara misaltuwa.

A hankali ya tafi zuwa wurin da takalmansa suke.
Kana ya d'auko wani sabon cover shoe brown color mai tsananin tsinin gaba, ya sanya k'afafuwansa da suke cikin brown d'in safa suma.

Wayarsa

Please Login or Register in order to submit comment