Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hudo k'irjinsu su futo waje.
Cigaba da kallon junansu sukayi suna masu jin tsanar junansu na lullub'esu.
Kafin daga bisani kuma Gimbiya Haddiyal ta janye idanuwanta daga cikin na Gimbiya Tasmir, tana mai fara d'aga k'afafuwanta ta doshi wurin da Bir yake zaune.

Tunda ta turo k'ofar get d'in daya sauke idanuwansa akan fuskarta yaji ya kasa janyesu har ta k'araso wurin.

Tsaye tayi a gabansa tana mai lumshe idanuwanta.
Kana daga bisani ta bud'e su a cikin tsakiyar nasa.
Girgiza kanta tayi tana mai jifansa da wani irin kallon da yake nuni da zallar k'aunar da take masa, kafin daga bisani kuma wasu hawaye masu tsananin gudu suka b'alle daga cikin idanuwanta.
Tukun ta bud'e baki cikin muryarta da take cike da rauni, tana mai fad'in.

"Na dawo garekane domin na nemi alfarma, ina son ka taimakeni ka tausayawa zuciyar data dad'e tana tsumayin jiranka, tare da dakon soyayyarka karta rasaka."

Ta k'arasa maganar cikin kuka, wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da Gimbiya Tasmir ta k'araso wurin, tana mai tsaye daga gefen wurin da Haddiyal take tare da zuba idanuwanta a cikin na Bir da kwata-kwata ma shi bai lura da zuwan nata ba.

Da sauri Bir ya lumshe idanuwansa, yana mai d'an tsotsar leb'ensa na k'asa.
Yayinda yake jin sautin muryarta na dukan har zuciyarsa, ta yadda har hakan yayi sanadin tsanantar gudunta.
Tukun daga bisani ya sake bud'e su cikin wani irin yanayi, yana mai sake jefa su a cikin na Haddiyal.

Ita kuwa Haddiyal ba tare data damu da ganin Gimbiya Tasmir da tayi a gefenta ba ta d'ago hannunta tana mai mik'awa Bir takardar da take rik'e a cikinsa.
Kana ta bud'e baki idanunta na zubar k'walla, tana mai d'orawa da fad'in.

"Al'adunmu na Fulani na da bambaci da sauran al'adu, d'aya kuwa daga cikinsu shine, babu mai tab'a mallakar yarinya da aure face ya jure bugun bulalun shad'i. To ajiya nima iyayena suka tsaida ranar da masu neman aurena zasu buga tasu gasar, wanda hakan kuma shine yayi silar dawowata a yau, saboda mahaifina ya sanar dani cewar na shaidamaka kazo a buga dakai, hakan yasa nazo domin na shaidamaka da abun da ake ciki."

Ta k'arasa maganar hawaye na cigaba da zuba a cikin idanuwanta, yayinda Gimbiya Tasmir kuma jikinta ya d'auki wata irin kyarma, sai dai kuma har yanzu bata iya furta komai ba sai aikin kallon Bir kawai da takeyi.
Tukun ita kuma Gimbiya Haddiyal ta d'ora da fad'in.

"Ga wannan takardar ka karb'a, kwatancen gidanmu ne a ciki, zakuma ayi gasarne nan da kwana shida masu zuwa, na rok'eka karkace bazaka karb'a ba, ka tausayawa zuciyar data haukace akan sonka ka karb'a, idan kuma harkak'i ni, ina mai baka tabbacin mutuwa zanyi Gid'ad'o am, saboda bugun zuciyata zai tsayane."

Ta k'arasa maganar cikin wani irin kuka abun gwanin ban tausayi.
Shi kuwa Bir sosai yaji jikinsa ya sake mugun sanyi, wani irin abu yake ji yana fuzgarsa akan Yarinyar, yayinda zubar hawayenta da yake gani kuma yake k'ona zuciyarsa.

Ba tare da Bir ya janye idanuwansa daga cikin nata ba ya mik'a mata lallausan tafin hannunsa, yana mai lumshe idanuwansa a lokacin, tare da fesar da iska, tukun daga bisani ya sake bud'e su a cikin tsakiyar nata.
Wanda hakan da Gimbiya Tasmir taganine kuma ya sanyata taji tamkar zata kife a k'asa, saboda yadda k'afafuwanta suke rawa.
Kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu tsananin gudu suka b'alle daga cikin idanuwanta, domin kuwa a yanzu ta tabbatar da Jarumi ya tashi daga nata ya koma na wannan bafullatanar, saboda ita kanta ta hango zallar azababbiyar soyayyar bafullatanar a cikin idanuwansa a tsayuwar da tayi tana kallonsa yanzu, sai dai kuma bata tabbatar da zargin nata ba har sai da taga mik'o hannunsa da yayi.
Tini taji nadamar biyosa da tayi ta baro kowa nata gaba d'aya ta lullubeta, lokaci d'aya taji zuciyarta tayi matuk'ar rauni.

Ganin da tayi Gimbiya Haddiyal ta d'ora masa takardar a cikin tafin hannunsa shi kuma ya rumtseta yana mai d'ora tafin hannun nasa akan cinyarsa ne, ya sanyata fara d'aga k'afafuwanta da suke rawa, tana mai matsawa kusa da shi ba tare data na ganin ko cikakken gabanta ba.

Ba zato ba tsammani Bir yaji saukar muryarta da take tafe da shasshekar kuka, tana mai fad'in.

"Ina son katuna alk'awarin da kayiwa Iya, ka kuma tina alk'awarin daka d'aukar mun kafin muzo nan. Ashe dama zaka iya juya mun baya Jarumi, ashe dama zaka guje ni tun kafin tafiya tayi nisa, katuna irin sadaukarwar da nayi dominka, ka tuna yadda na bar komai nawa tare da kowa nawa na biyoka, hak'ik'a idan ka barni zuciyata bugawa zatayi jarumi."

Ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka mai sosa zuciya da ruhi, tare da ban tausayi.

Shi kuwa Bir da yaji sautin muryarta a sama a wani irin matuk'ar firgice ya d'ago kansa yana mai watsa idanuwansa a cikin nata.
Lokaci d'aya shima jikinsa ya d'auki kyarma da karkarwa, kana kuma hankalinsa yayi bala'in tashi, saboda furucin da yaji tanayi tare da hawayen da yaga suna zuba daga cikin idanuwanta, sai dai kuma bai san dalilin dayasa yaji ya kasa yadda takardar da take rumtse a cikin tafin hannunsa ba, asalima ji yake ba zai iya yaddatan ba.

Ganin yadda hankalinsa ya tashi da Gimbiya Haddiy tayi ne, ya sanya jikinta sake tsananin d'aukar kyarma itama, lokaci guda kuma ruwan hawayenta suka sake tsinkewa da bala'in gudu.
Kana daga bisani ta bud'e baki cikin tsananin kuka tana mai fad'in.

"Na fara sonka tun kafin nasan meye so, na taso da burin ganinka tare da muradin jin sautin muryarka, a kullum daren duniya da kai nake kwana a cikin baccina, naci wahala iyakar wahala akan soyayyarka, nak'i kula kowane irin namaji saboda ina ganin tamkar idan nai hakan naci amanarka ne. Gaba d'aya ahalin gidan mu tundaga kan dangina har zuwa Hadimai duk sun san da labarinka, hak'ik'a idan ka k'ini zuciyata zata buga Gid'ad'o am, kasoni tamkar yadda nake sonka, saboda ina tsananin buk'atarka a cikin..."

Da sauri Gimbiya Tasmir ta katse mata tata maganar ta silar d'orawa daga inda ta tsaya da tayi.
Cikin matsanancin kukan tausayin kanta tana mai kallon fuskar Bir, ta d'ora da fad'in.

"Ka sani nafi Haddiyal buk'atarka a cikin rayuwa, domin kuwa ita tana da Iyaye, tana da Yayye, tana da K'anne, kana kuma ahalinta na tare da ita, amma ni kuma fa, bani da kowa bani da komai sai kai, kai kad'aine gatana, bansan kowa ba bayan kai a cikin K'asar nan. Na sadaukar da nawa gatan, Iyayena, matsayina tare da komai nawa dominka, amma ita Haddiyal fa, tana da duk abubuwan dana lissafo wa'yan da ni bani dasu, bata rasa komai ba ta silar sonka. Wallahi idan ka bita kabarni zuciyata zata buga Jarumi, idan kuma har nacigaba da rayuwa adoran duniya to kasani zan k'are rayuwata a cikin nadama tare da danasanin abunda na aikata akanka."

"A'a Gid'ad'o am, kar kayyada da duk abun da ta fad'a, domin kuwa ko nima da nake da kowa muddin babu kai a cikin rayuwata tamkar bani da kowa zan koma, kuma kasani na fara sonka tun kafin ta soka, wallahi tallahi idan har kak'ini mutuwa zanyi Gid'ad'o am, saboda duniya da jama'ar cikinta zasuyi mini dariya."

Ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka mai matuk'ar sosa zuciya da ban tausayi.

Shi kuwa Bir da k'arfi ya rumtse idanuwansa, jikinsa na wata irin kyarma. Sosai yake jin kukansu na matuk'ar tab'a masa zuciya.
Lokaci d'aya yaji kansa yayi wata irin bala'in sarawa. So yake ya gane wacce tafi zamtowa abin tausayi a cikinsu amma gaba d'aya yaji ya kasa bambancewa.

Jin da yayi sautin kukansu na k'ara tsananta ne, ya sanyasa bud'e idanuwansa yana mai fad'in.

"Na rok'eku gaba d'ayanku ku tafi ku bani wuri, muddin baso kuke ni tawa zuciyar ta buga ba kafun taku ta buga."

Kallonsa dukansu su biyun sukayi, kafin daga bisani kuma Gimbiya Haddiyal ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Kasani har abada kana cikin zuciyar Haddiyal, dan haka zan tafi amma ina tsumayen zuwanka nan da kwanaki shida masu zuwa, wato ranar talata."
Ta k'arasa maganar tana mai juyawa ta tafi da sauri.

Itama Gimbiya Tasmir aguje ta doshi cikin lambun gidan, tana mai sakin wani irin kuka mai matuk'ar sosa zuciya da rai, tana kuka wanda ya kasance na tausayin kanta, domin kuwa ta gama aminta da Bir ya kamu da son Haddiyal, wanda ita kuna bazata tab'a jurar hakan ba.

"Shin me yasa na aikata haka? Me yasa na zab'i namiji akan iyayen da suka kawoni duniya, suka kula dani suka bani farincikinsu da rai da zuciyarsu, shin a wane hali kike ciki yanzu Ammina."

Tayi furucin da k'arfi, kana kuma cikin tsananin kuka tana mai zama akan kujera.


A b'angaren Yarima Asad kuwa tsaye yake a cikin falonsa yana ta kai kawo, hannunsa rik'e da wayarsa da yake kallon screen d'inta lokaci bayan lokaci.
Kallo d'aya zaka yi masa ka fahimci irin tashin hankali tare da matsanancin b'acin ran da yake ciki, wanda hakan kuma ya farune ta silar kiran wayarsa da yaran daya sanya suyi masa gadin Haddiyal da sukayi, suka shaida masa cewar tazo wurin gayen yau, wanda kuma sun san hakanne ta sanadin biyo bayansu da sukayi a mota.
Hakanne yasa suna sanar masa ya mik'e tsaye cikin matsanancin b'acin rai tare da tashin hankali, yana mai jiran kiransu su shaida masa da tafiyarta domin yaje wurinsa.

Su kuwa da suke acan d'in suna ganin tashin motarsu suka kira suka sanar masa.
Hakanne ya sanyasa futowa cikin sauri tare da fushi yana mai tunkarar compound d'in su.
Da 'yar sassarfarsa ya k'arasa bakin motarsa yana mai bud'eta ya shiga, tukun yayi mata key yana mai juyata a cikin wurin.
Kana ya taketa da mahaukacin gudu yana mai fucewa daga cikin part d'insu.

Da matuk'ar sauri Alamin da yake shigowa ya kauce masa, domin kuwa kad'an ya hana ya bigesa ma.
Amma kwafa-kwata ko kad'an bai lura da hakan ba.
Yayinda Al'amin kuma ya bisa da ido cikin tsantsar firgici da tashin hankali, kana kuma da tinanin wurin da zai tafi a hakan.

Cikin mintinan da basu zarce ashirin ba duka ya isa k'ofar gidansu Sheikh Ahmad ta kwatancen da yaransa sukayi masa.

Bud'e murfin motar yayi a wani irin zafafe yana mai b'amosa.
Kana ya fara dosar get d'in gidan gadan-gadan.

Da k'arfi ya hankad'a get d'in yana mai danna kansa ciki ba tare daya tsaya wani neman izini ba.
Wanda hakan kuma ya sanya Bir da yake lumshe da idanuwansa ya bud'e su da sauri saboda k'arar da yaji.

Take kuwa idanuwansu suka sark'e cikin na juna, wanda hakan kuma yayi dai-dai da harbawar zuciyar Yarima Asad da azabar k'arfi.

Shi kuwa mai gadi da sauri yayo kansa yana mai fad'in.

"Lafiya dai Malam?"

Mugun kallon da Yarima Asad ya watsa masa da jajayen idanuwansa ne ya sanyasa ja baya da matuk'ar sauri.
Tukun shi kuma ya cigaba da tunkarar wurun da Bir yake har lokacin suna kallon cikin idanuwan juna.

Zama yayi akan kujerar da take facin d'in wacce Bir yake zaune akai, yana mai cigaba da kallonsa.
Shi kuwa Bir ganin hakan da yayine ya sanyasa lumshe idanuwansa, yana mai nuna tamkar bai san da zamansa a wurin ba.

Ba k'aramun firgita Yarima Asad yayi ba da kyawun Bir d'in.
Hakan yasa ya cigaba da kallonsa tun daga sama har k'asa, yana mai so ya gane ta wurin da yafi gayen kyau, amma kwata-kwata ya kasa gano hakan, a taik'ace dai gaba d'ayama ya kasa bambance tsakanin shi da Bir wane yafi kyau.

Hakan yasa ya d'ago kansa yana mai bin gidan nasu da wani irin matsiyacin kallo tamkar yaga kashi, tukun daga bisani ya k'ara sauke ganinsa akan kayan jikin Bir d'in.
Kana ya bud'e baki cikin muryarsa mai cike da b'acin rai a cikinta, yana mai fad'in.

"Kai dama kasan a wannan d'an akurkin gidan wanda ko wurin ajiyar karnikana ya fisa daraja kake rayuwa, shine kuma har kake tinanin zaka iya takara dani?"

Da sauri Bir ya sake lumshe idanuwansa, saboda jin abunda ya futo daga bakinsa, kana kuma lokaci d'aya tinaninsa ya basa cewar saurayin Haddiyal ne tunda dama ta shaida masa cewar bata kula kowa ta silarsa.

Shi kuwa Yarima Asad cikin tsananin bak'inci da takaicin ganin da yayi Bir yak'i kulasa, ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kasani nafi k'afinka har abada, dan haka ina mai shawartarka akan duk ranar da kuka sake had'uwa da ita ka shaida mata kalmar baka sonta, ni kuma na maka alk'awarin baka mak'udan kud'i wa'yanda zasu sanyaka jin dad'in rayuwa, tun daga kan 100 milion har zuwa 1 billion dolars. Idan kuma harkak'i yin abun da na saka, to kasani zan b'atar da kai gaba d'aya daga duniyar ne, zansa abi mun ta samanka, ta yadda hatta da babinka za'a manta da shi, kana kuma na sanya duk ahalinka a cikin tashin hankali, domin ko ramin kura ba wurin wasan makawo bane. Haddiyal kuma tawace ni kad'ai har abada, wannan gargad'ine na maka, muddin kuma kayi ganganci dashi to tabbas zan sanya rayuwarka a cikin matsala!"

Ya k'arasa maganar cikin k'araji, ta yadda har hakan ya firgita mai gadi da yaji duk abun da ya fad'a.
Tukun ya juya yana mai shirin tafiya.

Sai dai kuma ko taku biyu baiyi ba yaja ya tsaya cak, saboda jin dakakkiyar muryar Bir da yayi ta daki dodon kunnuwansa a kausashe, yana mai fad'in.

"Idan aka k'i kuma fa?"

Cak itama Gimbiya Tasmir data futo daga cikin garden d'in nan da niyyar ta koma cikin gida taja ta tsaya, saboda jin abunda ya fad'a zuciyarta na wani irin bugu da tsananin k'arfi.

Shi kuwa Yarima Asad cikin matsanancin b'acin rai ya juyo wurin da Bir yake a zaune suna masu kafe junansu da idanu.
Tukun ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Zan aikata duk abun da nace maka zan aikata, saboda Haddiyal tawace ni kad'ai."

"To meye abun kuma tada jijiyar wuya haka, tamkar kai d'in ba namiji bane. Ashe ma kai kanka ka raina kanka, shiyasa har bazaka iya k'watar soyyarka ba da zuciya sai da k'arfi. To kasani ko kad'an Bir baya tsoron wuya, ballantana kuma barazana, dan haka wannan kalamin naka ko kad'an basu firgitani ba, asalima sai karsashi da suka k'aramin, kana kuma suka sanya mun zazzafar soyayyarta a cikin zuciyata, dan haka ina ganin kawai kaje mu had'e a filin Shad'in da za'ayi a kwana shida masu zuwa, sai a tantance tsakanin Jarumi da raggo tsakanin ni da kai."

Yayi maganar babu alamun wasa ko barazana kwata-kwata a cikinta, asalima tun daga k'asan zuciyarsa ya futar da ita
Sosai kuwa jin hakan yayi matuk'ar firgita Gimbiya Tasmir tare da d'imautata, wato da gaske kenan Bir ya zab'i wata ya yadda ya barta ita da tayi komai kana tarasa komai nata dominsa.
Hak'ik'a daga yau daga yanzu ta gama zama a cikin gidan nan har abada, zata tafi ta barsa ko da futarta daga cikin na nufin rabuwa da rayuwartane, saboda bazata tab'a iya jurar wannan k'ask'ancin da Bir yayi mata ba, hak'ik'a yaci amanar al'k'awarin daya d'auka.

Sosai shima Yarima Asad ya firgita da jin kalaman Bir, kana kuma tsoro k'arara ya bayyana akan fuskarsa, sai dai kuma hakan bai hanasa sake bud'e baki yana mai fad'in.

"Kasani ni kuma na maka al'k'awarin b'atar da kai na har abada daga cikin duniya."

"Ni kuma namaka alk'awarin rabaka da ita rabuwa kuma ta har abada nan da kwanaki shida masu zuwa."

Shima Bir ya fad'a a wani irin kausashe.

Wanda hakan kuma ya sake dugunzuma zuciyar Gimbiya Tasmir. Saboda ita kanta ta sani bulala d'arima ba komai bace a wurin Bawan cikin Bak'ar Masarauta, ballantana kuma talatin, domin kuwa ko ita tayi masa azabar data ninka bulalai d'ari masu tsananin zafi amma baiyi k'wallaba, asalima ko murmushi bai denayi mata ba, wannan dalilin ya sanya ta riga tasan har dai ta silar bulalai Bir zai mallaketa to tuni ya riga da yagama mallakarta ma.

Da gudu ta shige cikin gida ba tare da tana kallon ko cikakken gabanta ba, saboda tsananin tashin hankalin da take ciki.

A kuma lokacin shima Bir ya tashi daga kan kujerar da yake yana mai tunkarar cikin garden d'in gidan.
Yayinda shi kuma Yarima Asad ya fuce ransa a matuk'ar dagule.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir ko da tashiga cikin gidan bata tarar da ko mutum d'aya a falon ba.
Hakanne ya sanya ta hucewa cikin d'akinta kai tsaye.

Cikin sauri ta janyo jakar da sukazo da ita tana mai bud'eta ta fara loda kayanta a cikinta, kana bayan ta gama ta rufeta tana mai d'aukarta, tukun ta futo rik'e da ita a hannunta idanunta na matuk'ar tsiyayar da k'walla, yayinda take jin zuciyarta kuma na wani irin rad'ad'i da suya, tana mai fucewa daga cikin falon...........✍



#Team Bir &Tasmir
#Team Bir & Haddiyal
#Team Asad & Billy
#Team Asad & Haddiyal.


_Ina buk'atar jin ra'ayin kowa a wannan had'in._


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*26*



Da sauri Alawiyya da futowarta kenan daga cikin kichin taga hucewarta d'auke da jaka a hannunta ta bita zuwa wajen a guje itama.
"Gimbiya!"
Ta fad'a cikin tsananin tashin hankali da firgici, saboda ganin da tayi da gaske tafiya zatayi.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir da take tafiya kanta durk'eshe a k'asa idanunta na zubar da k'wallai, cak taja ta tsaya a wurin da take, saboda muryar Alawiyya da tajiyo ba tare data waigoba.
Ganin hakan da Alawiyya tayine ya sanyata dosar wurin da take da matuk'ar sauri.

"Lafiya Gimbiya, ina zaki tafine haka da jaka a hannunki."
Alawiyya ta fad'a a tsantsar rud'e tana mai tsayawa a bayanta.

Ita kuwa Gimbiya Tamsir cikin wani irin yanayi ta juyo tana mai watsa jik'ak'k'un idanuwanta a cikin na Alawiyya, wanda ganin hawayen akan fuskarta da Alawiyya tayine kuma suka sake matuk'ar d'imautata.
Tukun ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Zantafi ne, duk da bani da ikon komawa wurin dana futo, amma sai dai kuma na sani bazan rasa mazauni ba ko da a saman bolane kuwa!"

Ta k'arasa maganar tana mai juyawa da niyyar tafiya, amma sai taji Alawiyya ta damk'i hannunta da k'arfi, tana mai fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, mene yake faruwa Gimbiya? Me akayi miki da zafi haka da har zaisa ki yanke hukuncin barinmu?"

Tayi maganar a wani irin firgice, jikinta na d'aukar kyarma, kafin daga bisani kuma ta sake damk'e hannun Gimbiya Tasmir a cikin nata, ruwan hawaye na b'alle mata daga cikin idanu.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir cikin wani irin yanayi ta sake juyowa gareta, yayinda zuwa yanzu kuma gaba d'aya fuskarta ta gama damewa da ruwan hawaye.
Kana ta bud'e baki cikin matsanancin kuka mai sosa zuciya da ruhi, tare da kuma murmushi alokaci guda, sai dai kuma kallo d'aya zaka mata ka gane murmushin ba irin murmushine na farinciki ba, murmushine na tsantsar takaici da danasani wanda yafi kuka ciwo, tana mai fad'in.

"Rayuwa cike take da k'alubale tare da abubuwan ban mamaki Alawiyya. Shin me yasa idanuwanmu suke rufewa, kunnuwanmu su kurmance, k'wak'walenmu kuma su dod'e, tayadda har muke gaza gane dai-dai alokacin da muka afka cikin kogin soyayya?
Da fari na dauki al'amarin soyayya da wasane, wasane na fidda kai, na zata idan kanada kud'i da jin dad'in duniya shikenan soyayya ba zata wahalar da kai ba, al'amarin da yake fizgar zuciyata zuwa ga sonsa, ya zarce al'amarin da yake tsananin son mulki ko kud'i. Na yi kuka, hawayena ya k'afe, k'afewa irin ta tafkin da ruwa ya k'are masa, jikina yayi rauni, burina ya fad'i, fad'uwa irin wacce rana take yi da maraice, shin ba zan samu salamar zuciya ba? Ashe abinda idanu yake hange, k'wak'walwa take tunani ba shi zuciya take samu ba?"

Sai kuka yaci k'arfinta mai matuk'ar sosa zuciya, jikinta na wata irin karkarwa, duk da kasancewar kukan nata bamai sauti bane ba kwatakwata, amma kuma ba k'aramun firgita Alawiyya yayiba.
Wanda har hakan ya sanya itama nata hawayen sake tsinkewa da bala'in gudu.
Kana ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Lahaula walak'uwwata illahi billah, Allahuma ajirni fimusibati wa'aklifni kairan minha. Shin meya farune haka Gimbiya? Me shi Bir d'in yayi mikine? Ya subanallahi na rok'eki da sunayen Allah kiyi hak'uri kiyi shiru kizo mu koma ciki."

Cak Gimbiya Tamsir ta tsaya da kukan da take, saboda jin abunda Alawiyya ke fad'e.
Kana daga bisani ta fara girgiza kanta tana mai cewa.

"Nabar kowa nawa, Iyayena, Yayyena, ba tare da nayi tinanin halin bak'incikin da zasu shiga ba idan suka tashi basu ganniba na biyosa, amma sai gashi lokaci d'aya ganin wata yasanya ya manta da duk hallacin da nayi masa. Dan haka zantafi, duk da dai a yanzu bani da ikon komawa cikin masarautarmu, amma dana zauna anan ina kallonsa, na gwammace na tafi na shiga duniya ko da hakan zai zamto silar bugawar zuciyatane kuwa, amma nida sake zama a cikin gidan nan har abada, dan haka kiyiwa su Ummi da Abba godiya ni natafi sai watarana."

Ta k'arasa maganar tana mai funcike hannunta daga cikin na Alawiyya tare da juyawa da matuk'ar sauri, idanuwanta na cigaba da zubar hawaye ta doshi get.
Hakan da Alawiyya ta ganine ya sanyata juyawa a guje tana mai nufar cikin garden d'in nan cikin matsanancin kuka tare da tsantsar tashin hankali.

Shi kuwa mai gadi a matuk'ar firgice yayo kan Gimbiya Tasmir yana mai fad'in.

"Lafiya Hajiya, ina zaki tafine a haka?"

Sai dai kuma inda yake bata d'ago ta kallaba, sai bud'e k'ofar da tayima tana mai fucewa daga cikin gidan gaba d'aya.

Ita kuwa Alawiyya cikin matsanancin kuka ta k'arasa wurin da Bir yake zaune akan kujera ya buga tagumi, tana mai nuna masa hanyar waje tare da fad'in kalmar.

"Gimbiya! Gimbiya!! Gimbiya dan Allah karka barta ta tafi."

A matuk'ar zabure, kana kuma cikin matsanancin tashin hankali da firgicin da kalamanta suka saukar masa ya mik'e tsaye yana mai kallonta tare da fad'in.

"Mene ya samu Gimbiyata? Me akayi mata ina takene?"
Ya jero mata tambayoyin a matuk'ar firgice, kana kuma cikin k'araji jikinsa na d'aukar wata irin kyarma.

"Karka barta ta tafi dan Allah, Gimbiya ta d'auki jakarta ta tafi, ta tafi!!"

Ta k'arasa maganar tana mai juyawa a guje ta doshi cikin gidan domin ta sanarwa dasu Ummi.

Shi kuwa Bir wani irin sarawa yaji kalamanta sun sanya kansa yayi, yayinda kalmar ta d'auki jakarta ta tafi, ta tafi da Alwaiyya ta fad'a suka dinga masa amsa kuwwa a kunne.

Lokaci d'aya gaba d'ayansa ya firgicce ya rud'e.
Wata irin karkarwa jikinsa keyi tamkar wanda yake a cikin k'ank'ara, kafin daga bisani kuma ya bud'e baki cikin matsanancin tashin hankali tare da k'araji yana mai fad'in.

"Inaaa k'arya kike na sani Gimbiyata bazata gudu ta barniba."

Ya k'arasa maganar yana mai fara zagaye a cikin lambun.
Kafin daga bisani kuma ya d'iba a guje tamkar mahaukaci yana mai d'aukar hanyar waje.
Gaba d'ayansa ya firgice ya rud'e, kana kuma ya d'imauce lokaci guda.

"Ina Gimbiyata ta tafi, meyasa kabar Gimbiyata ta tafi mai gadi?"

Bir ya fad'a a wani irin tsawace adai-dai lokacin dasu Ummi harma da Kaka suka futo daga cikin gidan a guje cikin matsanancin tashin hankali suma.

"Kayi hak'uri yallab'ai, naso na hanata tafiya amma ko kallona bata tsaya tayiba da nai mata magana."

Me Gadi ya fad'a a matuk'ar tsorace, saboda ba k'aramun firgita yayiba da ganin yadda idanuwansa sukai bala'in jajahur.

Jin abunda ya fad'ane ya sanya Bir bangajesa, yana mai zurawa a guje ya fuce daga cikin gidan, hak'ik'a babu wanda zai gansa a yanayin da yake na yanzu baiyi zaton mahaukaci bane tuburan shi d'in.

Ummi ma da take rik'e da gyalenta a hannu tare da Matar Sheikh Ahmad da kuma alawiyya, da sauri suka fuce daga cikin gidan suma.

Itama Kaka fucewa tayi tana mai binsu a baya idanunta har suna tsiyayar k'walla, kai idan kaga yadda hankalinta ya tashi bazaka tab'a tinanin itace take fad'in bazata zauna a cikin gidanba ada.

Duru-duru Bir ya fara a tsakiyar layin a matuk'ar haukace. Ganin da yayi bai hango ko mai alamunta bane ya sanyasa bin hannun hagunsa da bala'in gudu.
Yayinda su Ummi kuma sukayi hannun damansu a matuk'ar firgice, Matar Sheikh Ahmad kuwa suna tafiya ta futo da wayarta tana mai nemo number mijinta ta doka masa kira idanunta na zubar k'walla.

Wani irin gudu Bir yake tamkar zai tashi sama, kallo d'aya mutum zai masa ya fahimci baya cikin hayyacinsa kwata-kwata, hakanne yasa yana shan kwana ya hangota tana tafiya rik'e da jakarta, yayinda gashin kanta kuma yake d'an d'agawa sama, sabo da iskar da akeyi.

Yana k'arasawa wurin da take ya mik'a hannunsa yana mai damk'ar nata

Please Login or Register in order to submit comment