Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

Kai d'age sama ya doshi hanyar d'akinsa ba tare da ya tsaya kallon cikin falon ba ballantana ya lura da mutane a cikin sa ko babu.
To kasancewar kuma babu kowa a cikin nasa sai hadiman da suke aiki, shiyasa har ya shige lungun d'akinsa baiji wani ya kirasa ba.

Ko da ya k'arasa bakin k'ofar d'akin hannunsa kawai ya kai jikinta yana mai tura ta ba tare da ya tsaya cewa zai sanya mukkuli ya bud'e ta ba, duk da kuwa bai san da mutum a ciki ba, kasancewar gaba d'ayansa ba a cikin nutsuwarsa yake ba.

Da sauri Al'amin dake zaune akan kujera ya mik'e tsaye yana mai fara bin Yarima Asad da idanuwansa tun daga sama har k'asa cikin tsantsar firgici.
Saboda ganin sa da yayi gaba d'ayansa a wani irin haukace.
Yayinda shi kuma Yarima Asad ya hucewarsa zuwa cikin bedroom d'in sa ba tare da ya lura da ko Al'amin ba da yake kallonsa ba.

Ganin hakan da Al'amin yayi ne ya sanya sa mara masa baya cikin sauri shima, yana mai shigewa cikin bedroom d'in nasa.
Sai dai kuma yana shiga ya hangi shigewar Yarima Asad d'in cikin bathroom.
Hakanne yasa sa fad'awa kan kujrar da take kafe daga bakin k'ofa jab'ar, yana mai bin k'ofar bayin da idanu.

Yayinda tinanin abun da ya faru da Abokin nasa da har ya canza haka gaba d'aya ya cika masa zuciya.

Acan wurin Yarima Asad kuwa direct ya doshi wurin da shower take ba tare da ya tsaya cire kayan jikinsa ba.

Yana k'arasawa wurin ya kai yastun hannunsa zuwa wurin makunnarta yana mai kunnata.
Kana ya matsa k'ark'ashinta sassanyan ruwan da yake zubowa daga cikinta ya fara sauka a tsakiyar kan sa, ba tare da ya cire ko da takalmin k'afarsa ba.

Lokaci d'aya ya fara sauke wasu irin tagwayen ajiyar zuciya, tamkar wanda ya d'auki tsawon wata da watanni yana kuka.

Ya d'auki tsayin mintina ashirin tsaye a k'ark'ashin shower rumtse da idanuwansa yana mai sakin numfashi.
Tukun a k'arshe ya janye jikinsa daga wurin, saboda yadda har yanzu yake jin sauran damuwa dank'are a cikin ransa.
Domin kuwa ko da ya rufe idanuwansa ma babu abun da yake gani face fuskar Gimbiya Haddiyal, wanda hakan kuma yake sake sanyasa jin wani irin k'unci a ransa, saboda so yake ya manta da ita gaba d'aya a rayuwarsa, so yake ya manta da ya tab'a zuwa garin su ma gaba d'aya balle kuma har ya tuna ta.

Ba tare da ya cire kayan jikin nasa ba ya sake dosar hanyar da zata futar da shi daga cikin bathroom d'in, duk da yadda jikinsa ke d'igar ruwa kuwa.

Da matuk'ar sauri Al'amin ya mik'e tsaye daga kan kujerar da yake yana mai fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Lafiyar ka k'alau kuwa Asad?"

Ya fad'i hakan a tsantsar rud'e, saboda ganin Asad d'in da yayi ya koma tamkar mahaukaci.
Domin ko sosai ruwa ke d'iga daga jikin sa.

Girgiza kai Asad yayi yana zubewa akan gadonsa ya zauna ba tare da ya iya cire kayan ba, yana mai kafe Al'amin da jajayen idanuwansa.

Hakan da Al'amin ya gani ne ya sanya sa k'arasowa wurin da yake da sauri, yana mai durk'usawa a gabansa tare da fad'in.

"Shin me yake faruwa ne Asad, mene ne ya sameka acan Masarautar Fuld'en da kaje ne?"

Ya watso masa tambayar cikin tsantsar tashin hankali.

Shi ko Yarima Asad rumtse idanuwansa yayi da k'arfi, saboda jin sunan wurin da Al'amin ya kira yanzu, wanda yake da burin ya mantasa cikin gaggawa.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e idanuwan nasa akan fuskar Al'amin yana mai girgiza masa kai.
Kana ya d'aga lab'b'ansa cikin wata irin murya yana mai cewa.

"Shin dama k'azami ne ni Al'amin, shi ne kuma baka tab'a sanar dani ba dan na gyara a matsayinka na aminina Al'amin?"

Ya jefowa Al'amin tambayar da ta rikitasa, yana mai kafe sa da idanuwansa, tare da jiran jin amsar da zata futo daga bakinsa.

Shi kuwa Al'amin sosai kalaman Yarima Asad suka sake matuk'ar rikitar da shi, wanda har hakan ya sanya sa d'aga idanuwansa yana mai kallonsa tun daga sama har k'asa.
Kana a k'arshe ya sake sauke idanuwan nasa a cikin tsakiyar na Yarima Asad da yake kallonsa shima.
Tukun ya bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Wane ne ya fad'a maka cewar kai k'azami ne?"

Rumtse ido Yarima Asad ya sakeyi da k'arfi.
Kafin daga bisani kuma yace.

"Itace!"

Maganar ta futo a fuzge ba tare da yasan lokacin da ta tawo ba, sai kawai futowarta da yaji daga cikin bakinsa

Shi ko Al'amin da sauri ya zaro idanuwansa waje, bakinsa na rawa wurin fad'in.

"Wacece itan?"

Da matuk'ar sauri Yarima Asad yayi wani irin d'ago hannuwansa biyu, yana mai s...............✍



_UMAR DAYYAN_✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*08*



Sanya tafukan sa ya dafe kansa tare da cije leb'ensa, saboda jin katob'arar da yayi a gaban Al'amin, wanda baya son yasan abun da ya faru har abada.

"Ya dai Bro, wai dan Allah me yake faruwa ne, wacece ta kira ka da k'azami?"

Al'amin ya fad'a yana mai dafa cinyoyinsa da hannu biyu cikin tsantsar damuwa.

Shiru Yarima Asad yayi ba tare da yace komai ba.
Yayinda har lokacin kuma yake jin zuciyarsa na cigaba da tafarfasa, kalaman Gimbiya Haddiyal na sake dawo masa a cikin k'wak'walwarsa.

"To dan Allah ko ba zaka ce komai ba, yanzu ina son ka tashi ka cire wa'yan nan jik'ak'k'un kayan ko dan kar ciwo ya kama ka."
Ya k'arasa maganar yana mai janye tafukan hannayensa daga kan cinyar Yarima Asad, tare da mik'ewa tsaye, ya koma ya zauna a gefen gadon kusa da Yarima Asad.

A hankali ya zame tafukan hannayen nasa daga kan goshinsa, kana ya d'an juyar da kai gefe, yana mai fesar da iskar bakinsa.
Tukun ya mik'e tsaye a hankali.
Kana ya fara d'aga k'afafuwansa yana mai nufar gaban wardrobe d'in sa, ba tare da ya kalli ko inda Al'amin yake ba.

Yayinda shi kuma Al'amin ya bisa da idanuwa, yana mai jin wani irin tausayin sa na lullub'e sa, saboda fahimtar da yayi na bai samu nasara ba a wurin ta, gashi kuma ko da bai fad'a masa ba kallonsa kawai da ya k'arayi a yanzu yasa ya k'ara tabbatarwa kansa da ba k'aramun so yake yiwa yarinyar ba.

Shi ko Yarima Asad cikin sanyin jiki ya fara cire jik'ak'k'un kayan jikin sa yana mai a jiye su a gefe.
Kana a k'arshe ya bud'e wadrobe d'in tasa yana mai zaro riga da wando na shan iska bak'ak'e masu taushi, tare da singilet da boxer.
Tukun ya juya yana mai dosar hanyar bathroom domin yaje ya sanya kayan, kasancewar Al'amin na zaune anan cikin d'akin har yanzu, gashi shi kuma har boxer dole sai ya cire, saboda yadda shima d'in ya jik'e sharkaf.

Ya d'auki tsayin mintina har kusan goma a cikin bathroom d'in, tukun ya futo sanye da kayan da sukayi matuk'ar yi masa kyau, ruwa na d'iga akan fuskarsa, da alamun dai har Al'wala sai da yayo a ciki, kasancewar har an fara kiran sallah'r magariba a gari.

Ganin hakan da Al'amin yayi ne, ya sanya sa mik'ewa tsaye shima, yana mai nufar cikin bathroom d'in shima.

Duka baifi 5 minuts yayi a ciki ba sai gashi nan shima ya futo.
Tukun suka jera su biyun suna masu fucewa daga cikin d'akin suka kama hanyar masallaciinsu na cikin masarautar.
Har lokacin kuma Asad bai yadda sun had'a idanu da Al'amin ba, domin kuwa shi kansa kunyar kansa yake ji akan abun da ya aikata yau d'in, ballantana kuma ya bari Al'amin yaji, saboda ba k'aramun cika baki yake ba akan mata tun suna k'ananansu har kawo yau.

Ko da aka idar da Sallah zaune Yarima Asad yayi a cikin masallacin bashi da niyyar futa.
Yayinda shima Al'amin ya k'ara gyara zaman sa a wurin, duk da yadda kuwa kusan kowa na cikin masallacin ya fuce sai tsirari sukai saura, saboda shima yace ba zai tab'a barin Asad ba yau, har sai yaji dalilin zuwansa masarautar fuld'e, duk da dai ya riga da ya fahimci abun da ya kaisan ma, amma dai duk da hakan yana son jin ta bakinsa ne da kansa.

Ba zato ba taammani sukaji muryar mai martaba akansu, yana mai fad'in.

"Yau kuma 'yan addu'a ne suka tashi akan 'yan samari na kenan.
To dai kar ku manta da sanya Dady'n naku a ciki, kana kuma ku rok'i Allah ya k'ara shirya mun ku kunji ko."

Ya k'arasa maganar cikin raha, yana mai zama kusa da Yarima Asad.
Yayinda suma d'in duka suka juyo da kansu b'arin da yake, suna masu sakar masa murmushi.
Kana daga bisani suka bud'e baki suna masu fad'in.

"Barka da dare Dady?"

"Yawwa 'yan samarina fatan kun yini lafiya dai ko?"

Ya k'arasa maganar da kife tafukan hannayensa a tsakiyar kansu.

Da sauri ya mayar da idanuwansa kan fuskar Yarima Asad, saboda jin kan nasa da yayi ya d'au zafi rau, duk da dai dama tun da ya k'araso wurin da ya kalli fuskarsa ya fahimci baya jin dad'i, domin kuwa har 'yar rama yaga yayi masa akan jiya da suka rabu.

Da sauri, kana kuma cikin d'an firgice ya bud'e bakinsa yana mai fad'in.

"Shin me yake damunka ne Baba na, ba dai baka da lafiya bane ba dai ko?"

Da sauri Yarima Asad ya lumshe idanuwansa.
Kana daga bisani ya bud'e su akan fuskar mahaifin nasa, yana mai cewa.

"A'a Dady ka kwantar da hankalinka, babu abun da ke damu na ni."
Ya k'arasa maganar yana mai d'an fesar da iska.

Yayinda shi kuma mai martaba ya tsira masa idanuwansa yana mai nazartarsa, ba tare da yace masa komai ba.
Kana daga bisani ya d'an d'aga lab'b'an sa yana mai fad'in.

"To amma me ya kawo zafin da naji a jikin ka idan har lafiyar k'alau kamar yadda ka fad'a, bayan haka kuma ai ba haka na ganka jiya ba, gaba d'ayanka yau ka fad'a.
Shin me yake damunka ne Baba na? Ina fatan dai ba akan maganar da muka tattauna da kai jiya bace ta sanyaka cikin damuwa?"

Lumshe idanuwa Yarima Asad yayi yana mai d'an fesar da numfashi a hankali, domin ko gaba d'aya ma rasa abun da zai cewa mahaifin nasa yayi, dan da ace iya damuwar jiyan ce ma da da sauk'i da irin hulak'ancin da ya kai kansa yau akayi masa, a wurin da bai kai ayi masa hakan ba.

Jin da Mai Martaba yayi yayi shiru ne ya sanya sa dafa kafad'arsa.
Kana ya bud'e baki cikin taushin murya, yana mai cewa.

"Kwantar da hankalinka zakayi kayi duk yadda na ce maka kayi Baba na, domin kuwa gaba d'aya wannan abun bai kai wanda zai sanyaka har ka damu irin haka ba, kawai dai abun da nake so da kai yanzu shine, ka nutsu ka cire duk wata damuwa a ranka ka fara nemo yarinyar da kasan tayi maka, in yaso sai a had'a ayi abun a rana d'aya duka, wannan itace kawai mafuta a gareka, idan kuma ba haka ba fa to ka sani dolene kayi hak'uri ka auri ita bilkisun.
Dan haka yanzu kutashi ku tafi Al'amin ka nemo magani ka bashi ya sha kaji ko, nima yanzu zan shiga ciki ne."

Mai Martaba ya k'arasa maganar yana mai mik'ewa tsaye, tare da shafa kansu yace.
"Allah ya albarkaci rayuwarku."
Tukun ya juya ya tafi.

Shi ko Yarima Asad sake lumshe idanuwansa yayi, yana mai jin zuciyarsa na k'arayi masa zafi.
Tabbas yana ji a ransa tamkar iyayen nasa sun gaji da ganinsa a duniya ne, shi yasa har suke son su kawar da shi ta hanyar wannan gingimemen abun da suka k'irk'iro masa.
Dole ne ma ya koyawa Billy hankali tun da har ta rusa masa farin cikin sa.

Lokaci d'aya yaji duk wani haushin da ya kwaso a wurin Gimbiya Haddiyal ya koma kan Billy.

"Tashi muje ko Asad."

Al'amin ya fad'a yana mai dafasa tare da mik'ewa tsaye.
Ba tare da ya musa masa ba shima ya mik'e tsayen.
Tukun suka jera a tare suna masu fucewa daga ciki.

Anan cikin falon Mamy'nsu suka yada zango, saboda hangosu da sukayi gaba d'aya a dining area suna shirin cin abinci.

Kallo d'aya Fulani tayiwa Yarima Asad tun kafin sukaiga gaisheta ta fahimci da akwai abun da yake damunsa.
Da kuma suka gaisheta taji muryarsa sai ta k'ara tabbatar da hakan.
Kana kuma lokacin da suka fara cin abinci gaba d'aya tana lura da shi, duka baifi spoon biyar yayi ba ya dena ci, sai lemo kawai da ya tsiyaya a cup yasha.

Sai da ta tabbatar da sun gama duka har suna shirin mik'ewa su tafi, tukun ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Meke damunka ne Zaki?"

Ta fad'a idanuwanta akansa.

'Dan lumshe idanuwansa Yarima Asad yayi, yana mai jin duk ba dad'i, ta yadda kowa ya gansa yake fahimtar yana cikin damuwa.
Kana daga bisani ya bud'e idanuwansa akan fuskar Mamy'n tasa, yana mai cewa.

"'Dan ciwon kai ne kawai Mamyna, shima kuma d'in ba sosai bane ba."

"Bayan shi kuma fa sai me? Domin kuwa tun da safe kafun kafuta na fahimci kana tattare da damuwa, kawai dai nayi shiru ne bance maka komai ba."

Fulani ta sake fad'e tana kallonsa.

"Da gaske nake Mamy ciwon kai ne kawai."
Yarima Asad ya fad'a ahankali, yana mai kagara ya tashi ya bar wurin.

"Shin da gaskene abun da yace Al'amin, nasan kaine kad'ai kake riga kowa sanin damuwarsa."

Fulani ta fada tana kallon Al'amin.

"Eh Mamy nima hakan yace mun dai."
Al'amin y fad'a mata haka, saboda ganin da yayi na Yarima Asad d'in baya son kowa ya san abun da ke damunsa.

"Tom shikenan ku tashi kuje, Allah yayi muku Albarka ya k'ara shirya mana ku kuma."

Cewar Mamy ba dan ta yadda da abun da suka fad'a mata ba, sai dan kawai jin da tayi sunk'i su fad'a mata gaskiya, duk da dai a ranta tana tinanin ko maganar aurensa da Billy ce ta sanyasa komawa hakan, kasancewar Mai Martaba ya mata duk bayanin abun da ke faruwa tun a jiya da daddare, har yadda sukayi da Asad d'in.
Yayinda itama d'in ta aminta da zancen Mai Martaba na cewar ya nemo wadda yake son sai a had'a duk ayi bikin a rana d'aya.

Suna shiga cikin falon Yarima Asad ya nemi wuri ya zauna akan kujera, yana mai lumshe idanuwansa, tare da fesar da huci daga cikin bakinsa.

Zama shima Al'amin yayi akan kujerar da take fuskantar wacce Yarima Asad yake zaune a akai.
Kana ya gyara zamansa yana mai fuskantar Yarima Asad tare da yin gyaran murya.
Yayinda idanuwansa kuma suka kasance k'ur akansa.

Jin hakan da Yarima Asad yayi ne, ya sanya sa d'ago kansa a hankali, yana mai zuba jajayen idanuwansa akan fuskar Al'amin, domin ko har ga Allah ya gaji da zamansa a cikin d'akin, tini ya k'agara ya tashi yayi gaba ko zai samu damar hutawa.

"Wai dan Allah me yake faruwane Bros, domin ko gaba d'aya kai na ya kulle, kana kuma hankalina ya tashi, saboda kai da kanka kasan bana iya jurar ganin damuwa akan fuskarka."

Al'amin yayi maganar cikin sanyi.

A hankali Yarima Asad ya d'an lumshe idanuwansa, kana daga bisani ya bud'e su yana mai d'aga lab'b'an sa cikin sanyi, ya fara bawa Al'amin labarin abun da Billy tayi masa saboda jin abun da ya fad'a.

Da sauri Al'amin ya dakatar da shi tun kafin yayi nisa a cikin labarin da fad'in.

"Bashi nake nufi ba, domin ko na riga dana gama sanin duka wannan batun, asalima har zama munyi da ita Billy a d'azu gab da zaka dawo.
Dan haka dalilin komawar ka Masarautar Fuld'e da kuma abun da ya faru acan d'in da naga kadawo a hargitse nake son ji."

Da k'arfi Yarima Asad ya rumtse idanuwansa, saboda jin furucin da Al'amin yake yi.
Sosai abun da ya faru acan d'in ya sake dawo masa sabo fidigil a cikin k'wak'walwarsa, ta yadda har yake jin tamkar yanzu ne abun yake kan faruwa.

Yayinda shi kuma Al'amin ya kafesa da idanuwa yana mai kallonsa.
Kafin daga bisani kuma saboda ganin da yayi na basa da alamun zai fad'a masanne ya sanya sa sake bud'e baki yana mai fad'in.

"Ka tina ko wayene ni awurin ka Asad, kar kace zaka b'oye mun komai da ke damunka, domin kuwa ka riga da ka sani bazan tab'a yi maka dariya ba, asalima sai dai na tayaka neman mafuta."

Yarima Asad ya sake jiyo sautin muryar Al'amin a cikin kunnuwansa yana mai fad'in hakan.
Amma mai makon ya fad'a masan, sai kawai jajayen idanuwansa da ya bud'e yana mai girgiza kansa.
Kafin daga bisani kuma ya mik'e tsaye zumbur, yana mai shirin tafiya cikin bedroom.
Ganin hakan da Al'amin yayine ya sanya sa shima mik'ewa tsayen, yana mai yin sauri ya kamo hannun Yarima Asad a cikin nasa.

"Dan Allah ka tafi Al'amin, ka tafi, ka tafi kabarni na kwanta ko na samu sauk'in rad'ad'in da nake ji a cikin rai da zuciyata."

Yarima Asad ya fad'awa Al'amin haka da sauri, kana kuma cikin sanyi yana mai girgiza masa kansa.

Jin hakan da Al'amin yayine, kana kuma ya tabbatar da da gasken hutu Asad yake buk'ata, ya sanya sa sakar masa hannunsa yana mai fad'in.

"To sai da safe Allah ya kyauta."

Ya k'arasa maganar yana mai juyawa ya fuce daga cikin d'akin jiki a sanyaye.

Yayinda shi kuma Yarima Asad ya bisa da idanuwansa, yana mai jin tamkar bai kyauta ba da abun da yayi masa a cikin ransa, saboda masoyinka ne kawai zai ganka cikin damuwa har ya tsaya tambayarka abun da ke damunka, amma sai dai kuma ya ya iya, ko kad'an baya fatan abun da zai sanya wani ya san da labarin nan.
Domin kuwa shima da abun ya faru akansa k'ok'ari yake yaga ya manta da shi har abada daga rana irin tayau.
Kana daga bisani ya juya jiki a sanyaye yana mai d'an taune leb'ensa ya shige cikin bedroom d'in nasa.


*JAHAR KAGUL, CIKIN MASARAUTAR FUL'DE.*

Cikin tsantsar zafin rai da tafasar zuciya Gimbiya Haddiyal ta tunkari part d'in su.
Kallo d'aya mutum zai mata ya fahimci cewar tana cikin b'acin rai bana wasa ba, duba da yadda har take sakin huci tana tafiya tamkar wata zakanya.

Sosai take jin tsanar Yarima Asad a zuciyarta wacce ita kanta ba zata iya misaltata ba.
Yayinda har yanzu kuma muryarsa take cigaba da yi mata amsa kuwwa a lokacin da ya kira Gid'ad'on ta da shashasha.

Ji take aduk duniya bata da wani mak'iyi sama da Yarima Asad a halin yanzu, dan ko tana jin tsantsar tsanar sa fiye da yadda take jin ta Yariman Yamma a zuciyarta ma.

Ko kad'an bata san lokacin da ta kawo kanta cikin tafkeken falon su ba, saboda tashin hankalin da take a ciki, sai kawai sautin muryar mahaifiyarta da taji ya daki dodon kunnenta.

Hakan ne yasa ta tsayawa cak a wurin da take ba tare da ta iya juyowa ba, kasancewar har ta riga data huce saitin inda take.

"Kiranki nake fa kikayi tsaye anan wurin."

Ta sake jin sautin muryar mahaifiyartata tana mai fad'in hakan.
Hakanne ya sata juyowa cikin sanyin jiki tana mai nufo inda taken.
Tun da ta tawo mahaifiyarta take kallonta ba tare da ta iya janye idanuwanta daga kan fuskarta ba har ta k'araso wurin.
Kana ta bud'e baki tun kafin Haddiyal d'in tayi magana, tana mai cewa.

"Shin me yake damun kine Bello ta?"

Ta fad'a murya a tausashe, tana mai kallonta.
Yayinda ita kuma tayi durk'ushe abakin kujerar da Dadden tata take zaune akai.
Kana daga bisani ta d'ago rinnanun idanuwanta tana mai d'ora su akan fuskar mahaifiyar tata, sannan ta girgiza mata kai, tana mai had'awa da fad'in.

'Ba komai Dadde na."

Tayi maganar cikin harshen fulatanci tamkar yadda sukeyi dama, tana mai cigaba da girgiza kai.

Shiru mahaifiyar tata tayi ba tare da tace komai ba, kafin daga bisani kuma ta d'an juyar da kanta gefe, tana mai fesar da iska daga cikin bakinta.
Sannan ta sake juyowa b'arin da Haddiyal take tana mai cewa.

"Na san dai ba zai huce akan wannan mutumin na mafarkinki ba ne duk ya sanyaki kika koma haka ko?
Shin wai har sai zuwa wane lokaci ne zaki hak'ura ki sanyawa zuciyar ki salama, ki aminta da cewar Aljani ne kike tare da shi ba mu....

Maganar tace ta katse, saboda yadda taga 'yar tata ta fara ja da baya daga durk'ushen da take da sauri, tana mai girgiza mata kai.
Kafin daga bisani kuma wasu irin hawaye masu matuk'ar gudu suka b'alle daga cikin idanuwanta tamkar an bud'e famfo.
Tukun tayi wata irin mik'ewa tsaye a zabure, tana mai cigaba da kallon mahaifiyarta tare da cigaba da girgiza mata kai.
Kana kuma tana faman toshe tafin hannunta da bakinta, gudun kar kukan ya sub'uce mata tayi sa da karfi.
Tukun daga bisani tayi wani irin fuzgo magana cikin rud'u da firgici, tana mai fad'in.

"A'a Dadde na, na rok'ek'i da Ubangijn shanu da mutane akan karki k'ara cewa Gid'ad'o am ba mutum bane.
Wallahi mutum ne, mutum ne Gid'ad'o am lokaci yana gab da tabbatar muku da hakan."

Ta k'arasa maganar da wani irin kuka mai sauti, tana mai juyawa a guje ta doshi hanyar d'akinta.

Ita kuwa Mahaifiyar tata da idanuwa kawai ta bita, tana mai girgiza mata kai, tare da jin ba dad'i a ranta, ba tare data iya cewa komai ba.

A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa bata tsaya ba har sai da ta isa gaban gadonta, tukun ta fad'a kansa ribdaciki tana mai cigaba da sakin kuka, tare da dukan gadon da hannu bibbiyu tamkar wata mahaukaciya.


*BAYAN KWANA BIYU.*

*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Damuwa goma da ashirin sun yiwa Gimbiya Tasmir rubdugu, tun daga ranar da taji labarin Bir abakin mahaifinta har kawo yau.

Ta rasa dalilin da ya sanya take jin tausayin sa na k'ara lullub'e zuciyarta aduk bayan giftawar sa'a, ta rasa dalilin da ya sanya har kawo yau ta kasa manta labarin da mahaifinta ya bata, kana kuma tarasa dalilin da ya sanya har yanzu take da muradin jin dalilin dake sanya gabanta fad'uwa a duk lokacin da zasuci karo da shi.
Gaba d'aya a yanzu bata iyayin cikakkiyar awa d'aya ba ba tare data tuna da shi ba.
Tun daga ranar bikin godiya ga abun bauta gargabilu har kawo yau bata sake sanya sa acikin idanuwanta ba, kasancewar bama ta futa ba taje yawon ballantana har suci karo da shi.

Sai dai kuma kullum da tunanin ciwukan da ta sanya aka ji masa da wa'yan da ta jima sa da kanta sun warke daga jikin sa ko yaya take.

Gaba d'ayanta ta sake yin sanyi, duk da dai dama can ita d'in ba mai hayaniya bace ba, asalima had'uwar su da Bir ce ta fara sanya ta yin doguwar magana, hakan yasa ko kad'an iyayenta basu gano abun da yake damunta ba.
Domin kuwa ko futowa daga cikin d'akin nata ma bata fiye yi ba yanzu.

Yanzu haka kwance take akan tafkeken gadon ta lumshe da idanuwa tamkar mai yin bacci, sai dai kuma azahiri ba baccin da takeyi, asalima fuskar Bir kawai take gani a cikin idanuwanta yana mai watso mata murmushinsa na iskanci a cewar ta.


Acan b'angaren Bir kuwa tun daga ranar da yaji labarinsa ya k'ara k'udurtawa ransa cewar zai ni sanci Gimbiya Tasmir gaba d'aya, ko da kuwa hakan zai zamto silar tsayawar bugun zuciyarsa, ba dan komai ba kuwa sai dan ya sanya Iyar Bayi murmushi, tamkar yadda shi ma take sanya sa ako da yaushe, kana kuma ga jin da yayi na cewar bashi da wani mak'iya aduniya face mahaifinta.

Hakan ne yasa tun daga ranar ya fara k'ok'arin yakice ta a ransa.
Kuma Alhamdulillah ya fara jin sauk'in abun da yake jin dan gane da ita, domin kuwa yanzu haka ma tini ya fara walwalarsa cikin abokansa, kasancewar ciwukan jikin sa kusan duk sun warke saura kad'an ne kawai suka rage.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

Abu fa kamar wasa sai gashi ya zamewa Yarima Asad babba.
Domin kuwa tun daga ranar daya dawo daga masarautar fuld'e har kawo yau bai sake ko takawa ko k'ofar gida ba, saboda yadda damuwa tayi masa yawa.
Gaba d'ayansa ya rame yayi wani iri tamkar ba Prince Asad ba.
Saboda a kullum k'ara jin wata irin mahaukaciyar soyayyar Haddiyal yake yi tana dabai-baye zuciya da ruhinsa.
A duk lokacin daya k'udurtawa ransa cewar zai ya kiceta daga cikin zuciyarsa ya manta da babinta a rayuwarsa, sai ya sake jin wani irin matsanancin son ta na k'ara lulub'e sa.

Bai tab'a sanin haka so yake da matuk'ar zafi ba, idan akace wanda kake yiwa

Please Login or Register in order to submit comment