Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gimbiya Tasmir d'aukar kyarma, yayinda zuciyarta kuma take bugu da tsananin gudu.

Shi kuwa Bir lumshe idanuwansa yayi yana mai sauraron kalamanta da suke sanya zuciyarsa bugu da tsanain k'arfi.
Kana kuma yana jin wani irin abu dangane da ita, ga kuma zallar tausayinta da yaji ya lullub'esa, saboda shi dai Allah ma yasani bai tab'a ganin ko mai kama da itaba a cikin mafarkinsa ko a farke sai a yau, gashi ita kuma yaji tana fad'in cewar shekara da shekaru ta d'auka tana zaman jiransa.
Hak'ik'a labarin nata yayi matuk'ar sosa zuciyarsa, ga kuma wani irin zafi da yaji tanayi masa saboda kukan da yake jin tanayi bilhak'k'i, wanda kuma ya rasa dalilin dayasa yake jin hakan.

Sosai wurin ya d'auki shiru, kowa na sauraren labarin da take badawa, lokaci d'aya jikin mutanen wurin duka yayi sanyi.
Gaba d'aya tausayinta ya kamasu, hatta da Sheikh Ahmad kuwa.

"Amma ke musulmace?"

Sheikh Ahmad ya watso mata tambayar yana mai kafeta da idanu, adai-dai lokacin data gama basu labarin.

Jinjina masa kai tayi alamar eh, ba tare data iya amsawa ba.
Wanda hakan daya ganine kuma ya sanyasa rumtse idanuwansa da tsananin k'arfi.
Yana mai jin zuciyarsa na wani irin bugu, gaba d'aya tsoro da fargabar rashin sanin abun da zai kare kansa dashi a wurin Allah idan har aka tambayesa dalilin da yasa suke barin mutane da jahilci, suna aikata sab'on Allah a doron k'asa ba tare da sun shaida musu hakan ba dai-dai bane a matsayinsa na babban Malami.
Domin kuwa ya sani hakan alhakine a wurinsu, wato dai dolene ga duk wani Malamin masani ya sanar da Al'umma dai-dai, ya kuma hanesu daga aikata ba dai-dai ba ko da zaiyi bak'in jini a wurinsu, muddin yana son wanke kansa a ranar gobe k'iyama.
Ko daren jiya dak'yar ya iya rumtsawa, saboda tinanin irin al'ummar da k'aninsa yayi rayuwa a cikinsu da yaji labari, wato al'ummar cikin BAK'AR MASARAUTA da ko kad'an su basu san da wani addini na musulunciba adoron duniya. Sai kuma gashi yanzuma ya sake jin wasu wa'yan da su kuma musulmanne amma da alamu kwata-kawata basu san abunda musuluncin yake nufi bama.
Domin kuwa ga shaida nan ya gani a wurin Haddiyal, saboda koda bata bud'e baki ta fad'a masa cewar iyayentane suka bata tsafiba yasan su d'inne, kuma da alamun ma abun ya zame musu jiki.
Tabbas dolene zai sake gyara tsayuwa, sannan kuma yanemi 'yan uwansa malamai tare da manyan k'asa domin su tattauna akan irin wannan b'arnar da mutane suke tafkawa a duniya, saboda tsira a wurin Allah a ranar gobe k'iyama.

Ya jima yana tunanin, kafin daga bisani kuma ya bud'e idanuwan nasa da suke a rufe akan fuskar Haddiyal.
Hak'ik'a yaji tausayin yarinyar yayi matuk'ar kama zuciyarsa, hakanne kuma yasanya sa bud'e baki asanyaye , kana kuma cikin taushi yana mai fad'in.

"Naji duk abunda kika fad'a k'anwata, kuma na fahimceki, amma sai dai kuma yanzu ina son ki tashi ku tafi gida, ni da kaina zanzo har cikin masarautar taku domin muyi maganar."

Da sauri gaba d'aya mutanen wurin hatta da ita Gimbiya Haddiyal suka zuba masa ido suna kallonsa.
Yayinda Gimbiya Tasmir kuma taji zuciyarta tayi wata irin mahaukaciyar bugawa da tsananin k'arfi, lokaci d'aya tsoron abun da maganar Sheikh Ahmad take nufi ya lullub'eta.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal da sauri ta fara girgiza masa kai.
Kafin daga bisani kuma ta bud'e baki cikin kuka tana mai fad'in.

"Shekara da shekaru na d'auka ina zaman jiran ganinsa, dan haka bazan tab'a iya tafiya na barsa ba yanzu, bayan kuma nasan yana tare da wata."

"Ba ina nufin idan kin tafi shikenan kun rabu dashi ba, a'a, ina so ki tafine domin nayi tinanin ta inda zan b'ullowa al'amarin naku, saboda shima d'in dakike ganinsa b'akone anan d'in, jiya itace ranar farko daya fara zuwa garinnan, asalima ba a cikinsa yayi rayuwa ba duk da kasancewar iyayensa 'yan cikinsa. Sai dai kuma k'addara ta rabasa dasu tun alokacin daya fad'o gidan duniya, wanda hakan kuma ya sanya yayi rayuwa acan wata duniyar ba tare daya sansu ba ko su sun sansa, sai kuma a yanzu da k'addara ta sake dawowa dashi garesu ta silar Gimbiya Tasmir, ta kasance 'ya ga Sarkin garinsu, ta biyosa nan ne domin ta sadasa da mahaifansa, wanda cikin ikon Allah kuma ba tare da sun jigata ba yasa suka sadu.
Wannan dalilin shine ya sanya nace miki ki tafi, saboda a halin yanzu shima yana buk'atar natsuwa da hutune, ko kuwa kina son ya wahalane?"

Ya k'arasa maganar a hankali, yana mai kallonta.
Girgiza masa kai tayi ba tare da tace komai ba, domin kuwa sosai taji tausayinsa ya lullub'eta.

"To idan har dagaske ne abun da kika fad'a, ina son kiyi hak'uri yanzu ki tashi ki tafi, ni kuma namiki alk'awarin zuwa har cikin masarautarku muyi magana da iyayenki."

"To sandata."

Ta fad'a a sanyaye tana mai shirin mik'ewa tsaye.

"Kije kawai itama sandar zan kawo miki ita."
Cewar Sheikh Ahmad yana mai mik'ewa tsaye shima.

Shiru tayi ba tare da tace komai ba.
Kana daga bisani kuma ta juya b'arin da Bir yake tana mai kai idanuwanta kansa.
Karaf kuwa ta kamasa yana kallonta, wanda hakan kuma yayi sanadiyyar had'ewar idanuwansu wuri d'aya.

Kafe junansu sukayi da idanuwa ba tare da wani daga cikinsu ya iya janyewa ba.
Wanda hakan kuma ya sanya Gimbiya Tasmir da take kallon Bir taji zuciyarta na wani irin bugu, matsanancin kishi tare da zallar fargabar abunda Jarumi yake nufi da kallon da yake mata suka lullub'e zuciyarta, ta yadda har ta fara tsoron yin danasanin biyosa da tayi ta bar iyayenta.

Lumshe idanuwa Gimbiya Haddiyal tayi, kana daga bisani ta bud'esu tana mai bud'e baki tace.

"Kamar yadda ban tab'a gajiya da furta maka wannan kalmar ba a cikin mafarkina ba shekara da shekaru, haka kuma bazan tab'a gajiya da furtamaka ita ba a zahiri, wato dai ina sonka Gid'ad'o am, so mai tsanani!"

Ta k'arasa furucin tana mai juyawa ta tafi idanunta na zubar k'walla.

Yayinda jikin Gimbiya Tasmir kuwa ya d'auki wata irin matsananciyar karkarwa, ga wata irin tsanar Haddiyal data sake dukan zuciyarta. Tabbas da ace babu Sheikh Ahmad a wurinnan da bata tinanin akwai abun da zai hanata kasheta har lahira, ko taji sauk'in abun da takeji a zuciyarta.

Shi kuwa Bir wani irin mugun sanyi yaji jikinsa yayi, ga tausayinta daya sake lullub'e zuciyarsa, ta yadda harya kasa janye idanuwansa daga kanta duk da juyawar da tayi tana tafiya.

Ita kuwa Gimbiya Haddiyal sosai idanuwanta ke tsiyayar da ruwan hawaye, tana mai jin zuciyarta na wani irin rad'ad'i da suya.

Cak ta tsaya adai-dai lokacin data isa bakin k'ofa.
Kana daga bisani ta juyo da kanta ba tare da ta juyo da jikinta ba, tana mai watsa idanuwanta a cikin na Gimbiya Tasmir da tabi bayanta da kallon tsana.
Kana ta bud'e baki cikin wata irin kakkausar murya, tana mai fad'in.

"Ke kuma Gimbiya kike da suna kowa? To kisani zantafi yanzu domin farincikin Gid'ad'o am, amma kisa a ranki zaki iya sake ganina daga yanzu zuwa yamma, dare, gobe da safe, da rana, da yamma, ko kuma jibi, domin kuwa ban futa bane da niyyar na dena zuwa gaba d'aya, asalima a kowane lokaci ina iya dawowa muddin idanuwana suka buk'aci ganin Gid'ad'o am, saboda har abada nawane ni kad'ai, kuma bazan tab'a had'asa da wata 'ya mace ba."

Ta k'arasa maganar tana mai janye kanta tare da juyawa ta tafi.
Yayinda Gimbiya Tasmir kuma ta mik'e tsaye cikin wani irin yanayi idanuwanta na zubar k'walla, tana mai shirin shigewa cikin gidan.
Amma sai taji muryar Sheikh Ahmad yana mai fad'in.

"K'anwata!"

Cak ta tsaya a wurin da take kuwa ba tare data iya juyowa ba, sai hawayen idanuwanta da suke k'ara tsananta, saboda ganin da take kamar zasu aminta da Haddiyal ne suk'ita ita, tunda dama itan mai laifice a garesu.

"Kiyi hak'uri k'anwata, rayuwa ta gaji haka, wataran dad'i wataran akasinsa, haka kuma rayuwa tafe take da k'addarori tare da k'alubale iri-iri, dan haka ki kwantar da hankalinki, banason abun daya faru a yanzu ya sanyaki cikin damuwa, domin kuwa Bir naki ne bi'izinnillah, babu wanda ya isa ya rabaku aduk cikin mu, sabo da tare muka ganku, sai dai idan Allah ne ya tsaro hakan, domin kuwa ita rayuwar d'an adam gaba d'ayanta tsararrace, wacce Ubangiji yake tsara masa ita tun alokacin da mala'ika ya busa masa rai a cikin cikin mahaifiyarsa. Dan haka kisani Bir nakine kuma ke d'in tasace."

Ya fad'a cikin sanyi, wanda jin hakan kuma ya sanya zuciyar Gimbiya Tamsir tayi sanyi sosai, sannan kuma taji tana buk'atar k'arin sani game da yadda tsarin nasu Allah yake da tajisa mai burgewa ad'an abun da ya fad'a.

Shi kuwa Sheikh Ahmad ganin da yayi jikinta yayi sanyine, ya sanyasa d'orawa dayi mata nasihohi masu ratsa jiki da jijiya, har yana janyo ayoyi tare da hadisai yana fassarasu.
Wanda hakan kuma yayi matuk'ar tsayawa a zuciyarta harma da ta Bir da yake sauraronsu, domin kuwa ko daya tsaya da nasihar tasa sai sukaji inama ya cigaba, saboda ba k'aramun dad'inta sukaji ba, wanda hakan kuma ya sanya Gimbiya Tasmir taji zuciyarta tayi matuk'ar sanyi.

Ganin hakan da Ummi tayine ya sanya jiki a matuk'ar sanyaye, kana kuma cikin d'an tsoro tayi wurin Gimbiya tana mai dafa kafad'arta.
Kana ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Tabbas hakane duk abun da Yayanku ya fad'a miki, dan haka yanzu mu huce ciki kije ki wanke fuskarki gaba d'aya kin b'ata kwalliyarki."

Ta k'arasa maganar tana mai rik'e hannunta sukayi gaba.
Yayinda shi kuma Sheikh Ahamd ya k'aras wurin da Bir yake yana mai zama a kusa dashi.

Ita kuwa Matar Sheikh Ahmad a tsorace ta huce b'angarensu.

Yayinda Iman kuma da har yanzu zuciyarta take cike da tsoro tayi cikin gidan jiki asanyaye, da niyyar taje ta shirya ta tafi gidansu, domin kuwa dama yau d'in zata tafi, saboda gobe tana da lecture yau d'in ma dai kawai tak'i zuwane, saboda ganin Gimbiya, sai dai kuma a yanzu gaba d'aya tsoronta ma ita taji tana ji.

Shi kuwa Sheikh Ahmad cikin sanyi ya dafa kafad'ar Bir yana mai fad'in.

"Kar kabari hakan ya dameka balle har ya sanya ma tunani acikin zuciya k'anina. In sha Allah hakan ba zai zamto matsala ba, kai dai kawai kacigaba da nunawa masoyiyarka tsaftatacciyar soyayya."

"To Yayana, amma sai dai kuma gaba d'aya tinanin rashin sanin halin da Iyata take ciki shi zai hanani sukuni."
Cewar Bir jiki a sanyaye yana kallonsa.

"Ka kwantar da hankalinka K'anina, in sha Allah babu abun da zai samu Iyarka, kuma ina nan ina tinani akanta tun daga jiya har yau, dan haka kacire duk wata damuwa da take a ranka, yanzu ka jirani anan na shiga ciki na futo sai nazo mu futa tare."

Ya k'arasa maganar yana mai mik'ewa yayi part d'insa, hannunsa rik'e da sandar Haddiyal da kuma takobin Tasmir.

Acikin gida kuwa sosai Iman taci dariya harda su fad'uwa a k'asa alokacin data shiga d'akin Kaka ta ganta ta canza kaya, alamun ta wanke zawon da tayi a zani, gaba d'ayanta ta rakub'e a wuri d'aya tana ta faman muzurai hannunta rik'e da carbi tanaja.
Wanda hakan kuma shine ya sanya Iman taji duk tsoronta ya kau, ta yadda har tasamu damar yi mata dariya, kai a k'arshema da Kaka ta k'ulu mik'ewa tsaye tayi cikin fushi ta biyota waje tana zaginta.
Sai dai kuma tana lek'owa falo data hango Gimbiya Tasmir tare da Ummi zaune akan kujera, sai ta juya baya da sauri tana mai komawa cikin d'akin tare da fad'in.

"Nashiga ukku ni Zulai Aljanar na nan ashe."

Ai kuwa a yanzu ba iyakar Imance ta dara ba hatta da Ummi saida tayi dariya.
Yayinda ita kuma Gimbiya Tasmir ta saki murmushi, tana mai jin dad'in yadda taga tsowuwar ta fara tsoronta, saboda ta sani shikenan yanzu zata barta ta wala.

Haka dai gaba d'aya yinin yau sukayi sa jiki asab'ule.
Yayinda Iman kuma tini ta tafi gida, wanda hakan ya sanya Ummi ta had'a Gimbiya Tasmir da 'yar aikinsu mai suna Alawiyya, domin ta cigaba da d'ebe mata kewa.

La'asar kuwa tanayi saiga danginsu nan tundaga kan 'yan uwan Ummi har zuwa na Abba suna zuwa, domin su tayasu murna sannan kuma suga Bir.
Hakan kuwa shiya sanyasu sakewa hatta da Gimbiya Tasmir kuwa, sabo da sosai suka dinga janta ajiki duk da fad'a musu kowacece itan da akayi, saboda duk suna ganin itace silar dawowar d'ansu cikin su.


Ab'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa cikin matsanancin bak'in ciki ta shiga cikin motar da sukazo, Shima Buba da driver da gaba d'aya yake a tsorace da abunda ya gani suka shiga, tukun yaja motar suka fara tafiya.

Sosai hawaye ke zuba daga cikin idanuwanta tamkar anbu'de famfo.
Kana tana jin zuciyarta na wani irin rad'ad'i da suya.
Hak'ik'a ranar yau ta kafa babban tarih acikin rayuwarta, irin tarihin da bazai tab'a goguwa ba.
Domin kuwa ta kasance ranar data dad'e tana jiran zuwanta, ranar da take tinanin zata zamto rana mafi muhimmanci da kyawu a cikin ranakun da tayi aduniya, sai kuma gashi tazo mata abai-bai, ta yadda har ta kasance ta bak'inci amai-makon ta zamto ta farinciki, ta kasance mabud'in bud'e ruwan hawayenta amai-makon ta zamto makullin kullesu, ta zama rana mai tsananin duhu da haske dunk'ule a cikinta ama-makon ta zamto zallar haske.
Ko kad'an ko kusa bata tab'a tinanin riskar wannan ranar a yadda ta risketa ba, wai Gid'ad'onta data d'auki tsawon shekara da shekaru tana binciken wurin da yake tare da dokon soyayyarsa, shine tazo ta tarar dashi tare da wata macen, asalima shi ko sanain da zamanta baiyiba aduniya.

"Hak'ik'a bazan tab'a bar miki shi ba, saboda anhallicesa ne domin ni, dan haka zan dawo, kuma zan k'waci abuna daga wurinki kota halink'ak'ane."

Ta fad'a a fili, kana kuma cikin tsananin kuka, ba tare data damu da ba ita kad'ai bace a cikin motar kwata-kwata.

A haka dai har suka isa gida misalin la'asar bata bar zubar hawayen da take ba tare da surutai.


_Washegari_
Yau ce ranar da akasa za'aje nemarwa Yarima Asad auren Gimbiya Haddiyal Masarautar Fuld'e, kuma yauce ranar da mai girma Gwamna suka aiko zasuzo akan batun auren Billy da Asad.

Hakan yasa tun da safe suka tashi da shiri masu tafiyar.
Misalin k'arfe takwas da arba'in na safe suka futo wa'yanda zasuje d'in. Wa'yanda kuma suka had'a da Babban Yaya, wato Ciroma, sai Wambai, tare kuma da Galadima, sai kuma dogaran da zasu tafi tare dasu da kuma direbobin mota.

Motoci Biyu suka d'auka, d'aya Iyayen gayyarne a cikita, yayinda d'ayar kuma take cike da Dogarai, tukun suka fuce daga cikin masarautar wasai suna masu d'aukar hanya.

Sosai Al'amin yake cikin matsanancin farinciki, yayinda Asad kuma gaba d'aya aka rasa gane kansa, domin kuwa ko kad'an babu wani alamun farinciki daya bayyana akan fuskarsa, wanda hakan kuma ya sanya Al'amin ya tambayesa dalili.
Take kuwa ya sanar masa da cewar, bawai gangar jikinta kawai yake son aure ba, asalima so yake ya mallaki zuciyarta, yayinda ko kad'an hakan kuma ya gagara, saboda bazai tab'a iya jurar zama da ita ba hankalinta da tinaninta na wurin waninsa, sabo da idan hakan ta faru tsaf zuciyarsa zata iya bugawa, domin kuwa yana da tsananin kishi akan abun da yakeso tun usul.
Wannan dalilin ma shine ya sanya yau ya tura mutanen dazasu sanya masa ido akan shige da fucen Gimbiya Haddiyal, tare kuma da lura da wanda zaizo wurinta, saboda yana son sanin wanene wannan Gid'ad'on da take fad'i, domin yasan irin matakin da zai d'auka akansa.

Ab'angaren Gimbiya Fulani kuwa sosai take cike da farincikin neman auren da aka tafiyowa d'an nata, na mace da take sa ran itace zata zamto silar canzawarsa, domin kuwa ko yanzuma ta taka babbar rawa acikin rayuwarsa, sai dai kuma a k'asan zuciyarta cike take da fargabar rashin sanin abun da zai faru idan sunje d'in, wanda hakan kuma shine ya sanyata take ta faman addu'oin samun dacewa tun da suka tafi.

Yayinda ab'angaren Gimbiya Huwaila, Gimbiya Amina, Jakadiya tare da duk wasu magautansu suke cike da bak'in ciki da fargaba, saboda ganin da sukayi Asad yana shirin canzawa ta silar yarinyar, wannan dalilinne ya sanya suketa addu'ar Allah yasa kar adace idan sukaje d'in, domin kuwa ba k'aramun farinciki zasuyi ba idan akace zuciyarsa ta buga ya fad'i ya mutun, tamkar yadda ya fad'a.

Misalin k'arfe shabiyu da rabi na rana motocin su mai Girma gwamna suka k'araso cikin masarautar.
Tun daga bakin get Doragai sukazo suka tarbesu har zuwa bakin k'ofar part d'in da mai martaba yake ganawa da bak'insa.

Da sauri escot d'in mai girma gwamna da suke rik'e da uwayen bindigu a hannunsu suka futo daga cikin motocinsu gaba d'ayansu.
Kana mutum biyu suka matsa jikin mayyar motar dasu mai girma Gwamna suke a cikinta, suna masu bud'e murafanta na gidan baya.

Alhaji Saleh da yake sanye da wani d'an ubansu lallausan farin yadi a jikinsa ne ya fara futowa waje.
Yayinda shi kuma mai girma Gwamna ya zuro k'afafunsa da suke sanye da wani mayen bak'in cover shoe mai tsanain kyau da yake d'aukar ido.
Tukun daga bisani ya sako duka gangar jikinsa waje.

Sanye yake da shadda getzner ash color da take wani irin k'yalli da d'aukar ido. Yayinda kansa kuma yake d'auke da wata hula tangaran da taji sak'a da black and ash d'in zare da take wani irin k'yalli.

Ko kad'an babu alamun annuri akan fuskarsa, a haka suka jera shi da amininsa Alhaji Saleh suna masu dosar cikin falon.

Cikin muntuntaka Waziri da yake zaune a falon sanye da alkyabba a jikinsa ya tarbesu.
Yayinda gaban su kuma aka cikasa dank'am da kayan fruite tare da dafaffen naman da yake ta tururi da ruwan sanyi.

Zamansu baifi da minti biyar ba sai ga Mai Martaba nan ya shigo, ta cikin wannan k'ofar da take a cikin falon bakinsa d'auke da sallama.

A wani irin dak'ile mai girma Gwamna ya amsa sallamar, domin kuwa sosai yake jin zafin cin zarafin da d'ansu yayiwa 'yarsa abainar jama'a, wanda har hakan ya sanya gaba d'aya labarin ya cika gari.
Yayinda Alhaji Saleh kuma ya amsa fuskarsa d'auke da murmushi.

Direct mai martaba yayi wurin da suke yana mai mik'a musu hannu sukayi musabaha, tukun ya koma kan kujerar da take facing d'in wacce suke zaune akai da Waziri shima yake zaune akanta ya zauna.

"Bismillah ga abincinan kuci mana sai mu tattauna ko."

Mai Martaba ya fad'a fuska sake yana kallonsu.

"A'a Alhamdulillahi ak'oshe muke, kawai muyi maganar ina ganin zaifi."

Cewar Mai Girma Gwamna yana mai gyara zamansa ya sake fuskantar mai martaba, da alamun dai wannan karan b'acin raima bazai barsa yayi kara ba Alhaji Saleh ya wakilcesa wurin bayani.

"To Bismillah muna jinku."
Waziri ya fad'a yana mai kallonsu.

"Akan maganar da mukazo mukayi abaya ne, yanzu kuma muka sake dawowa, sai dai kuma a wannan karan ba iyakar wannan d'in za'ayi ba."

Alhaji Saleh yayi sauri ya fad'i haka kafun mai girma Gwamna yayi magana.

"Masha Allah muna jinku."
Mai Martaba ya fad'a murya a tausashe.

"Bamu sani ba ko kuma kunji labarin abunda yaron wurinku yayiwa Biliksu, amatsayinta na wacce zata zamto matarsa, wanda ko kad'an kuma hakan da yayi ba kyautawa bane ba, domin kuwa da ace bashi d'in bane bama da bana tinanin zan iya hak'ura na barsa, saboda har siyasata hakan daya aikata yake shirin tab'awa."

Mai Girma Gwamna ya riga Alhaji Saleh da fad'in haka da sauri.

"Subahanallahi! Menene ya faru mu bamu da labari ai."

Mai Martaba ya fad'i haka duk da dai yasan da zancen shima.

Hakan da Mai Girma Gwamna yajine, ya sanyasa zura hannu a cikin aljihunsa yana mai zaro waya a ciki.
Kana ya shiga wurin videos yana mai lalubo vidon abun da ya faru da wani cikin yaransa ya kawo masa.
Tukun ya tab'a play yana mai juyawa su mai martaba fuskar wayar.

Shiru falon ya d'auka, ba ajin komai sai sautin kukan Billy tare da muryar Asad alokacin da yake yiwa Haddiyal magiya.
Yayinda mai Girma Gwamna kuma yake jin zuciyarsa na masa wani irin zafi.

Nannauyan numfashi mai martaba yaja yana mai fesarwa alokacin da videon ya k'are, saboda koshi baiji dad'in ganin abunda ya faru ba kwatakwata.

Shi kuwa Waziri zama ya gyara, yana mai fad'in.

"Gaskiya Asad bai kyautaba ko kad'an, amma hak'uri zakuyi in sha Allah zamuyi masa fad'a hakan bazata sake faruwaba, saboda ko muma hakan bai mana dad'i ba, Yaran yanzu ne kunsan gaba d'aya abun da zuciyarsu ta raya musu shi sukeyi, amma in sha Allah zamuyiwa tufkar hanci."

Jinjina kai mai girma Gwamna yayi, kana ya sake bud'e baki yana mai d'orawa da fad'in.

"Yawwa sai abu na gaba kuma shine, muna son a tsaida ranar bikin domin ayi kawai kowama ya huta."

"To dama muma d'in koda bakuzo ba muna shirin muzo a kwanannan, domin ayi maganar, sai dai kuma kafun wannan shine, shi yaron ya nuna mana cewar biyu yake so yayi a lokaci d'aya, shi yasama har b..."

"Kamarya kuma biyu, shin menene za'ayi biyu alokaci guda Waziri?"
Mai Girma Gwamna ya katse sa da fadin haka cikin sauri.

Hakan yasa Waziri ya sake gyara zama.
Kana ya saukar da murya k'asa yana mai fad'in.

"Kamar yadda muka sani addinin musulunci ya hallatawa ko wane namiji auren mata d'ai-d'ai d'ai-d'ai har guda hud'u idan har zaiyi adalci, to alokacin da kukazo da waccan maganar, da muka sanarwa dashi yaron sai yake shaida mana cewar su biyu yake son ya aura duk a rana d'aya, wato ita Bilkisun da kuma ita wannan Yarinayar d'iyar Sarki Fulani da suka samu sab'ani, yanzu haka ma zancenan da mukeyi antafi ayo maganar ne ayau...."

"Dakata! Dakata Waziri!!."

Cewar mai girma Gwamna da sauri, kana kuma cikin 'yar tsawa ransa a tsananin b'ace.
Tukun daga bisani kuma ya d'ora da fad'in.

"Kana nufin kace mun 'yar tawace zai had'a ya auresu su biyu a rana d'aya tamkar wata mara gata da galihu, wannan wane irin zancene haka mara dad'in ji da yuwuwa kuma?
Shin ma da har kake maganar adalci, ta ina kuke tinanin yaronku zai iya wani adalci, bayan tun kafin a shiga daga ciki yana cin zarafinta, to kusani hakan bazai yuwu ba, saboda bazan lamuntaba, domin kuwa basontane banayi ba da har zaisa inaji ina gani na kaita wurin da zata hulak'anta, dan haka sai dai ya janye auren waccan, saboda bazan iya d'aukar wannan k'ask'ancinba."

"Kaga mai girma Gwamna, wannan fa duk abun bai kai a tada jijiyoyin wuyaba da girman mu, maganace kawai ta sulhu kuma ko a addinance ai hakan bai haramta ba ko?"

Cewar Waziri yana kallonsa.

Yayinda shi kuma mai martaba ma gaba d'aya ya kasa fad'in komai, sai idanu kawai daya zuba masa yana mai mamakin son zuciyarsa da tayi yawa a cikin ransa.

"Babu wannan maganar, har abada bazan tab'a kai 'yata wurin da zata hulak'anta ba, dan haka ni a wurina hakan ba zai yuwuba, dole ne sai dai idan a janye na waccan."

"Idan na fahimta gaba d'aya kana fad'in wa'yannan magan-ganun ne domin farincikin 'yarka ko? To ina son kasani mai girma Gwmana, kamar yadda kakeson 'yarka haka muma mukeson namu d'an, haka kuma muma muke san ganin farincikinsa, wanda hakan shine ya sanya har muka tursasasa akan dole sai dai ya auresu su biyu, saboda shi ya fad'a mana basa soyayya da yarinyar wurinka, kuma bazai iya aurenta ba, to amma saboda girmanka da muke gani shine dalilin daya sanya muka ce masa dole sai ya aureta, adalci d'aya kawai zamu iyayi masa, shine ya samo wadda yakeso ya auresu lokaci guda, kaga idan hakane kenan babu tayyada za'ayi muce masa sai ya hak'ura da wadda yake muradi ya auri zab'in mu har dai muna son farincikinsa muma."

Shima Waziri ya fad'i haka cikin zafi, sabo da yadda yaga mai girma gwamna baso yake su sulhuntaba.

"Okay haka kace ko Waziri, shikenan in sha Allah daga yanzu anbar wannan maganar har abada, sai dai kuma kafun nan inaso kasani kowa yana da ranarsa."

Ya k'arasa maganar cikin zafi yana mai mik'ewa tsaye.
Hakan da Alhaji Saleh ya ganine ya sanya mik'ewa tsaye shima.

Shi kuwa mai Martaba da sauri ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Haba your Exlency bai kamata ace da girman mu mun tsaya shed'an na shirin shiga tsakaninmu ba amatsayin mu na shuwagabanni masu jagorantar al'umma, dan haka dan Allah ku koma ku zauna muyi magana."

"Har abada har dai akan wannan maganarce nagama zama akan kujerar nan Mai Martaba, saboda bazan tab'a kai 'yata wurin da ba'a sonta ba, dan haka sai da anjimanku Alhaji Saleh muyi gaba."

Mai Girma Gwamna ya fad'a yana mai yin gaba.

"To ayi hak'uri fa sai da anjimanku."

Cewar Alhaji Saleh yana mai kallonsu mai martaba, tukun yayi gaba shima.

Shiru sukayi ba tare da sunce komai ba, sai dai kuma shi mai

Please Login or Register in order to submit comment