Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zafinsa ana b'arin nera tamkar basa wahala.
Kuma sosai Billy ta saki ranta ake shan hidima tamkar ba ita bace take cewa bazata iya rayuwa ba idan babu Asad, sai dai kuma duk da haka har yanzu tana jin soyayyarsa a cikin ranta, amma kuma kwata-kwata bata bari Sadik ya gane ba, saboda yadda taga yana mugun nan nan da ita .
Yayinda k'awayenta kuma suketa sakar mata habaici.


****
Tafiyar kwana d'aya da awanni sukayi, tukun suka iso cikin Jahar Wasai.
Cikin matsanancin farinciki Mai Martaba ya nemi wayarsa yana mai kunnata ya kira Babban Yaya, yace a turo motoci su d'ebesu sun dawo.
Wanda hakan kuma yayi matuk'ar bawa duk jama'ar masarautar mamaki, saboda kowa yasan da zummar suyi sati suka je, sai kuma gashi duka cikin 'yan kwanaki sun dawo, amma sai dai kuma ba tare da Babban Yaya ya tsaya jin daliliba ya tura direbobi ciki kuwa har dashi zuwa bakin ruwa.

Cikin k'ank'anin lokaci suka isa bakin ruwa.
Hakan yasa mutanen suka fara futowa suna msu shigewa cikin motocin, cikin matsanancin farinciki.
Shi kuwa Sheikh Ahmad da Bir cikin motar Babban Yaya suka shiga, yayinda Iyalan Sarki Barbaru kuma da jikinsu yake a matuk'ar sanyaye suna kalle-kalle aka zubasu acikin motoci biyu.

Tunda suka tafi Sheikh Ahmad yake bawa Babban Yaya labarin yadda ta kasance.
Jinda Babban Yaya yayi kuwa sunce har da Iyayen Gimbiya Tasmir akazo tare da Iyar Bir, ya sanyasa zaro wayarsa yana mai kiransu Al'amin yace masa suyi maza su tafi gidansu Sheikh Ahmad su kwaso su Ummi gaba d'ayansu.

Kasancewar kuma Babban Zaure bata da nisa da gidan Sarki shiyasa motocin matafiyan na shigowa dasu Yarima Asad da suka d'aukko harda Abba suka shigo suma.
Sai dai kuma gaba d'ayansu a cikin matsananciyar fargaba suke, saboda su Asad dan iskanci k'in fad'a musu abunda ke faruwa sukayi, sai haka kawai dai nemansu akeyi a fada ne.

Kai tsaye suma suka doshi Fada tamkar yadda sukaga motocin sunyi can.

Su kuwa su Mai Martaba suna k'arasawa Fada suka fara furfutowa daga cikin motocinsu.

Da sauri d'aya daga cikin jama'ar da suka dawo tare yaje ya bud'e murafan motocin da Iyayen Gimbiya Tasmir suke aciki yana mai ce musu su futo cikin tsananin girmamawa.
Wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da Gimbiya Tasmir itama ta bud'e murfin mota ta futo, tana sanye da bak'ar abaya a jikinta, sai mayafinta da tayi rolling d'in kanta dashi.

Juyawar da zatayi bayanta kuwa idanuwanta suka sauka akan fuskar yayanta Yarima Sairan.
Wanda hakan kuma shi yayi matuk'ar sanyata cikin tsananin mamaki, sai dai kuma kafun ta gama futa daga wannan mamakin ta sake yin arba da Mahaifiyarta tare kuma da kishiyar mahaifiyarta ta suma sun futo.

Ai kuwa cikin tsananin farinciki mara misaltuwa tayi kansu a guje, ba tare data damu da jama'ar da suke a wurin ba tana mai sakin kuka.
Da sauri suma dukansu suka d'ago idanuwansu suna msau d'orasu akanta.

Lokaci d'aya suma kuwa suka kid'ime suna masu had'uwa suka rungume junansu cikin matsanancin farinciki, gaba d'aya sai suka manta da damuwar da suka tawo da ita dank'are a cikin ransu ma.

Da matuk'ar k'arfi Gimbiya Salwa ta rungumi Gimbiya Tasmir, tana mai fad'in.

"Me yasa kika tafi kika barni d'iyata? Hak''ik'a nayi kuka kuma kullum cikin yinsa nake ta dalilin hakan?"

Sake rungumarta tayi da tsananin k'arfi, suna masu cigaba da sakin kuka.
Kana daga bisani ta saketa tana mai zuwa ta rungume Gimbiya Haiwa, tukun ta saketa itama tana mai bin yayyin nata a layi tai-ta rungumesu, gaba ki d'ayansu cikin matsanancin farinciki.
Tana shirin d'agowane taga Iya itama tsaye tana sakin murmushi.
Ai kuwa da gudu tayi kanta tana sakin dariya tare da fad'awa jikinta tace.

"Wayyo Iyarmu hardake ashe."

Da sauri Bir ya bar jikin Ummi yana mai rik'o hannunta ya matso da ita wurin Iya.
Kana ya janye Gimbiya Tasmir daga jikin Iya yana mai shigewa shi, tukun ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Iyata ga Ummina, Ummina ga Iyata nan mai sona da k'aunata yau ta dawo gareni, hak'ik'a ni d'in na zama d'an gata mai Iyaye da yawa."

Ya k'arasa maganar cikin kuka, yana mai sake rungume Iya a jikinsa.

Ganin da Mai Martaba yayi basu da niyyar dena rungume-rungume da koke-koken da suke yine, ya sanyasa yin gyaran murya, kana yacewa Jakadiya da take tsaye a wurin itama, ta musu rakiya zuwa wani part da yake a kusa da part d'in Mamy, saboda shine babu kowa a cikinsa.

Gaba d'aya kuwa suka had'u harda su Ummi suna masu nufar b'angaren.
Yayinda mamakin irin karamcin jama'ar kuma da rashin k'yamatar talakawansu da nuna isa da izzar da sukaga basayi, tamkar yadda su sukeyi ya cika zuciyarsu.

Shi kuwa Mai Martaba umarni yayiwa jama'ar tasu da shiga cikin fada.
Wanda hakan kuma ya sanya su Babban Yaya ma suka shiga.

Yayinda Bir, Al'amin tare kuma da Yarima Asad suma suka doshi fadar da niyyar shiga.
Sai dai kuma suna gab da k'arasawa ciki Yarima Asad yaji kansa yayi wata irin bala'ya'y'yar sarawa, yayainda jikinsa kuma ya fara karkarwa, gumi na yankomsa.
Hakanne ya sanyasa juyawa baya da matuk'ar sauri, saboda dama rabonsa da shiga ciki tun yana k'arami, wanda daga lokacin rayuwarsu ta koma Dubai sai a yau d'in daya gwada.

Hakanne yasa daga Bir har Al'amin suka juya wurin da yake suna masu kallonsa, amma sai kuma ya girgiza musu kai yana mai musu alamun da bazai iya shiga ciki ba, kana daga bisani ma ya juya duka da sauri yana mai nufar b'angarensu.

Hakan yasa sud'in suka shige ciki.

A cikin kuwa sosai suka yiwa Allah godiya akan nasarar da suka samo, kana Mai Martaba yayiwa Malaman nasu manya manyan kyaututtuka, shi kuwa Sheikh Ahmad ma Sarautar Garkuwar Malaman Wasai ya basa a take a wurin, yayinda aka yanke ranar da za'ayi nad'in biki kuma a matsayin ranar bikin Yarima Asad da Babban yaya ya fad'i lokacin da suka yanke yanzu.

Hakan kuma da Mai Martaba yajine ya sanyasa kallon Bir yana mai shafa kansa, kasancewar a kusa dashi suka zauna shi da Al'amin.
Tukun daga bisani ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kai kuma d'ana albishir d'in da zan maka shine, za'a had'a naku auren kai da taka Gimbiyar a yisa a rana d'aya dana Abokinka, kuma na d'auke nauyin komai tundaga kan lefe, gidan da zaku zauna, kayan d'aki da kuma komai da akeyi na aure ni zan muku shi, sannan kuma akwai babban jari da zan baka, kaima Al'amin zamu tura gidan Iyayen Yarinyar da kake nema kaima a rage ranar bikin, duka za'ayisu a rana gudane, kuma Sheikh Ahmad shine zai d'aura duka auren.

Take kuwa wurin ya d'auki kabbara cikin tsananin farinciki, yayinda Bir da Al'amin kuma sukaji tamkar an musu bushara da gidan Al'janna saboda tsantsar farinciki.
Kana a k'arshe ya sallami kowa shima ya mik'e domin suje su huta.

Cikin matsanancin farinciki Bir da Al'amin suka k'arasa d'akin Asad.
Zaune suka samesa akan kujera ya zuba tagumi yana mai tunanin irin tarbar da Gimbiya Haddiyal zatayi masa a gobe idan yaje.
A haka sukazo suka samesa suna masu basa labarin abun da yake faruwa.
Sosai kuwa shima yayi matuk'ar farinciki da jin hakan.
Kana Al'amin ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kun sanme zai faru, jibi zamuje muyo siyayyar kayan da za musa na free weeding pics, in yaso idan kaje wurin Gimbiya gobe sai ka fad'a mata, gata kuma sai muje ayi mana."

"To Malam idan kai baka da kishi ni ina dashi, dan haka babu gardin banzan da zan watsawa hotunan matata ya dinga yi mata kallon k'urilla yana zooming d'inta, kuma ma ai Yaya Sheikh yace mana duk hakan babu kyau ko ka mantane?"

Cewar Yarima Asad yana mai hararar Al'amin.

"A gaskiyane wallahi da gaske Asad ya musulunta sosai."

Al'amin ya fad'a yana mai kwashewa da dariya.

Shima Bir dariyar ya kwashe da ita, yana mai fad'in.

"To yanzu dai abunda za'ayi shine, ku taso muje mu gaishe da iyayen Gimbiyata, sannan kuma mu fad'a mata ranar bikin Ummina ma suna can, yawwa kuma kuga Iyata ma."

Mik'ewa tsayen sukayi gaba d'ayansu kuwa, shi Bir da akace suje su huta amma da alamu ko gajiyar ma babu a tattare dashi shi.

Zazzaune suka samu mutanen a cikin k'aton falon hardasu Gimbiya Fulani da su Ummi, Kaka da duk wasu mutane masu kirki na cikin Masarautar an jibgewa ahalinsu Gimbiya Tasmir abinci kala-kala anata nan nan dasu.
Yayinda su kuma gaba d'aga mamakin yadda jama'ar suke yayi matuk'ar kamasu, tare kuma da birgesu, saboda ganin da sukayi ko kad'an babu hulak'anci a tattare da su.

Ita kuwa Iyar Bayi tamkar Ummi zata goyata haka taketa tambayarta me takeso duk motsin da tayi.

Kaka kuwa kusa da ita ta zauna tana mai fad'in.

"Ai nima fa na samu k'awa yanzu, dan haka tare dake zamu koma ki zauna a d'akina, nasan kema tsaf zaki musulunta."
Yayinda Gimbiya Tasmir kuma take manne a jikin Mamanta.
A haka su Bir suka shigo cikin d'akin bakinsu d'auke da sallama.

Da sauri ya huce wurin iya yana mai zama tare da kwanciya a jikinta ko kunyar jama'ar da suke a wurin baiji ba .
Yayinda su kuma su Yarima Asad suka durk'usa a wurin suna masu gaishe dasu tare da yi musu barka da zuwa.
Tukun bayan sun amsa kuma suka juya wurin Yarima Sairan da suka gansa yayi jugum abun gwanin ban tausayi yake, Al'amin yana mai dafasa tare da fad'in sannuko Aboki.
Kasancewar shima d'in bazai huce sa'ansu ba a shekaru.
Murmushi shima kuwa yayi musu, yana mai jin dad'in ganin sun kulasa a cikin ransa.

Shi kuwa Bir da yake manne ajikin Iya a hankali ya d'ago kansa, yana mai kai bakinsa saitin kunnenta, tukun ya rad'a mata abunda Mai Martaba yace.
Ai kuwa bazato ba tsammani jama'ar cikin falon sukaji ta rangad'a wata uwar bud'a mai tsananin k'arfi.
Hakanne yasa gaba d'ayansu suka kai idanuwansu wurinta.

Shi kuwa Bir da sauri ya b'oye kansa a cikin jikinta.
Yayinda ita kuma ta fara shaida musu ranar auren Gimbiya da Jarumin nata da aka tsayar a yau.

Da sauri Ummi kuwa ta mik'a hannu tana rank'washin Bir tare da fad'in.

"Mara kunya kawai."

Hakan da yajine ya sanya sa mik'ewa da sauri, yana mai sahshshake fuska ya fuce daga cikin falon.
Yayinda Gimbiya Tasmir kuma ta b'oye kanta ajikin mahaifiyarta tana mai sakin murmushin farinciki itama.

Su kuwa Iyayenta cikin tsananin jin dad'i suma suketa sakin far'a.
Saboda ba k'aramun farinciki sukayi ba da ganin yadda 'yar tasu take lafiya k'alau tamkar tana a gabansu.

Gimbiya Fulanice ta kalli su Yarima Asad tana mai fad'in.

"Yawwa ku kaisa d'akinsa yayi wanka ya huta, kunsan sun kwaso hanya tunda ya gama cin abincin."

"Tom." Suka amsa mata da shi suna masu mik'ewa su duka ukkun suka doshi wani corridor da yake a cikin falon.
Yayinda suma Iyayen Gimbiya da sauran yayyinta duk aka nuna musu makwancinsu.
Kana a k'arshe Ummi tacewa Gimbiya ta tawo su tafi gida amma tak'iya.

Ita kuwa Kaka haka tacewa Iya dole saita tawo sun tafi tare.
Babu kuwa yadda ta iya haka ta tawo suka tafi, ita kuma Gimbiya suka barta da zummar gobe zasu dawo.

A b'angaren Sheikh Ahmad kuwa, yana komawa gida yayi wanka, tukun ya kwanta bacci kafin la'asar tayi.

Shi kuwa Bir ba shine ya dawo gida ba sai bayan magariba, suka tawo tare dasu Asad harma da Yarima Sairan daya sake a cikinsu tamkar dama sun san juna.

Suna zuwa kuwa Sheikh Ahmad ya tsaresu yace suzo yanzu zasu fara karatu akan mu'amalar aure a addinance, kafun lokaci yayi tunda dai yasan basu san komai ba.
Haka kuwa akayi Yarima Sairan ya zauna a gefe, su kuma suka hau kan shimfid'a sukai da'ira, Sheikh Ahmad ya fara basu karatu.
Tukun ak'arshe bayan an gama sunyi sallahr isha'i tare da cin abinci, sannan su Yarima Asad suka tafi su ukku, shi kuma Bir ya shige cikin gida yana mai hucewa d'akinsu kai tsaye domin ya kwanta.

WASHEGARI.

Sosai Gimbiya Tasmir tayi matuk'ar birge Iyayenta alokacin da sukaga tana sallah tare da karatu.
Haka kuma bayan ta idar da sallahr asubama tasa Baby data tawo wurinta suka kwana tare ta k'ara yi mata k'ari a cikin karaun Al'qur ani.
Kuma Alhamdulillah yanuzu har bak'i ta fara iyawa daga ita har Bir, saboda ba k'aramun mayar da hankali sukayi ba wurin koyon karatun.

A b'angaren Yarima Asad kuwa misalin k'arfe takwas na safe ya gama shirywa tsaf, cikin shigar manyan kayan da sukayi bala'in amsar jikinsa, kuma tare dayi masa kyau, tukun bayan yaje ya gaishe da Mamy ya huce zuwa cikin motarsa yana mai hawa ya d'au hanyar Masarautar Fuld'e.

Misalin k'arfe shabiyu na rana ya isa kuwa.
Sosai ya samu tarbar mutunci wurin Mahaifan Gimbiya Haddiyal tare da Yayyanta.

A cikin wani d'an k'aramin lambu da yake cike da had'ad'd'un furanni masu matuk'ar k'amshi da sanyi aka saukesa.
Tukun cikin d'an k'ank'anin lokaci aka cika masa gabansa da kayan abinci kala-kala.

Fura kad'ai ya iya sha, tukun ya koma ya kishingid'a akan tum-tum.

Kishingid'ar tasa ke da wuya kuwa ya hango b'ullowar Gimbiya Haddiyal kanta durk'ushe a k'asa zuwa cikin wurin.
Lokaci d'aya yaji gabansa yayi wata irin mahaukaciyar bugawa, kana fargabar rashin sanin irin tarbar da zatayi masa a yau ta lullub'esa gaba d'aya.

A hankali ya tashi zaune yana mai lumshe idanuwansa.
Yayinda ita kuma take cigaba da tawowa jikinta a matuk'ar sanyaye.

Sanye take da blue d'in kayan fulani da sukayi bala'in yi mata kyau.
Sai dai kuma daga nan wurin da take ya gane muguwar ramar da tayi ta k'asan idon da yake kallonta.

Fesar da numfashi yayi yana mai lumshe ido, tare da jin duk ransa ba dad'i, saboda sanin da yayi na duk wannan ramar tayi ta ne ta dalilin aura masa ita da ake shirinyi.

A kuma dai-dai lokacin ta k'araso wurin tana mai yin sallama acan k'asan mak'oshinta.
Wanda hakanne kuma ya sanya kwata-kwata Asad baiji sautin sallamar tata ba.
Tukun ta nemi wuri ta zauna tana mai tank'washe k'afafuwanta, tare da sake durk'usar da kai har yanzu batace komai ba.

Hakan da Yarima Asad ya ganine, ya sanyasa gyara zamansa a wurin da yake, yana mai fuskantar ta.
Tukun daga bisani kuma ya bud'e baki cikin sanyi, tare da raunin murya, yana mai fad'in.

"Kiyi hak'uri dan Allah, ba burina bane na ganki a cikin bak'in ciki, asalima ahalin yanzu nafi buk'atar farincikinki sama da komai a duniya, amma sai dai kuma ba..."

Ya kasa k'arasa maganar, saboda yadda muryrasa tayi matuk'ar rauni, kuka yake shirin k'wace masa.

Jin da Gimbiya Haddiyal tayi tamkar yana kukane, yasa taji jikinta ya k'ara yin bala'in sanyi, wani abu mai kama da tausayinsa na ratsa ko wane lungu da sak'o na jikinta.
Sai dai kuma duk da haka bata iya furta masa komai ba.

Hakan da Yarima Asad ya jine ya sanyasa k'ara fuskantarta sosai, tukun a hankali, kana kuma cikin sanyi tamkar mai jin tsoro, ya mik'a lallausan tafin hannunsa yana mai kifesa akan goshinta.
Tukun ya d'ago da kanta yana mai watsa jik'ak'k'un idanuwansa da hawaye suka fara zubowa daga cikinsu cikin nata da suka jima da fara ambaliya ma su.
Hakan yasa suka kafe junansu da idanun, ba tare da tayi k'ok'arin cewa ya dena tab'ata ba tamkar yadda ta saba abaya.
Kafin daga bisani kuma Yarima Asad ya bud'e baki, cikin wata irin murya data ratsa gaba d'aya ilahirin jikinta, kana ta daki zuciyarta, yana mai fad'in.

"Ki yadda da soyayyar da nake miki, hak'ik'a soyayyace ta gaskiya, kuma nayi miki alk'warin sanyaki cikin farinciki irin wanda baki tab'a mafarkin samunsa ba a wurin wani d'a namiji, saboda ina miki sone irin son da baki bazai iya furtasa ba. Hak'ik'a ke d'in kin huce rabin raina tamkar yadda wasu suke fad'e, ni sai dai na kiraki da karankaf raina d'in Gimbiya, dan Allah nima ki taimaka ki soni ko yayane, idan ma kuma bazaki soni ba, to ki dena nuna mun k'iyayyar da kike nuna mun, saboda hakan na matuk'ar azabtar da zuciyata."

Da sauri ta lumshe idanuwanta, saboda jin da tayi bazata iya jurar kallon cikin k'wayar idanuwansa ba, ba tare da tace masa komai ba, sai zallar shashshekar kuka kawai da take saki.
Hakan da Yarima Asad ya ganine ya sanyasa yin sauri ya sakar mata goshi, saboda shi duk a tinaninsa ko taji haushine.
Kana ya sake bud'e baki cikin sauri da kuma sanyi yana mai fad'in.

"Kiyi hak'uri, mantawa nake yi, amma in sha Allah bazan k'ara tab'aki ba tunda bakyaso."

Shiru tayi dai ba tare da tace masa komai d'inba har yanzu, sai dai kuma ba k'aramun sanyi taji jikinta yayiba, ta yadda har take jin inama ace zata iya bud'e baki tace masa tana sonsa ko da wasane da tayi, sai dai kuma bazata iyaba, tana tinanin ma har abada bazata sake iya furta wannan kalmar ba, wato dai ta gama fad'arta akan Gid'ad'o da yak'ita, godiyar Allah'nta d'aya a yanzu, itama, shine fara yakicesa daga cikin ranta ta silar adduo'in data dage tanayi.

A hankali Yarima Asad ya sake bud'e baki, bayan ya goge hawayen idanuwansa yana mai fad'in.

"Me dame za'ayi a bikin, kuma nawane kuke buk'ata da zasu isheku?"

Shiru tayi tamkar ba zatace komai ba, domin kuwa shi harma ya futar da tsammanin zatayi maganar ma gaba d'aya, sai kuma can ya tsinkayo muryarta a matuk'ar sanyaye, tana mai fad'in.

"Bama buk'atar komai, Hamma Habu kuma zai fad'a maka abubuwan da akeyi na bikin."

Da sauri ya lumshe idanuwansa, yana mai jin wani irin matsanancin farinciki na lullub'esa, tare da jin ranar yau d'in ta k'ara shiga cikin ranakun da bazai tab'a mantawa da suba a rayuwarsa, saboda yau d'in itace rana ta farko da Gimbiya Haddiyal tayi masa magana cikin sanyi, sannan kuma mai dad'i, kana kuma ta zauna a kusa dashi har na tsawon mintina goma, ba tare da tayi ko alamun tafiya ba.
Hak'ika ko yanzu yayi nasara.
Hakanne ya sanyasa bud'e baki, cikin tsananin farincikinsa da ya gaza b'oyuwa, yana mai fad'in.

"A'a Gimbiyata, ninake da alhakin bada kud'in komai basu Baffa ba, dan haka ga wannan, idan basu isaba dan Allah ki fad'a mun sai na k'aro miki wasu kinji ko."

Ya k'arasa maganar yana mai mik'a mata wata 'yar k'aramar jaka daya cikota da kud'i kimanin 1 million naira, ya d'ora mata akan cinya.

Ba tare da tace komaiba kuma tasa hannu ta d'auka, kana ta mik'e tsaye tana mai sanya takalmanta a k'afa.
Tukun ba zato ba tsammani kuma Yarima Asad da yake aikin kallonta yaji sautin sassanyar muryarta tana mai fad'in.

"Ka gaida gida."

Sannan ta juya cikin sanyi tana mai tafiya, kuma hakan duk ya farune ta sanadin wa'azin Sheikh Ahmad daya zauna a cikin k'wak'walwarta.

Shi kuwa Yarima Asad da ido ya bita tamkar ya samu tv, cikin wani irin yanayi na matsanancin farinciki.

"Yesssssss Alhamdulillah!!!"

Ya fad'a da k'arfi yana mai dunk'ule hannunsa, tare da jinsa cikin matsanancin farinciki.
Tukun shima ya mik'e da sauri yana mai tafiya, domin yaje suyi sallama dasu Habu, sannan kuma yaji tsarin yadda abubuwan bikin suke.

Gaba d'aya ji yake tamkar yayi firfiluwa ya gansa a gida ya bawa su Al'amin labarin abun da ya faru yau, saboda tsananin farincikin da yake a ciki............✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*31*



Tas Habu ya karanto masa kalar events d'in da sukeyi na aure, kana kuma ya shaida masa da cewar jibi ne ranar da za'a fara.
Sannan a k'arshe kuma ya fad'a masa irin kayan da ake sanyawa a kowace rana, tare da wurin da ake siyar dasu, tukun ya shiga cikin motarsa cikin matsanancin farinciki yana mai d'aukar hanya.

Acan b'angarensu Gimbiya Tasmir kuwa, yau ne Mahaifiyarta take fad'a mata duk yadda abun ya faru, har mutuwar da Yarima Sauman yayi tare da kuma Sarki Barbaru, sai dai kuma kasancewar suma basu san wanda ya kashe suba a cikin mutanen, shiyasa basuce mata gashi ba.
Sosai kuwa tayi kuka mai matuk'ar ban tausayi, tukun a k'arshe tayi shiru tana mai jin tausayin irin azabar da zasu had'u da ita a wurin Allah.
Ko da Bir yazo kuwa ya taddata tana kukanne, hakanne ya sanyasa janta suka futa waje sun masu tafiya wurin da babu mutane, yay ta aikin rarrashinta yana mai bata hak'uri.
Kasancewar kuma batasan shine ya kashesu ba shiyasa cikin k'ank'anin lokaci ya shaho kanta suka fara soyewarsu, yana mai fad'a mata irin tattalin da zai mata idan sunyi aure.

A haka kuma Al'amin da kuma Yarima Asad da yadawo harma da Yarima Sairan suka k'araso wurin.

"Kai aboki taso kaji yau akwai labari wallahi. Munyi soyayya da Gimbiya nima."

Yarima Asad ya fad'a cikin matsanancin farinciki, yana mai kamo hannunsa.
Hakan da yajine ya sanyasa mik'ewa tsaye yana mai sakin dariya, tare da tsokanarsa da basaban ba suka ja gefe.
Tukun ya zayyano masa duk yadda sukai da Haddiyal d'insa.
Sosai kuwa Bir ya tayasa farinciki, tare da yi masa fatan Allah yasa idan ya koma tace masa tana sonsa.
Tukun Bir ya raka Gimbiya har cikin gida wurinsu Ummi da suka zo, shi kuma ya futo suka fuce su hud'u domin su fara shiryawa.

Washegari.

Yau aka tashi da matsanancin farinciki a cikin Masarautar Wasai, saboda dangin Gimbiya Tasmir da suka samu Fulani da zancen suma suna son shiga musulunci.
Hakanne kuwa ya sanya aka kira Sheikh Ahmad a waya aka sanar dashi.
Ai kuwa tsabar farinciki daya tashi tawowa ma harsu Ummi biyosa sukayi.

Tukun da yazo aka basu kalmar shahada tare da karanta musu hukunce-hukucen musulunci.
Sannan kuma ko wanne ya zab'i sunan da yake so.
Subahanallah, zo kuga yadda suka ga soyayya a wurin jama'ar cikin Masarauta Wasai tamkar zasu goyasu tsabar farinciki.
Hakanne yasa bayan an gama komai Sheikh Ahmad ya samu mai Martaba da zancen yana son ya nemi alfarma, ya samu ayi duka d'aurin auren a cikin Masallacin masarautar wasai, harna Haddiyal da kuma budurwar Al'amin, saboda yanaso a hud'ubar da zaiyi a ranar yayi ta akan Shugabancine, kasancewar ranar juma'a ce ranar data kama za'ayi d'aurin auren.

Sosai kuwa Mai Martaba yaji dad'in hakan kamar me, kana kuma yace in sha Allahu a yau duk zai aika musu babu damuwa yasan zasu amince.
Haka suka rabu cikin matsanancin farinciki mara misaltuwa.

Washegari kuma itace ranar da za'a fara gudanar da shagalin bikinsu Yarima Asad a cikin masarautar Fuld'e.
Hakanne kuma yasa 'Yammatan masarautar wasai irinsu Baby suketa shiryawa tunda safe, domin su tafi, kasancewar kuma ba yau zasu dawoba idan sunje shiyasa suka d'ebi kaya da yawa.
Babu yadda basuyi da Gimbiya Tasmir akan ta shirya su tafi tare ba tace a'a ita tana nan.
Haka a b'angaren Bir ma Al'amin ya dage akan ya shirya su tafi, amma yace babu inda zasa, suje idan bikin ya dawo nan ayi komai dashi.
Haka kuwa suka rabu da shi, sai dai kuma yasa kayan fulani tamkar yadda suka sanya sukai hotuna dashi anan cikin gidan.
Tukun suka fuce harda Yarima Sairan daya saje dasu sak cikin shigarsu ta kayan fulani.
Sosai Asad yayi bala'in kyau a cikin shigar da yake yiwa kallon ta mahaukata, wato dai shima yau ya dawo mahaukaci ta sanadin soyayya.

Kallo d'aya mutum zai masa ya gane yana cikin matsanacin farinciki mara misaltuwa.
Tukun suka shige cikin mota suna masu bata huta suka d'au hanya.

Acan Masarautar Fuld'e kuwa, sosai shagali ya kankama, domin kuwa tun daga bakin masarautar mutum zai fahinci yau d'in ana gagarumin bikine a cikinta.

A b'angaren Gimbiya Haddiyal kuwa, zaune take akan wata had'ad'd'iyar kujera, wasu 'yammata guda biyu na zuba mata kwalliya irin ta fulani.
Wato dai aka shafa mata bak'in baki akan kyawwan lips d'inta, kana aka yi mata 'yan d'igun-guna da kwalli akan goshinta, da cikin idanuwanta, yayinda gashin kanta kuma akayi masa wani irin style da yay bala'in kyau.
Sanye take da riga da zani jajaye masu adon blue da baki ajikinsu, na fulani da sukayi bala'in yi mata kyau.
Yayinda tafukan k'afarta kuma suke sanye da wani takalmin fata mara tudu mai tsananin kyau da d'aukar hankali.

Wani irin jan k'unshine akan tafin k'afuwanta da yayi azabar yi mata kyau.
Sai dai kuma kallo d'aya mutum zai mata ya gane tana tare da damuwa, domin kuwa duk hirar dasu Baby da sukazo tun d'azu har sun shirya yanzu tare da k'awayenta sukeyi batacewa komai ba, sai murmushin da take ta saki kawai.

Misalin k'arfe hud'u aka fara shagali.
Cikin wani irin taku na musamman Gimbiya Haddiyal da Yarima Asad suka fara takowa ajera zuwa cikin filin da ake kid'a da rawa.
Banda murmushi babu abun da Yarima Asad yake saki, yayinda ita kuma Gimbiya Haddiyal take ta yak'e hannunta rumtse acikin nasa.
Zuwa yanzu kwata-kwata batajin tsanarsa a cikin ranta, haka kuma batajin sonsa ko kad'an, sai dai tausayinsa.
Sosai sukayi matuk'ar dacewa da juna.
Hakanne

Please Login or Register in order to submit comment