Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki, sannan ya futo sanye da bathrobe a jikin sa, yayinda kansa kuma keta ɗigar ruwa.

Direct ya doshi gaban wadrobe ɗin sa, yana mai zuwa ya buɗe wurin da kayan baccin sa suke.
Kana ya zaro wasu tausasan riga da wando masu ɗan santsi, yana mai fara sanya su a jikin sa ba tare da ya shafa mai ba tamkar yadda ya saba.

Wucewa yayi zuwa wurin da sallahyar sa take shimfiɗe, yana mai hawa kai ya tayar da sallah.

A daddafe yayi sallahr, sabo da yadda kansa ke ƙara rikicewa, ta yada har yake jin idanuwansa sun masa wani irin nauyi tamkar waƴan da aka ɗora duwatsuna a cikin su.

Cikin cizon leɓe ya tashi daga kan prayer mat ɗin, yana mai nufar kan gadon sa.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya haye saman sa yana mai janyo eskimo ya lulluɓe jikin sa da shi, domin kuwa ita kanta addu'ar da Babban Yaya yace yayi ta, sai da ƙyar ya iya fara karanto ta daga cikin bargon.

Babu abun da yake fatan yi a yanzu face bacci, ko Allah zai sa ya samu sauƙin damuwar da take cunkushe a ƙasan zuciyar sa.


*ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.*

Ba'a tashi daga wurin taron bikin nan ba har sai da gari ya fara duhu, wato dai magariba ta gabato, tukun gaba ɗaya kowa ya fara watsewa.
Suma gaba ɗaya Bayi ɓangaren su sukayi, kallo ɗaya mutum zai musu ya fahimci ba ƙaramar jigata sukayi ba, duba da yadda dukan su suke tafiya lahai-lahai daga mazansu har matan su, manyan sune kawai suke da kuzari a jikin su.

Ita kuwa Iyar Bayi tafi kowa sauri, domin kuwa hakalin ta ba ƙaramun tashi ya sake yi ba da taga har an tashi daga wurin biki Bir da Gimbiya basu dawo ba, hakan ne yasa ta gane cewar Gimbiya Tasmir ta riƙe Bir ɗin kenan.
Fatan ta ɗaya a yanzu shine kar Allah yasa ɗakin Azaba ta sake mayar da shi, domin kuwa duk da bata taɓa shiga ɗakin ba sun sha jin labarin sa tun suna yara, kana kuma sun san duk wanda kaga ansa sa a ɗakin to baƙaramun laifi ya aikata ba, kuma ba kowane yake shiga cikin sa ya futo da rai ba.
Wannan dalilin ya sanya gaba ɗaya hankalin ta yaƙi kwanciya.

A bayan ta kuwa su Mauzum ne biye da ita, suma gaba ɗayan su kallo ɗaya zaka musu ka fahimci irin halin da suke ciki, sabo da kusan akan idanuwansu komai ya faru.

"Wayyo Allah na na shiga ukku na lalace, wayyo Ubangiji Gargabilu ka kawo mun ɗauki.
Jarumi! Jarumi!! Jarumi!!!"

Iyar bayi ta ƙwala wata irin gigitattar ƙara a lokacin da ta shawo kwana, saboda idanuwanta da suka hango mata Bir yashe a gefe, babu alamun numfashi tattare da shi.

Da sauri ta cake guiwoyinta a ƙasa a lokacin da ta ƙaraso gaban Bir, tana mai ɗora hannuwanta aka.
Yayinda sauran jama'ar tasu ma suka danno a guje zuwa wurin, saboda ihun iyar bayi da yayi matuƙar rikita su.

Ita kuwa Iyar Bayi hannuwanta da suke akan kanta ta sauke ƙasa, tana mai sauke su akan lallausar sumar kan Bir da gaba ɗaya tabi ta ɓaci da jini da ƙasa.
Kana daga bisani ta cigaba da kiran sunan sa cikin tsantsar ruɗu, tana mai girgiza sa.

Ganin da tayi har lokacin babu alamun motsi tattare da shine, ya sanya ƙirjin ta ya sake yin wata irin mahaukaciyar bugawa.
Kana ta durƙusar da kanta ƙasa tana mai kai kunnen ta dai-dai saitin zuciyar sa.

Dip-Dip-Dip.

Haka taji sautin bugun zuciyar sa na tashi kaɗan-kaɗan.
Hakanne yasa ta ɗagowa tana mai fesar da wani irin zazzafan numfashi.
Kana ta juya ɓarin da Mauzum yake yana zubar da ƙwalla shima, tana mai faɗin.

"Yi maza maza kaje ka haɗo mun magani acikin ɗaki ka kawo munshi yanzu-yanzu."

Da gudu kuwa Mauzum ya juya yana mai kama hanyar ɗakin Iyar Bayi, yayinda ita kuma ta sake ɗago kan Bir tana mai ɗorasa akan cinyarta, wasu irin hawaye masu tsantsar zafi na futa daga cikin idanuwan nata da matuƙar gudu.
Fatan ta ɗaya shine kar Bir ya mutu, domin kuwa idan ya mutu bata san inda zata sanya ranta ba, sabo da ba ƙaramun so take yi masa ba.

Cikin ƙanƙanin lokaci Mauzum ya dawo wurin hannuwan sa rungume da ƙwarya tare da k'ullin ledoji.

Gaban Iyar Bayi ya ajiye su yana mai durƙusawa a wurin shima.

Ita kuwa Iyar Bayi cikin tsantsar sauri ta fara haɗa iccinan magun-gunan da suka sha hade-hade kala-kala, domin kuwa har da su gishiri a cikin su.

Fara ɗibar ruwan tayi tana mai zubasa a jikin Bir.

Wata irin ƙaƙƙarfar a jiyar zuciya ya sauke, yana mai fara bude idanuwansa da yake jin sun masa wani irin bala'in nauyi a hankali, har ya buɗe su duka a kan iyar Bayi.

Da sauri ya sake mayar da su, yana mai rufe su tare da cizon leɓen sa na ƙasa, saboda yadda yake jin ko ina na ilahirin jikin sa na wata irin kwankwatsa, ga wani irin azababben zazzaɓi da gaba ɗaya ya lulluɓe sa.

Ita kuwa Iyar Bayi lokaci ɗaya ta saki murmushi, hawaye na futowa daga cikin idanuwanta, saboda ganin da tayi Bir ya buɗe idanun sa.
Kana ta cigaba da watsa masa ruwan nan tana mai faɗin.

"Akan me akan me kake son ka kashe kanka da kanka Jarumi? Shin me yasa baka jin magana ne? Me yasa baka gudun wahalar da rayuwar ka? Me yasa bazaka futa daga harkar Gimbiya ba ko domin ka huta nima na huta."

Iyar bayi tace cikin wani irin kuka, saboda yadda take sake ganin ciwuka na bayyana a jikin Bir.

"Hak'iƙa zuciya da ruhina suna jigatuwa a duk lokacin da zan ganka a cikin mawuyacin hali Jarumi, raina na sosuwa, ta yadda har nake jin inama ace wahalar zata dawo kai na, amma me yasa bazaka temaki kanka ba, sannan nima ka taimake ni ka haƙura da shiga harkar Gimbiya.
Shin wai tunda kuka fara haɗuwa da ita wata irin nasara ka taɓa samu ma? Me ka ƙaru da shi bayan wahala.
Na roƙe da abun bauta Gargabilu Jarumi karka ƙara kusantar Gimbiya, kana ko idanuwanka bana son daga yau ka ƙara barinsu su haɗu da nata.
Alfarma ce nake nema a wurin ka Albarkacin Ubangiji Gargabilu ba dan ni ba Jarumi na."

Ta ƙarashe maganar cikin wani irin matsanancin kuka, yayinda jikin ta kuma ke wata irin karkarwa.

Shi kuwa Bir da ƙarfi ya sake rumtse idanuwansa, sabo da yadda yake jin kalaman Iyar bayi na dukan kunnuwansa, ga kuma yadda zuciyar sa ke cigaba da hasko masa fuskar Gimbiya Tasmir tare da komai nata ma, wanda hakan yasa yake jin tamkar Iyar Bayi ta ɗauki huƙa ta daba masa ne da abun da take cewa yayin, sai dai kuma ya ƙudiri aniyar gwada yin hakan ko domin farin cikin ta, duk da dai shi ɗin kuma ya riga da yasan ba ƙaramar cutuwa zaiyi ba.

Ɗan jujjya kansa ya farayi, yana mai san ya ɗago tafin hannun sa ya riƙe na iya domin ya lallashe ta, amma gaba ɗaya yaji ya kasa, saboda yadda yake jin duk jikin sa a mugun ɗaɗɗaure.
Hakan yasa dole ya haƙura yana mai sake kwantar da kansa akan cinyar Iyar Bayi idanuwansa a lumshe.

Sun ɗauki dogon lokaci a wurin, kafin iya ta gama shafe Bir da duka magun-gunan, kana ta basa nasha ya sha ta hanyar kansa da su Mauzum suka ɗago mata ita kuma ta ɗora masa kofin akan baki.
Sannan aƙkarshe ta sanya su Mauzum suka ɗauke sa sukayi ɗakin su da shi, domin ya huta a lokacin tini dare ya fara yin nisa.

Acan ɓangaren Gimbiya Tasmir kuwa ko da ta kwanta ta rufa a cikin bargon gaba ɗaya kasa yin baccin tayi, sai faman rawar sanyi kawai da take tayi, saboda azababben zazzaɓin da ya rufe ta.
Zuwa yanzu ko idanuwanta bata iya ɗagawa, amma duk da hakan-hakan bai sanyata ta manta da abun da Bir yayi mata ba, asalima ganin abun take a cikin idanuwanta tamkar yanzu yake kan faruwa, wanda hakan kuma shike ƙara rura wutar ciwon nata.

Acan ɓangaren Iyayen ta kuwa basu lura da bata filin biki ba har sai da aka kusa tashi.
Hakan ne yasa koda suka dawo cikin gidan kai tsaye Mahaifiyar ta Gimbiya Salwa tayo cikin ɗakin ta, domin taji abun da yasa ta bar filin bikin.
Yayinda shi kuma Sarki Barbaru yace ace tazo yana nemanta.

Tsaye tayi ƙam daga bakin ƙofar ɗakin, ƙirjin ta na wani irin harbawa da matuƙar ƙarfi, sabo da yadda ta hangi ƴarta ta ƙudundune a cikin tafkeken bargo a irin wannan lokacin, ga kuma yadda taga tana karkarwa, ta yadda har take jiyo sautin haɗuwar haƙwaranta daga nan wurin da take a tsaye, hakan ne yasa ta fahimtar bata da lafiya kenan.

Ai kuwa cikin tsantsar ruɗu da tashin hankali ta doshi bakin gadon, tana mai faɗin.
"Meke faruwa ne, mene ne ya same ki?"
Ta ƙarasa maganar a tsantsar ruɗe, tana mai hayewa saman gadon.
Kana ta miƙa hannun ta ɗaya tana mai yaye bargon da Gimbiya Tasmir ta rufa da shi.

Da azabar sauri, kana kuma hankali a tsantsar tashe ta saki bargon, tana mai zaro idanuwa, sabo da yadda taga f.................✍


*BAƘAR MASARUTA*

_BOOK 2_



UMAR FARUQ*D*



*03*



Fuskarta tayi wani irin ja, ga kuma idanuwanta da sukayi matuƙar ƙanƙancewa.
Kana tana jan wani irin numfashi da ƙarfi, wanda shi kaɗai ya isa yasa mutum ya fahimci irin wahalar da take sha.

"Na shiga ukku Tasmir! Tasmir!! Tasmir me ya same ki."
Mahafiyarta ta faɗa hankali a tsantsar tashe, tana mai sake mayar da hannuwanta kan jikin ta.
"Buɗe idanuwanki ki mun bayani abun da ke faruwa"
Ta ƙara faɗe cikin wata irin murya tana mai cigaba da shafa jikin ta da take jin sa tamkar wuta.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir sama-sama take jiyo sautin muryar mahaifiyarta ta, so take ta buɗe idanuwanta domin tayi mata magana, amma gaba ɗaya taji ta kasa, sai wasu irin hawaye da take jin suna cigaba da ambaliya daga cikin idanuwanta suna gangarawa gefen kunnuwanta.

Ganin hakan da Gimbiya Salwa tayi ne ya sanya ta miƙewa tsaye zumbur, tana mai sauka daga kan gadon.

Zame alkyabbar dake sanye a jikin ta tayi, tana mai cilli da ita gefe, sannan ta doshi bakin ƙofar futa daga cikin ɗakin gadan-gadan.

Ko da ta fuce falon kai tsaye ta doshi hanyar da zata kaita ɓangaren Sarki Barbaru hankalinta a tsantsar tashe.

Anan wurin Gimbiya Tasmir kuwa sosai take jin jiki, tunda take a rayuwar ta bata taɓa ciwo mai zafin na yau ba, hakan yasa gaba ɗaya tayi mugun laushi.

Tana cikin wannan yanayin Sarki Barbaru ya afko cikin ɗakin nata a matuƙar ruɗe, yayin da Gimbiya Salwa kuma take biye da shi a baya.
Ba tare daya tsaya ko cire takalman da suke sanye a ƙafar sa ba ya haye saman gadon.
Kana cikin sauri yakai hannuwan sa kan bargon da Gimbiya Tasmir ta lulluɓa da shi yana mai janye sa gefe.

"Ƴata! Ƴata!!"
Ya faɗa a wani irin rikece, yana mai janyo ta jikin sa, kasancewar da hakan yake kiranta dama.

Dasauri ya juya ɓarin da Gimbiya Salwa take a tsaye yana mai faɗin.
"Kiyi maza-maza ki futa ki tawo mun da likita, mintina ukku kawai na baki."
Ya ƙarasa maganar a wani irin rikice, yana mai sake mayar da duban sa kan Gimbiya Tasmir, gaba ɗayan sa yabi ya tayar da hankalin sa, domin kuwa shi kansa bazai iya cewa ga adadin tsawon lokacin da Gimbiya Tasmir ta ɗauka rabon ta da ciwo ba sai yau, hakan ko shine ya sake ruɗar da shi.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir da ƙarfi ta damƙi ƴan yatsun hannuwansa cikin nata, kana ta fara ƙoƙarin buɗe idanuwanta domin ta kalle sa, amma gaba ɗaya taji ta kasa yin hakan
Hakanne yasa ta buɗe baki cikin dashash-shiyar muryarta da bata futa sosai, tana mai faɗin.

"Waye shi, meye tarihin sa Baba?"

Ta ƙarasa maganar tana mai jan numfashi da ƙyar.
Yayinda shi kuma Sarki Barbaru ya gane magana take yi, amma kuma bai fahimci kome take faɗa ba, sabo da yadda muryarta ta tayi ƙasa sosai.
Hakanne yasa ya matsar da kunnuwansa dai-dai saitin bakin ta yana mai cewa.

"Shin mene kike son faɗa mini ƴata?"

"Zuciya na k'una, rai na zafi, gaba d'aya tinani ya d'auke, komai ya hargitse.
Hak'ik'a mutuwa zanyi Baba saboda bazan taɓa iya jurar cigaba da ƙunsar baƙin cikin Bawa ba, tunda har ka hanani ɗaukar mataki a kansa."

Ta ƙarasa maganar daƙyar, tana mai jan numfashi.
Yayinda shi kuma Sarki Barbaru ya ɗago kansa a matuƙar firgice yana mai zuba idanuwan sa akan fuskar ta, domin kuwa ba ƙaramun gigitasa kalaman ta sukayi ba, ko kaɗan baiyi tinanin abun har ya kai haka ba.

Haƙiƙa bazai iya jurar rashin ƴar tasa ba a duniya, haka kuma bazai iya jurar ganinta acikin baƙin ciki ba tamkar yadda bazai taɓa iya bari yayi kuskuren rasa Bir a rayuwar su ba, domin kuwa shi kaɗai yasan irin yadda yaji a lokacin da wancan abun ya faru kafun samuwar Bir, shi kaɗai yasan irin bala'in da ya shiga.
Kana kuma bai manta komai ba da akace zai faru muddin aka rasasa.
Hakanne yasa sa buɗe baki cikin rawar murya yana mai faɗin.

"Haƙiƙa bazaki mutu ba ƴata, domin kuwa ina sonki, kuma har kawo yau baki da tamka a cikin raina, shi kuma wancan Bawan bawai so ya sanya na hanaki hukuntasa ba, nayi hakan ne kawai domin samun tsirar mu, nayi hakan ne domin goben mu ta zamto mai kyau, nayi hakan ne gudun kar kafaffen tarihin mu ya rushe, domin kuwa wannan yaron da kike gani shine komai namu, ba da ban shi ba da tini ke kanki baki samu ba a duniya, shine ya zamto garkuwar a garemu gaba ɗaya, idan kuma nace garkuwa ina nufin duniyar mu duka.
Dan haka a yau a kuma yanzu nayi alƙawarin baki tarihin yaron nan ko hakan yasa ki fahimci dalilin da yasa na hanaki hukunta sa, sannan kuma kema ki tayani riƙon rayuwar sa."
Ya ƙarashe maganar yana mai shafa lallausan gashin kanta.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir hakan da taji ne ya sanya ta buɗe idanuwanta da suka yi matuƙar ƙanƙancewa sabo da kumburin da sukayi da ƙyar.
Kana ta ɗan taune leɓen ta na ƙasa tana mai jiran ta fara jin labarin data jima tana tsumayen ji.
A kuma dai-dai lokacin ne likitan da Gimbiya Salwa ta sanya aka kira wanda shine ke duba su dama, suka shigo tare cikin ɗakin.
Hakan ne yasa Sarki Barbaru yin shiru yana mai kaucewa ya bawa likitan wuri domin ya duba ta.
Ita kuwa Gimbiya Tasmir lumshe idanuwanta tayi tana mai jin babu daɗi da zuwan likitan a yanzu, domin kuwa ba ƙaramun ƙagara tayi ba taji labarin ƙasƙantaccen Bawan can mai ji da kansa, kota samu hanyar yin maganinsa ta huta.

Cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki likitan ya fara dubata bayan ya ajiye jakar sa a gefe.
Kana a ƙarshe yayi mata allurai.
Sannan ya ɗago kansa yana mai watsa idanuwan sa zuwa wurin da Sarki Barbaru yake a tsaye.
Kana ya buɗe baki yana faɗin.

"Ku kwantar da hankalin ku ya shugaba na, domin ko ba wani babban abu bane yake damun ta, zazzaɓi ne da ciwon kai kawai, wanda shima ya samu ne ta sanadin kukan da tayi sosai, amma nan da awa ɗaya ma muna sa ran zataji sauƙi gaba ɗaya ma."
Ya ƙarasa maganar yana mai fara haɗa kayan sa.
Yayinda shi kuma Sarki Barbaru tare da Gimbiya Salwa suka girgiza kansu, suna masu neman wuri suka zauna akan mayyar kujerar da take acikin ɗakin baccin nata.
Shi kuwa likitan haɗa kayan sa yayi tas tukun ya juya ya tafi.

Ko minti goma Gimbiya Tasmir ba ta sakeyi ba idanuwanta biyu wani irin nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
Hakan ne yasa daga Sarki Barbaru har Gimbiya Salwa suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya a tare, kana suka sake gyara zaman su a wurin tare da zuba ƙwayoyin idanuwansu akan fuksar ƴar tasu.

*WASHEGARI*

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASA.*

Abu fa tamkar wasa sai gashi ya zamarwa Yarima Asad gaske, sabo da ko da ya kwanta domin yayi bacci a daren jiya gaba ɗaya ƙin ɗaukar sa yayi, babu abun da yake faman tinani kuwa sai Gimbiya Haddiyal, tare kuma da abun da mai martaba ya faɗa masa.

Yana ganin kiran Billy gaba ɗaya yaƙi ɗagawa, a ƙarshe ma da yaga tana shirin takura masa sai kawai ya kashe wayar gaba ɗayan ta, domin kuwa a lokacin shi kaɗai yasan yadda yake ji, sabo da ciwon kan da ya addabe sa, ga kuma tinanin waccan mayyar yarinyar da ta tsaya masa arai a cewar sa, sannan ga tsanar Billyn da yake ji tana ƙara ruruwa a cikin zuciyar sa, saboda abun da tayi masa.

Bashi ya samu bacci ya ɗauke saba har sai misalin ƙarfe ɗaya har da arba'in na dare, wato dai biyu saura minti goma.
Sai dai kuma wani ƙarin abun takaicin shine, koda baccin ya ɗauke sa gaba ɗaya mafarkin Gimbiya Haddiyal ya dingayi kala-kala, har zuwa lokacin da Babban Yaya yazo ya ƙwanƙwasa masa ƙofa, wato da asuba kenan.
Wanda hakan kuma yasa koda ya tashi yaji a duk duniya babu abun da yake buƙatar sake gani face fuskar ta a zahiri.

Wani irin abu yake ji akan ta irin wanda tun da yazo duniya bai taɓa sanin sa ba.
Ji yake tamkar yayi firfiluwa ya koma wurin da suka haɗu jiya ko Allah zai sa ya tadda ta, ko da kuwa ace yauma zata sake kifa masa wata madarar ne.
Sosai yake jin ɗacin abun acikin ransa, domin kuwa yana ganin ko kaɗan bai dace ba ace kamar sa yana tinanin wata ƴa mace, ƴa macen ma kuma bagidajiya wacce bata da wayewa ko kaɗan.
Sai dai kuma ya ya iya da zuciyar sa, gaba ɗaya ta gaza manta haɗuwar su ta farko da ita, yayinda idanuwansa kuma suka kasa goge hoton fuskar ta daga cikin su.

Ko da yaje masallacin asuba ma kawai dai yayi sallah'r ne a daddafe, domin kuwa gaba ɗayan ta da tinanin Gimbiya Haddiyal yayi ta.
Hakan yasa yana dawowa ɗakin sa ya faɗa kan gadon sa, yana mai kwanciya ringin-gine idanuwansa akan haɗɗaɗen rufin ɗakin nasa.
Yayinda zuciyar sa kuma ke tariyo masa mafarkan da yayi jiya masu tsantsar daɗi akan ta.

Zumbur ya miƙe daga kwancen da yake zuwa tsaye yadda kasan wanda aka tsikara, sabo da wani tinanin da ya faɗo masa acikin ransa wanda yake ganin aiwatar da abun ne kawai zai sama masa sauƙin abun da yake ji.
Cikin sauri ya kama hanyar bathroom yana tafiya yana cire kayan sa a hanya.

Duka-duka baifi minti goma ya ɗauka a ciki ba sai gashi nan ya futo ɗaure da toweil a ƙugun sa, yayin da hannun sa ɗaya kuma yake riƙe da wani ɗan ƙarami yana tsane mayawaiciyar sumar kansa da take ɗigar ruwa da shi, kai bakace shine mai ɗaukar kusan awa ɗaya ba abayi idan ya shiga.

Direct ya doshi gaban dressing mirrow, yana mai zuwa ya janyo maya-mayan sa ya fara shafawa.

Gaba ɗaya yana aikata komai ne cikin sauri, da alamun wurin da yake shirin zuwan ba ƙaramun muhimmaci gare sa ba a wurin sa.

Gaban haɗaɗɗiyar wardrobe ɗin sa ya huce yana mai sa hannu ya buɗe ta.

Wasu sababbin kaya fidigil masu matuƙar tsada ya zaro tamkar yadda ya saba ako da yasuhe.

Black creazy three quater jeans ne daya kasance designer mai matuƙar kyau da tsada.
Sai white t.shirt mai azabar kyau da ɗaukar ido, wacce aka rubuta _I'M IN LOVE_ Da gwara-gwaran rubutu baƙi a gaban ta.

Wandon ya fara sanyawa a jikin sa bayan ya sa boxer da singilet daga ciki.
Kana ya ɗago rigar yana mai ƙarasa ware ta tare da zuba ƙwayoyin idanuwan sa akan rubutun dake ɗauke a gaban ta.

Cikin sanyin murya, kana kuma acan ƙasan mak'oshi, ya ɗan ɗaga jajayen laɓɓan sa yana mai faɗin.
"I'm in love."
Kana yayi shiru yana mai cigaba da kallon rubutun, yayinda yake jin tamkar ya fasa sanya rigar a jikin sa.
Lumshe idanuwansa yayi bayan ya ɗan tura lower lips ɗin sa zuwa cikin bakin sa yana tsotsar sa.
Kana daga bisani ya buɗe su yana mai fesar da iska daga cikin bakin sa.
Kome ya tuna kuma ya juya ɓangaren da haɗaɗɗen agogon bangon da yake manne a jikin bangon ɗakin yake, yana mai watsa idanuwansa akan sa.
Ganin da yayi har tara ta ɗauko yine, ya sanya sa juyawa da sauri, yana mai zura rigar a jikin sa ba tare da ya tsaya cigaba da tinanin da yake yi ba.
Kana ya huce wurin da takalman sa suke, yana mai ɗauko wani haɗɗaɗen farin boot mai matuƙar kyau da ɗaukar ido, ya sanya fararen ƙafafuwansa acikin su.

Wucewa yayi zuwa gaban lokar da yake a jiye sarƙoƙin sa tare da agogunan sa yana mai buɗe ta.
Wani farin agogon fata mai azabar kyau ya ɗauko, yana mai ɗaura sa akan tsintsiyar hannun sa da take kwance da uban baƙin gashi a kanta.
Mayar da murfin lokar yayi ya rufe ba tare da ya ɗau sarƙa ba yau, kasancewar dama ba koda yaushe yake sanya ta ba, kai hatta da agogonma wataran baya sanya shi.
Gaban dressing mirrow ya huce daga nan.

Tsaye yayi agaban mirrow'n, yana mai kallon yadda yayi bala'in kyau acikin shigar tasa.
Hakan da ya ganine ya sanya sa ɗan sakin murmushi, yana mai lumshe idanuwansa tare da jinjjina kai, domin kuwa yana saran samun abun da zaije nema a yanzun idan yaje.
Kana daga bisani ya buɗe idanuwan nasa, yana mai ɗauke turarruka ya fara feshe jikin sa ta ko ina da su.
Sannan ya juya cikin sauri yana mai tafiya gaban bedside loca, ya ɗauki mukullin motar sa tare da wayar sa ya rike, kana ya juya cikin sauri yana mai dosar hanyar waje.

Acan dignin area ya hangi Fulani da Baby zaune akan kujeru suna shirin fara cin abinci.

Ko kaɗan baiso ya sake tsayawa ba, saboda yadda yaga lokacin kamar ya tafi, amma ya-ya iya, dole ne ya ƙarasa ya gaida mamy'n tasa, fatan sa dai kawai karta ce dole sai ya tsaya yaci abincin shima, domin kuwa ba ƙaramun lokaci zai ɓata ba idan haka ya faru.

"Ina kwana Mamy na."

Ya faɗa a lokacin da ya ƙarasa gaban floor ɗin da kujerun suke akai, yana mai ɗan zama akan capet ɗin da yake a wurin ba tare da ya ƙarasa kai ba.

"Lafiya ƙalau Zaki na."

Fulani ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi tana kallon sa.

Itama Baby buɗe baki tayi tana mai faɗin.
"Good morning Yaya."

"Morning my lil how was your nigh."
Ya faɗa yana mai miƙewa tsaye tare da shirin juyawa.

"Ina kuma zuwa da wannan safiyar ba tare da ko break fast kayi ba?"

Muryar Fulani ta daki dodon kunnuwan sa adai-dai lokacin da ya ɗaga ƙafar sa ɗaya yana shirin yin gaba.

Hakan yasa ya ɗan rumtse idanuwansa, yana mai haɗawa da ɗan taune lips ɗin sa na ƙasa a hankali.
Kana daga bisani ya warasu yana mai juyowa ɓarin da su mamy'n tasa suke hannun sa dafe da ƙeyar sa.

"Mamy na dama kaya nane suka iso, shine nake son naje na gansu."
Yayi maganar idanuwansa na kallon ƙasa.

"Amma shine hakan kuma har zai hanaka tsayawa kayi break fast ka tafi da yunwa."
Mamy ta sake faɗe tana kallon sa.

"A'a mamy ai sauri nakeyi ne shiyasa, amma kuma nayi miki alƙawarin da zarar naje zanci abincin."
Yarima Asad ya faɗa yana mai fatan ta barsa ya tafi daga yanzu, domin kuwa lokaci yana ƙure masa.

"Tom shikenan Allah ya bada sa'a, rabbi ya shiga lamura ya kuma shirya mun kai, tare da baki ɗaya al'ummar musulmi.
Kaje Allah ya dawo da kai lafiya Zaki na."

Mamy'n tasa ta faɗa tana mai juyawa wurin plate ɗin ta.
Yayinda Asad kuma ya sauke wani ɗan gajeran numfashi.
Kana yace. "Amin Amin Mamy na."
Sannan ya juya ya tafi cikin sauri.

"Wallahi ka haɗu yau sosai, Allah ya dawo mana da kai lafiya"
Cewar Baby cikin ɗan daga murya fuskar ta ɗauke da far'a.

"Thank you my Baby."

Yarima Asad ya faɗa ba tare da ya juyo ba yana mai cigaba da tafiyar sa.

Direct ya doshi parkin space yana mai tsayawa a gaban wata azababbiyar farar motar sa mai lambar Prince Asad 08 ajikin ta.

Cikin hanzari ya buɗe murfin ta yana mai shiga ciki ya zauna a mazaunin driver, kana yayi mata key, yana mai yowa baya da ita,

Please Login or Register in order to submit comment