Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujerar, tana mai bud'awa Bir hannu daga zaunen da take, fuskarta d'auke da wani irin murmushi, idanuwanta kuwa na zubar da k'walla.

A hankali Abba ya saki hannun Bir, yana mai masa alama daya tafi gareta.
Hakanne yasa ya fara d'aga k'afafuwansa jiki a matuk'ar sanyaye, yana mai nufar inda take.
Tukun ya d'an duk'usa yana mai shigar da jikinsa cikin jikinta, yayinda ita kuma ta mayar da hannuwanta ta kullesu tsam, suna masu sakin wasu irin tagwayen ajiyar zuciya a tare.
Tare da jin wani irin yanayi, irin wanda baki bazai iya misaltasaba a tattare dasu.
Dan shi kuwa Bir jin jikinta yayi da wani irin d'umi, irin wanda bai tab'a jin makamancinsa ba ajikin Iya, duk da irin yadda take rungumarsa kuwa, ga wata irin nutsuwa da yaji tana saukar masa, zuciyarsa nayin sanyi, hakan yasa sa lumshe idanuwansa, yana mai kwantar da kansa akan k'irjinta yayi luf kamar jariri.

Ita kuwa Aishatu cikin tsananin kuka ta k'are matsesa acikin jikinta tamkar zata mayar dashi cikinta, kana ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Ashe kana nan Jaririna, Ashe da rabon zan sanyaka acikin jikina, ashe da rabon zan rungumeka da hannuwana.
Allah na gode maka, Alhmdulillahi. Allah ko a yau bank'i na koma gareka ba, burina ya cika d'ana ya dawo gareni."

Ta fad'a cikin matsanancin kukan daya sanya kowa kuka acikin d'akin, tana mai k'ara ruk'un-k'umesa acikin jikinta.
Tukun ta d'ora da fad'in.
"Sun rabani da kai alokcin dana haifeka, sun rabani da kai ba tare da sun bari ko d'aukar ka nayiba, sun rabani da kai alokacin da kafi buk'tata, sun rabani dakai ta k'arfi da yaji tun kan mahaifarka ta k'arasa fad'awa daga jikina.
Na rabu da kai tun a wannan lokacin, amma sai dai kuma akullum ina ganinka acikin mafarkina, ta yadda har na sanka nasan kammanninka acikin idanuwana, wanda hakan shi ya sanya na kasa jurar rasaka tsawon shekaru talatin har da d'aya kenan.
Amma kai nasan baka sanniba, baka sanniba ko d'ana, to nice nan Umminki, ni na haife na na raineka aciki cikina, naso kuma na rainaka aduniya, na baka tarbiyya na d'oraka akan hanyar dai-dai. Ashe zaka dawo gareni, zakazo ka sameni har inda nake alokacin da ban zataba.
Hak'ik'a Allah abun godiyane, ina sonka d'ana."

Ta k'arasa maganar cikin wani irin matsanancin kuka tamkar zata shid'e, tana mai sakar masa sumba aduk inda bakinta ya sauka a jikinsa, wato dai tundaga kan fuskarsa, gashin kansa harma da huyansa da gadon bayansa, tanayi tana murza fatar bayansa da tafin hannunta.
Wanda hakan kuma ya k'ara raunana zuciyar gaba d'aya mutanen cikin falon, domin kuwa ba k'aramun tausayinsu sukaji ya lullub'esu ba.

Ita kuwa Gimbiya Tasmir da matar Sheikh Ahmad ta zaunar da ita akan kujera, gaba d'aya ji tayi ta muzanta a wurin, sabo da ganin da sanin da tayi iyayenta ne suka aikata abun da dattijuwar matar take lissafowa, lallaine ba k'aramin cutarwa sukayi mataba, fiye da wacce sukayiwa Jaruminta ma.
Lokaci d'aya kuma sai taji tausayin kanta yayi matuk'ar lullub'eta, domin kuwa bata son irin tarbar da zasuyi mata ba idan sukaji cewar ita d'in d'iyar Sarkince, ga kuma tinanin nata iyayen daya taso mata da kuma tsantsar soyayyarsu, sabo da ganin yadda iyayen Bir suke kukan farincikin ganinsa a gabansu.

Bir kuwa sosai jikinsa ke karkarwa, yana mai jin kukan matar na tab'a zuciyarsa.
Yayinda shima kuma hawayensa suka gaza tsayawa acikin idanuwansa, banda aikin k'ara kwanciya a jikiinta da yake jinsa tamkar a wata duniyar yake daban ba wannan ba saboda dad'insa babu abun da yake yi.
Hakan yasa yake ta k'ara shige mata, sabo da ji yake tamkar idan ya saketa zai nemeta ya rasane.
Hak'ik'a a yanzu ya gane cewar iyaye daban suke da kowane mutum aduniya, ma'ana dai basu da tamka kwata-kwata, domin kuwa bai tab'a jin irin yadda yake jiba yanzu ajikin Umminsa dan iya ta rungumesa.

"Wayyo Iyata ko ya take yanzu."
Ya fad'a a cikin zuciyarsa yana mai k'ara fashewa da kuka, tare da sake shiga cikin jikin Umminsa.

"To Aishatu kukan ai ya kamata ace ya tsaya haka ko."
Cewar Abba murmushi d'auke akan fuskarsa, hawayen kuma na cigaba da futa a idanuwansa.

"A'a dan Allah ku barni nayi kukana, kukan yau d'in ba irin na baya bane da nakeyi, kukan yau d'in na dad'i ne, ku barni rik'e da Jaririna kar kuce in sakesa ban gaji da jin d'uminsa ba kunji ko."

Ummi ta fad'a cikin wata irin murya hawaye na cigaba da zubo mata, kana kuma tana sake damk'ar Bir a jikinta.

"To amma ai kya sakesa muyi magana dasu, sannan kuma su huta, ko kuwa bakiga alamun agajiye suke bane ba."

Abba ya sake fad'e yana mai matsawa kusa da ita ya fara k'ok'arin janyo Bir daga jikinta.

"A'a bammun shi nak'i wayon, kaima so kake in sakesa ka kamasa, naji zan sakesa amma a kusa dani zai zauna to."

Ummi ta fad'awa Abba haka tamkar wata k'aramar yarinya tana mai nok'e masa kafad'a.
Hakan yasa Abban ya samu wuri ya zauna a kusa da ita, bayan ya d'an bud'a space a tsakaninsu yace to ta sake sa ya zauna anan, sabo da zance gaskiya kuwa tamkar yadda ta fad'a d'in hakane, shima so yake ya sake jinsa gashi ga dan nasa, wato dai jikinsu ya sake had'uwa wuri d'aya, sai kuma yayi rashin sa'a ta gano dabarar tasa da wuri.

Ganin da tayi ya bud'e wurinne ya sanya ta sakin Bir, tukun ya zauna a tsakiyarsu ita da Abba, kana ko wanne daga cikinsu ya damk'i tafin hannunsa d'aya suna masu murzawa a hankali.

Shi kuwa Sheikh Ahamd cikin tsananin farinciki ya zauna akan kujerar da take a kusa da wacce suke akai, yana mai kallon k'anin nasa.
Yayinda Auta kuma da yaci kukansa ya more ya zaro wayarsa da sauri, yana mai kiran yayyinsa mata ya fara sanar musu da abun da ke faruwa.
Kana shima ya samu wuri ya zauna.
Haka duk suka zazzauna har Kaka, dan kuwa ita ak'asan capet ma ta zauna tana mai sharce k'walla, tare da fece majina da gefen zaninta.

Ganin da Abba yayi duk kowa ya nutsune, ya sanyasa yin gyaran murya.
Kana daga bisani yayiwa Allah godiya daya nuna musu wannan ranar.
Sannan ya d'ora da tambayar Sheikh Ahmad wurin da suka had'u dasu.

Zama Sheikh Ahmad ya gyara akan kujerar da yake.
Kana ya fara basu labarin abun da ya faru tundaga had'uwarsu a shago har tambayar k'asarsu da yayi suka fad'a masa, daga nan kuma yayi shiru.

Hakan yasa Abba ya juya b'arin da Bir yake yana mai fad'in.

"Daga ina kuke a jahar karfuz, kuma me kukazoyi anan d'in d'ana?"

Lumshe idanuwa Bir yayi tare da bud'esu, kana ya bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Daga BAK'AR MASARAUTA, mun kuma zo k'asar hausane ta sanadinta."
Ya k'arasa maganar yana mai yi musu nuni da Gimbiya Tasmir.

Ita kuwa Kaka da sauri ta bud'e baki tana mai fad'in.

"Ile kuwa shine, BAK'AR MASARAUTA, garin la'annanu da tsinannu marasa imani, masu Bak'ar zuciya ba!"

Da k'arfi Gimbiya Tasmir ta rumtse idanuwanta, sabo da jin furucin da tsohuwar tayi, wanda hakan kuma ya sanya ta tabbatar da cewar ba lallaine zamanta ya d'ore a cikinsu ba.
Kafin daga bisani kuma ta bud'esu tana mai durk'usar da kai k'asa, sabo da muryar Abba data sake ji yana mai fad'in.

"Ko meye wannan dalilin kuwa d'ana?"

A hankaki Bir ya d'ago kansa yana mai kallon Gimbiya Tasmir.
Kana kuma daga bisani ya janye idanuwansa daga kanta yana mai mayar dasu kan Abban nasa, tukun ya bud'e baki cikin sanyi yana mai fad'in.

"Ita d'in Gimbiyace, 'yar gata, wacce iyayenta ke sonta sama da kowa da komai nasu da suka mallaka.
Yayinda ni kuma na kasance Bawa k'ask'antacce, wanda na taso a hannun Iyar Bayi.
Soyayya itace silar data kawo mu K'asar Hausa, ma'ana dai gudowa mukai daga cikin masarautar mu."

Bir ya fad'a a sanyaye.
Yayinda gaba d'aya jama'ar dake cikin falon kuma suka sakeyin shiru jikinsu na yin sanyi, suna masu nutuswa domin suji labarin nan, wanda tun kafin su jisa suka san sark'e yake da muguwar sark'ak'iya a cikinsa, sabo da soyayya tsakanin Bawa da 'Yar Sarki ba k'aramun al'amari bane a ko ina.
Ganin da Bir yayi gaba d'aya idanuwansu yana kansa ne.
Ya sanyasa gyara zamansa a wurin da yake, yana mai sake bud'e baki ya d'ora da basu labarin soyyayarsu da Gimbiya Tasmir.

Sun d'auki kusan awa biyu ana labarin, domin kuwa yana cikin labarinne ma 'yan uwnasa mata gaba d'ayansu suka shigo da 'ya'yansu, suna masu zama suma a wurin.
Atak'aice dai sai da ya basu labarin tas, babu abun da ya b'oye musu sai rikicinsa da Gimbiya a farkon had'uwarsu, tare da irin azabtar dashi d'in da tayi.
Wannan kad'ai ya b'oye bai fad'a ba, saboda yana gudun kar hakan ya zama silar da zaisa wani a cikinsu ya k'ullaceta arai.

Sosai gaba d'aya jama'ar cikin falon suka girgiza da jin labarin.
Amai-makon kuma suji haushin Gimbiya na abun da mahaifinta yayi musu, sai sukaji wani irin mugun tausayinta tare da soyayyarta ta daki zuciyarsu, sabo da itace silar dawowar d'an su wurinsu, kuma tayi abun da ba kowace mace bace zata iyayin sa, ta sadaukar da farincikinta, iyayenta da komai nata domin masoyinta ya sadu da nasa.
Hakan yasa jikin kowa a wurin yayi mugun sanyi, banda na Kaka kawai.
Domin kuwa ita tana jin gaba d'aya wurin yayi tsit ta mik'e tsaye zumbur tana mai fad'in.

"Kafura a cikin ahalina, inaaa abun da bazai tab'a yuwuwa ba kenan, dan haka tashi tashi ki fuce mana daga cikin gida na tsaneki wallahi, jikana bazai tab'a had'a jini dake ba jinin azzalumai bak'ak'en kafurai, wa'yan da Allah ya tsinewa!"


*K'ASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAK'AR MASARAUTA.*

Tamkar ya samu tsumma haka badakaran ya suri Iya a sama da hannu d'aya yana mai kama hanyar d'akin azaba na Bayi da ita ko tsufanta bai duba ba ballantana yaji tausayinta.
Yayinda ita kuma Iya take ta faman zare idanuwa ba tare da tayi ko gigin yin wani shure-shureba, sabo da ta riga data sani kome zatayi bazai hana ta d'an-d'anar azaba ba, k'ilama gaba d'aya duniyar zata bari, shiyasa bama tayi gigin yin gardamaba.

Tsaye suka hangi Sarki Barbaru tare da Iyalansa abakin k'ofar d'akin azaba na Bayi, hankulansu a bala'in tashe.

"Sauketa anan wurin ta fad'a mini ta yadda akai amanar dana bata ta bar cikin gidan nan."

Sarki Barbaru ya fad'a da k'arfi, ta yadda har wurin sai da ya amsa gaba d'aya jikinsa na kyarma.

Daga tsayen da yake Badakaren ya saki Iya, ta yadda har gwiwarta d'aya ta daki dutse.
Amma ko kad'an bata tsaya bi takan azabar da taji ta ratsata ba ta sanadin hakan, sai ma zube gwiwoyinta da tayi a gaban Sarki Barbaru jikinta na wata irin karkarwa.
Yayinda idanuwanta kuma suke kallon k'asa suna d'igar k'wallar.

Tana cikin wannan yanayin taji saukar wani irin azabbaben mari akan kuncinta, jikake Tassss!!!
Sarki Barbaru ya d'auketa da marin babu ko d'igon tausayi a zuciyarsa.
Yayinda gaba d'aya jama'ar wurin kuma k'arar marin tayi matuk'ar razana su da firgitasu, ta yadda da yawa daga cikin su sai da suka rumtse idanuwa jikinsu na d'aukar rawa, hatta da matansa kuwa.

Ita kuwa Iya baya ta tuntsira kanta na dukan dutse, gaba d'aya jinta da ganinta ya d'auke na wucin gadi.

Cikin zafin rai Sarki Barbaru ya sake sanya hannunsa yana mai d'agota zaune.
Tukun ya bud'e baki cikin muryarsa da ita kad'ai ke razana mutane yana mai fad'in.

"Ya akai yaron wurinki ya gudu? Me yasa zakici amanata? Akan me zaki sanar da shi labarin da bai san da shiba har ya tafar mun da 'yata, bayan kuma kin riga da kin san shine duniyarmu?"

Ya fad'a cikin wani irin k'araji ta yadda gaba d'aya wurin ke amsawa.

Tsiiiii haka Iya ta saki fitsarin firgici a d'an guntun zanin da yake d'aure a k'ugunta.
Yayinda jikinta kuma ya sake d'aukar matsananciyar karkarwa.
Kafin daga bisani kuma ta bud'e baki a wani irin fuzge, tana mi fad'in.

"Bani bace ba, nima ban san ya taf..."

Farin gashin kantan da Sarki Barbaru ya damk'a da k'arfi yana mai funcikarsa ne ya sanya maganar da takeyi tsinkewa, tana mai sakin wata irin gigitacciyar k'ara da tsananin azaba ya sanya ko sautinta bai futo ba.

"Hak'ik'a azaba ta tabbata akanki mai rad'ad'i muddin baki fad'a mun wurin da suka tafi ba, kafun daga k'arshe kuma na raba numfashinki da gangar jikinki."

Kotsss!
Kakejin k'arar zawayin da Iya ta saki a sanadin murd'awar da cikinta yayi, jikinta na cigaba da kyarma.
Kafin daga bisani kuma ta sake durk'usar da kanta k'asa tana mai girgizasa tare da fad'in.

"Ni d'in Baiwace mai ladabi da rik'on amana ya kai shugabana, banci amanarka ba abaya dan haka babu abun da zaisa naci amanarka a yanzu, ballantana kuma wannan dana san bala'in har akaina zai rufta.
Hak'ik'a ban san da tafiyar Bir ba kuma ko alak'ar da take a tsakaninsu da Gimbiya bansan komai ba bayan fad'an da kowa yasan sunayi ya Shugabana."

Iya tayi maganar jikinta na cigaba da kyarma, yayinda muryata kuma take futowa a wani irin firgice cikin rawa da matsanancin kuka.

"Ku d'auketa ku sanya mun ita ad'akin azaba, zan tafi in dawo gobe da safe, idan har da sauran rayuwarta aduniya bata mutu ba, nasan alokacin zata bani amsar tambayar da nayi mata, idan kuma ta mutu shikenan sai na fara shiryawa tarbar dawowar Yaron."

Cewar Sarki Barbaru a wani irin kausashe yana mai juyawa ya tafi.
Yayinda Iyar Bayi kuma jikinta ya k'ara d'aukar tsuma, zawon da take ya k'ara tsananin k'aruwa, saboda tun suna yara sun riga da sun san har da aka sanya mutum a d'akin azaba ba afiya futowa dashi da ransa ba.
Haka sauran Bayi 'yan uwanta ma kuka suke hawaye na kwaranya daga cikin idanuwansu.
Yayinda rabi da kwatansu kuma suke zagin Bir, suna masu fad'in yaci amanar Iya baiyi halllaciba, duk da irin soyayyar data nuna masa, sabo da gaba d'aya a cikinsu babu wanda yayi tinanin da saninta ya tafi.

Su kuwa su Mauzum sosai suka rud'e suka firgice suna kuka, tare da jin tsanar Bir na lullub'esu, saboda abun da sukaga ya jawowa Iya duk da fifitasan da tayi sama da kowa a cikin Bayi.

Shi kuwa wannan Badakaran da hannu d'aya ya funciki Iya yana mai hurgata cikin d'akin azaba.
Kana ya bita ciki yana mai d'aure mata hannuwa da k'afafuwa a jikin k'arafa.
Sannan ya k'ara iza hutar cikin kaskwaye d'akin na k'ara d'aukar tsananin zafi tamkar gidan biredi.
Tukun ya juyo yana mai futowa ya rufe d'akin daya kasance d'an k'arami, kana kuma mara taga ajikinsa yayi tafiyarsa.

Ita kuwa Gimbiya Salwa a guje ta kom cikin d'akinta.
Tana zuwa ta kife a k'asa tana mai cigaba da sakin wani irin azabbaben kuka, tare da fad'in.

"Me yasa zakiyi mun haka? Me yasa zaki zab'i Bawa sama dani Mahaifiyarki? Me yasa idan ma kina jin ba zaki iya rayuwa bane ba tare dashi bane kika k'i sanar mun na nema maki mafuta? Me yasa kika zab'i ki cutar da zuciyata 'Yata? Akan me zaki zab'i guduwa ki barni bayan kinsan bazan iya rayuwa ba idan bakya a kusa dani?
Shin kuna inane ne? A ina zan ganki? Ubangiji Gargabilu ka bayyana mun 'Yata."

Ta fad'a tana mai dukan tiles d'in cikin d'akin tare da cigaba da sakin kuka, gaba d'ayanta ta gigice ta firgice ta futa hayyacinta.

A b'angaren Gimbiya Haiwa da sauran yayyan Gimbiya Tasmir suma gaba d'ayansu hankulansu a bala'in tashe yake, domin kuwa bayan tashin hankalin tafiyar Gimbiya harda fargabar abunda zai same su ta sanadin tafiyar Bir ya cika zuciyarsu.

Ita kuwa Hadima Fulaika sosai tayi kuka tai kuka tamkar ranta zai futa, sabo da gane wanda Gimbiya ta kamu da soyayyarsa da tayi, wanda har ta tambayeta alamun so akansa.
Hak'ik'a data san abun da zai faru kenan da babu abun da zai sanyata ta bata shawarar data bata, na ta furtawa koma wayene da tace mata.

Haka dai gaba d'aya yau masarautar ta hargitse, bikin da aka tashi da shirin yinsa duka ya wargaje aka dena yin ta kansa, ahaka har dare ya tsala babu mutum d'ya da ya mallaki hankalin kansa da za'ace ya rumtsa da sunan bacci acikin Bak'ar Masarauta.

A b'angaren Dakarun da aka tura subi sahu kuwa, sosai sukaiyi tafiya tare da bincikar duk jirgin dayazo hucewa ta cikin ruwa amma abanza.
Haka wa'yanda sukaje filin jirgin sama sukai bincike suma basu samuba.
Tukun ak'arshe lokacin yamma ta d'auko yima, sannan suka gane cewar sun tafi jahar Markuz ne da suka futa daga cikin Bak'ar Masarauta.
Sun gano hakanne kuma ta tsanadin sahun takun k'afafuwan su da sukabi ya kaisu har wurin da ake hawa jiragen ruwan Jahar Markuz.
Ba tare da b'ata lokaci ba kuwa suma suka hau jirginsu na Bak'ar Masarauta suna masu tafiya jahar.

Sai dai anan d'in ma kuma suna zuwa sukaji labarin ai ba adace ba tun acikin dare suka hau jirgin k'asar Hausa suka tafi.
An kuma ganosu ne ta sanadin kayan jikinsu da suffarsu da dakarun suka kwatanta.

Ai kuwa ba tare da b'ata lokaciba dakarun suka sake d'aukar hanyar kasar hausa ba dan suna tsammanin zasu same su ba.
Haka kuma sukayi tafiya sosai amma babusu babu alamunsu.
Tukun ak'arshe da suka tabbatar da bazasu tab'a cimmasu ba, kai sunma isa wurin da zasuje suka juyo jiki a matuk'ar sanyaye suna masu kamo hanyar Jahar Karfuz.
A lokacin tini dare ya tsalama sosai.
Hakan yasa basu suka dawo ba sai da safiya tayi, wanda hakan kuma yayi dai-dai da lokacin da Sarki Barbaru da sauran jama'a suka sake furfutowa aka tafi d'akin azaba domin a d'auko Iya.

Ko da labarin cewar K'asar Hausa suka tafi ya isa kunnen Sarki Barbaru ba k'aramun firgita yayi ba, domin kuwa dakarun sun sanar dashi duk irin bincike da sukayi.
Wanda hakan kuma ya sanya lokaci d'aya yaji jikinsa yayi d'an sanyi, saboda tuno lokacin da yake bawa Gimbiya labarin Bir da yayi, da kuma yadda yaga jikinta yayi mugun sanyi tare da tsantsar tausayinsa acikin idanuwanta, sai dai kuma ko kad'an bai kawo hakan zai sa wata alak'ar ta k'ullo a tsakaninsu ba.
Hak'ik'a a yanzun yana zargin 'yartasa ce ta zamto jagorar tafiyar, kuma itace ta bawa Bawan labarinsa, tunda ada can farko bai guduba har sai abayan ya bata labari, sanann kuma suka tafi tare da shi.
Hakan yasa lokaci d'aya yaji gaba d'aya tsanarta ta caki zuciyarsa, k'aunar da yake mata ta kau, ta yadda har yake jin inama za'a gano masa wurin da suka tafi, da babu abun da zai hana yayi mata kisa irin kisan da yayiwa Boka mai hutar kasko, tunda har ta zab'i wani sama dashi, bayan duk da irin soyayyar daya nuna mata aduniya.
Tukun bayan ya gama da ita ya kashe shima Bir, inyaso duk abun da zai faru sai dai ya farun.

Tamkar tsumma haka ya d'auko iya daga cikin d'akin nan babu alamun rai tattare da ita.
Gaba d'ayanta ta canza tayi wani irin bushewa, yayinda jikinta kuma yayi wata irin muguwar dafewa.

Da sauri Sarki Barbaru ya k'arasa wurin yana mai sauke idanuwansa akanta.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Kuyi maza akawo mun ruwa."

Su kuwa Bayi sosai suke kuka tamkar ransu zai futa, sabo da ganin iya da sukayi a haka, matar da babu ruwanta mai tsananin kirki da hak'uri ko acikin Bayi, tare da san jama'a.

Cikin k'ank'anin lokaci aka kawowa Sarki Barbaru ruwan mai sanyi a cikin botiki.

Shi da kansa ya karb'esa yana mai d'aga sa ya shek'awa iya shi.
Tukun yayi cilli da botikin gefe, yana mai durk'usawa a gabanta.

A hankali iya take motsa fatar idanuwanta tana mai so ta bud'esu dan taga a wurin da take, amma gaba d'aya taji ta kasa.
Yayinda take jin ko ina na jikinta kuma na mata wani irin rad'ad'i da ciwo.
Tana cikin wanna halin ta jiyo sautin muryar Sarki Barbaru tamkar acikin iska yana mai fad'in.

"Zaki fad'a mun yanzu ko kuma kin shirya bak'untar lahirane."

"Bani bace ba...nima ban san ya tafi ba."

Ta samu kanta da fad'in haka ba tare da ta shirya ba, muryarta ta na futowa a wani irin rarrabe, kana kuma acan k'asa, ta yadda Sarkin Barbaru ne kawai ya iya jinta, shima d'in dan ya durk'uso ne kana kuma idanuwansa suna akan bakinta ne.

Rumtse ido Sarki Barbaru yayi da k'arfi, sabo da tabbatarwa kansa da cewar Gimbiyace ta basa labari ba itaba da yayi.
Tukun ya mik'e tsaye da sauri yana mai jin zuciyarsa na wani irin tafarfasa.
Kafin daga bisani kuma ya bud'e baki yana mai fad'in.

"Hak'ik'a nayi nadamar haihuwarki Tasmir, Ubangiji ya wadaranki, tabbas da zan ganki da babu abun da zai hanani murd'e miki huya da hannuna ko naji sanyi akan amanata da kikaci."

Yayi maganar a wani irin haukace, wanda hakan kuma ya sanya gaba d'aya iyalinsa sukayi matuk'ar firgita, domin kuwa su dai ko da hakan ta faru basu ji tsanar 'yar uwartasu a ransu ba, sai babban d'an sane kawai yaji shima da zai ganta tsaf sai ya kasheta.
Kana ya d'ora da fad'in.

"Daga yau daga yanzu na cireta daga cikin 'ya'yana, ko bayan ba raina idan ta dawo cikin masarautar nan bance ku barta da raiba, idan kuma har naji labarin wani ya tafi nemanta, to kusani daga ranar bazai k'ara shurawa aduniya ba shima.
Ku kuma ku d'auke tsohuwar nan kuje kuyi mata magani.
Dakaru kuma ku huce a fara shirin yak'i da gasken gaske."

Ya k'arasa maganar yana mai juyawa cikin sauri ya doshi b'angarensu.

Su kuwa Bayi mata da sauri sukayi kan Iya suna masu d'aukarta suka tafi da ita b'angarensu.
Yayinda Gimbiya Salwa kuma ta fashe da wani irin gigitaccen kuka tana mai kama hanyar d'akinta a guje.


*K'ASAR HAUSA, JAHAR WASAI, BABBAN ZAURE LOCUS.*

Cikin tsantsar firgici, rud'u, had'i da tashin hankali kowa ya zubawa Kaka ido ana sauraren bala'in da takeyi.
Yayinda Gimbiya Tasmir kuma ta mik'e tsaye zumbur daga zaunen da take, jikinta na d'aukar kyarma.
Idanuwanta kuwa sosai suke zubar ruwa tamkar an bud'e famfo, gaba d'ayanta ta rud'e ta kid'ime.

Da sauri shima Bir ya fara shirin mik'ewa tsaye hankalinsa abala'in tashe, saboda yadda yaga tana kuka.
Amma sai yaji Abba ya rik'e hannunsa gam, yana mai mayar dashi ya zaunar.
Kana ya bud'e baki yana mai yin gyaran murya.
Tukun daga bisani ya kalli Mahaifiyartasa yana mai fad'in.

"Haba Ummata, ko kad'an Yarinyar nan bata cancanci haka daga garemu ba, asalima k'aunarta ya kamata muyi, sannan kuma mu riritata mu zame mata iyaye da danginta data rasa ta silarmu, domin kuwa da badan itaba da k'ila har abada bazamu tab'a sanya ji...."

"Kaddalacan rufemun baki sha-sha-sha wanda bai san ciwon kansaba, kai yanzu in banda rashin zuciya ace duk irin halin da kafuran iyayen yarinyar nan suka sanyamu aciki kamanta da shi.
To ku bud'e kunnuwanku da kyau kuji, bazan tab'a had'a jini da jinin kafuraiba, kuma idan kai kace haka ai ita Aishatu da abun ya faru da ita nasan bazata fad'a ba, tunda dama ku maza ba sanin ciwon kanku kukayi ba, ko ba hakane ba Aishatu?"

Ta k'arasa maganar azafafe tana mai kallon Ummi.

A hankali Ummi ta durk'usar da kai k'asa.
Kana ta bud'e baki murya asanyaye tana mai fad'in.

"Amma Umma ai idan kika duba wannan abun daya faru ko kad'an wannan yarinyar bata da laifi aciki, dan haka ni sai nake ganin kam..."

"Sha-sha-sha lambar farko wacce ta rako mata duniya! Kike ganin Uwaki, ke yanzu Aishatu ashe har kin manta da yadda kika dinga ciwo da kuka kamar zaki mutu, wanda duk iyayen wannan kafurar yarinyar mai zubin aljanuce suka sanyaki.
Ku dubi wani dogon hanci dan Allah sai kace karas, ga idanuwa k'wala-k'wala irin na mayu, to wallahi sai kin bar gidan nan kafurar banza jinjin azzalum..."

"Haba dan Allah Kaka akan me zakiyi haka? Shin ke kanki baki san wannan abun da kike fad'e laifine fad'arsa a addinance ba, ita kuma da kiketa zaginta kina ba zata zauna ba a gidan nan ba ai idan da hallaci ko kad'an bata cancan...

"Yi mun shiru sarkin malaman bogi, kai dama nasan mugun halinka dan haka ba takai nake ba, kuma wallahi sai ta bar gidan nan."

Kaka ta katse Sheikh Ahmad da fad'in haka tana kumfar baki tare da buga masa harara.
Hakan da sauran jikokanta mata sukaji ne ya sanya suma duka suka sanya baki, suna masu fad'in.

"Wallahi fa babu inda zata, haba Kaka wannan ai ba adalci bane ba."

"Kan ubancan, wato taran dangi zakuyimun kenan Iyaye da 'Ya'ya ko.
Wayyo Allah ni 'Yasu na shiga ukku na lalce yau naga k'arshen duniya, naga jaraba naga masifa, ke duniya ina zaki damu?"

Kaka ta fad'i haka saboda jin da tai kowa yak'i goyar bayanta tana mai fashewa da kuka.
Kafin daga bisani kuma ta d'ora da fad'in.

"Na rantse da Allah ko me zakuyi agidan nan ko mutuwa zakuyi sai dai kuyi amma wannan kafurar yarinyar jinjin bak'ak'en azzalumai bazata zauna acikin gidan nan ba, idan

Please Login or Register in order to submit comment