Join Our WhatsApp Group

A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1 Complete Hausa Novel Document by A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1


A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 63867



A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1

Reading Time: 5 Hours

Added On: 18, Feb 2024

Author: Mhiz Innocent ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08124818273

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 317.31 kb

File Type: txt

Views: 695+

Download: 519+

Last download: 1 day ago

Description/Story: https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw



*🌹A JINI TAKE🌹*
*(IZZATA)*

By
_*Zarah Maitama (Mhiz Innocent)*_



_Bismillahir rahmanir raheem_


_*CHAPTER ONE*_
Page _01



__La'asar ce sakaliya dan kuwa rana ma ta kusa faɗuwa. Babu laifi akwai iska, irin iskar nan me daɗi, duk da ba lokacin sanyi bane, se dai yanayin garin sosai yayi kyau da kuma daɗi. 'Yan mata ne guda biyu ke tafiya sanye cikin hijab dogo har ƙasa kala ɗaya. Ɗayar da niƙab a fuskarta ta saƙala jaka a kafaɗarta, yayin da ɗayar ke sanye da hijab kawai. Hannun wadda ke sanye da niƙab riƙe yake da wani ƙaramin kyakkyawan yaro, fari ƙall da shi, wanda ba ze wuce 5years ba sanye cikin uniform, wanda hakan ya alamta min cewar daga Islamiyya suka dawo. A hankali na kai dubana zuwa fuskar wadda babu niƙab a fuskarta, kwata_kwata kyakkyawar fuskarta ta babu annuri, da alama wani abun ne ya ɓata mata rai ko kuma akayi mata. Se dai duk da yadda fuskarta ta ke a haɗe hakan be hanani ganin tsagwaron kyawun fuskarta ba, wadda idan ba dan shigar da ke jikinta ba da kai tsaye zan iya kiranta da balarabiya, dan kuwa komai na ta yayi kama da nasu, dara_daran idanu masu ɗauke da baƙar ƙwayar ido me matuƙar ɗaukar hankali da wani irin ƙyalli, dogon siririn hancinta da ke zaune ɗass akan fuskarta kamar an zama, se kuma ɗan ƙaramin red lips ɗinta me matuƙar kyau wanda shi ne yafi komai ƙawata fuskarta. Har suka ƙarasa gida babu wadda tace da er uwarta komai.

Babban gida ne me kyau sosai, duk da ba wani ƙyale ƙyale ne a gidan ba amma kasancewarsa me girma da kuma yanayin ginin gidan na zamani ne yasa ya ƙawatu matuƙa. Tun a parlour AFAAF ta jefar da jakar hannunta da tun da suka fito daga makaranta ta kasa maƙalata a kafaɗa se riƙeta tayi a hannu, wucewa ɗaki tayi kamar wadda aka kora. Ammi ta bi ta da kallo kafin ta dawo da kallan nata kan AFRAH dake kwance niƙab ɗinta tace

"Ke lafiya kuwa? Yau kuma me aka yiwa Afaaf?" Dariya wadda aka kira da Afrah tayi daidai lokacin da ta ida kwance niƙab ɗin fuskarta, wanda hakan ya bani damar ganin kyakkyawar farar fuskarta wadda kallo ɗaya na mata na gane ita ɗin er biyun Afaaf ce, dan kuwa kamarsu ɗaya sak, kamar yadda Afaaf ke da manyan idanu haka Afrah ke dasu, dogon hanci da ƙaramin baki me kyawun gaske haka Afrah ke da shi, ba dan tsayawa nayi ina kwatanta muku kamanninta ba da bazan iya gano wani banbanci a tsakaninsu ba, saboda kamarta su ta ɓaci, banbancin da zan ce na gano guda ɗaya ne shi ne, saɓanin Afaaf da ke ɗauke da baƙar ƙwayar ido ita Afrah brown ne da ita me maiƙo.

"Tubarkallah Masha Allah!" Shi ne abin da na faɗa sanda na sake tabbatar da lallae waɗannan en biyun irin waɗannan da ake kira da identical twins ne, se dai su waɗannan nin sun fita daban ta hanyoyi da dama, a ƙiyasce ba zasu wuce 17 years ba, kowaccensu na da kyawun jiki me kyau, hatta kuma da jikinsu ba zaka iya banbance wani banbanci ba dan kuwa dukansu basu da ƙiba.

"Ammi ita da Gwani ne.." Afrah ta faɗa da siririyar muryarta me daɗi wadda ke ɗan rawa a duk sa'ilin da take magana, zaka ɗauka tsoro ko wani abun makamancinsa ke sanya muryarta ta rawa, se dai ba haka bane, haka muryarta ta take a halitta, hakan kuma shi ke ƙara ƙawata muryarta ta ta sake zama ta daban.

"Gwani kuma? Me ya faru? Wani abun ta sake yi?" Ammi tayi tambayar a jere. Girgiza kai Afrah tayi kafin tace

"A'ah Ammi, kawai dai an chanja mana malami ne, yanzu Gwani AFFAN ne malamin ajinmu."

"Auu shi ne take fushi saboda makarantarta ce ko kuwa me?" Ammi ta faɗa a ɗan zafafe. Se da Afrah ta ɗan yi kalar tausayi da fuskarta gudun kada Ammin ta fusata sosai sannan tace

"A'ah fa Ammi, ita abin da ya ɓata mata rai yadda ya aiko wai a faɗa gobe ze fara da karɓar hadda." Tsaki Ammi ta ja tana girgiza kai, wannan hali na Afaaf na ƙona mata rai wani lokacin, kamar ba za tace komai ba se kuma tace

"Idan ta so kada tayi, zata haɗu da ni ko da Abbanku." Daga haka ta miƙe ta bar parlourn. Bin ta da kallo Afrah tayi ba tace komai ba se dauke ajiyar zuciya da tayi sannan ta dawo da dubanta cikin ɗakin kana ta miƙe ta wuce ɗakinsu.


.. Se da Afrah ta gama komai sannan ta koma kan gado, ta ɗauko Qur'an ɗinta dake cikin jaka ta buɗe ta soma karantawa. Tana cikin yin karatun Afaaf ta fito daga toilet da alama wanka tayi, ta ƙarasa ta shirya cikin kayan bacci sannan ta dawo kan gadon tana ƙoƙarin kwanciya. Rufe Qur'an ɗin Afrah tayi sannan tace

"Me za ki yi?" Se da ta harari gefe sannan tace

"Bacci zan yi." Karo na farko kenan da na fara jin muryar Afaaf wadda itama cikin ikon Allah muryarta su iri ɗaya ce, dan idan wata a cikinsu ma tayi magana ko da ka sansu ba zaka banbance ba se dai idan ka ga fuskarsu.

"Malama ki ɗauki Qur'an ki yi karatu, kin san dai halin Gwani." Se da ta tura baki sannan tace

"Ai yau so nake na ƙure shi wallahi, mutum se faɗin rai da nuna shi wani ne bayan ba kowa bane. Ban da tsabar iyayi meye na wani cewa ze karɓi hadda a ranarsa ta farko a ajinmu? Ni babu haddar da zan yi." Ta faɗa tana neman waje zata kwanta. Da sauri Afrah ta riƙota tace bayan ta haɗe rai

"Lulu ki fita a idona wallahi. Gwanin kike faɗa wa haka? Ki tashi malama ki yi karatu kin san dai ba ɗaukar iskancinki ze yi ba."

"Don Allah Didi ki ƙyaleni." Afaaf (Lulu) ta faɗa a ranta tana sake tuna wannan ƙarfa_ƙarfar da Gwanin ke ƙoƙarin yi. Cika hannunta Didi tayi kana ta haɗe fuskarta waje ɗaya ta cigaba da haddarta a zuciya. Ita kuwa Lulu kwanciyarta tayi, se dai yanayin yadda ta ga fuskar Didin ya hanata yin baccin. Tsaki ta ja a hankali ta miƙe zaune tana tura baki. Ita kuwa Didi ko kallanta ba tayi ba, duk da dama ta san Lulun ba zata iya kwanciya tana fushi da ita ba. Sauka Lulu tayi ta ɗauko Qur'an ɗinta ta koma kan gadon itama, bata kalli Didi ba ta soma karatunta a zuci, se dai ba haddar take yi ba, dan kuwa ta riga ta ƙudurcewa kanta ba za tayi haddar ba, se dai kawai ta shiga muraja'a hankalinta kwance. Ta riga Didin idarwa, da ta ga har lokacin bata kalleta ba se ta ɗora kanta akan kafaɗar Didin da itama take kan aya ta ƙarshe a maimaita haddar da take yi. Se da ta idar sannan ta saka hannunta ta buge kan Lulun. Tura baki Lulu tayi kafin tace

"Kai Didi, nayi karatun fa. Kiyi haƙuri." Murmushi Didi tayi dan itama ba wai tana fushi da Lulun bane kawai dai ta ɓata ranta ne dan tayi karatun, dan haka tace

"Toh na ji, amma dai ki dena abin da kike yi musamman akan Gwani Affan, ni ban san me ya tare miki ba!" Taɓe baki Lulu tayi dan ita sam bata da buƙatar jin magana akan Gwanin, ko a makaranta ne kuwa ballantana a gida.

"Haka kawai fa Didi, ɗaga kansa yayi yawa kuma..!"

"Ni kam ya isheni haka nan Afaaf, ke kodayaushe zancenki kenan!" Riƙo hannun Didi Lulu tayi kafin tace

"Pls Didi mu bar maganar nan, Allah kuwa raena ɓaci yake yi."

"Naa ji." Didi ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Langaɓar da kai Lulu tayi kafin tace

"A'ah fa Didi, ta yaya zan san kin haƙura.. Smile.." ta faɗa tana murmushin da ya sake fiddo da ainahin kyawunta. Itama Didin murmushin tayi wanda hakan ya sake ruɗani akan tsananin kamarsu da ta sake fitowa fili, dan komai na su iri ɗaya ne hatta da murmushin kuwa.



... Washegari wajen ƙarfe 2 da rabi Didi ta gama shirin Islamiyya, tana kallan Lulu da tun dawowarsu daga boko ta kwanta a kan gado ita a lallai bata da lafiya. Kasancewar sun makara ne ya sanyata saurin ɗaura niƙab ɗinta a jikin ƙaton mudubinsu me kyau sannan ta ɗauki jakarta ta fito. Kallanta Ammi tayi tace

"Har kun shirya? Ba zaki tsaya ki ci abinci ba?"

"A'ah Ammi sauri nake yi, kada na makara. Idan na dawo zan ci.."

"Toh Allah ya tsare.." ta ƙare maganar tana kallan hanyar ɗakinsu

"Ina Afaaf ɗin?" Kallan ɗakin tayi sannan tace

"Ammi wai bata da lafiya.." Kafin Ammin ta sake cewa komai Abba ya shigo cikin ɗakin da sallama. Dogon babban mutum wanda kallo ɗaya zaka masa ka san twins ɗin nan shi suka biyo, dan kuwa shi ma a kallan farko zaka gano kyawun da yake da shi. Dukkansu suka amsa masa sallamar kafin Little ya tafi ya rungume shi.

"Abba sannu da zuwa." Afrah ta faɗa.

"Yawwah Didi an shirya ne?" Ya faɗa mata sunan da yawanci en gidan ke kiranta da shi, wanda har shi ɗin ma wani sa'in ya kan kirata da shi.

"Ehh Abba.."

"Toh Allah ya bada sa'a.. A'ah ina Afaaf?" Ya tambaya shi ma. A wannan karon ma se da ta sake kallan ƙofar ɗakin nata sannan tace

"Abba wai bata da lafiya."

"Ji min ja'irar yarinya, sauƙin ze sameta ne tana daga kwance.. Kai Little maza je ka tasota ta sha magani sauƙin ze sameta acan." Babu musu kuwa Little ya zura da gudu zuwa cikin ɗakin. Da ƙarfi ya soma kiran

"Lulu! Lulu!!" Yana saka hannu ya soma yaye ƙaton blanket ɗin da ta rufa da shi. Duka ta kai masa sanda ya sake buɗe murya ya kira sunanta. Be kuma saurara ba ya ɗora da

"Abba yace ki fito mu tafi makaranta." Ya faɗa da muryarsa me daɗi duk da akwai ɗan tsami kaɗan a cikinta. Dukan da ta masa ne ya sanya shi kai hannu ya riƙe wajen yana kwaɓe fuska

"Allah se na faɗa wa Abba.." ya faɗa yana shirin yin gaba.Da sauri ta riƙo shi ta ɗan sassauta fuskarta kaɗan kafin tace

"Ka je kace bani da lafiya.." maƙe kafaɗa yayi yana faɗin

"A'ah.." Tsaki ta ja dan ta san in dae ta biyewa wannan yaron se dai faɗan da Abban ze nata ya ƙaru, hakan ne ya sanyata sakinsa kawai ta shiga shiryawa tana sake cika tana batsewa. Ta san halin Abba sarai, gudun kada ya gane ciwon ba na gaske bane ya sanya ta yin kalar tausayi da fuskarta hadda aro ƙwallar ƙarya cikin idanunta sannan ta fito, a hankali tace

"Abba sannu da zuwa" ta faɗa da muryarta da ta sake yin rawa fiye da yadda take. Cikin tausayawa yace

"Yawwah. Bari na ɗakko miki magani ki sha se ku wuce" Tun da dai ta san makaranta ce dole se taje tun da Abba ya saka baki ya sanyata faɗin

"A'ah Abba ai na sha, ciwon kai ne dama kuma ya warke"

"Toh madallah. Se kun dawo Allah ya tsare." Didi da Little kaɗai suka iya amsawa ita kuwa Lulu ta kasa faɗin komai dan gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan yadda zasu ƙarke ne da Gwani bayan ba tayi hadda ba, duk da yadda hankalinta ke a kwance da rashin yin haddarta ta amma yanzu se da ta ji wani tsoro tsoro na neman kamata tayi saurin basarwa tana sake cika tana batsewa. Ita kuwa Didi dariya kawai take yi a ɓoye dan kada Lulun ta gani yanzu se ta sake fusata.

"Yau ba zaki biyawa Masoyiyarta ki ba?" Didi ta faɗa tana kallan Lulu sanda suke dab da wuce gidansu ƙawar Lulun. Hararar gidan tayi kamar shi ne ya mata laifi sannan tace

"Ehh ɗin.." ta faɗa tana wuce gidan ma da sauri. Ba tace komai ba Didi se bin bayanta da tayi suka cigaba da tafiya. Sakin hannun Didi Little yayi ya koma kusa da Lulu yace

"Ki riƙeni kin ji!"

"Ba za a riƙe ba" ta faɗa tana maka masa wata uwar harara, dan yau ɗin gaba ɗaya haushin kowa take ji, musamman ma Little ɗin da kamar shi ne ya janyo mata, da yace bacci take da yanzu tana can a matsayin mara lafiya tana bacci hankalinta kwance. A yanzu kam dariya Didi tayi sosai ta cikin niƙab ɗinta, ta janyo hannun Little suka cigaba da tafiya. A haka har suka ƙarasa makarantar..



*** ***
Gida ne da ya amsa sunansa gida, ƙato wanda idan baka sani ba daga kallan farko zaka iya kiransa da ƙatuwar plaza. Haɗaɗɗen gida ne wanda tsayawa faɗar irin haɗuwar da yayi ɓata baki ne, dan kuwa anyi ɓarin kuɗi kamar me, an gina shi cikin tsari da ƙwarewa kamar ba a Nigeria ba. Ko daga Compound ɗin gidan kaɗai se an tashi kanka saboda yadda ta matuƙar ƙawatu da abubuwa kala kala se dai marasa hayaniya. Idan kuwa tun farko dama a cikin Compound ɗin ka tsinci kanka to fa ba zaka taɓa cewa a Nigeria kake ba. Ƙaton parlour ne da ya lamushe kujeru saiti uku a gefe guda na cikinsa, wanda anan ne aka zuba kayan ado da ƙawa aka ƙawata haɗaɗɗen parlourn da ko na shugaban ƙasa albarka, parlour ne da ya amsa sunansa parlour, parlour ne da a karan farko zaka iya kiransa da aljannar duniya saboda matuƙar haɗuwar da yayi. Akan ƙaramar kujera wani kyakkyawan babban mutum ne dake sanye cikin wata dakakkiyar shadda da kallan farko zaka mata ka san ta lamushe kuɗi na musamman, fuskarsa kuwa a kallan farko baka isa ka ƙayyade adadin shekarunsa ba, saboda yadda jin daɗi da kuma hutu suka lamushe kaso masu yawa daga cikin shekarunsa. Kyakkyawan babban mutum wanda aƙalla ya bawa 50 baya, idanunsa saye suke cikin glass me matuƙar kyau da tsada, wanda yake amfani da shi idan ze yi wani aikin da ya shafi Computer ko waya. A yanzu ma idanunsa na kan hamshaƙiyar waya ne yana dannawa cikin ƙwarewa. A nutse take takowa cikin parlourn, duk da yanayin shekarunta da suka tura hakan be hanata cin kwalliya kamar yarinya er shekara 20 ba, ƙafarta saye cikin wani hill shoe, sanye kuma cikin rantststiyar atamfa me shegen kyau da tsada, ta sha ɗauri irin wanda ake kira da ture kaga tsiya. A haka take takowa zuwa cikin ƙaton parlourn da kafin ƙarasowarta inda mutumin nan ke zaune ta ɗauki sakanni masu yawa. A nutse ta nemi waje ta zauna cikin kissa da kisisina tace

"Barka da wannan...


Read / Download A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

2 months ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

2 months ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album