Join Our WhatsApp Group

BA MAHAUKACI BANE Book 1 Complete Hausa Novel Document by BA MAHAUKACI BANE Book 1


BA MAHAUKACI BANE Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 30684



BA MAHAUKACI BANE Book 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 27, Nov 2023

Author: Binta Umar Abbale ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08089965176

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 164.34 kb

File Type: txt

Views: 1484+

Download: 750+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: BA MAHAUKACI BANE!
NA
BINTA UMAR ABBALE



Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Ubangiji mad'aukakin sarki. Tsira da aminci su 'kara tabbata ga fiyayyan hallita Annabi Muhammadu S.A.W


'Kir'kirarran labari ne wanda ba'ayi don a ci zarafin wani ko wata ba. duk wanda ya ga ya yi dai-dai da rayuwarsa to a rashin sani ne.


TSOKACI:
Kasancewar Ubangiji ya halliceka da ji da ga ni tare da wadatacciyar lafiya, to kada hakan ya sanya ka d'auki kanka daban da sauran wanda aka hallita da wata larura makamanciyar wannan, Ubangiji ba yanda baya zartar da ikonsa, kuma yanda ya so haka shi yake faruwa. tabbas bawa baya shiryawa kansa rayuwa face wacce ya riski kansa a ciki.



1
KANO STATE
GADAR SALGA Unguwa ce mai zaman kanta wacce take daura da kasuwar kurmi tsohowar kasuwa mai d'umbun tarihi a jahar KANO
Cikin rukunin gidajen yaku bayi na cikin unguwar. Matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha tara Zuwa ashirin zaune a kan kujera 'yar tsuguno da tarin wanke-wanke a gabanta tana wankewa tare da kifewa a cikin wani babban kwando. wanke-wanken take tun k'arfi da alamar sauri a tare da ita.
Cikin rashin kintsi! Saliha Ta iso inda take, ba tare da tunanin komai ba ta kurma mata wani irin ihu! a cikin kunnuwanta! A Zabure! ta juyo har farantin dake hannunta yana fad:uwa a kasan gurin, idanuwanta sukayi rau-rau kamar zata fashe da kuka ta fara magana cikin yanayin na 'bacin rai! tare da yanayin hallitar da Allah yayi mata tace."Saliha menene haka."?

Cike da rashin mutunci tace." Yo idan ba haka akayi miki ba ai ba za kiji magana ba, yaushe zan dinga wahalar da kaina gurin kiran sunanki ai ihu! kawai shi ya cancanta ayi miki tunda kunnuwanki a toshe! suke."

Girgiza kanta kawai tayi tare da mayar da kanta 'kasa tana cigaba da wanke-wanken dake gabanta.

A fusace! tace."Au! Shahida mahaukaciya kika mayar dani ina miki magana kinyi min banza to bari naje na shedawa wacce ta aiko ni kiran ki.

Hanci ta shak'a ta sanya hannuna ta goge gumin goshinta cikin yanayin magana irin ta kurame! tace."Saliha kina dai ganin wanke-wanken nake ko."

Saliha ta watsa mata harara da fadin." To ba zaki bar wanke-wanken ba ki tashi ki je kiran da take miki ba."

A hankali ta ajiye sosan dake hannunta ta mike tsaye hanya ta nuna mata da hannu da k'arfi ta ce"Wuce muje." girgiza kanta tayi rai a b'ace tayi gaba Salihan ta rufa mata baya.


Baba Asabe tana zaune a tsakiyar rumfa tana d'aura gishiri su ka yi sallama Saliha kai tsaye cikin uwar d'aki ta shige tabi lafiyar gado. Ita kuwa tsugunuwa tayi a gabanta cike da ladabi tace."Baba gani Saliha tace kina kira na."

Ta ajiye d'aurin gishirin ta janyo jakarta dake gefe kudi ta dauko daure a leda ta kalleta da fadin." Bakin asibiti za ki je ki dauko min man gyda tun shekaran jiya ya k'are anata zuwa nema." bakinta kawai take kallo, nan ta fahimci abinda take nufi, tunda ba wai da 'karfi take maganar ba, shiyasa ta tsirawa bakinta ido, ta na ji amma ba sosai ba, shiyasa wani lokacin idan ana magana take bin bakin mutum. nan take fahimtar komai.

Cikin saurin magana da yanayi na harshenta ta ce." Ban gama wanke kwanukan ba."


Ta ce."Ki ajiye idan kin dawo ki k'arasa ai da sauran lokaci."

Ta amsa da "To" Tare da mi'kewa. uwar dakin ta shiga domin dauko hijabi nan taga Saliha a kwance da waya a hannunta tana game.

Girgiza kanta kawai tayi ta bude ma'ajiyar kayanta ta dau'ko hijabi tasa a wuyanta ta fito falon.
Ta kalleta da fadin."Dubu arba'in da hud'u ne man gyada galan d'aya manja ma galan d'aya kafin ki isa zan kira Garba a waya na sheda masa zuwanki ya tari a daidaita sahu ya sanya komai a ciki.

Tace."To shikkenan Baba sai na dawo." Tace." Ki kula sosai da kudin hannunki yau Juma'a akwai turmutsutsu na jama'a."

Kud'in ta ri'ke da kyau da fadin." Zan kula insha Allah.

Cikin nutsuwa take tafiya har ta fito bakin titi can tsallake ta
hango mutumin ta zaune a 'karkashin tsohuwar motar da yake zama tare da tarkacen kayansa na mahaukata!

Girgiza kai tayi tana me tsira masa ido yana kwance kan wani tattararran buhu ya takure jikinsa guri daya jikinsa duk yayi fururu! kasancewar lokacin sanyi ne shiyasa al'amarin ya tu'azzura.
Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke tana sake jin tausayinsa na bin ilahirin jikinta, hakika da tana da yadda za tayi da ta taimaka masa ya daina kwana 'kar:kashin mota duk yanayin da ake ciki na ruwa da iska anan yake wanzuwa tsayin watannin da yayi a cikin unguwar tasu.

Cike da tsantsar tausayinsa ta d'auke kanta daga inda yake ta fara laluben abun hawa Juma'a ce shiyasa abubuwan hawa sukayi k'aranci a kan titin.

Ihu! da hargowar yara ya sanya da sauri ta mai da kanta gurin, nan taga yara masu yawa sunyi masa rumfa suna tsokanarsa sai ihu! suke tare da fad'in "Baban- baba kazami! Baban -baba mai annakiya Baban-baba mai kashi a wando."! Shi kuma
Yana zaune yana kallonsu fuskarsa a sake kamar koda yaushe idan yara suna tsokanarsa sai ya yi ta murmushi koda kuwa cikinsu za'a samu masu jifansa da duwatsu! ba zai yi 'ko'karin 'kare kansa ba.

Ranta ya 'baci mutuk'a ganin yanda manya mutane ke wucewa wasu a kasa wasu abubuwan hawansu amma a cikinsu an rasa wanda zai tsawatarwa da yaran akan abinda suke.

Ba tare da tayi tunanin komai ba ta tsallaka titin kai tsaye gurin ta nufa.

Tana zuwa cikin 'bacin rai irin na kurame take musu fad'a tana korarsu........Sai suka kwashe mata da dariya suna nuna ta da hannu da fadin." Mu bama jin abinda kika cewa ke din kurma ce ko kuma bebiya?"

Abun yayi mata ciwo sosai ta sake d'aga muryarta cikin yanayin saurin maganarta da yanayin hallitarta take gargadinsu da fadin." Ita din kurma ce kuma haka Allah ya halliceta idan da wanda ya isa ya sauya mata hallita a cikinsu sai ya d'aura aniya.

Suka dinga kyalkyala mata dariya sunayi mata ihu! kawai sai ta durk'ushe a gurin ta fashe da kukan 'bakin ciki a wannan lokacin ledar kudin dake hannunta ta fad'i ba tare da 'bata lokaci ba wani matashi dake can tsallake yazo ya d'auke yayi gaggawar watsa yaran ya gudu da kudin a daure a leda.


Ido kawai ya tsira mata tana tsugune a kusa da shi kanta a tsakanin kafafunta sai kuka take.

Sosai yake jin zafin kukanta a cikin zuciyarsa to amma 'kudirin dake cikin zuciyarsa shi ya hana shi rarrashinta tun ba yau ba ya san da yarinyar a duk sanda zata gan shi a hanya ko a gurin zamanshi yana hankalce da irin kallon da take masa 'kwayar idonta kadai ita ke nuna masa da cewar ta damu da shi, duk da cewa wata magana bata ta'ba had'asu ba to amma ya yi imani da cewa ita d'in mai 'kaunarsa ce, Abinda tayi a yanzu shine ya tabbatar masa da zarginsa.


A nutse yace."Ki yi hakuri kinji ko." Shiru bata d'ago kanta ba, jim yayi yana nazari wani 'karamin icce ya d'auka ya zungureta dashi.

a firgice ta d'ago kanta idanuwanta sunyi fululu fuskarta har ta kumbura! Tsigar jikinshi ce tashi ya mayar da kanshi kasa yana wasa da icce hannunsa.

Tsaye ta mike tana karkad'e jikinta gabanta sai dukan uku-uku! yake!

Ta kalli gabas ta kalli yamma kudu arewa sai kawai ta d'ora hannu a ka ta kurma ihu! tare da fadin." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una!

Ya mike tsaye da sauri yana kallonta so yake yayi magana amma jama'ar da suka fara taruwa a gurin suka hana shi idanuwanshi kawai ya zuba mata.

Haladu wanda ya kasance ma'kocinsu ya 'karaso gurin da fadin."Ke Shahida menene? me kike a gurin wannan mahaukacin."?

Cikin kuka tace." Zuwa nayi na kori yaran da suke tsokanarsa shine suka sace kudin kuma Baba Asabe ce ta aike ni bakin asibiti na saro mata man gyada."

Yace."In ban da shashanci irin naki da hauka yaushe zaki iya watsa yaran da suka dad'e suna tsokanar wannan shashashan mutumin nan wanda bai san ciwon kansa ba, shashahar banza kawai gashinan garin hauka kin janyowa mutane asara to kada kiji da wai sai na fad'a mata yanda akayi komai ya faru."

Tana kuka take fadin." Don Allah kayi hakuri kada ka fada mata ." Tsaki yaja ya gyara zaman daddumar dake kafad'arsa ba tare da yace komai ba ya bar gurin.

Ganin haka yasa mutanan dake gurin suka watse.
Komawa yayi ya zauna tare da rungume hannuwansa a kirji, Ta kalleshi da fadin." Baban- Baba Don Allah baka ga wanda ya daukar min kudi ba?"

Girgiza kansa yayi alamun bai gani ba, hawaye suka sake zubo mata tace."To ko zaka duba min cikin takarcen kayanka ko Allah zai sanya suna ciki."

Beyi mata jayayya ba ya fara dudduba tsummokaran dake gurin yana musu filla-filla babu komai sai tarin ledoji na pure water da sauran robobin lemo da yake tarawa.

Ba tare da tsoron komai ba tazo ta tsuguna daf dashi tana sake hargitsa ledojin babban burinta ace taga ledar dake d'aure da kudin Baba Asabe.

Sosai yake mamakin rashin tsoron yarinyar da yawa yara duk fitsararsu daga nesa suke tsayawa su tsokane shi, basa iya kusantar gurin da yake duk da cewa baya doke-doke amma hatta da manya basa iya zuwa inda yake amma abun mamaki ita ba taji tsoronshi ba tazo ta tsuguna kusa dashi duk da ta san cewa shi din ba mai cikakken hankali bane.

Gabadaya jikinsa ya mutu wata iriyar kasala da kaunar yarinyar suka sanya shi kasa dauke idonsa daga kanta.

Ta kalleshi da jajayen idanuwanta da karfi tace."Babu kudin sun sace ban san wane irin hukunci Baba Asabe za tayi min ba."

Da yake ya fahimci kurma ce ita sai ya girgiza kansa ya had'e tafikan hannayensu guri guda alamun yana bata hakuri.

Tsaye ta mike tana gyara zaman hijab dinta ta kalli hagu da dama babu motar data sako kai da sauri ta tsallaka titin tana had'a hanya.

Cike da tsantsar tausayi yake kallonta har ta 'bacewa ganinsa, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi tare da sunkuyar da kansa 'kasa yana me cigaba da nazari da tunanin yanayi na rayuwa!

Tsoro da fargaba! ya sanya ta kasa komawa gidan sai kawai ta samu kan dakalin wani gida ta zauna tana kallon masu wucewa da nufin zuwa massalaci domin gabatar da sallar juma'a.
Har aka sakko daga massalaci tana nan zaune a gurin, Haladu yazo ya wuce ta yana girgiza kansa. itama kai ta girgiza tana kallonsa har ya karya kwanar layinsu, k'wafa tayi tare da d'auke kanta ta san duk wannan saurin da yake yana so ya je ya kai gulmar abunda ya faru babu shakka sai ta dauki mataki a kansa mutukar ya janyo mata 'bacin rai! dama sun saba tafkawa dashi a duk sanda yazo sayan abinci gidan nasu.


Da yake gidan ya kasance gidan gandu( na kowa da kowa) ya sanya ba tare da neman iso ba ya kutsa kansa ciki tare da sallama a bakinsa.

Ta amsa tare da fitowa daga kicin da wani kafcecen ludayi na juya miya a hannunta.
Ta ce."A'a Haladu har an sakko kenan?"
Ya amsa da "Eh wallahi" kai tsaye gurin zamansu ya nufa ya zauna tare da cire hular dake kansa.

Ta ce." Gurasa da miya zaka saya ko kuma shinkafa da miya?"

Hamma! ya saki ya sosa kansa da fadin." Yau dai shinkafa zan ci domin na gaji da cin kayan fulawa kwana biyu idan nazo bayan gida sai na rirri'ke kan famfo nake samun damar yi watarana har ihu! nake kurmawa! kai basir mugun ciwo ne wallahi."

Saliha dake yanka salak ta fashe da dariya tana kallonsa, Fuskarsa ya murtuke yana muzurai! Ita kuwa sai tikar dariya take sai da tayi mai isarta sannan tayi shuru.


Sai da ya kai loma uku na abincin sannan yace." Uwar towo ina ja'irar yarinyar nan ta shiga ne?"

Baba Asabe ta ce." Shahida kake nufi?" Yace."Eh kwarai kuwa." Tace."Kaga tun kafin tafiya massalaci na aike ta bakin asibiti shiru har yanzu bata dawo ba.

Girgiza kansa yayi da fadin." Can na ganta gurfane gaban tsohon mahaukacin nan dake bakin titi tana kuka koda na tambayata sai take sheda min cewa...........Duk ya kwashe komai ya fada mata.

Baba Asabe ta dafe kirjinta tana salallami! Ya ce."Wallahi kuwa ai wannan kudi kawai ki fitar da ranki dasu domin kuwa nayi imanin da cewar babu su an sace."

Jiki a sanyaye ta zaune bakin rijiya da fadin.'' Amma kuwa wannan yarinya ta cuce ni dubu arba'in da hud'u ne wace irin kaddarace ta ritsa dani a yau."

Ya ce." Hukunci mai tsauri zaki d'auka a kanta domin kuwa ita tayi ganganci har aka sace kudin idan ba haka ba mai zai sanya ta gurfana gaban mahaukaci irin Baban-baba wanda bai san kansa ba."

Girgiza kai tayi cikin 'bacin rai tac e."Haladu ni fa ban yarda da wannan mutumin ba, wallahi ban yarda cewa mahaukaci bane tunda duk abun masu hankali yana aikatawa bayan haka kuma sallah bata wuce shi bana tamtama shine ya sace min kudina.


Dariya yasa da fadin." In banda abinki Uwar towa ya za'ayi ki kira Baban baba mai hankali in da yana da hankali ba zaki gan shi a lalace ba. Sallah kuma da ki ke magana dayawa mahaukata irinsa suna daburawa amma ki daina sanya Baban-baba a cikin masu hankali.

Tsaye ta mike da fadin." Haladu dole naje da kaina na duba kudina yau koni ko shi duk haukansa wallahi na fi shi sai ya fito min da kudina 'barawo kawai
"

Tsaye ya mike tare da zaro kudi daga aljihunsa ya mika mata da fadin." To ni dai ga kudinki zan shiga gida na huta zuwa yamma zan shigo domin naji a'ina aka kwana.''

Kudin ta kar'ba tasa cikin lalitar dake d'aure a kugunta da sauri ta shiga daki ta fito yafe da mayafi.

Saliha ta kalleta da fadin." Baba kada kije ki tunkari mahaukacin mutumin nan kada garin neman gira a rasa ido ni dai na fada miki.

"Sai naje d'in ba zan lamunci wannan al'amarin ba domin kuwa ban yarda da asara ba." Tana 'kare maganarta cikin zafin nama ta kama hanyar fita da kud'irin zuwa yiwa Baban Baba A tare a tare.

Tunda ta hango ta gabanta yake faduwa sunkuyar da kai ...


Read / Download BA MAHAUKACI BANE Book 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
1 Comments On BA MAHAUKACI BANE Book 1
avatar
arfat-aliyu

5 months ago

Reply

Masha allh

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album