Join Our WhatsApp Group

PAPI NE Complete Hausa Novel Document by PAPI NE


PAPI NE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 61752



PAPI NE

Reading Time: 5 Hours

Added On: 03, Jan 2024

Author: NoorEman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07082281566

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 339.8 kb

File Type: txt

Views: 725+

Download: 779+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: 🍓🍓PAPI NE!🍇🍇

*Second edition*


_by Noor Eemaan_📚✍️


Wattpad
@NoorEemaan


In the name of Allah most glorious, most merciful.


Wanna labarin ƙirƙirarren labari ne, ban yarɗa a juya min shi ta ƙowacce siga ɓa idan ƙunne ya ji....



Alhamdulillah dukkanin yabo sun taɓɓata ga ubangiji mai sammai da ƙassai, a ƴau gani tafe da saɓon novel har ɓiyu ƙamar haƙa *PAPI NE DA ƘƳAUTAR KODA* ban san ya zan yi muƙu ɓayanin books din ba, sai dai shaƙƙa babu zaku ji ɗadin books ɗin in sha Allah, kuɗai ku cigaba da ɓina ɗan jin ƴanda ɗoguwar tafiyar da zamuyi ɗani ɗaku zata ƙasance. Banyi alkawarin yin typing kullum ba...


Wanna Littafin Sadaukarwa ne Gabadaya ga dukkanin Maraya(orphans) Dana gidan Marayu da ma ko ina Suke a duniya...



Page1-2

*SOKOTO STATE*

Misalin k'arfe takwas na dare ne, unguwar shiru tamkar babu halittu a cikin ta, wanda hakan baya rasa nasaba da ruwan saman da ake tsulawa tamkar da bakin kwarya, mafi akasarin gine-ginen unguwar na marasa karfine domin mutum na ganin tsarin gidajen unguwanin zai tabbatar da hakan.

A hankali wani yaro mai kimanin shekaru goma sha biyar a duniya ke tafiya, duk da uban ruwan da ake tsulawa hakan bai dame shi ba, ga wurin fakewa da yawa amma bai yi hakan ba. Duk da kananun shekarun sa yana da tsayi sosai, wanda mutum zai iya tunanin ya kai irin shekaru ashirin din nan.

Wasu kod'add'un jeans da riga ne a jikinsa sai wani snickers a kafarsa, yana da k'yau, da alama idan ya zama babban saurayi za a yi k'yak'yyawan gaske da yanmmata zasu yi ruɓuɓɓin sa, yana daf da shan kwanar da zai saɗashi da layinsu ya ji kukan jariri, cigaɓa yayi da tafiyar sa ba tare da ya ko kalli inda kukan ke tashi ba...

Har ya kai kofar gidansu wanda ya kasancewa na zallan jar ƙasa, ya ji Hankalin sa ya kasa kwanciya domin tunda ya taho sautin kukan jaririn ke amsa kuwwa a kunnuwan sa.
Runtse ido yayi kana ya juya da sauri har da guɗun sa....

Abun mamaki har yanzu kukan jaririn ke tashi, A hankali ya karasa gaban kwallin da jaririn ke ciki add'ua dauke a bakinsa yayinda wani tsoro-tsoro ke k'ok'arin shigar sa, sai dai yaki ɓawa tsoron daman samun muhalli a zuciyar sa...

Har ya kai hannu cikin k'wallin da niyyar daukar babyn, sai kuma ya sauke hannun, ya fara k'ok'arin daukan k'wallin gaba daya, a tunanin sa idan yaje kofar gida ya buɗe, faduwar gaba ce ta saukar masa dai-dai lokacin da kwallin ya rabe kansa sak'amak'on ruwa daya gama jika ta yayinda k'yak'yyawan baby'n yayi gefe yana daf da shan kasa...

Cikin wani sauri da bai san yana da shi ba ya cafko ta, k'asancewar akwai cak'walli sosai a wajen yasa ya fadi kasa, runtse idanun sa yayi sak'amak'on ɓugewa da kansa yayi jikin wani dutse, sai dai ya rike baby'n gam gam a jik'in sa, yama rasa wani jinsi zai bawa wanna baby'n shin _jariri ne ko jaririya ce_ ?
Sai d'aya dauki tsawon mintuna goma kana yaji kansa ya dan daina ciwon, ya mik'e tare da baby'n a jikinsa wanda zuwa lokacin ruwan ya fara tsagaitawa kadan da kadan, Kara kallon kwallin yayi yaga ta dame da kasa saboda tsananin jikewa, bayan haka babu komai a tare da baby'n domin ko riga babu a jikinta sai jini da bai gama fita a jikin ta ba har yanzu da alama haihuwar yau ce...

Cikin tsananin tausayin baby'n dake ratsa zuciya da jikinsa ya mike ya fara tafiya bayan ya shigar da ita cikin jikin sa, a dalilin sa na son kare ta daga ruwan saman dake dukan naked body d'inta har yanzu, duk da dai babu abinda rigar tasa ta karewa baby'n domin a jike take sosai, baby'n kuwa wani damke fatar k'irjinsa sa tayi tana k'ok'arin tsotsa, wani sabon tausayin baby'n ne ya sake dirar masa...

Cikin sauri-sauri gudu- gudu yake tafiya har ya isa bakin kofar gidan nasu, tura kofar gidan yayi wanda ya kasance na zallan langa langa ne, shiga yayi kana ya sanya sakata...Dakuna biyu ne kacal a gidan sai bandaki, daga can gefe akwai wasu manya manya dutsina uku, da kuma wata tukunya akai wanda aka kwashi tuwo a ciki da alama nan ne maɗafa, tsakar gidan ba wani babban bane, kana jar kasa ce wanda ya sake ca'bewa saboda ruwan saman da aka yi, ga robobi reras a jira cike da ruwa da alama ruwan sama aka tara cikin su...

Daki dake a farko ya nufa, hadi da daga labulen ya shige... wata tsohuwa mai k'imanin shekaru hamsin da tara zaune kan gadon ta irin na bunun nan ga tudu da laushi, wani kallo ta jefa masa kana cikin fad'a ta fara cewa......



*Ya kuka ga wanna labarin? Shin in cigaba ko in dakata? yawan comment dinku ne zai sa na cigaba da suburbudo muku shi...*✍

Don't forget to share
Comment and
Vote me on wattpad @NoorEemaan


NoorEemaan na muku sahihiyar kauna🥰



🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

_by Noor Eemaan_✍️📚




Wattpad
@NoorEemaan



Tnx all naga comments dinku da yawa hakan ya bani k'arfin guiwar typing, Sannan mutane da yawa sun tambayeni cewa menene ma'anar *"PAPI NE"* ? TOH Papi dai another name ne da diya kan kira uba da shi...

Page 3-4


" Kai Nu'aymu ka fita idona in rufe fa, bazai yu kullum ka dinga tayar min da hankali ba, dana Ahamadu bai taba sani magana ba" sai kuma tasa kuka tana cewa "Allah ya jikan ka Ahamadu, albasa bata bi halin ruwa ba" ta karasa tana fyato majina...

Kallon ta ya tsaya yi yana mamakin yawan rigimar ta, domin ba wani tsufa mai yawa tayi ba amma dukkanin wata alama na rikicin tsufa ya riga ya gama bayyane kansa.

Runtse idanun sa yayi wanda hak'an ya zame masa tamkar dabi'a, kai kace wani babban saurayi ne.
"Ooh Kaka rigima, nifa ba yaro bane da kullum zaki dinga sa min ido kan lallai sai na dawo gida da wuri, sannan sunana ba Nu'aymu bane, Nu'aym nake!"

"Kai dallah rufamin baki, ina abun yake? Idan kai ba yaro bane toh meye kai dan gidan ku, yaushe ma aka yaye ka?"

Bai kara kula ta ba, saboda baby'n dake tare da shi, cikin lalluma ya fara cewa"haba matar yi haku'ri, in sha Allah zan dinga k'ok'arin dawowa gida da wuri kinji?"

Tabe baki tayi kana tace "toh Allah yasa" Nu'aym na k'ok'arin magana baby'n ta canyare k'uka, wata zabura Kaka tayi ta haye gadonta ta lafe kuriyar dakin kana cikin tsananin tsoron da rudu ta fara cewa "Nu'aymu aljana jaririya cikin gidan mu innalillahi wa innah ilaihi raju'un, mun shiga uku" ta karasa tana zaro ido hadi da sake shigewa jikin gadon.

Wata dariyar mugun ta ya saki, cak! Kaka ta tsaya da k'ukan nata tana cewa "ya rahamanu ka taimake mu, shikenan aljana ta shiga jikin Nu'aymu jikana" jikinta har wani karkarwa yake, yayind'a ta dinga karanto duk add'ua daya zo bak'inta, har add'uar shiga bandaki ta karanto, saboda tsananin rudewa.

sam bata lura da baby'n ba, saboda bata da wani girma hak'an yasa kai tsaye mutum bazai fahimci haka ba.

Gimtse fuskar sa yayi ganin bilhakki da gaske kuka take, kana a hankali ya ciro baby'n daga cikin jikin sa, wanna karon kaka ta fi shiga rudu da tsananin firgici...

Bakin ta rawa yake alamun tana son furta wata kalma, amma ya gagara, kan gadon ya kwantar da baby'n hadi da cewa "relax kaka, baby'n dan Adam ne k'amar mu, kiyi mata wanka ina zuwa" ya karasa yana ficewa domin sanyi sosai yake ji so yake yaje ya sanja kayan jikinsa...

Sai a lokacin bakin Kaka ya bud'e ta fara cewa "wallahi Nu'aymu baka isa ba, kazo ka dauk'e wanna aljanan jaririya daga kan gadona, wanna 'ya karamar diyar da wanna uban madarar kyau kace mutum ce, san...." Kukan da baby'n ta sake sanyawa mai matuk'ar taba zuciya ne ya katse mata tunanin ta.... Take wani tausayin baby'n ya fara ratsa ta, add'ua dauke a bakinta ta dauki baby'n hadi da runtse idanun ta, baby'n sai girgiza take a hannunta, sak'amak'on rawar da hannun ta ke yi...

Ta kai tsawon mintuna goma a haka kana ta bud'e idanunta ganin babu abinda ya sameta, kwantar da baby'n tayi kana ta sauko daga kan gadon tana waiwayon baby'n still cikin tsoron domin gani take tamkar halittar K'yak'yyawar baby'n zai iya sauya wa...

Sif (wardrobe) dinta da ko murfi babu kuma tsahon yayin nan ne ta nufa, wani zanin ta ta dauko ta lullube baby'n da shi kana ta janyo wata tsohuwar stove (risho) ta kunna kana ta dauko wata sabuwar tukunyar ta dake da sauran sabunta ta, saboda tsananin son da take wa tukunyar shiyasa bata dorawa a wuta, cikawa tayi da ruwa ta dora, babu jimawa ya fara tafasa, dan sirkawa tayi da ruwan sanyi kadan, kana ta dauko wani babban roba, hadi da dauko baby'n ta fara yi mata wanka da wani sabulun ta dan saba'in da take ta lallaba saboda sosai take son kamshin sabulun, sosai ta gasa wa baby'n jiki kana ta sake nada ta da zani ta kwantar da ita kan gadon, Sif dinta ta dauko wasu riga da wando masu dan kwari data siyawa diyar kawarta data haihu, kan cewa jibi zata je musu barka, daga kayan tayi tana kallon su kana ta fara cewa "sai ka biya ni kudina, domin naira na gugan naira har dari takwas na cire na siya, atoh" ta karasa Cikin fada tamk'ar Nu'aym din ne a gabanta.

Sosai yarinyar tayi kyau cikin kayan, wani zanin ta sake dauk'owa ta lullube dukkanin jikinta, kana ta cigaba da mitar Nu'aymu zai d'awo ya same ta, kawai ya dire mata 'ya ba tare da yace komai ba ya fice...

Kwantar da baby'n tayi kana ta shiga goge ruwan daya zuba a kasa, fitar da robar ruwan wank'an waje tayi ta zubar kana ta fara juye ruwan saman data tara cikin robobi cikin wata tsohuwar duro dinta, tsakar gidan ta fara sharcewa, kana ta nufi wajen rariya ta fara dauraye kafarta, wanda yayi d'aidai da sallamar da ya yi.

Amsawa kasa kasa tayi, ita ala dole fushi take dashi, bai kulata ba ya nufi dakin kakan, hak'an ya kara bak'anta ranta "wato Nu'aymu saboda ka raina ni shiyasa kayi ficewar ka batare da ka ce min komai ba, saboda ga marainiyar wayon ka ko?" Tun daga tsakar gidan take wanna maganar har ta cimmasa a daki"

"Wato ga sabuwar kamu ko, ina maka magana kayi min shiru?"

"Dan Allah kaka kiyi Shiru, zan yi miki bayani komai"

D'aidai gaban sa ta tsaya ta rike kugu tana cewa "bazan yi shiru ba, nace bazan yi shiru ba dan gidan ku, tukunna ma yar waye kace ka dauko babu ko riga a jikinta, ga ta sabuwar haihuwa"

"Zanyi miki bayanin komai kamar yadda nace, ga madara irin na yara na siyo mata sachet daya ki bata da karamin feeder na siya, ga kuma awarar ki cikin ledan nan, sai da safe" ya karasa yana ficewa...

'Ka dawo ka dauke wanna yarinyar daga kan gadona, kana nufin a nan zata kwana ban san wacece ba" ta karasa tana binsa har kofar dak'in sa, sai dai ya rufe dakin nasa, kwankwatsa dakin ta shiga yi yayi shiru a dakin yana dariyar hadi da cin tuwon sa miyar kuka hankali kwance...
Bayan ta gaji da buga kofar ta koma dak'in ta tana sababi...

Ruwan zafin daya yi ragowa ta hada mata madarar da shi, sanya wa baby'n feeder'n tayi a baki ta bata fuska taki sha, cigaba da bata tayi har ta fara tsotsan... Tas baby'n ta shanye feeder'n, ga wani gumi daya tsatsafo mata saman goshi, tausayin baby'n ya kama kaka d'omin yanzu hank'alin ta ya dan kwanta saboda babu wata alama daya nuna cewa wanna baby'n aljana ce...

Bayan ta kwantar da ita ta janyo ledar awarar ta ta fara ci tana tunanin rashin mutuncin da zata yi wa Nu'aym go'be bayan ta gama ta fita hadi da dauro alwala, kan gadon ta kwanta tana karanto add'uar kwanciya bacci, domin kaka akwai ibada...Babu jimawa bacci ya dauke ta

2:30am
Baccin su suke hankali kwance, sai kawai k'uk'an baby'n ya karade dukkanin ila'irin gidan, yamutsa fuska kaka ta yi domin ba kadan ba take jin dadin baccin ta, tashi tayi zaune ta fara lallaba baby'n, sai dai ina tamkar kara cewa cigaba da kuka take...

Yana cikin baccin sa yaji tamkar cikin kunnen sa take yinsa, mikewa yayi ya bud'e kofar dakin sa ya fita, yana zuwa ya dauk'e ta izuwa dakin sa ba tare da ya sake cewa komai ba, jijigata yake sai dai taki yin shiru, labb'ansa na kasa ya sanya mata a baki, take ta kama ta fara tsotsa, wani zafi-zafi ke ratsa kwanyar sa a sak'amak'on tsotsan da take yiwa labb'ansa, k'ok'arin zarewa yayi saboda zafi da ya ishe shi, ta tsalla kuka, saurin mayar mata yayi, ya cigaba da jure zafin har tayi bacci, sauki ajiyar zuciya yayi kana ya kwantar da ita kan gadon sa da bai fiye girma da taushi ba, kwanciya yayi shima, yana add'uar Allah yasa kar ta tashi kafin safiya...





Har yanzu bamu shiga cikin labarin ba, just bear with me habeebt's, sannan Ku yi manage wallahi nayi typing ya goge, raina a bace yake😔


SHARE✔
COMMEN✔
VOTE✔
EDIT❌

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
Written by
Noor Eemaan

Wattpad
@NoorEemaan



This book this dedicated to all orphans in the orphanage home.

Page5-6

........Ciƙin ikon Allah kuwa bata ƙara tashi ba har gari ya waye, sai takwas na safe Nu'aym ya fito daga dak'insa baby'n dauk'e a hannun sa.

Ƙo ina tsaf tsaf alamun an gyara, gama shatin tsintsiya kwance kan jar kasar, d'aga gefen wajen mad'afa kuwa kaka ce tsukunne ta dora musu d'umammen tuwon su da yayi ragowa jiya, "my kakus ina kwana" ya fad'a cikin tsokanar ta.
Shan toka/kunu kaka tayi ba tare da ta bashi amsa ba, kan yaloluwar tabarman su ta nufa da kwanon tuwonta ta fara ci....Dariya ya saki d'omin ya san dole dama za a yi hak'an
Kan tabarman ya zauna gefen ta ya kara cewa "haba tawan kiyi haku'ri kinji"
Sai data kai wata katukar loma kana tace" k'ullum sai ka gama yin son ranka sai ka wani ce in yi haku'ri, toh baru kaji a yau sai ka fitar da yarinyar nan daga gidannan bazata sake kwana a nan gidan ba, ko tausayin ta baka ji, jaririya da ko cibiyar bai gama nuna ba ka dauko, nama rasa wacce uwa ce mara tunanin ta baka 'ya sabuwar haihuwa har ka kawo ta gidan nan cik'in ruwan sama, fisabilillah fa" kaka ta karasa maganar cik'in masifa kana cik'in daga murya.

Jikinsa yayi sanyi, d'omin d'uk rigimar su yana matuk'ar son kakar sa haka itama. Cik'in muryar daya san zata tausaya masa yace "ki gafarceni k'aka, banyi da niyyar bata miki rai ba, sannan tsananin tausayin wanna baby'n yasa na har na d'auko ta a hanyar dawowa na daga gareji Cik'in kwali...."
"Cik'in kwali kuma kuma Nu'aymu?" Kaka ta ce tana tsame hannunta daga Cik'in tuwon
"kwarai kaka...


Read / Download PAPI NE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album