Join Our WhatsApp Group

RAYUWA DA ƘADDARA 1 Complete Hausa Novel Document by RAYUWA DA ƘADDARA 1


RAYUWA DA ƘADDARA 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33156



RAYUWA DA ƘADDARA 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 13, Oct 2023

Author: Aisha Sabo Lemu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 816 776 8704

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 170.48 kb

File Type: txt

Views: 578+

Download: 247+

Last download: 15 hours ago

Description/Story: [10/4, 8:37 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA!* *Arewabook@ayshadansabo*

_©️Ayshat Ɗansabo lemu_

*Paid book 08167768704*

*Ina mai farawa da yabo tare da ɗinbin godiya ga Allahu (SWT) da ya bani ikon fara wannan rubutu,sannan ina miƙa godiya ga tarin makaranta littafaina waɗanda suka yi mini uziri tare da tayani farin ciki akan ƘADDADAR ZOYA da ya zama bai kammala ga makaranta ba ,a sakamakon saye labarin da aka yi domin a juyashi ya zama film.Sannan ina muku albishir da cewa wannan labari na RAYUWA DA ƘADDARA zai zo muku da tarin faɗakarwa da ɗibin darussa na rayuwa kala-kala,domin kuwa labari ne da zai taɓa ɓangarori da dama.Sannan zai nishaɗantar tare da sanyaya zukatan makarantansa da sassanyar soyayya mai tsayawa a rai,don haka kar ku bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta.Sannan kuma babban abin farin cikin shi ne, na sauƙaƙa kuɗin sayen wannan labari,duba da yanayi da ake ciki na matsewar tattalin arziƙi,domin ina ma kowa sha'awar ya shigo cikin tafiyar,don haka Regular zai zo muku akan 400 kacal VIP kuma 700.*

*GARGAƊI*

*Wannan labari da dukkanin abinda ya ƙunsa mallakin marubuciyar ne,don haka ban amince a juya min labari ko sauya shi ta kowa ce iriyar fuska ba.Ban amince a karanta min labari a kowani kafar sadarwa ba tare izinina ba,yin hakan babban kuskure ne,don haka a kiyaye.*


*Chapter 1*

*Free page*


*SHIMFIƊAR LABARI...*


*GARIN ZAZZAU.*

Ita dai masarautar Zazzau tana daya daga cikin muhimman masarautun kasar Hausa da ma yankin Afirka ta yamma.
Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni da cewa, Zazzau wata daɗaɗɗiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun ɗaruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci.

Yadda kalmar ‘Zazzau’ ta samo asali
Tushen wannan kalma ta ‘Zazzau’ yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin kasar ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo’, wato kasa mai laka, ba mai rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro.

A wani kaulin kuma ‘Zazzau’ na nufin wani takobi, wanda ja-goran jama’a yakan dauka ya jagoranci jama’a a wajen yaki. Mai daukar wannan takobi ba sarki ake kiransa ba, a wancan lokaci ana kiran sa ne ‘Madau-Zazzau’, wato ‘Mai Dauke da Zazzau’.

Asalin Kalmar Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa Turunku, wadda kanwa ce ga Sarauniya Amina

Bambancin Zazzau da Zariya shine,Zazzau masarauta ce, wadda ta kunshi dukkan ƙasashe da garuruwan da ke bin masarautar. Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da kasashe suna kawo wa sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni.

Kafuwar Masarautar Zazzau
A zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu wani addini da ya shigo, sai al’adu ko rayuwa irin ta maguzanci. Da kuma ƙaura daga wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a kokarin neman wajen da zai zauna ya sami ingatacciyar rayuwa. Mafi yawan ayyukan da jama’a kan yi a lokacin su ne, noma da kiwo.

Wannan lokaci ne kuma masana tarihi ke kira zamanin ‘Zo-zo’, wato zamanin maguzanci, wanda ya kasance tun kafin shigowar addinin musulunci.

Lokacin da al’umma suka rika taruwa, suna samun shugabanci, har sarakunan Haɓe suka fara mulki, aka samu kafuwar Hausa Bakwai, wato zuri’ar Bayajidda da Sarauniya Daurama.

Kuma Zazzau na daya daga cikin ƙasashen da aka ba ’ya’yan Bayajida mulki.
Bayanin da aka samo daga bakin Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Gunguma shi ne sarkin Zazzau na farko, kuma ya yi tafiyayya ne daga Daura, ya bi ta Kano da Rano, kuma ya fara yada zango a Kangi

Kafuwar birnin Zariya
Kamar yadda aka sami labari daga wajen Marigayi Malam Habibu Na-Turunku, wani uban gari na Turunku, ya nuna cewa, Zariya ‘yar Bakwa Turunku, kuma kanwar Sarauniya Amina ce ta kafa birnin Zariya, don haka ake kiran birnin da sunanta.

Hakan kuwa ya biyo bayan yadda hedikwatar mulki ta Zazzau ta yi ta sauya wuri saboda matsalar rashin ruwa, a zamanin mulkin Bakwa Turunku, wato mahaifin Sarauniya Amina da Zariya. Hedikwatar ta tashi daga Bomo zuwa Wucicciri zuwa Ancau zuwa Kargi, ta koma Turunku. A wancan lokaci an ce sai Bakwa ya ga Turunku ta yi wa mutanensa kadan a matsayin hedikwatar mulki, ga matsalar ruwa ana fama da ita. Saboda haka, sai ya koma Zariya a shekarar 1537. Daga nan ne kuma masarautar Zazzau ta koma Zariya.

Da aka gama sake shata gari, sai Sarauniya Amina ta sa wa wannan zagayen da’irar da aka yi sunan kanwarta, wato Zariya. Don ta girmama sunan ‘yar uwarta,kuma dalilin sunan garin Zariya kenan. Kuma ta gina gida a cikin gari, inda ya zama fadar Zazzau, inda mahaifinta ya zauna, kuma har yanzu nan ne masarautar Zazzau.
Zaria na da ƙofofi da dama na tarihi.


*MABUƊI*

*ƘOFAR DOKA ZARIA.*


Daga cikin ƙofar doka akwai wata unguwa da ake kira da suna jushi, cikin wani ƙaton family house da ake kira da gidan Alhaji Musa Mai Itace.Idan ka shiga daga cikin ƙaton filin wajen gidan,akwai manyan ɓangarori guda biyu masu ɗauke da sasanni.A kowani sasa zaka samu akwai ɗakuna ciki bibbiyu da falo kaman guda uku ko biyu,waɗanda duk matan aure ne a ciki na ƴaƴa mazan gidan da suka gada bayan mutuwan Mahaifinsu Alhaji Musa Mai Itace.

Sasa na farko a kuma ɓangaren farko da ke kallon gabas,ɗauke yake da ɗakunan matan aure guda biyu.Kowanne ciki biyu da falo,sai kuma daga waje ta ɓangeren hagu turakan Mai gidan ne mai suna Malam Adamu.Daga zaure kafin ka shiga akwai ɗakuna biyu masu ɗauke da ƙaramin bayi a ciki na samarin ɓangaren,waɗanda duk ba a gari suke karatu ba sai sun zo hutu suke buɗewa su shiga.Matan Baba Adamu su biyu ne, Inna Karimatu da Inna Amina.Dukkaninsu suna da ƴaƴa dashi,ƴaƴan uwargida Inna Karimatu su uku ne, biyu maza ɗaya mace. Abubakar, Usman sai Auta Zainab,sai ƴaƴan Amarya Inna Amina su kuma guda biyu ne duka mata,Aliya da Bushirah.
Sai ɓangaren sasa na biyu na Baba Auwalu,mai ɗauke da ɗakunan matan aure guda biyu jere reras suna kallo ƙofar zauren shigowa sasan.Sai ɗaki guda guda ɗaya mai ɗauke da ciki da falo a ware,wanda shi ne matsayin turakan mai gidan.Ɗakin farko na uwargida Inna Hauwa ne,wacce take da ƴaƴa mata guda biyu, Hameeda da Asiya.Sai ɗaki na tsakiya na Gwaggo Salamatu ce,ita Allah bai bata haihuwa ba sai ɓari da tayi ta faman yi har gashi girma ya fara kamata haihuwa bai samu ba.Daga wannan sasan sai sasan kusa da ƙarshe na Baba Mai Itace, kamar yadda ahalin gidan suke kiransa.Amma sunansa na yanka shi ne Malam Lawal Mai Itace, haka jama'ar unguwa suka san shi da shi.Amma da zaran ka shigo gidan da Baba Mai Itace kowa ke kiransa,sabida duk cikin zuriyyan Musa Mai Itace shi ne ya gaje sana'arsa na kasuwancin saye da sayar da Itace,da kuma sarin dabbobi yana kawo wa kasuwar ƴan awaki yana sayarwa.Ɓangarensa duk yafi na sauran girma da tsafta,kasancewar matan nasa duka biyu masu tsananin tsafta ne da kula da muhalli.Ɗakin Uwargidansa mai suna Halimatu da ake kira da Umma shi ne na farko,tana da Ƴaƴa guda uku duka mata,Raudah,Sumayyah sai auta Suhailah.Sai Amaryarsa da suke kira da Anty Safiya,ɗakinta shi ne daga ƙarshe kusa da turakar Mai gidan.Tana da ƴaƴanta biyu, Ibrahim Khaleel sai auta mai suna Maimunatu.Su biyu Allah ya tsayar mata,a haihuwa biyar da tayi suna komawa basa rayuwa.

Daga sasan Baba Mai Itace sai na ran gidan baki ɗayanta,wato Hajiya Zuwairah da ake kira da Hajiya Kakah.Ita ce Mahaifiyar duka waɗannan mazan gidan baki ɗayansu,kuma mace tilo cikin mata biyu da Alhaji Musa Mai Itace ya sama haihuwa dasu.Ita kaɗaice ta rayu da Musa Mai Itace har Allah ya amshi rayuwarsa,ya kuma nufa ita ce zata yi masa takaba,domin duk sauran matan da yake aure rabuwa suke yi.Daga Hajiya Kakah sai Amaryarsa uwar ƴaƴansa mata guda biyu mai suna Hajiya Hindatu,ita rasuwa tayi bayan ta aurar da duka Yaran nata Mata guda biyu da suka zama Hajiyoyi a yanzu.Hajiya Murja da Hajiya Aishatu,waɗanda Allah ya ɗaukaka su tare da azurtasu da auren mazaje masu kuɗin gaske.Suna Hajiya Kakah ya samo asali ne daga bakin Babban jikanta Abubakar da suke kira da Yaya Sadeeq,shi ne ya fara kiranta da hakan har sunan ya bita ya kuma ɓatar da sunanta na Hajiyar Mai Itace da ake kiranta da shi ada.Sasan na ɗauke da ɗakinta ne rak,sai wani warin ɗaki ɗaya da take sauke baƙin kwana idan tayi,wanda bata cika samunsu ba sai idan ana wani sha'ani a gidan na haihuwa ko biki. Ɗakinta na ɗauke da lafiyayyen ciki da falo manya masu kyau da tsari,wanda ƴaƴanta suka gatantata da kayan ɗaki na alfarma daidai rufin asirin da Allah ya basu,domin kafataninsu babu wanda za a ɗaga a kira shi da suna mai kuɗi sai dai mai rufin asiri.Sai kuma kasancewar wani dole yafi wani samu komin lacecewa,to hakan ce ta kasance domin duk cikinsu Baba Auwalu da suke kira da Baba Ƙarami, shi ne yafi ƴan uwansa rufin asiri da cima mai kyau.Domin shi kaɗai ne ya tsaya ya yi karatun boko,har ya samu aikin Lacturing a kwalejin FCE da ke Zaria.

Ɓangaren hagu na gidan mai ɗauke da babban sasa guda ɗaya,shi ne ɓangaren Amaryar Alhaji Musa Mai Itace, mai suna Hajiya Hindatu.Babban sashi ne mai ɗauke da ɗakunan bacci har guda uku,sai falo da kitchen da aka haɗe daga jikin ɗakin aka ɓusa ƙofarsa ya fita ta waje.Babu kowa cikin ɓangaren a kulle yake domin ƴaƴanta mata biyu da ta bari sune suka mallaki gadon ɓangaren bayan rasuwan Mahaifinsu Alhaji Musa Mai Itace,su kuma kasancewarsu mata da suke gidajen mazajensu sai suka sake zuba kuɗi suka gyara sashin tare da mayar dashi ginin zamani sosai.Sun zuba komi na kayan alatu a ciki, idan ana sha'ani nan suke sauka su da Iyalansu.Hajiya Murja wacce ƴaƴan gidan ke kira da Gwaggo Murja ƴaƴa uku gareta duk mata,Hibbah,Muhaseen da Zakiyyah.Sai Hajiya Aisha da suke kira da Gwaggo Shatuh, Yaranta biyu duk maza,Ayman da Basam.

Hajiya Kakah fitinanniyar tsohuwace,domin idan ta tada ballinta bata jin bari,kuma bata isa ta sanya doka akan jikokinta wani ya shata mata layi cikin matan ƴaƴanta ba.Fitinarta da rashin barin kota kwananta ya sanya kaf surukanta ke shakkarta,mutum biyu ne da suka gama da ita basa shayinta wato Amaryar Babban ɗanta Baba Mai Itace da kuma Uwargidan ɗanta na tsakiya Baba Adamu.Waɗanda suka haɗe kansu ba a taɓa jin cikinsu,suna shuka tsiyarsu yadda suka ga dama suna musgunawa abokanan zamansu.
Baba Mai Itace ko ince Malam Lawal Musa,shi ne babban ɗa a zuriyyan Musa Mai Itace.Daga shi sai mai bi masa Baba Adamu sai kuma Auta a maza mai suna Baba Auwalu.Sai ɓangaren matan gidan Aishatu da Murja,waɗanda sune ƴaƴa na baya domin basu da tsara a cikinsu su Baba Auwalu duk sun girme musu da ratan shekaru masu yawa.

Baba Adamu shi ne ya fara yin aure kafin Baba Lawal ya yi,har sai da ya haifi ɗansa na fari Abubakar Sadeeq sa'an nan Baba Lawal ya auro Uwargidansa Halimatu.Baba Lawal duk da kasancewarsa shi babba sai kuma Allah yasa ya fito a mutum mara kintsi sosai,domin tun yana matashinsa ya zaɓarwa kansa wace iriyar rayuwa na biye-biyen matan banza.Abinda ya hana shi aure da wuri kenan, har sai da Hajiya Kakah ta tashi tsaye sannan ya yi auren.Ya auro Umma ƴar mutanan Kaita da je jihar Katsina a lokacin yana tashen samu da sana'arsa na saida itace da kuma sayar da dabbobi,sabida shi da Baba Adamu tunda suka kammala secondary ɗinsu bayan rasuwar Mahaifinsu sai suka watsar da karatun boko.Sam suka ƙi cigaba da karatunsu sai neman kuɗi,duk kuwa da cewa ya barsu da rufin asirin da zasu iya juyawa har su tallafi karatunsu.Baba Auwalu da ya kasance ƙaramin cikinsu shi kaɗai ne Allah ya ɗaurawa son karatun boko,shiyasa ya maida hankali akan neman ilimi yana kuma haɗawa da sana'arsa ta ɗinki.A haka har ya kammala deegree ɗinsa,ya kuma samu lacturing abin sa yana yi.
Ƴaƴan Hajiya Kakah kusan za a iya cewa basu da wani haɗin kai,domin kowa na gudanar da kalar rayuwarsa ne irin yadda ya ga dama.Sam bata tsaya wajen ganin kan ahalinta ya haɗu waje guda ba,ita dai kawai duk wanda yafi faranta mata yafi samu shi ne nata.Sannan ƴaƴansa suma su ne abin so a wajenta,bata damu da ta ga cewa ta haɗa kan ƴaƴanta ba bare har jikokinta su taso suma kansu a haɗe.Baba Auwalu shi ne Auta kuma wanda yafi ƴan uwansa samu,domin bayan lacturing da yake yi yana gudanar da business ɗinsa na noma da kuma sayar da yadikan maza.Sai ya kasance shi ne ɗan gaban goshinta,sannan ƴaƴansa su ne mafiya soyuwa a zuciyar Hajiya Kakah.Daga shi sai Baba Lawal Mai Itace,shi ma yana cikin waɗanda suka shige zuciyar Hajiya Kakah, duk da cewa tana baƙin cikin yadda ya kasance mara cikakken kamun kai.Wanda kafatanin jama'ar unguwar sun san da halin neman matansa,domin tun yana matashinsa an sha kama shi da ƴaƴan unguwa ya saka su a ɗaki yana lalata dasu.Yana da rufin asiri na sa'arsa na saida Itace da Dabbobi,wanda Allah ya sanya masa nasibi a cikinsa.Sosai yake samu da sana'ar saro dabbobi a kasuwannin ƙauye ya sayar,musamman idan aka lokacin sallan layya ya gabato.Baba Adamu shi ne kaɗai bai kaisu samu ba,domin sana'arsa na ɗinkin manyan riguna ba kasafai yake shiga ba,yana dai haɗawa da ƴan buga-bugansa ne kawai yana samun rufin asirin da suka fi ƙarfin ci da sha shi da Iyalansa.Daga bayan nan nema ya samu aikin tuƙi a gidan wani mai hannu da shuni,to Alhajin na kyautata masa matuƙa da gaske,yana kuma biyansa albashi mai tsoka. Allah ya albarkaci Ƴaƴansa da son karatu,musamman Ababubakar da Usman,waɗanda suke matakin kammala deegree ɗinsu a jami'ar KASU(Kaduna state University.Da taimakon sana'arsu ta ɗinki suke taimakon kansu,da kuma yiwa kawunansu hidimar yau da kullum har su taimako Baba Adama da Inna Karimatu da wasu abubuwan.Abubakar ƙwararran telan mata ne,yayin da Usman ya kasance telan maza. Gwaggo Shatu ita ce kusan ƙashin bayan ɗaukar nauyin biya musu kuɗin registration,duk da irin ƙiyayya da rashin jituwar da ke tsakaninsu da kishiyar Uwarsu Hajiya Kakah.Hakan ko kaɗan bai shafi ƙaunar da take wa ƴan uwanta Mazan ba,musamman Baba Adamun da Baba Lawal da duk cikin Yayun nata uku da su tafi jituwa.

Kawunan surukan gidan baki ɗaya ba a haɗe yake ba,kamar yadda suka shigo gidan suka fahimci cewa kawunan mazajen nasu ba a haɗe yake ba.Sai suma kowacce ta kama abokiyar sabgarta wacce ta yi daidai da ra'ayinta cikin mata su shida da aka auro a gidan.Matan Baba Adamu Uwargida Inna Karimatu sam bata jituwa da Umma Halimatu,ba...


Read / Download RAYUWA DA ƘADDARA 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album