Join Our WhatsApp Group

HATSABIBIN BOKA 1 Complete Hausa Novel Document by HATSABIBIN BOKA 1


HATSABIBIN BOKA 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 123838HATSABIBIN BOKA 1

Reading Time: 10 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Gentle Lady ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Horror novels

File Size: 848.24 kb

File Type: txt

Views: 1497+

Download: 1251+

Last download: 2 days ago

Description/Story: HATSABIBIN BOKA
NA Gentle Lady
Ebook created Publish at www.hausaebooks.com.ng Shuraih Usman 99%
Published at www.hausaebooks.com.ng

☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


Page 1-2
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽


Dasunan Allah mai rahma maijinkai"" dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki maikowa mai komai ina kara godiya ga Allah subhanahu wata ala "" Wanda yabani ikon fara wannan labarin Allah yasa jama a zasu amfana da fadakar wardake cikinsa

Hakika komai kaga yasamu bawa mukaddarine daga Allah Amman kuma akwai sanadi wannan labarin kirkirarren labarine nayishi domin tsokaci dawadansu abubuwa dasuke faruwa acikin al umma""

Wacce wannan labarin yaxo daidai darayuwarta saita tuba tadaina domin ganin makomar Wanda yake kwatankwacin irin halintaa Allah yasa mudace Ameen

Wannan labarin narubutashine ra ayin kaina danhaka Wanda yaji zai iyah karantawa banhanashiba saidai kuma akiyaye karwani ya sarrafamun shitawata hanyaa idan kunne yaji gangar jiki tatsirah


*BISMILLAH*


***********************
Gabadaya unguwar cinkushe take da manyan motoci sai kaikawo sukeyi alamu sun nuna wani mihimnin buki akeyi na wani kasurgumin maikudii Dan la akari da yawan motocin dasuketa karakaina hakazalika masu tsadar gaske kaima kasan ba bikin"" fukara"u bane

Bakin kofar gidan tacika makill da maroka dakuma masu kidaa"" ahakan nasamu tattakawa zuwa kofar gidan duk da dakyar nasamu nakai wajen asheni banga jama a ba dankuwa cikin gidan tamkar anabikin nadin sarautane""

Sai rarraba ido nakeyi domin samun hanyar shiga wannan katafaren gidan ginane namusamman maihawa hudu anyimasa fentiii da farin fentiii maishegen kyau da shekiii wannan gidan kusan yafi kowanne gida kyau dakuma tsari gabadaya ya haskaka unguwar anayiwa gidan nan lakabida farin gidaa!! Tofa Allah yasa abunda yakecikinsafarine🠽򢠊
Kutsa kaina nayi Cikin gidan kofar shigama abar adubace""nagama zagayena nikam banga alamar matar gidan ba"" dankuwa irin wannan gidan yakamata ace matar gidan ta banbantaa dayanbukiii ajikinta kadai za agane""

Nayi zugum inabinsu dakallo nace tomezaihana insaurari firarsu watakil nagane matar gidan aciki🤔 wannna shawarar nayarda da itah nafarabi lungu dasako ina saurare abun takaici abun bakinciki duk inda nawulga zancensu kusan dayane kishiyaaa!!!!

Waimenene illar kishiyane??? Kumata kunada abun mamaki idan mijinku ya aureku yace zaikara aure kuyita fitinaa toyakenan idankuma keza a aura??? Itakuma matarsa taceme??? Yakamata zuwa yanxu mata sugane Susan kalar kishinda zasuyi kuyi koyi da matan Manzon Allah (S A W) suma sunada kishi saidai nasu sunayinsane abisa tsari kowacce tanarigengen wajen kyautata masa domin tasamu matsayi fiye Dana dayar

Amman wasufa saboda tsabar bala.i da masifa daga ranarda yasoma maganar kara aure tofa ya ballowa kansa likii zatadaina wanka tabar dafamasa abincii wata hatta gadonta baxata barshi yakwantaba dazaran yace yimun kaza tace bazanyiba kajecen wajen amaryarka taimaka tabar yayanta acikin wahala waifa a irintata wautar waita naso tazubawa mijin haushine shikuwa dayafita iyawa saiyabuge iskanta yayima dadai duniya kamarma baisan da zamantaba sai idan tayi masifar tagababuci kuma biki yanata karatowa sai afara yangyare gyare waidaga bayakenan sadaka da bajawara bayan kinzubarda girmanki kimarki darajarki

Bari nabaku wani sirri wlh idan mijinki zaiyi aure kika kwantarda hankalinki zakici arziki komai kikeso zaiyimaki domin yataushi zuciyarki kuma zai rika tambayarki menene kikeso haka zalika komai zaiyiwa amaryar zairika neman sha wararki"" sabanin idan kikasoma fitina zaiyibanza dake duk wuyartadai kece akasa bazaki hanashi auren ba

Saikiyi ba1 ba 2. Darajarki dayake gani kinbata bazaisake yarda dakeba kuma koda amaryar tashigo gidan akatada fitina kodakuwa kece mai gaskiya bazai yardaba zaice aiyaga take takenki tunkamin yayi aure kiketa fitina tosaidai kiyi abunda zakiyi matadai matar sace matsayinku daya awajesa uwargida kinga mutuncinki yaragu

Idan kikacigaba da fitina karshenta yasakeki yazauna da amaryarsa wagari yawaya???? Hakan yana faruwa sosai acikin al.umma

Iyayena mata iyayen gobe mukula mukiyaye kishii ba haukabane!!!

Nafara biyar lungu dasako cen saman hawa na uku nayi katari da matar gidan "" sosai nafirgita daganinta sam bazaka taba cewa matar gidan bace"" irin matan nan ne wadan da mazajensu suke dakudi amman idan kagansu bazaka siyesu kwandalaba duk kayanda suke siyamasu basa sakawa idan kagansu mai aikinsuma tafisu daraja amman fa idan zasuje gidan bukii kokuwa zasuje unguwa zakadauka basason taka kasa saboda tsabar tsafta""

Abokananta dasuke gefenta dayar tace wai lubabatu mezaihana kitashi kiyi wanka gidan nanfa yanbiki sunfara cikashi kosokike araina class nakii
Wacce take gefenta nadama tace hajiya larai kibarta hakan mana"" dame zataji dakishiyarda akai mata kokuma da kwachakwaimar kwalliya?? Kinsan Allah danice kotaron biki bazanyiba

Wata tace habadai hajiya larai aiyanzu andaina wannan yayin idan za akawomaka kishiya kahana kanka jindadin rayuwa yanxu kissa akeyi kikwantarda kai tamkar mumina ni wlh mijina yayi aure saina gasawa amaryar gyada ahannunta

Suka kwashe da dariya haryanzu uwargidan uwar iko batayi maganaba"""
Larai tace hajiya sadiya kenan ashe wacce tsautsayi yasaka tashigo gonarki zatafi gwammacewa kwana akabarintaa" suka sake shekewa da dariya"" amman banda itah""

Haba kukuwa banda abinku ai kishiya abokiyar zamace menene abunkishin??? Abunda akasaba bakifa badainawa za ayiba nisam banajin kodar akan auren nan
Hajia lubabatu ce mai wannan maganar""

Hajia larai tarike haba lallai hajiya kodayake wannan bashine nafarkoba bakyada jinkomai nikam wlh bazan sakewa mijina fuskaba dahar zaiyi sha awar karawani auren"" tirkashi ranarkuwa dahakan tafaru wlh sai yayi zaton aturu aka kwantoni dan zankoma masa mahaukaciyar karfi dayajii

Wannan karon harda hajiya lubabatu wajen dariya wata matashiyar budurwace tabude kofarda sallama""" sukabita dakallo babu wanda ya amsa tafara kallon mutanen dasuke cikin dakin daga bisani tadauke kanta kamar taga kashi
Hajiya lubabatu ce ta daka mata tsawa ke wacce irin shashashar yarinyace labila???? Zakishigo wamutane daki haka bakiganin bakine dani??? Baki tatabe nagansu mana mom kuma ainayi sallama "" takai karshen maganar tanasake wurgamasu mugun kallo ta murguda bakiii
Kinyi sallama gidanwa mu kuramene dabamujiba"" ta kwabe fuska to tayazakuji bayan kuna tazuba shegen surutu wanda bazai kareku dakomai ba""
Ido lubabatu tazaro sukam su hajia larai inda sabo yaci acesun saba dahalin labeela"" tace labila waiyaushe kikazama tsagera nifa mahaifiyarkice kinamun magana tarashin da a

Tasake mere baki"" tacee malamai niku gyara zanduba jakata "" tayi maganar tana rike kunkumi afusace hajia lubabatu tasauko daniyar dukanta su hajiya sadiya sukariiketa haba hajia baidace kidaketaba ai labila karamar yarinyace kuruciya ce take damunta

Kotakansu batabiba tahauduba jakarta"" tadauko sannan takallesu daibayan daya tace naji kuruciya tana damuna amman karani saudubu daku sakarkarun mataa mstw tsaki taja tafita tabar dakin

Gabadaya dakin yayi tsit bakajin motsin komai saina saukewar ajiyar zuciyarasu" labila karamar yarinya amman kullum tasamesu agidan saita soka masu miyagun maganganu

Dasauri tasauko kasan tana rike dajakarta"" sai kutsawa takeyi cikin taron mutane ranta yayi matukar kuna bataso mahaifiyarta tana hulda da wadan nan matan saboda dukansu babu Allah azuciyarsu amman mahaifiyarta batada wasu shakikan abokai bayansu
Wayarta tajawo takamo wata nomber tadanna kirah babu jimawa akadauka"" tayi sallama ya amsa dad dan Allah katuro driver yamiyar dani bazan iyah zama anandinba!!

Ajiyar zuciya yasaukar yace saboda menene labila bazakijirah akawo antyn takiba cikin sauri tagirgiza kai no dady"" dagabaya zandawo inganta yanzu akwai muhimmancin tafiyar tawa gobe munada harda a islamiyya"" amman inshaa Allah idan komai ya daidaita zandawo naga mom din kafin lokacin tazama yargida da murmushi afuskarta tafurta hakan shima murmushi yayi badamuwa labelaa yanzun bari nakirashi yazo amman nayi kewarki yata gashi zaki tafii amman bamudan zantaba"'

Tashafo gefen fuskarta bakomai dady zansake zuwa saimuyi firanko?? Yace yauwa yata kikasance cikin amincin Allah

Tasaki sassanyan murmushi tace kaima haka"" inasonka babana yace nima inasonkii tace Publish at www.hausaebooks.com.ng e yace ok Publish at www.hausaebooks.com.ng e taciro wayar akunnenta takuramata ido Allah sarki babana"" Allah. Yasa kayi dacen mata Allah yasa daka wannan auren kasamu kwanciyar hankali wasu sirarun hawayene suka sauko mata tasa gefen mayafinta tashare sake matsawa tayi saboda cinkoson mutane ga shi ankusa la asar"" batawani jimaba driver yazo bayan sungaisa tashige motar suka kama hanyar kano
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠Page 3-4
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle lady💃🏽

Sai bayan fitar" labila sannan hajiya lubabatu tasamu tashiga wanka ganin duk jikin kawayen nata yayi sanyi da maganganun da labilar tafadamasu yarinya tamkar banice nahaifeta ba sam bataganin mutuncina
Tayi kwabaa

Batajima dashiga wankaba tafito tasheka kwalliya tamkar wacce zataje gasar sarauniyar kyau" ta chanchade cikin wani tsadadden bugaggen less dan ubansu akalla kudinsa zasukai dubu dari da hamsin""
Tasaka sarkar diamond hannunta yasha awarwaraye na gwal"" nantake tasoma shekii tashi sukayi dukansu suka fara zaga gidan duk indasuka wurga sai anjinjinawa kwalliyarta nikuwa araina nace wato yangulma kikewa kwalliya illai kuwa kwalliya tabiya kudin sabulu dankuwa tayankesu kowacce takoma gidansu tana Allahummar zukuni""

Wani abun saigidan manya bakuga yanda akasoma fitowa dakayan ciye ciyeba bikin gidan masu kudi ko ba agayyacekaba kaje kodakuwa ba asakarmaka fuskaba kakwaso gara""
Dankuwa yanda akacika gidan kaima dagani kasan wadansu abincin kawaine yakaisu "" babujimawa akafara fitoda dakwalen kajiii dakuma babba kakkun raguna masu maiko"" anyimasu gashi Na musamman sunsha shafen barkono saizubarda mai sukeyi saikuma lemuna namanyan mutane wanidinma bantaba ganin irinshiba

Kowa kaganshi rabonsa yake yaga"" masu DJ ne sukafara sakin kidaa bayan suncika tunbinsu""" hajiya lubabatu ce tafara takarawa cikin murna kaikace ba itah za ayiwa kishiyaba babuwanda bata burgeba wasuma sunata rokon Allah yabasu uwargida maihalinta Sam batadauki kishi abakin komaiba

Kai ranarfa tasha rawa nikam nace jikinki zaiyi ciwo kuwa""duk wannan bidirinda akeyi banga ma mallakin gidanba""

Yinin ranarfa sunchashe son ransu DJ yakwashi kudii wadanda akaita masu likidasu kasan biki na kusoshin yan duniya wadanda sukarika

Shigar hajiya lubabu goma kowacce shigarkuma saiwanda yaganie komai kuma kalar kayan" anzuba hotona"" magrib tana kawojiki kowa yafara haramar barin gidan"" daki suka sake kowama"" suna nan kowadai saifadin albarkacin bakinsa yakeyi

Karfe takwas mukafarajin dirar motocin amaryaa"" sunata rangada gudaa"" akashigo da itah"" zuwa bangaren uwargida sukashiga da sallama ta amsa dasakin fuska marabanku lale marhabin kuzazzauna mana""
Daga kawayenta harmasu kawo Amarya bakisake suke kallonta sambatada bakinciki taja hannun amaryar tace zo Kanwata kizauna nan"" cikin jinkunya"" tazauna kanta yanakasa ayanda akebata labarin matarsa babu ruwanta ashema tafiyanda akabata labari""
Take tamike tafara jidomasu kayan makulashe dakuma kayan sha"" da gasassun naman kajie"" bayan sungaisa sukace ga amanar kanwarkinan munkawo maki
Duk dakowa yana shaidunki bakida wata illah Dan Allah kiyi hakuri dahalin kuruciyarta dan kingirmeta nesa bakusaba idan tayi badaidaiba kiyimata fada""
Tayi murmushi aibakomai abokin zama dadine dashi tadafa kafadarta"" Kanwata nandin kidauka gidane komai yashigemaki duhu karkiji shakkar komai kisanardani nikuma zanwayarmaki dakai

Allah yasa nandin gidan zamankine Allah kuma yasa ace karada akayi Allah yabamu zaman lafiya"" gabadaya aka amsa da amin""
Mikewa sukayi tace yabazaku taba koda ruwabane ai anzama daya nibazanji dadi idankuka kicin komaiba nima idan nazowajenku tareda Kanwata aibazakuji dadiba idan nakishan koda ruwane

Sukace tayi hakuri akoshe suke ganin tamatsa yasaka sukadan kurba lemun"" tareda itah akafita zuwa bangaren Amarya """ harkuryar dakin tazaunarda itah yanganin daki Duk suncika dakin"" sunfara tabe tabe"" hajiya lubu tasoma miyarmata"" dakayanda akasoma turewa tadade taredasu sannan tayimasu sallama takoma wajen kawayenta indasuma sunsoma haramar komawa gidan mazajensu"""

Tahadamasu shatara Na arziki tarakasu kowacce takama hanyar gidanta"" bangarenta takoma"" hawa na uku shine Nata nabiyu na Amarya maigidan shine hawana karshe""

Idanzakije bangarensa Mahayar Na ura zakishiga kidanna zuwa sama bàsàikin wahalda kanki wajen taka matakalaba

Tanashiga bangarenta tarage kayan jikinta tahaye saman makeken gadonta tasoma sharar barciii hardà minsharii hankalinta kwancee saijuyi takeyi sànyin Ac yanashigarta tako ina"""


Gabadaya gidan anwatse kowayatafi yana yabon lubabatu da kyawawan halayenta"" karfe shadaya motarsa tashigo gidan"" bayan driver yayi fkng yayi saurin fitowa yabudemàsaa kofaa

Yafito"" yacewa driver n ina" habu driver dubamun kagani nayita kiran"" wayarsa batashiga labila kuma bata dauki wayarba

Yadan gurfana dasaurii yayi hanyar dakinsu yanakwala masa kirah haryasoma barcii yaji anakiransa firgigit yamike yafito dasaurii taresuka koma wajen alhajin""

Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA*☠Chapter 5
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽Dukawa yayi yace yallabai andawo lafiya??
Qalau habu tundazu nake neman layinka Amman inajinsa akashe""
Ah yallabai wayarne batada chaji wlh" haba habu yanzu duk wadatacciyar wutar nan da ake sakowa kuma ga gen Amman asamu wayarka babu chaji??? Duk kacinye chajin wajen shiriritaccen cheating dakukeyi kaidai koyaushe maganata dakai akan rashin wayane
Yasosa kansa yallabai ayi hakuri kuskurene baza asakeba"" murmushi yayi yace hakan kake fada dai kullum"" ya labilar kun isah gidan lafiya ko????

Kai yagyada ah yallabai kafin magrib nihar najuyo tabada sakoma akawo maka"" yana murmushi yace to daukomun""
Dasauri yakoma cikin dakin yadauko key yabude motarda yaje da itah wata katuwar kulace dakuma leda"" yakarba ""
Sukai masa saida safe yawuce cikin gidan kaitsaye hawa nahudu yadosa nikuwa ina biye dashi huhuhu ashe banga komaiba saboda wannan yafi sauran kyau nesa bakusaba

Komai gashinan gwanin sha awa" tundaga flowers da kujerun dakin da center Capet" green color ne mai haske" sai makeken TV n bango" saikuma babban agogon bango""
Sai fream da ke dauke da ayatul kursiyyu dayan amanarrasulu gudan lakadja akum"" sai wadansu masu addu.o

Sosai tsarin yaburgeni"" kularda take hannunsa ya aje yakarasa kuryar dakin"" kayan jikinsa yarage yashiga yawatsa ruwa yafito jallabiya yazura yafeshe jikinsa da turare yafito kular yabuda danbun kaxane"" sai babbar ledar gasassun kajine gashin gida harda diminsu kansa yadafe shisam yama manta bairikowa Amarya kazaba shikullum cikin mantawa yake"" yayi murmushi labilaa kenan"" mikewa yayi yabude fridge yadauko madarar yoghurt yasauko zuwa bangaren hajia lubabatu da sallama yashiga tayi daidai sai kwasar barcinta takeyi"" ledar hannunsa ya aje yakarasa saman gadon yakura mata ido murmushi yayi yashafo fuskarta shikawai yasan abunda yace azuciyarsa ahankali yasoma tashinta ta ture hannunsa cikin alamun mai barcii kuma yanamata dadi yace maman laPublish at www.hausaebooks.com.ng kitashi kokinyi sallah??? Cikin barci tace ah nayifa alhaji harkadawo???

Yace gashi kinyi barci bazaki rakani gun kanwar takiba murmushi tayi wlh nagaji alhaji baxan iyah zuwa ko inaba saida safe tasake juya kwanciya
Murmushi yasakeyi

Yaja bargo yarufemata jikinta yafito zuwa bangaren Amarya Yanashiga daddadan kamshi yadaki hancinsa yalumshe ido sannan yabude ahankali yafurta Alhamdulillahi ala ni imati"
Yataka harcikin dakinta tana zaune tsakiyar gado yadine sanye ajikinta "" dashikuma akarufe mata kanta dashi""

Ahankali yataka yazauna saman gadon yayimata sallama ta amsa ahankali"" hannunsa yasaka yadage mayafinda akaimata rufadashi
...


Read / Download HATSABIBIN BOKA 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album