Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGARSA TAWADDUD Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGARSA TAWADDUD


HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGARSA TAWADDUD

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 10089



HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGARSA TAWADDUD

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Bukar Mada ,Danladi Z Haruna ,Prof Ibrahim Malumfashi ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08032767547, 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 54.39 kb

File Type: txt

Views: 620+

Download: 159+

Last download: 2 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

01 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

Ya zauna yana ta tumurmusar
dukiya, yana ci, yana sha cikin bushasha
yana ta rabar da zinariya da azurfa da jauhari. Kullum cikin cin nama yake da shaye
– shaye da yawan dariya ga kuyangi suna
masa wak’ok’i yana musu kyaututtuka. Bai gushe ba yana wannan d’abi’a har abin da
ya mallaka gaba d’aya ya k’are ya zamana ba shi da komai duk abin da ya mallaka ya
fice daga hannunsa, sai wata kuyangarsa
guda d’aya da ya mallaka daga mahaifinsa. Ita wannan kuyangar ta kasance babu kamar ta wajen kyau da cikar halitta da k’oshi da
hankali da ladabi biyayya. Ta fi ragowar kuyangin wajen ilmi da iya magana mai dadi.
Ta nak’alci yadda za ta jawo hankalin mutum zuwa gare ta, ta san yadda za ta rarrashi
masoyinta. Idan ka gan ta za ka yi
tsammanin watan sha’aban ne ya tsaya
saboda idanunta masu haske, tamkar an
gina su da lu’ulu’u, suna walk’iya kamar
kaifin takobi, jikinta kullum ba ya rabo da
k’amshi da taushi da ni’ima. Kundukukinta
kamar nunanniyar tuffa. Bakinta matsakaici
kamar hatimi, hak’oranta jere reras kamar
kibiyoyi. Jikinta mai kyan gani abin so ga
kowa domin bai zama ramamme ko mai
yawan k’iba ba. A taka’ice dai ita ta kasance
kamar yadda mai wak’a ke cewa:
Idan ta gabato ta fitinar da zuwanta,
Idan ta tafi nan ne abu mafi azabtuwa
Ta fi wata haske ta yi kama da rana
Kyawunta shi ne abin so ga duk kowa
Tana jan hankalin duk wanda ya gan ta da
kyanta da iya maganar ta mai cike da
tattausan lafazi da murmushinta ko
dariyarta. Musamman idan ta haskawa
mutum kyawawan fararen idanun nan nata.
Da yake Abu Hasan ya karkatar da dukkan
dukiyarsa ya zamana ba shi da komai sai ita,
ga shi kwana uku kenan ba su jefa wani abu
a cikinsu ba kuma ba su samu barci ba, sai
kuyangar ta ce da shi, “ya shugabana, ka kai
ni wajen Sarkin Musulmi Khalifa Haruna
Rashid ya fanshe ni.”
ka nemi biyana dinari dubu goma, hakan zai sa
ka samu biyan bukata daga damuwar da ka
shiga. Idan ya nuna cewar na yi tsada sai kace masa, “ya Sarkin Musulmi wannan kuyangar da kake gani k’imar kudinta ya fi
haka ma, amma ka jarraba ta da kanka ka gani ta fuskar ilmi da hankali. Domin ita
wannan kuyangar babu misalinta, kuma ba
ta dace da wani ba face kai.” Ta sake
gargadinsa cewa, “kada fa ka sallama ni
k’asa da abin da na fad’a maka, domin
wannan kud’in araha ce ga makamanciyata.”
Ubangidanta ya kasance bai san darajar ta
da k’imar ta ba, amma jin za ta kai wannan
darajar sai ya d’auke ta ya tafi da ita wajen
Khalifa ya shaida masa kamar yadda ta hore
shi. Khalifa ya dube ta ya ce, “yaya sunanki?”
Ta ce, “sunana Tawaddud.” Sannan ya ce,
“ya ke Tawaddud a wanne fannin ilmi kika
gwanance?” Ta ce, “ka sani ya Sarkin
Musulmi ni inda da ilmin nahawu da furu’a da
wak’ok’i da tafsiri da hisabi da k’ismi da
labarun mutanen farko. Kuma na san
Alk’ur’ani mai girma, na karanta ta fuskar
ruwayoyi bakwai da goma da kuma goma
sha hud’u. Na san yawan surorinsa da
ayoyinsa da haruffansa da kalmominsa. Na
san tsakiyarsa da rubu’insa da sumuninsa
da wuraren sujjada da k’irgen adadin
haruffan sujjadar. Na kuma san ayoyin da
aka shafe da wadanda ba a shafe ba. Na
kuma san surori Makiyya da Madaniyya da
sababin saukar da aya ko sura. Na san
hadisan Annabi da tarihi da hik’ayoyi da
labarun da ake kokwanto a kan ingancinsu.
Na san ilmin sanin rauhanai na san na
mutanen Hindu da na Falasd’inawa da
hikimomin jiya da na yau, na kiyaye da yawa
ilmin ma’ana da na bayani. Kuma na nak’alci
ilmin magani da kuma iya kad’a molo yadda
zan kad’a shi na b’ata zuciya da yadda zan
buga shi ya faranta rai. Haka nan na san
yadda za a kad’a shi a yi rawa da inda za a
kad’a a yi shiru kawai. Idan na yi ado na
fitinar, idan na shafa turare a fitina da ni. Na
zama babu wanda zai k’aru da ni sai wanda
yake da ilmi mai zurfi mai hangen nesa.”
Yayin da Khalifa ya ji wannan bayanin nata
sai ya yi mamaki saboda k’arancin
shekarunta da yadda ta iya bayani cikin
hikima da lafazi mai dad’i. Ya waiwaya ga
Abu Hasan ya ce, “bari na aika a kirawo
ma’abota sani da za su yi mata tambayoyi
kan abin da ta ce tana da shi na daga ilmi.
Idan ta kasance ta amsa dukkan tambayoyin
zan saye ta a wajenka, bisa kud’in da ka
fad’a kuma na k’ara maka wasu a kai. Amma
idan ba ta amsa ba, to babu wanda ya
cancanta da ita sai kai.” Abu Hasan ya ce,
“cikin farin ciki da so da yarda ya Sarkin
Musulmi.” Khalifa ya rubuta takarda zuwa
birnin Basra ya ce a kirawo masa Ibrahima
d’an Siyyari. Ya kasance masani ne a fannin
balaga da wak’e. Ya ce kuma ya taho da
masana Kur’ani mai girma da malaman
hikima da masana ilmin maganganu da
masana ilmin taurari da mahukunta da
masanan ilmin Hindu da Falsad’iya da hisabi.
Shi Ibrahima ya kasance duk ya fi su sanin
wad’annan ilman ya aika duka suka zo suka
tafi da hanzari domin amsa kira.
Yayin da suka isa fada suka zazzauna
Khalifa ya bayyana musu dalilin kiran su
sannan ya aika aka kirawo kuyanga
Tawaddud ta shigo ta yaye lullub’i ta nuna
kanta kamar walk’iyar tauraro. Khalifa ya sa
ta zauna a kujerar zinariya ta gaishe da
jama’a cikin murya mai taushi da fasahar
harshe, sannan ta ce, “ya Sarkin Musulmi, ka
umarci wad’anda suka hallara nan daga
malamai da masana ilmin taurari da masana
hindiya da falsad’iya su yi min tambaya duk
irin wadda suka ga dama.” Khalifa ya ce da
su, “ina so ku yi jayayya da wannan kuyanga
bisa abin da take tak’ama da shi na daga
ilmi cikin sha’anin addininta. Ku tambayi
hujja game da irin abin da ta fad’a.” Suka
amsa, “mun ji mun bi ya Sarkin Musulmi.” A
nan Tawaddud ta sunkuyar da kanta alamar
gaisuwa ga Sarkin ta ce, “a cikinku wanene
masanin shari’a da fik’ihu wanda ya nak’alci
Alk’ur’ani da hadisai?” Sai wani ya mik’e ya
ce, “ni ne wanda kike tambaya.” Ta ce, “to yi
tambayar ka gare ni.” Ya ce, “shin kin karanci
littafin Allah mai girma kuma kin san aya
shafaffiya da wadda aka shafe ta da ita? Kin
san adadin ayoyinsa da haruffansa?” Ta
amsa, “na’am na san wad’annan duka. “To
tunda haka ne zan miki tambaya a kan farilla
wajiba da sunna k’a’ima.
Ya ce ya ke kuyanga wanene ubangijinki?
Wanene Annabinki? Menene a gabanki? Ina
ne alk’iblarki? Su wanene ‘yan uwanki?
Menene tafarkinki?”
Ta ce, “Allah shi ne ubangijina, Annabi
Muhammadu mai tsira da aminci su tabbata
a gare shi, shi ne Annabina. Alk’ur’ani shi ne
a gabana, d’akin Ka’aba nan ne alk’iblata,
musulmi su ne ‘yan uwana. Sunnar Annabi
Muhammadu ita ce tafarkina.”
Khalifa ya yi mamaki da irin kalamanta da
cikar fasahar ta duk da k’arancin shekarunta.
Mai tambaya ya cigaba, “ya ke kuyanga, da
me ake sanin Allah?”
Ta ce “ana sanin Allah ta hanyar fahimta.”
Ya ce “menene fahimta?”
Ta ce “fahimta iri biyu ce; da wadda take a
b’oye da wadda take a bayyane.”

Zanci gaba insha allah gobe02 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

kuyanga tayi bayaninta sosai, tana cewa, “fahimta iri biyu ce; da wadda take a b’oye da wadda take a bayyane. Fahimta b’oyayyiya ita ce wadda Allah mai girma da d’aukaka ke halittar mutum da ita, yana bayar da ita ga wanda ya
so. Amma bayyananiyar fahimta kuwa ita ce
wadda mutum ke samu ta hanyar neman
ilmi.” “Kin amsa daidai.” In ji malamai. “To amma
ina ne mazaunar hankali?” Ta amsa da cewa “Allah ta’ala kan jefa shi a
cikin zuciyar mutum, daga nan sai haskensa
yakan tafi zuwa k’wak’walwa daga nan ya
tabbata kenan.”
“Wannan haka yake.” In ji malami mai
tambaya. Sannan ya ce, “ta yaya kika san
Annabin Allah?”
Ta ce “ta hanyar karatun littafin Allah da
wasu alamu da kuma tabbatattun hujjoji da
karamomi.”
Ya ce, “haka ne.” Daga nan ya ce, “fad’a min
game da shika-shikan Musulunci da sunna
k’a’ima.” Ta ce, “shika-shikanMmusulunci
guda biyar ne, na farko shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah mad’aukakin
Sarki, kuma Annabi Muhammadu bawansa
ne, manzonsa ne. Na biyu tsaida sallah, na
uku bayar da zakka, na hud’u azumin watan
Ramalana, sai cikon na biyar shi ne aikin hajji
zuwa ga d’akin Allah mai alfarma ga wanda
ya samu iko ga haka. Sunna k’a’ima kuwa su
hud’u ne; dare da rana, rana da wata, sune
suke kusatar da rai da buri su k’arar da d’an
Adam, bai sani ba cewa a kullum suna
kusatar da shi ne zuwa ga ajali.” Ya ce, “haka
ne. To ki fad’a min game da tabbatar imani.”
Ta ce ‘wad’annan su biyar ne, sallah da
azumi da hajji da kuma jihadi a tafarkin Allah
da nesantar haram.”
“Haka ne, to ki fad’a min abin da ke
k’arfafawa zuwa ga sallah.”
Ta ce da malamin “aniyar bauta zuwa ga
Allah, ka san kai bawa ne ka bi shi.”
Ya sake tambayar ta “wad’anne wajibabbun
sharud’d’a ne suka zama tilas a cika su kafin
a kai ga yin sallah?”
Ta ce “na farko tsarki da suturce al’aura da
nisantar kayan k’yale – k’yale da tsayawa a
wuri mai tsarki da fuskantar alk’ibla da
daidaita tsayuwa da niyya da kabbarar
harama.”
“Haka ne, to fad’a min abin da ake fita daga
gida domin sallah.”
Ta ce “ana fita da niyyar bauta zuwa ga
Allah.”
Ya sake tambayar ta “ da wacce niyya ake
shiga masallaci?”
Ta amsa “da niyyar bauta wa Allah.”
“Don me muke fuskantar alk’ibla a
sallolinmu?”
“Domin cika umarni uku daga K’ur’ani mai
girma da umarni d’aya daga hadisi.”
“Fad’a min game da sallah? Menene
farkonta? Menene k’arshenta? Me ya
haramta ta?”
“Ana yin sallah cikin tsarki. Rashinsa na
haramta ta. Farkonta shi ne kabbarar
harama, k’arshenta shi ne sallama.”
“Menene hukuncin wanda ya bar sallah da
gangan?”
Ta ce “an rawaito daga ingantattun hadisai
cewa duk wanda ya bar sallah da gangan ba
tare da wani dalili ba, to ya bar addinin
Musulunci.”
kuyanga ta rik’a bai wa malamin nan amsa daidai yadda ya tambaye
ta, shi kuma yana cewa, ‘haka ne.’ Sai ya ce, “ina so ki fad’a min menene ma’anar sallah?”
Ita kuwa ta ce da “Sallah ita ce wata hanyar ganawa tsakanin bawa da ubangijinsa, kuma
tana da darajoji guda goma su ne, na d’aya tana haskaka zuciya, na biyu tana haskaka
fuska, na uku tana sa yardar Arrahamanu, na
hudu tana fusatar da shaid’an, na biyar tana maganin masiba da bala’i. Na shida tana
juyar da muguntar abokan gaba, na bakwai
tana rub’anya lada. Na takwas tana hana yin
azaba a ranar lahira, na tara tana kusantar
da bawa zuwa ga ubangijinsa, tana kuma
hana shi aikata miyagun ayyuka, na goma ita
ce ginshik’in addini.”
“Wannan batun gaskiya ne, menene mabud’in
sallah?”
“Alwalla ko taimama.”
“Menene mabud’in taimama?”
“Niyya da kuma ambaton sunan Allah
mad’aukakin Sarki.”
“Menene mabud’in ambaton sunan Allah
mad’aukakin Sarki?”
“Cikakken imani.”
“Menene mabud’in cikakken imani?”
“Ban gaskiya ga Allah.”
“Menene mabud’in ban gaskiya ga Allah?”
“Sakankancewa.”
“Menene mabud’in sakankancewa?”
“Biyayya.”
“Menene mabud’in biyayya?”
“Kad’aita Allah da dagewa wajen bauta
masa.”
“Fad’a min game da farillan alwalla.”
“Farillan alwalla guda shida ne bisa
mazhabar Imamu Shafi’i, Muhammadu d’an
Idrisa, Allah ya yi musu rahma. Niyya yayin
wanke fuska, wanke fuska, wanke hannaye i
zuwa gwiwar hannu, shafar kai, sai wanke
k’afafu i zuwa idon sawu. Da kuma
jerantawa.
Sunnonin alwalla kuma guda goma ne, yin
bismilla da wanke hannaye kafin tsoma su a
cikin k’warya, kurkure baki, shak’a ruwa da
fyacewa. Shafar gaba d’ayan kai da shafar
kunnuwa da sabunta ruwa a gare su. Da
kuma tsettsefe gemu mai kauri da tsettsefa
yatsun hannu da na k’afafu da soma gabatar
da dama kafin hagu da yin wanki uku – uku
tare da jerantawa.
Idan ka gama alwalla sai ka ce, “na shaida
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,
kuma Muhammadu bawansa ne, kuma
manzonsa ne. Ya Allah ka sanya ni cikin
bayinka masu tuba, kuma ka sanya ni cikin
tsarkaka. Tsarki ya tabbata gare ka, yabo
naka ne kai d’aya. Na nemi gafara a gare ka,
ina tuba gare ka. Domin a ruwaito hadisi
daga Annabi mai tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi cewa, ‘duk wanda ya
karanta wannan addu’ar bayan ya yi alwalla,
za a bud’e masa k’ofofin aljanna ya shiga ta
wadda ya ga dama.”
Malami ya ce, “kin yi gaskiya, idan mutum ya
yi nufin yin alwalla a ina mala’iku da
shaid’anu ke tsaya masa?”
“Idan mutum ya yi nufin yin alwalla, mala’iku
kan sauko su tsaya a damansa, sannan
shaid’anu za su tsaya a hagunsa. Idan ya
ambaci Allah a farkon alwallarsa sai
shaid’anu su gudu. Daga nan sai mala’iku su
yi masa laima ta haske da fukafukansu,
kowannensu yana da fuffuke hud’u, suna
tsarkake sunayen Allah mai girma, suna
nemar wa mutumin gafara gwargwadon
lokacin da ya kasance yana alwallar bai yi
magana ba. Amma idan a farkon alwallar bai
yi bismilla ba sai shaid’anu su kewaye shi,
mala’iku su juya ga barin sa. Sai shaid’anun
su sanya masa waswasi cikin alwallar har ya
yi nak’asu a cikin ta. Manzon Allah mai tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce,
“kyakkyawar alwalla na korar shaid’an, ta
fusata shi.” Sannan an rawaito yana cewa,
“idan wata masifar ta fad’awa musulmi a
lokacin da ba shi da alwalla, kada ya zargi
kowa sai kansa.’

ZANCI GABA03 HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGAR SA TAWADDUD

“Me mutum ya kamata ya soma yi da zarar
ya farka daga barci?”
“Ya kamata ya wanke hannunsa sau uku,
kafin ya tsoma su a cikin k’warya.”
“Menene farillai da sunnonin wankan
janaba?”
“Farillan su ne, niyya, game jiki da ruwa da
sadar da ruwa ga dukkan gab’ob’i, ana nufin
ruwa ya tab’a dukkan sannan jiki duka na
daga gashi da fata. Sunnonin kuwa su ne a
fara da alwalla sannan cuccud’a jiki da
tsettsefe gashi da jinkirta wanke k’afafu sai a
k’arshen wanka.”
Yayin da yarinya
ta bayyana wa malamin farillan wanka da
sunnoninsa da na alwalla sai ya ce, “kin yi
daidai, yanzu fad’a min dalilan da ya sa ake
yin taimama da farillanta da sunnoninta.”
Ta ce, “dalilan bakwai ne, rashin wadatar
ruwa ko jin tsoron kada ruwan ya k’are, zama
a wurin da babu ruwan da ya kamaci alwalla,
rashin lafiya, ko karaya a gab’b’an alwalla da
samun rauni a gurbin alwalla. Farillanta guda
hud’u ne, su ne; na d’aya niyya, na biyu
turb’aya, na uku bugun k’asa na farko, na
hud’u shafar fuska da hannaye. Sunnoninta
su ne bugun k’asa na biyu da juyowar shafar
hannu da kuma gabatar da dama a bisa
hagu.”
“Menene sharud’d’ai da farillai da kuma
sunnonin sallah?”
“Sharad’an sallah guda biyar ne, in ji ta “na
d’aya tsarkin gabb’ai, na biyu suturta al’aura,
na uku cikar lokaci da sakankancewa da
ganin wani. Na hud’u fuskantar alk’ibla, na
biyar tsayawa a wuri mai tsarki. Amma
farillan sallah guda goma sha biyu ne; niyya
da kabbarar farko da tsayawa bisa karatun
fatiha da ambaton bismillah har k’arshenta a
bisa mazhabar Imamu Shafi’i. Da ruku’u da
daidaito cikin ruku’un da daidaita zama da
nutsuwa a cikin zaman, da sujjada da
nutsuwa cikin sujjadar da zama tsakanin
sujjadai biyu da nutsuwa a cikin zaman da
tahiyar k’arshe da zama a gare ta da salati
ga Annabi mai tsira da aminci su tabbata a
gare shi. Da kuma sallamar farko bisa niyyar
fita daga sallah da ambatonta.
Sunnoninta kuwa su ne, kiran sallah da
ik’ama da d’aga hannaye yayin kabbarar
harama da addu’ar shiga sallah da neman
tsari daga shaid’an da cewa ‘amin’ a
k’arshen karatun fatiha da karatun sura
bayan fatiha da kabbarori yayin tashi tsaye
da fad’in, ‘Sami’Allahu li man hamidahu’ da
kuma ‘Allahumma Rabbana wa lakal hamdu.’
Haka kuma da bayyanawa a wurin da ake
bayyanawa da sirintawa a wurin da ake
sirrantawa da zaman tahiyar farko da
karatun tahiyar farko da salati ga Annabi a
tahiyar farko da salati a farkon tahiya da
kuma sallama ta biyu.”
“Kin fad’i daidai, in ji malam, “ fad’a min a kan
me zakka ta wajaba?”
Kuyanga sai ta amsa masa, “zakka ta
wajaba a kan dinari da azurfa da rak’umi da
saniya da akuya da alkama da shinkafa da
sha’ir da gero da dawa da gyad’a da wake
da auduga da zabibi da dabino.”
Ya amsa, “wannan haka yake, a cikin nawa
ne zakka ke fita daga dinari?”
Ta ce...


Read / Download HIKAYAR ABUL HASSAN DA KUYANGARSA TAWADDUD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album