Join Our WhatsApp Group

JIKI MAGAYI Complete Hausa Novel Document by JIKI MAGAYI


JIKI MAGAYI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 18827



JIKI MAGAYI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 28, Sep 2023

Author: John Tafida Umaru Zaria ,Rupert East ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 90.86 kb

File Type: txt

Views: 1355+

Download: 331+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: JIKI MAGAYI-01

Copyright ©

Tafidan Zaria 1995

An fara bugawa 1955
An sake bugawa 1971
An sake bugawa 1973
An sake bugawa 1976
An sake bugawa 1978
Ansake bugawa 1980
An sake bugawa 1999 (Sabuntawa)

ISBN: 978-169-109-3
Published by
The Northern Nigerian Publishing Company Ltd., P. O. Box 412 Zaria.

Acikin Birnin Galma, akwai wani mai arziki, sunansa Malam SHEHU, Yana da jakunkunan kudi, da tufafi, da hajjoji, da kekunan dinki, da na hawa, da barori, da shanu a garkuna, da dawaki uku masu kyau suna harbin iska a barga tasa. Kullum da la'asar ya kan tafi barga ya zauna, barorinsa da mutanen gari masu son kwabonsa su zo su kewaye shi, ana! ta nishadi, fadi banza, fadi wofi.

Sabo da tajirancinsa ba inda sunansa bai kai ba, yana aikar yaransa fatauci ko ina, wadansu a jirgi, wadansu a mota, wasu su labta wa jakuna ko takarkarai ko rakuma hajjoji da goro, su shiga cikin kasa suna ciniki. Shi ma da kansa da wuya ya san iyakar dukiyarsa.

Shekararsa ashirin da yin aure, amma bai taba haihuwa ba. Ya yi aure da yawa, kullum gidansa ba a rasa matan aure hudu. Ya Batar da dukiya ba iyaka wajen malamai da bokaye da"yan bori garin neman maganin haihuwa, amma cikin matansa babu wadda ta taba ko batan wata. Ko yaushe idan ya tuna da wannan babbar hasara ta rashin ɗa sai ransa ya dugunzuma, ya dami dukkan mutanen gidansa da fade-fade, wani lokaci ma ba mai ganinsa a waje tun safe har wajen la'asar, yana can cikin dakinsa yana rokon Allah ya biya bukatarsa Ko yaushe addu'arsa daya ce, "Ya Ubangiji ka jikaina ka ba ni Ɗa
KO DA WANE IRI

Ana nan wata rana ya yi mafarki, ya ga wata godiya a gidan Malam Audu an kai ta kasuwa. Wani mutum kuwa yana sonta Kwarai da gaske har ya yi ciniki. Sai shi kuma da ya gan ta ya so ta kwarai kamar me, ya kara kudi aka sallama masa, ya biya, aka kawo masa gida ya daure. Wancan kuwa ya hakura tilas. Godiya tana gidansa har ta haifa masa dan dukushi kyakkyawa wanda kowa ya gani yana sha'awarsa. Da ya yi girma ya isa hawa, ran nan sai ya ce a yi masa sirdi. Aka yi, ya hau ya tafi kilisa. Daga can doki ya haukace ya ka da shi ya tsere, ya bar shi cikin ciwo kwarai.
Da haka ya farka daga barci, duk jikinsa na rawa, ya yi ta wasuwasin wannan abu cikin ransa har gari ya waye. Da assalatun fari ya aika aka kira masa wani malamin kasa. Da ya zo ya ce yana so ya ba shi labari. Malamin ya share kasa ya buga, ya ce, "Na ga maganar aure da kuwa haihuwa tsakani, na ga wani ya kwace gabanka, amma idan ka maida hankali za ka ture shi. Kuma na ga wahala cikin auren nan, in ka yi wata rana za ka yi danasani. In ka bi shawarata kada ka saka yatsa cikin wannan al'amari, ka bar shi yadda Annabi ya bar duniya. Saura Allah shi ya sani".

Bayan da ya tashi Malam Shaihu ya zauna yana birabini a ransa a kan mafarkinsa da abin da malamin ya gaya masa. Sai ya fado masa a rai Malam Audu yana da 'ya, sunanta Zainabu. Ya ce lalle ita ce aka nuna masa a mafarki, in kuwa haka ne in ya aure ta ya sami abin da ya ke bukata. Sai kuma ya tuna da sauran abin da ke cikin mafarkin, da shawarar da malamin ya yi masa. Amma don tsananin son ɗa ya maida duk wannan ba'a bakin kome ba idan dai bukatarsa ta biya. Ya ce watakila ma ba gaskiya ba ce, maganar matsubbata ce, sanin gaibu sai Allah. Da haka ya kwantar da ransa, ya gama shawara.

Daga nan sai ya aika aka yi kiran Malam Audu. Da ya zo suka shiga waje daya, ya ce masa, "Abin da ya sa na yi kiranka, na ga wani abu ne a wurinka wanda na ke so, ban sani ba ko watakila zan samu." Sa'annan ya buda masa.

Sai Malam Audu ya ce masa, "Wannan magana tana da wuya, domin kuwa ita Zainabu, tun suna kanana akwai wani yaro sunansa ABUBAKAR, tare suka taso, tana sonsa, shi ma kuma yana sonta, har kuwa kowa ya sani ita zai aura. Mutane da yawa da samari ba wanda bai zaburo yana sonta ba, amma ta ce sai shi. Shi kuwa Abubakar duk duniyan nan ba ya son kowa sai ita. Ka sani kuma yaro ne mai zafin zuciya kwarai, idan har bai auri Zainabu ba babu wanda ya san abin da zai yi. Ni ma da kaina ba na sha ba."

Malam Shaihu ya ce masa, "Idan ka ba ni izni in aika a kirawo ta domin in yi magana da ita, dukan abin da muka in sanar da kai."

Malam Audu ya ce, "Wannan fa ai ba maganata ba ce, sai wadda ka yi. Domin kuwa ina tsammani ko ka aika ba za ta zo ba, balle ku yi magana. Saura ni ba ni da ta cewa cikin wannan sha'ani."

Da ya koma gida ya shaida wa uwar yarinya ga maganar da suka yi da Malam Shaihu a kan Zainabu. Uwar ta ce, "Haba malam, wannan magana ma yaya za a yi ta? Idan muka yi haka ai a maida mu shashashai. Kada a ko fara yin ta ma

Da la'asar ta yi attajirin ya aika a kira Zainabu, Da aka shaida mata Malam Shaihu yana kira ta ce a koma a fada masa ba za ta zo ba. Aka koma aka fada masa. Sai ya sake aikowa a shaida mata jawabi daya kadai ya ke so ta zo su yi, shine jawabin aure.

Ta sake aikawa a fada masa ita ta rigaya ta yi miji, ba ta kowa da niyyar sake wani. Da aka zo aka fada masa ransa ya baci, ya yi fushi, ya ce, "Ashe akwai sauran mace a cikin wannan sarari wadda zan aika mata ina kira, sa'an nan ta kekashe kasa ta ce ba ta zo ba ?" Sai yaronsa da ya aika ya ce masa, "Haba, maigida, kai ka so. Ina kamarka mai kiran dubu daga wata kasa su amsa, sa'an nan ka bata kanka a wurin irin wadannan yara, ko da ya ke tana da kyau dai, ai bai kamata irinka a ci masa zarafi ba."

Ana cikin haka, sai kwaram wani cikin yaran Malam Shaihu ya tafi ya fada wa Abubakar, Malam Shaihu ya aika an kirawo uban yarinyar da ya ke tashi, ya kuma aika a kirawo ta, amma ta ki zuwa. Nan da nan sai ran Abubakar ya baci da jin wannan magana, ya rasa abin da ya ke ciki, ya yi ta doki yamma ta yi ya tafi wurin Zainabu.

Da yin yamma sai ya tafi gidansu, ya aiki kanenta ya fada mata, ta fito, suka tafi wurin da suka saba zama suna zance. Suka shiga cikin zancen duniya sai Abubakar ya ce mata, "Matar masu arziki!"

Ta ce, "Wace irin magana ce wannan da ka ke yi yau? Dama na gan ka yau duk harhar ka ke ji." Ya ce, "Abin da ya sa na fadi haka, domin na ji ance Malam
Shaihu mai arzikin garimmu ya aiko ki tafi." Ta ce masa, "Shi wanda ya ba, ka labarin bai faɗa maka jawabin da na aika a mayar masa ha?"

Mata, Halinku Na Da Wuya
"Ya fada mini, amma duk da haka raina ya tashi kwarai da gaske, domin kuwa na sani ku mata halinku na da wuya. Kin ji an ce da doki, da kogi, da mace, ba a ba su amana.
"Har ni ma watau ba ka yarda da ni ba mata ai duk halinsu daya ne." "To, sai ka ba ni dalilin da ka ce haka,"
Ya ce, "Abin da ya sa na ce miki haka, domin doki in kana sonsa, babu irin wahalar da ba ka yi masa, amma wata rana sai ya harbe ka. Kogi kuma sai kaje yanzu hanya ba ruwa, amma sa'ad da ka nufl komowa sai ka iske ruwa ya kawo, ba dama. Mace kuma an ce alkawarinta na kwana arba'in ne, idan ya wuce haka in ta sami wanda take so, komai son da ta ke yi maka ta bar ka. Malam Shahu attajiri ne, in baki so shi don kome ba za ki so shi don dukiyar tasa Sai ta yi murmushi ta ce, "Haba, Abubakar, ai da zai Yiwu kudinsa a ke takawa daga nan har mafitar rana, babu abin da zai sa in aure shi" Ya ce, "Kayya! Idan ka ga kare yana Sunsunar takalmi dauka zai yi. Amma duk abin da kika yi shi kenan." Suka yi sallama ya tafi gida, ya kwana yana ɓacin rai.

Da attajirin ya sami labarin abin da suka yi da Abubakar sai ya ce. "Bari in nuna wa yaron nan kowa ya ja da ni ya fadi." Sai ya aika aka kirawo masa wani mutum sunansa Malam SAMBO, wanda dukan mutanen garin suna tsoronsa, har da sarki. Da ya zo ya watsa masa kudi masu yawa, ya fada masa abin da ke tsakaninsa da Abubakar.

Malam Sambo ya ce, "Wannan magana mai sauki ce, wani ma ya yi rawa balle dam makada! Idan ma ka bukaci yaron nan ya mutu ne, ai Allah ya ba mu ikon da za mu yi wannan taimako."

Malam Shaihu ya ce. "Mutuwa dai ba ni so, abin da za ka yi ka juye zuciyar yarinyan nan da ta iyayenta daga gare shi."

Malaminsa ya ce masa, "To, shi ke nan, idan na koma gida yanzu ka aiko yaronka, zan ba ka wani taimako. Idan yamma ta yi ka yi abin da na aiko maka da shi, ka aika, idan ba ta zo ba ka aske mini gemu. Kuma zan aiko maka da wani magani ka san yadda ka yi ka kwaba shi cikin kudi kabata, idan dai ta karba har ta kai hancinta ta shafa, lalle magana ta kare, ko iyayenta suna so, ko ba su so, dole ne ka aure ta" Malam Shaihu ya yi farin ciki, ya kawo kudi masu yawa ya ba shi.

Da maraice ya yi ya aika aka karbo masą maganin, daya ya kwaba game da juda, dayan kuwa ya yi turare da shi. Sa'an nan ya aika a kirawo Zainabu. Da yaron ya tafi ya iske su suna zance da Abubakar Ya yi sallama, Abubakar ya amsa ya ce, "Me ka ke nema?"

Yaro ya ce, "Malam Shaihu ne ya aiko ni wurin Zainabu yana son ganinta." Sai Abubakar ya ce, "Koma, ka gaya masa ba ta zuwa."

Har yaron ya yi nisa, sai ta zabura ta tsunka a guje ta kirawo shi a gaban Abubakar. Ta ce ya fadawa maigidansa tana zuwa, amma waccan magana da ya aiko da fari lalle ba ta tsakaninsu. Daga nan Abubakar ya ce mata, "To, ai ga shi nan ko da jiya ban fada miki ba. "

Ta ce masa, "Haba, Abubakar, ai wannan ba kome ba ne. Gani ba ci ba ne, tafiyarta kuwa ba ita ce aurensa ba. Na rantse maka da gaskiyar zamani ba ni auren kowa nan duniya idan ba kai ba. Watau fadin ina zuwa ai domin ransa ya yi masa dadi ne kawai, kada ya ce na wulakanta shi sau biyu, domin kuwa ka san halin ku maza, idan aka yi muku gantsi a kan sha wuya wata rana."

Ya ce, "Shikenan, duk abin da kika yi daidai ne." Suka yi
sallama, ta yi masa rakiya,

Da komowarta gida sai ta yi wanka, ta yi shiri. Ta ce wa uwarta za ta tafi wurin Abubakar, yanzu tana komowa. Da fitarta ba ta zame ko ina ba, sai gidan Malam Shaihu, ta iske zaure tinjin ana ta hira. Sai ta wuce ciki ta jira shi a soro na uku. Jim kadan sai Malam Shaihu ya shuri takalminsa ya shiga gida, duk wuri ya gume da kanshin turare. Da jinsa yana zuwa, sai ta rufe kai.

Da shigowarsa sai ya ce, "Zainabu, kin zo? Don me na aika sau biyu a yi kiranki kika ki zuwa zan ci namanki ne?"

Ta ce masa, "Ai dama ce ban samu ba." Suka yi gaisuwa. Sa'an nan ya ce mata, "Abin da ya sa na
yi kiranki, na ji labarinki ne. Na kuwa ji akwai wani wanda ki ke sonsa, amma na sani ba a yi masa baiko da ke ba, ko an yi masa kuwa ni ina so, sai na ga abin da ya kore ni."

"Me zai kore ka, kai ba mutum ba ne? Mutum na kin
mutum ne ?"

"To, ina son ki da aure."

"Ni ma ina sonka, saura ba da aure ba," "Don me ba da aure ba ?"

Har Yanzu Ina Kaunarsa "Domin kuwa tun ina yarinya babu wanda na ke so tamkar Abubakar, har yanzu kuwa ina kaunarsa. Duk garin nan dai dai ne wanda bai neme ni ba, amma duk sun ga ba dama sun watsar. Kuma bari in gaya maka gaskiya, ka ga dai na sani kai
mai arziki ne, Abubakar kuwa talaka ne dan uwana, in na aure ka babu yunwa balle kishin ruwa. Saura da abu daya, na ji kai mutum ne mai zara, da yau za ka ga wadda ta fi ni kyau sai ka ce ita ka ke so. Kuma ka cika aure aure da yawa, duk wadda ka aura kuwa idan kuka yi 'yan shekaru ka ga ba ta haifu ba sai ka sake ta da cin zarafi, ga shi kuma, kana da matanka hudu, dukansu babu wadda ba ta girme ni ba. Ni ba zan iya kishi da su ba, ka sani kuwa ba a yin mata biyar balle ka ce za ka aure ni. Ya ce mata, "Wannan ba magana ba ce, tun da ya ke na ce ina souki da aure, idan kina sona ki amsa mini, ni nasan yadda zan yi. Ba a saki ?"

Ta ce, "Oho, tun da ya ke sakin wata za ka yi ka aure ni," ni kuma wata rana haka za ka sake ni, idan ka ga wata wadda ta fi ni kyau ka auro ta."

Kina Sona?

"Ba haka ba ne, Zainabu. Abu daya na ke so a gare ki, idan dai kin amsa kina sona, shi ke nan." "Babu dama!"

"Na ba ki damar kwana bakwai, dukan abin da kika shawarta ki komo ki shaida mini, domin in san abin da na ke ciki."

"Wace shawara zan yi? Ai shawarata ke nan."

"A'a, ke dai ki yi shawara."

Suka yi sallama. Za ta fita ya ce ta dakata masa. Ya shiga gida ya debo kudi da goro ya kawo mata

Ta ce, "A'a, wallahi ba ni karbar kome naka. Idan na karba aka gani a gida za a doke ni, kuma duk wanda ya ji tun yanzu na fara karbar abu daga hannunka, sai ya tabbatar mana da halimmu na mata." Ya ce, "Kwashe. Kin sani ko ba don wannan magana ba ni mai ba...


Read / Download JIKI MAGAYI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album