Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR KAIDIN MATA Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR KAIDIN MATA


HIKAYAR KAIDIN MATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 7114



HIKAYAR KAIDIN MATA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Bukar Mada ,Yusuf Abdullahi A Jibaga ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08071051138

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 39.25 kb

File Type: txt

Views: 626+

Download: 138+

Last download: 3 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

01 KAIDI!

Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan
sarakuna. Shi ne mafi tsarki daga dukkan
abubuwa. Tsira da aminci su tabbata ga
Manzonsa kuma Annabinsa, Muhammadu dan
Amina (SAW).
akwai wani sarki ne da ya kasance yana da
masaruta mai giman gaske.. - a takaice dai -
wannan sarki babu abunda ya rasa a duniya, sai
dai kawai matsalar itace : .. bashida (‘DA) na miji
da zai gajesa.
To sai wannan abun ya damesa sosai, sai ya yi
ta rokon ALLAH.. sai ALLAH ya arzuqtashi da
(‘DA) na miji kyakkyawa kamar farin wata. To
bayan wannan yaro ya girma , sai mahaifin nasa
ya hadasa da malamai masu hikima su koyar
dashi.
To ana nan sai wata rana daya daga cikin matan
wannan sarki ( mahaifin wannan yaro ) ta nemi
tayi lalalta da ( 'Dan) sarkin.. sai dan sarkin ya ki
amincwa, kuma yace sai ya sanar da mahafinsa
ya kasheta.
Da wannan mata taji haka sai tayi sauri ta
garzaya zuwa wurin sarkin, ta riga yaron zuwa
wajen wurin mahafin nasa, tayi ta kuka tana I’hu.
Da sarki ya tambayeta me ke faruwa ? sai
tacemasa : Ai ‘Danka ne ya so yayi lalata dani, ni
kuma sai na ki amincewa, sai yace sai ya
kasheni, ni kuma sai na gudu na zo wurinka ka
ceceni kuma ka dauka mini fansa.
Da sarkin ya ji wannan magana sai yayi fushi
sosai, ransa ya baci atake ya tara waziransa ya
umurcesu da su kashe wannan yaro (‘Dan nasa)..
To sai waziran sukayi shawara a tsakaninsu
sukace : yanzu sarki ya samu mu kashe wannan
yaro nasa , idan har muka bari aka kashe wannan
yaro, to babu shakka sarki zai yi nadama
dagabaya, saboda yanzu yana cikin tsananin
fushi ne shi yasa ya dauki wannan mataki.kuma
Bayan wani dan lokaci Idan sarki ya huce daga
fushinsa yayi nadama, to mu zai zarga, zai ce :
me yasa muka kyalesa ya dauki wannan mataki ?
me yasa bamu bashi shawara ba ? me yasa
bamu bullo da wata dabara da zata hana shi
kashe wannan yaro ba ?..
To sai wadannan wazirai suka yi shawara a
tsakaninsu gameda wannan al-amari, ra’ayinsu ya
zo daya, suka amince cewar zasu bullo da wata
dabara da zata hana wannan sarki aiwatar da
wannan danyen hukunci akan (‘DAN) nasa. Kuma
zasu sa sarkin ya canza ra’ayinsa.
To sai daya daga cikin waziran ya gabato yace :
A yau ni dinnan zan kareku daga sharrin wannan
sarki, zan canza masa ra’ayi. Sai wannan wazir
ya nufi fadar sarki, ya shiga ya tseya a gabansa
ya nemi izinin yin maga, sai yace masa : - ya
mai martaba : yanzu – misali - da ace kana da
‘YA’YA 1000, to bai kamata ka yiwa zuciyarka
da’a ka kashe daya daga cikinsu ba kawai
saboda maganar da matarka tafada akan wannan
yaro. Abu daya cikin biyu ne : ko ya zamanto
wannan matar taka ta fadi gaskiya, ko kuma
kariya da sharri ta masa, watakila wannan
makircine ta shiryamasa !
Da sarkin yaji wannan magana daga bakin wazirin
sai yacemasa : shin akoi wani labari da ka taba
ji – ya iso maka - gameda makircin mata ne ???
To a nan sai wannan waziri ya bawa sarkin wani
labari mai ban al-aljabi wanda yake kunshe da
makircin mata. Bayan sarkin ya ji wannan labari
sai ya huce ya sauya ra’ayinsa gameda kashe
wannan (‘DA) nasa.
bayan wazirin ya fita daga fadar sarki, sai
wannan mata ta ji labarin cewar sarki ya huce ya
canza ra'ayinsa gameda kashe wannan yaro, sai
ta garzaya ta shiga wurin sarki ta yi ta kuka tana
I’hu, ta tayarwa da saki hankali, tacemasa : idan
bai daukar mata hakkinta daga wurin dansa ba,
to zata kashe kanta, zata kona kanta, kuma zata
mutu ta bar hakkin a rataye kan wannan sarki,,
kuma sai tace masa : shin baka san halin maza
bane ? baka san makircinsu da kadin ba ? da irin
zalunci da suke yiwa mata ?
To a nan sai wannan mata ta bawa sarkin wani
labari da yake kunse da makircin maza da
zaluncisu a kan mata, kuma a karshe sai matar
tanemi sarkin da ya ya kashe wannan yaro
saboda ya tabbatar mata da hakkinta.

Da sarkin yaji maganar wannan mata da kuma
labarin da ta bashi, sai ya rikide hankalinsa ya
tashi ransa yabaci sosai, atake sai ya bada
umurnin akashe wannan (‘DA) nasa .
To bayan haka, labari ya iso wa waziran sarki
cewar sarki ya bada umurnin a kashe wannan
yaro. To a nan sai waziri na biyu ya shigo ya
tseya a gaban sarki ya rarrashi sarki ya lallabesa
ya gayamasa irin abunda dayan wazirn ya fada
masa, kuma ya bashi labarin makircin mata. To
da sarkin yaji wannan labari sai ya canza
ra’ayinasa gameda kashe ‘(DAN) nasa.
Washe gari sai matar taji labari, sai ta kara
garzayawa zuwa wurin sarki tayi kuka ta
maimaita maganra da tayi a baya, ta zuga sarki
akan sai ya kashe wannan yaro, kuma ta bashi
wani labarin daban gameda makircin maza. Da
sarkin yaji maganar wannan mata sai ransa ya
baci hankalinsa ya tashi atake ya kara canza
ra’ayinsa kuma ya bada umurnin a kashe wannan
yaro.

To haka aka yi ta yi, idan matar ta fita sai waziri
ya shiga ya bawa sarki labarin makircin mata sai
sarki ya huce ya canza ra’ayi, washe gari sai
matar ma tashiga ta zuga sarki ta bashi labari
gameda makircin maza, ta canza masa ra’ayi…
haka akayi tayi,, akayi ta zama cikin wannan hali,
har sai da wazirai 7 suka shiga wurin sarki suka
bashi labarin makirci da kaidi na mata. Kuma
kowannensu bayan ya fita, sai itama matar ta
shiga ta bada nata labarin gameda makircin
maza, ta zuga sarkin....

LABARIN YANA DA
YAWAN GASKE, AMMA ZAMU KAWO MUKU
CIKEKKEN LABARIN GABADAYA A CIKIN
LITTAFIN MU MAI FITOWA, WATO DARE DUBU DA DAYA. WANDA KE KAN HANYAR FITOWA..

yanzu dai ga daya daga cikin makircin
mata ku karanta ga labarin da waziri na shida ya baiwa sarki. Yanzu labari dai fara"

da waziri na 6
ya shigo sai yacewa sarkin ya mai martaba ! ya
kamata ka jinkirta aiwatar da wannan dayen
hukunci na kisa akan danka, saboda ita
batacciyar hanya kamar hayaqi take, shi kuma
gaskiya kamar gida ne wanda rukunanasa
(ginshikinsa) a tabbace yake , kuma ita gaskiya
tana da haske, haskenta yana kawar da duhu na
bata,kuma kasani fa kaidin mata yana da girma
sosai, makircinsu yana da yawan gaske, shi yasa
ubangijin ALLAH ya fada a cikin littafinsa : ﺇﻥ ﻛﻴﺪ
ﻛﻦ ﻋﻈﻴﻢ ( wato kaidin ku yana da girama) ..
hakika na taba jin labarin wata mata da ta yi wa
wasu dattawa kuma shuwagabanni wata kasa
makirci mai girma wanda ba’a taba yin irinsa ba
a baya , sai sarkin yace : yaya haka ya kasance ?
kabani labarin wannan makircin mana in ji ? sai
wazirin yace : ya mai martaba labari ya iso mini
cewar : akoi wata mata da ta kasance daya daga
cikin ‘ya’yan wani hamshakin attajiri, kuma mijin
wannan mata ya kasance mai yawan tafiye tafiye
ne, To sai wata rana mijin wannan mata ya yi
wata tafiya mai tsawo kamar yadda ya saba, ya
dauki lakaci mai tsawo bai dawo ba, To sai
wannan mata ta kasance ckin tasananin kewar
rashin mijinta, a dalilin haka sai hankalin wannan
mata ya karkata zuwa ga daya daga cikin
samarin da suke aiki a gidan mijin nata, sai ta
kaunace shi ta so shi so mai tsanani…
To ana nan,, wata rana sai aka wayi gari wannan
saurayi ya shiga cikin gari, ya yi chachar baki da
wani mutum sukayi fada suka tayar da tarzoma
da hayaniya a tsakaninsu, To sai wannan mutumi
ya kai karan saurayin zuwa wajen gwamnan
(governor) na wannan gari, atake sai gwamnan
ya sa aka kulle wannan sauri a gidan yari, bayan
haka sai labari ya iso wa wannan mata, cewar an
kulle wannan saurayi - masoyinta -, sai
hankalinta ya tashi ta rikide..

To bayan wannan mata ta ji labarin kulle
masoyinta, kawai sai tayi kwalliya ta sanya mafi
kyawun tufafinta ta nufi gidan gwamna,
(governor) da isarta gidan sai ta yi sallama ta
shiga ta samu gwamna yana a cikin ofishinsa, sai
ta mika masa takarda wanda yake kunshe da
bayani cewar wannan saurayi mai kamanni
..kaza.. da aka kulle ( 'Dan Uwanta) ne, kuma
wannan mutumi da sukayi hayaniya sukayi fada
da wannan saurayi har yasa aka kullesa ba shi
bane da gaskiya, kuma mutanene da suke wurin
lokacin da aka yi wannan rikici basu bada shaidar
gaskiya ba, yanzu gashi an kulle wannan 'Dan
Uwan nawa ( saurayin ) a gidan yari a karkashin
ikon ka, kuma zaluntarsa aka yi, gashi ni kuma
bani da kowa, bani da wanda zai ke lura dani a
gida, mijina yayi tafiya, shi yasa nake neman
alfarma a wurin mai girma gwamna ya taimaka
ya bada umurni a saki wannan ‘Dan Uwan nawa
( wannan shine abunda takardar wannan mata ya
ke kunshe da shi )
Da gwamna ya karanta takardan wannan mata
kuma ya fahimci abun da ke ciki. Sai ya daga
kansa ya kalli wannan mata, kuma yaga tana da
matukar kyau, to sai hankalinsa ya karkata zuwa
ga wannan mata ya ji yana son ta da lalata, sai
yacemata : yanzu ki tashi ki shiga gidana ki
zauna ki jirani, zan je in kawo miki ‘DAN Uwanki
ba tare da bata lokaci ba, yanzu zaki daukeshi ki
tafi da shi.. sai tace masa" ranka ya dade
gwamna ! ni fa bani da kowa a garin nan in ba
ALLAH ba, kuma ni bakuwa ce bazan iya shiga
gidan wani ba, sai mai girma gwamnan yacemata
: To bazan sake shi ba har sai kin shiga cikin
gida, na biya bukatana da gare ki, sai matar
tacemasa : idan kanaso ka biya bukatarka ne, to
ya zama dole kai ka zo gidana ka zauna ka huta
kayi bacci ka babu wanda zai sani.. To sai mai
girma gwamnan ya tambayeta yacemata.

gidan naki yana ina ne ? sai tace : gidana yana wuri
kaza … (sai tayi masa kwatance ) ta bashi lokaci
da zai zo.. daga nan sai ta fita abunta ta bar
gwamna cikin tunani, zuciyarsa tana tamasa raye
raye, shaidan na tunzurasa.
bayan wannan mata ta fita daga ofishin mai
girma gwamna, sai ta nufi ofishin shugaban
alkalain wannan gari. Bayan ta isa ofishin sai ta
shiga ta same shi tace masa : ranka ya dade
shugaban alkalai ! . sai alkali yace : NA’AM Ina
sauraronki kifadi bukatarki, sai tace : ya mai
girma inso ka yi min alfarma ka duba wannan
lamari nawa kayi A’dalci ALLAH zai yi maka
sakayya.. sai mai girma alkalin yace mata"

wanene ya zalunceki ? sai tace : ranka ya dade
akoi ‘Dan Uwana da aka kulle, kuma bani da wani
a garin nan in ba shi ba, a dalilinsa ne na fito na
zo wurinka ka taimaka ka kubutar da shi, saboda
mai girma gwamna shine ya kulle shi, kuma wasu
mutane ne suka masa shaidar kariya sukace
shine azzalumi mai laifi.. saboda haka nazo
wurinka ka taimaka ka je wurin mai girma
gwamna ka nema mini alfarma saboda a kubutar
da ‘Dan Uwana.
Da Alkalin ya ji wannan magana sai ya daga ido
ya kalli wannan mata, sai shima hankalinsa ya
karkata zuwa gareta ya sota da lalata, To sai
yacemata : ki shiga cikin gida ki zauna tare da
kuyangu zuwa dan wani lokaci, ni kuma zan aika
wa maigirma gwamna saboda ya kubutar da ‘Dan
Uwanki.. kuma ai da nasan kudin da za’a biya a
kubutar da shi da zan biya saboda nima in samu
biyan bukatata daga wurinki, saboda gaskiya
kyawawan kalamanki sun burgeni sosai.. sai
tacemasa : - cikin fushi - ashe duk kanwar ja ce,,
idan har ya kasance kai da kanka – al kali - kana
aikata haka To ai bazan zargi wani ba idan ya ai
kata haka,,, sai alkalin – cikin fushi – yacemata :
idan baza ki shiga cikin gidana ba to ki tashi ki
kama hanya ki tafi kiyi gaba.. sai tacemasa : A’A
ranka ya dade, ai ba haka bane ! idan har kana
so ka biya bukatarka ne Ai gidana yakamata ka
zo, saboda hakan ya fi kyau ya fi rufin asiri, akan
da hakan ya faru a gidanka, saboda a gidanka
akoi ‘yan mata kuyangu da masu aiki (hidima) da
masu shige da fice, saboda ni mace ce wanda
bata saba da irin wannan harka ba (lalata) amma
yanzu bukata da matsuwa ta sani cikin harkar..

sai alkalin ya tambayeta inda gidanta yake, sai
tacemasa : gidana yana wuri kaza..( ta yi masa
kwatance.) Sai ta bashi lokaci da zai zo, kuma
lokacin daidai yake da lokacin da ta bawa mai
girma gwamna. Daga nan sai ta kama hanya ta
fita abunta ta tafi.

Bayan wannan mata ta fita daga ofishin alkali,
sai ta nufi gidan waziri (minister).. da isarta ta yi
sallama ta shiga ofishin mai girma wazirin sarki,
bayan ta yi gaisuwa, ba tare da bata lokaci ba ta
gabatar da bukatarta ga mai girma waziri, ta
bashi labari daga farko zuwa karshe, ta koka
masa matsalar da ‘Dan Uwan ta – saurayin - ke
ci, kuma ta sanar da shi cewar mai girma
gwamna ne ya kulleshi.. To a nan sai shima
waziri hankalinsa ya karkata zawa ga wannan
mata yaji ta kwanta a ransa ya sota da lalata.
Sai yacemata : zamu biya bukatar zuciyarmu
daga gereki sannan sai mu kubutar da ‘Dan Uwan
ki.. sai tacemasa : idan haka kake to Ai
yakamata kazo gidana, saboda hakan yafi mana
rufin asiri dani da kai gabadaya, saboda gidanan
bashi da nisa daga nan, kuma ka san muna
bukatan tsabtataccen wuri mai kyau. Sai ya
tambayeta yace mata : A ina gidan naki yake ?
tacemasa : A wuri kaza .. - ta yi masa kwatance
- sai ta bashi lokaci daidai da lokacin da ta bawa
gwamna da alkali. Daga nan sai ta fice abunta
daga gidan waziri.

To Da wannan mata ta fita daga gidan waziri sai
ta nufi gidan mai martaba mai alfarma sarkin
wannan gari, bayan ta isa ta sumu shiga fadar
mai al farma batare da bata lokaciba, ta gabatar
da kokenta zuwa ga mai martaba sarki, ta bashi
labarin abunda ya faru daga farko zuwa karshe,
kuma ta roki taimako da alfarman a kubutar da
‘Dan Uwanta.. sai sarkin ya tambayeta yacemata
: wayene ya kulle ‘Dan uwan naki ? sai tacemasa
: mai girma gwamna ne ya kullesa. Da mai
alfarma yaji dadin kalaman wannan mata, sai
harsashin soyayya ta harba cikin zuciyarsa. Sai
ya umurceta da ta shigo cikin fada tare da shi,
zai aika wa mai girma gwamna da umurni da a
fito ‘Dan Uwan ta da aka kulle. Da wannan ta
fahimci abunda sarkin ke so - yanaso yayi lalata
daita -, sai tacemasa : ya mai martaba ! wannan
Ai abune mai sauki a gareka, saboda ko ina so
ko bana so idan sarki ya bukaci abu a wurina Ai
wannan abun al faharine agareni. Amma kuma da
zaifi kyau ace mai martaba sarki ya zo gidana,
saboda hakan zai daukakani idan ya tako da
kafafunsa masu al barka ya zo gidana. Sai ta
yabe shi da wannan baiti na kasida kamar haka.

ya ku Abokanaina shin kun taba gani ko kunji
ziyarar mutumin da karamcinsa ya yi yawa a
gareni
Sai mai martaba sarki yacemata : Ai ba zamu ki
bin umurninki ba . sai shima ta bashi lokaci
daidai da lokacin da ta bawa mai girma gwamna
da al kali da waziri. Kuma ta kwatanta masa inda
gidanta yake.
To Da ga nan sai wannan mata ta wuce wurin
kafinta…

RANAR LARABA INSHA ALLAHU , Zan dora daga yarda na tsaya misalin 9 pm02 KAIDI!

bayan wannan mata ta kwatanta sarkin inda gidanta
yake. Da ga nan sai ta wuce wurin kafinta ta
samesa tace masa : inaso ka kera mini drowa
(drewer) mai hawa 4 ajere daya bayan daya,
kuma ka sa masa wurin makulli da kwado a
kowanne bangaer (hawa) daga ciki ta yadda zai
yu a kulle, sannan ka gaya mini nawane kudin
aikinka in biyaka.. sai kafintan yace : kudin aikna
DINARI 4 ne.. amma ranki ya yade da zaki yi mini
alfarma ki bani dama in samu ganawa da ke in
biya bukata (lalata)...


Read / Download HIKAYAR KAIDIN MATA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On HIKAYAR KAIDIN MATA
avatar
hamisu-6

5 months ago

Reply

I have subscribed to one of your package but still I ca'nt download

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to hamisu-6

have You paid the package Money, if you paid contact me here 08140419490

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album