Join Our WhatsApp Group

CIN AMANA Complete Hausa Novel Document by CIN AMANA


CIN AMANA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17351



CIN AMANA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, Oct 2023

Author: Rashuna ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09037093702

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 95.94 kb

File Type: txt

Views: 743+

Download: 257+

Last download: 3 days ago

Description/Story: [7/3, 7:58 PM] Rabi: [9:23PM, 7/2/2022] RSN: https://chat.whatsapp.com/E4JKvmLLlKFDlPYRLgp
[9:24PM, 7/2/2022] RSN: BEBE'ARTH


CIN AMANA


Wattpad@Rashuna


Godiya mai tarin yawa ga sarki Allah, wanda babu wani sarki sai shi, shi zai bani ikon fara rubuta wannan littafi, Allah ina rok'onka ka bani ikon rubuta shi dai-dai, ka kuma saka na kammalashi cikin k'oshin lafiya da amici, Allahuma Amin.

Na sadaukar da wannan littafi ga mahaifina, don haka ina rok'on duk wanda ya karanta wannan littafi da yayi masa addu'ar Allah ya k'ara masa lafiya da nisan kwana mai amfani, yayi masa tukuici da gidan aljanna sakamakon babban JIGO da ya zamowa ahalinsa Allahuma amin.
i love u so much Babanmu abin alfaharinmu Yaya jigon tafiyarmu, Allah bar mana kai cikin aminci.

Ina sunkuyar da kaina gami da durk'usawa bisa kawo gaisuwa ga Iyayena na gari, ina adduar Allah ya k'aro d'aukaka da albarka,lafiya wadata, nutsuwa kwanciyar hankali, Amin.

Ina yaba muku 'yan uwana, ina rok'on Allah ya k'aro mana d'aukaka da cigaba gami da albarka a rayuwarmu ta duniya da lahira amin.
Ina ji da ku, ina al'fahari da ku Allah ya k'ara hada kanmu ya bar zumunci, amin.
Falalu Shu'ayb Nababa
Na'ima Shu'ayb Nababa
Halifa Shu'ayb Nababa
Fadila Shu'ayb Nababa
Rabee'ah Shu'ayb Nababa
Mardiyya Shu'ayb Nababa
Abdul Rahaman S Nababa
Murja Shu'ayb Nababa
Allah kaiwa mahaifanmu tukuici da gidan Al'janna, sakamakon gina KATANGAR k'aunar dake tsakaninmu Allah kuma kar ka bawa wani damar rusa mana ita, Amin ya Allah.

Babban tukuici ga yarana.
Aseep,Aydha,Abrar,Aseefa.
Allah ya kawo albarka cikin rayuwarku, ya k'aro mana zuri'a mai tarin albarka da wadata Amin.


1
――――――
Da gudunta ta shigo falon, ta na k'walla kiran ‘’Dad‘’ tana nbaza ido taga ta ina zai fito, kacibis sukai a k'ofar da za ta sada ka da falonsa na biyu, jikinsa tai saurin fad'awa tana ruk'unk'umeshi yayin da shi kuma ya k'ara matseta a cikin jikinshi yana me lumshe idanuwansa·
‘’Nayi kewarka Dad‘’
Ta fad'a da siririyar muryarta mai taushi, yayin da shi kuma ya kuma shigar da ita jikinsa sosai kamar zai tsagata biyu kana yace.
‘’Nima nayi kewarki shalelena, amma meyasa ba ki gayan yau za ki dawo ba?‘’
‘’Suprise zan baka that is why.‘’
Takai k'arshen maganar tana sakar masa kiss a wuya, wanda yai sanadiyar dakatawar maganar da yai nufin yi, jikinsa ya d'au d'umi sosai, yayin da ita kuma ta fara k'ok'arin barin jikinsa amman ta kasa saboda ba k'aramar matsa yayi mata ba·
‘’Dad‘’
Ta fad'a da k'arfi ganin tunaninsa ya tafi wani guri da ban, murmushi ya sakar mata yana me sauke lab'b'ansa kan lab'b'anta ya bata,hot kiss, murmushin itama ta sakar masa ya ja hannunta suka fita daga falon zuwa falo na biyu, dining area suka nufa yaja mata kujera ta zauna, da kansa ya zuba mata abincin ya kuma zauna ya ciyar da ita, wannan ya zame masa jiki ko kuma nace k'aida, muddun yana gari, itama tana gari da kansa zai zauna ya ciyar da ita, inkwa ba ya gida baza taci ba har sai ya dawo.
Bayan gama cin abincin nata ya dubeta da kulawa yace·
‘’Yanzu kije ki wanka ki huta sai kizo ki sameni a d'aki mui magana·‘’
Mik'ewa tayi tana murmushi ta d'an durk'usa ta gefensa tai masa kiss a kumatu kana tace.‘’Thank you so much Dad.‘’
Ta juya ta bar falon, yayin da shi kuma yabi bayanta da mayun idanuwansa kamar ya cinyeta d'anya yana ayyana abubuwa masu yawa a ransa·

Idan tana tare da Dad d'inta dukkan wata damuwa mantata take, yanzunma hakanne ya faru da ita, tana barin sashensa damuwar da ke ranta game da mahaukaciyar nan ya dawo mata sabuwa, ta rasa me yasa matar ta shiga ranta ta zauna, tausayi ne ko kuwa son taimakonta ne? babu me bata wannan amsoshin kuma zucitarta ma ta gaza bata, wayo to zai bata? shi d'inma dai babu·
Tana shiga d'akinta, wanda tsayawa gaya muku tsaruwar da yayi b'ata lokacine kawai ku k'iyasta, kayan jikinta ta shiga cirewa ta fad'a toilet ta dad'e sosai cikin ruwan d'umi kana tayo wankan ta fito had'e da d'auro alwala, don ta jiyo ana kiran sallah ta masallacin dake cikin gidan, don yanzu lokaci ya juya shida dai-dai ake kiran sallar magariba·
Riga mara nauyi ta samu ta zira, ta saka zumbulelen hijabinta ta kalli gabas, yadda ta nutsu ku baza kuce NAFISA ce SHA LELEN Dad ba·

Ba ita ta fito daga d'akinta ba sai da ta gabatar da sallar isha tukunna, d'akin Dad ta nufa suyi maganar da zasui don wani nishad'an d'an bacci take ji, idanuwanta har wani lumshewa suke, tare da Mom ta tarar da shi suna hira dukkaninsu murmushi suka sakar mata tare da bud'e hannuwansu alamun ta taho garesu, tsayawa tayi tana binsu da ido, tana tantance tsakanin Mom da Dad wa ya fi k'aunarta amsar da har yau ta gaza samunta a k'wak'walwarta idan tana wannan tunanin kanta,har ciwo yake, kusan had'a baki sukai wajen fad'in·
‘’Tawo mana·‘’
Tsakiyarsu taje ta zauna, ta kamo hannuwansu ta rik'e ta kwantar da kanta a kafad'ar Mom, yayin da Dad ya matso yana kai hannunsa wuyanta·
‘’Baki da lafiya ne shalele?‘’
‘’UMUM bacci kawai nake ji·‘’
‘’Yau ba fita kenan?‘’’
Kai kawai ta d'aga masa, Mom tace·
‘’Ai in kika fita sai kin fi jin dad'i, amman bacci da farar safiyar nan ai sai ki gaji da kwanciya kafin gari ya waye tashi maza muje na shirya ki·‘’
‘’To ai magana zamui da Dad·‘’
‘’Kwayi maganar idan Allah yai mana yawan rai zuwa gobe‘’
Takai k'arshen maganar tana mik'ar da,ita tsaye, yayin da ita kuma takai dubanta zuwa fuskar Dad ganin baice komai ba yasa ta bin Mom d'in·
Hmmmmm masu karatu, idan zan shekara inai muku rantsuwar Nafisan d'azu ce da ta kalli gabas itace yanzu Mom ta shirya ba za ku yarda ba, cewa zakui wannan Rani Mukhraji ce ta cikin film d'in india don basu da maraba hatta k'wayar idonsu, da kyakkyawan murmushin da ke k'ara fito da zallar kyansu, wata arniyar rigace a jikinta black nd white, samanta ne black in me gashi-gashi sai walwali yake,da d'aukar ido k'asan kuma white shikumar kamar net yake, iya kacin rigar guiwarta, sai santala santalan k'afafuwanta dake ta shek'i, ba kwalliya a fuskarta sai jan jambaki kawai da ya k'ara k'awata lab'b'anta masu gwanin burgewa, girarta a gyare take sai ku rantse jagira tayi, sai dogayen eye leshers inta da suke a tsaitsaye gazar -gazar,gashin kanta kuwa yasha gyara sai shek'i yake tai mata parking insa a tsakiyar kanta da black nd white in riborm jelar sai reto take kasancewarsa ba mai cika tsayinma dai ba wani can ba, wata had'ad'd'iyar bandana ta saka black mai d'an fad'i don ta kusa rufe rabin kanta, stone d'in jikinta white ne yane ta walwali, a santalelen wuyanta siririyar sark'a ce ta diamond haka abin hannu da agogo da zobuna. A ko da yaushe ba ka rabata da su, kuma iri da ban da ban, plat in takalmi ta saka white, kasancewarta me tsayi ba ta fiya saka heals din takalma ba, sai dai idan tai ra'ayi·
Har cikin mota ta rakata, taso taje gurin Dad Mom ta hana ta, rafar 'yan dubu ta bata, don tasan ba kud'i a hannunta sai A·T·M shiyasa ta bata don ta wutar da ita, cike da jin dad'in wannan soyayya da Mom take mata ta bar harabar gidan, yayin da Mom ta juyo idonta ya sauka akan Dad da ya saki labilen tagar da ya gama lek'e tsaki ta ja had'e da fad'n·
‘’ Jarababbe·‘’

‘’Yanzu ita kad'ai ta tafi?‘’
‘’To ni kake so naje na kaita?‘’
Itama ta jefo masa tambayar a zafafe, ganin hakan yasa shi kwantar da kai had'e da fad'in·
‘’Ba haka nake nufi ba, da kin bartan tun da tace bacci take ji, zuwa gobe drivern nata zai fara aiki, shine ma maganar da nake son muyi da ita don ni sam bana son fitarta ita kad'ai·‘’
‘’Nifa ina jin tsoron d'aukar mata irin drivern da ta lissafa tana so, don kasan nak'i jinin saka ido cikin rayuwata·‘’
‘’Haba-haba Jamila ni jakin ina ne zan d'auko abinda zai zame mini matsala, kema kin san sam bazai yuhu ba, amman kuma kinsan ya zamo mini farilla na cikawa Shalelena burinta, na samo mata drivermara muni, kuma me tsafta, amman bagidaje ne sam bashi da wayewa, kuma yana da tsagu a fuskarsa har da bille, bashi da asali don nayi bincike sosai a kansa kafin na daukeshi aiki, mahaukaciya ce mahaifiyarshi, kuma ta mutu, a wani gida yake gadi, to shine me gidan ya rasu iyalansa suka koma kano da zama, dalilin da yasa yake neman wani aikin kenan har aka kawosa gurina sai naga shi ya can canta da drivern Shalelena, kuma kan na d'aukesa sai da na kafa masa sharud'a·
‘’Auho, to har naji sanyi a raina, don da har na tsorata da zsbin FANAN kar muje mu d'ebo ruwan da zai dafa kawunanmu gaba d'aya‘’
Takai k'arshen maganar tana dariya yayin da Dad ya tayata kafin su shiga wata hirar ta da ban, wacce sam ba fahimta nake ba·


# N·W·A
[7/3, 8:01 PM] Rabi: BEBEARTH

https://chat.whatsapp.com/JPKVCkDzizKFRFZcpvfF1v
[11:51PM, 11/24/2021]
Ga link na gruop nan, dan Allah dan Allah, don soyayyarku da manzon Allah duk wacce ta san ba karanta littafin ne zai kaita ba kar ta b'atawa kanta lokaci, nima ta b'ata mini gurin fiddata.


CIN AMANA



Wattpad@Rashuna


2
A hankali take driving kasancewar akwai baccin sosai a cikin idanuwanta, a haka dai har ta isa harabar k'ayataccen Hotel, wanda sai d'an wane da wane ne ke shigarsa saboda mugun tsadarsa, parking in motarta tayi ta fito tai locking inta, ba ta d'auko komai ba sai rafar 'yan dubun da Mom ta bata, gefen hannunta na hagu ta bi wanda ya sadata da clube in da ya tara maza da mata, musulmai da k'abila yare da ban da ban, ko wanne yana harkar da ta kawo shi, tana shiga gurin aka saka ihu da sowa ana mata kirarin da aka saba, musamman da sun kwana biyu ba su ganta ba.
‘’'YAR DA DUNIYA KE YAYI, KI TAKA A SANNU SHALELEN DAD, SARAUNIYA AMARYA A GIDAN SAMEER‘’
Babu gefen wanda ta kalla, kujera kawai ta jaho ta na yatsina fuska, in da sabo dama sun saba da miskilancin nata, yayin da wasu kuma suke mugun jin haushinta, wasu kuma take birgesu ainun.
Sameer ne ya shiga yi musu ruwan kud'i ko ta ina, saboda jin dad'in kalmarsu ta k'arshe, kana ya isa ga gimbiyar tasa da take ta cin magani, kujerar da ke facen inta ya jaho ya zauna, yana binta da wani shu'umin kallo me fito da zulamarsa a bayyane, siririn tsaki ta ja had'e da kautar da fiskarta gefe a dai-dai lokacin wetres in gurin ya ajiye mata tire a gabanta me d'auke da kwalbar giya da glass cup a kai, yayin da Sameer ya saki shu'umin murmushin da shi kad'ai ya san ma'anarsa, kana yayi saurin d'aukar botle in giyar yana k'ok'arin bud'ewa ya zuba mata zazzak'ar muryarta ta ratsa kunnuwansa.
‘’Kar ka wahalar da kanka yau ban jin shanta‘’
Tsayawa yayi yana kallonta rik'e da botle in a hannu, kallon cikin ido tai masa, had'e da d'an zaro idanuwanta ta juyasu gami da cewa.
‘’Yes‘’
Ta mik'e ta nufi filin casu, don jin an saka wak'ar da take mugun k'auna, ta shiga tik'ar rawa ba ji ba gani don FANAN gwana ce wajen iya rawa.
Sameer kuwa wani mugun dafi ta zuba masa, wanda yayi sanadiyar sumansa na wucin gadi a zaune, har sai da sowa da tafin da ake mata ya dawo da shi tunaninsa da hanzari ya mik'e yana cin alwashin sai tazo tasha giyar nan da kanta, don yau so yake ta mallaka masa kanta, babu musu babu jayayya, yau yake so yai bankwana da k'ishiriwar da ta dad'e tana damun mak'oshinsa.


――
‘’ Likita ya jikin nata?‘’
Sai da likitan ya fara zare gilashin idonsa kana ya kalli I.G Mustapha da ya jefo masa wannan tambayar kana yace.
‘’To Alhamdlillh za'a ce, amman muddun ba ta cire tunani da damuwa ba to ciwonta kullum jiya iyau zai kasance, kuma hakan zai haifar da babbar matsala, don yanzu haka ma jininta yai mugun hawa ba komi nake jiye mata ba sai ciwon shanyewar b'arin jiki, Allah dai ya kiyaye faruwar hakan.‘’
A sanyaye I.G Mustapha yace.
‘’Amin, insha Allahu zanyi k'ok'arin gurin ganin na kwantar mata da hankali, dama a kwana biyun nanne abin ya juyo mata, na gode likita.‘’
Daga haka ya bashi hannu sukai musabaha ya fita daga ofis in, d'akin da aka kwantar da ita ya nufa, dukkan familyn gidan suna cikin d'akin ganin shigowarsu yasa suka fara fita d'aya bayan d'aya, daga gefenta ya samu ya zauna had'e da kamo hannunta.
‘’Muddun kema kika bari na rasaki to tabbas banga amfanin cigaba da tawa rayuwarba don ko wa'adina bai cika ba to zan k'are rayuwata ne cikin rashin lafiya, ki taimakeni ki rage tunani da damuwa dan Allah Ummu Aymana.‘’
‘’Ka sani kaima ina k'ok'arin fitar da komai daga raina, abinne ya juyo mini yake k'ok'arin fin k'arfina, amman insha Allah zan danneshi da k'arfin addu'a kaima ka tayani.‘’
‘’Rana ba ta hudowa ta fad'i ba tare da na miki addu'a ba Ummu Aymana. Insha Allah komai ya kusa zuwa k'arshe, muna bin komai daki-daki ne don mutumin yana da mugun had'ari, kuma komai yana yinsa cike da wayo, idan ya fuskanci muna bibiyarsa yana iyai mana b'atan dabo, b'atan da baza mu sake ganinsa ba, kiga wuyar da muka sha kafin samuwar tan'ameme inda yake zaune ba, amman insha Allahu sai na kaiwa Hajja shi gabanta ya durk'usa ya nemi yafiyarta.‘’
‘’Ba yafiyarsa muke buk'ata ba, ya gaya mana inda Fina da Faruoq suke kawai muke da buk'ata.‘’
‘’Wannan ba matsala ba ce insha Allah kamar yau za kiga Finanki da Farouq a gabanki.‘’
Kyakkyawan murmushi ne ya bayyana a fuskarta tace.‘’Allah yasa amin.‘’ Har lokacin murmushi bai bar kan fuskarta ba, da ‘’Amin‘’ D'inma shima ya tayata yana jin dad'in yadda yasata cikin farin ciki amman k'asan zuciyarsa fal tarin damuwa da fargaba ne, yana fargabar zatonsa ya tabbata na Faruoq ba ya tare da shi Finan ma bai da tabbas d'in itace..



KATANGA labarine mai tab'a zuciya, da sanyayar da jikin mai karatu, zai yi wuya ka gama karanta shi ba tare da ka zubar da k'walla ba, da dad'in dad'awa kuma littafin yana da shiga rai.
Babban abinda ya kuma birgeni ga littafin KATANGA marubuciyar ta baje nutsuwarta, hikima, fasaha,hazak'a,basira,tunani duk a cikin wannan...


Read / Download CIN AMANA

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album