Join Our WhatsApp Group

NUFIN ALLAH BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by NUFIN ALLAH BOOK 1


NUFIN ALLAH BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 76547



NUFIN ALLAH BOOK 1

Reading Time: 6 Hours

Added On: 20, Oct 2023

Author: Aisha Sabo Lemu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08167768704

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 395.07 kb

File Type: txt

Views: 782+

Download: 570+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: [2/28, 1:08 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH...!* 🤲🏻 _*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*

*Chapter 1*

_Free page_


Misalin ƙarfe biyar da rabi shida saura na asuba, kyakykyawar baƙar budurwar ta isa ƙofar gidan Hakimin garin giwa. Mai suna Alhaji Haruna Musa giwa, wanda shine Hakimin garin kuma aminin mahaifinta marigayi Malam Mahmuda. Tana kuka wurjajan ta ci burki daga bakin zauren shiga gidan, tana faman raba idanu jin sautin karatun da ke fitowa daga masallacin kusa da gidan.Da alamu lokacin ake sallar asubi a masallacin,sai ta dawo da baya tana zama akan dakalin ƙofar gidan.Kuka sosai take yi iyakan ƙarfinta,baƙin kyakykyawar fuskarta gaba ɗaya ya tasa idanunta sun kumbura domin tun cikin dare take aikin kukan tashin hankalin halin da Innarta ke ciki. Tana nan zaune tana sharan hawaye da sauke ajiyar zuciya, su Hakimi suka fito daga cikin masallaci. Tun daga nesa yake hango wata da jan hijab zaune bisa dakalin ƙofar gidan nasa, hakan ya sanya shi ɗaga ƙafa yana riga Yaransa isa ƙofar gidan domin zuciyarsa na gaya masa cewa ba lafiya bane.

"Najmatu lafiya, ko jikin Mairo ne ya sake motsawa kuma? Hakimi Alhaji Haruna Musa giwa ya furta hakan, a lokacin da ya isa wajen dakalin da take zaune akai ya fahimci cewa Ƴar amininsa ce zaune mai suna Najma. Wacce ya kira da Najma tayi saurin dubansa wasu hawayen na zarya akan fuskarta,taja ajiyar zuciya tana faɗin "Jikin ne Baba Hakimi, kwana mukai bamu runtsa ba.Yanzu haka na baro tana jin jiki." Ta kai ƙarshen maganar tana rushe masa da kuka mai motsa zuciyar mai saurarenta. Hakimi ya ja salati yana faɗin, "Subhanallah!" Ya waiwaya bayansa yana yafuto ɗansa Auwalu da hannu, wanda ya tsaya suna magana da wasu samari. Ganin Hakimi na kiransa ya sanya shi isowa da sauri yana faɗin, "Baba gani." Hakimi ya dubesa da zallar damuwa akan fuskarsa ya ce, "Maza shiga cikin gida ka ɗakko mukullin mota ka fito mu wuce asibiti, jikin Mairo ya sake motsawa." Auwalu ya ruga a guje zuwa cikin gidan yana jan salati a zuciyarsa, domin suna tsananin son Inna Mairo da ganin mutuncinta.

Cikin hanzari ya fito daga cikin gidan hannusa riƙe da mukullin motar Hakimi.Ya isa garejin gidan ya fiddo motar, Hakimi ya shiga gaba yayinda Najma ta shiga baya tana faman jan ajiyar zuciya.

Kamar yadda Najma ta sanar da Hakimi Inna Mairo na tsananin jiki, a haka suka sameta. Da taimakon Auwalu da Najma suka kamota zuwa mota, suka wuce da ita asibitin zaɓawa dake garin. Taimakon gaggawa aka bata har aka samu ta dawo hayyacinta.Likitan da ya dubata ne ya basu tabbacin cewa rashin shan magungunanta akan ƙa'ida shike maido da komi baya, don haka dole a kula da sayensu akan lokaci da zaran sun ƙare. Ya kammala dukkanin jawabinsa sannan Ya rubuta musu wasu magungunan kala biyu, Ya ce idan ta shayesu bata ji daidai ba su wuce da ita babban asibitin koyarwa dake shika domin ta samu ganin babban likita. Hakimi sukai godia bayan sun amsa takardan maganin. Najma da sai lokacin hankalinta ya fara kwanciya, ganin Inna ta dawo hayyacinta. Sai ta kama hannunta suka fito daga ofishin Likitan, wanda duk yawancin sanda za a kawo Inna Mairo shi ne ke dubata, kuma shi ne babban likita baki ɗaya a asibitin Zaɓawan.

Suna tafe cikin mota don komawa gida Hakimi na mitan yadda ƴan uwan Inna Mairo da matar mahaifinta da suke kira Gwaggo suka juya mata baya. Ya cigaba da faɗin, "Yanzu saboda Allah Mairo idan su sun yanke zumunta dake sai ke ki biye musu ki daina zuwa inda suke? Karki manta fa kece ƙaramarsu Mairamu, duk yadda zasu gujeki su juya bayansu gareki don sun yi arziƙi, ke bai kamata ki yanke zumunta dasu ba. Ina giwa ina kaduna da za a ce kin yanke dukkan alaƙa da ƴan uwanki, kin zaɓi ki cigaba da rayuwa cikin tsananin maraici da ciwan zuci?" Ya dakata da maganar zuciyarsa na shiga ƙunci mai yawa, domin yana tsananin jin ciwon yadda Ƴan uwan Inna Mairo duka biyu suka wofintar da ita tun bayan rasuwan Mahaifinsu. Inna Mairo dake sauraren Hakimi ta kasa magana sai kuka, kukan da ke tasowa tun daga ƙarƙashin zuciyarta yana ƙona ruhinta.

Sanin da Hakimi ya yi Inna Mairo har da ciwon zuciya ke barazanar kamata,sai ya koma yin rarrashi da nusar da ita illar yanke zumunta koda ace an yanke maka, kai ance ka sadar ga wanda ya yanke maka ɗin. Har suka isa ƙofar gidan Inna Mairo Hakimi nasiha yake mata cikin rarrashi, Inna ta dinga saurarensa kalamansa na ratsa zuciyarta da sake raunatata.

"Najma kamata ku shiga daga ciki,zuwa anjima Auwalu zai je ya samo magungunan da aka rubuta ɗin. Mairamu Allah ya ƙaro afuwa, ki daina sanya yawan damuwa a zuciyarki domin kin fi kowa sanin cewa ba a son mai hawan jini na yawan tunani da sanya damuwa a rai. Musamman ke da zuciyarki ke barazanar kamuwa.Na horeki da ki daina sanya yawan tunani ki maida dukkan lamuranki zuwa ga Allah. Na sani ke ɗin mai tawakkalice amma ki ƙara ninka jururiyarki domin shi komi na rayuwa NUFIN ALLAH ne Mairo, yadda duk Yaso haka yake kasancewa. Allah zai baki lafiya ya kuma ganar da ƴan uwanki da Gwaggo cewa sun yi kuskure, sun kuma ci amanar dattijon arziƙi marigayi Alhaji Muhammad da basu rungumi wasiyyarsa sun riƙe amanarki da ya bar musu ba." Hakimi ya dakata da maganar yana kallon Inna Mairo da hawaye ke gudu akan fuskarta, ta gyaɗa kanta murya a shaƙe ta furta, "Na gode Hakimi, Ubangiji ya biya maka buƙatunka na alkhairy duniya da lahira. Allah Ya duba gaba da bayanka Ya albarkaci zuriyya.In Sha Allah zan yi ƙoƙarin ganin na rage yawan damuwar." Ta kai ƙarshen kalamanta lokacin da Najma ta zagayo ta buɗe mata murfin motar ta fito. Hakimi ya sake mata fatan samun sauƙi yana jin tausayinsu ita da Ƴarta Najma na sake mamaye zuciyarsa. Tabbas Ya yi rashin amininsa mai ƙaunarsa, Yana kuma jin cewa kulawa da Iyalinsa tamkar tilas ne a garesa domin ba zai iya zuba ido rayuwar su Inna Mairo ya tagayyara ba. Shiyasa tun bayan rasuwar aminin nasa Malam Mahmuda shi ne yake ɗawainiya da su Inna Mairon,bai taɓa gajiyawa ko gazawa ba,da taimakon Ubangijinsa yake musu komi.

Najma a hankali take takawa hannunta riƙe dana Inna Mairo har suka dangana da cikin gidan nasu, wanda ginin ƙasa ne da ya samu aka filascesa da siminti.Tsakar gidan ma an filascesa babu ƙasa sam a tsakar gidan,ko'ina fes yake don suna da tsanani tsafta da kula da muhalli.

Ƙaramin ɗakin nasu mai ɗauke da falo da ɗakunan bacci biyu a jere suka buɗe, Inna Mairo ta zame hannunta daga na Najma tana nufan hanyar ɗakin baccinta.Najma tabi bayanta da kallo tana mata sannu cike da tausayi. Inna Mairo ta amsa ba tare da ta waiwayo ba, don burinta shi ne ta dangana ga tsohuwar katifarta ta yi kukan da take riƙewa na tunawa da gwarzon mijinta da Mahaifinta da suka kwanta dama. Domin tabbas da suna raye da sun share mata baƙin ciki mai yawa na rayuwa,da bata yi kukan rashin gata ko makusantar da zata kwanta a kafaɗunsu ta yi kuka ba. Sai dai dukkanin gatan nata sun ƙare, ta rasa uwa tun tana tsummar goyo. Gashi yanzu ta rasa miji da uba,duka sun tafi sun barta cikin wannan duniyar mai cike da tarin rikita-rikita da ruɗin zuciya.

Ta kifa ciki tayi kuka mai yawa har Najma dake zaune a falo ta zabga uban tagumi, sai da ta jiyo sautin kukan da Innar ke yi. Ta nufo cikin ɗakin baccin Inna Mairo a rikice, tana mai durƙushewa a gaban katifar da take kwance ta ce, "Inna lafiya, jikin ne? Don girman Allah Inna ki tausayamin ki daina sanya damuwa a ranki, domin ke kaɗaice kika rage gatana a yanzu. Sannan lafiyarki ita ce abinda tafi komi muhimmanci.Ki dubi girman Allah karki bari lafiyarki ta salwanta akan baƙin cikin waɗanda basu san ma kina yi ba." Najma ta ƙare maganan tana riƙo hannun Inna Mairo ta saki kuka mai ban tausayi, hakan ya sake karya zuciyar Inna Mairo.Ta riƙe hannun Najma da kyau tana faɗin, "Ba don su nake wannan kukan ba Najma, ina kokawa ne don rashin Mahaifinki da nawa.Tuni na daɗe da cire damuwar su Gwaggo a cikin zuciyata,na danne dukkan ƙawazucinsu a raina.Bana ganin laifin su Yaya Kabeeru, laifin Gwaggo nafi gani Najma domin na san ita ce tayi musu katanga dani, ta kuma hana su raɓemu sabida da tsananin ƙiyayyarta garemu ni da Mahaifinki." Inna Mairo ta dakata da maganar zuciyarta na mata wani irin suya, ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta da ke mata wani irin zafi. Ganin hakan ya sanya Najma taya ta dafe wajen tana mata sannu cikin tsananin jin tausayin Innartata.

Sun ɗauki lokaci a haka hannunsu na dafe da ƙirjin Innar,kafin ta zare hannun Najma tana faɗin, "Tashi ki kunna wuta ki ɗaura abin karin kumallo Najma." Najma ta jinjina kai tana tashi tsaye ta zare hijab ɗin jikinta, idanunta akan Inna ta ce, "Sannu Inna, bari in je kicin ɗin in ga ko akwai ragowar gawayin da za a iya kunnawa." Daga haka ta fito daga ɗakin cikin takunta mai cike da nutsuwa ta halitta. Na dinga bin budurwar da kallo, wacce zata kai shekaru sha bakwai.Ina yaba kyawu da tsarin halittarta,domin babu ƙarya Allah Ya yi mata baiwar kyawu da cikar halitta mai asalin fisgar hankali. Baƙace sosai amma kyakykyawar da aka ƙera halittarta tamkar ita tayi kanta. Tana da tsayi matsakaici ba mai yawa ba, sannan tana da gaba da baya wanda suke a cike. Musamman ƙirjinta da yake a tsaye cir! Da cikakkun dukiyar fulani.Dogon hanci gareta har baka,sai manyan idanu farare tas! Masu turawan ƙwayar ciki baƙi siɗik! Ɗan ƙaramin bakinta so cute da cinkusassun gashin giranta baƙaƙe siɗik! Sun fi komi ƙawata kyawun fuskarta. Bata da jiki kuma ba za a kirata siririya ba, sai dai a kirata mai murjajjen jiki.saboda fatar jikinta a cike yake da tsoka babu alamar rama ko siranta a tattare da ita. Koda ta nufi cikin kicin ɗin kai tsaye wajen robar da suke zuba gawayin ta nufa, ganin akwai ragowarsa da ɗan yawa ya sanya ta ɗakko murahun gawayin guda biyu ta zuzzuba wanda zai isheta amfani. Bayan ya ruru ne ta ɗaura ruwan wanka a guda ɗaya, ɗaya kuma ta ɗaura ɗumamen ragowar tuwo miyar kuka da suka ci a daren jiya suka rage.......✍🏻


🤳🏻 *INA MASU RIƘE DA WAYAR HANNU KUNA TA'AMMULI DA KAFAFEN SADARWA? TO ALBISHIRINKU DOMIN KUWA GA A.ƊANSABO DATA SERVICES.* *TA ZO MUKU DA TSARIN SAYEN DATA AKAN FARASHI MAI SAUƘI. DATA BUNDLES KAMAR NA👇🏻*
*MTN*
*GLO*
*AIRTEL*
*9MOBILE*
*MONTHLY VADILITY 💃🏻*


*DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI KUMA A SAUƘAƘE.KE DAI KAWAI KI NEMI A.ƊANSABO DATA SERVICES AKAN WANNAN LAYIN NATA 08167768704 DOMIN ƘARIN BAYANI KO BIYAN KUƊINKI DOMIN SAYEN DATARKI A SAUƘAƘE* 💃🏻💃🏻💃🏻

















#Najma#
#Hot lovestory#
Aysha Ɗansabo ce✍🏻
[2/28, 1:09 PM] Aysha Dansabo Lemu😘😘: 📱 *NUFIN ALLAH....!* 🤲🏻
_*Arewabooks@ayshadansabo*_

*Paid book:500*

*Chapter 2*

_Free page._


Kafin ruwan ya tafasa tuwan ya ɗumamu Najma ta kammala sharan ɗakinsu, wanda ba wani girma bane da shi. Bayan ta haɗa musu shayi ruwan bunu(ruwan lipton), ta juye ɗumamen a kula ta nufo ɗakin Inna Mairo da shi. A falo ta aje komi ta nufi bedroom ɗin wajen Inna Mairo, ta sameta a kwance har lokacin tayi lamo akan katifarta tana faman zurfafa tunani. Cikin sanyin murya Najma ta zauna daga bakin bed ɗin tana faɗin, "Inna na kammala, ga ɗumamen da ruwan lipton can a falo. Inna Mairo ta muskuta ta tashi zaune tana sauke manyan idanunta da Najma ta gada a kanta, ta sauke numfashi a hankali ta ce, "Sannu Najma da ƙoƙari, Allah ya yi albarka ya zaɓa muku mazajen aure na gari." Najma da tuni ta gane jam'u da Inna Mairo tayi tana nufin ita da su Luban gidan hakimi take wa addu'ar, sai ta kauda kai tana amsawa a zuci. Inna Mairo ta cigaba da cewa, "Da zaran mun kammala karin kumallon sai ki bani ruwan wanka, watakila idan nayi naji ɗan ƙarfin jikina." Najma ta murmusa ta ce, "To Inna!" Daga haka suka fito zuwa falon da Najma ta shareshi tsaf, ta goge yagaggen ledar tsakar ɗakin. Suna cin abincin suna taɓa hira akan ciwon Inna Mairo da irin yadda ake samun kuɗin sayen magungunan da ƙyar.Ba don Hakimi ba da tuni watakila Innar ta mutu,sabida rashin gata da wanda zai tsayawa lamuransu har ya ɗauki nauyinsu. Ba kuma don Innar ta rasa Ƴan uwa ba, sai don Ƴan uwan nata sun gujeta sun juya mata baya shekaru kusan bakwai kenan rabonta dasu.Tsakaninta dasu sai dai aiken kayan abinci da zanin sallah da suke mata duk shekara, amma baya ga haka babu mai takowa inda take domin sunyi arziƙin da suke ganin tamkar ci bayane su tako ƙauyen garin giwa su ce suna da ƙanwa bare har su ga halinda take ciki su tallafa mata. Wani irin abu mai ɗaci ya tsayawa Inna Mairo a maƙoshinta, lokacin da ta tuno zuwan Gwaggo na ƙarshe garin giwa, bayan rasuwar marigayi Malam Mahmuda. Najma ta kwashe komi ta kai kicin ta aje, ta ɗauki bokiti ta ɗebowa Inna ruwan zafi ta surka, ta kai mata banɗaki don tayi wanka ko zata ji daɗin jikinta kafin Baba Hakimi ya aiko da magungunan da zata sha.

Ɗakinta da ke kusa dana Inna ta shiga ta share tare da gyara shinfiɗar lafaffiyar katifarta, wacce tun ta makarantar kwanan da suka yi ne ta dawo da abin ta tana kwanciya akai. Gefen katifar ta samu ta zauna ta sauke numfashin a hankali, zuciyarta na kwaɗaita mata son jin asalin tarihin Innarta da yadda aka yi ta auri Mahaifinta Malam Mahmuda. Tana matuƙar son sanin musabbabin da Gwaggon kaduna take nuna wa Inna ƙiyayyar da har ta kai ta rabata da Ƴan uwanta, ta hana su raɓeta ko ita Innar ta rabesu. Tana nan zaune tana zurfafa tunani har ta ji shigowar Inna ɗaki alamun ta dawo daga banɗaki yin wanka, tayi saurin tashi ta fito tana faɗin, "Inna har kin fito?" Inna Mairo ta dubi tilon Ƴarta da take duba ta ji sanyi a ranta ta bata amsa da faɗin, "Na fito Najma, ke ma sai ki je ki yo wankan kafin asan abin yi zuwa rana ko?" Najma ta jinjina kai tana faɗin, "To Inna, amma ina ga da rana ɗinnan da wuya mu samu abin girkawa domin babu sauran kayan abinci sun ƙare." Inna Mairo tayi shiru, kafin daga bisani ta dubi Najma tana faɗin, "To shikenan Najma, Allah zai rufa asiri. Ina ga Hakimi...


Read / Download NUFIN ALLAH BOOK 1

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album