Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

CUTA TA DAU CUTA Complete Hausa Novel Document by CUTA TA DAU CUTA


CUTA TA DAU CUTA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 24228



CUTA TA DAU CUTA

Reading Time: 2 Hours

Added On: 20, Jun 2024

Author: Bilyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 09166221261, 09033181070

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 134.03 kb

File Type: txt

Views: 1001+

Download: 770+

Last download: 7 hours ago

Description/Story: _Typing📲_*








*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_Shafi na ɗaya_



*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._


........“Ango! Ango!! Ango!”. Itace kalma mafi rinjaye da tafi fita a bakunan taron matasan dake cike da ƙofar gidan. Yayinda wanda suketa faman kira da angon bakinsa ya kasa rufuwa dan farin cikin da yake a ciki a wannan rana data kasance ta aurensa da masoyiyarsa mafarkinsa. Magana da ɗaya daga cikin abokansa ya gwargwaɗa masa a kunne ta saka shi jan hannunsa suka koma gefe. Cikin ɗan nuna yanayin damuwa da hasala ya ce, “MB ya akai haka kuma? Nifa bana son matsala wlhy, duk abinda zan ɓatama Love rai bana son shi musamman a wannan ranar ma data kasance mana ta daban.....”
      “Na sani kwantar da hankalinka, kaima kasan dai bazan bari wani abinda zai ɓata farin cikinka faruwa ba JJ. Na faɗa maka ne kawai dan kar kaga an samu canji, dan yanzu haka ma nariga na daidaita matsalar, wajen da aka samu yanzu ɗin ma yafi wancan komai...”
     “Amma karka manta wajen farkon muka saka a invitation card”.
    “Hakan bazai zama matsala ba shima, dan kusa-da-kusa suke, dabarar da zamuyi zamu ajiye su Nure a ƙofar wancan hall ɗin duk wanda yazo sai su turosa inda aka canja ɗin. Yanzu sai ka sanarma amarya kawai, ko hakan baiyi ba?”.
          “A yayi, kunyi ƙoƙari, ALLAH ya bar zumunci bari na sanar mata”.


     *_DINNER HALL_*

       Matuƙar ƙyau da ƙayatuwa wajen yayi tamkar dama tun farko nan suka shirya yin shagalin. Kalar decoretions ɗin wajen kalar ankon ƴammatan amarya da suka sha ƙyau har suka gaji, haka suma abokan ango shar da su. Shigowar ango da amarya ta shafe duk wani ƙyawun kowa a wajen, dan adonsu na musamman ne. Atake hasken flash ya shiga tashi tako ina, tsakanin wayoyi da camaras, a gefe mc na faman kwarzantasu, yayinda dj ya saki wani cool music mai ratsa zuciya. Ta ko'ina dai taro ya cika taro kam sai masha ALLAH, abokan ango da ƙawayen amarya nata taka rawar gani irin na bajinta tare da dangi takowace ɓangare. A yanda aka tsara komai zaka iya saka masu bikin a layin masu hannu da shuni, sai dai sam ba haka bane ba, ana dai tsaka tsaki, wato babu tsiya babu hamshaƙin arziƙi. Sai dai akwai rufin asirin ALLAH ta kowanne ɓangarorin guda biyu. Anyi taro an tashi lafiya kusan ƙarfe ɗayan dare, ango na son maida amaryarsa gida da kansa yayarta tace karya damu yaje gida ya huta zasu wuce da ita. Babu yanda ya iya dole ya haƙura suka dunguma shi da abokansa zuwa hotel da suka kama. Amarya da danginta suma suka wuce nasu gida dan sai gobe in sha ALLAH za'a miƙata gidan mijinta.....

           *_WASHE GARI_*

   A kaf ƴan rakkiyar amarya babu wanda baiyi santin gidan da aka kawota ba. Dan kuwa dai gida ya cika ya tunbatsa komai zam. Tabbas angon yayi ƙoƙari sai kuma fatan a zauna lafiya. Bayan kammala ƴan kai da kawo na al'ada da rabe-raben kayan gara kowa ya kama gabansa aka bar amarya da ƙawayenta. Sune suka sake gyare mata gida ana faman raha da wasa da dariya komai ya koma kan saitinsa. Sai dai amarya bata da wani kuzari tattare da ita, ba komai ya jawo hakan ba sai ƴar fargabar da aka san duk wata amarya kamila da ita a irin wannan ranar, dama ita gata bamai yawan hayaniya bace, ko ƙawayen ma ba wasu ne daban ba, daga ƴan uwa sai maƙwafta da aka tashi tare. Bayan idar da sallar magrib kowacce ta shiga sake gyara kwalliyarta sukai zaman jiran abokan ango. Ƴan halak ɗin kam basu taushe hannu ba, dan idar da sallar isha kaɗan suka iso gidan. Amarya dai na lulluɓe, yayinda ango yay tsallen turare ɗan goma zuwa inda take ya zauna kusa da abarsa kamar zai rungume, itako tana ta faman matse jiki waje guda abinka da farin shiga ga kunyar baƙunta. Suko abokan ango nata faman masa shaƙiyanci da ido yana musu daƙƙuwa ta ƙasan riga da sakin murmushi. A haka dai akai ƴan abubuwan daya dace tsakanin abokan ango da na amarya, zuwa tara da rabi ango da yaga basu da niyyar basu filin ya murje idanu ya korasu waje. Sun fito suna dariya, yayinda MB babban amininsa ya sinna masa wasu ƙwayoyin magani tare da miƙa masa gorar ruwan hannunsa yana faman ƙyafta masa idanu da masa magana a hankali. “Adai yi tuƙi a hankali, dan wannan motar ƙirar larabawa ce, idan bakai wasa ba amaimakon horn ƙira'ar Alkur'ani zakaji”. A tare suka kwashe da dariya tare da cafkewa bayan ya afa maganin batare da tambayar na miye ba ya kora da ruwa. Ango JJ ya ce, “Shege abokina, kune malaman duniya, dan shugaban mai jan ƙyalli ma a ƙarƙashin koyarwarku yake baza komarsa”. Dariyar suka sake kwashewa a tare, MB yay gaba yana saɓa babbar riga da faɗin, “Idan da matsala kai dai kai kirana da wuri na turo makanike dan ka samu damar fita shan iskar yammaci, na barka lafiya a tuna da maƙota kar'a ishesu da...” bai ƙasa ba ya wani kashe masa ido ɗaya yana ficewa a gate ɗin. Shi dai ango JJ rufe gate ɗin yay yana cigaba da dariyarsa. Kafin ya juya cikin gidan ransa fes yau ranar baje koli ta duniya a cikin rayuwar sa...
     Shuuu!! Aka gitta kamar ta gefensa a dai-dai yana kai hannunsa ga handle ɗin ƙofar, kamar zai share da tunanin iskar sanyi data fara kaɗawa ce sai kuma dai ya ji an sake gitta masa yana ƙoƙarin tura ƙofar. Wawwaigawa yay damansa da haggu sai dai kuma babu kowa, cikin nuna halin ko'in kula ya ɗage kafaɗu da taɓe baki ya ƙarasa shigewa a falon.
     “Amarya kin sha ƙamshi, amarsu baƙya laifi koda kin kashe ɗan masu gida!”. Ya jero kalaman kirarin tamkar shine ya fara ƙirƙirarsu saboda tsaruwarsu a bakinsa kai kace waƙace a bakin shata ko barmani coge. Bai damu da jin ba'a amsa mar ba, ya murzawa ƙofar key harda gyara labulaye da ƙyau. Turus yaja ya tsaya ƙirjinsa na bada wani irin turururumm tamkar sautin gangar Ado gwanja a tsakkiyar filin biki. Wayam falon babu komai, duk kayan alatun nan da aka ƙawata falon da shi  tamkar wata almara babu su babu alamar su. (Kai ina, wannan almara ce JJ dawo hankalinka) wata zuciya ta ayyana masa. Yawu ya haɗiye da ƙyar, tare da sakin murmushi mai kama da kuka shi adole yana son dawo da hankalinsa jikinsa. Bakinsa na rawa da karkarwa ya furta, “L-o-v-e!” a rarrabe yana runtse idanunsa da ƙarfi. Ba'a amsa mar ba yanzun ma dai, dan haka ya sake ƙarfin halin buɗe ido ɗaya da ƙyar, da sauri ya sake buɗe ɗayan ma ya shiga waige-waige yana haɗiyar yawu da sauri-da-sauri. Yanzu kam falon komai ya dawo kamar yanda yake a da, sai dai kuma kalar kayan ta canja. (JJ! Farin ciki fa ke neman juyar maka da brain, ka daidaita kanka mana). Kansa ya shiga gyaɗawa kamar tsohon ƙadangare cike da son gamsar da kansa akan dole, sai kuma kamar wanda aka ingiza ya nufi bedroom da sassarfa, yana tafiya yana waigen falon. Har ɗan datse hannunsa yake wajen ƙoƙarin rufe ƙofar bedroom ɗin da danna mata key saboda yanda jikinsa ke rawa. Cikin dauriyar azabar dake ratsa masa hannun da ya datsa ya jingina da ƙofar yana sauke nannauyar ajiyar zuciya irin ta na sha da ƙyar ɗin nan. Yakai minti ɗaya a haka kafin ya dai-daita kansa da ƙyar yana sauke ajiyar numfashi a jajjere. Kasancewar sai ka ratsa ɗan lungu daga jikin ƙofar kafin ƙarasawa tsakkiyar bedroom ɗin sosai saboda bathroom dake a wajen ya bashi damar share gumin ɗaya tsatstsafo masa da dai-daita yanayinsa da ƙyar sannan ya cigaba da tafiya a takun da bai gaza huɗu zuwa biyar ba. Bedroom ɗin ƙato ne, ga kayan gado yaji masu ƙyau dan iyayen amarya sun taka rawar gani suma. Ƙoƙarin hana kansa kallon komai yake saboda abinda ya baro baya, dan haka ya nufi gadon kansa tsaye dan yasan dai anan zaiga amaryar tasa sarkin kunya da nutsuwa. Sai da ya kai zaune yana faɗin, “Afuwan Love na barki ke ɗaya, na sallami waɗan nan ƴan matsalar ne, kin san in su MB na waje bakin mutum baya hutaw......”
     Ya kasa ƙarasawa sakamakon abinda idonsa ya gane masa. Wata irin murɗaɗɗiyar macijiya ce baƙa ƙirin an mata wata kwalliya da kalar jaja-jaja mai haske kamar ƙwan lantarki. Ba'a
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download CUTA TA DAU CUTA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album