Join Our WhatsApp Group

SALMAH Complete Hausa Novel Document by SALMAH


SALMAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 78660



SALMAH

Reading Time: 6 Hours

Added On: 26, Sep 2023

Author: Tawakaltu Abubakar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08142087575

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 424.9 kb

File Type: txt

Views: 467+

Download: 401+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: Alhamdulillah ya Allah for giving me the ability to write this novel SALMA. I pray to almighty Allah to guide and protect me through the journey of this novel 🙏

Bismillahir'rahmanirraheem
SALMAH... ✍️ by tee





Salmah... Sunan da Mama take Kira na dashi kenan. Sunan da tasamun da kan kanta. Suna me tsadan gaske, sunan da daga ita sai mutun daya rakk a duniyan nan yakuma sanin ta... Yau tun safe mama taketa kayekaye da gyaregyare a gida nikuma inadan tayata da kananun abubuwa,... SUFYAAN zaizo.. duc ranan da zaizo kuma ranan sai Mama tayi kuka ko waye sufyaan??? Masu karatu mudai je zuwa....


Bayan mama tagama gyaregayaren gidan, gida yayi rass dashi, ta Kama ni tamun wanka tasa mun ubansun rika kalan blue ( colorn damn sufyaan yafi so aduniya) takamun suman kaina da ya nannede Wanda ake ma lakabi da "coily hair" takamashi ta rubke da pink 🎀 ribbon saiga ni tafito kaman ka sure ka gudu dani Don kyau. Ina daki naji mama ta kwalo mun kira cikin farin ciki, a guje nafito nima.. Kyakkyawan mutum ne dogo a tsaye fari amma ba fari chan ba, ga gira a cike kuma a kwance sai hanci kaman anza na mishi da leben shi a Dan cike (big lips) palon duc ya gauraye da kamshin turenshi. fuskar nan tashi murtuke kaman bai taba Daria a rayuwarsa ba. Nan da nan farin cikina ya gushe. "isn't she beautiful, sufyaan?" mama tace muryarta a Dan tsorace... Bata da kyan da Kai kanka baka taba tsammaniba? Na daga Ido na na kalla fuskar sa , furkar nan a murtuke kaman an aiko mishi da sakon mutuwa. kirin yanayin da mama take shiga idan nai ta damunta da tambayoyi.yana tsaye ya karemun kallo tass tun daga sama har kasa, kalan suman kanshi na dauka da manyan idanunshi Wanda yake Kama da bacci (sleepy eyes) sai kuma goshi na kalan nashi sakk. hanci da kuma dan tsukeken baki na da hasken fata ta kuma na Mama wannan na dauka. "da gangan kika sa mata blue dress din nan, Haleema? Kalmominshi sunsa jikin mama yayi sanyi.na kasa hakuri na kalla idon Mama da take kokarin boye hawayenta. Na sauke ido na kasa, na tambayi kaina toh wai me ke faruwa?? Mahaifina baya farin cikin ganina ne? Ko bashi bane mama take bani labarin shi? Ko bashi bane mai turo mun kayan ciyeciye da turaruka masu tsada?? Kodan banmishi godiya bane yayi fushi? Aiko nan da nan na je kusa dashi na taba rigan shi BABA.. nagodeee da su perfumes and candy din da Kake aiko mun.da farin ciki fal a fuska na na fada "DON'T CALL ME THAT " yafada yaja da baya. Shiiiii salma Mama tasa hannun a baki tace mun ba yanzuba, da wani kallo ya bi Mama yace meyesa zaki hana magana? Ba abunda kike ta so ba kenan? Isn't this what you want?? Ya matso kusa da ni ya saito fuskarsa daidai da nawa yace dame kuma? Na Kalli fuskar Mama.. nace da wani diamond necklace amma sai na girma mama tace zansa "thank you" nace mishi. Ya juya ya Kalli mama yace did you do all this? You think I'm still going like her?? Da sauri mama tace salma run go and play in the backyard I will call you when I'm done talking with your father. Toh nace nafita da baby doll dina hannu. Tass kakeji ya dauke mama da Mari, karan da mama tayi naji ina backyard nazo da gudu na tsaya a windown palon..yanzu kayan da nake aiko miki ne ki kwashe wa kina bata da Sunana? Mama tadago kanta a hankali ta kalleshi, haba sufyaan meye abun fada a nan? Yar ka ce fa jininka katse ta yayi da cewa nacemiki ina bukatan wani da ne? Yaran da Matata ta haifamun sun isheni, bancemiki ina bukatan Kari ba idon mama a rumste ta bude tace miyesa zakace haka sufyaan? Ashe baza kaso gudan jininka ka ba? ai na fada miki ki zubar da cikin ko bamuyi haka dake ba? Mama ta share hawayenta tace nima banso haka ba amma Allah yafimu sanin dalilin ya yasa tashigo cikin mu. to Allah yamun kyauta sai in butulce masa? Kuma bayan ni da Kai munsan Kirin azaban Da Allah yatanada ga duc Mai yin aikin nan, zata kara magana ya dakatar da ita ya isaaa!!! Magana daya zuwa biyu zan miki, indai kinason mucigaba da rawuya to kar in Kara dawowa in tarar da abun nan a gidana idan ko ba hakaba toh ki manta kin taba sanin me suna SUFYAAN a duniya. Ya dauki hulanshi ya fice. Da sauri nabar jikin windown nadawo inda nake kar Mama ta ganni, ko kallo na baiyi ba ya shiga motar shi mai gadi yabude mishi gate ya figi motar kamar zai tashi sama...



Bayan tafiyar shi nashigo cikin gidan banga mama a Palo ba, sai na yi hanyan dakin ta... a hankali na tura kofa na shiga, Chan na hango ta karshen gado, da sauri na naje na zauna dab da ita "mama... Nakira sunan ta a hankali.. tadago kanta cike da murmushin karfin hali. "salma. are you sick mama? No deary, kaine ne yake dan mun ciwo but Mama will be just fine, babanki yawuce wajan aiki, sunkira shi. zai dawo?? Najefo ma mama tambayan da sauri dan bana Kara fatan ganin shi ko da a mafarki ne indai mama zata rinka kuka idan yazo."kila bazai dade ba zai dawo. Babanki mutum Mai kwazo wajan aiki, ga yawan tafiye_tafiye takarashe maganan Da mursmushi cike a fuskar ta, tajawo ni ajiki ta kankameni . Nidai bance kala ba. Kara rumgumeni tayi kaman wani zai kwaceni, ta lunshe ido.. everything will be alright sweetheart. and the rest of the moment went silent..

tun daga ranan sufyaan bai sake dawowa ba, mama sai Kara rame wa takeyi kyan ta da haskenta dai bai gushe ba amma damuwa aranta yau daban na gobe ma haka. Ina dakinta a kan gado na jingina da pillow ina karanta story book dina "the little princess" tafito wanka ta Kalle ni tayi murmushin nan nata Mai bala'in kara mata kyau mama kyakkawa ce ajin karshe meyesa baba baiga haka ba? duc dai tana kokarin kare damuwanta kar in gani tayi gaban dressing mirror tana shafe-shafen ta. ajiye takaddan nayi a gefe, idan natafi zai dawo ku zauna tare mama? Da sauri mama ta juwo ta kalleni zuciyanta na bugawa da addu'a a zuciyanta Allah yasa banji komai ba lokacin da baba yazo. Kar kira cewa haha Salma, kar inkara jin kirin wanna maganan a bakinki !! tun danake bantaba ganin Kirin wannan bacin ran a fuskar mama ba. da tsoro karara a fuska na nace toh. Dawowa tayi kusada ni ta zauna ta rumgume ni "I love you so much salma, non of this has anything to do with you OK? OK mama nace mata nima na Kara rungumeta kowa da abunda ke ranshi.
tundaga ranan, mama bata Kara barin koda wasa naga alamun damuwa a fustar ta ba cikin walwala da farin ciki take mu'ala duc da cikin dare takan tashi tai ta kuka tana rungume da hoton baba a qirjinta intayi ma ishi sai ta tashi ta dauro alwala tayi ta jero nafilfili tana rokon Allah yakawo mata sassauci idan ta sallame kuwa sai ta dauki qur'ani tai ta karatu har ta Kai hudu kafin sallahn asuba, sannan ta tasheni in shiga bayi in kama ruwa inyi alwala muyi sallahn tare. Muna idarwa zan dauko qur'ani na inbiya har inzo inda muka tsaya sannan ta kara mun inyi ta biya wa har sai ta tabbata ya zauna mun sannan tarufe mana da addu'a kuma qa'ida sai munsa baba cikin addu'an. Muna gamawa Zata ciremun hijabi ta linke sanna ta cire nata itama ta linke ta bude Press tasa nikuma in dauki kur'anan mu in maida su saman side drawer in ajiye dakanan mukoma bacci bamu ke tashi ba har sai goma. Muyi addu'an tashi daga bacci(Alhamdulillahill-lazee ahyana ba'adama amatana wa-ilaihin-nushoor) daganan sai tamun wanka infito Palo ta kunna mun cartoon sannan tahadamun tea da toasted bread wata rana kuma custard to indomie itakuma tafara aikace-aikacen gida dan Mama bata karyawa da wuri.. Kafin sha biyu kaga komai har tayi wanka, daga nan kuma kuma mu tsunduma karatun boko dan mama Allah yabata ilimi both Arabic and western education, mama bata yadda ta kaini makaranta ba saboda da tsoron kar watarana ta nimeni ta rasa tanasane da Kirin kiyayyan da mahaifina yakemun. Alhamdulillah karatu ina ganewa yanda yakama ta dan nima akwai kwakwalwa ba kadan ba, domin ance kwakwalwar uwa ake dauka toh ni dai na dau na uwata. turanci kuwa ko a engila aka haifeni sai haka. Sai ka rantse wani hamshakin makaranta nake zuwa nan kuwa duc aiki mama ne. ranar wata juma'a ina Palo ina cin cake da mama tamana baking. ita kuma tana daki.saiga aunty maimuna ta shigo da sallama, a guje na tashi naje na rungumeta ina ta zuba mata ruwan shagwaba dan aunty maimuna na ji dani. aunty maimuna kawar mama ce kud da kud dan tun da nayi wayo na santa da Mama kuma ita kadai ce kawar ta dan Mama ba mai shiga mutane bane kuma batason hayaniya. aunty maimuna a bayan layin mu take tayi aure amma Allah bai bata haihuwa da wuri ba, ayanzu haha Tana dauke da karamin ciki. Ina makale da da ita a jiki tana kara rubke mun suma na da ribbon sai ga Mama ta fito daga daki da ash and pink fitted gown a jikinta. Rigan yabi shape din jikinta dan mama akwai shape ba kadan ba. aunty maimuna ta Kalle ta tace "hali duba na mussanman" kirin kirarin da take mata kenan. Mama race kedai kika sani, aunty maimuna tajawo ni muka karaso Palo muka zauna ina jikinta, mama ta Kalle ta tace come inside please let's talk, alright tace tare da mikewa take ajiyeni a kan kujera tace jira mu anan my angel yanzu zandawo yau dai abani labarin "little princess din da aketamun tadin shi a waya" na daka tsalle nace toh. sunkai minti talatin sannan suka fito, mama tazo kusa dani ta zauna tace " sweetheart, yau zakibi aunty maimuna kuje gidanta gobe zata kaiki yazo smart kids kisha ice cream, nan da nan zuciya na ya buga na Kalli fuskokin su da suke ta zuba mun murmushi. "I don't want to go Mama, I want to stay with you" nasan kila sufyaan zaizo ne shine Mama take niman inda zata boyeni to ko dai itama ta gaji da ni ne? Mama ta katse mun tunani na da cewa haba Salman mama, bakiso kifita ki ga gari? Kin dade baki fita ba kuma aunty maimuna zata kaiki wajaje da yawa ina dai rungume da ta ita. Katse mu aunty maimuna tayi da daria tace wai wannan shakuwa haka ke da Mama, my angel, don't worry gobe zandawo da ke kinji? OK nace, mama ta kara rungumeni "that's my baby girl" sannan ta tashi ta shiga daki hada mun kaya, aunty maimuna kuma ta matso kusa dani tana kara rubkemun suman kaina dan santsi ne da shi. chan sai ga Mama tafito da dan cute bag dina tana dube dube a palon "where's your doll salma" zaki tafi da ita ko? "NO" nace, meyesa bakison ku tafi tare aunty maimuna ta tambaya. Ina so ta zauna da Mama nace mata, aunty maimuna tana daria ta mike. Mama ta goyamun jakana a baya ta matso da ni kusa da ita "be a good girl and always know that I love you so much. I love you too mama. aunty maimuna na mana daria taja hannuna muka wuce....


Bayan munfito, aunty maimuna ta karba jakan tabude mun gaban motan ta na shiga sannan tazagayo ta shiga mazaunin driver tare da aje jakana a bayan mota. mama tana jikin kofa a tsaye har aunty maimuna ta juya mota Mai gadi ya bude mana gate muka fita. tafiyan minti sha biyar mukayi muka iso gidan aunty maimuna, horn tayi Mai gadi ya bude mata gate muka shiga ciki. A daidai flat dinta tayi parking motan ta dan gidan aunty maimuna flat ne su uku ne a ciki itace a karshe. kashe motan tayi sannan ta dauko mun jakana a bayan motan, tafito ta tazagayo tabude mun nima tana rike da hannu na ta kulle motan da key sannan muka wuce ta bude kofan palon muka shiga ciki. a nan Palo aunty maimuna ta zaunar dani ta kunna mun TV "let me get you something to eat my angel" tana magana tayi hanyan dakin ta. Sai gata ta fito da chocolates a hannu tabani. na amsa tare murmushi karara a fuska na dan ina son chocolates "thank you" nace mata. tana murmushi bata ce komai ba tayi hanyan kitchen zata dora dinner nikuma ina makale a kujera da chocolates Dina ina ci sai ga shigowan uncle Dee da sallama, a hankali na amsa ina kara takurewa jikin kujera, uncle Dee mijin aunty maimuna ne a FIRS yake aiki ( federal inland revenue service) babba ne a wajan nidai tunda nasan uncle Dee bashida da Fara'a duc sanda muka zo da mama ko yana gida fita yake dan bayason Mama ko meye dalilin ohoo. yayi yayi yaraba aunty maimuna da mama amma taki dan ma yana bala'in son aunty maimuna ne bayason baccin ranta. shiyasa mama da wuya take zuwa wajan aunty maimuna dan sai aunty maimuna tayi ta fama tukunna, kuma muna zuwa bama dadewa. da wani Kirin kallo da bazan iya fassarawa ba yabini da shi . Kafin inbude baki in gaishe shi sai ga aunty maimuna ta fito dan taji shigowan shi. da sauri ta shigo polon tana cewa" well come my Dee" tana kallon cikin idon shi, yadan yi murmushi yace tnx babe. baki kikayi ne? tace Salma ce yau ita kadai dazo mun kwana daya, Tana magana tana matsowa kuma da ni," ko salma? na gyada mata kai kawai. Uncle Dee yayi hanyan dakin shi, aunty maimuna nabiye damn shi. Inaji tana mishi magana kasa_kasa chan naji muryan shi yace toh saike ce mai gidan...


Read / Download SALMAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album