Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Alhamdulillah ya Allah for giving me the ability to write this novel SALMA. I pray to almighty Allah to guide and protect me through the journey of this novel 🙏

Bismillahir'rahmanirraheem
SALMAH... ✍️ by tee





Salmah... Sunan da Mama take Kira na dashi kenan. Sunan da tasamun da kan kanta. Suna me tsadan gaske, sunan da daga ita sai mutun daya rakk a duniyan nan yakuma sanin ta... Yau tun safe mama taketa kayekaye da gyaregyare a gida nikuma inadan tayata da kananun abubuwa,... SUFYAAN zaizo.. duc ranan da zaizo kuma ranan sai Mama tayi kuka ko waye sufyaan??? Masu karatu mudai je zuwa....


Bayan mama tagama gyaregayaren gidan, gida yayi rass dashi, ta Kama ni tamun wanka tasa mun ubansun rika kalan blue ( colorn damn sufyaan yafi so aduniya) takamun suman kaina da ya nannede Wanda ake ma lakabi da "coily hair" takamashi ta rubke da pink 🎀 ribbon saiga ni tafito kaman ka sure ka gudu dani Don kyau. Ina daki naji mama ta kwalo mun kira cikin farin ciki, a guje nafito nima.. Kyakkyawan mutum ne dogo a tsaye fari amma ba fari chan ba, ga gira a cike kuma a kwance sai hanci kaman anza na mishi da leben shi a Dan cike (big lips) palon duc ya gauraye da kamshin turenshi. fuskar nan tashi murtuke kaman bai taba Daria a rayuwarsa ba. Nan da nan farin cikina ya gushe. "isn't she beautiful, sufyaan?" mama tace muryarta a Dan tsorace... Bata da kyan da Kai kanka baka taba tsammaniba? Na daga Ido na na kalla fuskar sa , furkar nan a murtuke kaman an aiko mishi da sakon mutuwa. kirin yanayin da mama take shiga idan nai ta damunta da tambayoyi.yana tsaye ya karemun kallo tass tun daga sama har kasa, kalan suman kanshi na dauka da manyan idanunshi Wanda yake Kama da bacci (sleepy eyes) sai kuma goshi na kalan nashi sakk. hanci da kuma dan tsukeken baki na da hasken fata ta kuma na Mama wannan na dauka. "da gangan kika sa mata blue dress din nan, Haleema? Kalmominshi sunsa jikin mama yayi sanyi.na kasa hakuri na kalla idon Mama da take kokarin boye hawayenta. Na sauke ido na kasa, na tambayi kaina toh wai me ke faruwa?? Mahaifina baya farin cikin ganina ne? Ko bashi bane mama take bani labarin shi? Ko bashi bane mai turo mun kayan ciyeciye da turaruka masu tsada?? Kodan banmishi godiya bane yayi fushi? Aiko nan da nan na je kusa dashi na taba rigan shi BABA.. nagodeee da su perfumes and candy din da Kake aiko mun.da farin ciki fal a fuska na na fada "DON'T CALL ME THAT " yafada yaja da baya. Shiiiii salma Mama tasa hannun a baki tace mun ba yanzuba, da wani kallo ya bi Mama yace meyesa zaki hana magana? Ba abunda kike ta so ba kenan? Isn't this what you want?? Ya matso kusa da ni ya saito fuskarsa daidai da nawa yace dame kuma? Na Kalli fuskar Mama.. nace da wani diamond necklace amma sai na girma mama tace zansa "thank you" nace mishi. Ya juya ya Kalli mama yace did you do all this? You think I'm still going like her?? Da sauri mama tace salma run go and play in the backyard I will call you when I'm done talking with your father. Toh nace nafita da baby doll dina hannu. Tass kakeji ya dauke mama da Mari, karan da mama tayi naji ina backyard nazo da gudu na tsaya a windown palon..yanzu kayan da nake aiko miki ne ki kwashe wa kina bata da Sunana? Mama tadago kanta a hankali ta kalleshi, haba sufyaan meye abun fada a nan? Yar ka ce fa jininka katse ta yayi da cewa nacemiki ina bukatan wani da ne? Yaran da Matata ta haifamun sun isheni, bancemiki ina bukatan Kari ba idon mama a rumste ta bude tace miyesa zakace haka sufyaan? Ashe baza kaso gudan jininka ka ba? ai na fada miki ki zubar da cikin ko bamuyi haka dake ba? Mama ta share hawayenta tace nima banso haka ba amma Allah yafimu sanin dalilin ya yasa tashigo cikin mu. to Allah yamun kyauta sai in butulce masa? Kuma bayan ni da Kai munsan Kirin azaban Da Allah yatanada ga duc Mai yin aikin nan, zata kara magana ya dakatar da ita ya isaaa!!! Magana daya zuwa biyu zan miki, indai kinason mucigaba da rawuya to kar in Kara dawowa in tarar da abun nan a gidana idan ko ba hakaba toh ki manta kin taba sanin me suna SUFYAAN a duniya. Ya dauki hulanshi ya fice. Da sauri nabar jikin windown nadawo inda nake kar Mama ta ganni, ko kallo na baiyi ba ya shiga motar shi mai gadi yabude mishi gate ya figi motar kamar zai tashi sama...



Bayan tafiyar shi nashigo cikin gidan banga mama a Palo ba, sai na yi hanyan dakin ta... a hankali na tura kofa na shiga, Chan na hango ta karshen gado, da sauri na naje na zauna dab da ita "mama... Nakira sunan ta a hankali.. tadago kanta cike da murmushin karfin hali. "salma. are you sick mama? No deary, kaine ne yake dan mun ciwo but Mama will be just fine, babanki yawuce wajan aiki, sunkira shi. zai dawo?? Najefo ma mama tambayan da sauri dan bana Kara fatan ganin shi ko da a mafarki ne indai mama zata rinka kuka idan yazo."kila bazai dade ba zai dawo. Babanki mutum Mai kwazo wajan aiki, ga yawan tafiye_tafiye takarashe maganan Da mursmushi cike a fuskar ta, tajawo ni ajiki ta kankameni . Nidai bance kala ba. Kara rumgumeni tayi kaman wani zai kwaceni, ta lunshe ido.. everything will be alright sweetheart. and the rest of the moment went silent..

tun daga ranan sufyaan bai sake dawowa ba, mama sai Kara rame wa takeyi kyan ta da haskenta dai bai gushe ba amma damuwa aranta yau daban na gobe ma haka. Ina dakinta a kan gado na jingina da pillow ina karanta story book dina "the little princess" tafito wanka ta Kalle ni tayi murmushin nan nata Mai bala'in kara mata kyau mama kyakkawa ce ajin karshe meyesa baba baiga haka ba? duc dai tana kokarin kare damuwanta kar in gani tayi gaban dressing mirror tana shafe-shafen ta. ajiye takaddan nayi a gefe, idan natafi zai dawo ku zauna tare mama? Da sauri mama ta juwo ta kalleni zuciyanta na bugawa da addu'a a zuciyanta Allah yasa banji komai ba lokacin da baba yazo. Kar kira cewa haha Salma, kar inkara jin kirin wanna maganan a bakinki !! tun danake bantaba ganin Kirin wannan bacin ran a fuskar mama ba. da tsoro karara a fuska na nace toh. Dawowa tayi kusada ni ta zauna ta rumgume ni "I love you so much salma, non of this has anything to do with you OK? OK mama nace mata nima na Kara rungumeta kowa da abunda ke ranshi.
tundaga ranan, mama bata Kara barin koda wasa naga alamun damuwa a fustar ta ba cikin walwala da farin ciki take mu'ala duc da cikin dare takan tashi tai ta kuka tana rungume da hoton baba a qirjinta intayi ma ishi sai ta tashi ta dauro alwala tayi ta jero nafilfili tana rokon Allah yakawo mata sassauci idan ta sallame kuwa sai ta dauki qur'ani tai ta karatu har ta Kai hudu kafin sallahn asuba, sannan ta tasheni in shiga bayi in kama ruwa inyi alwala muyi sallahn tare. Muna idarwa zan dauko qur'ani na inbiya har inzo inda muka tsaya sannan ta kara mun inyi ta biya wa har sai ta tabbata ya zauna mun sannan tarufe mana da addu'a kuma qa'ida sai munsa baba cikin addu'an. Muna gamawa Zata ciremun hijabi ta linke sanna ta cire nata itama ta linke ta bude Press tasa nikuma in dauki kur'anan mu in maida su saman side drawer in ajiye dakanan mukoma bacci bamu ke tashi ba har sai goma. Muyi addu'an tashi daga bacci(Alhamdulillahill-lazee ahyana ba'adama amatana wa-ilaihin-nushoor) daganan sai tamun wanka infito Palo ta kunna mun cartoon sannan tahadamun tea da toasted bread wata rana kuma custard to indomie itakuma tafara aikace-aikacen gida dan Mama bata karyawa da wuri.. Kafin sha biyu kaga komai har tayi wanka, daga nan kuma kuma mu tsunduma karatun boko dan mama Allah yabata ilimi both Arabic and western education, mama bata yadda ta kaini makaranta ba saboda da tsoron kar watarana ta nimeni ta rasa tanasane da Kirin kiyayyan da mahaifina yakemun. Alhamdulillah karatu ina ganewa yanda yakama ta dan nima akwai kwakwalwa ba kadan ba, domin ance kwakwalwar uwa ake dauka toh ni dai na dau na uwata. turanci kuwa ko a engila aka haifeni sai haka. Sai ka rantse wani hamshakin makaranta nake zuwa nan kuwa duc aiki mama ne. ranar wata juma'a ina Palo ina cin cake da mama tamana baking. ita kuma tana daki.saiga aunty maimuna ta shigo da sallama, a guje na tashi naje na rungumeta ina ta zuba mata ruwan shagwaba dan aunty maimuna na ji dani. aunty maimuna kawar mama ce kud da kud dan tun da nayi wayo na santa da Mama kuma ita kadai ce kawar ta dan Mama ba mai shiga mutane bane kuma batason hayaniya. aunty maimuna a bayan layin mu take tayi aure amma Allah bai bata haihuwa da wuri ba, ayanzu haha Tana dauke da karamin ciki. Ina makale da da ita a jiki tana kara rubke mun suma na da ribbon sai ga Mama ta fito daga daki da ash and pink fitted gown a jikinta. Rigan yabi shape din jikinta dan mama akwai shape ba kadan ba. aunty maimuna ta Kalle ta tace "hali duba na mussanman" kirin kirarin da take mata kenan. Mama race kedai kika sani, aunty maimuna tajawo ni muka karaso Palo muka zauna ina jikinta, mama ta Kalle ta tace come inside please let's talk, alright tace tare da mikewa take ajiyeni a kan kujera tace jira mu anan my angel yanzu zandawo yau dai abani labarin "little princess din da aketamun tadin shi a waya" na daka tsalle nace toh. sunkai minti talatin sannan suka fito, mama tazo kusa dani ta zauna tace " sweetheart, yau zakibi aunty maimuna kuje gidanta gobe zata kaiki yazo smart kids kisha ice cream, nan da nan zuciya na ya buga na Kalli fuskokin su da suke ta zuba mun murmushi. "I don't want to go Mama, I want to stay with you" nasan kila sufyaan zaizo ne shine Mama take niman inda zata boyeni to ko dai itama ta gaji da ni ne? Mama ta katse mun tunani na da cewa haba Salman mama, bakiso kifita ki ga gari? Kin dade baki fita ba kuma aunty maimuna zata kaiki wajaje da yawa ina dai rungume da ta ita. Katse mu aunty maimuna tayi da daria tace wai wannan shakuwa haka ke da Mama, my angel, don't worry gobe zandawo da ke kinji? OK nace, mama ta kara rungumeni "that's my baby girl" sannan ta tashi ta shiga daki hada mun kaya, aunty maimuna kuma ta matso kusa dani tana kara rubkemun suman kaina dan santsi ne da shi. chan sai ga Mama tafito da dan cute bag dina tana dube dube a palon "where's your doll salma" zaki tafi da ita ko? "NO" nace, meyesa bakison ku tafi tare aunty maimuna ta tambaya. Ina so ta zauna da Mama nace mata, aunty maimuna tana daria ta mike. Mama ta goyamun jakana a baya ta matso da ni kusa da ita "be a good girl and always know that I love you so much. I love you too mama. aunty maimuna na mana daria taja hannuna muka wuce....


Bayan munfito, aunty maimuna ta karba jakan tabude mun gaban motan ta na shiga sannan tazagayo ta shiga mazaunin driver tare da aje jakana a bayan mota. mama tana jikin kofa a tsaye har aunty maimuna ta juya mota Mai gadi ya bude mana gate muka fita. tafiyan minti sha biyar mukayi muka iso gidan aunty maimuna, horn tayi Mai gadi ya bude mata gate muka shiga ciki. A daidai flat dinta tayi parking motan ta dan gidan aunty maimuna flat ne su uku ne a ciki itace a karshe. kashe motan tayi sannan ta dauko mun jakana a bayan motan, tafito ta tazagayo tabude mun nima tana rike da hannu na ta kulle motan da key sannan muka wuce ta bude kofan palon muka shiga ciki. a nan Palo aunty maimuna ta zaunar dani ta kunna mun TV "let me get you something to eat my angel" tana magana tayi hanyan dakin ta. Sai gata ta fito da chocolates a hannu tabani. na amsa tare murmushi karara a fuska na dan ina son chocolates "thank you" nace mata. tana murmushi bata ce komai ba tayi hanyan kitchen zata dora dinner nikuma ina makale a kujera da chocolates Dina ina ci sai ga shigowan uncle Dee da sallama, a hankali na amsa ina kara takurewa jikin kujera, uncle Dee mijin aunty maimuna ne a FIRS yake aiki ( federal inland revenue service) babba ne a wajan nidai tunda nasan uncle Dee bashida da Fara'a duc sanda muka zo da mama ko yana gida fita yake dan bayason Mama ko meye dalilin ohoo. yayi yayi yaraba aunty maimuna da mama amma taki dan ma yana bala'in son aunty maimuna ne bayason baccin ranta. shiyasa mama da wuya take zuwa wajan aunty maimuna dan sai aunty maimuna tayi ta fama tukunna, kuma muna zuwa bama dadewa. da wani Kirin kallo da bazan iya fassarawa ba yabini da shi . Kafin inbude baki in gaishe shi sai ga aunty maimuna ta fito dan taji shigowan shi. da sauri ta shigo polon tana cewa" well come my Dee" tana kallon cikin idon shi, yadan yi murmushi yace tnx babe. baki kikayi ne? tace Salma ce yau ita kadai dazo mun kwana daya, Tana magana tana matsowa kuma da ni," ko salma? na gyada mata kai kawai. Uncle Dee yayi hanyan dakin shi, aunty maimuna nabiye damn shi. Inaji tana mishi magana kasa_kasa chan naji muryan shi yace toh saike ce mai gidan ajiye shegu ko? ta turo miki ita saboda ta faranta mishi rai, da sauri aunty maimuna ta tashi taja kofar ta kulle. Daganan bankara jin komai ba. Bayan minti goma sai gata ta fito ta kalleni tana murmushi tace my angel barin karasa girki ko, yanzu zandawo nace toh sannan ta wuce kitchen. Uncle Dee yafito bai ko Kalle ni ba ya wuce masallaci. aunty maimuna na gama wa ta fito ta jera komai a dining sannna taja ni muka wuce dakinta. Wanka tamun sannan tace inyi alwala bayan nafito itama ta shiga tayi wanka ta dauro alwala. ina daure da towel a bakin gado ta kwaso mai da turaruka ta shafe mun jiki sannan tasamun dan nigh wear dina dogon riga har kasa mai guttun hannu, sannan ta feshe ni da spray kafin itama ta shirya cikin dogon riga me dan kama jiki. Cikin ta ya fito dan dib dashi agaban rigan sai tai kyau sosai. tana gamawa tasa hijab nima tasamun nawa mukayi sallah, mun idar mukayi addu'a sannan muka tashi. ciremun hijabin tayi ta linke ta Dora a kan dadduman sannan ita ma ta cire nata tajani muka fita. Uncle Dee na Palo dawowanshi kenan daga masallaci ya bimu da kallo.. Ko ince yabi yar matar shi da kallo, dan uncle Dee kirin mazan nan ne masu kallon tsiya sai gashi yahada da aunty maimuna akwai diri. ta wuce da ni dining tasamun abinci hade da juice sannan tadawo Palo ta zauna kusa da shi duc wannan abun yana bin ta da kallon mayata wanda bai ma lura ta matso kusa da shi ba. Iskan da ta hura mishi ne yadawo da shi duniyan tunani, ta sakar mishi murmushi tace Wannan kallo haka Babe.baza ki gane bane yace da ita. to muje kaci abinci tajashi har dining tagama serving dinshi sannan tayi nata, ba wanda yace Kala a cikin mu shima har muka gama ko inda nake bai kalla ba.. ni nafara tashi nace ma aunty maimuna " I want to pee" tace to inje daki inyi. Na sauka a kan kujera na wuce uncle Dee yabini da wannan kallon mayatan har na shige daki. Juyowa yayi ya kalli aunty maimuna " kar yarinyan nan ta wuce gobe a gidan nan" aunty maimuna bata kula shi ba ya tashi yawuce dakin shi dan dauro alwala yawuce masallaci. tabe baki aunty maimuna tayi sannan ta tashi tayi clearing komai a dining ta wuce kitchen dasu. tana gama gyara kitchen dinta ta kashe wutan kitchen din ta jawo kofar ta fito tashiga dakin ta a kwance tasameni duc damuwan Mama ya isheni " is she alright?" ko mugun nan yazo yana sa ta kuka? aunty maimuna ta katse mun tunani na tare da dago ni ta rungumeni, "missing mama?, na boye fuska na a jikinta ina murmushi. Kar ki damu gobe zan maida ki idan muka dawo daga smart kids kinji? Toh nace mata. tashi to kije kiyi alwala kizo kiyi sallah ina nan shigo wa tafada ta tashi tafita. da fitan ta nima na shiga toilet nayi alwaya nafito nayi sallahn isha, ina idarwa na dora da Shafa'i da wutiri yanda Mama ta koyamun.. bayan na idar na karanta ayatul kursih Kafin inyi addu'o'i na kaman yanda mama ta koyar dani. na tashi na linke hijabina na sa a jakana sannan na linke dadduman na ajiye na hau kan gado na kwanta na lumshe ido har bacci ya dauke ni. chan naji kaman a mafarki naji aunty maimuna na ta salati da sallallami da sauri na bude ido.. toh yanzu ina yakeso ku tafi haleema? Nan nagane da Mama take waya takara cewa innallillahi'wa'inna'ilaihi raji'un...


..na mike a rikice na matso kusa da ita na riketa gam nasaki kuka, meyasamu mama?? aunty maimuna takara jawoni jikin ta batace komai ba waya kare a kunnenta. Chan tace to karki damu Allah kaimu safen, ki daure kici abinci ki kisha magani please. amma wallahi dan dai kawai bazaki yadda bane da mun maka Dan iskan nan a kotu dan ubanshi, waye kuma sufyaan?? nawa yake?...tagama sauraren mama sannan tace bakomai in sha Allahu goben zamu zo da safe. katse wayan tayi ta Kara rungumeni. Kuka ya kubcemun Mai karfi, da sauri aunty maimuna ta Kai tafin hannunta baki na ta na girgiza kanta itama trying so hard not to let her tears out. ba abinda yasameta my angel, mama is fine kinji. I want to see her nace mata, tayi karfi halin tsayar da hawayenta tace, I will take you to her in the morning, yanzu dare yayi. ta gyramun kwanciya itama ta matso kusa Dani ta dora Kai na a jikinta.. Kafin sha biyu bacci Mai nauyi ya daukeni. ahankali ta sauka a kan gadon ta jawo bargo ta lullubeni sannan ta tofeni da addu'a ta fita. tana shiga dakin uncle D ta tarar yagaji da jiranta har ya kwanta a hankali ta hau kan gadon ta shiga bargo. Juyowa yayi yace mata wallahi kar kibari akan matan nan da yarinyanta musa mu babban matsala dake, I mean my words sannan ya juya ya lumshe idon shi. aunty maimuna abu ya hadu ya taru mata tunani take yanzu gobe ina mama zata daukeni mu koma? Kiran da mama tamata dazu, fada mata tayi kirin tashin hankalin da sukayi da baba akaina tace daga karshe yamata dukan tsiya tare da saki har uku.. duc a kaina. wani hali nida mama zamu shiga? da wannan tunanin bacci ya dauki aunty maimuna. Da asuba aunty maimuna tashigo ta tasheni inyi sallah sannan ta fita. bayan na idar da sallah tashigo da rike da keyn motan ta abayane baki a jikinta ta yafa gyale. Ta ajiye keyn tawuce bandaki ta hada mun ruwan wanka sannan tafito,taimakamun tayi na cire rigan jikina muka shiga bandakin tare tamun wanka sauri-sauri muka gama komai sannan tafita ta hadomun tea ta kawomun mun, nagama sha ta dauki jakana dare da bude side drawer ta fito da kudi zasu Kai 150k ta sa a jakana da ke rike a hannunta sannan takama hannuna muka wuce. Munfito gari ko gama wayeba baiyi ta bude mota ta sani sannan itama tazagaya tashigo da dauri ta aje jakana a bayan mota muka kama hanyan gida... Da isanmu gidan muka tatar da mama har Gama hada kayan mu. Da gudu har zan fadi na shige jikinta "don't break me salma" tafada a raunane hawayen da taketa kokarin boyewa suka gangaro mata. kana ganin idon ta kasan batayi bacci ba ga uban kukan da

Please Login or Register in order to submit comment