Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiya... al'amin dake lura dashi yace " ai su abbah ne kawai zasu koma yau ko?" Sadeeq da baison aga zakewar shi yace " no, we are going back together" karfe 3 su Sadeeq suka fara shirin dawowa gida, bayan dinbin godiyan da su abbah sukai ma baba na yobe da su uncle abubakar. dan ba kadan aka karrama su ba. daga nan kuma akasa biki nan da wata daya kawai. har su Sadeeq suka dawo kano bai samu damar ganin matar tashi ba. Dan ko waya ma baisamu damar yi da ita ba, through out yana tare dasu al'amin.. Baba na yobe kuwa ba lomai yasa yama iyayen Sadeeq haka ba, sai yadda uncle abu yamishi bayani sosai akan Sadeeq. Sosai ya yaba da halin shi dakuma jarumta irin na Sadeeq din yasa suka yanke shawarar kawai su aura mishi ita basai anwahalar da iyayenshi da zirgazirgan bin hanya ba... Suna dawowa gida su abbah sukai part dinshi, sadeeq kuma yai hanyar shiga part din mami. yana shiga yaji anrabka uban guda kamar za'a fasa mishi dodon kunne. yan uwan abbahn shine da na mami a palon, saiga hauwa tafito daga dakin mami da sauri tayo kanshi " a big congrats to you big bro.. dama you once told me zaka rigani yin aure, I never knew you were that serious" Sadeeq kanshi akasa ya rusuna ya gaishe da kowa a palon sannan yaja kanwar shi sukayi hanyar dakin mami. da shigar su mami ta fadada murmushinta ta mike daga zaunen da take " yanzu muka gama waya da abbanka.. just heard the good news" Sadeeq yanima waje ya zauna a gefen gado yace " wlh mami,.. sun mana kara sosai" mami tace toh ubangiji Allah ya yasa albarka son. hauwa ta amsa da amin tare kallon yayan nata tace " ya Sadeeq can I see my auty's picture please?" Sadeeq ya mike yai hanyar fita tare da cewa "idan tazo bikin ki sai ki ganta da kyau" karfe 9:17pm Sadeeq ne kwance akan gadon shi, bayan yadawo daga raka nabeel ya wuce gida. Daukar wayar shi yayi yashiga kiran damsel da har ya chanza sunan daga noor zuwa "wife" har ya kusa tsinkewa aka dauka.. ahanakli tamishi sallamah.. Sadeeq yace " wifeyy.. Alhamdulillah.. You're now mine, mine forever..." damsel ta kalli mimi dake kokarin saka pyjamas dinta.. kasa mishi magana tayi, dan sosai takejin kunyar Sadeeq ko awayan nema yanzu. Sadeeq yace " haka zamuyi ta azumin magana babe?" Mimi da har tagama chanza kaza, daukar wayar ta tayi tai hanyar fita. tana fita damsel tace " wai khadija tace zasu kawoni Kano" Sadeeq yace "ko kefa babe, kirinka mun magana please,.. Yeah you will come to Kano and meet my family. they can't wait to meet you wifeyy... when are you coming?" ahankali damsel tace " nima bansaniba" sunkai har karfe goma suna waya. shirun da Sadeeq yaji ne yasan tayi bacci, kafin ya yanke call din. yau bikin hauwa saura kwana hudu, gida kuma ya cika makil da yan uwa da abokan arziki. bangaren mami kuwa ita da su hajiya khdija maman nabeel tare da wasu yan uwanta su uku, sosai suke shirya lafiyayyen abinci kiri da Kala, dan tun jiya abbah ya tura yan uwan shi mata su uku akan suje akara masu baba na yobe godiya sannan su dauko damsel, dan yadda aka tsayar da magana kenan lokacin da suka zo akan zatazo dangi na nesa aganta kafin ayi biki kuma su suwuce. karfe 5 na yamma suka iso dan basu taso da wuriba saboda ba'a gama mata gyaran jiki ba. acikin Wanda suka biyo damsel har da matar uncle abu sai haj. Ummahr maman al'amin. suna isowa gida yakara hargitsewa da guda har Suka isa dakin da aka tanadar musu dan su huta. tunda suka shigo gaban Hafsat ya dinga fadi, ducda tariga tasama ranta dangana, amma sosai gaban ta ke fadi dan kwanan ta biyu kenan da zuwa gidan saboda bikin Hauwa, ga event din da suke dashi na friends washa gari.. bayan su aunty Ummahr Sun dan huta Sun ci abincin da aka shigo musu dashi, suna idar da sallahr magrib suka kara shirya damsel cikin wani tsadaddar leshi da gold necklace din da uncle abu yasiya musu ita da mimi,sai turaruka da Suka feshe ta da su masu azabben kamshi, suna gama shirya ta ko minti biyu basuyiba, saiga wata mata acikin wanda sukaje yoben ta shigo akan tamusu jagora zuwa dakin mami. Har cikin dakin takai su, su hudu acikin dakin, yan uwanta biyu sai maman nabeel sai kanwar abbahn Sadeeq dake aure a abuja. Fuskar damsel rufe da shantly vail kalan leshin jikinta sai uban kamshi da take zubawa. Sosai aka tarbe su, damsel na makale kusa da aunty Ummahr fuskar ta a rufe, ga uban faduwa da gabanta yakeyi.. gaisuwar mutunci suka shiga yi tare da sama auren albarka, mami na zaune tana zuba murmushi, aunty Ummahr tafara magana " toh ga amana munkawo muku.. noor ko kadan ba mai matsala bace, kuma in sha Allahu baza'a samu matsala daga bangarenta ba, kamar muma yadda muke ganin baza mu samu a bangaren ku ba. Dan sosai mukaga karramci da girmamawa tunda muka zo, muna godiya kuma Allah yakara mana karfin zumunci." kowa ya amsa da ameen. haj khadija tace " in sha Allahu kuwa kun kawo amana gidan da ya dace, fatar mu Allah tayamu riko." ameen duc kowa ya amsa kafin aunty husnah kanwar mami ta Mike ta isa inda damsel take da fara'arta ta tsuguna ta bude mayafin damsel ahankali .. Sosai suka shiga gudu ganin wani sheki da takeyi tun kafin su ganta da kyau... aunty husnah tace "welcome to the family gorgeous.."Damsel ta tuna abunda aunty Ummahr tafadi mata, nan dan nan ta mike ta daga zaunen da take ta tsuguna agaban aunty husnah cikin sanyin muryar nan nata tace " inawuni.." duc suka amsa mata, daganan suka shiga mata kananan nasihohi kafin su aunty Ummahr suka musu tare cewa su gobe sa safe zasu koma in sha Allahu, ita kuma zasu barta tadan yi musu kwana biyu duc yan uwa su ganta.. nan damsel taji gaban ta ya tsinke. dan duc tunanin ta tare zasu koma. haka kuwa akayi, washa gari da karfe 8 har Sun gama shiri, damsel kuwa taci kuka har ta gaji dan sosai su aunty Ummahr Suka dinga mata nasiha tare da nuna mata muhimmacin aure,sallamar da Sukaji yasa sukai shuru tare da amsawa. Nabeel yafara shigowa cikin cream shadda dinshi sai Sadeeq daya biyo bayan shi farin shadda ne ajikin shi. abayan nabeel sadeeq ya tsuguna, sannan Sula shiga gaishe da su aunty ummah, ta gefen ido Sadeeq yake kallon damsel da duc tadawo kamar mara lafiya. Sosai jan super wax din da tasa sukai masifan mata kyau. Nasiha sosai aunty aunty Ummahr da matar uncle abu suka musu. Nabeel ne ya iya musu godiya dan Sadeeq kam ba baki dan kunya. 100k Sadeeq ya ajiye musu kafin ya mike ya fita kanshi akasa, nabeel kuma yafada musu idan Sun shirya mota na jiran su awaje. Mikewa aunty Ummahr tayi tare da cewa a shirye muke.. Damsel ta mike itama tana kallon aunty Ummahr " I'm going with you.." tana fada ta fashe da kuka.. Nabeel ya Kalle ta so daya kafin ya fita, aunty Ummahr ta juyo tana kallon damsel kafin tace " kunya kikeson bamu ko daughter?? So kike yan uwan mijin ki suce ya auro yar kauye ko?? " matar uncle abu ta matso ta rungume damsel kafin tace " kiyi hakuri daughter, su mimi suna nan zuwa anjima kinji? " damsel ta gyada kanta kawai. aunty Ummahr tace "toh koma ki zauna" ahankali damsel takoma ta zauna gefen gado. Saida har aka kai su aunty Ummahr part din abbah sukai mishi sallahma sannan suka fito suka dau hanya tare da dunbin arzikin da mami tacika su dashi.. Nabeel ya kalli abokin nashi kafin yace " sai kashiga kafara uban lallashi dan kuka takeyi, haka kurin mata su rinka kuka for no reason, toh ta ina ma zan dauki wannan shirmen? " Sadeeq murmushi kawai yayi kafin yashiga cikin gidan, yana shiga ganin ba kowa a palon yasa ya dau hanyar dakin da sauri. da shigar shi yaga Hafsat tare da hauwa a dakin,.. suna ganin shi duc sukai shuru da maganar da suke ma damsel...

...mikewa sukayi dukkansu zasu fita, Sadeeq ya kalli Hafsat da tunda yashigo takasa hada ido da shi, kallansu yayi kafin ya kalli damsel da kanta akasa yake tunda ya shigo. da sauri Hafsat ta fice sannan hauwa tabi bayanta. Sosai abun ya daure ma Sadeeq Kai, har suka kullo kofar kafin yadawo da kallon shi kan damsel da fuskar ta yatara hawaye.. ahankali yakarasao ya zauna kusa da ita sannan yakira sunan ta " Noor " kasa dago kanta tayi. Sadeeq ya tsuguno da kanshi ya dan leko fuskar ta " why are you crying?? You don't like it here? mu muce gida? " Kamar jira takeyi da sauri ta daga mishi kai... Sadeeq yace "me suka ce miki da suka shigo? " kamar baza tace komai ba at first, sai kuma tafara magana kanta akasa " they introduced themselves to me" Sadeeq yace "as?" damsel tace " one of them said she's your sister and she's getting married next tomorrow, and she want me to attend her wedding event ltr.. and the other said she's Hafsat and.." kasa karasawa tayi, Sadeeq dai yana kallonta "uhmm and??" Damsel ganin baza ta iya fadin me Hafsat tace ba, yasa kawai tace, "and she said they like me" murmushi Sadeeq yayi sannan ya dago kanta suna kallon juna.. "of course,they should like their big brother's woman.. Because she's gorgeous and more.." damsel ta sauke kanta kasa, kara matsowa kusa da ita yayi zaiyi magana aka bude kofar, da sauri ya yajadabaya, ganin mami ne yasa ya mike yai hanyar fita.. karasowa mami tayi tayi ta kalleta tare da murmushi a fuska tace "sa mayafin ki kibiyoni. Damsel ta dauki red Vail din da ke kusa da ita ta yafa. sannan ta mike, suna fita takai ta dakinta, lokacin har haj. asabe tazo, mahaifiyar Hafsat. sosai suke kama da Hafsa. Kan damsel a sunkuye suka shigo dakin da mami, zata zauna akasa mami tai saurin rike mata hannu ta kaita har kan kujeran dakin. Haj. asabe tabisu da kallo kafin tace "masha Allah, Allah ya sanya alkhairi." sai lokacin damsel ta dan dago da kanta, ganin mutane a bakin gado yasa ta sauko ahankali ta tsuguna tafara gaishesu.. mami ma sosai taji dadin abunda damsel tayi. Duc suka amsa. ganin bata mike ba yasa aunty husnah ta mike takaraso har inda take ta dagota ta maida kan kujeran sannan ta zauna kusa da ita, dan sosai takejin damsel aranta, sai take ganin kodai itama mixed ce, dan kyan ta da hasken ta is something else. waya Kare a kunnen mami tace " wai Kana ina ne da sai cemun kaketayi mami gani nan zuwa? ba yanzu na ganka ba?.." ba ayi five minutes ba sai ga shigowar Sadeeq din, wanka yasakeyi tare dasa wani hadadden bakin yadi daketa faman sheki, ahankali yayi sallama ya shigo kanshi akasa, nan kawayen mami da aunty husnah suka shiga mishi tsiya,.. aunty husnah tafara mishi magana da larabci tace " Sadeeq ina ka samo kyakkawa haka? Kodai Egypt katafi ka dauko ta, kawani fake da yar Nigeria?? Ko kadan batai Kama da yan Nigeria ba" Sadeeq yai murmushi kawai, yaso bata amsa, amma ganin mamin shi agurin yasa yai bai ce komai ba.. Sosai haj. asabe tashiga jero musu addu'o'i. Sadeeq kanshi akasa ya amsa da ameen a dan kunyace.. nan mami tace yi maza ku tafi kafin takara Kiran abban naka tace ni na hana akai ta. mikewa Sadeeq yayi, aunty husnah ma ta mike tajowo hannun damsel suka fita. suna fita Palo ta riko hannun Sadeeq ta damka mishi na damsel tare da ce musu sai sundawo.. sun fito harabar gida suka ga yan mata, haddadun big girls kowa na latsa wayar ta dan 4 daidai zasu wuce event din su da abokanan ango suka shirya. Hafsat na hoto da kanwar nabeel xee data sha ubansun abaya, tana ganin fitowar su Hafsat tace "Innalillahi, Xee wlh I can't" Xee ta daga kai ta Kalle Sadeeq da har ya bude ma damsel gaban mota ta shige, ganin bataga fuskar ta da kyau bane yasa tace ma Hafsat "inazuwa" sannan ta isa parking space din da sauri, har Sadeeq yazago zai shige tace "Big broo" Sadeeq ya juyo, ganin Xee ne yasa ya tsaya tare da cewa " my fav." tana daria ta karaso ta rungumeshi tana fadin " congratulations ya Sadeeq, Allah ya sanya alkhairi,. can i greet her? Sadeeq yace "sure Sis" karasa tayi ta bude gaban motan tana murmushi tace " good afternoon our beautiful aunty.." dagowa damsel tayi ta dan saki murmushi, dan sosai yanzu takoya yanda ake tarban mutane. Damsel tace "hi" mutuwar tsaye xee tayi ganin Damsel hadaddiya ce ajin karshe. Sadeeq da har yashiga mota yace bari muje mudawo lil sis. Xee tace "alright.. event dinmu fa ya Sadeeq 4 ne, hope you will be back before then?" Sadeeq yace in sha Allah sannan ya ya tada mota yai reverse. xee nakomawa wajan friends dinsu taga bata ga Hafsat ba, tana kokarin shiga ciki taga wata ta rikota " kai xee bura'uba... Matar yayarku ta hadu." xee tai murmushi kawai kafin tace "please ina hauwa da Hafsat suke?" budurwar tace I think sun shiga ciki. Xee ta shige da sauri tai hanyar dakin hauwa, tana taba kofar taji shi agarkame..waye taji antanbaya, Xee tace "open the door hauwa, it's me" da sauri hauwa ta sake Hafsat sannan ta karaso ta bude kofar. Xee na shigabsuka maida kofar suka kulle. Hango Hafsat tayi akan gado tana kuka. hauwa ta kalli zee sannan Suka karasa kan gadon. Sosai Xee tashiga ba hafsat baki suna lallashin ta. xee tace " kuma fa kawai haske zata nuna miki, so meye abun damuwa??" Hauwy tace "exactly wht I said to her nima wlh" hauwa ta Kara da cewa " inbanda ke ma,.. kina da ya nabeel, then why worried??" Xee ta bude ido kafin tace "SERIOUSLY??" hauwa tai daria tace "uhumm haka mami tace mun" nan xee tashiga tsalle kafin ta Kalli Hafsat tace "haba mana aunty Hafsyyy" duka Hafsat takai mata, sannan suka sa daria dukkansu. Saida Suka tabbatar Hafsat tadawo Normal sannan suka bude dakin suka fito.. Sadeeq kuwa yana fita ya sau hanyar bonpai inda kakar su take, mahaifiyar abbansu. ahanya ya tsaya a wani super market kafin yadawo da kallon shi kan damsel da har tafara bacci yace " my sleeping beauty.." ahanakali damsel ta bude ido tana kallon shi " wht do you think we should get for grand ma?" damsel tai shuru tana kallon shi.. Sadeeq ya kashe motar tare da saukowa yazagawo ya bude mata kofar ta fito. haka Suka dunga zagaye super market din, shidai binta yaketayi da kallo, chan itama bayan tagaji yasa takai hannun ta gurin turaruka, tasa kamar guda 4 basket din sannan ta kalli Sadeeq tace " inkara?" Sadeeq yace "no, let's go for something else Babe" sosai Sadeeq ya mata siyayyan kayan tea sai wasu abubuwa naci dayasan yan diabetes zasu iya ci ya dauka sannan suka biya ya fito. Suna isa gidan ya bakowa a palon sai uban kamshi dake tashi. ajiye ledojin yayi yana kokorin bin hanyar dakin ta yaga fitowar ta daga kitchen, ita da mai tayata zama. nan tace " aikuwa gaskiyar ki ce hinde, baki mukayi" kallon damsel dake nan a stsaye tayi kafin tace " zauna mana kishiya, halan shi ya kitsa miki mugun abu yace ni mayya ina tsotse jinin mutane ko? " Damsel ta girgiza mata kai. Hajiya ta gyara daurin zanin ta tace " atohh dan karamin aikin shi ne, tsab zai iya wlh maza zauna ga girki lafiyayye chan ina miki" Damsel ta nima waje a kan carpet tai zamanta, sanyin ACn palon na buga ta. Sadeeq ya Kalle kakar nasu yace " ni baza kice in zauna ba hajiya?" maimakon tabashi amsa, sai tashiga gwala ma hinde kira, tace maza ki Fara fitowa mata da kajin da lamurjen da yanzu nagama hadawa kamin miyan yagama kama jiki inzo insa ganye.. Sadeeq yai murmushi sannan ya nima waje ya zauna a kan kujera.. ahankali damsel tace "inawuni.." hajiya ta mimmike tana kallon damsel tare da washe baki tace "lafiya kalau yar baturiya, halan kema daga misiran kike? ducda dai Muhammadu yace mun yar pataskum ce ke, toh yana iya yuwuwa zuwa kukayi ko?" Damsel ta girgiza mata kai kawai, chan sai ga shigowar hinde da katon tray a hannu, zata ajiye agaban Sadeeq hajiya tace "amma hinde baki hankali, yaya kina ganin bakuwa zaki wuce da tray wani wajan? " hinde tai daria tare da matsowa da tray din kusa da damsel, sannan tafara gaishe da Sadeeq, Sadeeq ya amsa tare da tambayar ya suke, juyowa tayi suka gaisa da damsel, sannan ta shiga yi mata wasa " Aa dole Sadeeq ya dauke kafa wurin uwar gida, ashe baturiya ce ta rikitar mana da shi haka" Sadeeq yace atoh kema kya gani yanxu ina da dalleliya a Leda toh inani ina tsohuwa?? Hinde tai dariya sannan ta mike ta shige kitchen.. Hajiya kuma ta shiga bude kuloli tana kallon damsel kafin tace " maza zo kici abinci yar nan, hajiya ta mike tace inazuwa sannan ta wuce kitchen.. Sadeeq yana zaune a kujera yana kallon su, ganin hajiya ta mike ne yasa ya kalli damsel yace "give those things to her when she comes back " bai rufe baki ba saiga hajiya da serving spoon a hannu, tana kokarin diba ma damsel abinci taga damsel ta miko mata lodoji yace "naki ne" nan hajiya ta washe baki kafin tace "tun yanzu yar nan? baki kam ya toshu tunda an kwace miji ya zanyi? toh Allah yai miki albarka, haka akeson aga hannun mutum abude, dakuma son mutane, ai zaki rinka zuwa tunda kinga hanya ko?" damsel tace "A" Hajiya yauwa, yar albarka. ai rahin son mutane ko kadan baiyi ba. Sadeeq yasan shi take jefa ma maganganu amma bai ce komai ba, mikewa yayi yana kallon agogo sannan yace "hajiya barin yi sallah indawo" kallon gefen ido tamishi sannan tace " Aa inkaga dama ma wlh kai wucewar ka.." dariya Sadeeq yasa yace " sai inbarma ma Matata waye?? yana fadin haka ya waje, hajiya taciga da sa damsel abinci tana ta faman zuba surutu. bayan damsel tagama ci har daki hajiya ta shiga da ita dan tayi sallah, Damsel na idarwa hajiya ta nima gefen gado ta zauna, sosai tashiga yi ma damsel nasiha. bayan tagama kuma ta kara gyara zama tace " sannan magana na gaba, dan Allah yar nan kiyi kokari ki rinka fahimtar da mijinki muhimmancin yan uwa, dan baisaniba. yanzu ni din nan da kike gani fa ni na haifi ubanshi, amma wlh rabo na da inga abubakar a idona, toh inban yi karya ba, yau shekara daya kenan, yanda kika jin nan. sosai kisa shi gaba yaso yan uwanshi, dan inbahaka, yayan da zaku Haifa ma haka zasu gani su dauka, yoh ina anfanin haka..? sallamar Sadeeq da taji yasa tahajiya mikewa tace toh taso muje kici lafiyayyen tuwo miyar taushe.. a kofa Damsel ta tsaya tana kallon Sadeeq dake danne danne a waya, hajiya har ta shige kitchen.. Dagowa yayi suka hada ido.. sauke idon ta tayi ahankali tace "you haven't eaten anything" Sadeeq yai murmushi yace " nakoshi babe, I ate snacks din da su hauwa sukayi agida." karfe uku Sadeeq ya mike yana duba agogo dan yasan nabeel zaizo gida yace "hajiya zamuwuce yamma yayi " hajiya tamike tai hanyar daki. Sai gashi ta fito ma damsel da dan kunnen azurfa mai shegen kyau acikin box tace "ungo ashe rabon ki ne" Damsel tai murmushi ta amsa ahankali tace "nagode" Sadeeq ya shafa kanshi sannan yasa hannun aljihu yafito da mint min 500 yamika mata dan he knows how's she's soo obsessed with mint. hannu na rawa hajiya ta karba kamar bata taba ganin kudi aduniya. har mota suka rakasu, Sadeeq yaba hinde 10k tana ta godiya. Suna fitowa suka dau hanyar gida,... Nabeel ne yai parking motar shi Wanda shigowar shi kenan, kananan kaya ne jikin shi Blue Jeans da sai ash T-shirt mai guntun hannu. ya dau phone din shi zai kira Sadeeq kenan sai ga bullowar su Hafsat da kanwar shi za'a kaisu gurin event.. sosai fitted gown din da suka sa yamusu kyau dan dinkin su kiri daya sukayi. tun daga nesa nabeel ya hango su. xee kuwa tana ganin yayan nata ta karasa da sauri tana murmushi "thanks God you're here ya nabeel, please ka kaimu petals dan har mukusa muyi latti ma wlh" nabeel yasa eye classes din shi yace " I have somewhere I want to go wit Sadeeq" sosai xee tashiga rokon shi, Hafsat dai na make a gefe. ganin motar Sadeeq yashigo gidan ne yasa nabeel yakara hada fuska " ina wasa dake ko zainab" har Sadeeq yafito bata bar wajan ba, Hafsat kuwa tunda suka fito take kallon su.. ahankali tarinka furta Innalillahi a zuciyanta Damsel kuwa kallo daya tama Hafsat ta dauke kai.. kafin tafara tunanin abunda suka ce mata da safe.. inko dagaske ne toh lallai baza tauna da Sadeeq ba. She will find her way again....


....har inda Hafsat take Sadeeq yakaraso, ahankali yake mata magana Wanda ba Wanda yakejin me Sadeeq din ke fadi idan ba hafsan ba, damsel naganin haka ta kau fuskarta, wani abu taji ya tokareta a mokoshi, abun da bata taba ji ba a rayuwar ta kuwa, batasan sadda ta shige ciki ba, direct tai dakin da suka sauka. sadeeq da baima san damsel ta shige ba, nan yacigaba da ma Hafsat magana ahankali yace "inajinki.." Hafsat tace " toh ya Sadeeq bai ce komai bafa, ko ranar ma da kasani inkira shi awaya, yana jin murya na yace zai kirani, har yau bai Kira ba.. ya Sadeeq I don't think I can do this.. Sadeeq ya juyo yana kallon Xee dake waya, tana fadin "OK gamu nan fitowa" Sadeeq yace " who are you on a call with?" xee ta tace " friend dinmu ce tace mufito sai mu wuce tare" Sadeeq yace " ke kije, Hafsat za'a kawo ta" xee ta tai murmushi sannan ta karba hand bag dinta a hannun Hafsat ta wuce.. Sadeeq yacema Hafsat " zo muje" kamar tana nazarin wani abu, sai kuma ta kama hanya ta bishi. Har bakin motar nabeel Suka isa,.. ya bude mata front seat din motar nabeel tare da cewa "get in" a dardar Hafsat ta shiga sannan Sadeeq ya maida motar ya kulle. Nabeel na tsaye bakin kofar motar shi yahada girar sama da ta kasa. Sadeeq ya Kalle shi "stop the foolish acting and do the needful please.." yana fadin haka ya barshi a gurin yai hanyar motar shi, wanda duc tunanin shi damsel ta koma ciki ne. ganin bata nan sai box din da hajiya ta bata ne a kan seat din. daukowa yayi tare da rufe motar, ganin nabeel har ya tada mota yasa ya girgiza kai kawai ya shige cikin gida.. inda yasan zaiga damsel yashiga, ganin gyalenta a kan gado yasa ya nima waje ya zauna. Minti biyar saigashi yafito daure da al'wala.. tana ganin shi ta sauke kanta kasa tare da cewa "I need hot water to bath.." Sadeeq da yasan ba water heater a dakin, ajiye mata cute box din yayi tare da cewa " yi sallahr to sai muje daki na kiyi wankan.. I

Please Login or Register in order to submit comment