Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace ma Sarah "add more onions" Sarah tace yes aunty kafin ta juya... sosai damsel tabi duc process din da sukayi nayin stew so biyu da khadija ta hada hadadden miyan stew dayaji meat balls. bawani spices da tasa sai ginger and garlic. dan khadija ba kowani abinci take jibga ma spices ba, most especially stew.. su iman har sundawo daga school lokacin kuma har su damsel sungama girki..


.....nabeel kuwa yagaji da hanyahanyar da al'amin yake mishi, dan kullun magana daya yake mishi idan yakira shi, akan cewa baya samun time ne amma in sha Allahu he will call him.. yanke shawaran zuwa gidan al'amin din yayi idan yatashi daga aiki dan yayi tunani tabbas ba inda Sadeeq zai kaita duc cikin fadin garin Lagos inba gidan al'amin ba. tunda yana da mata. karfe biyar yatashi a awajan aiki. yana fitowa yakama hanyar gidan al'amin tare da daukar waya yakira al'amin din...

....al'amin yana waya da khadija a office dinshi, suna magana akan zuwan uncle abubakar. khadija tana tambayar shi ko me yakamata a dafa, ganin call din uncle abu yashigo.saurin tsinketa al'amin yayi tare da cewa I will call you back babe, sannan yai picking call din shi. Suna gama gaisawa yace mishi al'amin zuwa na bazai yiwu yau ba sai gobe in sha Allahu, dan na tsaya a abuja, kuma ga Muhammad ma yace zai biyoni, toh mundaga tafiyar zuwa gobe in sha Allahu.. al'amin yace "bakomai uncle abu, nidai fatana Allah yasa adace" uncle abubakar yace "ameen ameen, amma naso da kunyi magana da shi Sadeeq din.." al'amin yai saurin cewa "Aa a barshi kawai har yadawo, kar a tado mishi da magana kirin haka yana wajan aiki." yakara da cewa, munyi chat dazuma yace mun in sha Allahu cikin Week din da zamu shiga ma zaidawo. uncle abubakar yace "toh shikenan ba matsala." daga nan sukai sallama...

... Damsel ne zaune a daki wuraren karfe hudu da rabi, waya ne kare a kunnenta suna waya da sadeeq, Sadeeq yace talk babee, me kike ganin zamu siyo ma khadija and the kids??" damsel da har tagaji da cema Sadeeq ko meye ya siyo,.. ahankali yaji tace " buy new lunch boxes and chocolates for the kids" dan taji ranar iman na ma babanta magana that she want new lunch box, Dan iman is so obsessed with lunch box.. Sadeeq yai murmushi, dan yasan ahaka ma sosai tayi tayi kokari.. ahankali yace toh "what about khadija??" nan damsel tayi shiru tana nazari, rasa abun cewa tayi yasa tace "buy her chocolates too" Sadeeq da baisan sadda yai daria ba yace "chocolate kuma babe??" toh shikenan, any thing you say babe.. suna gama waya, takoma tai kwanciyar ta, dan yau she's moody... khadija lokacin da har ta dawo daga kasuwa, dan suna gama waya da al'min ta dauki mota zuwa kasuwa Dan karo wasu abubuwan da babu, text din al'amin tagani akan zuwa uncle abubakar wai sai gobe.. itama tana dawowa ta shige daki ta kwanta kafin lokacin dawowar su iman daga islamiya yayi..
.... Uncle abubakar ne zaune a palon hajiya Maryam, dan basma da hanifa har labari ya Kai musu kila angano inda yar uwar su take.. basma dake abuja har ta karaso gidan su jin uncle abubakar yazo kuma washagari zasuwuce Lagos din shida da yayansu Muhammad. nan itama ta hado kaya akan zata bisu.. uncle abubakar ya kalleta kafin yace "saboda rashin hankali duc sai in dauke ku muje gidan mutane, yarinyar da ba wai muna da tabbaci akan ta bane, ai duc sai su dauke mu marasu hankali, shima Muhammad dan kawai ya matsa ne." haj. Maryam tai murmushi kawai.. kafin tace, nima dai haka nagani, ai ba taruwa za'ayi aje musu haka ba, mussanman ma kirin wannan lokaci da ake aciki, kowa naji da kanshi.. Kiyi hakuri babanku yaje da yayanku kawai.. Hanifa ma ni na dakatar da ita da tazo tun jiya. Mudai fatar mu, Allah yasa andace." duc Suka amsa da ameen....

...sosai khadija da damsel suke ta faman hada verities of abinci a kitchen dan jirgin karfe biyu su uncle abubakar zasu shigo... al'amin kuwa yana office yana duba wasu files, yana yi kuwa yana kallon agogo dan zaije dauko su uncle Abubakar a airport. knocking yaji anyi a kofa, kafin yabada izinin ashigo har anbude kofar anshigo.. Nabeel ne cikin kananan kaya dasu kai masifar mishi kyau, sai pcap din shi baki da yasa anrubuta "NIKE" ajiki. al'amin yana ganin nabeel ya mike yana murmushi ya iso gare shi.. sosai yaga hutu ba nawasa ba a jikin nabeel din amma dan kawai ya tsokaneshi yace " kaii aboki kaga yadda rashin aure yasa kawani rame da baki da kayi kamar wani mara galihu kuwa??" nan da nan nabeel yahada rai, tare da cewa, "Kaga idan iskancinka zaka fara Mun, wlh yanzu sai in juya inyi komawa na gida." al'amin ya tuntsire da daria tare da jawo abokin nashi har kan kujera yace, "haba dai, kama isa?? ba bansa nurses Sun riko mun kaiba."yana fadin haka yai hanyar mini fridge din da ke office din... Nabeel ya gyara zaman shi tare da cewa, "da na karya yarinya kuwa wlh" al'amin kuwa dariya ya dunga yi dan Sosai yai missing friend din nashi.. ajiye mishi cold bottle water yayi agaban shi dan yasan baicika son drinks ba. tare da duba agogon hannunshi yace "please nabeel zaka dan raka ni airport." nabeel ya dauki ruwan yana kokarin budewa yace "kaidai you don't stay in one place ko kadan, who are you seeing there?" al'amin yace, you remember that my uncle? uncle abu?? Nabeel ya cire goran ruwan a baki yace "yeah yeah, shine yazo?" al'amin yace yeah, in 20 minutes nasan sun sauka, so please let's go kafin yafara mun fada, dan ko kadan baison jira... Mikewa nabeel yayi tare da bin bayan al'amin har suka fito zasu shiga mota. wata nurse ce tabiyo al'amin tana mishi magana, bayan tagama tajuya zata wuce suka hada ido da nabeel dake kokarin shiga motar shi, wani kallo tamishi kafin ta kara gaba dan tunda yashigo ta dinga bin shi da kallo. kallon shi kawai al'amin yakeyi ganin kirin kallon da yabi nurse din da shi. girgiza kai al'amin yayi kafin yace " a asibitina zaka dauko mun surukar kenan??" saikuma ya tuntsire da daria. kallon shi kawai nabeel yakeyi dan yaga yau sosai al'amin ke niman bata mishi rai,.. bin yarinyar yakarayi da tuni har ta shige ciki yayi da kallo, sannan ya Kalli al'amin yace "mezan yi da chubby girl??" yana fadin haka yai tsaki ya shige motar shi. Sannan al'amin ma ya shige nashi suka kama hanya... Da isar su kuwa basu kai ko minti biyar ba, suka iso. nabeel yafito suka gaisa sannan uncle abubakar yashiga motar al'amin, Muhammad kuma yashiga motar nabeel. Har Sula isa gida hira sosai nabeel ke ma Muhammad, dayake shima Muhammad yana da saurin sabo da mutane, nan da nan kuwa suka dinke, har suka iso gidan al'amin. suna isowa kuwa iman da amar suka fito sukai wajan Muhammad da gudu dan Sosai Muhammad keji da su in sunje abuja. Kafin suka isa wajan babansu kuma.. Nabeel yashafa kai ya dauki amar yana mishi wasa kafin yace "saboda ba uncle Sadeeq bane, shiyasa ko kallona bakayi ba ko boy?" dukkansu sukai daria, Muhammad yakama hannun iman suka shige ciki.. bakowa a palon sai kamshin turare dake tashi, da sanyin AC.. al'amin direct ya haura sama bayan kowa ya nima waje ya zauna. direct dakin khadija ya shiga, maroon color lafaya tasa sai bakin inner tare da bakin dan kwali da ta daura, tayi daurin "kallabi" sosai tayi kyau. al'amin yana ganin ta yace "mata agidan al'amin, daka ke ba wata" khadija tai daria sannan tace "idan tazo ma ai she's welcome, indai ba'a kaina za'a dorata ba" al'amin yajawota jikin shi ya rungume kafin ya kai bakin shi daidai kunnenta, " bakin mu Sun iso babe.." tare Suka sauko, tana biye da al'amin abaya har palon... tana shigowa ta tsuguba tafara gaishe da uncle abubakar, amar na jikinshi yana zuba mishi ruwan surutu, da fara'a ya amsa mata,kafin tajuya ta Kalli nabeel da Muhammad, Muhammad ya gaisheta sannan suka gaisa da oga nabeel, wanda tunda ya shigo gidan yake raba idanu ko zaiga Damsel.. (lol) mikewa khadija tayi ta shiga dakin Sarah takirata. ruwa mai sanyi da drinks aka dunga shigo musu dashi palon.. sundan sha kadan kafin duc suka fita zuwa masallaci.. Suna dawowa kuwa nabeel ko shiga gidan baiyi ba yacema al'amin zai wuce dan akwai inda zashi. al'amin yayi yayi ya tsaya dan suci abinci amma yaki. Sallama yama Muhammad akan kila ya shigo gobe, bayan Muhammad din yafada mishi hotel din zasu sauka... Suna shiga gida kuwa batare da bata lokaci ba suka wuce dining suka fara cin abinci. Khadija tai hanyar dakin damsel daketa ta bacci. pink and blue atanfa ne ajikinta, anmishi dinkin "Abuja bubu" tashinta khadija tashiga yi akan ta tashi tai sallah sannan tazo su gaisa da baki a Palo... tana idar da sallahn kuwa ko hijabinta bata cireba ta fito ahankali... har sungama cin abinci suna tattaunawa da al'amin a Palo, saiga saukowar ta, Muhammad ya dinga binta da kallo gaban shi nafadi, dan sosai yake ganin fuskar babansu. har cikin palon takaraso sannan ta tsuguna kanta a kasa tace "inawuni.." uncle abubakar da sai yanzu ya juyo ya kalleta shima gaban shi na fadi, ducda kuwa kanta a kasa yake. ahankali uncle abubakar yace "lafiya kalau baiwar Allah" muryar da taji yasa ta dago ahankali, cause the voice sounds familia... suna hada ido da uncle abubakar ta mike da Sauri jikin ta na rawa tafara ja da baya... shi kanshi uncle abubakar shock ne yakama shi ganin fuskar dan uwan nashi sosai... mikewa al'amin yayi ganin tana komawa da baya da basu san dalili ba. kafin yai saurin zuwa ya riko ta dan ganin har takai kusa da karfen steps din su, wani kirin buguwa tayi da karfen da har saida yasa Muhammad ya karaso da sauri.. ya riko ta. dishi dishi take gani kafin idon yarufu ruff..

....khadija ne zaune a gefen gado hannunta rike da na damsel. al'amin har yamata alluran bacci, dan buguwan ba sosai bane. ana idar da sallahr isha kuwa su uncle abubakar suka wuce hotel, kuma har sannan bacci takeyi... khadija duc tabi ta damu, al'amin ne yaketa dan kwantar mata da hankali akan in sha Allahu zata tashi lafiya kalau, ta dan firgita ne kawai.. su uncle abubakar kuwa jimami suketayi akan ko me ya firgitar da damsel haka.. Baba na yobe kuwa yakira uncle abubakar yafi a kirga, wani kiran ma Muhammad yake dauka yace mishi har yanzu su basuje gidan al'amin ba sai gobe da safe.. Sadeeq kuwa da har yagaji da kiran Damsel dan yafada mata good news akan yadda sukayi nasara sosai awajan aiki.. ganin bata dauka ba yasa kawai yayi hakuri yai kwanciyar shi... wuraren karfe biyun dare damsel ta bude idon ta a hankali, wani mugun nauyi taji kan yana mata, ahankali ta mike kafin ta dan jingina da jikin gadon, abubuwan da suka faru ya dinga dawo mata ahankali.. rike kirjinta tayi jin wani zafi da yake mata, tadade bataji abunda takeji a kirgin ta ba... mikewa tayi tafara tafiya ahankali zata isa gaban mirror, wani jiri ne yadibeta tafadi akasa.. idon ta rufe ta dinga maida nunfashi. dakyar ta rarrafa har kan kan dressing table din tai unplugging wayan ta achaji sannan ta jingina da jikin dressing table din tana maida nunfashi ahankali.. kallon wayan ta dunga yi tana ganin uban missd calls din da Sadeeq yamata.. takai minti uku tana kallon wayan kafin tai sliding ta shiga call logs. numbern kenan dama nashi awayan, nan tafara kira.. Sadeeq da har yayi nisa cikin bacci yaji wayan shi na vibrating a kan side drawer.. ga kiran sallahn farko dayakeji ana Kira a masallaci, har wayan ya tsinke yakasa motsawa, damsel kuwa ganin Sadeeq bai dauka ba yasa ta ajiye wayan sannan takara mikewa ahankali ta isa bakin gadon ta zauna, sosai kanta ke juya mata, jira take kawai safiya tayi tafice ta gudu, dan ko a mafarki bata fatan ta kara ganin fuskar da tagani... Muhammad kuwa ko kadan bai rumtsa ba, dan gaba daya ya nima baccin ya rasa, tunani sosai ya shigayi, meyesata firgita dataga uncle abubakar?? Shidai yanda uncle abu yafada musu, tun tana karama babansu yarabu da mamanta, kuma bawai sun sake haduwa da babansu bane balle yace kila taga kamane yasa ta firgita. And kodama tagani, why woud she acted that way?? does that mean she's not happy to meet her relatives?? or is there something deep uncle abu is not telling them?? idan kuwa bincike ya tabbatar mishi da kanwar shi ce ita, toh ba abunda zai hana shi dauko ta su dawo Abuja tare su zauna mummy, dan tun da yaganta sosai yakejin ta aranshi, kuma tun ma kafin akai ga bincike yaga fuskar babansu sosai a fuskar ta, even the way she's walking majestically, exactly like their father. yasan ana kama, but This is so obvious.... sai wajan 4:30 Sadeeq ya iya mikewa ahankali, har zai shiga bathroom, sai kuma ya dawo ya dauki phone dinshi, dan yaga wa yakirashi.. gaban shi ne yai mugun fadi ganin miss call din noor. nan da nan yashiga kiran wayan, har ya tsinke ba'a dauka ba, kara kira yayi, har ya kusa tsinkewa aka dauka.. anankali ya nima waje ya zauna kafin yakira sunan ta ahankali... "NOOR" kukan da yaji ta fashe mishi da shi yasa ya mike da sauri.. " what's wrong noor?? me yasameki??" bata dai cemishi komai ba kuma bata fasa kukan ba... Sadeeq da ya rasa me ke mishi dadi aduniya ba yace.. "talk to me please wifeyy... you want my heart to bust??" muryar ta adishe tace " come and take me away from this house please... I.. don't ever want to see him again..." da wani matsanancin kuka mai cin rai takarasa maganar.. Sadeeq yace "whoo?? Nabeel??" dan Sadeeq ba Wanda yakawo at that moment sai nabeel din.. damsel da ta rike kirjin ta da dayan hannun tace "I saw SUFYAAN he came to this house..i don't know his intentions towards me Now, because he pretended like we have never met before... I CAN'T ANYMORE PLEASE.. I..." yanke ta Sadeeq yayi tare da cewa " don't go anywhere please babe.. I'm coming back very early tomorrow morning to take you away.. far far away.. did you hear me noor??" tari ya dinga ji tanayi kamar zata amayo hanjin cikin ta.. Sadeeq da ji yake kamar yai tsuntsuwa yaganshi agabanta.. muryar shi da har yakaraya yafara yafara magana " don't do this to me please noor.. Please I'm begging you.. this is not what you promised me.. don't let anything happens to you pleassss... please noorrr" jin shiru yasa yasa ya dinga kiranta. but no response.. yanke call din yayi yashiga kiran al'amin.. al'amin yana bacci yaji wayan shi na ringing.. dan baya sa waya a silent saboda emergency.. bude ido yayi sannan ya mike yakai hannun shi kan wayan, ganin Sadeeq ne ke kiran shi yasa ya bude idanuwanshi kafin ya dauki wayan, yanayin yadda yaji Sadeeq din yai mishi magana akan damsel ne yasa yai sauri ya mike tare da zura jallabiya yana kiran khadija ,tana bude ido yace "Noor" a rikice itama ta Mike har ta riga shi fita. suna shiga suka ganta kwance.. kamar bata nunfashi, sai jini da duc yabata mata dogon orange rigan da ke jikinta.. ihun da khadija ta kwala ne yasa Sadeeq sake wayan shi akasa...

....drip ne a hannun ta, khadija kuma na zaune kusa da ita taci kuka har ta gaji.. kuma har yanzu damsel bata bude ido ba.. baqin dogon rigan da kdadija tasamata yakara haskakata sosai, sai dankwali data daura mata. al'amin kuma yana zaune a office dinshi bayan yagama ba nurse instructions din alluran da zasu ma damsel. tana fita kuma call din uncle abubakar yashigo, yana dauka basu ko gaisa ba yace " ameenu wani magana ne haka nakeji wai anyi mutuwa a gidanka??" al'amin yace "mutuwa kuma uncle abu??" Muhammad dai yana gefen uncle abu yana sauraron su, dan tunda suka shigo gidan sarah tafada musu aunty ta mutu sunkai ta asibi yaji komai na jikin shi ya tsaya. uncle abu kuwa yana gama jin me al'amin kecewa yaji hankalinshi yadan kwanta kadan tare da cewa gamu nan isowa asibitin yanzu.. yana hanging call din ya juya ya kalli Muhammad dayadafe kan shi dake mugun sara mishi a jikin bango yace "yi sauri ka shiga ciki kace ma yarinyar tabaka keyn motar hadiza kafito mutafi".. Muhammad yai saurin juyowa yana kallon kawun nashi kafi kuma ya shige cikin gidan da sauri.. Sarah na Palo tana goge goge jikin ta itama duc ya mutu, dan zaman da damsel tayi agidan har Sun saba. Muhammad ya kalleta so daya kafin ya kauda kai yace "give me your aunty's car key" Sarah ta juyo ta Kalle shi ahankali sannan ta ajiye towel din hannunta tai hanyar steps. ba'a dau lokaci ba ta sauko ta mika mishi keyn. Muhammad yana fitowa yaga har uncle abu yaje wajan motan ya tsaya. bude mishi yayi ya shiga sannan shima yazagaya da sauri yashiga ya tada motar Suka fita daga gidan. Suna daukan hanya ya tambayeshi ko wani asibi zasu, uncle Abu yace " asibitin da aminu yake aiki." Muhammad bai kara cewa komai yacigaba da tuki, har Sun kusa yaji wayan shi na vibrating a aljihu, cirowa yayi yaga bakon number, yana dauka suka fara gaisawa yaso ya dago muryar.. Nabeel yace " it's nabeel, i got your contact from al'amin jiya." Muhammad yace ohh, that's great, sorry bangane muryar bane at first. Nabeel yace no P, kana wannan hotel din da ka fada mun ne? Muhammad yace "nahh muna ma hanyar zuwa asibiti ne,.." nabeel da sauri yace " hope no problem??" Muhammad da yarasa me zaice,.. kallon uncle dinshi yayi da fefen ido, sannan yace "yeah, my sister is sick, so we need to be there." nabeel yace subhanallahi, dama you have a sister a nan? wani asibiti ne? Muhammad yafada mishi nan inda al'amin yake. nan sukai ending call din inda nabeel yace mishi, shima gashinan zuwa..
... da isar su, wuraren 11:30 am direct suka wuce office din al'amin.. yadawo kenan daga dakin da akayi admitting din damsel, kuma har lokacin bata tashi ba. suna waya da Sadeeq sai ga shigowar su Muhammad din, al'amin na ganin su yace ma Sadeeq zai kara kiran shi sannan ya yanke call din. mikewa yayi tare da gaishe da uncle abu, yana nuna musu kujeran dake office din, duc suka zauna. Muhammad dai ba bakin magana, dan tunda suka gaisa da al'amin yanima waje ya zauna baisake cewa komai ba. Uncle abu yafara magana "wai menene matsalar aminu?" al'amin yadan yi Jim kadan kafin yafara magana " test result din ya nuna tana da heart attack, so jiya da tsakan dare yatashi mata, but Alhamdulillah I think with the help of medication din ake ta bata tun jiya, she will be fine in sha Allah." Muhammad dai bin al'amin yake da kallo. kafin ahankali yabude baki yace " where you able to speak to her jiya da muka bar gidan?" al'amin ya sauke ajiyan zuciya, yafin yace "NO, amma fa for all indications inaga fa kamar andace." uncle Abu yace "how?" al'amin yace dazu muka gama waya da Sadeeq din, cemishi tayi taga babanta jiya,.. Muhammad ya dinga kallon su duka kafin ya Kalli al'amin yace "but she only meet him since she was young, how comes she remembered his face??" al'amin da shima tunanin shi kenan, yace "exactly wht I told Sadeeq, but he keeps on saying I won't understand.." uncle abu kuwa tunda Muhammad da al'amin suka fara magana, baice komai ba, kanshi akasa, sai hawaye da ya taru mishi a fuska.. lallai yarinyar da suka gani jiya yar SUFYAAN ce,.. ahankali ya dago kanshi, idon shi yai ja kamar garwashi, ya Kalli al'amin wanda dama jiran shi suke yace wani abu.. " kakiramun sadeeq din yanzu, I want to speak to him now." nan al'amin yashiga kiran Sadeeq har sau biyu, amma not reachable. yana kallon kawun nashi yace "muyi hakuri mujira dawowan nashi, in sha Allahu." uncle abu bai iya cewa komai ba ya mike sannan ya Kalli al'amin din yace " can we see her" al'amin yace "sure" tare da mikewa kafin shima Muhammad ya mike suka fita... khadija na jingine a akan dagon da damsel take. har lokacin kuma idon ta a rufe, sai dan nunfashin ta dake fita ahankali... bayan allurorin da al'amin yasa aka mata.. tana ganin shigowar su ta mike ahankali da dan murmushinta tafara gaishe da uncle abu, kafin Muhammad yakaroso shima suka gaisa. Uncle abu yakaraso har inda Damsel take yarinka kallonta ko kifta ido babu.. Muhammad ma haka. juyowa yayi ya Kalli al'amin sannan yace "ameenu kodai inyi mana making arrangement ne mukai ta India?? akwai wani likita da nasani, ta fannin wannan ciwon kawai" al'amin yai dan jim... kafin yace "mudan jira ko nan da gobe ne muga farfadowanta tukunna" inda khadija ke zaune da, Muhammad yaje yaje ya zauna. al'amin ya Kalli khadija kafin ya ciro mukullin motar a aljihu yabata. akan taje gida tai wanka sai ta dan huta kafin takawo. dakanan kuma ta ma su uncle abu abinci.. karba tayi tamusu sallama sannan tafita... karfe hudu dai dai lokacin khadija har ta dawo abincin da takawo ma ba Wanda ya iya ci, Kuma har lokacin damsel bata farka ba. shigowar nabeel ne yadawo da uncle abu daga cikin duniyan tunani. sundai gaisa ya tambayeshi ya mai jiki sannan ya juyo dan su gaisa da Muhammad, ganin hannun shi rike da na damsel ne yasa nabeel mutuwar tsaye,.. baigama farfadowa ba kuwa, sai ga shigowar al'amin Sadeeq na biye da shi abaya...

...uncle abu kuwa ganin Baba na yobe ke kiran shi, rumtse idon shi yayi kadan kafin ya Kalli damsel, idon ta a lumshe yake kamar ta koma bacci. mikewa yayi yai hanyar waje tare da amsa call din. Sunkai minti kusan goma akan waya tare da shi kafin suka yanke call din. yana fita kuwa Sadeeq ya Kalli al'amin tare da cewa "when you discharging her?" al'amin yakara kallonta kadan kafin yace "I think we can all go home, I mean she's ok now sauran medication din za'a karasa a gida." Sadeeq yace "OK toh that's fine, how about the bill? Where am I paying?" al'amin ya kalleshi da kyau kafin yace "are you for real?" sai kuma ya girgiza kai sannan ya Kalli khadija yamata alama da ta shirya damsel suwuce. Sadeeq yashafa kan shi yana murmushi sannan ya juyo direction din da nabeel yake yace "friend.." nabeel da duc kunya yagama hargitsa shi, murmushin karfin hali kawai yayi, without looking at his face yace "welcome back bro.." zaiyi magana aka bude kofar aka shigo. uncle abu ne yashigo, ganin har khadija tasama damsel hijabi yasa yace " anyi sallamah ne?" al'amin dake danne danne awayan shi yadago kai" a uncle abu, naga jikin nata is normal yanzu" uncle abu yace toh masha Allah. Zaro ATM Card dinshi yayi a wallet yana kallon Muhammad da duc ya tattara attention dinshi ya maida kan kanwar nashi,

Please Login or Register in order to submit comment