Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana gama shinfida mata ta matso ta mika mata hijabin tare da murmushi karara a fuskar ta. karba damsel tayi itama da dan guntun murmushin, fita yasmeen tayi itakuma ta mike tasa hijabin ta tada sallah. rama sallolinta tayi sannan ta sallame. Deena na kallon ta, tana tunani kirikiri a zuciyan ta, ta mike kenan ta cire hijabin ta linke. matsowa kusa da gadon a hankali zata zauna, Deena tace zo ki zauna kusa dani. Matsowa kusa da ita tayi a hankali tazaunata gefenta. Deena ta dauko abincin ta ajiye saman cinyanta, kallon jollof rice da kazan tayi sannan ahankali tace bana jin yunwa. Deena ta dauke abincin ta ajiye a gefe, matso wa tayi dab da ita sannan tace daga ina kika fito? Shiru ta dan yi sannan Ahankali tabude bakinta...Salma..✍️14
Iyaye na sun rasu... nazo ina zama awajan uncle dina ne, shine kullun yake shigo mun daki yana knwana dani. Kuma yace zai kashe idan nafada, guduna na hudu kenan, duc inda na gudu Kuwa sai ya bincikoni. tana fadin haka ta sauke kanta kasa, dan taji mamakin karyar da ta gillah nacewa alhaji tanimu kawun ta ne. Deena har cikin ranta taji wani kirin farin ciki yana ratsa ta, tasamu abunda take nima, meaning baza ta sha wahalar shawo kanta wajan kulla business mai karfi bakenan. amma a fuska sai ta nuna taji tausayin ta ba kadan ba. tana ta girgiza dan kan nan Nata kaman kadangare, sannan tace gaskia bai kyautaba, akwai mugayen mutane haka ashe? Allah dai ya tsine ma wannan kawu naki, ina ma laifin ya rinka kyautata miki tunda yana rabarki? ( kunji yan iskan bariki ko?) gaki kyakkawa baiwar Allah, halan ku yan Somalia ne? Damsel ta girgiza mata kai kawai, Chan takara cewa toh duc yadda akayi kin hada jini da larabawa, nan ma Damsel ta girgiza mata Kai. ahankali tace mu yan Nigeria ne,daga katsina muke. dan ko kadan bata son tafada gari daya inda tayi rayuwa a ciki sunan ma bataso ta tuna. Deena tace toh gaskia baiwar Allah kima Allah godiya dan ko hindiyawa baza su nuna miki kyau ba. chan tace to sunan ki fa? Murmushi yayi escaping lips dinta, "Damsel" tafada. Abunda yasa ta murmushi kuwa, Deena ce, dan yanayin maganar ta yana bata dariya saidai batayi dariyan ba, dan rabonta da daria tun kafin Mama tarasu. murmushi ma bakaramin abu kesata tayi ba, saidai tayi murmushin takaici. Deena tace mata asalin Sunan ki fa? Sunana kenan. Dan tayi ma Kanta alkawarin da sunan da mama tabata zata koma ga Allah, tana ganin gadon ta kenan da mama tabar mata, takuma dau aniyan ba mahalukin da zai kara jin sunan nan aduniya. Deena tace gaki kalan turawa, sunan ki ma haka. To batare da bata lokaci ba barinyi miki bayani. Kin ga nan da nakawoki, duc yanmata ne sa'o'in ki kuma duc taruwa muke mu rufawa juna asiri. namiji zaizo yabiya kudi sannan su gana, kedai ba yarinya bace kin gane me nake nufi, ducda dai dayawan wasu muna fukan suna kiranshi da karuwanci. kuma bamu yafe ba, tunda sana'ace kuma ana Biyanmu, bamuje mun roka an wulakanta mu ba. Ko ba haka ba? Damsel nan da nan tace hakane. Yauwa yar gari Deena tace, toh yanzu yadda naga kina da kyau ga iliminki, ga kamala,toh kudi zamu tara ba nawasa ba. Kuma zan rinka tara miki har sai lokacin da kike bukata, zankuma rike ki tsakani na da Allah kaman ni na tsuguna na haifeki. kinji ? Damsel tace toh. Deena ta matso ta rungumeta.warin sigari duc yadame Damsel, muryar Deena taji daga sama, ki rinka kirana "Deena" damsel ta girgiza mata kai alaman taji. sannan ta kara da cewa shikuma la'anannen kawun naki zai san inda zai rika diban nabati. toh tundaga ranan shakuwa mai karfi ya kullu tsakanin Deena da damsel. Anqaya ta mata dakin ta ba kadan ba abincinta ma daban ake mata. kuma gashi ko Kadan bataso taga bacin ranta, dan tana tsoron kar ta rasata. haka yaruwa yaci gaba Damsel ba abunda ta iya a duniya ko rike tsintsiya bata iyaba dan komai yi mata akeyi. Iya handling namiji akan gado kawai ta iya, kuma ta kware banawasaba. Sannan bata shiga harkar kowa a wajan. wayama bata rikewa dan aganinta baida anfani awajanta, bata da wani dan uwa ko masoyi a duniya. bata yarda soyayya yana existing a duniya ba. Kawai abunda tasani ta ta gamsar da namiji a biyata. Kamar yadda Deena tafada mata sana'a ce. (toh Allah ka karemu da mutane kirin Deena. Ameen ya Allah)
Salma..15

the meeting was successful, dan sunyi kokari banawasa ba, yadda zasu fito da wani sanfari na sabuwar mota, me anfani da mai kalilan, saboda yadda tsadar mai ta kasance yanzu akasa, ahaka meeting din yatashi akan bayan sati biyu Sadeeq zai je Spain din dan sufara aiki gadan gadan, but for now zasucigaba da research sosai... bayan sun fito daga daga dakin su na meeting, yaraka bakin nashi har mota inda za'a koma dasu masaukin su, washagari su koma kasar su. yana dawowa ya zarce ofishin shi inda yafara kananan ayyukan shi. nan yaji yafara jin yunwa. anan ya dauki Wayan shi yayi dialing numbern wani daga cikin ma'aikanta shi akawo mishi coffee. ya ajiye Kenan, call din hafsat yashigo, da kamar bazai dauka ba, sai kuma ya dauka tare da cewa salaam.. lil sis, how are you you? Hafsat da wani sanyi ya ratsa jikin ta, nan da nan ta Mike daka kwanciyan da takeyi. I'm Fine ya Sadeeq, sai Kuma ta rikice mishi kamar zata kuka, I've been calling and calling but you're not responding, whyyy? Sadeeq rasa abunda zaice mata yayi, dan shi har ga Allah bai taba jin sonta a zuciyar shi ba hasalima abunda yasa yake biye mata kawai dan tana da hankali ne yarinyar ba kadan ba. Kwankwasa kofar akayi sannan yabada izinin shigowa. Coffee aka shigo mishi dashi, godiya yayi ma wanda yakawo mishi sannan yabashi izinin fita. dawowa kan hafsat yayi yace lil sis wlh ayyuka ne suka cushe mun, kiyi hakuri idan nasamu chance zanso kanon ai, sai muyi magana kinji? toh kawai tace mishi sannan sukayi sallama, ajiye wayan yayi sannan a hankali yadauki coffeen yafara sipping. Damsel ce tafado mishi a rai, yana tunanin yadda zai fara, kokuma ya nima shawaran nabeel ne? Shidai yasan kawai he just want to help her and nothing more. idan yayi kokari yaga yayi convincing dinta, toh sai ya maida ta koma ina tafito tare da bata kudi mai yawa tayi koma me nene amma banda prostitution. damm fada sannan ya rike kanshi , is he even making sense to what he's thinking?? Wayar shi ya dauka har zaiyi dialing numbern nabeel, sai kuma ya fasa. duba wristwatch din hannun shi yayi yaga har shabiyu da rabi ya kusa, mikewa yayi don yayi haramar barin office din, yagama tattara komai sannan ya fito rike da briefcase dinshi a hannu. sallama yamusu sannan yafita ya shiga motar shi ya tada. tunani yakeyi ko yafara zuwa badagry, kokuma yakoma gida ya huta, da yamma sai ya tafi. dahaka yayi deciding wuce wa gida kawai akan anjima ya dau hanyar badagry. da isar sa gida yayi parking motar shi sannan yafito yayi hanyar masallaci. ana idarwa yafito ya karasa gidanshi, Mai gadi ne yake fada mishi nabeel bai dade da wucewa ba, yazata yadawo ne. alright kawai yace mishi, har ya wuce saikuma yakara dawowa ya cire dubu biyu a aljihu yabashi akan ya dan gangara kasan su yasiyo mishi watermelon. shikuna yayi shigewar shi gida, da shigar shi yafada bandaki ya sakar ma kanshi shower, yagama kenan yafito, ya shirya cikin three quarter baki da white T-shirt, sannan ya feshe jikin shi da turaruka. wayarshi da ke palo yaji tana yana ringing, ahankali yake takowa har kusa da inda wayan yake, "my everything" sunan da yasa ma me kiran knan. Har ya katse bai dauka ka ba. Da murmushi a fuskar shi yayi dialing number sannan ya nima waje ya zauna. Ringing daya aka dauka, yakara fadada Fara'ar shi, afuwan ummi na, chan Wanda yakira da ummi tace Aa dadai kawai danakira ka dauka, ni insamu ladan. Yana murmushin nan nashi yace "I MISS YOU MOM" kiyi hakuri,aiyuka ne sukamun yawa wlh. chan tace haka babanku yace mun jiya, nidai problem dina da kai, sai animeka dib arasa, yanzukuma idan kayi aure ai kuma shikenan. zaiyi magana saiga nabeel nan yashigo. chan yace haba dai ummi... Fusge wayar nabeel yayi yasa a speaker, ummi ashe dake yake waya, inawuni. Ummi tace nabeel, dama kuna tare, nabeel yace shigowa na knan ummi. Toh ya kuke? yakuma zaman gwauronci, tunda kai da shi ba me ma wani fada acikin ku. Nabeel ya susa keya yace kar kidamu, soon in sha Allah ummi na. Sadeeq dai yakafa mishi ido. ahaka har sukayi sallama ya kashe wayan. Nabeel ya karasa kitchen ya dauko bottle water sannan yafito, chan kan two sitter ya zauna sannan yace, dude about last night, bai bari nabeel yace komai ba yace, no I don't want to hear it please. tashi yayi ta dalilin knocking din da yaji anayi, Joseph ne tsaye da ledan watermelon a hannu, karba yayi sannan yamishi godiya ya maida kofar ya kulle. Wucewa kitchen yayi dan bare watermelon din. bayan yagama yafito da shi cike da plate sai fork biyu a ciki tare da karamin saucer. akan centre table ya ajiye, nabeel ya sauko ya diba a cikin karamin plate din tare da cewa kaman kasan banci komai ba wlh since morning. Sadeeq baice komai ya dauki watermelon dinshi yafara sha. chan ya juwo ya Kalli nabeel, da kaman bazai ce komai ba, sai kuma yace.. I need your advice. Nabeel ya mike daga kwancen dayakeyi, wht about Bro? ya tambayeshi. chan kuma Sadeeq ko tunanin me yayi kawai sai yace maybe later.. Alright kawai nabeel yace mishi. Suna zaune ahaka har 3. wayan nabeel kuwa ankira yafi so hamsin daga karshe ma kashe wayar yayi gabadawa shidai Sadeeq bai ce komai ba. karfe uku ya gota chan nabeel ya Mike da sauri tunawa da yayi sunyi da wani abokinshi zasu hadu karfe uku akan wani tafiya da zasuyi next week, da sauri ya dauki car key din shi yace ma Sadeeq zai je gidansu yaseer. Ko zaibishi ne, Sadeeq ma ya mike yace nop nima akwai inda zanje daganan ya shige bedroom dan yafara shirin zuwa badagry...




Sadeeq yagama shirin shi kenan yafito, Jeans da navy blue T-shirt ne ajikin shi sai pcap baki dayasa. ya dauki makullin motar shi sannnan yakashe TVn yafito ya kulle gidan shi. yana fito wa ya kira Joseph, da sauri yazo yace oga u wan commot? Yeah, and please I'm expecting my laundry today, if the guy comes, get the bag from him and keep it for. Joseph yace yes oga. 5k ya kirga yabashi sannan ya fara bude motar shi zai shiga, Joseph yabiyo shi yace make I give the man? Sadeeq yace mishi no, it's for you. Joseph ya washe baki yace thank you very much oga, sannan yawuce ya bude mishi gate. yana fita ya tsada a dadai masallacin da ke kusa da su yayi sallahn la'asar. ana idar wa ya fito ya shiga motar shi ya dau hanyar badagry. ahankali yake tukin tare da bin wakar Jacquees ft lil baby,"your peace". karfe biyar da rabi dadai ya shugo badagry, da isar shi Dollars and pounds aka bude mishi gate, yau kam yakare ma wajan kallo sosai. tana tsaye a jikin windown dakin ta tana kallon shi, duc da bata ganin fuskar shi saboda hulan da yasa, but he looks familiar to her. he looks so handsome and gentle, even the way he walks. Ahankali tabar jikin windown takoma bakin gado ta zauna. Hopping and praying no one will come for her today. Knocking din da taji ne yasa ta rumtse idon ta, ahankali ta tashi ta isa bakin kofar, tana budewa ta bar wajan. Yana shigowa kamshin turaren shi ya mata maraba. ahankali ya cire hulan dake kanshi. Juyowa tayi suka hada ido. She looked soo disturbed. matsowa tayi ta Kai soft palms dinta fuskar shi, sannan takai dayan hannun zata daga T-shirt din shi. baiyi kokarin dakatar da itaba har takai hannun ta cikin jikin shi. and he can feel how her temperature in high, jikin ta yayi zafi. kara matso ta yayi sannan ya cire hannunta a cikin rigan shi, ya sauke dayan ma da ta dora a fuskar shi. this is not what I'm here for again, Noor. haushi ne yakata, amma ko kadan bata nuna a fuskar ta ba. My name is Damsel not noor. what ever, this is now your new name. ahankali ta juya ta bar gaban shi, zama tayi bakin gado sannan tayi crossing kafarta. So, what are your intentions about me? Da jin haka ya matso ya zauna dab da ita, noor stop making me repeating the same thing, over and over.. I want to help you return to your family and then find something good doing but not this. I will pay any amount. Please noor. ahankali ta juyo suka hada ido, cikin ido suke kallon juna, kara matsowa tayi dab da shi ta kai bakin ta daidai kunnen shi. Sadeeq da har murmushi yayi escaping lips dinshi dan yaga kaman yafara samun nasara. Bude bakin ta tayi a kunnenshi, speaking to his ears softly... Now listen to me "mister" stay... away .....from me, far far awayyy from me. And my name is not noor, my is Damsel.. Now get up, and then get...out. tana fadin haka ta mike ta ta koma jikin windown dakin, tana fuskantar waje. sai tsoro fal dake cike a zuciyar ta. To wannan da wani nufin yazo mata? what is he planning on doing do her, since he refused to have sex with her. Meaning there's something more dangerous, she's so scared... he's lying to her by saying he want to help her. men are nothing but bunch of deceivers, they are just created to take advantage and go... there's no way she can ever believe a man. Never in her life. karar rufe kofar ne yadawo da ita cikin duniyan tunanin da tashiga. ahankali taji sanyi cikin zuciyar ta, koba komai ta kona mishi rai... tare da fatan ya tafi kenan bazai kara dawowaba...


da yamma damsel na downstairs sun hadu a dining, tana jiran madarar da tasa akawo mata. Yasmeen da sauran suna cin abinci, hanifa tacigaba da cewa toh ke yanzu yasmeen kina zamanki ba abunda da kika rasa, zaki wani dauko ma kanki maganar aure? Kije kiyi me agidan miji? Haka Kurin ka zauna wani yana controlling dinka, gaskia kisake shawara. Wanda aka kira da yasmeen tayi murmushi kawai, sannan tace to banda abunku, miye ribar bariki? yanzu ko wani baima mana fada ba ai yakamata mu muyi ma kanmu fada, tsufa fa mukeyi kullun. Kuma koma yayane zamuso muma muga kudan jinin mu. dan haka gaskia ina kira garemu, kafin lokaci ya kure mana, to musan me muke ciki. Yau inasu nusaiba da xeexee? Nusaiba har ta bar duniya bata koma ga Allah ba xeexee kuya inace mu muke contributing kudi muke aika mata na magani? Wani kudi ne bata yi ba? Kasashen da taje har yau acikinmu ba wanda ya taka, to yau munga Kirin rayuwar da ta shiga, ga aya nan muna gani akanta. Dan haka gaskia idan har alhaji muntari da gaske yakeyi, dan shima yace wlh yakoma ga Allah kodan tsoron kar abunda yakeyi yafada ma yaranshi. toh wlh zan nima hanyata. Kundai ji. Acikin su ba Wanda yabi ta kanta sai mardee, cewa tayi wlh yasmeen jikina duc yayi Sanyi, tabbas abunda kika fada gaskia ne, ni Dama tuntuni nakeson komawa chan garin mu innima gafarar iyayena inkuma koma islamiyya daganan idan Allah yafitomun da miji inyi aure na. duc abubawan da suke fada kaff,Damsel na jinsu kuma sosai tasan gaskia yasmeen takefada, it's high time ace tabar "dollar and pounds. Itama she wants to start living on her own, without no one controlling her. saidai ko kusa bata jin zata yi wani abu wai shi aure. Never in her life to be with a man. zadai ta karba kudinta, taje Chan wani gari takama gida, dakanan da san kirin sana'an da zata farayi. da wannan tunanin da dau kofin madarar ta ta kai baki... ahaka hirar ya watse, sai ita daya takk Suka bari a wajan. takai minti goma a zaune, sannan ta mike a hankali ta haura sama ta shiga dakinta...
Kwana hudu kenan da wannan shawarar da Damsel tayi akan barin dollars and pounds. bayan kuma tasamu Deena da maganar tanason abata kudadenta, Deena kuma batace mata komai ba. Takara komawa the next day dakanan Deena tace mata kar ta kara zuwa mata da wannan batun. tana tsaye a jikin windown dakinta, Sadeeq ne yafado mata arai, ganin tun daga ranar da ta Kore shi har yau bai dawoba, meaning ya Hakura. ahankali Chan kasan lebenta tace "good for him,. Bude kofar da akayi yasa ta juyo da sauri,... Deena ce tashigo..gefen gado ta nima ta zauna, tunda ta Damsel ta kalleta so daya ta dauke fuskar ta. Deena da duc abun duniya ya isheta tace meyesa jiya da yau kikaki attending ma wa'inda ke zuwa wajenki? Damsel bata kula ta ba, Deena tagane tayi fushi kenan, dan idan kanason kagane she's angry, toh duc maganar duniyan nan idan zakayi toh baza ta kula ka ba. tashi Deena tayi takaraso inda take dan tafara jin haushi itama, juyo da ita tayi sannan tace yau nice abun wulakanci awajanki? Damsel da ranta yagama baci tace, I want my money let me get the hell out of here. dauketa da mari Deena tayi, abunka da hasken fata, nan da nan wajan yayi ja. Damsel na kallonta amma batace komai ba. Deena masifa takeyi ta inda take shiga ba nan take fita ba. Na daukoki ko inda zakije bakidashi, na miki gatan ba wadda namata anan, abincin ki, tufafinki, mayukan da kike shafawa daban ne da na kowa anan, duc wannan bai isheki ba? Me kikeso? Toh inhar kina niman zaman lafiya lafiya dani, ko kada wasa karki kara zuwa mun da wannan maganar banzan, kuma ki shirya, nan da anjima alhaji Zaidawo, ki wulakantashi irin na jiya kigani. tana fadin haka ta fita ko Rufe kofar dakin bata yiba. yau ran Damsel yakai kololuwa wajan baci kuma tananan a jikin windown bata motsa ba.

...... Sadeeq kuwa tun ranan da yadawo daga wajan Damsel ya tattara al'amarinta ya ajiye a gefe, ducda wani sashen na jikin shi is telling him to go back for d last time, amma ko kadan bayason kawo wannan tunanin.. yau kasance weekend kuma tafiyar shi Spain saura one week, tashi yayi da bala'in fargaba, dan mafarki yayi yaga Damsel cikin wani mawuyacin hali. tunani ya dunga yi kodan saboda yasa damuwarta ne a cikin ranshi yasa yayi wannan mugun mafarkin akanta? da haka ya kauda wannan tunanin, yananan har sha biyu a dakin shi bai fito ba, kuma ba bacci yakeyi ba. Knocking din da yaji ne yasashi mikewa da kyar, ahankali yatashi ya zura jallabiyanshi sannan ya fita. Cleaner dinshi ne dayake zuwa every Saturday yana gyara mishi gida. Sun gaisa sannan yabashi hanya ya shigo. ba inda bai gyara mishi a gidan ba sannan yamishi sallama ya wuce. tea kawai ya hada yasha sannan yakoma dakinshi. Masallaci kawai yake fita yaje inyadawo kuma ya shige dakin shi, dan yau ko zaman palon bayajinyi, he's moody all through. ahaka har 4:30 yayi. Wayan da ke kusa da shi ne yafara ringing, Gee aka rubuta a jikin wayan, yana dauka ya kai kunni. Nabeel yace mishi wani kirin wulakanci ne haka Sadeeq, munyi da kai 4 daidai Kana gidana, shine zaka wani ajiyeni kamar banda abunyi. Ahankali yace m sorry, can we please go tomor, dip nabeel ya ajiye wayanshi, kallalon wayan Sadeeq ya dinga yi kafin ya ajiye yakoma ya kwanta.
.... Damsel na tsaye a windown dakinta kuma har lokacin kofar dakinta a bude yake tana idar sallah zata koma jikin windown ta tsaya. masu mata aiki ne suka shigo, tunda ta juya ta kallesu bata Kara juyo wa ba, dayar ce tace Deena ta aiko su sukara gyara mata dakin dan alhaji yana hanya. Nan da karfe biyar. Batace musu komai ba. gyara dakin sukayi tass sannan suka fita. Bayan sunfita da minti goma sai gashigowar alhaji, tanan a jikin windown har lokacin, alhaji zama yayi a gefen gadon tare da cire malunmalun dinshi,cikin nan a gaba kamar kwarya , bata ko juyoba. Jin hannunshi a jikinta ne yasa ta juyo da sauri, duka karfinta gaba daya tasa ta tureshi. saura kadan yafadi a jikin gado. baiko bi takan malunmalun dinshi ba ya bude kofar yafita, kwala ma Deena kira ya dunga yi tun daga sama har yasauko kasa. tana kirga dalolin dayabata taji muryar shi, da sauri ta Mike tanacewa alhaji lafiya? fiske kudinshi yayi ya bi kofa ya fita. Deena da ranta yakai kololuwa wajan baci, nan da nan ta kira securities biyu awaje, kudi ta kirga tabasu sannan tace su hau sama suma Damsel dukan tsiya.
Sadeeq da har bacci yafara daukan shi, kaman an tsikareshi ya mike dan mafarkin Damsel yakarayi. yafi minti 5 kan shi a rike, duba wayar shi yayi yaga shida dadai, ajiye wayar yayi sannan ya mike ya dau jallabiyar shi ya zuwa. Daukan makullin motar shi yayi yafito, yanashiga motar mai gadi ya bude mishi gate, yana fitowa ya hau main road. dakanan kuma yakama hanyar badagry....
Salma..✍️19
securities kuwa suna karban kudin, nan da nan suka haura sama. Dashigan su dakin suka hauta da duka ba kadanba, ihu takeyi kaman zata fasa dakin. Saida suka mata dukan tsiya dan ko motsin kirki bata iyayi, sannan suka fito daga dakin... Sadeeq yana isowa yayi hanyar wajan biyan kudin, Deena tana ganin shi tace "yau bazata ga kowa ba" rasa abun cewa yayi yana dai tsaye, securities din da yagani ne idon su ba alaman imani sun sauko, batatare da sun lura dashi ba suka nufi Deena. aiki yacika suka cemata, suka kara da cewa munyi aikin kudin mu ba kadan ba, dan ko motsi ma bata yi. Sadeeq da yaji gaban shi yayi mugun faduwa, baisan sadda yayi hanyar steps din ba, kwakwalwar shi na juya mishi, ko kadan bai kawo dukanta sukayi ba, he thought of something else, and he felt so bitter in his heart.

Please Login or Register in order to submit comment