Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah yama dan su na fari muttaseem rasuwa yaga Sun rage yawan suje nan suje Chan. Sai wata Rana yana gida ne suna tare a Palo yaga ankirata waya, tana duba wayan yaga ta mike da sauri tayi hanya daki. ta dau mintocinta sannan tafito tana mishi kame kame, daga karshe tace asma'u ce zata aiko a dauki su basma wai zata kaisu children's world tare da yaranta. Nan ne yamata yamata hauka banawasa ba akan koda wasa yaranshi suka kara fita bada izinin shi ba toh abakin auren ta. toh dahaka ne yasamu saukin fitar yaran. Sufyaan yana tuna wannan, baisan lokacin da ya furta innalillahi wa'iina ilaihi raji'un tare da wasu zafafan hawaye da ke gangaro mishi. baba na shagamu da kan shi duc yagama kullewa da wannan al'ajabi. Juyowa yayi ya kalli nura da daman jira nuran yakeyi. tun kafin baba na shagamu yayi magaana nura ya mike da zafin nama ya isa wajan haj. maryam kamar zai tsunka mata mari. Yan uwan shi sukai saurin rike shi suka zaunar da shi. Yana huci ya kalli Baba na shagamu yace... " Baba wannan makiran da kake gani anan. ya nuna haj.. Maryam da yatsa. yacigaba da Cena aljana ce a suffar mutum, kafin dai infara cewa komai, Allah ya isa tsakani na da ke. Kin cuceni, cin cuta mun yan yara na kuma Allah ya isa. Nan ya cigaba da magana.... kamar yadda tace muku ni tsohon saurayinta ne, toh haka yake. Munyi soyayya da maryam mai tsanani, rana daya kwatsam ta sameni tana kuka akan iyayenta zasu mata auren dole. ga yan uwa na sheda, har ciwon zuciya saida nayi akan anrabani da Maryam, haka dai yan uwana suka dunga jinyata suna bani baki har Allah yakawo mun sauki. tun daga nan nacire ta araina na kuma dangana ma Allah komai. Ga yan uwana shed Shedu na ne duc ba wanda bata sani cikin su ba. Ta dalilinta har yau banyi aure ba. Bayan shekaru uku da rabuwar mu da maryam, ina wajan aiki na, dan lokacin nasamu babban aiki a abuja, saiga bakon number yakirani, mun gama gaisawa. Nan take shaida mun auren ta ya mutu kuma tanan a garin abujan, abunda bata boyemun ba kenan yayanta maza biyu. dakanan naji tausayinta har kudi ina tura mata, bayan wata daya da haka soyayyar mu ta dawo sabo. Nan na nuna mata inaso inturo magabata akan muyi aure. Daganan tafara mun hanya da karya kalakala, ban yi saurin fahimta ba saboda yanda so ya rufe mun ido. Ahaka har yan uwana suka gane, ga babbar yayata anan har gaba sai da na dauka da ita akan tamun fadan cewa Maryam dai ba aurena zata yi, kudi na Kawai takeso, ban kara bi takan kowa a familyn mu ba naga tunda ba Sonta sukeyiba, itakuma bata shirya muyi aure yanzuba, yasa kawai na biyema sharrin shaidan da Kuma nata, tunda abunda taketa nima na da shi kenan har muka samu yaya mata biyu bata hanyar aureba. kuma bantashi sanin tana da aure ba sai wata rana naje gidanta ina kofar gidan ina ta kira tana rejecting, wani mota ne naga yazo yayi horn mai gadi yabude mishi yashiga. bayan shigar shi da mintoci ne nafito na kwankwasa mai gadin yafito, mun gaisa sannan nake tambayar shi ko wanene wanda yashiga, cemun yayi mai gidan ne. Bansan sanda na hada zufa fa, nan nakara tambayar shi ko yaushe ne akayi auren, baki bude yace mun shekarar shi takwas kenan yana aiki a gidan kuma da aurenta. ai kodaye bari na inshigowa ma cemashi tayi ni wanta ne. ban ma tsaya nakara jin komai ba namishi Godiya nashiga motana na koma gida. Ban dade da shigowa gida ba takira ni, ina dauka tarinka mun karya akan wayar na Palo itakuma tasha magani tayi bacci kanta na ciwo, bacci ne ya dauke ta a
daki. Bantsaya watawata ba na mata zagin da tunda nake ban taba ma kowa kirin shi ba, kuma nacemata tabani yarana ko wallahi tayi regretting sani na da tayi aduniya. Toh tundaga ranan muka dunga samun matsala banawasa ba. Har kashe ni maryam ta turo ayi, Allah ne baiyi ba. Nan yafito da wayar shi inda yayi Playing maganar su ta karshe kafin tayi blocking dinshi. Bayan yagama kenan ya maida wayar shi aljihu. Salati kawai kakeji a palon, haj. Maryam kam ta zaune ne kawai awajan amma da zata ga bindiga da ta harbe Kanta atake. sautin kukan yayan ma kadai da takeji, ciwo ne azuciyanta. Ahankali sufyaan da kamar baya palon ya mike....

Sadeeq na isa wajan, ya karasa inda damsel take, riko hannun ta yayi ahankali zuwa palo, tare da cema ma nabeel da ya tsaya a wajan kamar gunki, dan ko inda yake ma bata kalla ba."ba alwala kace zakaje yi ba? Nabeel da kan shi yayi mugun daure wa ga wani bala'in shock din da yakamashi. kara dawowa palon yayi dan ya tabbatar ma idon shi, shi ba wai dan yaga mace gidan Sadeeq bane ya razana shi, duc da ba wai ya tabagani bane, shi kawai wacce yagani ne ya sa shi mutuwar tsaye, tare da millions of questions running through his mind. kallon ta yayi da kyau sannan a take yafada ma zuciyanshi ba ita bace, saidai mai kama da ita, barinma yadda yaga shigar mutunci ne jikinta ta. Sadeeq yana zaune kusa da ita, ita Kuma ta dan jingina kadan da kujera. Sadeeq yace "look nabeel, stop this nonsense please kasan dai ba jiran mu zasuyi a masallaci ba ko? Kofar fita nabeel ya nufa tare da cewa muje sai inyi kawai a mosque din, yana fadin haka ya fita. Sadeeq ya mike yadawo kusa da ita, ahankali tajuwo suka hada ido, "let me pray noor, i Will be back soon. batace mishi komai ba ya mike ya fita. suna idarwa suka fito. ba Wanda yace komai har suka isa gida.. shidai nabeel tafiya Kawai yakeki, amma da za'a bude kwakwalwar shi, toh gani za'ayi duc a kulle suke. He really doesn't want to believe what he saw. damsel agidan innocent Sadeeq dinshi. How comes?? Yasan abokinshi nada bala'in tausayi amma what??? idan kuwa ita din ce to lallai wayau zata ma abokinshi, da kuma Allah kadai yasan karyar da ta zabga mashi har ya amince ya kawo ta gidan shi. lallai zai ci ubanta kuwa idan yashiga gidan. badai abokinshi ba. Sadeeq yana lura da nabeel amma bai ce mishi komai ba, murmushi kawai yayi har suka shiga gidan. Nabeel yafara shiga.. ba kowa a palon, saiga ga shigowar Sadeeq din, ganin bai ganta a palo ba yasa yai hanyar dakin.. Nabeel dai yana tsaye ran shi duc yagama baci. ahankali yai sallama ya shiga, baiganta a dakin ba, zama yayi gefen gado for like 3minutes, kome yazo kanshi ohoo, da sauri ya mike yai hanyar bandakin, bata ciki a rikice yafito suka kusa cin karo da nabeel da hakurin shi ya riga ya kare, dan baisan karyar da take cigaba da da fada mishi a dakin ba. ganin shi a rikice yasa yadawo da baya, yana kallonshi. Sadeeq ba inda bai duba ba a gidan ba amma no signs of her.. nabeel dai na kallon ikon Allah, chan ya bude kofar palon ya fito "Joseph!! Da gudu ya fito dan baitaba jin ogan nashi haka ba, yana fitowa yace mishi "did you you see anyone go out of this gate?? Joseph da hankalinshi a tashe ya maimaita tambayar da sadeeq din yamishi. Ko dan shigan shi daki wani yashigo gidan ne baisaniba. dan idan zai je masallaci to bayasa lock a gate din har sai yashigo gida. a rikice yace mishi "noo oga, no be only you and oga nabeel dey for the house? I no see any body.. Nabeel dai hannunshi a nannade yana ganin ikon Allah, wato Joseph din ma baisan wata na gidan ba. Sadeeq da baida lokacin tambayoyi sai kawai ya juya ya shiga gidan
.. yana fitowa yai hanyar motar shi zai shiga.. Nan ne nabeel din yakasa hakuri ya biyoshi, rike murfin motar yayi yana kallon Sadeeq din da duc a birkice yake. " where do you think you're going? What has come over you Sadeeq?? Akan prostitute? nan ne Sadeeq yamishi wani Kallo trying to hold his anger yace, nabeel am not in the mood please, let me. yana fadin haka ya shige motar, nabeel dai yana rike da murfin motar har locakin, looking at his friend "akan prostitute?? Sadeeq yaga nabeel na niman bata mishi lokaci yafito daga cikin motar yana kallon shi "you don't know a thing... Sannan yayi hanyar gate din, Joseph yana tsaye ya bude mishi gate da sauri jikin shi na rawa.Sadeeq ya fita....


a chan yobe kuwa,
Sufyaan yana fita yayi hanyar part dinshi dasuke sauka idan sunzo, kowa yabishi da kallon tausayi, barin ma kanin shi, dan kirin labarin da ya fada mishi shekaranjiya ya firgitar da shi ba kadan ba. shiyasa ma ko kadan bai firgita da abun al'ajabin da ya afku a wajanba dan yasan ba komai bane, illah kamun Allah. Dan duc abunda kayi aduniyar nan, wala mai kyau ko akasin haka, toh lallai sai Allah ya nuna maka tun kuwa a duniya. Salati kawai ake yi a palon. Baba na yobe ne yayi kokarin gyaran murya, kowa ya natsu a palon, inda yayi jawabi mai tsayi Kuma me shiga zuciya, inda yama nura da haj. Maryam nasiha da kuma nuna rashin jin dadinshi game da abunda ya abku a tsakanin su, mussanman haj. Maryam, yanda take da auren ta. Yanzu taima yayanta adalci kenan? kuka ne ya subuce mata inda ta fara niman gafarar kowa a gurin musamman yayayenta uku Muhammad, hanifa da basma. nan Kuma tafara bayani inda ta nuna harda laifin sufyaan din, inda ta bayyana cewa baya wani bata kulawan da ya dace, idan ya tsallake kafar shi toh sai ta ganshi, ka niman mata, tayi fadan har ta gaji. baba na yobe dai yasan tabbas gaskia take fadi dan tasha kawo karar shi suna mishi fada amma a banza. tana magana ne tana kuka mai cin rai tare da nadama a zuciyanta. Nan yaran sukazo suka rungumeta suna kuka mai tsuma zuciya. Shi kan shi nura da yan uwan shi jikin su duc yayi sanyi... Ihun da sukaji a cikin gidan ne ya fito da kowa a palon, yarinya kanwar sufyaan din ne hannu a kai takasa magana sai nuna part din sufyaan din takeyi, dasauri har suna rige rigen shiga.... Akwance Suka ganshi kunfa Na fita abakinshi, da gudu dan shi Muhammad ya isa wajan ya tallabo shi hayawe na sauka a fuskar shi.. Yana kallon dan shi amma ba bakin magana, he really want to apologize for everything but he couldn't.. Muhammad na rike da uban nashi, kanin sufaan din ne yai saurin karasowa ya durkusa, ahankali ya kai hannun shi saman fuskar yakarasa rufewa. ranan dai yanda suka ga safe haka Suka ga dare. tuni har ankai sufyaan gidan shi na gaskia.. Bayan sadakan uku ne su nura sukai haraman koma wa gida, kuma sunsamu fahimtar juna tsakanin yaranshi da haj. Maryam. bakuma abunda ya chanza maganar auren saidai dagawa da akayi akan sai nan da wata daya... Shikuma kanin sufyaan mai suna abubakar, bayan kowa ya watse da kwana biyu ne yakara tara yan uwan shi aciki harda haj. Maryam ya labarta musu komai akan labarin da marigayi sufyaan yabashi akan matar da ya aura bada sanin kowa ba. Sai Kuma yar su daya da suka haifa. Saidai ba komai abubakar din yafada ba, dan bakin shi bazai iya furta wannan kazamin aikin da wan nashi yayi ba. Da haka dai taron ya watse akan shi abubakar din zai nemo ta duc inda take zakuma su riketa subata gatan da bata taba mafarkin samu ba....
Sadeeq na fitowa ya dinga bin street din da ido. baiga wulkawar kowa ba, haka ya dunka tafiya har ya iso kan titi, motoci kawai ke ta kaiwa da komowa. wani mut, Sadeeq ya karasa wurin mutumin da sauri, Allah Allah yakeki yagama kwatancen da yake ma wata a waya. Yana gamawa yabashi hannu suka gaisa. tambayar shi yayi ko yaga wata budurwa. mutumin yayi wani dan dogon nazari sannan yace mishi dazu yaga wata tana ta fafiya, and even try stopping her yamata magana amma bata kula shi ba. Sadeeq da duc yagama rikicewa baisan sadda ya rike hannun mutumin ba yace "please which direction did she follow?? " Guy din ya kara nuna mishi wani hanya a street din yace nan yaga tabi. "godiya banawasaba Sadeeq yamishi sannan ya bi hanyar da Guy din ya nuna mishi... tafiya Sadeeq ya dinga ci baima san inda yake jefa kafar shi ba. dan baitaba cin tafiya kirin haka ba. tunani yaketayi ko kawai yayi uber ne yaje badagry? " yasa hannu a aljihu kenan, yaji ba wayan, nan hankalin shi yakara mugun tashi, tunawa da yayi ya bar wayan a gida. hannun shi duka biyu yasa akai, wani kirin mugun sara da yaji kan namishi. Juyowan da tayi akan ya dau hanyar gida dan ya dauko motar shi. "ganin ta yayi tare da wani dan saurayi, fancy leda ne a hannun shi itakuma ta na biye da shi, da wannan tafiyan nata kamar batason yi. "Sadeeq da ji yayi kamar anmishi albishir da gidan aljanna. har jiri yafara ji, yana biye da su har ya isa inda suke. Basu ma Ankara da shi ba, mutun taji kawai charab ya rike mata hannu. "afirgice ta juwo dan dama a tsorace take. Nan shima saurayin ya juyo. Ganin kirin kallon da Sadeeq din yake mishi, ga kuma yadda damsel take fiki fiki da ido, dan itama ta tsorata da yanayin shi. Nan ne guy din yasan toh lallai suna da halaka, kila kanwar sa ce. nan da nan ya
daga hannuwan shi biyu alaman baruwana sannan yace "guy no offense oo, she asked me to have one hour with her, and then pay her" Sadeeq bai ko kalli Guy din ba ya jata suka fara tafiya. "kallo yabisu da shi sannan ya girgiza kan shi kawai ya cigaba da tafiya. Sadeeq da ran shi ke mishi radadi baisan ma yana jan ta da karfi ba. turjewa tafarayi tare da ce mishi yasaketa. "baiko saurareta ba har suka kusa gida. Nan taji tafara jin jiri, dama ga jikinta da sauran ciwo, ga uban tafiya da suke ci, ga yunwa. kuka kawai takeson yi amma ko kadan ta kasa, zuciyanta yariga yakame tun shekarun baya, ko me zai faru da ita, bata taba yadda tayi kuka. Saidai tayi ta jin radadi a zuciyanta. ahaka har suka isa gida. Joseph yana zaune a bakin gate din, abun duniya duc ya dame shi, tuna ni ya dunga yi, waye agidan da har baitaba ganin wulkawar kowa ba? kuma kodaya tambayi oga nabeel cemashi yayi ya tambayi ogan shi. yana ganin su ya mike da sauri ya bude musu karamin kofar gate din. "welcome oga, welcome madam. duc a rikice yake maganan. "tnx kawai Sadeeq yace sannan yaja ta suka shiga ciki. Kallon mamaki Joseph yabisu da shi. direct dakin ta yanufa da ita, a kan gado ya zaunar da ita sannan yawuce bandakin. Ruwa mai zafi yahada mata sannan yafito. har baccin wahala yafara daukar ta. Kallon ta kawai yakeki, sannan ahankali yazo dab da ita. afirgice ta mike jin ya dauketa. Abun da ya lura da ita kuwa, tana da tsoro. yana shiga da ita ya ajeta yafito. dakin shi ya nufa ya shiga bandaki dan yayi wanka. Yana gamawa ya dauro alwala yafito, dan har anyi la'asar. yana idar da sallah yafito yai hanyar kitchen. tea yahada mata Mai zafi sannan ya dora a tray yafito. Yana shiga dakin yaganta a gaban dressing mirror dauke da lotion a hannunta. karasowa yayi har inda take ya aje tray din dan nesa da ita kadan ya ajiye mata. Bata ce komai ba tacigaba da shafa lotion din. Niman waje yayi a fegen gado ya zauna. a lots of things running through his mind. har tagama bata kalli inda yake ba, tasowa ahankali tayi tazo tabi gefen shi tawuce, bude press din tayi, tafito da wani gown coffee brown mai gundun hannu, karamin drawern ta kara budewa ta dauko pant kawai banda bra. dqgowan da zata yi suka hada ido, shiya fara sauke idon shi kasa tare da mikewa yayi hanyar fita. yana zaune a Palo for like five minutes kafin ya mike ya fita. Joseph na zaune akan benci, ganin shi yasa ya mike da sauri. Hanyar fita ya nufa tare da ce ma Joseph din "don't allow her to go out, make sure you lock the door I will knock when I'm back." da dauri Joseph yace yes oga sannan yana fita ya maida kofar yasa lock. Fitan da sadeeq yayi bai tsaya a ko ina ba sai gidan nabeel...

Sadeeq na isa gidan nabeel ya sameshi a palo yana kallo tare da kofin Lipton dinshi yana sipping. tunda ya Kalli wanda yashigo saudaya, ya dauke kanshi baikara juyowa ba. ahankali Sadeeq ya karasa palon ya zauna. suna dai zaune ahaka, yarasa ta inda zai fara ma nabeel din magana. chan dai yayi karfin hali yace "the girl you saw... shiru yayi. Nabeel ya ajiye kofin hannun shi yace "yeah, what about her?" dan shi har yanzu mamaki ne fal zuciyanshi. he still couldn't believe what he is seeing. Sadeeq ya kauda fuskar shi daya side din, sannan yace "I just want to help her nabeel, she needs that... she's in pain.. soo much pain... Kallon shi kawai nabeel yakeyi ko kifta ido babu. ganin Sadeeq din bakara cemishi komai zaiyi ba yasa yace "when did all this happened?. Sadeeq da kamar bazaiyi magana ba... ahankali ya juyo yana kallon shi. haka nabeel din duc ya tattara attention dinshi guri daya yana kallon shi. sauke nunfashin shi yayi "that very day we saw her at the beach.... ba abunda ya boye ma nabeel har zuwa yau. Ajiyan zuciya mai karfi nabeel ya sauke, sannan yace toh that's good, Allah yabaka lada. But I'm advising you "first thing in morning kabata duc koma me kayi niyya ka sallameta. Idan taga dama ta koma garinsu, inkuma barikin zata cigaba da yi, ita ta sani, Allah dai yaga zuciyanka, wallahi ko ganinta banson yi, she irritates me. Sadeeq kallon shi yake yi kawai, chan yace "she's staying in my house." bai bari nabeel yayi maganar da ya bude baki zaiyi ba. he continues.. Idan na sallameta yanzu ta koma abunda takeyi da kuma fa? nafada maka she told me that her mom is late, her dad hated her mum for.. m not suppose to say much. nabeel ya ce "you must be kidding me wlh, kasan Allah baza ta zauna a gidanka ba. Mikewa sadeeq yayi dan yaga lokaci na wucewa, dan yanaso ya yasiyo musu abinci. mikewa yayi tare da daukar keyn motar nabeel da ke kan center table ya fita. bai wani bata lokaci ba yadawo, lokacin ana kiran sallahn magrib. suna idarwa yafito ya shiga motar yakarasa gida.. Yana shiga Joseph ya yakaraso yana gaishe shi. leda daya na abinci da drink ya mika mishi, tare da tambayar shi ko ta fito. Joseph ya girgiza yace tunda ya fita bata fito ba. godiyan abunda Sadeeq din ya bashi yayi sannan yafara kokarin karban na hannun Sadeeq din zai shiga mishi da shi ciki. sadeeq yace ya bari kawai tare da kulle motar yai hanyar ciki. a Palo yasameta a zaune kan one sitter, karasawa dining yayi ya aje komai sannan ya shiga kitchen din ya fito da plate. yana kokarin zuba abincin a plate yaji muryarta."I want just tea" juyowa yayi yana kallon ta, sai kuma ya rufe abincin ya shiga kitchen. Minti biyar yayi saigashi da karamin tray dauke da tea, akan stool din da ke kusa da ita ya ajiye mata. Kai hannunshi fuskar ta yayi, yaji da dumi. daukan tea din tayi tafara sha, shikuma ya koma dining din ya ciro take away daya na jollof rice with chicken part, yadawo palon ya zauna. ahankali yakecin abincin, tare da tunanin abunda nabeel yace, wai she irritates him.. Dagowan da zaiyi suka hada ido. You want something noor? ya tanbayeta bai kuma daina kallon ta ba. tasowa tayi ta zo ta zauna a kujeran da yake zama. ajiye plate din yayi akan centre table sannan ya dawo ya zauna kusa da ita. Kamo hannunshi tayi a hankali.....

kallon shi cikin ido tayi sannan tace "are you planning to sell me? " Sadeeq ya juyo gabadaya yana facing din ta, riko hannun ta yayi duka biyun, dauke da murmushi a fuskar shi yace "No.. I'm not a bad person noor, I don't know the amount of Bad people you've come across, but count me out." ahankali ta dauke idon ta daga kallon da yake mata... Hannun ta rike cikin nashi, kuma bata kara cewa komai ba. azuciyanta ta kuwa, tunani takeyi, tayaya zata nima hanya ta gudu? bata ma san ko wani unguwa bane nan din inda suke .. ina zata samu kudin da zai koma da ita badagry? tana karban kudinta kuwa ko minti daya bazata kara ba zatai gaba abunta. ko kawai kasar zata bari?? Sadeeq ne yadawo da ita daga duniyan tunaninta. "hey gorgeous" dan tunda ta sauke kan ta kasa yake kallonta, kuma yaga ko kadan bata da da alaman saukowa, tuni yagane kirin tunanin datake yi. "dagowa tayi ahankali ta kalleshi. "you still want to go back there right?.. Batace mishi komai ba. "talk to me please." nan tace mishi "I want to go and get what's mine.. I can't let her go with what i worked so hard for... Sadeeq da yaji wani daci a zuciyan shi da ta fadi haka.. "i can't let you go back to that dirty place noor" takaici ne yakama ta ba kadan ba, fusge hannunta tayi sannan ta mike, afusace tafara mishi bala'i "you have to return me back to where you picked me immediately!!! You know nothing about me, and now you want me to trust you just like that. for no any reason.. You must be joking... take me back now!!! "calmly Sadeeq yace mata or what?? or I kill myself, tabashi amsa immediately ... tana kallonshi ganin yadda idon shi tuni ya tara ruwa, ganin haka takara dacewa "yes I will kill myself wallahi.. because there's nothing left for me in this world.. Mama is gone.. I heard my father several times telling my mother,... he.. hawaye ne yataru a idanun ta.. "he wishes I was never born.. My uncle sold me into prostitution at very tender age" with so much bitter in her heart... she broke in to tears. So tell me what's left for me again in this world.. I ha... hate... I hate men. I ha.. Sadeeq da tuni yafara hawayen shima bai bari taci gaba ba dan kunnuwansa baza su iya cigaba da saurara ba, da sauri ya mike ya jawo jikin shi ya rungumeta, kuka take yi kamar ranta zai fita. kukan da taketason yi tun shekarun baya da suka wuce, sai yau tasamu damar yi... Kuka takeyi tsakaninta da Allah kuwa, tananan rungune jikinshi, scent dinshi duc ya cikata. saida tayi mai isarta sannan tayi shuru. Jawota yayi suka zauna kan 3sitter din da ke palon. ahankali ta sauke kanta daga kirjinshi... "let me go back

Please Login or Register in order to submit comment