Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

the floor and asked for my forgiveness..." SUFYAAN IS NOT WORTH FORGIVING... wani kirin rumguma taji ta bayanta kamar zai maida ta cikin shi.. Sadeeq ba abunda yafi tsaya mishi arai yanzu kirin Alhaji tanimu... dan damsel tafada mishi bazata iya haihuwa ba ta dalilin mahaifar ta da alhaji tanimu yasa wata doctor amina ta cire, akan baison ta haihu.. itakuwa Damsel abun bai taba damun ta sai da Sadeeq ya dauko mata maganar haihuwa. Ita dai tasan ba son shi takeyi ba dan ko ada da tahakura zata aure shi ma, zata aure shi ne kawai just to pay for all the kindness he did for her, bata taba tsammanin akwai maza kirin haka a duniyan nan ba. tayi tunanin har ta koma ga Allah she will never have a good life that she deserves. Sai ga Sadeeq... but then she changed her mind, a yadda take haka ga kirin banzan rayuwar da tayi, idan ta aure Sadeeq bata mishi adalci ba. He deserve to marry a good woman that will give him children and live a happy life. Not someone like her... Nabeel was right about her.. saboda da haka shiyasa tafada mishi asalin wacece ita. With this, zai Hakura ya barta ta gama gabanta.. ahankali tabude bakinta "you deserve better, not a person like me... Jin soft lips dinshi tayi a goshinta.. "I'M NEVER LEAVING YOU YOU NOOR, EVEN IN JANNAH, YOU WILL STILL BE MINE.." bakaramin shock damsel taji ba with his words. bata gama farfadowa ba yaci gaba "I love you noor, I want to you to trust me enough to show how much I adore you, I want you to marry me so we can build a life together.. you're now part of me Noor" damsel was so touched.. hawaye ne kawai yake sauka a idonta.. ahankali ya mike ya sauka daga kan dadon. bude press dinshi yayi ya fito mata da T-shirt dinshi, samata yayi sannan ya gyara mata kwanciya ya rufeta da duvet.. bathroom ya shiga yai wanka sannan ya dauro alwala ya fito.. jallabiyar shi yasa sannan ya shifida dadduma, nafilfili ya dunga jerowa yana mika kukan shi wajan ubangiji.. har ya idar ya dauko kur'ani yana karantawa. Duc abunda yakeyi kuwa tana kallonshi. He so reminds her of her late mother.. sai wajan karfe biyu yarufe kur'anin. lokacin har tayi bacci.. mikewa yayi ya bude kofar ya fito Palo ya kwanta.. nan da nan bacci ya dauke shi..

......kiran sallahr farko ya tada shi.. mikewa yayi tare da salati a bakin shi yai hanyar dakin. Bacci kawai takeyi.. Wucewa bathroom yayi ahankali without making any sound.. yana fitowa ya karasa kan dressing table ya feshe jikin shi da turaruka.. Saida yayi nafilfilin sannan ya mike yafita zuwa masallaci.. Karfe shida daidai ya shigo gida, ganin bata dakin shi ne yasa yafito ya shiga nata dakin. bacci yaga tanayi akan sallayar, murmushi yayi yakaraso dakin. daukar ta yayi dora kan gadon sannan yafito yakoma nashi dakin. 7:30 har gama abunda zaiyi, yana zura takalmin shi yaji wayan shi yafara ringing..ganin al'amin me ke kiranshi yasa ya dauka da sauri, sungama gaisawa al'amin yace naji ka shiru, dan har na fada ma madam zatayi bakuwa fa tun ranan.. Sadeeq yace kace mata gobe Friday insha Allahu zan kawo ta, dan jibi ne tafiyan, dahaka sukai sallahma yace kashafun kan iman. Sadeeq yagama shirin shi ya mike saurisauri dan yayi latti. leka dakinta yayi yaga har lokacin bacci takeyi. yana fitowa ya data mota yai hanyar office...Salma.. ✍️42

....Damsel na tashi daga bacci tafada bathroom, tana fitowa ta shirya cikin abaya ash color sai stones da suka kashe abayan tundaga gaba har baya stones ne. fitowa palo tayi tahada tea kawai tasha, tana gamawa ta mike nan kan kujeran idon ta na kan TV saidai ko kadan ba kallon takeyi ba. tana nan ahaka har 12:30...Sadeeq kuwa yana wajan aiki, bayan sungama sallama da mamin shi akan tafiyan da zasuyi,.. nan yashiga kiran damsel.. Har so biyu bata daga ba. ahaka dai ya hakura yacigaba da aikin shi...4 daidai ya tashi daga office ya dau hanyar gida.. yana shigowa yanufi dakin ta.. bakowa ciki ga dakin a gyare fess, mamaki ya cika shi, karasowa dakin cikin dakin yayi, wayan na nan ijiye a inda ya bar mata kan side drawer din gadon. Knocking yayi a kofar bathroom din yaji shiru... budewa yai da sauri yaga ba Damsel aciki.. da sauri yafito yashiga dakin shi... bata ciki.. ai baisan sadda ya wurgar da suit din hannun shi ba yafito zai yi hanyar fita yaji karan ruwa acikin... yana budewa ya ganta tsaye bakin sink, karamin towel ne a hannunta alaman tan gogegoge. haka kurin taji yau tana son yin wani abu, she's tired of being idol... Sadeeq yana ganin ta ya rumtse idon shi. azuciyan shi kuwa hamdala yakeyi... Suna hada ido da shi ta sauke. Karasowa kitchen din yai ahankali yaga me takeyi, ganin plate da cups biyu an kife a gefen sink din yasa yai murmushi. "you did all of this??" Kai ta gyada mishi. Kara bin kitchen din yai da kallo, nothing really intact amma yace "wow you did so well Noor" sosai taji dadin abunda yace. dan har saida tayi dan murmushi. Sadeeq ya dunka kallon pretty face dinta, kafin yace "what did you eat?" shiru tamishi... talk to me babe yace yana kallon ta. fuskar ta sauke a kasa tace "tea" murmushi yayi tare da jawo hannun ta suka fito daga kitchen din, dakin ta yawuce da ita. "get ready babe we are going out.." yana fadin haka ya juya ya fito yashige nashi dakin..in less than 20minutes yagama shirin shi yafito.. bakaken kaya ne ajikin shi. dan Sadeeq is a fan of anything black.. dakin ta ya shiga da sallama..tana zaune a gefen gado, yellow material bubu tasa with a touches of white flowers ajiki, kirin masu zuwa da medium gyale nan. tana rike da gyalen a hannu, tarasa yadda zata yafa, aganinta yamata girma.. Sadeeq kallon ta kawai yakeyi kamar ranan yafara ganinta.. azuciyan yana fadin "ya Allah, please make her mine forever.." kan ta a duke bata dago ba.. tsugunawa yayi kusa da ita,.. hannu yasa a hankali ya dago fuskar ta suka hada ido.. "you look gorgeous my angel.." nan itama ta kalle shi da kyau, dan shima bakaramin kyau yayi ba cikin kananan kayanshi komai baki ga pcap din shi yakara mishi kyau.. mikewa yayi tare da riko hannunta suka fito palo, Karban Vail din yayi yashiga yafa mata, shima ba iyawan yayi ya, haka ya dunga nannada mata yana kwancewa.. gajiya tayi ta karba ta yafa kawai tare da rikewa ko wani gefe da hannunta.. Sadeeq yace "that looks better" suka fita har mota, bude mata yayi ta shiga ya rufe sannan yazagayo yashiga yada suka kama hanya.. suna mota kuwa gyalen yazame yafi sau a kirga.. chan dai tai mishi wani nannada ta shigar da sauran takasan wuyanta. aikuwa saitai kyau kaman kirin Sudanese din nan... har suka iso wani babban restaurant kanta na jingine a jikin motan kamar me bacci..hura mata iska yayi tabude ido, suna shiga ya nima musu table for two suka zauna. tunda Suka shigo wani guy ya dinga kallon ta ko kifta ido babu.. waiter ne yakarawo wajan tare da gaishe su, Sadeeq da har ya riga yagama deciding musu abunda zasuci. kallon waitern yayi tare da fada mishi me zai kawo musu, waitern nawucewa ya maida kallon shi kan noor. itakuwa duc atakure take, ta dalilin yadda duc tabi ta cukuikuye gyalen a wuyanta. ganin haka yasa Sadeeq mikewa yazo dab da ita yafara kwance gyalen sannan ya yafa mata kawai akai yadawo ya zauna.. duc abun nan akan idon guy din.. ana kawo musu orders su Sadeeq yai serving dinta, ahankali suke cin abincin dagowan da zaiyi kuwa yaga vail yafadi akan kafadarta. ganin kuwa kallonta akeyi yasa yaji duc abincin ya isheshi, dama shi yakeci itakuwa tsakura kawai takeyi.. mikewa yayi da sauri yazo ya rufe mata kan tare wucewa ya biya bill dinsu.. yana barin wajan kuwa guy din yakaraso. magana ya dunga mata kuwa, ko inda yake bata kalla ba "I can see you left dollars and pounds.. I went there twice but you weren't there.." yana magana ne yamata kallo Kirin na yan iskan duniyannan.. "tell me your new location, or rather put your digits we will discuss better on phone" yana fadin haka ya mika mata phone... ji yayi an fuske wayar an roda shi da tiles din kasan wajan... Sadeeq ne a tsaye, calmly yake kallon shi kamar bashi ya buga wayar akasa ba, kallon kirin karfin halin shi kawai yakeyi, nan ya bude bakin shi ahankali.. "didn't she tell you she's married??" guy din da har yayi niyyar mikewa yai bura'uba, yana jin abunda Sadeeq yace jikin shi yai sanyi, kallo daya yamata tare da risinawa ya dauki wayar shi da duc screen din a rotse yake yai wucewar shi.. Sadeeq bai wani bata lokaci ba ya dagota suka wuce.. duc inda yaso kaita ma duc sai yaji ya fasa.. gida suka dawo.. suna dawowa ta shige dakinta shima yashiga nashi dan yin sallah.. yadade a dakin bai fitoba har akayi isha.. wanka yayi yasa pyjamas dinshi yafito yai hanyar dakinta. Har ta fara bacci. zama yayi gefen gadon.. yana yan wasu tunani, kafin ya juyo yana kallonta ahankali yakira sunan ta, sai da yakira ta so biyu kafin ta bude ido, saidai bata tashi ba. chan yace "wake please, I want us to talk" Damsel da duc tunaninta na maganan guy din dasuka hadu a restaurant dazu zaimata. Mikewa tayi daga kwancen da take sannan ta kara jawo bargo ta rufe jikinta.. ahankali taji muryar shi "am traveling out next tomorrow in sha Allah,... I will spend like two weeks before I come back.. I will take you to my friend's house tomorrow to stay with his wife before I return" tunda yafara magana take kallonshi har ya gama.. tuni baccin da takeji ya fita.. ganin yanayinta yasa yashafa kanshi tare da dan murmushi a fuskar shi sannan yace "come on babe you will like it there, khadeeja is a nice person to be with...ok?" kallon shi kawai takeyi, chan Kasan makoshi yaji tace "o..k" Good girl yace... matsowa yakarayi dab da ita, yana kallon ta da kyau.. "one more thing Noor.." jin ya riko hannunta yasa tadaga kai tana kallonshi.. "please don't do anything that will hurt me, I mean don't run again.. Promise me that.." ganin batace komai ba yasa ya sunkuyo da kanshi yana kallon ta.."I promise tace mishi ahankali..." wani sanyi yaji aranshi, jin ta fadi haka... Hada fuskokin su yayi guri daya.. "thank you... thank you Love.." tare da kai mata kiss a forehead dinta ahankali.. sannan yasake ta koma ta kwanta, shima mikewa yayi yafito tare da rufo mata dakin..

......tunda Sadeeq ya dawo daga masallaci yashiga dakin shi, ba'ajima ba yafito da dan medium size trolley yashiga dakin damsel.. tana cikin duvet ta dukunkune ganin sallahya akasa ba'a nannade yasa yasan tayi sallah, abun na mugun birge shi kuma.. har yagama hada mata kayan ta aciki bata tashi ba. yanagamawa yafito mata da bakin abaya tare da vail dinshi, sai pink small hand bag dayasiyo mata tun siyayyan dayamata na farko. ayiyewa yayi akan kadon sannan ya fita,... yana gama shiryawa ya fito. wani hadadda shadda sky blue yasa tare da hulan shi yai hanyar dakinta tare da duba wristwatch din hannunshi. tana nannade acikin bargo, tashin ta yashiga yi ahankali. tana bude ido yace "kar inyi latti Babe" mikewa tayi tana murza ido.. m waiting yace tare da jawo akwatin yai hanyar fita.. binshi tayi da kallo kafin ta mike tawuce bathroom... 25minutes tayi kafin ta fito.. yana ganinta ya mike yakaraso har inda take yana mata murmushi.. bude handbag din yayi yaga bakomai ciki.. dagowa yayi yana kallonta kafin yace "where's your phone?" kafin tai magana yai hanyar dakin, fitowa da wayan yayi tare da charger ya bude jakan yasa mata sannan yaja hannunta Suka fito. yana shiga mota ya tada sannan ya dau wayar shi yashiga kiran al"amin.. yana dauka suka gaisa tare da cemishi yanzu zasufito gida, sama sama ya amsa gaisuwar Joseph dan har lokacin suna waya da al'amin.. Har Sun dan yi nisa, yasamu gefen hanya ya tsaya awani babban supermarket.. ba'a jima ba yafito rike da ledoji yashiho motan. Mika ma damsel yayi tare da cemata "give the kids when we get to the house" kallon ledojin takeyi chan Kuma tadago tana kallonshi.. murmushi yamata yace "yeah, aunty noor tama ma kids tsaraba" karba tayi ta ajiyesu ahankali a gefenta.. tana dagowa kuma taga yana mika mata mint 1000 bandir .. Kallon kudin takeyi.. Kafin ta karba zatasa a daya daga cikin ledojin.. nooo yace da Sauri ya karba kudin ya bude handbag dinta yasa mata.. "this is for aunty noor, not for the kids" yana sawa ya rufe jakan tare da tada motar suka dau hanya.... in 25 minutes suka shigo cikin lekki... horn yayi mai gadi yabude mishi gate, yana ganin Sadeeq ne ya washe baki..tare da cewa "longest time sir" Sadeeq ya tsaya suka gaisa sannan yakarasa da motar ciki... Al'amin yafara fitowa ya tsaya a kusa da motar sannan Sadeeq ya fito.. rungume juna Sukayi.. al'amin yace the great bachelor himself" Sadeeq ya shafa kan shi yana murmushi. al'amin yace wai wa kake tacewa zaka kawo mana ne? Nayi tunanin ko Hauwa tazo ne. Sadeeq yama rasa me zaice, dan baifada mishi ko wacece zai kawo ba, nan dai yace ba Hauwa bace wlh.. kallon motan yayi kafin yace.. the woman I want to marry.. wani dadi al"amin yaji tare da ware idonshi... "you don't mean it" Sadeeq na daria. al"amin yazagaya inda damsel take yana fadin finally, zaka ma nabeel wayau kenan tunda ya tsaya iskanci a garin Lagos... Bude kofar yayi tare da cewa "our very own madam.." damsel na dagowa suka hada ido, gaban al'amin ne yai mugun fadi......


....tunda Suka hada ido kuwa Damsel ta dauke idonta, ganin kirin look din da al'amin ke bata.. al'amin kuwa nan da nan dai ya kauda da tunanin da ke zuciyanshi, dan baida tabbaci. atake kuma yakara fadada murmushin shi tare da cewa "welcome madam.." nan sadeeq shima ya zagayo tare da karasowa kusa da ita.. "come down babe" saukowa tayi ahankali kanta a kasa.. al'amin dai yana kallon su.. har suka karasa ciki.. Khadeeja matar al'amin da saukowanta kenan daga steps, da murnar ta takaraso har cikin palon, tana kallon su tace "idon Sadeeq ne wai yau a gidan nan?" sadeeq ya shafa kan shi yana murmushi ahankali yace "the chef herself.." tare da niman guri suka zauna shida damsel.. itadai damsel kanta a kasa kamar tana jin tsoro. suna zama kuwa takara matsowa dab da shi.. khadeeja dai tana kallon ta, kasa hakuri tayi tana kallon Sadeeq tace bakuwar tamu kenan, yar kyakkawa da ita.. kafin yai magana al'amin yai saurin cewa "finally yayi deciding yadena zaman gwauronci.." khadeeja bakin ta bude.. al'amin na kallon matar nashi with a smile on his face yace "yeah babe.. His wife to be" aikuwa da sauri khadeejan tazo ta rungume damsel.. sannan tace " now I see the reason why you're delaying".. ashe kirin ka sakk kake nima.. Sadeeq dai murmushi ya dunka yi tare da mikewa yana kallon abokinshi, "barin shigo mata da kayan ta, I will be on my way nayi latti wlh.." mikewa khadija tayi tare da kwalo ma mai aikinta kira.. akan tazo ta kwaso kaya awaje. al'ameen na kallon shi yace "ko breakfast baza kayi ba?" Sadeeq da ke kallon agogon hannun shi yace noo nayi latti wlh. sarah har fito kiran da khadija tamata, Sadeeq naganin ta yai hanyar waje, damsel tabishi da ido. Ji take kaman ta mike ta bishi da gudu.. suna waje tare da al'amin Sarah har ta shige da kayan da Sadeeq yafito mata dasu daga mota. yana kallon al'amin tare da tambayar kids. cemishi yayi suna school, nan da anjima zasu dawo dan yau Friday. Sadeeq yace that's nice, mazaa barin wuce, we will talk on phone. Alright then al'amin yace tare da daga mishi hannu har ya bar gidan.. yanashigowa ya tarar har Sun haura sama. zama al'amin yai a Palo yacigaba da aiki a system din shi..

.... Sadeeq kuwa yana isa office around 11:am yagama duc abunda zaiyi ,tare da hada brief meeting a office din.. suna gamawa ya dauki phone dinshi ya shiga kiran cleaner dinshi, yana dauka yace yasameshi a gida yanzu...ahanyar komawar shi gida call din abban su yashigo wayar, dauka yayi tare da mishi sallama sannan suka dan gaisa.. har ya shigo cikin ungwan shi suna waya da abban nashi, kuma duc akan aikin da zaije yayi ne.. kafin sukai sallama tare da sa mishi albarka. horn yayi Joseph ya bude mishi gate, yana shigowa ya tarar da cleanern na zaune kan plastic chair yana jiran shi.. yana gama parking yafito suka gaisa sannan ya bude gidan Suka shiga tare.. ba batare da bata lokaci ba yafara aikin shi. Sadeeq Kuma Shiga dakin yayi yafara hada kayan shi. Saida cleanern yagama komai tass kafin Sadeeq yamishi transfern kudi tare emptying komai naci a kitchen din ya bashi.godiya sosai ya mishi tare fatan Allah yadawo da shi lafiya.. yana wucewa Sadeeq yashiga wanka tare da dauro al'wala dan zuwa masallaci yin sallahr la'asar, dan yayi azhar kafin ya baro office.. yana dawowa daga masallaci kuwa yadan hada tea yadawo ya zauna a Palo yana sha.. tunanin damsel kawai yakeyi ko ya take copping awajan ohoo.. though yasan khadeeja is friendly.. baison kiran ta yanzu sai dan anjima kadan.. yana gama shan tea din kuwa ya dauki waya yashiga kiran mamin shi.. nan ma Sun dan dade suna waya tana zuba Mishi addu'oi kafin Salukai sallama ya ajiye wayan...


.....Damsel kuwa suna haurawa sama da khadija ta kaita dakin da suka gyara mata na saukan baki. bai kai na gidan Sadeeq girma ba, saidai dakin ya tsaru, komai purple.. har cikin dakin tarakata ta zauna bakin gado kafin khadija ta juya ta fita dan ta hado mata breakfast.. ta lura ko kadan damsel batason magana dan tunda tazo magana bai hadasu ba, sai dai intamata magana ta girgiza mata kai kawai. azuciyan ta kuwa tace (Sadeeq yasamo kirin shi haka zasuyi ta zaman kurame a gidan) tana saikowa ta Kalli mijinta yana ta faman aiki a system, bata cemishi komai ba ta karasa kitchen dan baison distraction idan yana aiki. saida tahada ma damsel psoup din kaza a bowl tare da soyayyen dankali, sai tea da ta hada mata ta fito tai hanyar dakin.. har ta fara bacci. tashin ta khadija ta shigayi, ahankali damsel ta bude ido sannan ta mike ta zauna. khadija ta jawo wani karamin table ta dora mata abincin akai tana kallonta with a smile on her face tace "saidai bansan sunan kawar tawa ba." nan ne damsel tabude baki ahankali tace "NOOR" khadija da taji muryar damsel tace Masha Allah, wht a beautiful name.. have your beakfast please.. yanzu zan dawo, tana fadin haka ta fita tare da jawo mata kofar.. ahankali damsel ke kallon abincin kafin ta dauki tea tafara sha....

....khadija kuwa saukowa tayi tabar damsel dan tasamu daman cin abinci. zuwa wajan al'amin da har yagama abunda zaiyi a system. niman guri tayi ta zauna, ahankali ta jingina da kafadar shi.. murmushi al'amin yayi tare da juyoya ya Kalli khadija, kiran sunan ta yayi,.. "my Deeja" na amm my Doctor ta amsa. al'amin yace kinbar bakuwar ki ita kadai.. khadija tace "no, nayi excusing dinta ne dan samu tayi breakfast babe." chan kuma tace yaushe kakeson anyi baking maka cake din? al'amin dake kokarin cire farin classes din idon shi yace "no babe kibari ko gobe weekend kiyi tunda yau kinyi bakuwa"... nan khadija ta mike daga jikin shi tace "babe bakaga yanayin ta ba? I mean kirin halin Sadeeq din kaman itama take shi, dan har kaman ta fishi ma, na lura bata son magana.."zata cigaba, al'amin yai saurin jan hancin ta tare da dora yatsun shi daya akan lebben shi.. "come on Dee, daga ganin mutum yau yau din nan ,sai kurum kiyi concluding.. even though gaskia nasan Sadeeq dama bazai dauko me hayaniya ba dan shima ga yadda yake.." murmushi khadija tayi tare da mikewa tai hanyar hawa steps. "lemme be with her before the kids comes back.." al'amin yace alright babe sannan ya mike a kujera.. khadija na shiga dakin ta tarar da damsel tsaye a jikin window, (niko nace anfara sana'an) kadan tasha pepper soup din sai tea din da ta shanye duka.. juyowa tayi jin anbude kofar, ganin khadija ce ta shigo, har zata juya baya sai kuma ta tsaya saidai bata kalleta ba. Khadija ta bi tray din anincin da kallo, nan tafara magana "Noor, baci komai ba ai, Aa gaskia nan gidan fa ba'a bakon ci ko kadan, ko kinason amiki wani abu ne? " damsel na tsaye kanta sunkuye, girgiza mata kai kawai tayi. Khadija tace toh ina zuwa. daukan tray din tayi ta fita. damsel ta bita da kallo. ba'a jima ba sai gata ta shigo da wani dan plastic bowl me kyau a hannu dauke da graphs. ajiyewa tayi akan gadon kafin ta zauna. damsel dai na kallonta.. khadija ta kalleta kafin tace zo ki zauna mana.. karasowa tayi ta zauna ahankali. tura mata graphs din tayi kusa da ita bayan ta dauki biyu tasa daya a baki.. da murmushi fuskar ta tace ki Saki jikin ki da ni please noor, naga kaman baki Saki jiki da ni ba... nan khadija ta rinka janta da hira, dan khadija kirin exposed mutanen nan ne gata tana da saurin shiga rai, dan ta iya bi da mutane sosai.. yar zariya ce amma cikin garin kaduna ita da iyayenta suke. babbar chef ce dan tun tana karama take da sha'awar girki, dan haka tana gama secondary school kafin ta samu addmition a KASU iyayen ta suka sata a Dee bakers dake cikin garin kaduna, da haka nan da nan kuwa cikin kankanin lokaci ta kware a fannin girkegirke, baking da dai sauransu. daga nan tasamu admission a Kasu inda takaranta food and nutrition.. tana final year dinta tahadu da al'amin lokacin sunzo wani taron su na likitoci a arewa house, kuma ita tayi snacks da abincin da sukaci for three days. nan al'amin yanima contact dinta dan tama kanwar shi abincin da za'ayi a dinner dinta, saboda kirin kwarewar da yaga tayi a Fannin sarrafa abinci. toh daga so mai karfi ya kullu tsakanin su har ya Kai ga sukayi aure, shekaran 7 kenan da aure, yayan su biyu, mace da namiji, na farkon mace ce suna kiranta iman sai na biyun amar.... khadija sosai take ba damsel labarin.. friendship din mijinta da Sadeeq... gajiyan da damsel tayi Kanta a duke ne yasa ta dago. Itakuwa khadija ganin damsel tadago Kai yasa tai tunanin ko dan labarin da take bata ne. khadija tace "wlh kuwa, tunda nai mishi maganar cousin dita amira, shikenan fa ya dauke kafar shi daga gidan nan.. Sai yau. ashe yasan yana da zukekiyar Babe ce." ko kadan damsel bata sauraron abunda khadija ke cewa, duc hankalinta na gidan Sadeeq, da yanzu tana daki ita kadai ba hayaniyar kowa.. khadija ta dan taba kadan, ahankali ta sauke idonta kan khadija.. nan khadija takara maimaita tambayar "where did you and Sadeeq met?" Damsel tai shiru for a moment... kafin ahankali tace "dollars and pounds" khadija tace " where's is the place? a restaurant

Please Login or Register in order to submit comment