Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

I guess??" damsel ta girgiza mata kai, zatayi magana kenan aka bude kofar.. da gudu yaran suka shigo tare da sallama suka haye jikin uwar su. Damsel ta rinka kallonsu kamar yau tafara ganin yara a duniya.. haka suka dunga jakwalgwala uwar tasu.. khadija ta rike hannun amar dake kokarin kaiwa bayan kunnen ta, dan yasaba mata haka. Kallonsu tayi tace Baku gaishe da aunty Noor ba. duc yaran suka juya suna kallon Damsel. Damsel dai na kallon yaran.. ganin kirin Kallon da damsel take musu ne yasa su ka tsaya sukai tsiritsiri da ido. iman ta bude baki ahankali kamar tana jin tsoro,.. (good afternoon aunty..n..) Maman takarasa mata.. "aunty noor..) iman tace aunty noor... shidai ammar yana jikin mamanshi.. damsel datarasa me za tayi, nan ta tuna da ledan da Sadeeq yabata yace for the kids.. ganin ledojin kusa da trolley dinta da Sarah ta ajiye mata kusa da wardrobe din dakin yasa ta mike ahankali tai hanyar wajan.. dauko musu ledan tayi ta karaso kusa da su ahankali ta mika ma iman.. aikuwa nan amar ya sauko daga jikin mamanshi shi yana kokarin kwace leda daya. nan rigima ya barke, haka damsel ta shagala tana kallon yaran dan Sun bata sha'awa sosai.. tsawar da khadija tadaka Musune yasa suka tsaya, amar dai baidena kuka ba. khadija ta Kalle su tace "what are suppose to say to aunty noor?" yaran duc suka isa suka rungume damsel tare da cewa "thank you aunty noor" damsel har cikin ran ta taji yaran a jikin ta. bata san sadda ta tsuguna dab dasu tace "you're welcome.. tare da murmushi a fuskar ta" khadija tana kallon su tana murmushin itama sannan tace "now go and show daddy. and tell him who bought it for you" aguje suka Saki noor suna rike da ledan suka fita.. khadija ta dawo da kallon ta kan Noor "I see you like kids kema kaman Sadeeq, dan shima yana bala'in son yara gaskia, kullum maganar shi kenan inyazo" with a big smile on her face tace "Allah dai ya nuna mana naku.. tare da mikewa tai hanyar kofa "barin ma yaran nan wanka please, you can on the TV if you want to watch dear. tana fita ta kullo mata lofar... Damsel kuwa dawowa bakin gado tayi ta zauna ahankali, dan maganar da khadija tamata Yayi mugun kashe mata jiki... nan tashiga tunani ( yanzu da gaske baza ta iya haihuwa ba?? and bugu da kari Sadeeq mai son yara ne even though he agreed to be with her for who she is... but that's not fair for him...) rumtse idon ta tayi sannan ta mike ahankali tai hanyar bandaki... wanka tayi kafin ta dauro alwala ta fito. dogon riga ta Sa sannan ta shinfida dadduman da tagani a cikin wardrobe tare da hijabi.. tana idawar kuwa ta mike nan bacci ya dauketa...

....sadeeq kuwa yana nan palo yana dannedanne a system dinshi.. wayan shi dake kusa da shi yai kara, yana dubawa yaga nabeel ne. Bayan ya dauka sundanyi maganan minti uku kafin daga karshe sukai sallama akan kar ya manta, flight din shi 8 ne daidai so yazo da wuri dan shi zai kaishi airport. dahaka Sukai sallama... yana Yanken call din kuma ya shiga kiran Damsel an rubuta "NOOR" ajikin wayan, har so biyu amma bata dauka ba.. yaso kiran al"amin akan yahadashi da khadija suyi waya, dan yaji ko ya Damsel take, amma ya kasa,.. bayaso suyi wani tunanin daban. shikuma he just want to know if she's OK ne, dan yasan yadda ko kadan bata sakewa... haka dai yai hakuri akan he will try calling her later.... Sadeeq yana dawowa daga sallahr isha ya ya tattara sauran abubuwan ci a kitchen din tare da duka kayan tea yafito ma Joseph dasu.. sai kudin aikin shi na wannan watan da ko rabi bai kai ba yamishi transfer tare da kara mishi 20k. sosai Joseph ya dinga ma Sadeeq godiya har saida ya shige gida..

.....karfe 6 daidai nabeel na gidan Sadeeq kafin 7 har sunkama hanyar airport. In 27minutes suka isa, fitowa Sadeeq yayi tare da zagayawa yabude boot din ya sauko da trolley dinshi. har nabeel yafito shima daga motar ya kulle. nan suka kama hanyar shiga ciki dan sunkusa tashi... suna tafe ne ba Wanda yace kokai cikin su.. Nabeel kuwa tunani yaketayi inda Sadeeq yakai damsel,.. Kuma yarasa ta yadda zai bude baki ya tambeyshi,...chan bayan sunshiga har Sun dan zauna kadan, akafara announcing in 10minutes passengers zasu fara shiga jirgi.. gathering courage nabeel yayi tare da juyawa ya Kalli Sadeeq dake ta faman rubuta text a phone dinshi, ahankali nabeel ya bude baki yafara magana "so where did you take the girl? " sarai Sadeeq yasan wa nabeel ke tanbayar shi akai, amma sai ya juya yana kallon shi with confusion look "which girl is that??" sosai nabeel ke kallon Sadeeq din.. kafin yai magana har anfara announcing akan passengers sufara shiga jirgi... mikewa Sadeeq yayi tare da murmushi a fuskar shi.. " I took her to somewhere safe..." yanaSalma..

...yau kwanan Sadeeq daya a Spain, kuma har yau bai samu yayi magana da damsel ba. yana cikin hotel room dinshi tare da system agaban shi, dan gobe Monday zasu fara aiki gadan gadan. kasa hakuri yayi ya ya dauki wayan shi dake gefen shi yai dialing number al'amin, har yakusa tsinkewa aka daga wayan. sun gaisa da al'amin sai kuma yadan Sosa kan shi kadan kafin yayi gathering courage yace "ya take?" al'amin ya tuntsire da daria dan tunda yaga yafara kame kame ya dago shi, al'amin yace "kwana daya kawai, har kafara tunanin ko mun yanka ta ne? toh ba kuna waya ba?" murmushi kawai Sadeeq yayi tare da cewa "no bahaka bane friend, her line is not going through ne" al'amin da jin haka ya mike yai hanyar kitchen dan yaji hayaniyar su a kitchen din, tare da cewa ok let me give the phone to khadija. dahaka yai hanyar kitchen din. tana tsaye bakin gas din kusa da khadija, duc ta tattara hankalinta ta maida kan abunda khadija keyi, abaya ne cream a jikinta sai gyalen shi da tayafa. daidai kofar kitchen din al'amin ya tsaya tare da cewa "sannunku da aiki" dukansu suka juyo, nan ne al'amin yakara ganin fuskar ta da kyau,.. khadija ya mika ma wayan yace "pass the phone to her, Sadeeq want to talk to her" yana mika ma khadija phone din yafito ya dawo palo.. tunani ne fall zuciyanci, aina Sadeeq ya hadu da ita? where's her family from?? Anya??? khadija kuwa tana karbar wayar ta mika ma Noor. ahankali noor ta kalli wayar kafin ta karba, khadija dai na kallonta, ganin batasa wayan a kunni bane yasa taga kamar ko kunya takeji. rike hannun noor tayi takara mata wayan a kunne tana daria tare bin hanyar kofa tana cewa "yi wayan ki dear tunda kunya ta kikeji" duc abunda sukeyi kuwa Sadeeq najinsu a wayan... chan yace "NOOR" ahankali tace na am... Sadeeq da yaji kamar yayi shekara ne baiji muryar ta ba, yace "why are you not answering your calls ??" Damsel da nan ne ta tuna Ashe wai da waya a hand bag dinta. Shirun da yaji tayi ne yasa yace "or you don't know how to operate it??" itadai batace komai ba. Sadeeq yace "talk to me please babe.." ahankali tace "I know.." Sadeeq yace ok anjima I will call you kafin kiyi bacci, please keep the phone close to you kinji Noor?? ahankali tace "ok..." good girl yace tare da hanging phone din... khadija kuwa tana fitowa, palo tazo ta zauna kusa da mijinta.. al'amin yana ganin khadija ta zauna yace "wifeyy..da wa kike ganin bakuwar ki ke kama?? khadija ta kalli mijin nata sai kuma tafara nazari... chan tace kaman uncle abubakar.. da sauri al'amin yace "exactly my thoughts too babe, but how?? " khadija tace "come on babe kama ne fa Kawai and you know that" tana fadin haka ta mike zuwa sama dan taga ko sarah tagama aikin da tasata... binta al'amin yai da kallo.. tunani yake ya zai fara bullo da al'amarin?? ina ma suka hadu da Sadeeq tukunna? yasan dai bazai fara ma Sadeeq kirin wannan tambayar ba. nan ya yanke shawarar kirar nabeel gobe idan yafita aiki, dan yasan nabeel will definitely know something about her..
.... Sosai damsel takoya hadaddan "pasta salad" suna gamawa khadija ta hada komai sannan damsel ta tayata suka fito da komai suna jerawa a dining... duc damsel tana kallon komai and duc abunda sukayi kuma duc tana rikewa akai, sai dan abunda baza a rasa ba. al'amin da har ya fita zuwa dauko yara a islamiyya dake kusa da su. suna gamawa suka haura sama, damsel ta wuche dakin ta, khadija ma ta shige nata.... har damsel ta dan kwanta bayan tayi sallahr magrib, sai ga shigowar khadija, sosai kayan jikin khadija suka mata kyau, Damsel dai na kallonta har tazo ta zauna bakin gadon tare da cewa "don't tell me yau ma you're not coming downstairs for dinner??" damsel da dan kwana dayan da sukayi har ta dan sake da khadija, dan duc abunda khadija tace mata, instead of nodding her head, toh magana take mata. ahankali tace "I'm full" khadija tai daria sannan ta mike zata fita tana fadin " ban yadda wlh ko kadan ne sai kinci" bayan khadija ta fita ba'ajima ba sai ga Sarah ta shigo dauke da tray, pasta salad ne acikin karamin plate da yaji uban tuna fish tare da apple juice din da sukayi. chan kuma sai ga iman ta shigo da dan cute pyjamas dinta dan suna dawowa aka musu wanka.. Sarah ta ajiye mata abincin akan karamin table din dake kusa da gadon bayan ta gaisheta, ta juya zata fita ta kama hannun iman da ke manne ajikin damsel. turjewa tafara yi. ahankali damsel tace "leave her" juyawa Sarah tayi tafita ta jayo musu kofar. haka iman ta dunga mata surutu kalakala, Damsel dai na kallonta.. daukan abincin tayi tafara ba imam a baki. har ta kusa cinyewa iman ta kauda kanta wai ta koshi, damsel itama spoon biyu kawai tayi kafin ta ajiye sauran tayi ta dauki apple juice din da iman ta rage itama ta sha. ahaka har akayi sallahr isha sannan iman ta bingire a jikin damsel tai bacci.. har wurin 9:30 na dare damsel na kallon yadda iman ke bacci abunta hankali kwance, tunani damsel takeyi kalakala azuciyan ta...bata taba tunanin zatayi rayuwa kirin haka ba. suna nan ahaka har bacci itama yafara daukan ta. Vibration din da ta dunga ji cikin wardrobe ne ya farkar da ita.. kallon iman ta dunga yi data makale ajikin ta, ahankali ta gyara mata kwanciya sannan ta mike ta isa gurin wardrobe din ta bude. fito da jakan tayi a hankali ta bude, dauko wayan tayi dan har ya tsinke. 15 missed calls tagani ajikin wayan. wayan na rike a hannunta tadawo ta kwanta kusa da iman.. ba'ayi minti uku da kwanciyanta ba saiga call ya kara shigowa.. kallon wayan ta dunga yi.."SADEEQ" in bold taga anrubuta.. Sliding tayi sannan ta kai kunnenta a hankali amma bata ce komai ba.. Sadeeq yace "Noor" sai sannan noor tace "good evening.." dan taga duc sadda khadija tayi picking call, ko kuma ankira ta, to sai tayi gaisuwa.. Sadeeq da mamaki soosai yacika amman bai nuna ba, saima murmushi da yayi tare cewa "evening dear, how are you?" I'm fine tace mishi. Sadeeq yace mata "hope you're comfortable staying with khadija and her kids?" kallon iman tayi da take ta sharban baccinta, kafin tace "yeah" sunda dade sosai suna waya da Sadeeq, ducda bawani magana take mishi sosai ba, daga A sai Aa, ganin har sha daya na Nigeria yayi yasa yace" go and sleep babe, we will talk in the morning.. and.. I love you.." kallon wayan kawai takeyi har Sadeeq yayi dropping call din. Saida taga wayan ya tsinke kafin ta ajiye a side drawer tadawo kusa da iman ahnkali ta kwanta.. kiran sallahr farko ya tada damsel dan masallacin na kusa da gidan.. bude ido tayi amma bata tashi ba saida takai minti biyar sannan ta mike ta shiga bathroom.. tana fitowa kuwa ta shinfida sallahyah. ta idar da nafila kenan, lokacin har an tada kabbara a masallaci, mikewa itama tayi dan tada sallahr.. tana idarwa kuwa ta dauki charbi tafara ja ahankali.. Mama kawai take tunawa... she misses everything about her mother.. tana nan ahaka, taji anbude kofar dakin da sallama. Khadija ce ta shigo daukan iman, dogon hijabi ne har kasa ajikinta. da murmushi ta Kalli damsel sannan ta haye gadon ta dauki iman, tana kallon damsel tace ai nashigo jiya da daddare naga sai baccin ku kuketasha, shiyasa nace barin bar maki ita toh.. damsel tana kallon yadda khadija ta shiga kiran imaan dan ta bude ido. nan ne tayi magana ahankali "don't wake her, she's still sleeping.." khadija tai daria tana rike da imaan tace "school bus dinsu 7 daidai yake zuwa wlh, so idan ban shirya su da wuri ba, wucewa yakeyi saidai inkaisu" tana fadin haka tace barin mata wanka da sauri dan har amar yayi.. khadija na fita ba'a jimaba wayan damsel yafara ringing.. mikewa tayi ta isa inda wayan yake ta dauka sannan ta zauna a bakin gado.. tunda ta dauki wayan batace komai ba. Sadeeq yai breaking silent din tare da kiran sunan ta ahankali.. Damsel ta amsa da na'am Sadeeq yace " when you answered a call, you will say salamu'alaikum.. kinji?" damsel "ok" Sadeeq yace good girl, have you prayed? ahankali tace "yes" Sadeeq Masha Allah. So good morning.. Damsel tace morning.. saida yayi shiru for some seconds sannan yace " I need your prayers noor, we are starting our work today in sha Allah.." jin baikara cewa komai yasa tace "ok" murmushi kawai Sadeeq yayi tare cewa I will call you when I'm back from work.. take care.. yana hanging wayan yakoma ta ajiye tare da komawa kan sallaya tacigaba da jan charbinta.. tana idarwa ta mike tare da cire hijabinta ta haye gado.. har tafara bacci taji anbude kofar, iman ce tashigo amar na biye da ita abaya cikin cute uniform dinsu tare beret. iman har ta haye gado tare da cewa "good morning aunty noorrrr" mikewa damsel tayi da sauri tana kallonsu cikin cute and neat uniform dinsu.. tana kallon yaran tace "morning cuties.." amar yace bye aunty noor iman ma tabi bayanshi.. dunda suka fita tananan a yadda take kafin takara komawa ta kwanta.. karfe bakwai da rabi al'amin har ya dau hanyar zuwa wajan aiki.. tunawa yayi yace zai kira nabeel, sau biyu ya buga amma not reachable, ajiye wayan sannan yacigaba da tukin shi. yana isa hospital din da yake aiki kuwa ba bata lokaci yafara duba wata emergency patient da aka kawo....


....nabeel kuwa yana gama shirin zuwa aiki karfe 8 daidai yafito, saida ya fara shiga motar Sadeeq yayi worming, dan tun ran da zaikai Sadeeq airport Sadeeq yabashi Keyn motar, yana dawowa gida kuma yaje ya dauko motar dan yarinka dan worming kar battery din yayi sanyi.. yana gama worming yafito yashiga nashi yatada sannan ya fito. saida ya tsaya gidan Sadeeq yaduba Joseph to make sure everything is fine kafin yafito, har zai shiga motor shi, saikuma yadawo yana tambayar Joseph ko yasan inda ogan shi yakai damsel. Joseph yatsaya nazari sannan yace "Who be damsel oga??" nabeel ya dan yi tsaki kafin yace "the lady that was in this house" Joseph yace "okkkk, u mean oga wife?? na together them go na."nabeel da baikara bi takan Joseph ba yashige motar shi ya dau hanya.. daukan wayar shi yayi ya kunna dan tun jiya da daddare yakashe, ta dalilin damun shi da nadeerah tayi da kira.. (niko nace ashe har yanzu bata hakura ba" bayan ya kunna ne yacigaba da tukin shi har office... karfe goma daidai damsel ta tashi daga bacci, wanka tayi tasa abaya baki da gyalenshi sannan ta sauko downstairs ahankali.. khadija na palo tana packaging small chops a very cute container da akayi ordering jiya da daddare. tana ganin damsel da kamshinta duc yagama cika palon, tace "aunty noor is awake.." tare da murmushinta.. Damsel kallon abunda khadija takeyi sannan takaraso cikin palon. Sosai packaging din yamata kyau.. khadija na kallonta kafin tace "you want to learn how to do this too??" da sauri damsel tace "yess" khadija tace don't worry dear bari sarah tahada miki breakfast dinki, idan kika gama sai muyi tare. kwala ma Sarah kira tayi, tana fitowa tace "you can make her the breakfast now please" Sarah tace "yes ma tare da kallon noor tace good morning aunty" damsel ta kalleta itama tace "morning" khadija taciga da abunda takeyi tare da nuna ma noor wasu abubuwa awajan..

....bayan al'amin yasamu break yadawo office yafara duba wasu files..wayan shi dake kusa da shi yafara ringing, yana dubawa yaga "uncle abu" bayan ya dauka Sun gaisa ne yafara ma uncle din nashi magana "uncle abubakar dama inaso in maka magana akan yarinyan da kazo kwanaki har sau biyu kana nima, toh bansan ko anganta ba" abubakar yace "kajika da shashanci fa ameenu, da anganta da bakaji labari ba, tunda ai yar uwar ka ce kaima." al'amin da baiso yace komai tukunna, dan bai tabbatar ba yasa ya dan yi murmushi tare da cewa "toh Allah ya bayyanata cikin lafiya" abubakar yace "ameen ya Allah, ka gaida mun da iyalin" da haka sukai sallama... nazari soosai al'amin yashiga yi kafin ya dauki wayar shi kara dialing numbern nabeel.. ringing biyu nabeel ya dauki wayan, nabeel yafara magana tare da cewa "dan iska ashe Kana da number na har yanzu.. ai kallon ka dama nakeyi" al'amin yai daria sosai kafin yace "kaidai baza ka taba chanzawa ba wlh. anyways nakira intambayeka ne, and don't even dare saying bakasaniba, dan nasan kasani" nabeel yai shuru kafin yace "what about??" ahankali al'amin yace "do you have any idea about that girl ??" nabeel yace which girl?? al'amin yace "Sadeeq's wife to... " bai karasaba nabeel ya mike da sauri.. " where's is she??? ".

....shock ne yakama al'amin ta dalilin yadda yaji nabeel yayi mugun zabura. immediately al'amin yace "calm down guy,.. what's the issue??" nabeel yace noo baza ka gane bane, dama gidan ka ya kaita?? al'amin da yaga nabeel na niman birkita mishi lissafi, yace "haka nafada maka??.. we spoke about the girl tare dashi ne some few days before he left, kasan guy din naka da nukunuku... so gani nayi yakamata muyi bincike akanta as a friends concern you know.." nabeel ya sauke ajiyan zuciya kafin ya koma ya zauna.. "now please al'amin, I want you to do something for me,... tunda har yayi maka maganar yarinyar, telling you her whereabout won't be an issue.. al'amin yai cutting dinshi da sauri. "so wht are you trying to say now?? " calmly nabeel yace "call him right now and ask him where he took the girl.. amma kar ka nuna munyi waya da kai please...sosai al'amin yaji mamakin rainin hankalin da nabeel keson yai mashi, saidai bai nuna ba. "soo, now tell me about the girl, whre do they meet??" nabeel yai shiru for a moment kafin yace.. "dude.. I can't say anything to you right now.. but please do me this favor by calling Sadeeq" al'amin da baison suyi ta dragging maganar yace "aright friend, I will do that.. lemme attend to a patient yanzu, we will talk duc yadda ake ciki..da haka yai hanging call din. Nabeel kuwa yana ajiye wayan ya buga table din gaban shi da karfi.. Praying and hoping, Allah yasa Sadeeq yafada ma al'amin inda damsel take.. He needs to bring an end to this stupidity...


....al'amin shima tunani ya dunga yi a office dinshi. hada hannun shi yayi duka biyu a kanshi ya dunga dogon nazari..." why is this issue getting complicated?? and why is nabeel refusing to say anything about the girl?? sannan meyesa ya kawo ta gidanshi?? where is her family,... and if that is the case, meaning yasamu answer din da yake nima kenan.. tohh indai haka ne, ina Sadeeq ya hadu da ita? Uncle dinshi dai yace mishi tana cikin wani rayuwa ne da be dace ba, but wani kirin rayuwa kenan da har suka hadu da Sadeeq.. Knowing fully who Sadeeq is, dama dai nabeel ne da zaiyi saurin gane me uncle din nashi ke nufi.. kara rike kan shi yayi tare da furta Innalillahi'wainnailaihi'raji'un....

......aiki sosai Sadeeq sukeyi a Spain ba kama hannun yaro. yau kwanan shi hudu kenan and sosai kuma akesamun improvement a aikin, dan ko samun kiran damsel bayayi, locakin da zai dawo gida Kuma dare yayi sosai and bayaso ya tasheta.. damsel kuwa yau yawo sosai sukayi cikin garin Lagos ita da khadija sunje gidan wata kawar khadijan suyi congratulating dinta dan ankara ma mijin ta girma awajan aiki. dakanan suna hanyar dawowa gida suka tsaya a wani babban shago na dinki.. suka amsa hadaddun dinkunan da suka ma damsel.. wajan kala bakwai, kuma duc khadijan tasiya mata atanfofin ganin kayayyakin nata ba atanfa aciki..suna Karba suka kama hanyar gida.. da dawowar su gida kuwa damsel ta shige daki tai wanka tare da dauro alwala dan har karfe uku ya gota. daya daga cikin atanfofin da suka karbo ta cire riga da skirt tasa.. sannan tasa hijabi ta tada sallah.. tana idarwa ta cire hijabin ta dauki bakin hula tasa dan takasa daura dankwanlin kayan. kallon kanta ta dunga yi a madubi, ganin kirin yadda shape dinta yafito soosai yasa tasamu Kanta da jin kunya.. dawowa tayi ta maida hijabinta sannan ta fito dan yau khadija tace ita zata hada musu dinner.. a steps suka hadu da khadija tana kokarin haurowa dakin ta. khadija ta kalleta sai kuma tayi daria kafin tace, meye kuma nasa hijabi acikin gida?? Halan you're not a fan of native wears ne?? Damsel dai tana kallonta. khadija da batasan sadda ta jawo hannunta suka koma sama ba. dan sosai takeson damsel ganin yarinyace sosai and there's soo much she needs to learn, barin ma kirin maganar da mijinta yamata akan damsel din shekaran jiya, idan ya tabbata da gaskene, to zatafi kowa farin ciki dan sosai takejin damsel a ranta. Komai nata yana birgeta sosai. Suna Shiga daki kuwa ta cire mata hijabin... mutuwar tsaye khadija tayi, ganin hallitar jikin damsel... bata san sadda ta rungumeta ba tare da cewa halan shiyasa Sadeeq ya cika miki akwati da abayas and jalbabs.. rufe ido damsel tayi ahankali.. khadija ta jawo mata hannu suka fito daga dakin tare da cewa wlh dan dai kawai kar insa bawan Allah dawowa Nigeria bai shirya bane, yanzu da na dauki Mad pictures dinki na tura mishi wlh... da haka suka shiga kitchen. khadija ta nima kujeran daya daga cikin kujerun dining din kitchen ta zauna, Sarah Kuma ta fara hada kayan miyan da zata ma damsel blending. bayan tagama hada komai tazo gurin khadija tana nuna mata ko ya isa, khadija dake ta faman yin ma damsel hotuna tace "I'm not the one cooking ai, show it to aunty noor" damsel na jingine da cabinet din kitchen din, sarah ta karaso tana nuna mata ko ya isaa. kallon kayan miyan damsel ta rinka yi tana nazari da tuna abunda khadija tace mata.. ( idan tanaso stew yayi dadi sosai to kar ta cika mishi tumatur, tattasai da attarugu yaji, sai albasa yafi yawa) ahankali

Please Login or Register in order to submit comment