Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

firgice na ganni a wanni babban daki ya tsaru ba kadan ba, a hankali nafara recalling komai, ihuu na kwala tare da salati. Wani mutum ne ya shigo dakin idon shi kaman garwashin wuta ya dakamun tsawa. ba alaman yana sa goshin shi akasa, where's is my mother please, na tambayeshi ina kuka, so you don't even know your mother is death? nima ya jefomun tambaya ya na mun wani matsiyacin kallo, kafin ingama comprehending abunda yafada aka bude dakin aka shigo, wasu Mutane maza su biyu a kalla zasu kai shekara hamsin da biyar, dayan yace ka ganta fa dazun nan kawunta ya siyarmun da ita wai uwar ta tarasu shikuma bashida kudin kula da ita. Dayan ya na girgiza kai yace amma kayi sa'a fa dan wannan danya take jagab. dariya Dayan yayi sannan suka juwa suka fita, sun fita ba da dadewa ba sannan daya daga cikin wa'innan mutanen yashigo, a zabure na mike, matsowa kusa dani yayi, meye sunan ki? ya tambayeni, ban bashi amsa ba, kada kafadanshi yayi sannan yace I will be calling you " damsel" jayo ni yayi da karfi ya wurga ni kan kado da karfi, ina kuka ina kiran mama yarabani da budurci na... And that was the beginning of everything...

10 years later..
"coconut beach,badagry", mutane ne kalilan a wannan Beach din ranan, kowa na harkokin gabansa. Kasancewar weekdays ne ba mutane sosai. Chan sai ga wata kyakkyawar matashiyar yarinya tashigo, doguwa Fara soll da ita, suman nan nata baki sidik har gadon baya. yar kimamin shekaru ashirin da uku ne a duniya. Bikini ne a jikinta, bakin bra da dan short skirt me tsagu a gefe, a cikin tsagun kana ganin baqin pant dinta, sai baqin madubin ido dake idon ta, hips dinta kuwa kaman zasuyi magana. Salma kenan. tana tafiyan nan nata a hankali kamar ana tilasta mata, tare da bodyguards dinta guda biyu a baya. da shigowanta kuwa kowa ya sauke idon shi akanta, kaman za'a cinye ta da kallo. itako ba Wanda ta kalla, chan wajan ruwan ta matsa sannan tafara sana'an nan nata na kura ma ruwa ido. takan sa akawo ta idan bamutane dayawa,tazo tai ta kallon ruwa har yamma sannan a koma da ita. A chan dan nesa da ita kuwa, wasu yan samari ne guda biyu, daya na kwance a kan dan kujerun nan da ake huta wa a beach, dayan kuma yana tsaye hannun shi duka biyu a aljihun wandon sa, yana sauraron magananar da aminin nasa yake mishi. wlh Sadeeq ina fada ma, yarinyan ko kaska albarka, ta takura mun ga naci, ni na fada mata bani da ra'ayin aure nan kusa. Wanda aka kira da Sadeeq yana dai tsaye ya kafa mishi ido yana sauraron sa, Chan ya bude bakin shi a hankali kaman baya son magana yace, then why sleeping with her when you know you're not going to wife her? daria dayan yasa yace dude, baza ka gane bane, she's kinda sweet and after all ita take kayo kanta. ido Sadeeq ya kura mishi, sannan yace nabeel.. when will you ever change? Nabeel yakara tuntsirewa da daria yace kaidai kayi tazama a haka, kana da kudi ga kyau, ga ilimi and duc inda kabi mata binka sukeyi amma kai kawai ba wannan bane agabanka. Haba Sadeeq, you need to grow up wlh. Sadeeq da nabeel abokan juna ne tun suna kanana, Sadeeq da nabeel haifaffun yan kano ne. Sadeeq su biyu iyayensu su suka haifa a duniya, shine na farko sai kanwar shi Hauwa'u. Baban su Alhaji Muhammad babban dan kasuwa ne da ba wanda baisan shi a Nigeria ba ta fannin motoci yanzu haka yana da babban kanfanin motoci a Lagos inda yaba danshi Sadeeq yana kula dashi. Maman su kuwa balarabiya ce, a Egypt suka hadu da Alhajj Muhammad, yatafi wani business na wata biyu, anan ya hadu da hajiya Aisha, Maman su Sadeeq, inda suka kulla so Mai karfi har suka Kai ga yin aure sannan ya dauko ta zuwa garinshi Kano. Nabeel kuma yaron abokin Alhaji Muhammad ne baban Sadeeq. Mai suna Alhaji Mukhtar, shima haifaffan Dan Kano ne inda yake business din man fetur "Mukhtar petroleum", yana da gidan Mai ba iyaka. Matar shi daya hajiya khadeeja yar cikin kano ce itama, sai yaran su uku. Nabeel ne babba, sai Mai binshi Abdulrazak, sai autar su zainab ana kiranta da zee.. tun primary Sadeeq da nabeel suke tare, kuma suna abokanta ka mai ban Sha'awa, nabeel baya son yaga bacin ran abokin shi yanzu sai kaga ya dabur ce. Nabeel shine mai dan haya niya idan yaso, Sadeeq dai saidai yayi ta binshi da ido.
Bayan Sadeeq yagamajin abunda nabeel ke cewa, ya girgiza Kai kawai, hayaniyan da yaji a bayansu chan dan nesa dashi su ne, ya yasa ya juya da sauri ya na kallon wajan. Bodyguards din salma ne suka dunga dukan wani, wai yazo yanamata magana. they warned him amma yaki ji. Ito kuwa kaman bata wajan, dan duc wannan draman da akeyi idon ta na kan ruwan take ta kallo yana ta ambaliya, bata ma juyo balle tasan me ke faruwa. sai ma tattara suman kanta da takeyi tana kitse wa waje daya, dan ya dameta. Ido Sadeeq ya kura mata, Chan ya juyo ya kalli abokin nashi yana tambayan shi akan yarinyan dan yasan nabeel baya rabuwa da zuwa nan beach din, shiko zuwan shi na biyu kenan, yau ma dan yamishi alkawarin ba zaizo da nadeera bane, shiyasa ma ya biyo shi. Kallon wajan nabeel yayi sannan ya juyo ya gyara kwanciyan shi. Kai kuma duc ajinka da wanchan zaka fara? nabeel yana magana ne yana mike wa dan yasa kayanshi su yi haraman gida. Who's she? Sadeeq ya kara jefo mishi tambayan. ganin seriousness din da ke fuskar Sadeeq ne yasa nabeel yace Look here man, take your eyes off that girl, she's not in anyway your type, da kake ganin ta haka toh karuwa ce wallahi, high class prostitute kuwa. Yana gama fadin haka yasa kayan shi tare da Zura wayoyin shi a aljihu yace su wuce. juyowan da salma zata yi dan ta gaji da kallon ruwan, Suka hada ido da Sadeeq... Wani mugun faduwa gaban shi yayi, shi yafara dauke idon shi da sauri sannan yabi bayan nabeel suka kama hanyan gida.. Suna hanyan komawa gida, acikin mota Sadeeq ya ce look nabeel joke apart, wacece yarinyan? nabeel da har ya manta sunyi maganan wata mace da Sadeeq, dan ko kadan ba halin Sadeeq bane magana akan mace. Da mugun mamaki nabeel ya kalleshi yace Sadeeq banji mamaki ba yanda naga farat daya ka rikece akan yarinyan nan, she's mind blowing tabbass amma wlh bawasa nake maka ba, karuwa ce, expensive one kuwa, Damsel is her name. a " dollars and pounds" take zama, ba kowa ke ganinta ba, over one point ake sawa kafin a ganta. saidai ko dawasa nabeel bai fada mishi yana zuwa wajan ba ducda dai zuwa kawai yakeyi ya Shaka ta. Kuma ko kadan baikawo Sadeeq zai yi wani halaka da mace kirinta ba, dan yasan wanene Sadeeq. Da haka har Suka shigo cikin garin Lagos. direct unguwan su yawuce da su, a banana island, dukkan su gidagen su anan yake, ajiye Sadeeq nabeel yafara yi yace mishi zai shigo anjima,sannan Shima ya yi hanyan gidan shi, dan basu da nisa.. Sadeeq na shiga gida yafada bandaki ya watsa ruwa, yana fitowa ya sa jallabiya ya feshe jikin shi da turaruka kaman baisan zafin su ba, sannan ya tada sallahn LA'asar din da suka yi Missing, yana idarwa ya cire jallabiyanshi sannan yafada kan gado ya hau tunanin abunda nabeel yafada mishi akan damsel.. Da wannan tunanin ya dau aniyan komawa cikin badagry a ranan dan ya hadu da Damsel...
Suna iso wa bodyguards dinta suka tsaya a daidai kofar dakin ta, itakuma ta shige domin ta dan watsa ruwa. tana gama wankan ta dauko alwala sannan ta fito daure da guntun towel a jikinta, takowa tayi ahankali har gaban dressing mirror dinta dayake ashake da mayuka ga turaruka masu mugun tsada. Da sunkai rabi dama za ayi mata ordar wasu. a hankali tagama shafe shafenta sannan ta karaso closet dinta ta tafito da jallabiyanta Mai tsanyi da taushi. tagama shirinta sannan ta feshe ko ina da turare. Hawa kan sallayan tayi a hankali da dau hijabinta tasa sannan ta tada sallah, ta dade tana addu'o'i tana nima ma kanta da hahaifiyar ta Rahma. sannan ta Mike ta cire kayan ta maida komai inda suke domin yau tace bata bukatan kowa yamata, dan komai yi mata akeyi. ba komai a jikinta, daga ita sai pant, nan ta bude wani drawern da ke tare da madubi ta dauko wani matsiyacin nighty tasaka ta dan kwanta kenan aka kwankwa sa kofar aka aka shigo, wata budurwa ce da baza ta wuce sa'ar ta ba takawo mata wani hadin madara mai zafi a kofi. Ajiye mata tayi akan karamin table din da ke kusa da ita sannan ta juya ta fita. a bangaren Sadeeq kuwa yana fitowa daga masallaci bayan sunyi sallar magriba, yadawo gida ya chanza kayan jikin shi zuwa T-shirt da Wando. daukan makullin matar shi yayi tare da Cash card dinsa sannan ya kara feshe jikin shi da turaruka sannan ya fita. In less than one hour 15 minutes ya shiga badagry, daukan wayar shi yayi yafara binciko inda location din " dollars and pounds" yake. Nan da nan yagano gurin, sannan yaci gaba da tuki har cikin wajan, waje ne kayatacce inda sai wane da wane suka shiga. Horn yayi aka bude mishi gate, waje ya nima a parking a parking space, yayi parking motar shi sannan ya zauna na wajan minti goma yana tunani kalakala a zuciyanshi, chan yayi karfin halin bude motar yafito. Manyan mutane ne awajan da yan mata Sun zagaye wajan, kowa ta na nuna bajintar ta, a hankali yake takowa har ya isa cikin wajan, inda wata ta taso tana takowa kusa da shi kamar za ta karye dan yauki sannan ba kayan mutunci a jikinta. da isowar ta gareshi, ta kashe mai ido sannan ta matso dab da shi, kafin tayi magana sai ga wata hamshakiyar mace yar bariki na karshe, a kalla zata Kai shekara hamsin a duniya. Sigari ne a hannun ta tana busawa. hannu ta bude mishi hannu alaman tambaya, Sadeeq duc ya rikice dan bai taba zuwa waje Kirin hakaba ko a mafarki. da kyar yayi gathering courage sannan yace I want to see damsel. Kallon sama da kasa su biyun suka mishi sannan batare da bata lokaci ba suka fada mishi price dinta ko dan ya girgiza shi. Where am I paying? ya jefo musu tambaya, kallon sa da kyau suka kara yi sannan matar ta nuna mishi inda zai biya, cash card dinsa yabada aka cire kudin sannan aka hada shi da wani suka haura sama tare, knocking mutumin yayi, sai da ya minti biyu sannan ta bude kofar, juyawa mutumin yayi ya sauka kasa, Sadeeq ya shiga dakin...
Salma..✍️11
Da shigowar shi dakin ya maida kofar ya kulle. tana tsaye a bakin windown dakinta fuskar ta na kalllon waje, well come "mister" that's how she addresses every of her customer. I'm not mister, I'm Sadeeq, yafada ya kara gyara tsayuwar shi yana Kare mata kallo. What ever tace tare da juyowa tabar jikin windown, dawowa tayi ta tsaya daidai kusa da shi, ta Kai hannu kenan zata fara unbuttoning mishi shirt din jikin shi, a hankali ya yasa hannun shi ya dora akan nata sannan ya sauke hannunta kasa. Kara gyara tsawuwan shi yayi sannan ya Kalle ta cikin ido, " I'm not here to have sex with you" he said it in a low voice still looking straight in to her eyes. Wani kallo ta bishi da shi sannan a hankali ta juwa ta koma jikin window ta bashi baya. Then, what are you here for? Mister. tajefo mishi tambayan still not looking at him. I want to help you, I want get you out of this mess, you don't belong here. Wani sauti me ma'anoni dayawa ta sauke, still looking outside the window. If you want to help, I think there are millions of less privileged people out there that needed help. You can also go to the hospital, orphanage and many other places, but definitely not here. What is your name? Ya jefo mata tambayan, "Damsel" tabashi amsa a takaice. Wannan ba suna bane. yace da ita. Sunana kenan ta kara bashi amsa. I don't believe you. Yace mata. And I don't care tabashi amsa and getting furious at the same time. you spend that amount of money just to come here and ask silly questions? "Funny" zai kara magana ta juwa a fusace, look mister, I think your time is off, you can leave now. Nan yasamu daman kallon ta sosai, not just to talk about her beauty, but her calmnes gentleness is breathtaking... Yana tsaye, saima hannunshi da yasa a aljihu. When do you want me to come again so we finish our conversation? Kara juwo tayi ta kalle shi, never and mind you, there's nothing like "we" tana fadin haka, ta tako a hankali ta bude mishi kofa, a hankali Sadeeq ya cire hannun shi a aljihu sannan ya nufa kofar fita, yana fita ta maida kofar ta ta rufe... Sadeeq na dawowa wuraren shadayan dare, direct bedroom din shi ya wuce inda ya fada ban daki yayi wanka sannan ya dauro alwala. Yana fitowa yayi sallahn isha sannan yafito ya shiga kitchen, inda ya dafa indomie daya da kwai Dan Sadeeq ba Mai cin abinci bane dayawa. Yagamawa ya juye a plate sannan ya fito kitchen din tare da abincin da goran ruwa a hannun shi. Ajiye wa yayi akan centre table din dake palon sannan ya kunna TV ya dawo ya zauna. Ahankali yake cin abincin abubuwa da yawa suna yawo a kwakwalwar shi. yana gama wa, ya mike ya shiga kitchen ya dauraye plate din ya daura awajan inda ake tsane su. Sadeeq mutum mai tsabtar gaske, yana da kyankami ba kadan ba, ba ko ina yake cin abinci ba. Yana fitowa ya kashe kayan kallon shi sannan yayi hanyan daki.. da isan shi ya tar da wayan shi da haske alaman yanzu kira ya tsinke. daukar wayan yayi ya duba, ganin missed calls hudu yayi, daya na nabeel sai uku na hafsat. Hafsat yarinyan kawar ummin su ne, mahaifiyar Sadeeq, tana son shi kamar ranta zai fita, taki kowa sai shi, shikuma yana mata kallon Hauwa'u ne matsayin kanwar sa ya dauketa. dan karamin tsaki yayi sannan yayi dialing numbern nabeel, har ya kusa tsinke wa, sannan aka daga. Muryar nadeera yaji. yarinyar da ya tsana a rayuwar shi... Salma..✍️12
chan gefe kuma yaji muryar nabeel nacewa Who asked you to pick my call, da sauri Sadeeq ya tsinka wayan ya jefar a gado sannan ya cire jallabiyan jikin shi, kara wayan yafarayi, ko kallon inda wayan yake baiyi ba har yagama ya tsinke. rataye rigan yayi sannan ya shiga bandaki ya kara dauro alwala. Yana fito wa ya kunna ACn dakin sannan ya hau gado yayi addu'a ya kwanta. har bacci yafara daukan shi, Kira ya kara shugowa wayan, bai duba ba, hannu ya kai ya kashe wayar gaba daya sannan ya koma bacci. bangaran nabeel kuwa fitowa yayi daga ban daki, ganin wayan shi Kare a kunnen nadeerah tana cewa ya shiga wanka, yasa ya karaso da sauri yana mata mugun kallo tare da tambayanta waya bata daman daukan wayar shi. ganin Sadeeq ne kuma ya yanke, yasan yaji haushi ne shiyasa bai kira immediately ba. Juyowa yayi ruwa na diga a jikin shi, yakara bin nadeerah dawani matsiyancin kallo sannan ya nuna ta da yatsa yana surfa mata bala'i kaman zai yi aman wuta, Wlh kika kara daukan mu waya zanyi mugun bata miki rai, I warned you to stop doing this nonsense but you wouldn't listen. tsayawa tayi da taunar cingam din da takeyi dan taga yadda ranshi yayi mugun baci. Shiyasa aduniyanta ta tsane Sadeeq dan aganinta shiyake zuga nabeel akanta. bata dai taba gigin nuna ma nabeel bane dan tasan yadda nabeel din keji da Sadeeq kamar yamishi asiri. toh haka bangaren Sadeeq baya kaunar nadeerah ko kadan basaboda komai ba dan kawai rashin kamun kanta, ga son abun duniya, shiyasa ko kadan bata burgeshi. yayi yayi yaraba nabeel da ita amma abu ya gagara, shiyasa Sadeeq yabashi shawaran kawai ya aure ta tunda daman meya rage a tsakaninsu, ba abunda basayi. nabeel yasan dalilin dayasa nadeerah ta makale mishi. Kawai dai yana tare da itane dan ya rinka rage zafi sannan gashi she's very clean to his liking, sai dai ducda haka idan sukayi fada sai yayi wata bai saurare taba, ta rinka bin shi kenan kaman zata yi hauka sannan yake saukowa. Nadeerah kirin yaran nan ne masu bala'in son abun duniya, tun a makaranta ta dauki wannan hali na duc abunda taga wata da shi to itama sai ta yi ko ta halin kaka, yar ungwan shanu ce a kaduna babanta na nasa'ar kilishi a ungwan sarki, uwar ta kuma malamar islamiya ce ita kadai suka haifa. tana zuwa KASU ne tana karanta mass communication. tana 300 lvl aka koreta ta dalilin fada dasukayi akan wani saurayinta lecturer yana koyar wa a department of applied biology. bata fada ma kowa a gidan su ba dan gidan su gidan yawane kuma da kyar ubanta yake hada kudin makarantar ta, sannan tasan halin babanta, zai iya karya ta takan haka. ahaka har tafara gantalin zuwa abuja Bin manyan mutane iyayenta kuma basu Sabina dan a hostel take, da kyar suka yadda ta koma dan anata karyar anfi karatu sosai. lokacin har yan ajinsu sunkai final year. tana jin haka ta zabga ma iyayenta karya akan ankaita Lagos bautar kasa. toh da zuwanta Lagos anan ta hadu da nabeel a nitre nigh club dake lekki a cikin Lagos. tun daka ranar suka saba har aka Kai iwar haka. Saidai shima karya ta gilla mishi cewa tana tare da aunt dinta ne a garin, iyayenta kuma sun rasu, auntyn ta kuma bata riketa tsakani da Allah, ahaka nabeel yaji tausayin ta Kuma ba Kirin kudin da baya kashe mata to tun daga ranan ta kan kwana a gidan shi, da safe kuma ta koma Chan gantalinta... ahankali ta matso kusa da shi tana mishi kirin kallon nan me dauke mishi hankali, tana zuwa dab dashi ta dora hannunta a kan kafadan shi tanamishi kisisina, runtse idon shi yayi ya Sa hannunshi ya ture ta da karfi har ta kusan buguwa da gado. bai cemata komai ba ya dauki wayar shi ya barmata dakin. tasan koda wasa bata isa ta bishi ba, ahaka tayi kwanan bakin ciki... Salma..✍️13
Sadeeq kuwa yana dawowa sallahr asuba yafara shiri saurisauri dan yana da meeting da manyan baki daga Spain akan new model din mota da suke so suyi producing. Karfe 7 daidai yagama shiri cikin hadaddan bakin suit din shi da yayi matukar amsan kalar fatar shi, yafito kenan zai shiga motar shi 2021 Mercedes AMZ. mai gadi ya bude gate da sauri, motar nabeel ne ya shigo, shiga motar shi yayi yafara worming. Nabeel ya sauko daga nashi motar yazo har inda Sadeeq yake. Ka kyauta yacemishi. Sadeeq da baiko kalla inda nabeel yake ba yace mishi " good morning to you too" nabeel daria kawai yayi dan yasan kafin ya shawo kan abonkin nashi sai yayi da gaske, tun ba akan nadeerah ba. Nabeel ya gyara tsawuyar shi yace going out early today? yeah I have important meeting, alright then we will see in ka dawo. sure yace dashi sannan ya rufe kofar motar shi ya kulle, Mai gadi ya bude mishi gate yadan tsaya suka gaisa sannan ya wuce. Nabeel shima shiga motar shi yayi ya tada yabar gidan. Yana dawowa gida ya tarar har nadeera ta wuce. Dan tasan inyai fushi to kawai tabashi space. Shiryawa shima yafarayi dan yayi haramar office.
yau Damsel ta tashi da mugun ciwon kai, ahaka masu mata hidima suka dunga shige da fice, abinci kuwa kala kala anyi mata ducda tsakura kawai tayi. Suna gama mata komai tabasu umarnin su fita. Ba ajima da fitarsu ba, har bacci yafara daukanta aka bude kofar aka shigo. Deena kenan, tana shugowa ta matso kusa da ita, ohh my babe, ciwon kan ne kuma yatashi yau? Kodai customern jiya ne yayi stressing mun ke haka da yawa? dan naganshi lafiya ya ishe shi ba nawasa ba. girgiza kai kawai damsel tayi without uttering a word. Deena bata kara cewa komai ba, dan tasan Damsel magana na mugun mata wahala, daga a sai aa kawai, yan matan da suke aiki tare ma ko sun hadu wajen cin abinci a downstairs saidai tayi ta binsu da ido, kowa na fadin yanda ta Kaye musu da customomunsu. Sai dai tayi da binsu da ido. Suna zaune ahaka har bacci ya tafi da ita. Lullebeta Deena takarayi sannan tafita ta jawo mata kofar...Deena magajiyan su ne awajan, Hamshakiyar yar bariki ce tun tana da kuruciyar ta. da girma yafara kama ta ne tadena barikin, kudaden da ta hada tare da kadarorunta da ta siyar ne ta hada ta bude "dollars and pounds" anan cikin badagry. akalla tana da karuwai zasu kai goma sha biyar anan wajan saidai Damsel itace jigon ta dan har wajan yafara rugujewa, zuwan damsel wajan ne yadawo mata da martabar wajan. Manyan mutane wanda bata taba tsammaniba ba suna zuwa wajan, da haka kudi banawasaba suka fara shigo mata. Shiyasa yanzu wajan ya kayatu sosai ba kadan ba. Deena ta hadu da Damsel ne a cikin garin Lagos inda taje duba wata kawarta da tayi accident a asibiti. Tafito kenan ta hadu da Damsel zata tsallaka titi ko takalmi babu akafar ta. nan da nan takashe motar ta tafito dan taga Kirin yan matan da take nima, da dukkan alamu kuma taimako take nima. tana fitowa ta nufeta ta, dafata ta tayi, a tsorace Damsel ta juwo har zata kwala ihu, ganin ba Alhaji tanimu bane yasa tayi shuru. ba tare da bata lokaci ba Deena ta jata Suka shiga mota har zuwa cikin badagry. Da isar su tasa aka shiga da ita wani daki tayi wanka aka kawo mata dogon riga ta chanza sannan taci abinci. nan da nan wani wahalallan bacci ya dauketa. tana tashi kuwa tashiga bandaki tayi alwala tafito, tana ta dube dube aka bude dakin aka shigo. Deena ce tashigo da tray dauke da abinci, tana murmushi ta karaso dakin. Me kike nima ta tambayeta, Damsel tabude bakinta da kyar tace sallah zanyi. Deena ta ajiye abincin akan side drawer sannan ta fara danne danne a wayan ta kirar iPhone 13 pro, ana daukar wayan tace yasmeen kawo dadduma da hijabi a dakin da na aiko ki dazu, tana fadin haka ta katse wayar. Cemata tayi zo ki zauna kafin ta kawo. ahakali damsel ta matso ta zauna a gefen gado. suna zaune aka yi sallama, wata yar budurwa zata kai 27 tashigo dakin rike da sallaya da hijibi a hannu.

Please Login or Register in order to submit comment