Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

infada ma babanku, ko shi sai ya tafi ko kawai a daga, kai kuma kadawo gida.. da sauri yace Aa mami zan iya wlh, ina dawowa kuma zaki ganni. mami ta tabe baki sannan tace toh ai shikenan, ganin ka Kuma ai yazama dole, tunda dai abunda mukai niyya ba pasawa zamuyi ba.. Sadeeq da gaban shi yafadi amma bai Cema mamin nashi komai ba, sai ma murmushi dayayi. ahaka Sukai sallama. yakai yan mintoci yana tunanin abunda mamin tace mishi a karshe kafin ya tashi ya yashiga kitchen. mug ya dauko yafito yai hanyar dining, tea ya hada ma Noor yakai mata daki. tana nan jikin windown har lokacin.. ajiyemata yayi, bai cemata komai ba yafita a dakin.. keyn motar shi ya dauka yai hanyar fita. yana fitowa yasama gidan key, juyowan da zaiyi ya shiga mota yaga Joseph a rabe a jikin bango, girgiza kanshi kawai yayi sannan yace open the gate for me. jiki narawa Joseph ya bude mishi gate tare da daga mishi hannu. Hanyar gidan nabeel Sadeeq ya dauka fuskar shi a hade...

....sadeeq na isa gidan nabeel yabude kofar palon ya shigo.. Nabeel yafito kenan daga dakin shi zai shiga gari, face cap ne a hannunshi yana kokarin sawa.. Kallo daya yama Sadeeq, saida yasa hulan shi sannan yadawo ya Kalli Sadeeq din. afusace yace "mr man can i help you???" Sadeeq da kaman jira yakeyi, ya matso dab da nabeel din "I thought yadda nake da kai nabeel yau ko da ache mahaukaciya na dauko, nazaci kai mai taimako na nane...tsinke shi nabeel yayi tare da cewa wlh Sadeeq har gwanda da mahaukaciyar ka dauko than that trash... kasan illar mace me bin maza kuwa?? you think you can change her from Who she is?? ni ba ma wannan ba, uban me take maka a gida har yanzu? after all she's proven to you that she's who she is.. and nothing can change her.. so let her go..wlh idan baka koreta agidan ka ba, kanaji kana gani zata bata maka suna, dan wlh ko niman aure kaje yi akasan kasan yarin yan nan wlh kanaji kana gani za'a hanaka. and Kasaan yadda abbah yake yanzu idan yaji kirin wannan bala'in dayasameka.. Yes dan gaskia sai ince bala'i ai ba kai kadai ba har ni wallahi nashiga uku. duba duc yadda ta chanza ka, kawani fita hayyacinka kamar ba Sadeeq din da nasani ba... Nahh.. taimakon ya isa haka, Wanda kayi abaya kuma Allah yabaka lada.. Sadeeq duc yana kallon nabeel tun da yafara magana har ya gama bai ce komai ba. karasawa cikin palon nabeel dan ya dauki keyn motar. ahankali Sadeeq yabude bakin shi "now listen to me NABEEL.. that girl... she's now part of me.. I want to marry her and I Will marry her in sha Allahu... Wani kirin juyowa nabeel yayi yana kallon Sadeeq din tare da cire pcap din shi, zaiyi magana Sadeeq ya daga mishi hannu, "I'm not done talking.. ahankali ya tako har inda nabeel yake sannan yacigaba da magana,... we've been friends since childhood,.. nothing has ever come between us.. and nothing Will.. dan haka ina rokon ka.. hannun shi yakai ahankali ya riko na nabeel din duka biyu, idon shi duc ya tara hawaye yana kallon abokin nashi.. Please nabeel this should be a secret between us, no one has to know who Damsel is.. No one, her past is her past.. I know this is going to be hard on you, but don Allah for my sake, don't look at her as damsel ever again.. But noor. kila wannan shine jarabawa na aduniya kuma insha Allahu Allah zai bani ikon cinyewa, you know me soo well nabeel, kasan bin mata ko kadan banawabane, so like i said kila nawa jarabawan kenan... I need your full support, Brother.. hawayen shi suka gangaro a fuskar shi ya karishe maganan tare da rungume nabeel din.. sun kai minti biyu ahaka sannan yasake shi a hankali yai hanyar kofa ya fita.. yana fita nabeel ya nima waje ya zauna, jikin shi duc yayi sanyi.. fitan da baiyi ba kenan. Sadeeq kuwa yana fita ya dawo gida. wani mugun ciwo kan shi ke mishi. adaddafe ya bude motar shi yafito, Joseph ne yakaraso zai fara aikin roko.. dakatar dashi Sadeeq yayi, tare da rike kanshi da yai mishi mugun nauyi.. Ahankali yakarasa har ya cire Key a aljihun shi ya bude gidan ya shiga.. yana shiga ya maida kofar ya kulle.. akan 3sitter ya zube hannunshi na rike da kanshi...

....ya Kai minti goma yana kwance kuma kan shi a rike, tafito ahankali sai kuma taja ta tsaya,.. Kallon shi takeyi.. bata san ko bacci yakeyi ko kawai ya lumshe idon shi ne. tajuya zata koma daki taji muryar shi," you want something Noor? dawowa tayi ahankali ta tsaya daidai kan kujeran da yake.. " I want... sai kuma tayi shuru.. ganin haka yasa ya mike, yabude baki zai mata magana.. toshe bakin shi yayi ya mike da sauri yai hanyar daki... bin shi tayi da kallo har shiga.. karasawa cikin palon tayi zata zauna, sai kuma ta juya tai hanyar dakin.. takai minti uku a tsaye, kafin ta murda kofar ta shiga.. ranan farko da ta shiga dakin kenan, everything is so intact kaman ba dakin namiji ba. ducda ba sosai take gani ba dan yamma yayi kuma wutan dakin a kashe ne tana tsaye a bakin kofar tana jin yadda yake amai acikin bathroom din. bin dakin tayi da kallo "everything is white sai curtains din dakin baki with white inners, unlike na dakin ta da komai cream. tana tsaye har ya fito.. bai lura da ita bama dan dakin da dan duhu.. gadon shi ya nufa ya kwanta yana maida nunfashi.. ahankali takaraso ta tsuguna kusa da shi. bude idon shi yayi jin mutun akusa da Shi "Noor ya kirata sannan ya mike a hankali.. You want tea? ta tambayeshi. murmushi yayi sannan yace "zaki raka ni insiyo magani? baibari ta amsa ba ya mike ya kunna wutan dakin, nan takara ganin kyan dakin soosai. tana durkushe a inda ya barta, sai kuma ta mike tai hanyar fita.. wanka ya koma yayi a daddafe dan lokacin zazzabi ke shirin rufeshi. yana gama komai da kyar yayi sallah sannan yakara bin gadon ya kwanta.. nan kuma bacci ya daukeshi. ta kai minti biyar tana zaune a Palo, hijab ne tasa har kasa.. ganin baifito ba yasa ta mike ta koma dakin..takai minti biyar a tsaye tana kalllon yadda bacci mai nisa ya daukeshi, ahankali ta isa gefen gadon ta taba jikin shi.. a tsorace taja da baya yanda taji jikin yayi zafi soosai. nan da nan ta tuna kirin zafin da jikinta mamanta yayi kafin tarasu.. aibata san sadda tafito ba tai hanyar waje, Joseph na wanki a kofar dakin shi.. yana ganin ta yai hanyar gate ya tsaya.. (lol) Kare mishi kallo tayi sannan tarasa abun cewa,.. chan dai tace mishi "can you drive?" Joseph yace madam I can't take you anywhere ooo please.. tsaki tayi ahankali sannan tace "he's sick.. can you drive? nan Joseph yagane me take nufi.. ido waje yace oga no well?? juyawa tayi tai hanyar shiga gidan, Joseph yabiyota da sauri suka shiga gidan. har dakin shi Joseph na biye da damsel.. bacci kawai yakeyi, ganin Joseph din kaman he's dumb yasa takarasa har kan gadon. ahankayi takai hannun ta fuskar shi. tarasa yazatai ta tashe shi. Joseph dai na ta wikiwiki da ido. "wake up tace tare da dan buga hannun shi kadan. Sadeeq kuwa kaman a mafarki yake jin duc abubuwan nan, Joseph yakara cewa ogaa, ahankali Sadeeq ke bude idon shi. Da sauri taja da baya. nan Joseph yakara cewa sorry oga. Sadeeq ya bude idon shi gabadaya daya ji muryar Joseph, tare da mikewa. Itadai tana rabe a gefe. matse idon shi da hannu sannan ya mike a hankali yana kallonta, "let him drive you to the hospital" Sadeeq ya kalleta sosai.. he wanted to say no but da yakara wani tunani, for her to even think of calling Joseph.. "OK kawai yace mata sannan ya kalli Joseph din yace wait for me outside. Joseph na fita itama ta juya zata bi bayanshi, riko ta yayi ta baya sannan yace " So you care about me Noor?" batace komai ba, murmushi yayi sannan riko hannun ta har kan bedside drawer ya dauki car key dinshi sannan suka fito har waje.. Joseph na tsaye yaga Sadeeq ya nufa hanyar motar shi tare da damsel.. open the gate yace ma Joseph sannan ya bude mata front seat tashiga. zagayowa yayi ya tada motar ahankali suka fita.. a daddafe suka isa pharmacy. allura suka mishi tare da hada mishi magunguna.. tana mota har yafito ya shiga ya tada sukadau hanya, saida ya tsaya ya siyamata Pizza da drinks, saikuma take away dayasima Joseph na fried rice and chicken part sannan dau hanyar gida.. ahankali yace noor, juyowa tayi suka hada ido. maida kan shi yayi wajan tuki kaman bazai ce komai ba.. chan yace "where are you from?" I don't want to talk about it tace. baisake cewa komai ba har suka isa gida. Jinginar da kanshi yayi kan seat din motar bayan ya kashe duc ya gaji ga jiri dayafara ji dan cemusu yayi yaci wani abu sannan suka mishi allura. Joseph yakaraso yamusu sannu da zuwa. Da hannu kawai ya amsa mishi tare da mika mishi Key yabude gidan. yana budewa yadawo ya bude bayan motar ya kwashe komai ya kai ciki ahankali yace "let's go inside noor" saukowa tayi shima ya sauka ya kulle motar sannan yabita a baya.. cema Joseph din yayi ya tsaya, yana shiga ya dauko abincin ya mika mishi. Komawa ciki yayi ahankali ya isa palo.. Itadai tana kallon shi. zata shiga daki taji yace "make me a cup of tea please" yadda taga yayi ranan ta mishi takawo. mikewa yayi ya karba yana murmushi. "I bought you pizza" yana fada ya nuna mata ledan akan centre table, shikuma yafara shan tea din. daukan ledan tayi ta koma kan kujera ta zauna, dan tana bala'in son pizza. kussan kullun abunda Deena kemata ordering kenan da daddare. Sadeeq har ya kusan gama shan tea din shi, kamar ance yajuya.. har taci slice biyu tana kan na uku suka hada ido da Sadeeq.. maidawa tayi ta ajiye dan batama san ya kallonta ba.. ajiye cup din Sadeeq yayi tare da mikewa yazo kusa da ita... daukan Wanda ta ajiye yayi, ahankali yakai bakinshi yaci kadan sannan ya kai mata sauran baki.. zata kauda fuskar ta yace "eat" ganin kirin kallon da yake mata yasa ya rufe ido sannan ta bude bakin.. cold lips dinshi taji instead of the pizza.. bata bude idon ba saida taji ya dauke fuskar shi. tana bude wa kuwa suka hada ido.. "you're gorgeous Noor" murmushi yayi tare da ajiye pizzan sannan ya mike yakoma inda yake... tunanin inda zai kaita ta zauna yashiga yi kafin ya dawo. dan yaso tafiya da ita, amma hakan yaga baidaceba, ganin ba auranta yayi ba. yasan tare zasu rinka kwana and he can't endure being in the same bed with her without nothing happen between them, he doesn't want to do anything that will make her thinks otherwise about him.. dole ya nima mata inda zata zauna.. ko yakira abokinshi al'ameen ya rokeshi tadan zauna tare da matar shi kafin yadawo? da wannan tunanin ya yanke shawaran yakira shi gobe.. damsel kuwa tagama cin iya Wanda zata iya sannan tadau chivitan ta tafara sha. tunanin yadda zata gayamishi tana bukatan pad takeyi, dan dazu abun da tazo fada mishi kenan takasa, she's expecting her period any moment. kallon shi tayi zata fada mishi, sai kuma ta pasa, mikewa tayi tai hangar dakinta, dan hijabin da ke jikin ta ya isheta, tana shiga tafara cire kayan jikinta sannan tayi wanka, tai shirin bacci..


.....Sadeeq ma dayaga ma abunda yakeyi, dauka sauran pizzan yayi ya kai kitchen yasa a fridge, sannan ya kullo kofar yashiga nashi... da asuba damsel ta mike zata yi sallah, mezata gani inba stain all over ba..

....rasa abunyi damsel tayi, dan haka bai taba faruwa da ita ba. karfin hali tayi ta mike ta shiga bandaki. minti goma tayi sannan tafito daure da towel. Chan bakin window ta tsaya dan takasa zama ma, kallon yadda duvey din yai stain kawai takeyi. gajiya tayi da tsayuwa, ahankali takaraso bakin gadon ta tsuguna sannan tadora kanta a bakin gadon... Sadeeq kuwa 6 daidai ya shigo gida, yana shigowa ya dauki wayan shi yai dialing numbern wani a office din, sunkai minti 7 suna magana yana fada mishi duc abunda yakamata ayi for the day, sannan sukai sallama akan if there's anything yakirashi.. suna gamawa ya mike ya shiga kitchen dan ya dan hada tea yasha.. yanagamawa ya babbale magungunan shi yasha, sannan yakara mikewa akan 3sittern palon.. tunanin nabeel kawai yakeyi dan yayi missing din dramas din shi, murmushi yayi tare da daukan wayar shi yayi yakira nabeel din. bugu biyu nabeel yadaga Sadeeq yafara magana "are you still mad at me friend?" Nabeel ya ce "nahh, not anymore ai, hope you're good?" Alhamdulillah Sadeeq yace tare da cewa I miss you bro. Nabeel yace "same" zanshigo ai idan nadawo, yau da noodles dinka zanyi dinner. Sadeeq da har ya manta when last ya dafa indomie, murmushi yayi sannan yace "alright then, I will be expecting you" har Sadeeq zai ajiye wayan, nabeel yai sauri yace "hope Joseph is still around??.. Sadeeq yakara wani murmushin tare da cewa idan kazo zakagani, sannan yai hanging wayan tare da mikewa yai hanyar dakin damsel... Sallama yayi tare da tura kofar.. Noor!! yakira ta da dan karfi tare da karasawa cikin dakin da sauri dan ganinta yayi a kwanche a kasa sai towel da ke daure jikinta.. Dakota yayi zai kwantar a kan gadon, ganin blood stains a towel din ne yasa gaban shi yai mugun fadi, kwatar da ita yayi tare da tallabo fuskar ta yana kiran sunanta. ahankali ta bude idanuwanta dan ba bacci takeyi, tsaban kunyar shi ne yasa ta rufe ido, tarasa dalilin dayasa take kunyar Sadeeq yanzu. ta tabbata dawani namijin ne, toh abunda zai dameta, amma yanxu Sadeeq ko jikinta ma baso take yanaganiba. yana ganin ta bude ido sai kuma tai sauri tajawo blanket din ta rufe jikin ta. Sadeeq is trying to understand what's going on,.. "go out please" tace mishi tare da kara kudundunewa. fita yayi da sauri yazo Palo, daukan wayar shi yayi har zaiyi dialing numbern sistar shi,sai kuma yai wani tunanin yakira nabeel. Nabeel da tuni ya dau hanyar office, yana driving yaga kiran abokin nashi, dauka yayi tare da sawa a speaker, Sadeeq da duc a daburce yake, yace Nabeel please what can man do when a lady is bleeding? Nabeel da tambayan yai mishi wani kiri.. chan dai yace bleeding kuma? who's bleeding? Chan kuma bayan ya dago abunda Sadeeq din yafada, yace "dallah kar ta raina maka wayau,.. Period din ne bazata ta iya fada maka ba? Ko pad din ne baza ta iya cemaka kasiyo ba?" Sadeeq nan da nan yagane, dip yai hanging call din, tare da daukan phone din shi da car key yafita. minti 20 yayi yashigo gidan.. da sauri ya nufi dakinta da katon leda a hannu, tafito daga bandaki kenan daure dawani sabon towel ajikinta. kunyar hada ido da shi takeyi, Amma ganin whole pack din pad a hunnun shi ne yasa ta dunga kallon shi da mamaki.. ajiyemata yayi tare fita ya kullo mata kofar. tunani ya dinga yi a palon, dama abunda taketaso ta tambayeshi kenan takasa?? yayi 15 minutes kafin ya mike yai hanyar dakin ta da sallama. dogon rigan da tasa jiya yaga ta maida. more reason why he wants to take her out today."you need more wears ko yace mata". batace komai ba, duc kunya ya kamata, wucewa gurin gadon yaga tayi zata fara cire zanin gadon.. haka ta dunga dragging kaman suna dambe, kallon ta kawai yakeyi,.. chan dai da taga ba iyawa zatai ba, haushin bala'i yakamata ,ga sadeeq ya nannade hannu yana kallonta. bude baki tayi furiously tace "look, I don't know how to do all of this, if you want to see what i can do perfectly, then come lie down on the bed." Sadeeq ya kalleta sosai cikin ido, sai kuma yai murmushi, takowa yayi har inda take ya riko hannayenta duka yana kallonta.. "let me get married to you first, then I will see how good in bed you are.. but for now...,go to my room and sleep, I will do all of this"
... bata yarda ta kalleshi ba tafita ahankali ya bita da kallo.. tana fita ta wuce Palo ta kwanta.. hawaye ne ya gangaro mata. to meye anfaninta a rayuwan nan, a matsayinta na ya mace ache ba abunda ta iya a duniyannan? only to sleep with men?? wasu zafafen hawaye suka Kara gangaro mata... Sadeeq sai da ya chanza mata komai na dakin sannan yacire zanin duevey din yahada da zanin gadon yafito da su yai hanyar dakin shi dan ya zuba acikin washing mashing.. har tafara bacci a palon. saida ya gama komai yai wanka sannan yafito. bacci kawai takeyi sai hawaye da suka bushe mata a fuska. tsugunawa yai ahankali yana kallon Eyebrows dinta, sumanta da ya gangaro ya rufe idon ta yasa hannun ahankali yana gyrawa.. tsuke bakin ta tayi tana niman juyawa, "wake up sleepy head.." yafada tare da hura mata iska a fuska.. ahankali ta bude idanunta.. ganin shi a gabanta yasa ta mike da sauri tana kame kame. all of a sudden tafara jin kunyan shi.. mikewa shima yayi tare da cewa "ki shirya zamu fita" tashi tayi tafara tafiya ahanka..binta da kallo yayi , yadda take tafiya.. her shape... tuna randa ya ganta a tsaye bakaya agaban wani yayi... har ta kusa shiga yakira sunan ta with a broken voice. "NOORR" juyowa tayi ta kalleshi.. idon shi har chanza kala, "don't run away from me ever again please.." ahankali ta sauke fuskar ta daga kallon da take mishi sannan ta shige ciki. tana shigewa ya dauki phone din shi yashiga dialing numbern al'amin.. yana dauka suka gaisa, al'amin yace maza kayi wuyan gani fa, ganin ka sai ancika form. Sadeeq yai murmushi kawai.. sun dade suna magana, sannan yamishi bayani akan dan Allah zai kawo ma Matar shi bakuwa su dan zauna tare Kafin yadawo, dan zaiyi tafiya Saturday, idan yadawo zai dauketa suwuce kano ne. al'ameen da bashida da damuwa, kuma bai nima wani Karin bayani ba yace mishi bakomai, sai yakawota. dahaka sukai sallama ya yanke call din. 10:am daidai Damsel yafito cikin wani bakin material mai tsantsin gaske da sheki, sai bakin gyalenshi da tai rolling, ducda bawai ta iya sosai bane dan bai zauna ba. tsayawa tayi a inda take tafara wasa da yan yatsunta ganin kirin kallon da Sadeeq yake mata, kaman yau yafara ganinta... Underneath his breath.. ya mike yazo har kusa da ita ya mika mata hannushi.. ahankali ta dora nata hannun kan nashi.. (bazan tsaya bata lokaci gurin fada muku yadda Sakai kyau ba)... tunda suka fito Joseph yake kallon su yana washe baki. saida suka fita sannan yasamu ya rufe bakin, tare dacewa "oga don go marry fine oyiboo.. him too na oyinbo that's why. Chaii" Sadeeq na fita suka dau hanya....




........ By Tawakkaltu abubakar

add me on what's up 08142087579

....sadeeq bai tsaya a ko ina ba sai a "Bella beauty salon" cikin garin Lagos.. yanagama parking ya fito ya shiga ciki. big girls ne acikin wurin, daga Wanda ake ma fixing, kitso, retouching sai masu pedicure and manicure. duc idon yan matan a kan shi, suna jira suga wayazo dauka, ganin daya daga cikin ma'aikatan gurin takaraso wajan shi, yasa ya cire eyeglasses din shi suka gaisa. nan yafada mata matar shi yakawo a wanke mata Kai. tare suka fita da budurwar har bakin mota, bude mata kofa yayi tare da cewa "come down noor".. ahankali ta fito daga motar, matar da murmushi a fuskar ta, tace "well come MA" Damsel dai tabita da kallo sannan ta Kalli Sadeeq. murmushi yamata sannan ya rike hannunta har cikin saloon din, ko kadan Sadeeq baison shiga inda mata suke, amma for damsel sake.. kowa kallon su yake awajan. Matar ta riko hannun damsel har inda za'a wanke mata Kai sannan Sadeeq ya juya ya fita dan ya jirata mota.. matar tana bude kan damsel taga natural hair ne, so washing and setting kawai yake bukata, nan tafara aikin ta. daya daga cikin Wanda ake ma kitson attachment ta taba kawar ta dake kusa da ita tafara mata magana kasa_kasa.. "look Becky, I don't care if he's married, so what? you know me now.." wacce aka kira da Becky tace "please Annabel I don't want trouble oo.. can't you even see the kind of woman he brought? Shey you no dey fear face??" Anabelle tai wani daria sannan ta Kalli direction din da ake wanke ma damsel Kai.. ko inda suke ma damsel bata kalla ba. nan da nan Annabel din tace ma me mata kitson tana zuwa, parking suman tayi da ribbon tare da mikewa,.. wani matsiyancin riga ne iya daidai cinya ajikinta sai high heel baki da tasa, mikewa tayi rike da iPhone 14 pro max dinta a hannu, tana tafiya kamar zata balle, kana ganinta kaga gogaggun yan Lagos... tana fita kuwa bata sha wahalan gano motar shi ba dan manyan motoci ne gurin. yana motan shi yana danne danne a phone din shi, bai ma lura da ita ba. knocking din da yaji ana mishi ne yasa ya dago, bude motar yayi tare da murmushi a fuskar shi, sannan suka gaisa. "are you guys done??" ya tambayeta dan shi duc a tunanin shi daya daga cikin masu aiki a salon din ne, duc da dai uniform ne masu aikin suke sawa. wani kallon gogaggun yan bariki tamishi, tare da cigaba da da taunan chewing gum dinta, sannan tace "my name is Anabelle, but you can call Bella.." kashe mishi ido yayi sannan ta mika mishi wayar ta "your digits, handsome.." Sadeeq dayagane me ke tafe da ita, ai bai san sadda ya hada rai ya gimtse ba, dan bai dade da sallamar wata ba, shiyasa ko kadan baison shiga inda mata suke. dalilin haka yasa yadena tsayawa a restaurant yaci abinci.. zata kara magana yace "look here woman, I'm not that guy OK?? Please kindly respect yourself and leave." yana fadin haka ya shige motar shi ya kulle, pretending like babu kowa kusa da mortar dan he's very good at that. tuni yacigaba da latsa wayar Shi. Anabelle kuwa wani kallo takara mishi, instead of taji haushin abunda yamata, sai ma birgeta ta da yayi. murmushi tayi tare da juyawa ta koma cikin saloon din. kawar ta na zaune tana waya ta karaso, cema ma wanda take mata kitso tayi zata bata kudi mai yawa akan duc randa yakara kawo matar shi toh takirata. Matar tace ba matsala sannan tacigaba mata da kitson, ko kallon Becky batayi ba, dan tasan dariya zatamata... basu wani dadeba aka gama gyra mata gashinta, wani sassanyan kyau takarayi abunta, matar ta Kalle ta tace "we are done ma" damsel dai binta da kallo takeyi, chan matar taga kamar damsel kurma ce, yasa tai

Please Login or Register in order to submit comment