Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kalli mimi tace " shatu, yar nan na jin hausa kuwa? Kafin mimi tai magana damsel tabude baki ahankali tace "inawuni" tsohuwar tai wani kabbara tare washe bakin ta da ko hakora babu. nan mimi tajata suka wuce ciki, dan tuni har su uncle abu sun shige ciki. suna shiga mimi tai sallahma kafin Damsel ma tayi, duc aka amsa. Baba na yobe na zaune cikin kan kujeran shi na marasu kafa, dan tun shekarun baya yasamu matsalar kafa baya iya takawa. tun da suka shigo Baba na yobe ya kura mata ido, nuna ma mimi kusa da shi yayi yace " shatu kawo mun mata na kusa dani nan ina ganinta" daria akasa a palon sannan Ummahr ma dake kallonta tana al'ajabi, ganin fuskar Dan uwan nata tace " ai kamata tsufa tace" mimi ta karasa da ita har kusa da inda Baba na yobe yake sannan suka nima waje suka zauna a kasa. Kafin Baba na yobe yai magana, Damsel tace " inawuni" Baba na yobe yaji sanyi sosai ya ratsa mishi zuciya ga wani kirin kauna atake dayaji yana ma yar jikan tashi. riko fararen hannunta yayi kafin yace " lallai nayi mata, dama tunda kishiyar ki tarasu ban Kara wani auren ba, ashe ke kike ta rike ni har kizo ko?" damsel data tuna abubuwan da khadija tace mata, nan tai murmushi tare da cema Baba na yobe "A" nan kuwa aka dunga daria, Baba na yobe ma sai daria yakeyi abunda yadade baiyi ba kuwa. nan da nan yai gyaran murya, kafin yafara bude taro da addu'a sanna duc wa'inda suka rasu har kan babanta duc Baba na yobe ya anbato su tare musu addu'an niman rahama. daganan ya kalli damsel yace " toh meye sunan Matar tawa? " damsel ta dan kalleshi sannan ahankali tace "NOOR" baba na yobe yace "masha Allah nooriyya, toh kinga mutanen gurin nan?" noor ta daga kai tafara kallon kowa Baba na yobe yace "duc dangin ki ne nawajan mahaifin ki.. daganan Baba na yobe ya shiga gabatar mata da kowa awajan har da wa'inda ma basa wajan, daga karshe yakara niman kafarar ta tare kara shimata albarka. kowa awajan yaji dadin yadda komai yakance. chan Baba na yobe yakara gyaran murya, nan kowa yai shiru Baba na yobe yace " ni Muhammad isah Aliyu, kowa anan yai shaida, ko bayan rai na, nabama nooriyya campanyna na "MIA" da kenan yobe halak malak... Sosai wajan ya dauka da farin ciki. Mini ahankali ta rada ma damsel a kunne tace "tell him thank you" ganin batace komai ba. ahankali damsel ta kalleshi sannan tace "thank you.." Baba na yobe yakara damke mata hannu sannan yace "you're always welcome my grand daughter." dahaka aka fara gudanar da walimar da Baba na yobe ya hada, ciye ciye sosai akeyi. Muhammad kuwa sosai yake nan nan da yar kanwar tashi. tana zaune itadai akan table dan mimi ce mata tayi tana zuwa, taje wajen Muhammad dayakirata, saiga Aliyu yazo ya zauna gefen ta, at first yi tayi kamar bata ganshi ba, chan kuma sai tace "hi" Aliyu ya sauke glasses dinshi sannan yanamata wani kirin kallo mai dauke hankali kafin yace " don't you think we will make a perfect couple? " NO yaji anche abayan shi, juyowan da zaiyi, wa zaigani inba al'amin ba....

...shafa kai Aliyu yayi tare da mikewa yana kallon al'amin... murmushi yayi kafin yace " inawuni ya al'amin" al'amin ya dan kalleshi kadan kafin yace "lafiya" daukan glasses dinshi yayi ya bar wajan, dan ko kadan Aliyu bai shiri da al'amin. yana wucewa al'amin yanima waje ya zauna, kafin yacema ma Damsel " why are you here alone Noor?" zatayi magana sai ga Muhammad tare da mimi. mimi tana ganin al'amin takaraso da gudu, Muhammad kuwa mamaki ne yacika shi, ganin jiya suka rabu, kallon mamaki ya shiga yi mashi kafin " what happened?" al'amin yana daria yace " your grand father happened.." daria kawai Muhammad yayi dan sosai yasan halin baba na yobe. Mimi ta gaishe da al'amin tare da cewa " ya al'amin ina aunty Khadee? tare kuka zo?" al'amin ya mike tare da cewa " no, nabarsu a gida, nima I'm going back tomorrow ai, barin gaishe su aciki" yana fadin haka yafara tafiya. Muhammad ma yabi bayan shi, Mimi kuma ta dawo kusa da damsel ta kanta akasa yake tana wasa da igiyan jakanta ta zauna tare da dago kan damsel ahankali tana murmushi tace,. "congratulations Noor,.. so you're now the owner of the whole "MIA"??" Damsel dai kallonta takeyi, trying to to understand what Mimi is saying.. al'amin tare suke jerawa da Muhammad har suka shiga ciki. Baba na yobe na zaune a kan kujeran shi sai maman al'amin hajiya Ummahr sai uncle abu da ke gefen su, sosai suke tattaunawa, shigowar su Muhammad yasa sukai shiru, baba na yobe yace " aminu kai da mukayi kafin karfe 6 kana garin nan?" karasowa al'amin yayi yana kallon kakan nashi kafin yace " tsuntsuwa kaso nayi kenan" uncle abu yace " ameenu kasan zakazo shine baka biyo mu ba tun jiya?" murmushi kawai al'amin yayi tare da gaishe da kowa a palon. kafin Baba na yobe yace " wai abokin ka ke niman nooriyya?" al'amin yace "A Baba" Baba na yobe yakara kallon shi da kyau kafin yace " kuma Garba yace Sun hadu da shi chan gidan ko? " al'amin yace haka akayi baba kafin yakara da cewa " Sadeeq mutumin kwarai ne baba, abokina ne tun da dadewa, a Kano iyayen shi suke da zama amma shi tare muke a Lagos.." baba na yobe yai shuru yana nazari kafin yai gyaran murya yafara magana " Allah kan yi ikon shi ne akan bawa duc yadda yaso, kuma alokacin da yaso yin sa, kuma ko me yafaru, mukkadari ne daga Allah, dan haka sai ince bakomai, Allah yasa haka shine mafi alkhairi kuma naji dadin haka, tunda dai bata wulakanta ba. yanzu in sha Allahu bayan komai ya daidai ta, sai a fara niman dangin mahaifiyar nata." kowa yai na am da maganar a wajan kafin Baba na yobe ya rufe taro da addu'a.... karfe 6 daidai su mimi suka koma gida, damsel ta fada bathroom dan yin wanka. Aliyu kuwa ana idar da sallahr magrib yafito yai hanyar dakin umminsu..

.... Yau bikin kanwar Sadeeq saura sati biyu yau, mamin Sadeeq ne a kitchen take ta faman hada wannan da wanchan dan idan Sadeeq zai shigo kano, toh ita kadai take mishi girki dan tasan yadda yake akan masu aiki, shiyasa sosai take zuba ido taga kirin wannan mata da kullun sadeeq kemata sanbatu akai, dan sosai abun ke bata mamaki,.. wai Sadeeq ke mata tadin mace, abunda baitaba yi ba. lallai ta yadda komai lokaci ne. 12:PM daidai tagama hada mishi abincin kafin ta fito Palo, kanwar mamin Sadeeq din ne tare da hauwa'u ana gurje mata kafafuwanta da wasu ganye masu azababben kamshi da ta taho dashi daga Egypt. ko zama mami batayi ba saiga sallahmar Sadeeq tare da nabeel, a zabure hauwa ta mike, ta ma manta da gyran da ake mata. aguje taje tafada jikin yayan nata dan ba kadan tai kewar shi ba. mami ma ganin dan nata yasa taji wani sanyi azuciya, ji tayi kamar kamar Sun shafa shekaru ne basa tare. Nabeel yakaraso palon kusa da mami, saida ya gaishe da auntyn su Sadeeq da bata jin Hausa sosai sai larabci da turanci, sannan ya juyo gurin mami suka gaisa, Sadeeq ma ya karaso yaba mamin shi side hug sannan yadawo inda nabeel yake yazauna. mami duc tasa su gaba tana kallon su abun sha'awa. rufe fuska Sadeeq yayi ganin kirin kallo da kanwar mum din tashi ke mishi kafin tafara mishi magana da larabci.. Sadeeq da ya dukar da kanshi sannan yashiga bata amsa shima da larabcin. mami ta kyalkyale da daria kafin tace " atoh ai gwanda ki mishi fada sosai wlh, ache mutum ko kadan baya waiwayon yan uwan shi? ina fata surukar tawa ba kirin ka bane? sai abun yai mana yawa" Sadeeq ya shafa kan shi yana kallon yadda aketa faman Salle kafar kanwar tashi, sosai kamshi ganyen ya mishi dadi, kallon auntyn nashi yayi sannan yace " you will do this to my wife too before you go" hararan da ta balla mishi ne yasa mami da hauwa ballewa da daria, hauwa tace "kaima yaya kayi kokari ka rinka zuwa mana, ko once in a while ne, kallon nabeel tayi tace ko bahakaba ya nabeel? " nabeel daketa faman danna waya ya dago ya Kalli hauwa yace "haka lil sis, baya kyautawa ai" mami tace yimun shiru, saikace halin ku ba daya ba, yaushe rabon da kaleka bishi? Sadeeq yadawo da kallonshi wajan nabeel din dan yaga mai zaice? mikewa nabeel yayi yai hanyar dakin Sadeeq "mami barin dan watsa ruwa" Sadeeq yai daria tare da mikewa ya bi nabeel din. Suna gama cin abinci Sadeeq yai hanyar dakin mamin shi, su biyu ne a dakin ita da kanwar ta, Sadeeq ya karasa kusa da small mum din nashi ya rada mata abu a kunne,.. dago kai tayi tana kallon shi, Sadeeq yace " Deal?" aunty husnah tai daria tana gyada mishi kai. mami tace "bribing dinta za'ayi kenan?" Sadeeq yai dariya sannan ya mike yace "mum zamuje gidan su nabeel, amma bazan kwana ba tunda bamu hadu da abba ba, anjima zan dawo in sha Allah." mikewa mami tayi tare da ciro wani leda a wardrobe ta mika mishi, tare da cewa kace mata zamuyi waya anjima. OK Sadeeq yace tare da karba yafita.... sai bayan sallahr isha Sadeeq ya shigo gida, ganin motan abbanshi yasa yasan yadawo gida. direct part dinshi ya shiga, dan ba a hade yake da na mamin ba. yana shiga yaga mamin shi a dakin a zaune kan kujera. niman guri yayi ya zauna a kasa sannan suka gaisa da abban nashi. mami ta mike tai hanyar fita tare da ma Sadeeq idan Sun gama ya shigo wajan ta. Sosai yai hira da abban nashi dan sun jima basuyi kirin hiran nan ba, kafin yafara mishi tambayoyi akan yarinyar da yace zai aura, shiru Sadeeq yayi na dan wani lokaci dan kunya da fargaba yakeji, kafin ahankali yafara ma abban nashi bayani, tsinke shi abban yayi tare da cewa, gobe in sha Allahu zan tambayi alhaji Mukhtar ko yasan su, dan sosai yake shiga yobe, idan bawani matsala, to insha Allahu cikin satin nan muyi making arrangement aje kawai. Sosai Sadeeq ya shiga yi ma abban nashi godiya dan ko kadan bai zata abun zaizo mishi da sauki haka ba. hira kadan suka taba kafin yai mishi sai dasafe ya fita. cikin farin ciki yai hanyar dakin mamin shi... da mugun farin ciki ya shiga dakin da sallama, dankunnayenta yaga tana cirewa agaban dressing table. so daya ta Kalle shi, ta cigaba da abunda takeyi, Sadeeq yace "mami guess what??" karasowa bakin gadon tayi, tace " Sadeeq yanzu duc akan noor din ne kake wannaan kikirin ciki?" Sadeeq ya chanza kafin yace " mami kardai bakya farin ciki da auren nan? this is what you've been wanting to see tun shekarun baya fa mami.." mami ta sauke ajiyan zuciya kafin tace " bahaka babe son, it's just I've never seen you like this, gashi rana daya akan mace kana niman zarewa, kaga dole infara jin tsoro, gashi bansan wata kirin mace zaka auro ba, ga hauwa takusa tafiya itama, yanzu kai kadai ne, toh idan ba mai son mutane bane kirin ka kaga ai da matsala son, balle idan ta san yadda kake dardar da yan uwanka, ai kuma shikenan.. shiyasa wlh naso da Hafsat ce, kaga ita nasan halinta kai kanka kasan da haka" ganin mamin nashi tashiga damuwa yasa yakara matsowa dab da ita ya kwanto kan shi a kafadar ta.. " you need not to worry about this mami, trust me you will be the luckiest mother in-law on earth. ko kadan noor bata da matsala mum. I assured this.." mami ta sauke nunfashi kafin tace " I wish nothing but the best for you son, Allah ya tabbatar da alkhairi." Sadeeq yaji dadin haka, sannan ya shiga mayar ma mamin nashi yadda sukayi da abbanshi. sosai suke hira da mamin nashi. wayar shi ne yafara ringing, ganin Noor agaban screen din yasa ya dan kalli mamin nashi, tare da mikewa yace "mami barin barki kiyi bacci, saida safe" bin kawai tayi da kallo har ya fita. Sadeeq dakin shi ya nufa kafin ya shiga kiran noor, tana dauka ya karasa kan kujeran shi hadadde da ke dakin ya zauna, ahankali yafara magana sallama yafara mata kafin yace " matar Sadeeq " damsel tace "good evening" sosai Sadeeq yakejin mamakin damsel, he never zata sauko da wuri haka. murmushi yayi sannan yace "how have you been wifey? " damsel dake kallon mimi namata magana ahankali.. bayan tagamajin me mimi ke cewa, tadawo da hankalinta gurin Sadeeq, kamar dai bazata iya fadin abunda mimi tace ta fadi ba... " I... m... " Sadeeq yace talk to me babe. rumtse idon ta tayi sannan ta furta ahankali " I miss you " Sadeeq ya tsaya for some seconds kafin yace "did you just say that babe??" mimi ahankali tace kice yessss. damsel ganin bazata iya ba yasa ta yanke call din da sauri tana maida nunfashi... mimi tace "gaskia noor kidena kirin wannan abun, haka kika ga ina ma yaya Muhammad?" nan kiran sadeeq yakara shigowa, kasa dauka tayi, mimi tace aiko wlh yanzu zankira aunty khadija ince mata.. da sauri damsel ta dauki wayar ta kai kunne...

....mimi tana ganin damsel tai picking call tafita daga dakin, Sadeeq yace did you really mean what you said babe?? Damsel tai shiru.. Murmushi yayi ya shafa kan shi sannan yace " I called you in d morning baki dauka ba, nima na shigo Kano yau, and guess what babe?" Damsel tai shiru tana jin shi, kafin Sadeeq yacigaba " in sha Allahu cikin satin nan za'a turo.. Jin shirun yayi yawa yace Noor.." damsel da har tafara gyangyadi ta bude ido tare dacewa "na'am" kinji me nace? damsel tace mishi A kawai. ganin kamar da bacci a idonta yasa sukai sallamah kawai... mikewa yayi yashige bathroom.. Shiryen biki sosai akeki gidan Alhaji Muhammad dan Rano, mahaifin Sadeeq, amarya kuwa har sheki takeyi.. Nabeel na tare da Sadeeq a dakin shi wayan Sadeeq din yai ringing.. ganin abbahn shi ne yasa ya mike da sauri yai picking call din,.. OK Sadeeq yace tare da mikewa ya kalli nabeel " I will be right back, abbah na kirana." OK nabeel yace sannan yacigaba da cin dambun kazan da mami ta aiko musu dashi. Sadeeq yana shiga dakin yagan su tare da baban nabeel, Alhaji Mukhtar. niman waje yayi ya zauna akasa sannan yashiga gaishe da iyayen nashi. Alhaji Mukhtar yai gyaran murya yana kallon Sadeeq " abubakar mungama bincike akan gidan yarinyar da kake nima,..yanzu zaka bamu contact din shi kawun nata dakace kana dashi, zamuyi magana yau insha Allahu, idan sun bamu dama zamuje karshen satin nan in sha Allahu.. Sadeeq dayaji kamar ya mike ya rungume abokin abban nashi,.. kanshi a sunkuye yace "toh abbah, nagode Allah yakara girma, zan maka forwarding numbern idan nakoma daki, nabar wayar a ciki." alhaji Mukhtar yace toh bakomai, Allah ya sanya alkhairi, Allah yamuku albarka. Sannan ina fatan kana ma dan uwan naka fada shima? Sadeeq yakara sauke kanshi kasa yace " in sha Allahu Kwanan nan Shima abbah" daga haka suka sallahmeshi ya mike yafita.. yana fita alhaji abubakar yacigaba da mishi maganar kasuwancin su. Nabeel ne yasa Sadeeq agaba yana ta faman jero mishi tambayoyi.. " toh ni wai cemaka nayi inason ta?" Sadeeq yace "kasan Allah kabari nashawo maka kan yarinyar ta amince kuma kaki auren ta, toh wlh bazaka taba samun mace kirinta, baka gode ba ma, with this attitude of yours zanbaka hadaddiyar yarinya" nabeel yai mishi wani matsiyacin kallo sannan ya maida kanshi kallon da yakeyi... Hafsat ce zaune cikin motar Sadeeq, coffee colour hijabi ne jikinta har kasa, nan yafito da ainihin farin fatar ta, hawaye kwance a idanunta tajuyar da fuskar ta dayan gefen tana kallon waje,.. Sadeeq da Shima yaji duc jikin shi yayi sanyi. ahankali tafara magana muryar ta na rawa " ya Sadeeq da kasan haka ne, ai da tun awaya ka fada mun ba sai kazo kano ba, bakasan kirin adadin mutanen da na rinka ba excuse ba, kila ma hakkin sune yakamani,.. tana fadin ta rufe fuskar ta da hijabi tafara sabon kuka.." Sadeeq da duc yaji ya tsana kanshi, ducda yasan baitaba mata alkawarin aure ba, amma ko kadan baiji dadin yanda yaga hankalinta yatashi ba. ahankali yace " haba my lil sis, why are you making me to feel like a bad person??" ahankali Hafsat tace " you're not a bad person ya Sadeeq." Sadeeq yace " then stop crying and wipe those tears please.." ahankali Hafsat tayi yadda yace,.. Sadeeq yace can I go on?? gyda mishi kai kawai tayi.. Sadeeq yace " not without you not looking like my gorgeous lil sis.." Hafsat da bata san sadda ta sake murmushi ba, dan ko kadan bata da rike abu. Sadeeq shima yai murmushin dan sosai yakejin Hafsat kamar kanwar shi, saboda kyawawan halayenta.. " ko kefa my lil sisa.. yanzu kinsan meye lil sis?" girgiza kanta Hafsat tayi. Sadeeq yace " idan ni as your big brother namiki miji, would you like that??" gaban Hafsat yafadi amma bata ce mishi komai ba... kallonta yayi shima, dan yarasa ma ta inda zai bullo. chan yaji Hafsat tace " I will think about it ya Sadeeq" sure?? Hafsat tace "sure" tafada tana murmushi.. ganin har five ya gota yasa yace tashiga gida yamma yayi, tare miko ledodin abubuwan daya sissiyo mata a shop rite.. godiya ta mishi sannan ta shige gida...

....sosai ake girke girke dasaka canopies a tsakar gidan baba na yobe, banda snacks da akai ordering dan yau zaka'a kawo gaisuwar Damsel, kowa mamaki yakeji ganin dangi da baba na yobe ya gayyato, Kai kace auren za'a daura a ranar. wannan zuwan da al'amin yayi kuwa, harda su khadija yazo. bayan angama shirya komai ne su khadija suka bade palon baba na yobe da turaren wuta Mai azaban kamshi. sannan al'amin yakaiku gidan uncle Abu. Damsel dake ta shan bacci, batama san meke faruwa ba. al'amin na ajiyesu ya koma, dan uncle abu har ya isa.. Mimi na wanka khadija ta shigo iman na biye da ita a baya. tashin Damsel khadija tashiga yi tare da cewa "yanzu bacci kikeyi, ko dan yin wanka da kwalliya ma bazakiyi ba Noor?? haka kikeso Sadeeq din yazo ya ganki?" mimi da fitowar ta kenan daga bathroom daure da towel a jiki, da sauri takara ta suri iman dan tun jiya da sukazo bata ganta ba. gaishe da khadija tayi tare da cewa " aunty khadija ai tayi wanka, nayi nayi tazauna inmata make up taki, wai bata so, nima naga tunda ba fita zamuyi yasa na kyaleta.. kumaa ai ance iyayenshi ne kawai zasuzo ko?" khadija ta mike tana bude labulayen dakin tare da cewa " yayanku yace mun Sadeeq din ma wai zaizo, wai Baba na yobe yace yana son ganin shi. ko me tsohon yake planning ohoo." mimi ta daka tsalle tare da cewa " yau dai zanga Sadeeq, wlh aunty khadija so daya muka taba waya da shi, amma he sounds soo nice. Damsel dai sai murza idanu take ta faman yi. iman na ganin damsel ta mike daga kwancen da take, da gudu ta karasa ta fada jikinta. Damsel takara rungumeta tare da tambayar ta ina amar? Iman tace yabi daddynsu. khadija ta kallesu kafin ta dawo da kallonta kan mimi " mimi please yi sauri kisa kaya kije Palo ki shigo mun da akwati na." mimi tace barin dauko miki yanzu, ai ba kowa a gidan. mimi nashigo da akwatin, khadija ta mike ta bude. wahi haddaden bakin Swiss less tafito da shi sannan ta kalle ta " you're wearing this now.." damsel ta Kalli khadija sannan ta Kalli less din, mimi takaraso tana kallon hadadden dinkin da akama less din kafin tace " woww, aunty khadija nima ki dinka mun kirin shi please." no problem khadija tace tare da sauke iman daga jikin damsel. mikewa damsel tayi ahanakali ta dauki kayan tai hanyar bathroom, ba'a jima sai gata tafito, sosai rigan ya amsa kalar fatar ta, ga yanda yabi jikinta sai kasan dake flowing..mimi tace " noor wlh yau idan Sadeeq yaganki, kila yace saidai yau din nan a aura mishi ke ya dauke ki ku wuce" dariya khadija sa sannan ta kalli mimi tace "sa kayanki da sauri please di dauko make up box dinki kifara mata, light makeup kawai zaki mata" nan da nan mimi ta shirya cikin silk material dinta burnt orange, Wanda yai mata kyau sosai sannan tashiga drawing ma damsel brows dinta.. iman da har tayi bacci.. ana gab da gamawa saiga call yashigo wayar khadija, al'amin yakira,.. Ji sukai khadija nace wa " you're joking babe!!! sai kuma tace dukkan su biyun?? tare da juyowa tana kallon mimi da damsel..." tana ajiye wayan mimi ta bude ido gaban ta na fadi tace " wai meyafaru aunty khadija???" khadija har da kwallar farin ciki, nan tagane dalilin tara uban mutane da Baba na yobe yayi, mikewa tayi ta rungumesu gabadaya, tace " Alhamdulillah... I'm so happy for you guys.." mimi dai kallonta takeyi, damsel ma haka. khadija na daria tace " Mrs Muhammad sufyaan and mrs Sadeeq Muhammad rano. Baba na yobe yanzu yabada auren ku." wani ihuu mimi tayi Wanda yasa ni kaina tee na toshe kunni na. typing dinmma duc nakasa yi nima dan farin ciki ( ohh ko wa zai hango mun Sadeeq a gurin ohoo 💃🏻💃🏻💃🏻 )

... koda Sadeeq suka fito waje tare da su al'amin, ko kadan yakasa amince ma ranshi wai shine yau SADEEQ MUHAMMAD RANO aka daura ma aure da Wanda yake ganin itace bugun zuciyar ci. can this be real?? nabeel ya kalli al'amin kafin yace " wannan fa sai mundinga rike hannun shi duc inda zashi for Now, kafin ya zare" sosai al'amin yake dariya kafin ya matso dab da Sadeeq din ya rungume shi " I'm so happy for you friend, Allah yasa albarka mai dunbin yawa a wannan auren, Allah yasa nan da nine month cip cip muzo sunan twins,..." al'amin dayaga nabeel ya kura musu ido yasa yakara da cewa " a twince din asamu mace aciki, kaga sai ataimaka aba dan iskan nan tunda baida shirin yin auren nan kusa" murmushi kawai Sadeeq yayi and at the same time duc jikin shi yai mugun sanyi, jin haihuwa da al'amin ya anbato. he can't tell al'amin his cousin can't conceive, yana ganin sirrin su shida matar shi. wani murmushin yakarayi ganin yadda nabeel ya cika kamar zai fashe. Sadeeq ya shafa kanshi yana kallon al'amin yace "idan kaga yarinyar da zai aura wlh baka isa kazo ko inda take ba" haka dai suka dunga wasan su, wayar al'amin ne yai ringing ganin uncle abu ke kiranshi yasa ya dauka da sauri, al'amin yagama sauraron me kawun nashi ke cewa kafin ya yanke call din. kallon Sadeeq yayi yace "mushiga wai suna niman mu aciki" abinci aka shiga serving musu. Nabeel da al'amin ne kawai suka sake suna diban abincin su, Sadeeq tsakura kawai yakeyi, duc tunanin yadda zai hadu da damsel kafin su koma yakeyi, dan rabon shi da jin muryar ta tun shekaran

Please Login or Register in order to submit comment