Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taci, aunty maimuna dai na tsaye mama kuma na jikin bango ina gankame a jikinta. Mama tayi breaking silent din da cewa Bari mu wuce maimuna dan mu isah da wuri. toh haleema kina ganin zasu karbe ki idan kika koma? kar kidamu maimuna idan ma basu amince ba, I will find a way out. Kuka ne ya subuce ma aunty maimuna ta matso da sauri da rumgume mama, da kyar mama ta bude baki tare da murmushin karfin hali tace it's all going to be fine in sha Allah.. mama da aunty maimuna suka shiga da kayan mu cikin motan aunty maimuna zata kaimu moto park da zamuwuce Yola..

asalim labarin mama da sufyaan....



Asalin su mama fulanin Yola ne, su uku iyayensu suka haifa a duniya, babban yayansu umar sunan kakansu yaci nawajan uwa anacemishi baffa , mai binshi kuma Yusuf,sunan kakansu na wajen uba, ana kiran shi Madibbo. Sai Mama itace autan su,sunan kanwar baban su da tarasu tun tanada shekara shida aduniya akasa mata Haleema, ana kiranta da haleeman ta. baban su baban likita ne ta fannin pata wanda turawa suke kira da ( dermatologist) anan Madibbo Adamu university teaching Hospital da ke garin yola. mahaifiyan su kuma yar jarida ce babba a NTA da ke amadu Bello way a cikin garin yola. haka suka reni su mama cikin aminci da da tarbiya me kyau ba abunda suka rasa na jin dadin rayuwa, haka sukatashi cikin soyayyan juna kuma bakadan suke ji da kanwar su ba har dai lokacin da suka girma sukayi makaranta baffa ya hada degree dinshi ta fannin Zane, ( architect) sai Madibbo da kyar ya lallaba ya gama secondary dan Madibbo sam yaki makaranta a haka har yafada shaye-shaye, Mama kuma kuma chan UNILAG tayi ( university of Lagos) anan takaranta business administration. Mama akwai kwazo wajan karatu, ba wanda baisanta a makarantan ba saboda tsananin kyanta da diri ga kokari. maza ba kadan suke kawo mata Hari ba amma ko kadan basa gabanta. mata yan uwanta ma ba shiga cikin su takeyi sosai ba dan ko kadan batason hayaniya. a tunaninta har tagama ta koma gida bazatayi mu'amala da ko wani da namiji ba. a tunaninta bata da lokacin su. Shiyasa few friends dinta mata da suke dan mu'amala da sunfara tadin samari zata gimtse. a haka dai har ta kai 200 Level. ranan wani alhamis basu da lectures tayi deciding kawai Bari taje mallmart super market dayake kusa da su, ta danyi few shopping. Da wannan tunanin ta mike ta zura abayanta maroon color da ya fito da ainihin kyanta na Fulani, abunta ta, ta fito titi niman abun hawa, ahankali ya karaso kusa da ita " good afternoon ma'am" hada rai ta kara yi tayi banza da shi kaman ba mutum a kusa da ita, murmushi mai sauti yayi yace zaki mun magana ko sai na tara miki mutane? da mugun mamaki ta juwo gabanta na faduwa a fusace tace " saboda kaga barauniya?" babba kuwa ya ce da ita, yaciga ba cewa kawai dan mutane na wucewa ki sace mishi zuciya farat daya? Haka akeyi a garinku? Anyways, without wasting much of your time, Sunana SUFYAAN mijin barauniya and you? rasa abubcewa tayi dan sufyaan ya hadu ba na wasa ba ga uban kwarjinin da yamata. Chan ta kara gimtse wa tace in na tambayo Susan zanzo infada maka. Muje in raka ki sai ki tambayo yace mata ya na murmushin shi me daukan hankali, da nan da nan yasace zuciyan ta. Batadai tanka shi ba still. Let me drop you to wherever you are going please.Yana fadin haka wuce inda yai parking motar shi yadawo daidai inda take tsaye. Tsare ta da ido yayi bai ce komai ba. ahankali ta matso ta shiga motan suka wuce... tun daga ranan soyayya Mai karfi yashiga tsakanin mama da sufyaan. abunda kuma mama batasani ba shine jiranta akeyi a gida a hada ta aure da Ahmad yaron abokin babanta. Yadawo daga Ghana inda ya kammala digirinshi na biyu ta fannin economic,yanzu haka yana koyarwa a federal college of education yola. Sufyaan dan yobe anan iyayenshi suke amma a Abuja yake da zama, yayi aure da yayanshi hudu maza biyu mata biyu a NNPC yake aiki babba ne a wajan sai business din motoci da yakeyi. yakan shigo Lagos idan aiki ya shigo da shi anan suka hadu da mama har Suka kulla so Mai karfi. Ahaka har takusa kammala karatunta kuma kullun sufyaan da sabon salon son da yake dasa ma mama a zuciya. yaima Mama alkawarin aure amma yace mata bazasu haihu nan kusa ba. So ya rufe ma Mama ido har ta kasa gane dalilin rashin son haihuwan da yace. abunda mama bata sani ba kuwa jikinta kadai sufyan yakeso dan baimayi planning kara aure ba ko da wasa, saida ya hadu da mama. a haka ma bai sanar ma kowa ba. ana haka har Mama ta kammala karatunta ta dawo gida. bayan sati biyu da dawowan ta babanta yafara mata maganan Ahmad. mama tace ita tana da wanda zata aura, daganan mama tafara samun matsala da iyayen ta akan sufyaan inda ta turje itadai baza ta auri Ahmad ba. anan babban yayan su mama baffa, yafara bincike me karfi akan sufyaan inda yagano cewa sufyaan ba mutumin kirki bane, a Abuja ma ba wanda baisan kirin iskancin shi ba. toh daganan magana yai karfin gaske inda baffa yahana mama fita ko nan da chan ya kuma hadu da sufyaan inda yabashi gargadi mai karfin gaske ya rabu da ita. Mama tashiga tashin hankali ba misaltuwa dan ko mamanta tadena ko amsa gaisuwan ta ba wanda yakebi ta kanta sai Madibbo idan yana cikin hankalin shi baiyi shaye-shayen shi ba, yakan dan kwantar mata da hankali. A haka har akasa ranan auren su da Ahmad. Da jin haka kuwa watarana cikin dare sufyaan yazo ya dauketa suka gudu... Bacin ran da iyayen mama suka yi ba iyaka. Bayan kwana biyu da yin haka baffa yashiga cikin garin Abuja ya nemota ta hanyan wani abokin shi da yasan sufyaan din. Har Sufyaan ya Kama mata gida cikin garin Abuja. duka ba nawasa baffa yama mama ba sannan ya tattarota yadawo gida da ita. Washagari Baban su yatara kowa a Palo shida yan uwanshi aka kira mama, rai bace yafara magana, inda yai jawabi mai tsawo daga karshe dai yace indai ta dage sai dai sufyaan, to ta nemi wasu iyayen ba su ba. ita kuma ko mai yafaru da ita kar ta kuskura ta nemesu inba haka toh duc abunda ya mata, ita taja ma kanta. kan ta akasa tana ta yarfa hawaye. a haka kowa yana tofa albarkacin bakinshi taron ya watse. Yau saura kwana uku biki aka nima mama aka rasa tun daga nan Baban su yace kar wanda ya kara nimanta. da dawowan Mama tare da sufyaan kuwa ya dauke ta ya kaita wani kauye da sunan nan ne iyayenshi suke yahada ta da wasu tsofaffi suka gaisa da sunan iyayenshi. limamin masallacin kauyen ya wakilce mama bayan karyan da sufyaan ya gilla musu cewa ita marainiyace ce taimakonta yakeson yayi limamin ya amince tare dashi dawasu su biyu a kauyen suka wakilci mama sai wanda yayi karya yazo da su a matsayin iyayenshi. nan da nan aka daura auren mama da sufyaan akan sadaki subu dari biyu...

ana daurawa ya dauketa sukayi na kaduna da ita sun kwana biyu a hotel sanna ya kama mata haya a ungwan dosa yan majalisu two bed room flat. satinshi daya ya koma abuja. ko wani karshen sati yake zuwa duba mama ran Monday ya koma da safe, har suka cika wata shida. To daganan idan saida yayi wata biyu bata sake ganin shi ba saidai yayi ta gilla mata karya wai aiki ne yamishi yawa. ahaka har yan unguwan su mama suke zargin ko zaman daduro Mama takeyi da sufyaan. ahaka har Mama tagane tana dauke da juna biyu. takira sufyaan ta shaida mishi, tun kan ta karasa yacemata saidai ta zubar da cikin, kudi mai yawa ya aiko ma mama akan ta zubar amma taki da haka sufyaan ya dauke kafanshi ya dena zuwa kaduna kwatakwata...

anahaka har cikin Mama yakai wata shida, ba sufyaan ba dalilinshi kuma ko takira shi baya dauka. amma baidena aiko mata da sako ba. toh wannan yasa hankalin mama ya dan kwanta, tana ganin fushi kawai yayi amma idan ta haihu yaga gudan jininshi, zai sauko. a haka har watarana mama ta hadu da aunty maimuna a "buy more" taje shopping, ganin tafito da kaya nikiniki tana jiran adaidaita sahu, ita kuma aunty maimuna tafito zata shiga mota, tausayin mama ya Kama ta, ta ganta da tsohon ciki.zuwa tayi kusa da ita suka gaisa sannan ta amsa duka ledojin hannun ta tace mata bari ta sauketa a gida. godiya sosai mama ta mata sannan tabita ta shiga motan. kwatancen layin tamata dajin sunan layin, aunty maimuna tace ashe bamu da nisa. Nan dai ta kaita har gida daka nan sukayi exchanging contact. tun daga ranan aunty maimuna suka zama very close friends da mama, dayake bata san kowa a kaduna ba kuma ita ba shiga mutane takeyi ba. ana haka har mama ta shiga watan haihu wanta, aunty maimuna na leko ta kullun ta tabbatar ba wani matsala. suna zaune a Palo suna hira wayan mama yafara ringing, da sauri ta duba, ganin bakon number ne yasa gaban ta ya fadi, kare wayan tayi a kunnenta... Muryan Madibbo ya daki dodon kunnenta."Haleema" jikinta na rawa tace ya modee, dan haka take kiran shi. Kina inane ya tambayeta, kaman baza tace komai ba, ta rumtse ido ta faki idon aunty maimuna ta miki ta yi hanyan daki, aunty maimuna ta bita da ido. Kinajina ya kara tambayanta, Ina kaduna a hankali ta amsa mishi jiki a sanyaye. Ya kowa a gida? Chan yayi karfin halin cewa Allah yayi ma mahaifiyar mu rasu... A zabure ta mike ta ma manta da ciki a jikinta. Nooo ya modee, please please don't.. Sai kuma ta toshe bakinta. Chan dai yace zanzo wajan ki next week in sha Allah but don't call anyone a gida kinji? Sautin kukan ta kawai yakeji, addu'an mu kawai take bukata ahaka dai yasamu yadan kwantar mata da hankali har suka ajiye wayan. rike cikin ta tayi wani Kirin juyi da taji ya mata kara ta Saki mai karfi. Aunty maimuna da har ta tashi za tazo yin mata sallama dan yamma yayi taji karan, da sauri tayi hanyan takinta, nan ta same ta a durkushe. Da kyar aunty maimuna ta taimaka mata suka fito da bude mata motan ta ta shiga da kyar tana salati nan da nan Suka isa "GARKUWA HOSPITAL" dan nan take zuwa. batasha wahala sosai ba ta haifi yarta mace. Kyau kuwa ba'acewa komai, yan asibitin haka sukarinka yabawa. kafin nan aunty maimuna takoma gida ta dauko kayan da mama ta hada na zuwa asibiti. Basu wani jimaba aka sallamesu tunda anga bawani Marsala... ahaka mama take samun kulawa sosai wajan aunty maimuna, sufyaan kuwa ba shi ba dalilin shi, dan ko da tura mishi text tafada mishi ta haihu, replying dinta back yayi da cewa sai ta San yanda zatayi da abunda ta haifa. damuwa sosai tashiga, aunty maimuna na kula da ita saidai batace komai ba. ahaka har tayi kwana biyar da haihuwa. ana gobe suna mama ta tura ma kanin aunty maimuna dubu Dari da hamsin yasiyo ragon suna dirkeke. a daddafe dai akayi sunan, dan ko kadan Mama bata cikin hayyacinta, ga rashin sufyaan, ga rasuwan mamanta. Yan uwan aunty maimuna da few friends dinta sukazo, akayi shagalin suna, naci suna "SALMA" sunan mariga yiya mahaifiyan su mama naci. Bayan kwana biyu da yin suna, modibbo ya kira mama yana hanyan zuwa, da kwatance ya isa har gidan da mama take. da isowan shi ko zama baiyi ba mama ta fashe mishi da kuka, ashe zata kara ganin wani nata? Shima cikin farin ciki ya matso kusa da yakama hannunta duka biyu yana kallon kirin raman da tayi, shima yana nan yanda ta sanshi sai ma kara dishewa da yayi wannan kuma sharrin kwaya ce dan abu kara ci gaba yakeyi. sunanan ahaka sannan ya jata suka zauwa, mike wa tayi ta shiga kitchen ta kawo mishi drinks da ruwa, ta kara dawowa kusa shi ta dan gingina da kafadan shi. ahaka ya dinga bata labarin gida, yanda mahaifiyan su tadan yi ciwon sati biyu kafin ta bar duniya. Baffa kuma yayi aure. Kuma haryan zu fushi sukeyi da ita, ba Wanda yake ko tambayanta, sai modibnon da idan yana cikin hankalinshi yakan yi maganan ta. Suna nan ahaka Yana ta bata labari, kuka na suka jiyo a daki, mama ta mike da sauri da dauko ni tana jijjigani, da mamaki Madibbo ya bi mu da kallo. Har kin haihu? Ya jefo ma mama tambaya, a dan kunyace ta mika mishi ni, ya karbe ni yana kallo na yana yaba kyauna. Har har dare yana gidan, mama tamishi hadaddan tuwo miyan danyen kubewa, yana gama ci yace zai shiga cikin gari zaidawo washe gari.. da karfe sha biyu yadawo lokacin har aunty maimuna ta zo dan Mama ta kirata dan su gaisa. Kwanan Modibbo uku a garin kaduna sannan ya koma. tun daga lokacin har girma ya dan leko mu yayi kwana daya ko biyu sannan ya koma, amma ko kadan baya wani sona, kiyayyar da suke ma sufyaan nima ya bini. Sufyann kuwa tunda mama ta haife ni, har nakai shekara hudu, so baifi sau uku ya tako kafan shi kaduna ba. Kuma ko yazo har ya tafi baya ko kallon inda nake. Sai wannan ranan dayazo bayan nayi wayau na girma, ranar ne na san na sanshi da wayo na... Tohh kunji yanda Mama ta hadu da sufyaan. da isarmu motor pack muka yi sa'a mutum daya ya rage, nan mama suka yi sallama da aunty maimuna akan duc yanda ta kasance zasuyi waya, aunty maimuna ta manna mun kiss a goshi, sannan muka shiga motan Minti biyar yan union suka gama komai mota yatashi...
Da isar mu wuraren karfe tara na dare, mama ta nima mana taxi da yakaimu har cikin unguwan su. unguwan Yana nan yadda ta sanshi sai yan kakanan chanji da yasamu. daidai kofar gida ya sauke mu,tayi ta kiran uncle modibbo a waya amma baya shiga, sallaman mai taxi din tayi sannan ya sauke mana kayan mu duka ya shige motan shi ya wuce. duc na gaji na galabaita dan ban taba tafiya ko nan da chan ba balle kirin wannan dogon tafiyan. mama ma jikinta ba dadi dan har lokacin akwai dan zazzabi a jikinta gashi ya hada da na tafiya. rikemun hannu tayi tare da karanto duc addu'an da ke bakinta ta kwankwasa gate, muryan baban su ne ya daki kunnenta, "WAYE?" kara damke mun hannu na tayi ta kasa magana. Chan tayi karfin halin kara kwankwasa wa, bude kofan akayi.. Babanta ne a tsaye tare da tocila a hannun shi dan ba wuta lokacin, a tsorace taja da baya. danno mana hasken yayi dukan mu a ido, tass yakare mana kallo, mama kasa kallon shi tayi dan tsoro. Sarai yagane mama amma ya jefo mata tambaya, baiwar Allah wa kike nima? Mama da kasa hakuri sai ta fashe da kuka tace baba Dan Allah ka gafartamun nayi kuskure, hada hannun ta biyu tayi ta durkusa har kasa, nima sai na fashe da kuka ganin kirin yanayin da ta shiga. Babanta dai bai motsa ko nan da Chan ba, gyaran murya yayi yafito ya tsaya akanta, to anan ne ma ta iya ganin fuskan shi da kyau, tsufa ya kama shi sosai, saidai haryanzu da lafiyanshi ga hasken nan nashi na fillo.amma ya mukayi da ke halima? Ya jefo mata tambaya fuskar nan tashi a hade kaman hadari, zata yi magana ya dakatar da ita tare da cewa wallahi kika bari na shiga gida na fito na ganku anan wajan, na rantse miki sai dai azo a tar da gawanki da safe a nan, dan haka tun kafin mutara makota wasu ma sunyi bacci to ki tattara yanzun nan ki koma inda kika fito, yana fadin haka ya shige gida da sauri har jikin shi na rawa, da ganin haka kuwa Mama ta mike taja ni da sauri sauri cikin tsoron kar baba ya kara fito wa. Da isar mu bakin titi kuwa muka yi sa'a wani mota zai wuce, tare shi mama tayi hannu bibbiyu, yana tsayawa taja ni muka shige ciki da sauri sannan tace miki yakoma baya dan Allah akwai kaya. Har kofar gidan su mama mai motan ya koma, a tare suka shigar da kayan mu duka a boot sannan ta shiga motan jiki na rawa ta kulle motan. Driver yaja mota yana tambayan inda zai kaimu. Gongola summit suites hotel da ke cikin jimeta tace ya kaimu. Da isanmu hotel din muka sauko, cema driven tayi ya jira mun Dan Allah, sannan muka shiga ciki tamana booking daki ta biya, a reception ta kaini na zauna, itakuma ta fita. Saida ta gama shiga da kayanmu duka sannan tazo ta daukeni muka shiga dakin. Ruwa Mai zafi ta hada tamun wanka sannan itama tayi. bude dan karamin jakan da naje da shi gidan aunty maimuna tayi dan tasan akwai kayan bacci na, kudin da aunty maimuna tasa ta gani a ciki, murmushi kawai tayi sannan tafitomun da riga nasa. tafeshi da turare. tana gama shiryani ta zunbula hijabi tacemun yanzu zandawo babe let me get us something to eat, tana fadin haka ta fita. Bata jima ba ta dawo rike da take away kuda biyu sai drinks da ruwa. Har na fara bacci dan nagaji, tashi na tayi inci abinci sannan ta tada sallah. kafin ta idar har na gama ci na fara bacci. tana idar wa ta tashe ni na nashiga bandaki na wanke baki sannan na fito na hau gado na koma bacci. Mama kadan taci abinci sannan tasha drink, kwanciya tayi ta matso kusa da ni ta rungumi tsam a jikinta, ta shiga tunanin next plan din inda zamuje ta shiga yi, dan koda wasa bazata koma kaduna ba.. da safe ta tasheni nayi sallah dan Mama har tayi wanka ta shirya, wanka nima tamun tasamun pink T-shirt da bakin jeans sannan ta daure mun suma na da ribbon tasamun pink hula. nan da nan nayi wani kyau, kallo na kawai ta rinkayi tana murmushi. Wayan mama yayi ringing ta juya ta dauko da sauri ganin aunty maimuna ne mai kiran, sun gaisa Sannan taba aunty maimuna labarin yanda sukayi da da baba, kome aunty maimuna tace mata oho, mama dai tace kar kidamu wlh maimuna komai zai wuce in sha Allahu yanzu idan nayi settling a Lagos din sai muyi wannan magana nan. Sun dade suna waya daga karshe sukayi sallama dan kar muyi missing flight din da Mama tayi booking, a airport sai bin mu akeyi da kallo dan kyan da nayi. munshiga ba da dadewa ba jirgin mu ya tashi zuwa Lagos....
in less than one hour 48mins muka shigo Lagos. Daga nan mama ta dauka mana taxi yawuce da mu cikin gari, inda mukasamu wani affordable apartment, mama ta biya muka shiga. Kwananan mu biyu a ciki, mama kuma tana ta binciken inda zata sama mana gida Mai dan sauki muyi rayuwa a ciki, saboda kudin account Din ta ba wani yawa bane da shi, gashi credentials dinta suna gida. Sai yanzu rashin credentials din yafara mata ciwo. ahaka har mama tasamu wani self contained a festac town da ke cikin garin Lagos, wajan ba wasu mutane sosai. bayan kwana biyu da komawan mu sai ga kiran uncle modibbo, sun gaisa sannan yake tambayanta ya kaduna? a nan ne mama tagane baisan tazo gida bama, nan dai tabashi labarin komai yanda sukayi da babansu har kiran wayan shi da tayi bai shiga ba. Uncle modibbo yaji mamaki sosai ba kadan ba dan koda wasa Baban su baima kowa maganan ba. batare da sunyi dogon magana ba yace kar ta damu zai samu lokaci yazo lagos din. Muna nan a haka da mama muna manejin yaruwa kuma kullun karatu take koya mun ba wasa, a bayan gidan mu akwai wani restaurant inda mama tasamun aikin girki suna biyanta. da haka rayuwa yacigaba har nakai shekara goma sha uku a duniya. Locakin kuma uncle modibbo zuwan shi biyu yana duba mu, amma har locacin kaman kara dasa mishi tsana ta akeyi a zuciyanshi, saidai ba yadda zaiyi ne. watarana cikin dare naji jikin mama yayi zafi gau sai rawan sanyi takeyi, da hanzari na tashi nafara kiran sunan ta mama, mamaaa. da kyar ta bude ido tana karkarwa, jiki na na rawa na diro daka kan katifan mu na dibo mata ruwa na dago ta na bata, ahaka muna tare har safe lokacin ko magana bata iya yi. Safe nayi na fita da gudu wajan makotan mu anan bayan gidan mu naje wajan wata mata, nashiga gidan ta ina kuka nafada mata halin da mama take ciki, da sauri tasa hijabinta tabiyo ni muka zo, tare da matan muka dago mama nasamata hijabi, matan ta koma gida da sauri ta dauko motan ta muka kama hanyan asibi. Muna hanya wayanta dake hannu na yayi ringing, ya modee nagani, da sauri na dauka na fashe da kuka, nan nake fada mishi halin da mama take ciki, wai ashe ma yana hanyan zuwane, nan dai muka dunga waya dashi har ya zo asibitin da muke, lokacin matan da takawo mu har ta koma gida. Ba alaman mama zata bude ido duc kiran da na dunga mata kuwa, muna tare da uncle modibbo har sha dayan dare, kala baicemun ba nidai inata share hawayena, a hankali Mama tabude idonta da sauri muna rigerige nida uncle modibbo har muka isa wajanta. Tari Mai karfi ya kubce mata, tana kallo na tana kallon uncle modibbo ta riko hannu na tasa a na uncle modibbo, "take care of my little girl" da salati a bakin mama ta bar duniya.... a hankali uncle modibbo ya sauke a hannuna sannan ya jawo blanket din ya rufeta har har fuska, a sanyaye na Kalle shi nace mishi bataso a rufe ta haka idan tana bacci, bai ko Kalle ni ba ya juya ya fita. Matso wa nayi kusa da ita na ja blanket din daidai wuyanta, ina kallon fuskar ta daya Kara haske dall. mama please wake up and stop being ill, i hate it. Nafada hannu na rike gam da nata. har bacci yafara dauka na sai ga shigowan uncle modibbo da wasu mutane su biyu.. ashe fitan da yayi zuwa gidan mu yayi ya tattara everything that is important, including the diamond necklace din da mama ta ajiyemun ya hada a jaka sannan ya shiga chan kicin gari yasamo mutanen da yashigo da su. agaba, a idona aka ba uncle modibbo kudi mai yawa. kafin inyi magana suka toshe mun bakina da wani farin kyalle daka nan bankara sanin inda kaina yakeba. uncle modibbo kuwa masallaci ya nufa yasamu liman aka tara mutane aka ma mama sallah yanda musulunci ya tsara aka kaita gidanta na gaskia.. washe gari ya nade ya komai a gidan sannan yadawo Yola, anan dai aka mata addu'a yanda ya dace, sadakan uku da na bakwai. Koda babansu ya tambayi uncle modibbo ni, cemashi yayi bai ganni tare da mama ba kila yan uwan uba na Sun karbe ni... bayan na farka a

Please Login or Register in order to submit comment