Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar duc abinda take fadi baya saurara.. nan kuwa duc yana jinta, ta yadda zai fara mata bayani yadda zata fahimta ne bai sani ba.. ahankali ya dago kanshi yana kallon mami wani jiri ne ya dibe shi. salati hajiya ta rabka ganin Sadeeq din a tsakiyar dakin.. mami tayo kanshi da sauri aunty husnah jiki na rawa tafara tambayar yar uwarta meke faruwa.. hajiya har ta fita tashiga bangaren abbah kiran shi. yana palo yana kallon news, a rikice tace muhammadu kafito fa, gida ba lafiya. abbah kuwa ganin mahaifiyar nashi da baima san tazo ba, gata kuma arikice yasa ya mike da sauri yace " hajiya yaushe kika zo? Jikin ne?" kuka ta balle dashi tana fadin kazo dakin Aisha nace" abbah yafito arikice yai hanyar dakin mami,.. aunty husnah na rungune da shi mami kuma waya Kare a kunnenta tana waya da doctor dinsu. abbah nashigowa yai wurin Sadeeq yana tambayar meke faruwa.. mami tai karfin hali tace wlh bansaniba.. hajiya har ta karaso ciki itama " nidai nasan habubakar ba ruwanshi wlh, mutumin da magana ke mishi wahala ma, yaushe har akayi auren da har zai bata mata?? saidai idan ku kuka kun tata mata" abbah da har ya kai Sadeeq kan gadon mami, duc shima a rikice yake... hajiya banda kuka ba abunda takeyi. abbah ya Kalli mami yace "wai what's going on ne wai??" hajiya tace " wai bacemaka nayi Sun mata mugun abu bane yasa ta wuce, yanzu da wani ido zamu kalli yan uwanta idan munje? kakira kawun nata, yanzu haka kila takai ma, dakanan naji ko me su aishan sukai mata" mami dai duc attention dinta na wajan Sadeeq, dan har yanzu bata ga alaman ko motsi yana yi ba. aunty husnah tafara mata magana da larabci. mami da kanta duc yadau zafi tace "husnah nace miki bansaniba" wayan mami dake kusa da husnah yafara ringing.. tana amsawa tace ka shigo kawai. likitan na shigowa yafara gaishe da abbah sannan yashiga duba Sadeeq. abbah kuwa fita yayi yakoma bangaren shi, yana shiga palo yadau waya yashiga kiran nabeel, bayan nabeel yadauka abbah yace " yanzun nan ina nimanka" gaban nabeel ne yafadi, dan shi duc tunanin shi maganar Hafsat za'a mishi.. so biyu nabeel na kiran Sadeeq amma ba'a dauka ba. bashiri yafito yai shiga mota ya dau hanyar zuwa gidan su Sadeeq din..... Sosai damsel take bacci a mota, kafin matar dake kusa da ita ta tasheta tace ko tanason siyan wani abu taga sunshigo gidan mai. Damsel ta fara dubedube tana tana kallon masu bin mota suna talle, sosai taji tana jin yunwa. crackers tasiya da ruwan gora tafara ci ahankali, sosai Sadeeq yafado mata arai, ko wani hali yake ciki yanzu ohoo, ahankali tace " I will miss you too" saurin goge fuskar ta tayi kar hawayen da ya taru ya gangaro mata.. motar su kuma yacigaba da tafiya... Nabeel ne a palon abbah mami tasa shi agaba tana rabka uban salati, abbah kuma al'ajabi yacika shi bakadan ba. dan nabeel ba abinda ya boye musu game da maganar damsel, iya abun da yasan zai iya fada ya fada.. mami tace " toh wlh wahalar ya isa haka, ko da itace autar mata kuwa sai ya sake ta." abbah dai kanshi jingine ajikin kujera, abunda kuwa yasa bai girgiza da lamarin sosai ba, Uncle abu yadan yi briefing dinshi dasukaje yobe.. dan sosai uncle abu ya dunga yabon Sadeeq. Abbah kuwa koda uncle abu yafada mishi, bai dauka abun da wata manufa ba ko kadan,dan yasan kaddara ba yadda bata zuwa dan adam, kuma duc musulmin kwarai dole yai imani da kaddara. sosai yai alfahari da dan nashi. toh shi yanzu abunda ya daure mishi kai, meyesa takara gudu?? sanbatun mami ne yasa ya dago ahankali yana kallonta, cema nabeel yayi yai excusing dinsu. Nabeel nafita abbah yajuwo yana kallon mami, " kinsan me kike cewa kuwa Aisha?? yanzu fatan inda za'a ganta zamuyi ko raba auren ne agaban ki? tunda naga kamar igiyar auren a hannun ki yake" mami tace " haba alhaji, bakaji me nabeel din yafada bane? na haifo mata Sadeeq din ne dan ta kashe min shi, duc abinda ya fadi baka ji ba kenan? toh me akai mata? ai kawai tasaba da yawon duniya ne, dan haka kawai yasaketa taje tacigaba, amma badai da auren data akanta ba wlh"... nabeel na fita yashiga dakin Sadeeq din, dan har anmaida shi dakin shi, drip ne a hannun shi, aunty husnah na zaune kusa dashi, hajiya kuma taci uban dammara da hijabi sai kofin tea a hannunta. Sallaman nabeel ne yasa duc suka juyo suna kallon shi. Hajiya tace "yauwa nabilu, ungo kai kokari ka lallabashi yasha, yanzu zanje gida inmishi abinci" karban kofin tea din nabeel yayi hajiya kuma ta kwance hijabinta tasa sannan ta fita, aunty husnah ma ta mike bayan Sun gaisa da nabeel ta fita. Idon Sadeeq a lumshe bai bude su ba. har kusa dashi nabeel yazo ya zauna yana kallon shi kafin yace " so, where do you think we will start looking for her now? Lagos??" ahankali Sadeeq ya bude idanunshi yana kallon nabeel " I'm never going to look for her again,.. she has to come back herself this time around" nabeel ya bude idanun shi yana mishi kallon mamaki, abun da ko a mafarki baitaba expecting Sadeeq zaice ba. " are you insane?? do you know what you are saying kuwa?? she's now your wife fa" Sadeeq zaiyi magana mami ta banko kofar rike da biro da takarda a hannun ta...


...mami na shiga dakin ta kalli Sadeeq " amma bantaba tunanin a matsayi na na mahaifiyarka akwai abunda ashe zaka boyemun ba Sadeeq, in haifeka, inbaka tarbiya mai inganci, ace wai yar bariki zaka Kare da,... ina iliminka ya tafi Sadeeq ina wayewar ka?? toh wallahi tun kafin kaga other side of me, rubuta mata takardar ta a aika mata chan wurin dangin ta, idan ma ba nan ta tafi ba, toh chan takarata, badai inhada zuri'a da irinta ba.." ajiye mishi takardan tayi kusa shi.. Sadeeq kuwa yana kwance ko motsi baiyi ba yana jin mamin nashi tunda ta fara har ta sauke aya. shidai yasan ko bindiga za'a sa mishi bazai taba sakin Damsel ba. nabeel kuwa ganin dagaske mami takeyi, dan tunda yake bai taba ganin fushin ta ba.. Jikin shi duc yayi sanyi, ahankali ya dago yana kallon mami " mami don girman Allah kar..." dakatar dashi mami tayi a tsawace tace " kasan Allah sai ya saketa" muryar abbah yadawo da Sadeeq cikin tunanin akan yadda zai bullo ma mami.. a tsawace abbah yace " ashe ban isa dake ba Aisha?? yanzu ina mutunci da girma anan, kizo kisa yaro agaba kina bashi umarnin Saki?? Saki fa Aisha.. kinsan me kike yi kuwa?? meyesa wai ku mata ko kadan baku da tunani ne?.." Sadeeq kuwa yana kwance Amman zuciyan shi ke faman boiling from the inside.. wai yau akan shi ake drama... dan drama ya dauki abun.. rumtse idon yayi hawayen dake makale suka gangaro mishi.. me damsel take nufi dashi?? sai taga baya nunfashi ne a duniya zata dena wahalar dashi?? Nabeel kuwa mikewa yayi ya fita, dan shima jikin yai mugun sanyi, bazai iya jure ganin abokin shi a wannan halin ba, for Sadeeq to bring out tears from his eyes, lallai bakaramin abu bane, dan haka indai Sadeeq dagaske yakeyi bazai je niman Damsel ba, toh shi yayi alkawarin nimo ta duc inda take.. ciro wayar shi yayi a aljihu yashiga kiran al'amin.. abba kuwa kallon dan nashi yayi bayan mami ta fita, ganin hawaye kwance a fuskar dan nashi yasa yasan lallai bakaramin abu bane, yasan Sadeeq da hakuri da juriya tun yana karami. karasowa abbah yayi ahankali ya zauna kusa dashi, ahankali abbah yakira sunan shi.. "ABUBAKAR.." Sadeeq yabude idon shi yana kallon mahaifin nashi, murmushin karfin Hali yayi sannan yace " na am abbah" abbah yace " in sha Allahu zata dawo, cikin yardar Allah,.. bana son kasa damuwa a zuciyarka please, mata da kake gani rauni ne dasu.. amma komai zai wuce in sha Allahu, and about your mother, I will talk to her" Sadeeq da har dan ji relief a zuciyar shi jin maganganun da abban nashi ya mishi, yace, " bakomai in sha Allahu abbah, thank you.. " abbah yace kayi magana da iyayenta ne? Sadeeq ya girgiza kai kawai. abbah yace " zanyi magana da shi uncle din nata, idan ba nan din tajeba, za'a nimota in sha Allahu." nan Sadeeq ma yakara mishi godiya. abbah na fita Sadeeq yakara maida kan shi kan pillow, nan yaji bacci yafara daukar shi.. mami ne tare da abbah a dakin shi..abbah na mata magana, sunkai minti kusan talatin da abbah a daki, mami najin mijin nata har ya dasa aya., mami ta dago tana kallon abban " ai alhaji ni sainaga idan har bayan duc wannan gwagwar mayar da aka sha zata kara guduwa, toh ba son shi takeyi ba, wahala kawai take bashi" abbah yace, "kar kice haka Aisha, ba'a saurin yanke hukunci batare da anyi bincike ba,. zama zakiyi da shi kuyi magana ta fahimta, nan zaki san ko ma wani abune ya hadasu, haka kurin baza ta Kama hanya ta gudu ba, tsuntsuwa ce ita?" mami tai ajiyan zuciya sannan tace " toh Allah ya sassauta lamarin, Allah kuma ya bayyana ta duc inda take" mami dai taji wasu shawarwarin da abbah yabata amma bataji wasu ba, anata tana ganin bazata zuba ido wata ta hallaka mata da ba... cikin bacci Sadeeq yaji muryar mutane, ahankali yake bude idanuwamshi,.. mami yagani a zaune a bakin gadon shi, sai doctor sulaiman dake cire mishi cannula a hannun shi, dan ruwan yakare. doctor yace " babu wata Matsala in sha Allahu hajiya, yanzu dai yasamu yaci abinci, sai a bashi magungunan nan. godiya mami tamishi sosai, yana wucewa mami takaraso kusa da Sadeeq din tana kallon yadda yau kawai amma duc idanuwanshi Sun fada ciki. bata son yin mishi wata magana yanzu, ganin yadda condition dinshi yake. Sadeeq kuwa azuciyan shi fata yake kar mami ta dauko mishi wata maganar, dan ko kadan baida energy.. tambayar da yaji ta mishi ne yasa shi bude idon shi gabadaya.. " indama maka kunun tsamiya ko zaka sha tea?" Sadeeq yai shiru yana nazari kafin ahankali yace " kunun dai mami, and it should not be too thick.." mikewa mami tayi takara ja mishi duvet ta rufe shi sannan ta fita.. ba'ayi minti 8 da fitar ta ba saigata da karamin tray mai dauke da bowl aciki, aunty husnah na biye da ita abaya suka shigo. da kyar mami ta lallaba shi yasha kusan rabi sannan ta balla mishi maganin da doctor sulaiman ya kawo mishi yasha.. ba Wanda yai magana acikin su, kowa da abinda ke ranshi.. mikewa Sadeeq yai ahankali,. mami tace "me kake so? " Sadeeq ya cire bargon gabadaya ya sauko da kafafun shi kasa yace " mami sallah zanyi, lokaci yawuce sosai" mami da aunty suka bishi da kallo har ya lallaba yashige bathroom.. Karfe 4:30 Sadeeq har yayi wanka ya dan ji karfi ajikin shi waya yakeyi da Joseph yaga shigowar wayar al'amin, dan yaga 2missed call dinshi dazu, cema Joseph yayi zai kira shi anjima sannan ya dauki wayar al'amin,.. sun dan jima suna waya, ko kadan al'amin baiji dadin meyafaru ba " wlh da nabeel yakira ni dazu, I find it hard to believe until when my mom called me. amma Sadeeq wht really happened??" Sadeeq yai murmushi kawai, dan baya son arinka sanin halin da suke ciki, yace mishi kawai " we had a little misunderstanding ne jiya,.. kar yatada muku da hankali please, she will come back in sha Allahu" al'amin yai shiru dan yasan Sadeeq karfin hali kawai yakeyi,.. al'amin yace zan shigo gobe in sha Allahu.. saurin dakatar dashi Sadeeq yayi yace " noo, don't bother friend, nima zan dawo ai cikin Week din nan, gobe nakeson zuwa yobe ma ko jibi, dakanan zamu kamo hanya dan nabeel ma is suppose to resume work jibi, let's see how it goes dai" da haka sukai sallahma.. Sadeeq yashafa kan shi da hannuwanshi duka biyu sannan yashiga duniyar tunani.. where could she be this time around? shidai yasan yadda yasan zai mutu, haka yasan noor will never go back to prostitution, wannan kadai idan ya tuna saiyaji natsuwa azuciyanshi, tuna maganganun da ta dunga mishi jiya da daddare ya dunga yi.. yagano abubuwa da dama aciki.. murmushi kawai yayi knowing fully noor is madly in love with him.. ahankali ya furta " you will come back to me noor, this.. I'm certain.." har akayi sallahr isha hajiya na gidan, ganin Sadeeq din ya sake ne ma yasa tace a maida ta gida... Har sha biyu Sadeeq bai rumtsa ba, yana kan sallahya ya jingina da jikin gado charbi a hannun shi, yana aikin aika ma matar shi da addu'o'i, duc inda tashiga Allah yakare mishi ita..


......damsel kuwa karfe 1:30 na dare suka sauka a tasha, dan kadan suka rage a motar ma, wasu Sun sassauka a hanya dan ba cikin gari zasu shigo ba.. raba idanu ta dunga yi ganin kowa na daukar hanyar shi wasu kuwa anazuwa a dauke su.. tafiya take bata san inda kafafuwar ta zasu kaita ba.. tana fita daga tashar kuwa chan tsallaken titi sai ga wani tsohon truck zai wuce, tsayar dashi tayi, wani dan tsohon dan iyamuri ya tsaya " young woman, where are you going??" Damsel tafara kamekame kafin tace " I'm looking for restaurant please" dan tsohon ya dan kalleta, ganin abaya ne jikinta ya tabbatar mishi bakuwa ce. nan ya paka motar shi ya fito, describing wani restaurant dake tsallaken titi yamai ta.. godiya damsel tai mishi sannan ta tsallaka titin dayake dare ne, mota daddaya kawai Kake gani.. da isar ta gurin taga ansa close a jikin glass din wajan.. tsayawa tayi tana tunanin next plan dinta, ga dare ya tsala. ganin mutum tayi tacikin glass din yana tahowa, middle age Man. bude kofar yayi yana missike idanun shi kafin yafara mata magana " you want something young lady?" Damsel tace, " can I get something to eat please? " mutumin yabude mata " come in but we are close oo, where are you from by this time" Damsel dai ta shigo ciki tanima daya daga cikin cute kujerun dake wajan ta zauna. mutumin yace " we make indomie, pan cake, fried rice and chicken and then swallow. but of course you can see its late, so I can only make you noodles, is that OK?" Damsel tace "Ok" tana zaune mutumin ya shiga kitchen ya hado mata noodles da fried egg, har tafara gyangyadi ya tasheta.. bayan ya ajiye mata ya nima wani kujeran ya zauna dan nesa da ita, dan Shima bacci ne a idon shi.. yau sunyi aiki dayawa bailkoma gida da wuri ba. shiyasa yai deciding ya kwana. dan watarana idan yai dare toh anan yake kwana. damsel kadan kawai taci tasha ruwa, kallon noodles din kawai takeyi tana wani tunani, dago kai tayi tana kallon mutumin, wondering if he's the owner or he's just working there. ahankali tace " if you can hire me, I can make a better noodles than this" mutumin ya bude idanun shi yana kallonta ta, dan yagaji da daukan masu aiki, dan baya dacewa, shiyasa yai deciding shida kanin shi kawai su lallaba wurin, tunda ba wani girma restaurant din keda ba.. damsel dai na kallon shi. mutumin yace " did someone directed you to me? " damsel tace "No" mutumin yace " and you said you can cook, how I'm sure??" damsel tace " you can try me tomorrow morning, but if you are to hire me, you have to accommodate me.. I don't have a place to stay" mutum yace " if you're to make a fried rice, wht are the ingredients you need?" damsel tai shiru tana nazari kafin tafara magana " I'm going to need vegetables likes diced carrots, slice onions, green beans, peace, garlic, ginger and kidney.. the rest of the spices depends on how you want fried rice to look " kura mata ido mutumin yayi.. sannan yai murmushi.. " madam you're hired, but talking about accommodation, can you manage the one bed room at the back? because I can't take you to my house" ahankali damsel tace "no problem" jefo mata tambaya yayi " what can I call you?" damsel tai murmushi, hawaye nan da nan ya taru a idon ta.. " you can call me Mrs Sadeeq" mutumin yace " you're married??" damsel tace " I was" mutumin yaduba agogon hannunshi tare da mikewa yace " alright Mrs Sadeeq, let me take you to your room, and I will see wht you have for us tomorrow.. and you can call me oga uche" damsel ta mike tare da bin bayan mutumin..

...har daki oga ache yakai damsel, daukan wayar shi da yayi plugging a chaji yayi sannan yafito ya bar mata dakin.. Mikewa damsel tayi tashiga bathroom din dakin, dakyar ta iya yin alwala a ciki a tafito, bata ma san ina bane gabas, itadai tayi magrib da isha a haka, dan sun tsaya a hanya sunyi azhar da la'asar.. tana idarwa ta kwance gyalen kanta sannan ta mike a katifan, nan bacci ya dauketa... hasken dataga ya gauraye dakin ne yasa ta bude idanuwanta ahankali.. sai kuma ta mike da sauri,karfe 8:am tagani a jikin agogon bangon dakin.. bayan ta idar da sallah taji uche na kwankwasa mata kofa, tashi tayi ta isa kofar tare da budewa, uche yace "good morning Mrs, please you need to get ready now so we can start preparing something in the kitchen, we open by 10:am" OK kawai damsel tace. shidai uche bai ganta da kaya ba, kuma bai damu ya tambaya ba hasalima so yake tayi abinci yaga kwarewar ta tukunna kafin ya yanke decision.. karfe 9:42 har damsel ta gama hada mishi lafiyayyen fried rice da pepped chicken nan suka zuba a kulolin da suke packaging su ajiye. idan customer yazo saidai adiba ayi microwaving
. uche was so impressed at damsel, dan har noodles saida yai testing dinta, kanin shi na zuwa yai introducing mishi damsel akan tare zasu rinka aiki.. sosai damsel ta maida hankali a kan aikin da takeyi,.. ta kuma yi dace uche mutum ne mai mutunci da sanin yakamata, ganin ko kaya bata da shi, sai uniform din da sukewa na restaurant din, yasa yaba kanin shi kudi ya raka damsel kasuwa tasiyo kayayyaki akalla Kala hudu, duka dogayen riguna masu dan kyau sai hijabi guda biyu, da Man shafawa sai turare kala biyu.. haka kuma sosai ta maida hankalinta tana aikin ta tsakani da Allah.. yau kwananta hudu kenan, Kuma ba laifi uche nasamun customers.. sosai Hafsat take kuka a dakin Sadeeq tace "ya Sadeeq this is all my fault, I shouldn't have said wht I said to her, wlh I didn't mean it.. I.. I" Sadeeq yai murmushi yace "banace miki ya isa ba lil sis, of course it's not your fault, who said it's your fault?" Hafsat dai tai shiru tana ajiyar zuciya kawai, dan sosai yayan nata yabata tausayi.. sai taji tayi mugun tsanar kanta, meyesa zatace ma noor she's supposed to be his wife, amma yace mata they will get married. aiko itace akama haka bazataji dadi ba. tarasa me yazo kanta alokacin, kishi ne ko Kuma wauta??.. Sadeeq yace " so, yaushe kika bamu damar turowa lil sis?" kasa magana tayi kanta a kasa tace " ya Sadeeq duc randa kuka shirya" Sadeeq yace " I'm happy you go for my choice Hafsat, and in sha Allahu u won't regret being married to nabeel, I promise you.. now go and meet him kar yaita jiran ki" ahankali Hafsat tace " ya Sadeeq bakace kayafemun ba" Sadeeq yace " ba abunda kika mun lil sis kinji?" Hafsat ta tace "toh" cikin sanyin murya tare da mikewa ta fita.. Sadeeq yacigaba da hada kayan shi dan gobe karfe 8 na safe zasu bar Kano.. Hafsat na fitowa daga dakin Sadeeq ta shiga na mami tai mata sallahma sannan tafito, nabeel na jingine jikin motar shi, ganin fitowar Hafsat ne yasa yai hanyar motar shi yabude ya shiga yana jiran ta shigo ya kaita gida.. har suka isa gida ba Wanda yai magana cikin su. yana ajiye ta kuwa, Hafsat tace "nagode" sannan ta bude kofar ahankali zata fita,.. muryar nabeel taji yace " ki gaishe da mum" tajuyo ta Kalle shi, fuskar shi na kallon gabar motar shi kamar bashi yai maganar ba,.. bin ta da kallo yayi har ta shige gida kafin yatada motar shi yadau hanya.. har ya kusa shiga layin su Sadeeq yaga me water melon, nan ya tuna Sadeeq yace yasiyo mishi in zai dawo, Manya guda biyu yasiya mishi sannan yakama hanyar gidan.. Sadeeq na zaune a kujeran dakin mami, itakuma tana kan gado tana facing dinshi.. tace " kaga yadda kadawo kuwa cikin dan kankanin lokaci kuwa Sadeeq, wani kirin so ne kake ma baiwar Allahn nan haka? sukansu dangin nata dakaje sun baka shawarar kai wani auren, idan Allah yasa ta dawo shikenan idan kuma bata dawo ba haka Allah ya rubuta, sai duc mu rungumi kaddara, amma ina haka kazauna ba mata, ni kaina hankalina bazai kwanta ba Sadeeq.. ga kanwar ka tai aure, so kake zuciya na ya buga ko?? " Sadeeq ya Kalli mahaifiyar nashi da sauri yace " dan Allah mami kar ki kara fadin haka, in sha Allahu zanyi mami, nidai dan Allah kar ki kara magana kirin haka" mami tai shiru tausayin dan nata ya cika ta, sarai tasan waye Sadeeq, tasan ya amsa mata ne kawai.. ahankali tace " ko insa husnah ta nima maka yarinya ne a Egypt?" Sadeeq yace "har chan Egypt kuma mami? kibari zan nima da kaina" zatayi magana taji ana knocking a kofa, mami ta bada izinin shigowa. mariya ce rike da water melon din da nabeel ya bata ta ta bare musu sai ta diba ma mami. Sadeeq na ganin mariya yace "nabeel yadawo?" mariya tace "A yana dakin ka" mikewa Sadeeq yayi yace mami bari muje muma hajiya sallahma, daganan zamuje gidan su nabeel muyi ma ummi sallama dan tare zamu kwana anan dashi.. mami da har tafara shan water melon din da maria ta kawo mata tace " toh ku gaishe su" Sadeeq yace toh mami sannan ya fita, kadan yasha water melon din nabeel kuma yasa maria ta dafa mishi indomie, saida suka gama ci sannan suka fito suka Kama hanya. basu wani bata lokaci gidan hajiya ba, dan rabin maganar ta akan damsel ne. Kudi nabeel ya ajiye mata sannan suka fito. a gidan su nabeel kuwa sosai ummin nabeel tai musu nasiha tare da ba Sadeeq shawarar yakara yin aure, inda hali ma ahada da na nabeel tunda anfara magana, Sadeeq yasan wannan aikin mamin shi ne. Toh kawai yace ma ummi, karfe biyar suka bar gidan bayan Sadeeq yaba kanin nabeel 50k yafita da xee washe gari... ana sallahr isha suka shiga part din abbah Suka dan mishi hira, abbah yace ma nabeel karshen watan nan zasu kai kudin gaisuwa gidan su Hafsat. Nabeel baice komai ba, Sadeeq kuwa murmushi yayi tare da fatan alkhairi.. washe gari karfe bakwai mami na bakin motar su Sadeeq hijabi ne jikin ta, duc mood dinta ya chanza. Sadeeq yace "haba mami na, nafa miki alkawarin every month end zan rinka zuwa, kafin in samo miki kawa kuma" mami ta Harare shi tace " alkawarin kenan da ba'a cikawa" kallon nabeel tayi tace ai kai yanzu bama

Please Login or Register in order to submit comment