Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakin ta kullo kofar tacire key. tanaji matar na bubbuga kofa.. bude wardrobe din dakin tayi ta shiga niman wani abu tasa ajikinta, ganin wanin jan kimono tayi nan ta jawo shi tashiga sawa har jikinta na rawa. towel din kuma ta daura akai tabude kofa ta fito..body guards ne biyu a jikin kofar.. tana ganin su tahada rai kafin tace " I want to see him" daya body guard din yace " he's with visitors " nan damsel taji sanyi aranta, ducda batasan ko wasu kirin visitors bane tace "yeah I know, he requested to see me" kallon juna body guards din sukayi kafin dayan yace " let me lead you" haka ta dunga binshi tana kara kare ma ko'ina kallo har suka kai daidai kofar shiga sannan body guard din yaja ya tsaya. zuciyarta na bugawa ta bude kofar a hankali ta shiga, mutane ne aciki sunkai shida. tana shiga taji alhaji tanimu nacewa " You have nothing to investigate here, I'm clean " damsel najin haka tazube akasa ta rushe da kuka tare da cewa " save us please, our lives is in danger, this man you're seeing is a criminal.. " nan tashiga tarin karya, alhaji tanimu har yana in-ina dan rudewa, ya akayi ma tafito? dayan yace " see, I've been suspecting this house for a very long time" mikewa alhaji tanimu yayi suka damke shi. ganin haka yasa damsel mikewa da sauri tace "please come and save some innocent young girls" Dan damsel lokacin tana gidan tasha ganin alhaji tanimu na shigo da kananan yara yana kulle su awanin daki. nan wasu su biyu suka bita suna fitowa kuwa tai hanyar dakin da tasan zata gansu..aikuwa su uku aciki harda Wanda ta hada mata ruwan wanka dazu. ganin suna shirin yin kuka yasa takarasa dakin da sauri ta rungumesu tace " don't be afraid, you are safe now" body guards din gidan kuwa har sungudu.. damsel kuwa dakin alhaji tanimu tashiga ta kwashe kudi mai uban yawa tare da chanza kayan jikinta zuwa wani coffee brown abaya da tagani da gyalen shi.. yaran kuwa an tasa su agaba za'a nimo iyayen su.. suna fita wajen gate da alhaji tanimu da aka Riga akasa mishi chain ahannu, suka hadu da wata middle age woman a waje tana jingine da motar ta, kallon alhaji tanimu tayi kafin tace " ai nafada maka in sha Allahu sai asirin ka ya tonu.." Alhaji tanimu zaiyi magana wani daga cikin police din yace " my friend will you shut up!!! " sannan suka tasa keyar shi har cikin babban motan su tare da yaran... damsel kuwa fitowa tayi zata kama gaban ta matar ta ganta, ganin damsel a rikice yasa tace tazo, har inda take damsel ta karasa..matar ta kalleta tace " yanzu shekarun ki nawa kina mishi aiki?" Damsel nan tashiga bata labarin inda so uku kenan tana guduwa yana nimota, saidai bata ko dawasa fada mata ita matar sure bace.., matar tace " are you ready to be a better person for good??" Damsel tai shiru kafin tace " yes I'm ready " matar tace ta shiga mota su wuce... har gidan ta matar ta kaita dake agege.. babban gida ne sosai, wanda yatara bangarori kalakala kamar su fannin islamiyya, boko, koyar sana'ar hannu da dai saurran su. tun amota matar tayima damsel bayanin ko wacece ita." sunana hajiya rabi'a anan cikin agege nake, bantaba haihuwa ba har mijina Allah yai mishi rasuwa, tunda yarasu na tattara al'amarina na mika ma Allah. ganin mata sa'o'in ku suna yawo da bariki a garin nan, kuma wasu ma ba yin Kansu bane, tsadar rayuwace da rashin wadata yakesasu shiga hali kirin wannan, toh kawai Na yanke shawarar gina katon gida mai bangarori kalakala akan inrinka taimaka ma mata masu bukatan taimako.. sau biyu yan mata suna gudowa daga gidan da na dauko ki yanzu suna dawowa wajena ina taimaka musu,.. dan haka tun wata biyu da suka wuce naci alwashin sainasa an kama shi." Damsel sosai tai farin ciki da wannan labari.. kallon matar tayi tace " may Allah reward you with janna" matar tai murmushi tace ameen ameen. ai da nakowa ne." toh yanzu ke idan mukaje wani fannin zaki shiga?" damsel atake tace " I want to improve in my Islamic knowledge" masha Allah matar tace sannan tacigaba da tukin ta har suka iso gidan...


suna isowa gida damsel ta bude kofa ta sauka sannan matar ma ta kashe mota ta fito suka shiga ciki. yan mata biyu ne a palon daya na cin abinci, dayar kuma na kwance akan 3sitter tana karanta wani littafin addini. suna ganin hajiya rabi'a suka mike suna mata sannu da zuwa.. damsel dai tana tsaye, bayan hajiya rabi'a ta karasa cikin palon ta zauna sannan ta tacema damsel shigo baiwar Allah. karasowa damsel tayi tashiga cikin palon ta zauna kanta a duke.. hajiya rabi'a ta koma da kallonta kan mai karatun tace " zarah ga kawa namiki, ajinku tace takeson shiga, gobe idan Allah ya kaimu sai aimata register" zarah tai murmushi sannan tace " Allah ya kaimu mummy, Allah kuma yabamu sa'a" kallon damsel hajiya rabi'a tayi tace " kinga na manta bantambayi sunan ki bako?" Damsel tai murmushi sannan tace " sunana noor" dukkan su suka ce masha Allah.. hajiya rabi'a ta kalli zara tace "kaita dakin ku tai sallah sai akawo mata abinci." zahra ta tacema damsel "taso muje"mikewa damsel tayi tabi bayanta.. da asuba hafsa ta farka ta shiga bandaki dan dauro alwala, bayan tafito ta shinfida sallahya ta tada kabbara. Nabeel ne yafito cikin cream jallabiyar shi. Har ya sauko, sai kuma ya tuna da Hafsat, hauro wa yasake yi ya bude kofar dakin ta da sallama,ganin tana kan sallaya yasa shi rufo mata kofar ya sauko ya wuce masallaci.. karfe takwai Hafsat ta farka ta shiga wanka. cikin maroon lace mara nauyi ta shirya, flay gown da yai mata kyau sosai amma bata daura dankwaki ba, tafara bin scope din da Hauwa ta bata. tana downstairs tana hada burner a socket tana son sa turaren wuta taji an bude kofa, da sauri tajuyo dan batasan nabeel yafita ba.. Nabeel ne yashigo rike da ledoji biyu daya bread ne sai dayan kwai ne ciki. Hafsat ta kunna burnern tare da mikewa gaban ta na fadi, nabeel yaso yai ignoring kallon dayake ma Hafsat amma ya kasa, suman kanta datai parking ya dinga kallo, karasowa inda yake tayi tana kokarin karban ledan dake hannunshi tace " good morning" kasa amsa gaisuwar ta nabeel yayi ya tsaya kallon sumar kanta. har ta shiga kitchen da kayan nabeel baidane kallon ta ba, ajiye car key dinshi yayi kan centre table sannan ya haura sama.. shabiyu saura nabeel na zaune a palo yana aikin duba agogo dan tun dazu yakeson fita Sadeeq ya tsayar dashi. yafara dialing numbern Sadeeq kenan yaji knocking a kofar. mikewa yayi ya isa kofar ya bude, Sadeeq ya shafa kanshi akasa yafara murmushi, nabeel yace " don't even think of that " bayan sun karasa palo Sadeeq yanima kujera ya zauna, nabeel ma ya zauna sannan yace " kasan jibi yakamata mukoma right?" Sadeeq yace " yeah ban mantaba guy, ya amarya ta kwana? Hope you are taking care of my lil sis?" Nabeel yace "jiya jiya fa kuka bani ita" yana fadin ya mike tare da cewa " a minute please" dakin Hafsat ya shiga, tana gaban dressing table tana shafe shafe dan wanka tasake yi. jin anbude kofa yasa hafsat juyowa " kauda kai nabeel yayi da sauri ganin ta daure da towel, sannan yace " Sadeeq is downstairs" kullo mata kofar yayi ya sauko.. kallon shi Sadeeq ya dunga yi ganin yananyin shi, saurin dauke kai yayi ganin nabeel din ya dago kai. suna zaune ahaka. nabeel kuwa addu'a yake kar hafsa tafito bata rufe jiki ba.. ( su nabeel da kishi) bude kofar da sukaji yasa nabeel daga kai yana kallon Hafsat. hijabi har kasa sky blue tasa ajikinta, wani sanyi nabeel yaji sannan ya kauda kanshi. Sadeeq kuwa kan shi akasa har hafsat takaraso palon, da murmushi a fuskar ta tace " ya Sadeeq welcome" sai sannan Sadeeq yadago shima da murmushi sosai a fuskar shi yace " amarya.. ya kwanan bakon wuri" murmushi tayi batace komai ba, kafin ta mike tai hanyar kitchen, binta da kallo nabeel yayi da gefen ido har ta shige. Sadeeq kuwa wani murmushin yasake yana ganin al'ajabi,. shidama yasan nabeel yanason hafsat kawai taurin kai ne ke damun shi. fitowa hafsat tayi rike da tray dauke da ruwa da cups guda biyu, dan ruwa ne kawai agidan tukunna. mikewa nabeel yayi tare da cewa barin shirya, yanzu zan fito.. Hafsat kuwa ajiye ma Sadeeq tray din a side stool din dake kusa dashi sannan ta dawo ta zauna kan 1sitter. daukan ruwan Sadeeq yayi ya bude ya zuba a cup yasha sannan ya juyo yana kallon Hafsat.. sosai yashiga mata nasiha dakuma kuma nuna mata hakurin zaman gidan miji. kanta a kasa har ta fara hawaye, sai yan wasa da yatsunta da takeyi. saukowa nabeel yayi yana kallon Sadeeq da duc attention din shi akan hafsat yake.. Sadeeq ya mike tare da cewa "toh lil sis, I wish you nothing but the Best, and I know you won't fail me.." Sadeeq yafara fita, nabeel ya juyo yana kallon Hafsat da sunkuyar da kanta hawaye baidena zuba mata ba.. rasa me zaicemata yayi kafin yai gyrarar murya yace " I'm going out.. anything you need idan zan dawo?" girgizamishi kai kawai tayi dan ta kasa magana. Nabeel ya bude kofa ya fita.. hafsa kuwa bayan sun wuce ta haura sama, ganin missed call din zee tayi, saida ta cire hijabin jikinta sannan ta haura saman gado ta shiga kiran zee. zee na dauka ta shiga ma hafsat tsiya " matar yayana.. ana dakin oga ne haka da ranar Allah? wayace miki ana haka, ko dan jan ajin nan babu, j kamar kina jira??" tunda zee tafara magana hafsat ke jinta batai interrupting dinta ba har saida tagama kafin hafsat tace " toh sannu da kokarin bayani, yaushe zakuzo keda Hauwa?" xee tace "kibari kawai sai kundawo kar aga zakewar mu, tunda kinga jibi zaku koma garin yarbawan ku" Hafsat tai saurin cewa " tafiya kuma? wayafada miki?"tuntsirewa Xee tayi da dariya sannan tace "au baima fada miki ba ? saboda tsananin wutan da akeba ma yayana kinga har ya manta ma bai fada miki ba, toh nidai wlh a bimun yaya ahankali" ba iskancin da xee takema Hafsat bane yasa tai shiru, tunani tashiga yi yanzu da ita nabeel zai koma Lagos?? ta ina zata fara? batadai nuna ma xee komai ba har suka yi sallahma ta kashe wayar ta sannan ta mike ahankali jiki a sanyaye tashiga bathroom dan ta dauro alwala.tana idar da sallah ta sauko kasa dan tafara dan jin yunwa..tea tahada sannan ta fito ta haura sama, tana gama sha ta hau gado tai kwanciyar ta.. sai wajan karfe hudu da rabi nabeel yadawo gida, shima dan Sadeeq ya matsa mishi ne yakoma, kafin nabeel yakoma gida saida yasiyo gasassun kaji sai milk drinks da ruwa ya dau hanyar gida.. Sadeeq kuwa yana shiga gida yai part din abbanshi zuwa amsa kiran da ya mishi. su biyu ne a dakin shida alhaji muktar. yana shiga bayan sun amsa mishi sallaman yanima waje kasan carpet din ya zauna sannan yashiga gaishe su.. alhaji mukhtar yadawo da hankalinshi kan Sadeeq yace " Abubakar matar ka shiru ba labari har yanzu ko?" Sadeeq yai murmushi kawai kafin yace " za'a ganta in sha Allahu abbah." alhaji muhktar yace " toh Allah ya bayyana ta cikin lafiya,saidai abubakar zamanka haka bazai yiwuba gaskia, mahaifiyar ka ta mana bayani jiya akan wata yarinya, ai kasan da maganar ko?" Sadeeq yace "nasani abbah" alhaji Mukhtar yace toh Alhamdulilah, yanzu mu baza mu matsa maka ba,kai yaushe kake ganin zaka shirya sai afara magana?" Sadeeq yakara sauke kanshi kasa yace " kudan bani lokaci abbah, in sha Allahu idan nakoma nadan gama wasu ayyukan da nakeyi, zan muku magana in sha Allahu" abbanshi da tunda aka fara maganar bai ce komai ba sai yanzu " toh ita yarinyar kana sonta ??" Murmushi Sadeeq yayi tare cewa " we are getting to know each other abbah" alhaji Mukhtar yace toh shikenan, Allah ya maka albarka, sai munji daga gareka, you can take your leave.. godiya Sadeeq yai musu sannan suka ya mike ya fita... yau ya kama Sadeeq zasu koma Lagos, a tsaitsaye sukai sallama da mami sai hauwa da tazo gidan gaishe da mami ranar. Sadeeq na duba agogo yace in sha Allahu mami kar ki damu.. I will call her idan na isa, barinyi sauri mal idi najira na..mami tace " toh shikenan Allah ya kaiku lafiya, ka gaishe min da hafsat din" har waje Hauwa taraka shi sannan driver yaja shi suka wuce.. karfe hudu suka shigo lagos, bayan Su nabeel sun shiga gida Sadeeq ma yawuce nashi gidan... sosai damsel ta maida hankali kan karatun ta kuma dama tunda tanada kwazo nan da nan take daukan darasinta, sai abubuwan zaman rayuwa da take koya, kuma har ta fara sabawa da sauran yan matan wajan..hajiya rabi'a kuma sosai ta dage akan su kuma, ba abunda bata musu, da sunkai wajan su 17 yanzu su tara suka rage dan duc ta aurar dasu wasu kuma na kan hanya... Sadeeq kuwa yana dawowa ya koma kan aikin shi gadan gadan. yau kwanan su uku da dawowa kuma basu hadu da nabeel ba, ganin yau Saturday yana gida yasa tai deciding bari ya leka su.. da Isar shi gidan ya bude kofar palon..nabeel yagani tsugune a gaban hafsat dake kan kujera, idanun ta duc ya kunbura da kuka.. yana ganin Sadeeq yamike tare da dan susa kai yace " welcome man"Sadeeq ya sauke kanshi kasa yana murmushi ganin aika aikan da abokin nashi yayi. saiyaji dama bai shigo ba ganin privacy din su ne.. a kunyace hafsat ta gaishe shi da muryar ta dabaya fitowa sosai.. Sadeeq ya amsa mata duc tabi tabashi tausayi, mikewa tayi ahankali tana kokarin takawa, saiga nabeel ya riketa da sauri yana kallonta kamar zai maida ciki.. Sadeeq na ganin haka ya juya yafita...


...Sadeeq na dawowa gida ya shiga ya dan watsa ruwa dan yana son fita anjima to get some few things a super market. yana gama shirin shi ya bude daki yafito, a zaune ya tadda nabeel ya dora kafa daya kan daya yana latsa waya. Sadeeq na ganin shi yai murmushi tareda karasowa palon ya nima 1sitter ya zauna sannan yace " har ka gama jinyan ne? Ko barin musu yar mutane kayi" nabeel yai shiru kan shi akasa dan bai taba tunanin akwai heaven on earth ba, jiya hafsat ta birkita mishi lissafi da daddare, sai yadawo kamar ba nabeel din ba.. Kallon Sadeeq yayi tare da dan murmushi yace " cewa tayi tanason cin shawarma.. don't know if you can escort me to get it for her please" Sadeeq ya kura ma nabeel ido yana ganin abubuwan mamaki kalakala a tare da shi, yadda yake abirkice har lokacin..sannan yace " har kanwar tawa tafara aiken ka kenan ?? anya nabeel din da nasani ne kuwa??" yana fadin haka ya dauki car key dinshi tare da cewa "I'm so happy that you have finally found Peace nabeel, I've been praying for so long to witness this day. Allah yakara hada kanku Bro... I'm so proud of you" rumtse ido nabeel yayi trying hard not to shed tears sannan ya mike ya rungume abokin nashi " this is all your doing, you try so hard to make this possible, and I will forever be grateful..hafsat has become someone that I can't leave without. thank you so much for this precious gift that you have blessed me with, brother.. may Allah bring back your happiness soonest..I'm soo sorry for what happened back then, I couldn't support you when you needed that from me,.. I'm sorry bro.." Sadeeq yai murshi zuciyan shi na niman karaya, amma sai yai anfani da jarumtar shi yace " stop this please nabeel, you're breaking me with all these your words, you've done nothing wrong to me, you were looking out for me, which I understand.. don't worry nabeel, Allah knows best.. Just be happy. this is all I want" suna dawowa Sadeeq ya ajiye nabeel a gate din gidan shi sannan shima ya karaso gida... haka rayuwa tacigaba da kasancewa akwana a tashi ba wuya..yau hafsat da nabeel suka samu karuwa na dansu namiji kyakkawa yaro wanda yai kama da uwar shi..anci suna suna sosai a kano anyi shagali inda yaro yaci sunan "ABUBAKAR SADEEQ"sannan bayan sati suka tattaro suka dawo gida.. Mami kuwa har tayi mita akan Sadeeq yakara aure ta gaji, tayi kuka har tagaji, saidai kawai yanzu tadage mishi da addu'a sai sadaka da duc ranar juma'a takeyi tare da dunbin addu'o'i duc inda damsel tashiga Allah ya bayyanar musu da ita ko hankalin danta da nata zai kwanta.. yan yobe kuwa ko kadan basu yanke zumuncin su da mami ba, watarana sukan kawo mata ziyara, itama takan je. Hauwa danta namiji har yayi wayau wanda yaci sunan kakanshi,mahaifin ubanshi,"Umar" suna kiran shi adeel.. yau da asuba nabeel ya shirya yafitabl saboda meeting din da suke dashi, hafsat na kokarin hada mishi breakfast a kitchen yashigo rike suite dinshi a hannu, rungume ta yayi ta baya yace " babe koma kawai kiyi baccinki, I can't wait for breakfast dan nayi latti ma ahaka, idan boy ya tashi,tell him I love you both" dariya hafsat tayi tare da juyowa ta kai mishi kiss.." alright my hubby, I will tell him, ya Sadeeq yace zai zo karfe hudu su fita ma" nabeel yace " za'a ware ni kenan yau, fitan na namesake da namesake ne kenan? No problem.. I'm off babe" har mota hafsat taraka shi tare da mishi tuni kar ya manta da ayayon da tace ya siyo mata.. Karfe hudu nabeel ya tashi wajan aiki, sannan yashiga niman ayayo.. ganin baisamu ba yasa ya dauki waya ya kira al'amin, nan al'amin ya shiga yin mishi kwantancen inda zai samu sannan sukai sallama.. al'amin kuwa yanaahigowa unguwan ya sauko daga motar shi ganin yai hanyar dan karamin kasuwar da yagani..wazai gani tazo zata wuce shi..Damsel,..hijabi ne har kasa ajikinta mai bala'in kyau da sheki sai dan karamin leda da ta rike a hannu.. arikice nabeel yace "Damsel!!" Juyowa tayi da sauri gaban ta na fadi tana nanata innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un azuciyar ta.dan rabon da taji ankira ta da wannan sunan ta dade.. juyowa tayi ahankali tana son ganin ko waye. Nabeel kuwa ganin ita din ce ba wataba mai kama da itaba yasa yace "ALHAMDULILLAH YA ALLAH" aganin shi kamar bai taba shiga farin ciki kirin wannan ba.. Damsel tana ganin nabeel ta gane shi, murmushi tayi sannan tace " NABEEL" kasa rufe baki nabeel yayi sannan yace " where have you beel all this while?? we have been looking for you for so Long.. sadeeq is so worried.. why did you do that??" Murmushi kawai damsel tayi sannan tace " I hope he's happy now??" Kasa ce mata komai nabeel yayi, bude motar shi yayi yace " get inside please let's talk " shiru damsel tayi tana kallon cikin motar, amma bata shiga ba. Nabeel ya tsinke mata tunanin ta sannan yace " trust me, I just want us to talk" kallon shi damsel tayi sannan ta shige motar ahankali ta zauna. Nabeel ya kulle kofar tare da zagayawa ya shige shima, sai yake ganin kamar mafarki yakeki, yana shiga ya kalli damsel sannan yafara magana, halin da sadeeq yashiga akanta ya shiga bata.. Shiru damsel tayi kafin tace " don't tell me he's still not happy even after he married hafsat" kura mata ido yayi for ten seconds, wato she left sadeeq because of hafsat ?? ahankali nabeel yace " I married Hafsat" arazane damsel ta juyo tana kallon nabeel.. kafin tayi magana nabeel yace " yeah, hafsat is now my wife we even have a child now .. Sadeeq never dated hafsat.. he looks at her like a sister and nothing more..you left him in pain Dansel, he's still in pain.. and he promise never to go after you, come home please.." Kasa rike kukan ta damsel tayi.. yanzu sadeeq baiyi aure ba yana nan har yanzu yana jiranta?? to ko ta koma me zatabashi? tunda ba haihuwa mishi zatayi ba..wani kukan tasa sannan tace " I can't go back nabeel, I can't ..I want him to be happy.. he's better off without me" nabeel yai shiruu sannan ya fito da paper da pen ganin har tabude kofa zata fita.. ahankali yagama rubutun sannan ya bude jakan ta yasa mata yana kallon ta "if you change your mind, this is the address.. I can't force you.. this is going to be your decision, you have to make that yourself..".. har ta fita ta kulle mishi kofar tafara tafiya bai dena kallonta ba saidayaga ta shige wani layi sannan ya dauke kanshi.. yakai minti goma yana zaune a mota kafin yafito yasiyama hafsat abunda tabukata sannan ya shige mota ya wuce gida..damsel kuwa tana komawa gida ta ajiye abunda ta siyo a kitchen ta shige daki.. Kuka sosai taci banawasa ba ga tausayin sadeeq dake niman hallakata, komawa ne dai bazata iyaba.. har sukayi sallahr isha hajiya rabi'a da sauran yan matan gidan na lura da rashin walwalar ta, saidai basu ce komai ba ganin itan dama ba mai yawar magana bace..nabeel kuwa ba Wanda yafada yaga damsel in ba hafsat ba..itama saida akayi two days yafada mata, taci kuka kuwa ranar, nan tashiga rokon shi akan yakoma ya dauko ko bata yadda please... Nabeel yace, abarta tayi making decision dinta da kanta, dan ko andauko ta batare da yardar taba zatasake guduwane, and that will break his friend completely.. nan yace mata kar ta fada ma kowa.. Saidai farin cikin shi, baiganta cikin halin banzan da yai tunani ba., kila idan da rabo toh zata dawo..yau sati daya kenan hajiya rabi'a tana lura da damsel sai wata da suka shaku da damsel agidan Zubaida.. suna zaune da Zubaida adaki tana tanbayar ko me ke damunta kwana biyun nan, dan karo na uku kenan zubaidan na tamyarta dan itama ta damu, sosai take ma damsel kallon yar uwar ta najini. zubaida na kallonta idon ta har yafara tara hawaye tace " noor baki dauke ni amatsayin yar uwar ki bako? so kike nima nashiga damuwa har ciwo yakamani kafin kifada mun me ke damunki ko?" ganin hawaye a fuskar zubaida yasa damsel mikewa daga kan sallahya ta karaso kusa da ita ta kanta kan kafadar zuby sannan tace " zuby bansan ya zanyi da rayuwata ba, tun da na fito duniya har yau ban samu farin cikin da kowa ke samu ba, koda na rana dayane, da na fita daga wani nake shiga wani" zubaida ta rungume damsel sannan tace " me yake damunki yar uwata?" damsel tai shiru kafin tabude baki tafara magana, " zubaida ni matar aure ce.." banda zubaida, har hajiya rabi'a dake kofar dakin tana jinsu saida taji mamaki, ducda tasaba jin cases haka, amma na damsel yabata mamaki. zubaida tace " kina da aure fa kika ce??" Damsel na jikin zubaida tace " kwarai kuwa, ina da aure, mijina mai sona, mai kaunata, Wanda sanadiyyar shi nasan abubuwa masu kyau na rayuwa, sanadiyyar shi na fita cikin duhu nashigo haske,shine dalilin dayasa rayuwata haske, yamun son da shi kanshi baima kanshi wannan son ba, son dayakemun mahaifiyata kadai ta taba mun,.. but i failed him at the end.." nunfashinta har yana niman tsayawa saboda kukan ma ya gagara fitowa.. zubaida kanta yai mugun kullewa, kafin tace " toh meyesa kika barshi

Please Login or Register in order to submit comment