Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga tunani iriri dayakeyi a zuciyanshi. yace " zo gashi Muhammad, kabi ameenu inda ake biyan kudin, sai kabiya.." Muhammad yana kokarin cema uncle abu ya barshi zaibiya, al'amin yace "I've settled that uncle abu" uncle Abu yace toh Allah yayi albarka. Suna fita khadija ta na rike da damsel har gurin motar ta sannan tabude mata front seat tashiga. uncle abu kuma shida da Muhammad suka shiga motar al'amin Muhammad yaja motar, Sadeeq yashiga motar nabeel tare da al'amin din kafin duc suka kama hanya. nabeel naso yaima abokin nashi magana, amma ganin al'amin agurin yasa bai ce komai ba. al'ameen kuwa yana bayan mota ya Kalli Sadeeq yace "sharifan duniya, har yanzu wlh Sadeeq kwakwalwana yakasa daukan wannan al'amari, you're indeed a hero.. and thank you so much for..." Sadeeq bai bari yakarasaba yace " come on dude, no need please. ai ni yakamata in ma godiya. You're the reason for everything, da yanzu bansan ta inda zan fara niman familyn ta ba. you don't know how happy I'm right now." "oga nabeel dai tukin shi yaketayi without uttering a word, har suka isa gida. suna dawowa sallahr Magrib kuwa har khadija tagama arranging musu abinci a dining kafin ta haura ma damsel da nata, har tayi wanka ta chanza kaya sai ga shigowar khadija da tray a hannu. Bubu na material ne ajikinta, sai suman ta daya kwanta abayanta, comb ne a hannunta tana tacewa. Khadija na ganin kirin kyan da tayi, nan ta washe baki tace "mata agidan ABBBAKAR SADEEQ da kanta" damsel kallon ta kawai takeyi kafin ta ajiye comb din ta koma gefen gado ta zauna. khadija ta takaraso ta ajiye mata abicin akan karamin stool din da ke dakin, sannan takaraso gurin damsel daketa wasa da dan yatsun ta kanta akasa. rungumeta khadija tayi soosai ajikinta na wajan minti biyar kafin tai karfin halin cewa "I'm so sorry for everything you went trough my love... we have so many things to talk about, but not today, barin barki ki huta kikara jin karfi tukunna. kinyi sallah?" damsel ta girgiza mata kai, alamar aa, khadija tace yi sallahr ki barin yi wanka nima inyi sallah, and make sure kinci abincin please, dan idan nadawo zanbaki drugs dinki. khadija na fita damsel ta mike taje kan sallahya tare da daukan hijabi ta zura tafara sallah. su Sadeeq har Sun dawo daga masallaci sunfara cin abinci. Suna gamawa, uncle Abu ya duba agogon hannunshi kafin ya Kalli Sadeeq. " toh abubakar, mu zamuwuce masaukin mu yanzu in sha Allahu, karfe biyu kuma zamu koma washe gari in Allah ya kaimu. Kuma zamu koma tare da noor, naso barinta tadan kara samun kafiya kafin inzo in dauketa, amma kakanta ya matsa sosai. Insha Allahu bakomai. duc yadda kayi da iyayenka, sai ka kirani, ai makobta ne mu, kano da yobe ai kamar baki da hanci ne. zanbaka number na. Allah kuma yasaka ma dukanku da alkhairi." duc Suka amsa da ameen kafin sukai exchanging contact, al'amin ya mike dan yakira khadija suyi sallahma. Hijabinta har kasa ta sauko, uncle abu yafada mata tare zasu wuce da damsel gobe karfe biyu kafin sukai sallahma, Muhammad ya mike yama su Sadeeq sallama kafin yabi uncle abu suka fita. Nabeel ma ya mike yabi al'amin dan su raka su mota. Suna fita Sadeeq ya Kalli khadija yace " can I see her please?" khadija tace "sure sannan tai directing dinshi dakin da damsel take kafin ta sauko. da sallama ya bude kofar yashiga. tana zaune gefen gado tana kallon abincin, jin sallaman Sadeeq yasa ta dago da sauri. Sadeeq yakaraso dakin sannan ya maida kofar ya kulle. yana tsaye a jikin kofar yana kallonta, ahankali yace "Noor.." dago kanta tayi tana kallonshi.. Sadeeq yai murmushi.."I'm so happy that you have found your family.. and your uncle said you're going with them tomorrow.." kukan da take ta rikewa ya kubce mata jin abun da Sadeeq yace.. Sadeeq yana ganin haka yai saurin karasowa ya tsuguna agabanta ya riko hannayenta duka biyu tare da kallon cikin idon ta " why Noor, let it go please, Komai ya wuce dan Allah, ain't you happy.." fisge hannunta tayi tare da mikewa tace "NO!!!"....

...inda damsel take shiga ba nan take fita ba, wasu abubuwan ma da take fadi, bawai suna da ma'ana bane. ita dai she has nothing to do with them anymore..sadeeq kuwa sosai ya shagala yana kallonta, sosai ya fahimci abubuwa da dama a tattare da ita,.. na farko ya fahimci tana da rauni sosai, and she doesn't easily let things go. kuma tana da tsiwa idan taso yi... jin tight hug din da Sadeeq yamata abaya ne yasa tai tsit, sai kuma ahankali tai kokarin ja dabaya, amma Sadeeq yaki barinta. Jin cool voice dinshi tayi yace " is this how you are going to be treating me in your house babe? meaning idan nayi miki laifi kawai kar indawo miki gida that day kenan.." juyo da ita yayi suna facing juna, fikifiki tayi da ido kamar ba damsel din da tagama tsiwa yanzu ba. kallon bakin kawai Sadeeq ya dinga yi kafin yace " Noor... kinsan kirin billions of laifukan da kullun muke ma ubangijinmu?? and guess what? muna rokon shi yake yafemana, toh meyesa ke kike da riko? ko kadan ba abu me kyau bane ba asan musulmin kwarai da riko ba, and if anything ma, basu da laifi ko kadaya, idan akwai mai laifi toh abbah ne kadai, I mean your father, kuma he asked you for forgiveness. look at how they love and cherished you, I can boldly see the love in their eyes most especially your brother.. kuma na tabbata you heard everything that uncle abu was saying back there at the hospital, tunda nashigo naganki nasan ba bacci kikeyi. I can always tell when you're sleeping or not.... riko hannayenta yayi duka biyu kafin yakara kiran sunan ta ahankali... sosai yashiga mata maganganu masu ratsa zuciya kafin daga karshe ya jawota ya zaunar akan gado yana kallonta.. " do this, and make mama proud please. and she's in a better place in sha Allah.. sosai yasa jikin damsel yai sanyi, and for the first time maganganun da yamata yasa sukai tasiri azuciyanta, jin ya anbato mata mahaifiyarta...Kallon abincin da khadija ta shigo mata da shi tun dazu yayi, ganin ko tabawa batayiba yasa yace " bakici abincin ba Noor, or you want me to get you something?" da sauri tace "No.. I will take tea." are you sure?? damsel ta gyada mishi kai kawai. duba agogon hannun shi yayi yaga har lokacin sallahn isha yayi kafin yadawo da kallon shi gun damsel " I will be on my way Babe, I will come back tomorrow morning in sha Allah kafin ku wuce." ahankali noor tace toh, zuciyanta namata wani kiri. saida ya fita sannan ta dago kanta tabi kofar da kallo kafin ta mike tai hanyar bathroom.. Sadeeq na saukowa yaga al'amin da nabeel sunata faman musu akan kwallo.. Sadeeq ya kallesu duka kafin yace "musun ya tashi kenan?" al'amin yai daria, nabeel kuma yace "barshi dai ya raina ma kanshi wayau" Sadeeq ya kalli al'amin "can I speak to khadija please? dan muna fitowa masallaci zamu wuce." al'amin ya mike tare dace "why not.." a tare suka sauko dan lokacin har ankira sallah, nabeel ya mike ya kallesu kafin ya fita, al'amin kuma ya shiga guest toilet din dake kasa dan yai alwala. Sadeeq daga tsayen da yake ya Kalli khadija" the chef the chef.." khadija tai daria abunta. Sadeeq yakara da cewa " I'm grateful for wht you've been doing dija.. thank you so much. Allah kuma yabar zumunci. and please, gobe in sha Allahu uncle abu yace zasuwuce yobe,...kamar Sadeeq na nazarin wani abu, sai chan kuma ya Kalli khadijan dan duc maganar da sukeyi kanshi akasa. yana kallonta yace " please talk some sense into her. it seems like she's still holding it, you know how to do this, I trust you." khadija ta dago kanta, lokacin har al'amin yafito. "that won't be an issue in sha Allahu, and about the thanks, you said earlier, don't ever say that again please, saboda ba wannan tsakanin mu, noor is my sister.." tana fadin haka tai mishi saida safe ta haye sama... Suna fitowa masallaci sukai sallahma da al'amin kafin suka wuce. Khadija kuma tana idar da sallah ta dauki wayanta tasa ma su iman game, dan sosai ta killace su adaki dan kar su damu kowa. tana mika musu wayan ta nufi dakin noor. Kofin tea tagani a hannunta har ta kusa shanyewa, an dauke tray din abincin kuma. bayan tagama bata magungunanta, ta nima waje ta zauna. ahankali takira sunan ta. Noor ta dago fararen idanunta tana kallonta...sunkai wajan 9:30 da khadija a daki. khadija ta rike hannunta sannan tace " do you understand all wht I said to you??" ahankali damsel da jikinta duc ya mutu tadago ta kalleta "Yes" with a big smile on khadijas face ta rumgume damsel.. nabeel tukin shi kawai yakeyi, ko kadan he's not comfortable, yakasa sakewa ma da abokin nashi, yaso yabashi labarin nadeerah, amma kawai sai ya share. Sadeeq da ya lura nabeel na dardar, abun ma dariya yaso bashi, ashe akwai abinda zai iya mayar da nabeel haka, nabeel dai dayasani? juyowa yayi yana kallon shi ganin sunkusa karasowa gida.." muwuce gidan ka kawai, nasan mine is dusty by Now" nabeel yace "dama cemaka nayi gidan ka zan kaika??" Sadeeq azuciyan shi yace " the nabeel I know..." sannan yai murmushi. Suna isa gida Sadeeq yafada bathroom din nabeel yai wanka,yana fitowa ya ciro daya daga cikin pyjamas din nabeel yasa sannan ya feshe jikin shi da turaruka ya kwanta. yana son kiran damsel, amma ganin nabeel har lokacin a zaune bakin gado yana kallon sport a makeken plasma TVn dakin yasa yai addu'o'in shi kawai yaja duvet ya kwanta.. sai wuraren 11 nabeel ya mike ya shige bathroom, shima wankan yayi ya chanza kaya kafin ya dauki wayoyinshi ya fita daga dakin.. washe gari Karfe daya daidai, uncle abu ne zaune a palon gidan al'amin, daga shi sai damsel.. maganganu sosai yamata Kuma duc yawanci tarin hakuri ya dinga bata, sai kuma rokon ma dan uwanshi Kuma ubanta garafa daya dunga yi awajanta. kuma duc yawancin maganar dayai mata, khadija ma tamata jiya. da haka hankalinta ya kwanta sosai. Su Sadeeq duc suna waje tare dasu al'amin. Nabeel kuwa yazage yana uban zuba surutu da Muhammad, ba akan komai ba, sai akan kwallo. dayake club dinsu daya da Muhammad din, unlike al'amin da kowa club dinshi daban, shiyasa Idan suka fara musu toh fa baji. Uncle abu yanagama ma damsel nasihohin dayake mata ya Kalli agogo yaga har daya ta gota. Shiyafara mikewa kafin yace " this all I can say to you for now my daughter, Allah kuma yamiki albarka. Now, jeki ki sallami yayarki Hadiza kizo muwuce." ahankali damsel ta mike, atanfa ne ajikin ta dinkin riga da skirt, sai stones da yasha agaban rigan. Sai gyale medium da tasa tare da handbag dinta baki sai black bakin flat shows dinta da ta zura. Sosai bakin lallen da khadija takira wata tazo tamata da safe yai mata masifan kyau, gashi yahadu farin fata. tare suka sauko da khadija bayan takara mata fada mata wasu kananan abubuwa akan na jiya. suna fitowa har su uncle abu sun shiga mota, al'amin da Sadeeq ne kawai a waje.. har ga Allah at first Sadeeq baigane damsel ba, sai da takara matsowa. kallonta yakeyi ko kifta ido babu, anfani yayi da calmness din dake tare dashi ya nuna bai girgiza da yanda khadija tai transforming mishi Noor ba. nabeel da kam yana cikin motar shi tare da Muhammad, gabanshi shi ya dunga fadi da ya ganta, sai yanzu ya tabbatar da dalilin dayasa ya tsaneta. "he has feelings for her" da sauri ya kauda wannan tunanin azuciyan shi. har suka karasa airport nabeel couldn't stop feeling whts he's feeling inside him. damsel na motan sadeeq, ita da shine kadai amotan, shi kanshi tsoro ne fal zuciyanshi, gani yake kamar idan ta tafi Sun rabu kenan. saidai idan ya tuna da alkawarin uncle abu ya mishi saiya dan ji sanyi. suna isa yai parking sannan ya juyo yana kallonta, hannunta ya riko duka biyu da idanuwanshi da suka chanza kala yafara magana " Noor, ...promises me that no one will take you away from me please.. please noor" damsel ta dinga kallonshi, kafin tafara wani tunanin itama ( someone like who kenan?? yana tunanin yadda ta yadda da shi zata kara yadda da wani namiji ne a duniyan nan? So wht is trying to say exactly?) yanke mata runani yayi yace bakice komai ba?? zatayi magana al'amin yakaraso ya kwankwasa motar. Sadeeq ya saketa da sauri yafito, al'amin yace " uban me kasa musu yar mutane agaba kana kimtsa mata?" Sadeeq baiko kalleshi ba dan yasan waye al'amin, bai yadda yabiyeshi mishi kamar yadda nabeel ke biye mishi. Zagayowa yayi ya bude ma damsel kofa ta sauko ahankali.. In 10 minutes jirgin su yadaga.. zuwa maiduguri dakanan su shiga mota yakai su damaturu dan ba direct flight to yobe....

...karfe 4:45 suka shigo cikin maiduguri. har drivern abokin uncle abu yakaraso. Karban motan sukayi sannan Muhammad yabashi 5k akan yayi kudin motan komawa gida, kafin yaja su suka dau hanya. Bacci sosai damsel takeyi abayan mota, ga wani kirin gajiya datayi. tafiyar 1:30 minutes sukayi sai gasu acikin damaturu, dan sosai Muhammad yake gudu, dama uncle abu bai da matsala da over speeding... direct cikin unguwan su uncle abu ya shiga. "Ben kalio estate" dake cikin garin damaturu. suna isa Muhammad yai horn maigadi ya bude musu gate. sosai damsel take bacci. Uncle abu har ya fita yana ma mal. yakubu magana. juyowa Muhammad yayi yana kallon kanwar nashi dake ta faman shan baccinta. Sosai yake ganin fuskar mahaifin su idan ya Kalli fuskar ta.. har yaran uncle abu Sun fito.. Muhammad yana ganin su mimi sun fito, shima ya bude mota yafito da sauri. da gudu mimi takaraso da ihunta ganin Muhammad, wanda yasa damsel ta bude ido da sauri. uncle abu da har lokacin yana magana da mai gadinshi. shima juyowa yayi jin ihun da yar tashi ta saka yasa yafara mata masifa " meyesa wai bakida hankali ne wai Aisha??" Muhammad yai daria kawai tare da zagayowa ya bude ma damsel kofa.. "come down sis" Mimi da har ta karaso inda damsel take, ganin tana kokarin saukowa yasa mimi ta rike mata hannu da sauri suka sauko tare. suna shiga ciki, Muhammad yabi uncle abu suka wuce masallaci.. sosai matar uncle abu hajiya karima sukai welcoming damsel kamar zasu hadiyeta... karfe 8:30 su uncle abu suka shigo, lokacin kuma damsel har tayi wanka a dakin mimi ankai mata abinci.. Muhammad kuma ya shiga part din yayan mimi shima yadan watsa ruwa, sannan aka shigo musu da abinci..

.....Sadeeq kuwa suna dawowa, ya dau hanyar gidan shi. Sosai Joseph yai farin cikin dawowan ogan nashi, sai gani yake kamar ya shekarane da tafiya. gidan kuwa fess dashi, tundaka compound har cikin cikin gidan, sai dan kura da yayi kadan. Sosai Joseph ya shiga ya gyara mishi gidan, tunda ba wani aiki bane sosai. Bayan yagama Sadeeq ya shiga dakin shi yai wanka sannan ya fito palo. tunawa yayi baida komai a gidan gashi ko kadan baya son fita. daukan wayan shi yayi ya shiga kiran mamin shi, tana dauka suka gaisa sannan ta shiga sa mishi albarka " I'm so proud of you son.. Allah yakara basira. Abbanku ya nuna mun new model din kuke kokarin fitowa da shi. You need to see how proud he is when showing them to me. Sadeeq yai murmushi kawai, sannan yace " kibari yafito kigani mami" daria tayi sannan to Allah ya fito dashi lafiya son... and ita yarinyar da kamun magana akanta wanchan ranar, kace itama yar Kano ce?" Sadeeq da kamar jira yake, nan yace " no mami, yar yobe ce, jiya ma kanin abbanta yakara mun magana akan duc randa abba ya shirya suna son suje in sanar da su." mami tace " toh Sadeeq aje maganar aure ba'ayi bincike ba? na dai fara ma abbanku magana, idan kazo sai kuyi magana ta fahimta dashi sosai, kaga idan akayi bincike ko yar wata gida ce, ai sai kawai abbanku ya tura tunda kawun na gari har yanzu bai koma ba. Mudama ai abinda mukeso kenan. Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Sadeeq ya amsa da ameen duc jikin shi a sanyaye jin wai za'ayi bincike, amma idan ya tuna daga familyn su al'amin take, sai ya danji hankalin shi ya kwanta.. Mami tace " ashe halinku na maza Kake ma Hafsat? yarinyar da kullum tana gidan nan, bikin hauwa'u da za'ayi komai tare sukeyi, ducda nasan kawar ta ce, amma wasu abubuwan ai don Kai takeyi, yanzu da wani ido zan Kalli mahaifiyar ta?" Sadeeq ya lumshe idon shi ahankali kafin yabude ya fara magana " mami ku kuka dauki maganar nan dama tun farko, ni wlh kallon hauwa nake mata, dama nabari idan nazo kano inje insameta muyi maganar fahimta.. amma.." sai kuma yai shiru. mami tace inajinka.. Sadeeq yace " amma ai nabeel yanasonta mami." mami tace " toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi" ameen Sadeeq yace tare da mikewa yai hanyar fita.. yana gidan nabeel bayan sundawo masallaci yai dialing number damsel har so biyu ba'a dauka ba, nan ya shiga kiran Muhammad,.. Muhammad da ke ta faman hira da Aliyu yayan su Mimi, duc ya birkice akan cousin din nashi dayagani, shi aganin shi yasamu mata, sai ga call din Sadeeq ya shigo, Muhammad ya kalli Aliyu ya girgiza sannan yai picking call din Sadeeq, gaisawa kawai sukayi da Sadeeq yafada mishi Sun isah kafiya sannan sukai sallahma. Sadeeq yakasa tambayar ko ya damsel take. nan Muhammad ya juyo ya cigaba da kallon shirmen da Aliyu ke mishi, kafin yace " wai kai baka gajiya ne? yau amira, gobe Hanan jibi ummi.. duc kai kadai aalee?" Aliyu ya Kalli cousin din nashi yace "okk wulakanci zakamun kenan ko moh? Kai me kanwa.." Muhammad yai daria kafin yace " no bahaka bane wlh aalee, I would love that but kaga Wanda yakirani yanxu? toh shi zai aure ta wlh dan har uncle abu yabashi ita ma fa, kaidai kawai ganin ta kayi, u don't even know what and what happened, anyways Allah yakaimu gobe, let's see what this old man Will decide...damsel kuwa bayan taci abinci tayi sallah, har bacci yafara daukanta wayan mimi yai ringing, ganin ganin khadija ne takira yasa ta dauka da sauri kafin ta shiga tashin damsel ahankali.. tana bude ido ta mika mata wayan tana murmushi, tace "aunty khadija want to speak to you" damsel ta mike sannan ta karba wayan takai kunne, sunkai minti biyar suna magana kafin daga karshe khadija tace mata " please noor kar ki manta, call him Now, I know he's worried baijiki ba, tell him kun isa lafiya and lastly kar ki manta, gobe idan kuka shiga family house ki Saki jiki sosai please, be friendly to everyone kar suga kamar you are still holding something in mind kinji??" damsel ahankali tace Toh. Sannan sukai sallahma da khadija. Lokacin har 9:30 yayi. Mimi ta kalleta kafin tace " natasheki ko?" damsel tai murmushi kawai ta girgiza kanta, kafin ta mike a hankali ta karasa inda handbag dinta yake ta ciro wayan, 2missed calls din khadija tagani sai 5missed call din Sadeeq. Dawowa tayi ta zauna mimi tace " ko zakizo muje parlour muyi kallo? Damsel tace " I want to sleep" Mimi tace Ok sannan tafita tajawo mata kofar. dialing numbern Sadeeq damsel ta shiga yi,... Sadeeq da shigowan shi kenan daga gidan nabeel, yana zaune a mota yanata faman latsa wayar shi, saiga shigowar wayar damsel, da sauri yai picking call din, dan har ya cire ran jin muryar ta a ranar. yana dauka yai mata sallamah. Damsel ta amsa tare da cemishi " good evening.." Sadeeq yai murmushi sannan yace "evening my Noor.. hope kun isa lafiya?" damsel tai shuru for sometimes kafin tace "Alhamdulillah"... Shiru dukkansu sukayi kafin Sadeeq yai breaking silent din dacewa " kin tafi kin manta dani kawai abinki, tun dazu I'm outside inside my car nakasa shiga cikin gida" murmushi tayi " are you scared?" Sadeeq sosai yake daria sannan yace "yes babe I'm so scared,i can't sleep alone in the house without the owner.. so, wht did suggest??" damsel tai shiru... sai chan yaji tace mishi " toh you should call the owner" Really?? Sadeeq yace kafin yacigaba " she's far away noor, she can't be here now." damsel da bagane yaren Sadeeq takeyiba ko kadan, kuma da gaske tayarda tsoron yakeji. nan ta shiga tunani kirikiri kafin tace " toh go and stay with your friend" da sauri Sadeeq yace " who's my friend?" "nabeel" mamaki sosai Sadeeq yaji jin sunan da ta kira, dan ko kadan baiyi tunanin tasan sunan nabeel ba, ganin kirin yadda nabeel din ke mata. meaning bazai sha wahala wajan convincing dinta akan nabeel is not what she's seeing him as ba. baisan koda mutane a inda take ba yasa yace "alright babe, tunda kince inje wajan nabeel, barin je toh har sai lokacin da mai gidan tadawo permanently ko?" damsel tace " Yes" Sadeeq yaji sosai kafin yace " let me allow my house owner to have a rest, we will talk tomorrow in sha Allah. and Noor.. please don't forget our promise, please noor. Good night" Sadeeq yana hanging call din, yakashe motan shi sannan yafito ya shiga gida....

.... 10:AM har Sun gama shiri, damsel ne tafito tare da Mimi, dukkansu abaya ne ajikin su mimi tasa coffee brown daya amsa chocolate skin color dinta, damsel kuma tasa cream abaya da yai mugun mata kyau sai lallenta da yakara fitowa sosai, dan powder da chapped lips stick Mimi ta shafa mata, sosai suka dinga snap a wayan mimin sannan tai mata hadaddu ita kadai. Saida uncle abu ya yakara tura autar shi nadia takirasu, dan su kadai ake jira. Aliyu ko ya kagu yakara ganin damsel dan dashi za'aje gidan, sosai ya dade rabon shi da family house din dan ba wai yacika zuwa bane, ganin damsel ne yasa yafasa zuwa aiki yace dashi za'aje. ganin basu fito ba yasa Aliyu yafara sauke ruwan bala'i " mimi baza ta bari su fito yanzu ba, tana nan tana goga ma baqin fuskar nan jan powder wai tana kwalliya" Muhammad ya Kalle shi yace " bakasan haske kawai kafita ba? amma wlh mimi na duc tafiku kyau" bai rufe baki ba, saiga fitowar su, kallo daya Muhammad yai musu ya shige mota, Aliyu bin noor ya dinga yi da kallo, mimi dake kallon yayan nata tunda Suka fito kuwa ta kwashe da daria sannan tace " ina gaisuwa yayana" Aliyu yadawo da kallon shi kan mimi sannan yace " baki da hankali" motar Aliyu suka shiga Wanda shi yake ja, sai Muhammad a gaban motar. uncle abu abu kuma ya shiga jeep dinshi shida matar shi haj karima. Sai autar shi Nadia, suka kama hanyar shiga cikin yobe... suna isa aka bude musu gate, gidan cike yake da dangi kai kace biki akeyi, nan kuwa duc aikin baba na yobe ne. sosai Muhammad yaji mamakin ganin dangi na nesa a gidan, Damsel kuwa kanta a kasa gashi tun kafin su shiga ciki hayaniyan mutane ya isheta. Wata tsohuwa ta matso ta rike hannunta, sai kuma ta fashe da kuka tana cewa "ashe sapiyanu yana da baturiya ne haka bai taba gaya mana ba? sannu yar nan" sai kuma ta

Please Login or Register in order to submit comment