Join Our WhatsApp Group

DR AHMAD Complete Hausa Novel Document by DR AHMAD


DR AHMAD

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 51405



DR AHMAD

Reading Time: 4 Hours

Added On: 16, Nov 2023

Author: Maman Khadija ,

Ebook Compiler : Umar Dalha

Author Group : HASKE WRITERS ASSO

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 289.83 kb

File Type: txt

Views: 2334+

Download: 992+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: ο»ΏCompiled by Umar Dalha.


: *πŸ’—DR. AHMADπŸ’—*

1

*NA MAMAN KHADIJA.*πŸ™‡πŸ»β€β™€


*HASKE WRITERS ASSO.*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)


Kusan a jiga ce ya shigo gidan idanun shi duk sunyi ja sabida masifar tafiyar daya shawo fatan shi kawai ya jishi yana watsama jikin shi ruwan sanyi, "Assalamu alaikum." ya furta cikin siririyar muryarshi.

"Wa'alaikumussala na Maman shi ka dawo kenan, sannu da zuwa kawo jakar in ta yaka d'auka kaji Allah yayi maka albarka insha Allahu wataran za kayi alfahari da wannan wahalar da kake sha kaji?"

Cikin jin dad'i ya mika mata jakar littatafan sannan ya d'auki bokitin ruwan dake cike wanda dama ya san nashine kullum ya kan dawo ya tadda ruwan wankan shi Mama ta zuba ta ajiye mai. Ya jima yana wankan sannan ya fito kallon d'aya zakai mishi kasan cewa yanzu ya dawo hayyacin shi ba kamar d'azu daya shigo ba.

Saida ya shiga d'akin shi ya gama shirin shi sannan ya nufi d'akin mahaifiyar tashi cikin shi nata kukan yinwa. gaida ta yayi sannan ya amshi samirar da take miko mishi ya faracin shinkafa damai da yajin dake cikinta, kamin yace

"Mama ina aminu yayine naji banji motsin shi ba?"

Tace "iko yanzu khadija tazo nemanshi wai Maman ta zata aike shi."

"Babana ya karatun naka ina fatan lafiya lau ko?"

"Alhamdulillah wallahi mun kusa shiga aji shidda ai ni sonake kawai inganni cikin jami'a Mama."

"karka damu na Maman shi insha Allah kamar yaune kai-dai kaci gaba da maida hankali domin zaka zama duk abinda kakeso a rayuwa idan har ka dage."

"Mama bari in d'an kwanta kamin la'asar saina leka wajan d'inkin."

gadon shi ya haye wanda yaci gadon shi bayan mituwar mahaifinshi babu wata katifar kirki ammafa yaji gyara domin saika rantse ba kwana akeyi kanshi ba. tabbas bacci yaso yayi idanunshi cike suke da bacci da gajiya saida yana hawo godon yajishi cikin wata irin matsananciyar bukatar mace, nan da nan ya fara juye- juye jikin shi yai wani iri cikin kasala ya tashi ya koma kan dardumar shi dake k'asa shimfid'e ya kwanta tare da dukunkune jikin shi waje d'aya. Tun yana jin wani mugun sanyi har ya samu da temakon addu'o,in da ya keyi wani barci yayi gaba dashi.


Saida ya kuma watsa ruwa sannan yafice masallaci bayan ya gayawa Maman shi cewa zai wuce wajan d'inki daga masallaci domin Ahmad ya kan yi d'in kuna awani shagon abokinshi dake cikin unguwar aduk lokacin da ya dawo makarantar boko.


********

"Kai babana idan ka gama sharar ka bar wanke bayin nayi idan nagama abinda na keyi kajiko? kai maza kazo ka karya ka tafi kadda ka makara kasan dai tafiyar dake gabanka ko?"

"Mama ki bari na gama miki kuma ni azumi na keyi yau, kai Aminu zoka amshi kud'in tara ka wuce."

kusan da mamaki take kallonshi bayan ta isa gaban shi tace "kai babana bani son sakarci yau yaushe?"

Sadda kanshi k'asa yayi kamin yace "Mama yau laraba."
"To me yasa ka tashi da azumi yau tunda kasan alhamis da litinin kawai na amince kayi azumi iye?" kiyi hakuri Mama bawai nasab'a umarninki hakan nanba wallahi ba haka bane kawa gani nayi azumin shine mafita agareni shi yasa na tashi dashi amma kiyi hakuri bazan Kara ba."

Jinjina kanta tayi sannan tabar wajan zuciyarta cike da tausayin yaron nata ammadai ta d'auki alwashin jin damuwarshi yau idan ya dawo daga makaranta domin ba taso wata lalura ta kamashi.

Cikin biyayya ya duka ya amshi kud'in kamin yace "yayana nagode Allah yasaka maka da Alkhairi kuma jiya aunty khadija tace tana gaida ka." cewar Aminu kanin Ahmad wanda ke sanye da kayan primary na gwamnati.

murmushi Ahmad d'in yayi kamin yace to madallah ina amsawa kai maza katafi kaji ko banda wasa me kakeso in siyo maka idan zan dawo? "Aminu ya washe gibin dake bakin shi daya ke yafara famfara kamin yace "yaya alawa me tsinke."

Dariya Ahmad d'in yayi kamin yace "to wawulo sai naga idan kayi karatu sosai sannan nikuma zanyo maka tsaraba."

"Babana baza kazo ka tafi ba ka biye ma Aminu da surutin shi ko?" cewar Mama daga cikin d'akin ta domin tana jin duk maganar da su keyi.


*****

Lafiya lau yaje ya dawo babu wani damuwa cikin ranshi fatanshi arayuwa be wuce yaga ya zama wani abuba kodan dangin mahaifinshi wa inda kullun burunsu be wuce ganinshi awukance ba.

Suna zaune suna tattauna halin rayuwa bayan gama cin abincin su na dare yayin da Aminu tuni ya bingire ajikin Ahmad d'in yana barcinshi sabida shi indai cikin shi ya cika to babu abinda ke biyo baya sai bacci.

cikin nutsuwa ta kalleshi kamin tace "babana ina son kabani duk nutsuwarka anan yanzu sabida bani son ka boyemin damuwarka domin duk duniya baka da kamata kanaji ko? sabida haka ka gayamin banda karatu menene damuwarka??"

marairaicewa yayi kamin ya kalleta sai kuma ya kuma sadda kanshi k'asa yana wasa da dogon hancin aminu wanda keta bacci abinshi.

"Ina jinka babana
a hankali kamar me rad'a ya furta kiyi hakuri Mama wallahi aure nake bukata wallahi nayi bakin kokarin ya kice tunanin araina kodan karatuna sannan ba wani karfine da muba amma na kasa shi yasa nake ya waita yin azumin.....


_TIRK'ASHI......_







*MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€
*πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

2

*NA MAMAN KHADIJA.*πŸ™‡πŸ»β€β™€


Edit by *Hajja ce*πŸ‘ˆ


*HASKE WRITERS ASSO.*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)



Wata irin zufa ce taji ta fara karyo mata lokaci guda tunanin mahaifin shine ya taso mata idanunta ta zuba mishi tana karantar duk wani yanayin daya ke ciki kamin ta sauke ajiyar zuciya tace,

"Babana tun yaushe kake son auren?"

kanshi a k'asa yace "tun shekaru biyu da suka wuce Mama na rasa yadda zanyi dan Allah Mama ki temakeni."

Lissafin shekarunshi ta fara yi inda lissafinta ya nunamata yanzu yana shekara ta cikin goma shabakwai.

"To tashi kaje ka kwantar dashi kaima sai ka kwanta da safe za muyi magana."

A sanyaye ya kai Aminu kan shimfid'arshi kamin ya bar d'akin yana cike da tausayin mahaifiyar tashi dan yasan ba k'aramin tashin hankali yasa ta ba.

kusan kwana yayi yana gayama Allah damuwar shi duk da cewa shi Allah masani ne abisa dukkan komai na fili dana b'oye, amma yana so ka kwantar da kanka gareshi ka kai kukanka gareshi bawai dan be san halin da kake ciki ba. yaso ya kuma tashi da azumi sai dai sam baya san damuwar Maman tashi domin ita gani ta keyi kamar cutar yunwa zata iya kamashi.

kanshi a k'asa yake gaidata bayan dawowarshi masallaci kamin yace "Mama me zan dora yanzun?" d'an murmushi tayi kamin tace "ah'ah babana so nake zaka huta yau."

Murushi kawai yayi har lokacin be kalleta ba domin samun kanshi yayi da wata irin kunyarta, jin yayi shiru ya sata cewa "taliyar murje zaka dafa mana yau saika zabi kalar wacce kakeso ta manja kota mangyad'a kayi mana akwai komai na bukata na ajiye cikin kitchen."

Gidan ya fara gyarawa kamar yadda ya saba kamin ya d'ora girkin yana yi yana bin sautin karatun Alqur'ani a cikin wayarshi k'aramar nokia a gidan wani Redio da akasan ya.

Yana ta zullumin zatai mishi magana sai yaga sab'anin hakan domin har yayi mata sallamar tafiya makaranta beji tace mai komai ba.


Bayan tafiyar su makarnta ne ya sata d'ora tuwon masara wanda ta juyeshi cikin kulla sannan miyar ma haka, shiri tayi cikin riga da zani na atamfa da dogon hijabinta sannan ta rufe gidan ta nufi gidan aminiyarta kuma matar aminin mahaifin su Ahmad gida hudune kawai tsakanin su.

Murna kamar zasu cinye junansu kai kace watanni suka d'auka basu had'u ba. Bayan sun gaisane Maman Ahmad tace "uhum Maman khadija nifa tafe nake da magana bakina Allah yasa malam yana nan yanzu?"

Maman khadija tace "aiko yana nan sabida yanzu ya dawo daga gidan gaisuwar malam iliya, wanka ya keyi yanzu Allah yasa dai lafiya?"

Mama khadija ta tambaya cikin jimami "To bari dai malam d'in yazo kyaji yaron kun wallahi ke son d'auko min magana..!!!"

Saida malam Mamuda ya gama shirin shi cikin d'akin shi sannnan ya taddasu sunata hirarsu. Bayan sungaisa ne yake tambayarta lafiya ko Maman Ahmad?

Tace "Eh to malam dama akan babana ne."

Malam Mamuda ya gyara tsayuwa tare da cewa "To to naji dai ina jinki ainasan Ahmad beda wata illa arayuwa kuma insha Allah bamafatan yasa meta nan gaba meya faru dashi d'in?

Tayi shiru ita kanta maganar nauyi take mata tajima cikin yin shiru sannan tace "Tun watan nin baya naga ya dage da yin azumi kusan kullun to shine naimishi fad'a sosai sabida ina gudun kadda cutar yunwa ta kamashi (olsa) toh kuma dai be dena ba tun yana yi alhamis da litini duk sati sai naga yanzu duk sanda yaga dama yi yake, to jiya na turke shi da tambaya shine yace min wai bukatar aure ke damunshi to nikuma naga babana duka nawa yake da zai san wannan abin shine nace bari nazo naimaka magana ko zaka ganar dashi ya bari sai nan gaba karya ja mana surutun mutane."

Malam Mamuda ya ajiye asuwakin shi gefe kamin yace "ikon Allah to Alhamdulillahi tabbas wannan lamari dole mugode ma Allah domin Ahmad yana da nutsuwa sosai kuma tunda ya nuna yana so to insha Allah baza mu tauyeshi ba domin gashi yana da kokarin ganin ya kare kanshi daga sab'awa Allah ta hanyar yin azumi, dan haka dole mu samami shi mafita tun kamin abun yafi karfin shi a zo ana da ansa ni."

"Maganar karatu kuma wannan babu abinda zai gagara insha Allah zai kai duk matakin da ya keso ya kai." cikin farin ciki Maman khadija tace "kin ga shike nan sai mu aura mishi kanwarshi khadija hankalin mu kwance ko malam?"

Shima cikin farin ciki yace "Nima tinanin da nayi kenan sabida haka gobe kije ki shaidama dangin mahaifin shi sabida afita hakkinsu sannan ki shaida mishi cewa yazo su gaisa da kanwar tashi Allah yayi mana jagoranci cikin lamarin."

Tsabar farin ciki yasa Maman Ahmad sakar musu kuka domin tabbas wa innan mutane sun cika mutane sannan kuma sun rike amanar zumunci da sanin hakkin makotaka.
Da kyar suka lallashe ta sannan tayi musu sallama.
sai kuma zullumin yanda dangin mijin nata zasu amsheta idan ta je musu da zancen. A hanya ta had'u da khadija tun daga nesa take karema yarinyar kallo lokaci guda ta kalli kirjinta babu komai na daga dukiyar kirjin kai daka ganta kasan yarinya ce sharaf innalillahi ta furta kamin ta kauda tunaninta akan abun tana amsa gaisuwarta tace "Mama zanzo na tayaki hira yau tun da babu islamiyya."

Cikin jin dad'i Maman tace "To d'iya ta dama gashi yau mutuminki nayi da ranarnan tuwo sai kinzo sai kici ki koshi."

"To mama sai nazo wanka da salla kawai zanyo in taho gidan ki......"









*MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€
*πŸ’—DR.AHMADπŸ’—*

3

*NA MAMAN KHADIJA*πŸ™‡πŸ»β€β™€

Edit by *Hajja ce*πŸ‘ˆ


*HASKE WRITERS ASSO.*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)


Da sallama ta shiga gidan nata sannan ta d'auki buta bayan ta rataye hijabinta akan kyauren kofarta har yanzu mamakin irin k'irkin mutanen take yi tabbas sun jima suna yi mata halacci tana fatan itama Allah ya bata ikon ganin ta kyautata musu kamar yadda suma koda yashe burunsu suga hankalin ta ya kwanta.

Ta jima cikin sujjadarta ta karshe da kyawawan adduo'i ga mijinta da iyayenta sannan ya ranta guda biyu kacal wanda Allah ya azurtata dasu. Tun kamin ta gama lazumin da ta keyi Aminu yayi sallama hankalin shi nakan kulolin abincin dake ajiye kowa dai ya san yanda ake dawowa makaranta da yunwa da kyar ya zare takalman sandal d'in dake kafafunshi ya zauna sai kallon Maman tashi yake da alama jira yake kawai yaga ta mike ko tayi mai nuni tace ya d'auka.

"Mama ki tashi ki zuba min yunwa zata kasheni." dariya tayi kamin tace "Toh rago kai kam Aminu baka wasa da cikinka ba kamar yayan kaba kaje ka wanko hannu kamin nan na zuba maka."

Yanaci tana kallon shi sosai take ganin kamar da yayi da ita bakamar Ahmad ba wanda yake kallo d'aya zakai mishi ka gane agwai ne.

Sai wajan biyu da rabi sannan ahmad ya shigo gidan kai tsaye d'akin shi ya shige sai da ya kwale kayan jikin shi sannan ya nufi d'akin Maman, "Mama sannu da gida na dawo."

"Yauwa babana sannu da dawowa ga ruwan wankan ka can ka farayi saika zo kaci abinci."

Saida yayo wankan ya kintsa sannan ya nufi d'akin nan ya tadda Aminu zaune yana kallon tv. Gaishe ta yayi sannan ya zauna shima yaci tuwon hankalin shi kwance lokaci zuwa lokaci yana kallon Maman tashi sabida yaga sai murmushi ta keyi.

"Mama ki gaya min mana ta samu ne naga kina tayi min murmushi?"
dariya tayi kamin tace "kawai dai ina cikin nishad'i ne sabida yarona zai ajiye iyali."

Kusan da gudu yabar d'akin yana dariya kamin ta bud'e miryarta itama tace "kaje babanku na kira idan ka huta...!!"

Saida yaji anfara kiran sallar la'asar sannan ya tashi kayan ya saka sannan ya fito waje dan d'aura alwala.
Da khadija ya fara cin karo cikin doguwar riga ta material tayi kyau sosai tayi acuci da gashinta Aminu take yan kema farcen shi sabida ta fishi wayo da dabara tana ganin shi tace.

"Lhha ya Ahmad sannu da tashi tun d'azu nazo Mama tace bacci kake yi ina yini?"

Murmushi yayi kamin ya amsa da "lafiya lau ya makaranta?" Murmushi kawai tayi wucewa yayi yana mamakin rashin maganarta wani lokacin yana k'okarin fita yace.

"kuce ma Mama na fita masallaci Aminu naga ta fara sallah."

A dawo lafiya su kayi mishi sannan ya fice.

A masallaci suka had'u da malam Mamuda ganin irin kallon da yake bin shi da shi ne ya sashi jikin shi yin mugun sanyi domin yana jin mutumin kamar mahaifinshi tabbas idan be yarda da bukatarshi ta aureba to zai hakura yaci gaba da danne abinda ke taso mishi.

Hannun Ahmad malam Mamuda ya rike a haka har sai da suka je gidan shi sannan ya tsayar dashi a zaure. Lokacin jikin shi harya fara rawa sabida be san me zai faruba.

"Ka kwantar da hankalinka Ahmad insha Allah zan tsayamaka akan duk abunda kake so matukar be sab'ama shari'aba d'azu Mamanka tazo min da sakonka shine nace me zai hana ku dai-daita da kanwarka duk da dai tayi kan kanta da yawa ammadai nasan zata iya ragemaka wani abun sannan kuma kaga kaima kayi yarinta da yawa yanzu duk gun wanda naje nemamaka auren abin ma surutu zai zama koba haka ba?"

Cikin wani mugun jin nauyi jikin shi na rawa zuciyar shi na bugawa yace "haka ne baba." Malam Mamuda ya gyra tsayuwa kamin ya fara yi...


Read / Download DR AHMAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album