Join Our WhatsApp Group

MAGAJIN IZZAH Complete Hausa Novel Document by MAGAJIN IZZAH


MAGAJIN IZZAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 113663



MAGAJIN IZZAH

Reading Time: 9 Hours

Added On: 19, Sep 2023

Author: Mai Dambu ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08130269641 , +22796515805

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 627.52 kb

File Type: txt

Views: 1233+

Download: 999+

Last download: 2 days ago

Description/Story: a: MAGAJIN IZZAH!!!

{CIGABA KWARKWARAH}

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

Tukwaicin gare ku!
Mommyna
(Aunty Zeey)
Hajiya Maryam
(Jikar kulu)
Aunty Sa'a
(Kawar Mommyna)
Ummu Adam
(Mama me Voice)
Maman Abuna
(Mamana)
Maman Amatullah
(Kishiyar Muwaddah)
Aunty Aisha Abuja
(Aunty na😍😘♥️)
Tare da fatan Alkhairi a gareku.

_Idan mai karatu bai manta ba! Mun tsaya inda aka sace Yarima Jalal! Kuma magajin masarautar Daura_

بسم الله الر حين الرحيم

Sokoto
birnin Shehu Usmanu danfodiyo! Cibiyar musulinci na arewacin kasar Nigeriya!

Masarautar Sokoto 2019

Ɗaya
"Kinga Hanisah! Wallahi bazan iya ba, shima mutuwa zai yi. Kawai zan guduwa wannan kaddararren auren ne! Ba zan iya auren Ikrama ba!"
Zaro idanu Hanisah tayi, cikin kaduwa tace.
"Amma baki tunanin yadda, Babi zai ji? Ace kin tserewa aurenki."

Tsaki naja tare da juya mata, baya na turawa Ansah sakon.
_Kai banza na shirya! Ina jiran ka!_

Kwace wayar tayi, cikin damuwa tace.
"Wani irin Kuskuren kike aikatawa ne? Wani irin cutarwa kike shirin aikatawa ne! Saura mintinan arba'in da biyar a daura miki aure."
.kallonta nayi sanin zata iya b'ata min shirina, nace mata.
"Toh shikenan! Na hakura yayi miki!"
Yadda nayi maganar, sai da na bata tausayi, rike hannuna tayi sannan tace.
"Addah Aanih kiyi hakuri! Idan kika yi wani abu yan uwan Babu zasu iya juya mishi baya!

Kuma wannan auren wata dama ce da kika samu, dan mahaifin yaron gwamnar jahar nan ne, don Allah karki zubdawa Iyayenmu kumar su."

Murmushi tayi sannan tace.
"Babu komai! Na fasa!" Ina gaya mata, amma kudirina yana raina.

Fita tayi tace min tana zuwa, na rufe kofar dakin, shiru nayi ina nazarin abinda yake shirin faruwa, nan da minti talatin da wani abu, sakone ya shigo min. Na duba naga yace min.

_Kin shirya?!"_

Da sauri na tura mishi da
_Na shirya_
Shiru nayi ina tausayawa Baabi!
Buga min kofar dakina aka yi, nazo zan bude nace.
"Waye?!"
"Me gyaran banɗaki ne ba ance pampo ya b'aci ba?!"
Shiru nayi domin ban san waye ya turo shi ba, kawai nayi kumdubalar bud'e mishi, fuskar shi rufe makari, kallon juna muka yi naga kamar kasan ƙwayar idanun shi.

Matsa mishi nayi ya shiga cikin dakin, yana tambayana.
"Ranki shi dad'e, ina ban dakin yaƙe!"

Shiru nayi sannan na nuna mishi wani kofar dake kallon gadona, shiga yayi can yace.
"Ranki shi dad'e! Nace ba!"

Cikin gundura da halin shi nace mishi.
"Meye ne?!"

"Don Allah ki shigo ki kwashe wannan abubuwan ki!"
Sai kuma naji kunya ta kama ni, mace an santa da boye kome nata, bawai tallatar dashi ba, kawai ina shiga, na juya tare da kwashe wanduna.

Kafin na kai da kwashewa sai ji nayi ya saka min abu akan fuskana, komawa jikin shi nayi ta baya na mike! Murmushi yayi yace.
"Hmm! Da wuri haka!"
A ban dakin ya kwantar da ita, ya cire abin kunenta da abin wuyar, sanan ya daukota zuwa dakin ya zage buhun shi ya nad'eta a cikin babban bargo, sannan ya dakata a cikin buhun, me L, ya sab'ata a kafad'arshi. Ya fito daga dakin babu wanda ya damu da shi, dan an san yace zai shiga gyara pampon dakin ta.

Koda ya fito dauke da ita a kafad'arshi, yana fitowa harabar gidan, ya isa gurin motar shi, Bugatti, ya bude sannan ya juya yana kallon dandanzon mutanen da suke shigowa gidan.

Daga nesa, sarki Jaamal na daura, yake kallon shi dai-dai lokacin da yaja abin kariyar da ya saka a fuskar shi, sannan ya rufe bayan motar ya shiga motar cikin isa da kasaita. Yadda yake tafiya yana juyawa zaka rantse a gidan iyayen iyayen shi yake.

Yana shiga motar, ya bata wuta.
Sai da ya finciketa, da sauri mutane suke bashi hanya, har zuwa lokacin idanun sarki Jamal yana kan shi, koda yazo zai bar gidan, sai da ya kuma kallon fuskar shi. Amma ya rufe gilashin motar da sauri sabida akwai ledar kariya wacce take sanya cikin motar baki.

Da gudu ya cilla motar kan titi da masifar gudu, kamar zai tashi sama.

.....
A cikin gidan kuwa babu wanda ya kuma bin takaina, sabida basu kawo a ransu za a sace ni ba, sai Hanisah da take kokwanto, kawai tazo da sauri akan zata duba abu a kayana, kawai tana shigowa, taga turus babu ni, wani irin tsoro ne ya shige ta. Ta juya dakin Mamanta da gudu, tace.
"Ammih! Don Allah zo"

"Kinga Nisah barni ina zuwa!" Ganin taki bata fuskata juya gurin Amaryan Baban su, Ummih Rahil, tana shiga taga nsn ma da mutane.

Riko hannun ta tayi suka bar falon, d'akina suka nufa ta gaya mata kome! Wani irin dauke wuta Rahil tayi jikinta na rawa, ta kalli agogon dakin, saura minti goma daurin auren. Da sauri ta fito kafarta babu takalmi, ta nufi inda shashin mai martaba sarki Aryan yake, inda yake dauke da mutane, tana shiga ta janyo hannun shi suka fita daga gidan.

Har can lambu, suka nufa. Tare da fashewa da kuka, tana gaya mishi Aanih Fatimah Khatoon ta gudu! A tsorace ya ke kallonta, sanya hannunta tayi akan fuskar shi. Tana girgiza kai tace.
"Allah ya albarkace ka da yara mata biyu! Zaka iya amfani da wannan damar, karka damu, ita kuma Aanih a bazama nimanta, dan bata yi nisa ba. Kuma nafi zargin sace ta akayi dan wallahi bazata aikata hakan ba!"
.wani irin yanayi ya shiga Dakyar yake d'aga kafar shi, har ya isa kofar babban masallacin da za a daura auren, ya dauki amsa kuwa.

Ajiyewa yayi sannan ya riko hannun Mai girma Gwamnan Sokoto, suka fita ya fara mishi bayani, amma fir yaki amincewa karshe ya tilasta Aaryan ya fadawa kowa abinda ya faru, jikin shi a mace! Ya tako har gaban masallacin yace kuma ɗaukar amsa kuwar.

Ya fara bayani kamar haka.
"Assalamu alaikum warahmatullah! Ina me baku hakuri da abinda zan gaya muku! Tare da bawa Mai girma Gwamna Ziyad Almustapha hakurin abinda ya faru!"

Sunkuyar da kanshi yayi, tsabar tashin hankali, muryan shi na rawa ya kuma buɗe baki zai magana.
Sarki Jaamal yace.
"An mai da Auren Gimbiya Fatimah kan Gimbiya Hanisah, abisa wata lalurar da ta taso, sannan kuma ina mai bawa Mai girma Gwamnan Jahar sokoto hakuri ya amshi wannan tayin da kima.

..... A dukkan sarakuna ne! Babu wanda zai so yaga kan shi a irin halin da Sarkin Yake ciki, idan bazan manta ba yau shekaru ashirin kenan! Da rasa Yarona Yarima Jalal, kuma nasan irin zafin da ake ji, don Allah kar mu kuma kara mishi zafin da yake ji."

Aikuwa Ikrama yayi tsagal yace.."Kawu nifa ina son Aanih dan haka zan iya jiran har ta dawo, kawai Baba ka sanya a baza jami'an tsaron, dan wallahi bazan iya rayuwa da wata mace ba sai Ita."

Daurin auren da ba ayi ba kenan, aka kuma baza jami'an tsaron, suka shiga nimanta.

----
Irin gudun da yake yi, zaka zata dan yana da wata abu me muhimmanci ne, sai dai kawai yau burin shi ya, isa Sahara. Ya ci mutuncin Yarinyar da ta keta mishi haddi a cikin dubanin jama'a, ta Mishi abinda ba a tab'a mishi ba.

A cikin dandazon dalibai na jami'ar Calgary University Canada, ta lalata mishi farin cikin shi. Ta sanya shi fita cikin makarantar kan shi a sunkuye!

... Ta zubda mishi da duk wata ji kimar shi, na rayuwar da yake jin kan shi,.
Shi din kamar sarki ne a cikin makarantar ko fada ake da zaran an gan shi toh an daina, amma sai da yarinya b'arar mishi da Izzar shi, bai tab'a jin tsanar kanshi ba, sai a wannan lokacin, inda ya ajiye muguwar tarihi ba.

Dan haka dole yau ya rama abinda tayi mishi, buga kan motar yayi, tare da cizon lebben shi na kasa, sannan ya kuma bawa motar wuta, kamar walkiya haka yake tafiya, har ya isa bakin bodar najeriya da Nijar, wanda yake elaile. Suka gama duba kome, bayan motar ce basu duba ba, sannan suka bude mishi kofar fita ya cilla kan motar a guje.

..... Doguwar tafiya yayi kafin ya samu bakin iyakar Nijar din, sannan ya mika musu shedar, shi dan kasa ne, ganin takardan shi, yasa suka barshi ya wuce.

Idan ya tuna abinda ya faru sake dukar motar yake, sai da yayi dogowar tafiya har dare yayi suna hanya, kafin ya sauka a gefen hanya, ya tsaya idanun shi jajjur, ya fito daga motar da abin sallar da kuma, ruwa, yana fitowa abinda ya fara shine buɗe bayan motar ya fidda ita, ya wurga ta kasa sannan ya zazzage ta kamar wata mara daraja.

Yaje ya buɗe ka motar ya dauko ruwa cikin galan yazo ya bude bakin ya juye mata akanta, tsaf sannan ya d'agota yana kallon yadda take layyi cikin mayye, da marisa.

Ya kifa mata Mari sai da ta nemi tambelan da take, ta bude idanun ta. Tar akan shi. Yana tuna yadda ta keta cikin dinbun Jama'a ta iso dandamalin ta kifa mishi maruka har biyu, tare da tofa mishi yawu, wani irin rintsa idanun yayi cikin baƙin ciki ya kuma tsinka mata mari, yana huci.

Alola yayi tare da gabatar da sallar da ake bin shi, ina zaune kamar wata gumki, rarrafewa nayi na dauki butar na fara gabatar da alola tare da niman abinda zan kare jikina, can na hango bargona na dauka na lullube kaina, na gabatar da sallar azhar da la'asar tare da isha da magarib, ina idarwa kafin na fahimci me ake ciki ya kuma ta sowa, yazo kaina janye bargon yayi sannan ya shiga b'alle botirin rigarshi.

Wani irin kuka ne ya kwace min na takure kaina guri guda ina cewa.
"Don Allah! Jaheed! Karka min haka! Wallahi ba zan kuma ba! Karka manta wata rana ba zaka ji dadin kaga ayiwa Yarka haka ba, Don Allah! Mujaheed."

Cukume wuyar rigana yayi ya mikar dani, sai da ya yaga rigar har kasa, da sauri na kare kirjina, ya kuma shiga yaga duk wata abinda zata rufe min jikina, sannan yace.
"Boye jikinki kike?"

Cikin wani irin tsoro na fashe da kuka jikina na rawa, nace.
"Wallahi bazan kuma ba!"

Wani irin kallo yake min, tun daga fusakana, har zuwa cibiyata.
"Zazzafa! Shi yasa kike jin kanki ke wata ce ko? Toh bari na rabaki da abinda kike dashi sai mu zama (0-0)! Ban tab'a dogon magana ba sai da na hadu dake Shaidaniya! Ban tab'a fuskarta tozarci ba sai da na hadu dake! Koda yake! Akwai yan matan da suke zuwa gabana tsirara suna niman Alfarmar na kalle su me zanyi da kayan yar talatin da hudu!

Dan haka ki rike aranki anan zaki dawamma, sai an jima!"
#MI
#HWA
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:49 AM - Ummi Tandama: MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

   
Fatan Alkhairi Maryam Kolo da Maman Ummite😍🌹

BIYU
Da gudu nabi bayan shi tare da rike rigar shi cikin kuka da tashin hankali nace.
"Don Allah ka rufa min asiri! Bani da kowa anan! Jay! Idan Yayarka kace a wannan halin zaka tafi ka barta"

Juyawa yayi cikin zafin nama, ya ture ni sai da na zube a kasa, na sake mik'ewa zan tashi har ya shiga motar shi ya bata wata irin wuta.

"Jayyyy!" Na kwala mishi kira! Tare da sake kukan da yafi nada karfi, ina  da nasanin abinda na aikata a cikin shekaru uku da suka wuce, zuwa huɗu.

               ........
Aanih Fatimah Aryaan! Cikakken sunana kenan!

     Shekaru ashirin da biyu baya..

      ---
Cikin tashin hankali! Suka nufi asibiti da ni, ranar da aka sace Yarima Jalal, abinda aka fara shine kara min jini, abin mamaki jinin kowa yaki Dai-daito da jinina, sai da Aka dibe na Sarki Jaamal, aka gwada take jinin yayi daidai da nawa, hankali Baabina ya tashi, tare da Ummi, sai kaiwa da komowa suke.

Sai da na kwana na wuni, sannan na farka, ina tashi a firgice, na fara ihu, tare da niman inda zan b'oya. Sai da U mmih ta rungume ni, amma a haka na ture ta sabida karfin da yake shiga na, ihu nake tare da kiran sunan Jay! Tunda Baabi yaga matsalar haka take, sai yayi maza aka mai dani Sokoto.

       Inda aka kaini shashin kakata, Umman Baabi. Tunda aka kira malamin masarautar, yana zuwa yayi min addu'a, sannan yace.
"Zaku yi hakuri zuwa gobe! Insha Allah zamu duba Alamarin."

    Haka suka amince, dake na samu barci, har washi gari da malamin yazo shiru yayi sannan yace.
"Tabbas rayuwar mu da mutuwa duk na Allah ne! Sannan babu wanda ya tab'a zanawa kanshi ƙaddara! Sai dai  ƙaddarar yarinyar nan ta shiga na shi.

      Haka ya sanya masu faffutikar ganin cewa sun dauki fansa! Sun yi tarayya akan ta! Dukda ban san meye ba! Akwai matsala. Sai dai zamu iya magance abin da Allah ya nuna mana!"

   Daga haka bai kuma magana ba, ya mika musu addu'o'in da zasu na bani, ina sha.

          A hankali na soma samun sauki tare da samun kulawa daga Matan Babana! Ummi da Ammih.

          .....
Bayan na warke na cigaba da zuwa makanta, kamar yadda na saba.

    --- A masarautar Daura.

Gimbiya Sarah! Sai da tayi dogon jinya dan ya hadu mata da kewar D'anta da kuma ciwon zuciyar da yake barazanar kamata! Hakan yasa ta daina shiga cikin duk wani abinda yake faruwa a cikin gidan, dukda Abba Jaamal yayi kokarin fahimtar da ita! Hakan kaddara ce, dan haka su godewa Allah tunda ya basu wasu yaran.

            Cikin zubda kwalla tace mishi.
"Don Allah! Kawu karka sani jin wani abu a raina domin, kuwa bana raba daya biyun, Akwai Sannun wasu manyan mutane na cikin masarautar nan!

     Wanda dama basu kaunar mu! Taya zanyi hakuri bayan nasan akwai mutanen da ban san su ba, a bayan Inuwar mu!

     Kawu bazan tab'a samun nutsuwa ba, sai naga yarona!"

         Cikin damuwa ya zuba mata ido, tare da tausayinta, sannan yace.
" Zato zunubi ne! Kuma babu kyau don Allah ki cire tunanin wani zai iya cutar da shi."

              Kwalla ne ya zubo min, na ciro takardan da aka kawo min na mika mishi, kallon rubutun yayi, sannan ya kalli agogon dakin yace.
"Ina mai baki hakurin abinda na gaya miki! Tabbas akwai mutanen da suke son ganin bayan mu! Ganin haka ba zai samu ba, shine suka dauke min Yarona! Tunda sun zab'i haka."

Mik'ewa yayi sannan ya isa bakin kofar, sannan ya juyo tare da zuba min ido yace.
"Zan  yi murabus! Kafin Allah ya dawo mana dashi! Zan ajiye mulkin amma abisa sharadin kujeran masarautar na shine! Nan da shekaru ashirin idan ina raye! Bai dawo ba a bawa wani! Idan kuma ya dawo!"

   Daga hakan ya fita daga dakin, yana jin ciwon abinda aka mishi,

  .kai tsaye masarautar...


Read / Download MAGAJIN IZZAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album