Join Our WhatsApp Group

ALAKALAMIN KADDARA PART 1 Complete Hausa Novel Document by ALAKALAMIN KADDARA PART 1


ALAKALAMIN KADDARA PART 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 84934



ALAKALAMIN KADDARA PART 1

Reading Time: 7 Hours

Added On: 13, Dec 2023

Author: Lubna Sufyan ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 473.54 kb

File Type: txt

Views: 698+

Download: 328+

Last download: 19 hours ago

Description/Story: [11/30, 10:15 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

Alkalamin Kaddara

Prologue

"Na sha dauka mahaifiyar kowa haka take kamun inyi hankali, sai daga baya na fahimci ni kadai nai rashin sa'a. Na sha fatan in kwanta bacci in tashi a gidan da ba nan ba, har sai da na fahimci ba komai rubutun ALKALMIN KADDARA yake iya canzuwa ba. Ta wani fannin yau burinki ya cika...ta wani fannin ke da kanki kinyi nasara wajen wargaza burin naki..."

Muryar Tasneem ta sarqe saboda sabon kukan dake shirin kwace mata.

"Tsakanin yau zuwa gobe idan aurena ya mutu kece...Idan mutuwar shi bata faru a daren yau zuwa safiyar gobe ba, makomar shi kece sila. Abba bazai yafe miki ba Umma, kaman yanda nima bazan yafe miki ba..."

"Tasneem..."

Bara'atu ta fara muryarta da duk jikinta na kyarma, maganganun Tasneem din na zauna mata a wajajen da bata san da su ba. Girgiza mata kai Tasneem take hawaye na zubar mata.

"Bana son jin komai...lokacin da na sha jiran jin kalamanki ko bayanin ki ya wuce umma. Bazan roqi komai daga gareki akan su Hamna ba...Zan tuna miki mu duka Amana ne a wajenki... Idan baki dubi Allah ba bansan me yasa kalamaina zasu canza komai ba..."

Tana karasa maganar ta sa hannu taja mayafin da ta dage lokacin da aka shigo da ita daga dakin, tana rufe fuskarta dashi lokacin da hawaye masu dumi suka zubo mata. Dan ko zama batai ba daman, wani irin zafi kirjinta yake mata yau wajen wata biyu kenan, tari Tasneem ta soma ba kakkautawa da yasa Bara'atu da sai lokacin ta samu motsi tashi da sauri ta karasa wajenta tana kamata hadi da daga mayafin dake rufe da fuskarta.

Hannuwan da Tasneem ta sa ta rufe bakinta ta dawo dasu dubanta jin lema a jikinsu, har lokacin tarin da take bai tsagaita mata ba, tsilli-tsillin jini tagani a jikin tafukan hannunta.

"Tasneem tarin jini kike..."

Bara'atu ta fada hankalinta a tashe, zame jikinta Tasneem tayi daga riqon da tai mata tana nufar hanyar kofa, dan tarin ya fara tsagaita mata. Sai dai kirjinta da yake kaman ana hura mata wuta, har numfashinta sama-sama yake saboda azaba...!

**

Ko ina na jikin ta kyarma yake, musamman zuciyarta da take dokawa har cikin kunnuwanta, kallon shi take da bayanannen tsoro a kan fuskarta. Gam yaja kofa yana kulle zuciyarshi da duk wani emotions dazai iya samun fitowa, fuskarshi babu komai akai ya sauke idanuwan shi cikin nata

"Ni da ke bamu taba wuce wani abu da ya girmi nisha di ba, bansan me nayi daya saki tunanin ko zuciyata kin isa ki hango ba balle ki samu waje a ciki, bakuma zan baki hakuri ba dan babu kuskuren da nayi, banyi komai da babu amincewar ki ba..."

Hannu Fadila ta sa tana dafe cikin ta da yake yamutsawa da sabon tashin hankali. Inalillahi wa ina ilaihi raji'un take son furtawa amman kaman an kulle mata baki, sai lokacin nauyin komai yake danne ta, abin da yake tsaye a wuyanta take son hadiyewa amman ta kasa, sau uku tana bude bakinta da niyyar magana amman babu abinda yake fitowa. Numfashi take ja ta bakinta tana fitar dashi a wahalce.

"Nawfal???"

Ta kira sunan shi cike da shakku da alamun tambayoyi da dama, muryarta can kasa, idanuwanta na kasa yarda shine tsaye a gabanta. Zuciyarta na qin aminta da abinda kunnuwanta suka ji. Nawfal bazai mata haka ba, ba zuciyarshi kawai ta iya hangowa ba, tana da yaqinin har cikinta ta shiga ta samu wajen zama.

Ganin yanayin dake fuskarta yasa Nawfal kama hannunta yana janta, mamaki ya hanata yin komai banda binshi, har yakai ta bakin kofa ya hankada ta, badon bangon da ta dafa ba, babu abinda zai hanata mummunar faduwa.

"Ko meye kike tunanin yake tsakanin mu ya zama tarihi a yau!!!"

Bakin shi kawai take ganin yana motsi, kunnuwanta sun daina jin sauran kalaman, tashin hankalin da take ciki da maganganun shi na farko sun sa komai tsaya mata cik. Girman kuskuren yarda dashi na danne ta...!!

**

Hannun shi Tariq yake kokarin kwacewa yana juyawa hadi da kallon gidan, hawaye masu dumi na zubo mishi. Sakin hannun shi Ashfaq yayi yana tallabar fuskar shi ya juyo dashi.

"Ba mu da dalilin juyawa baya Tariq, babu abinda ya rage mana, komai ya kare, ni da kai ne kawai..."

"Ta ina zamu fara? Ina zamu je? Yaya haka rayuwa take da wahala?"

Tariq ya karasa wasu sabbin hawayen na zubo mishi, da ganin su kesa zuciyar Ashfaq wani irin ciwo marar misaltuwa. Fuskar Tariq din ya tallaba da dukkan hannayen shi, a zuciyarshi ya fara jin zaman kalaman kamun ya fito dasu.

"Ban sani ba nima...babu abinda yake da tabbas, na so labarin rashin tabbacin rayuwa kawai zan baka Tariq, bawai ka tsinci kanka a cikin shi ba, zuciyar dake bugawa a kirjina kanta babu tabbacin zata kai anjima, abu daya na sani a wannan matakin, da duk numfashin da zan fitar daga yanzun zuwa na karshe zan tabbatar ko yayane taka rayuwar akwai sauqi a cikinta...zan tabbatar hawayen ka sun zuba ne badan kunci na rayuwa ba. Kana jina? Baka bukatar kowa in ina nan..."

Idanuwan shi Tariq ya kalla, a cikin su yana ganin gaskiyar alkawarin da Ashfaq yai mishi, a cikin su Yana ganin rubutun ALKALMIN KADDARAr su da yaren da yafi karfin fahimtarshi...!
[11/30, 10:15 PM] LubnaSufyan: ®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

LubnaSufyan
Calmlubna@gmail.com

01

Zaune take a gaban mudubin, jikinta sanye da doguwar riga ta material mai fari da purple mai haske a jiki, hannunta riqe da dankwali purple da take daurawa akanta. Turaruka ta dauko kala biyu tana feshe jikinta. Duk da kyan datai bai hana damuwa bayyana a fuskarta ba.

Idan tace ga yanda tayi rayuwa a wata dayan nan, cikin gidan Rafiq ba zata iya fada ba. Komai zuwa yake yana wuce mata, hannu tasa tana dafe kirjinta, wajen zuciyarta da yake mata zafi kaman zai kama da wuta. Kanta ta kwantar jikin mudubin tana maida numfashi ta bakinta saboda azabar ciwon da take ji.

Badan bata tsammaci kauce ma abinda yake faruwa yanzun ba, badai ta dauka zaiyi ciwo irin na yanzun ba, hukuncin data tsammaci Rafiq zai mata daban da wanda ya dauka. Duk da banbancin kalilan ne, da igiyar auren shi har ukku akanta. Wannan ma wani abu ne, zuciyarta ta fada mata.

Runtsa idanuwanta tayi, daren ta na farko a gidan Rafiq din na dawo mata, kamar a lokacin yake faruwa.

*

Kuka take da yake jin shi har kasan zuciyarshi yana kara mishi ciwon da takeyi, kamun ya janye jikinshi daga nata yana jin daudar dabai kamata ace yanajin ta ba. Hannunshi yasa yana goge bakin shi cikin son cire yanayinta daga jikin labbanshi. Runtsa idanuwa yayi yana kirga daya zuwa goma cikin kanshi, nutsuwa yake bukata ko yaya take kamun yayi abinda su dukan su zasuyi dana sani.

"Ni ya kamata inyi kuka Neem...ni ya kamata in zubda hawaye bake ba..."

Kamar maganganun shi take jira dan karama kukan da takeyi gudu. Muryarta na sarqewa ta soma magana

"Sugar...ka fa...ka fahimce ni dan Allah..."

Wata irin dariya Rafiq yayi da bata da alaqa da nishadi, yana dafe kanshi dake juyawa da duka hannuwanshi biyu, kamun ya mike yana nufar bandakin dake cikin dakin ya tura ya shiga yana doko kofar, karar da tayi na gauraye dakin kasancewar dare ne.

Mikewa zaune Tasneem tayi tana jingina bayanta da kan gadon hadi da janyo kafafuwanta ta hade jikinta waje daya. Kuka take har numfashin ta na barazanar daukewa, idan tace ga yanayin da take ji karya take, sai yanzun tasan in tashin hankali yai girma bashi da yanayi sam.

Hannuwa take sawa tana goge fuskarta da wasu sabbin hawayen ke sake batawa, jikinta ko ina bari yake, dakyar takai hannunta ta lalubo wayarta dake ajiye kan drawer din gefen gadon. Dannawa tayi tana swiping key din dake jiki. Karfe uku da rabi na dare.

Hakan bai hanata lalubo number din Samha ba. Bata jin zata iya magana dan haka ta tura mata text:

'Yagane Samha... Wallahi bazan iya rasa shi ba. Shi kadai ne dai-daito dana samu a rayuwata na tsayin lokaci, bazan iya rasa shi ba... Bazan iya ba'

Ko wayar bata ajiye ba kiran samha ya shigo, sai da Tasneem ta share hawayen da ya zubo mata tukunna ta daga ta kara a kunnenta, muryar samha na saka sabon kuka kwace mata.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Tasneem.... Ya Allah. Wallahi na kasa bacci tun dazun gabana sai faduwa yake.... Yana ina yanzun?"

Cikin kuka Tasneem ta amsata

"Yana bandaki...na shiga ukuna samha..."

Ta karasa tana kokawa da numfashin ta da baya kaiwa inda ya kamata yakai.

"Ke! Ki nutsu! Ki saurareni.... Babu abinda zai faru In shaa Allah.... Shisa naso ki fada mishi gaskiya sanda ya tambaya..."

Har lokacin numfashinta bai koma yanda ya kamata ba, hakan bai hana maganganun da samha tayi su dauki tunaninta su watsa wani lokaci can baya ba.

*

A zaune ta same shi cikin motarshi, driver dinshi na dayan gefen. Sanin ko gaisuwa ba zata hada su ba yasa bata bi takanshi ba. Hankalinta nakan Rafiq da kafafuwan shi na daga waje, ya dafe goshin shi da hannuwanshi duka biyun. Bata san dalilin da yasa zuciyarta bugawa ba. Cike da shakku ta kira shi

"Sugar..."

Dago fuskarshi yayi yana sauke mata idanuwan shi da suka canza launi saboda bacin rai.

"Waye Alhaji Madu?"

Gyara tsayuwarta tayi dan zata iya rantsewa tana jin bugun zuciyarta har cikin tafukan kafarta. Ta bude bakinta yakai sau hudu tana rufewa saboda babu kalma ko daya data iya fitowa.

"Neem tambayar ki nake. Waye Alhaji Mando?"

Gudu tunaninta yake cikin kwakwalwar ta da hada karyar kamun ta dorata kan harshenta da fadin

"Kaman na taba jin sunan, ina tunanin ko a ina"

Tayi mamakin muryarta da batai rawa ba, da dukkan karfin halin da take dashi take jure idanuwan Rafiq da suke cikin nata da wani yanayi.

"Na gaya miki abu na farko dazai iya wargaza alaqar mu shine karya, ni da karya muna da tarihi marar dadin ji..."

Muryarta a karye, zuciyarta cike da wani irin tsoro da take addu'ar bai nuna akan fuskarta ba tace

"Ehen...Nasan na taba jin sunan, wani mutum ne da yasha zuwa kofar gidan nan wai yana sona. Sugar kallo daya zakai mishi kasan ba mutumin kirki bane ba...saida na daina fitowa in ya aiko tukunna ya hakura ya daina zuwa..."

Kallon ta Rafiq yake yi, kallon ta yake yana son fahimtar gaskiyar maganganun da tayi ta cikin idanuwanta.

"Ba koda yaushe nake yarda da shaidar mutane akan yan uwan su mutane ba... Allah yasa kar inyi dana sanin yarda dake"

Kai take daga mishi da sauri tana kokarin dora murmushi akan fuskarta.

"In shaa Allah ba zakayi ba...ka shigo mana"

Girgiza mata kai yayi yana jan kafafuwanshi ya mayar cikin motar. Hadi da jan murfin ya rufe kamun yace mata

"Akwai inda zanje... Abinda nazo tambayarki kenan daman"

Matsawa tayi daf da motar sosai tana yawata idanuwanta kan fuskarshi hadi da sauke muryarta

"Ranka a bace yake har yanzun... Zuciyata ba zata samu nutsuwa ba"

Numfashi yaja yana saukewa a hankali. Ranshi a bace yake batai karya ba, maganganun da yaji sun tsaya mishi, duniyarshi a birkice take, wajenta kadai yake samun nutsuwa, in ya rasata baisan abinda zai kama ba. Kallon ta yadanyi

"Abubuwa ne sukai mun yawa..."

"Are we okay? Ni da kai?"

Kai yadan daga mata. Yanajin ta sauke wani dogon numfashi da ita kanta bata san tana rike dashi ba. Tana kallon shi yaima driver din nuni da hannu alamar su tafi, batare da ya sake ce mata komai ba har driver din ya tayar da motar suka wuce. Sai lokacin kafafuwanta da sukai sanyi suke barazanar kin daukarta.

*

"Tasneem!!!"

Muryar samha ta katse mata tunanin da take, jan hanci tayi, muryarta a dakushe da kukan da takeyi tace

"Zamuyi magana da safe...ina son zama ni kadai..."

"Neem please..."

Samha ta fadi ta dayan bangaren muryarta na karyewa. Cikin karfin halin da Tasneem bata ji ta katse ta

"Karki damu...kawai banHa son magana ne yanzun"

Bata jira amsar da samha zata bata ba ta janye wayar daga kunnenta tana yaddar da ita kan gadon. Dai-dai fitowar Rafiq da kugunshi yake daure da towel. Da busassun idanuwanta da suka sha kuka har tana jin hawayenta sun kafe take binshi da kallo.

Sif din kayan dake cikin bangon ya bude wandon da hannunshi ya fara kaiwa kai ya dauko yasa ma jikinshi yana dauko riga batare da damuwa da kalar su ba. Asalima basu bane damuwarshi, wajen gadon ya karaso yana sa hannu ya dauki mukullin motarshi dake ajiye a kan kafet da wayarshi yana zurawa a aljihu.

Ganin yana shirin fita yasa Tasneem saurin sakkowa daga kan gadon tana shan gabanshi. Kauda kai yayi gefe baya son ganinta sam-sam. Rabata yayi zai wuce ta sake shan gabanshi. Hawayen da take tunanin sun kafe suna zubo mata, tasa hannunta ta goge.

"Ina zaka je cikin daren nan? Ba tuqi kake iyawa ba..."

Bai amsata ba yasa hannun shi yana ture ta gefe hadi da takawa ya nufi kofa, cikin zafin nama ta kamo hannun shi.

"Kabari saida safe"

Hannun shi ya kwace daga cikin nata yana kallonta cike da wani abu da bazai iya fassarawa ba, zuciyarshi naci gaba da tafasa, komai zai iya faruwa in yana ganinta a gabanshi.

"Bana son ganinki... Neem bana son ganinki wallahi"

Runtsa idanuwanta tayi tana jan numfashi, maganganun shi na sukar zuciyarta da ciwon da bata taba sanin shi ba a rayuwarta.

"Control dina gab yake da samun matsala, komai zai iya faruwa in ina ganinki..."

Tasan shi, tasan halin shi, saidai bata taba jin bacin ran da take ji a muryarshi ba tunda take dashi. Komai ciwo yake mata, zuciyarta na rarraba radadin da take zuwa ko ina na jikinta. Tana jin takunshi da murza kofar da yayi kamun tace

"Abinda yake faruwa yanzun...Shine dalilin yi maka karya. Tsoron rasa ka ya hanani fada maka gaskiya..."

Bugo kofar dakin da yayi ta fada mata cewa ya fice, nan inda take tsaye ta durkushe tana sakin wani kuka daya fito tun daga zuciyarta...!

*

Ringing din da wayarta take ne ya katse mata tunanin data ke, hannu tasa tana goge fuskarta saboda hawayen da bata ma san suna zuba ba sun jiqa mata kunci, mikewa tayi da niyyar karasawa kan gadon ta inda wayar take tana kara, babu shiri ta koma ta zauna tana runtsa idanuwanta gam, dakin jujjuya mata yake.

Ga kirjinta kaman an dora dutse saboda nauyin da taji ya mata.

"Ya Allah..."

Ta fadi tana sake runtsa idanuwanta gam ko zata samu jirin da yake dibarta ya daina. Tana jin wayar harta yanke, kiran ya sake shigowa amman ta kasa mikewa, tana alaqanta jirin da take ji da rashin cin abincin da rashin nutsuwa yake hana mata. Wajen mintina sha biyar ta dauka a haka kamun dakyar ta mike ta karasa kan gadon ta kwanta.

Wayar ta dauka ta cire key din dake jiki tana dubawa, Azrah ce, yanayin da take ji bai hana dan karamin murmushi...


Read / Download ALAKALAMIN KADDARA PART 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On ALAKALAMIN KADDARA PART 1
avatar
khadija-7-4

5 months ago

Reply

Yayi

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album