Join Our WhatsApp Group

TAKUN SAKA Complete Hausa Novel Document by TAKUN SAKA


TAKUN SAKA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 9798



TAKUN SAKA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 03, Aug 2023

Author: Billyn Abdul ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08184017082

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 59.83 kb

File Type: txt

Views: 2585+

Download: 656+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [12/31, 6:20 AM] Abbu Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_*


. *************************⬇**********************
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************


*_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_*



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



_ZAFAFA BIYAR 2K22_



*_Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'umma. Ka haneni rubuta abinda zai cutar da wanina da ni kaina. ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan bayin ALLAH da suka bar duniya😭🙏🏻_*.

_Masoya abokan tafiya ga ZAFAFANKU BIYAR sun sake dawowa a karo na biyar insha ALLAH☺️🤗_



*_______________________________*


*Chapter one*


............Sosai motocin ƴan sandan guda uku na farin kaya ke zuga uban gudu a titi tamkar suna a jerin gasar tsere, bakajin komai sai jiniya mai tsanani da zata iya tada hankalin duk wani mai tsoro. Da yawan sauran motocin dake a kan titin sauka suke gefen hanya domin basu fili, dan duk mai hankalin da yaga wannan gudun yasan bana lafiya bane ba. Sai dai kowa mamakinsa da tambayarsa shine (Mike faruwa haka?).
       Basu da mai basu amsa, kamar yanda nima bani da amsar. Sai dai mu cigaba da binsu domin sanin mike faruwar? Baki ɗaya.

★★

      A lokacin da waɗancan motocin ke tsere-tseren gudu mai kama dana kai agaji ko ceton rayuwaka anan headquarters na ƴan sandan jihar a kusan hargitse take a wani yanki na cikinta, hargitsin nata kuma yanada tabbacin alaƙa da waɗan can motocin.
      Kusan gaba ɗayan ma'aikatan department ɗin tsaye suke cirko-cirko a ɗakin na'urorin bincike cikin matuƙar taraddadi da ƙaulanin fargabar abinda ke faruwa. Yayinda kusan ma'aikata bakwai ke zaune sun duƙufa wajen sarrafa Computers ɗin cike da ƙwarewa da nuna matuƙar ƙwazo. Bakajin sautin komai sai na keyboards da ajiyar zuciyoyi.
      “Sir mutumin nan yana da matuƙar wayo, bana tunanin zamu iya dakatar da shi da ga zuƙar kuɗaɗen nan fa a wannan karon ma”.
       Ɗaya daga cikin masu sarrafa computers ɗin ya faɗa yana yarce uwar zufar daketa faman tsatstsafo masa a goshi, duk da ac dake aiki a ɗakin. Dafe kai wanda yake ma maganar yayi cikin matuƙar dagulewar tunani. Sai kuma ya ɗago a fusace yana kallonsa. Cikin tsawa ya daki desk ɗin gabansa yana kallonsu da idanunsa da ke jajur na ɓacin rai.
       “Idan har kuka bari ya cimma burinsa a wannan karon kuma bazan yafe muku ba. Har sai yaushe ne zamu iya daƙile wannan tsageran ɗan ta'addan yaron dake ganin a kullum yafi ƙarfin hukuma?!!”.
     Yanda yay maganar da bugar desk ɗin a tsawace ya saka da yawansu zabura. Wanda yay maganar yay saurin maida hankalinsa ga computer ɗin gabansa jikinsa na ɓari ya cigaba da sarrafata da sauri-sauri. Shima ɗayan dake gefensa tsawar ta rikitashi matuƙa, dan haka ya ƙara ƙaimi wajen sarrafa na'urar gabansa.
        Ogan nasu ya cigaba da masifar data sake hargitsa sauran harma suka rasa nutsuwarsu wajen sarrafa na'urorin. Ɗif komai dake wajen ya tsaya, hakan ya jawo yin tsitt ɗin ɗakin lokaci guda. Gaba ɗayansu suka zubawa Computers ɗin ido a hargitse, dan sun san aikin gama ya gama kawai. kamar yanda ya saba cin nasara a kansu yauma ya sake ci........


                 
        A ɓangaren motoci masu rera gudu bisa titi kuwa sun isa banki ne, inda suka iske mutane da duk ma'aikatan bank ɗin hankalinsu a tashe. Musamman ma shugaban bankin da yafi kowa birkicewa. Dan kuɗin da guy ɗin ya ɗiba ya tatsesune cikin asusun matar gwamna. Duk da dakatar da shi da aka samu nasarar yi ya zuƙi biliyoyin kuɗin da su kansu tsoron bayyanama duniya sukeyi saboda gudun abinda zaije ya dawo kuma.
      Cikin ƙanƙanin lokaci jami'an nan na hukumar farin kaya da ƴan sanda sun gama zagaye bankin dan ana ƙyautata zaton wanda ya aikata laifin ko wani nashi yana cikin bankin har yanzun basuyi nisa ba.
An garƙame ko'ina da ina, duk wanda ke a ciki baida damar fita sai an bincikesa ciki da bai ɗinsa, musamman ma wayoyin hannu da bags.
      Al'amarin tamkar rufa ido har aka gama bincike mutane aka koma kan ma'aikatan banki babu mai ko alamar aikata laifin. Zuwa yanzu kuma babban ɗa ga gwamna ya iso wajen tare da mahaifiyarsa matar gwamna ɗin da securitys ɗinta. Hakanne yasa wajen ƙarayin tsamari dan ta nuna tsananin ɓacin ranta na ƙarancin tsaro da bankunan ƙasarmu ke fama da shi. Inda kake tunanin ka ajiye kuɗinka ka koma kai barci mai daɗi a gidanka shine kuma ya zama gidauniyar wawaso na salon ɓarayi masu aiki da ilimi, ta tabbatar musu bazata yardaba, kodai kuɗinta su dawo cikin asusunta kokuma ta ɗauki tsatstsauran mataki akan bankin da ma'aikatan cikinsa. Wannan shine ya ƙara ɗaga hankalin duk wani ma'aikaci dake a reshen wannan banki.
      Abu ya ƙara tsamari dan har C.P da kansa ya iso wajen tare da mataimakin gwamna da wasu manya-manyan ƙusoshin gwamnatin dan ɓarnace ta ɗunbin kuɗi wannan ɓarawo ya aikata wadda a ƙiyasi bama ya taɓa aikata kwatankwacin irinta ba a duk hatsabibancin da ya aikata, dan babu hukumar tsaron da babu sunansa a ƙasar matsayin mai-laifi saboda tsagerancinsa.
          Takaici da baƙin cikin halin da ake ciki ne ya saka wani ɗan sanda yima mabaratan dake zaune a ɗan gefen bankin korar kare, dan yanda suka zauna zuru-zuru suna kallon duk wainar da ake toyawa ne yasa takaicinsu kamashi. Ya fatattakesu tare da bada umarnin idan sunƙi barin wajen a saka musu barkonon tsohuwa maisa hawaye.
        Tuni suka fara haɗa kayansu suna barin wajen da sauri-sauri. Wani gurgu dake a tsohon kekensa (Wheelchair) ya murzata da ƙyar yana barin wajen, keken sai wani irin mugun ƙara yake saboda tsabar tsufan da yayi.
       Cikin layi na uku dake akan titin da bankin yake ya shiga, sai da ya iso saitin wani kango makahon dake biye da shi a baya yana raira ƴar waƙarsa da laluben hanya da sanda yace, “Boss mun iso point”.
      Wani irin ƙuuu! Yaja birki da keken, ya waiga bayansa ya kalli makahon da ya buɗe idanunsa ras yanzu, ɗauke kansa yay ya maida idanunsa ga ko'ina na layin babu kowa sai jefi-jefin yara dake wasa. Cak ya miƙe daka saman keke yana jan wani uban tsuki dasa hannu ya yaga daddauɗar rigir malun-malun ɗin shaddar jikinsa data fita hayyacinta saboda tsufa. Ya fincike rawanin daya aza akai da hular suma duk ya jefa saman keken.
        
Ba ƙaramin ɗunbin al'ajab da mamaki bane suka lulluɓe ni saboda ganin lafiyayyen mutum ƙyaƙyƙyawa tsaye akan ƙafafunsa, a yanayin jiki dai daka gansa kaga matashin mai tashen ƙuruciya da cikakkiyar lafiya, amma abin mamaki fuskarsa ta tsoffi ce, hasalima harda tarin furfura a saman kansa da sajensa zuwa gemu. Sosai raina ke cike da ɗunbin mamakin hakan, dan nidai ban taɓa gani ba tunda nake. Ace matashin saurayi da fuskar tsoffi............✍🏻



*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI......_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_


*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA'AYI NA DABANNE_*

*MAZA 'YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300
2____400
3____500
4____700

Duka gamayyar biyar din(1k)
1,000

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
       
[12/31, 6:20 AM] Abbu Saleh AlQuyraemey: *_Typing📲_*




*_🔮TAKUN SAAƘA!!🔮_*



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



_ZAFAFA BIYAR 2K22_


*________________________________*

*Chapter two*


.........Idanu sosai na ware domin ƙare masa kallo, sai dai isowar mashinan power bike guda biyar cikin layin ya rabamin hankali biyu, tuni makaho shima ya yaye kayan dattin jikinsa ya fito a lafiyayyensa. Cikin girmamawa ɗaya daga cikin wanda suke a saman mashinan ya faka nasa gabansa, ya sakko tare da sauke jakkar bayansa dake goye ya ciro takalma masu azabar ƙyau da sauran kayan bada kariya daga haɗari na mashin ɗin.
Cikin sauri wani ma ya sakko a nasa mashin ɗin ya warware kujera ya ajiye masa sai kace wani sarki.
cikin wani salo na isa da ƙasaita yakai zaune tamkar wanda ya samu kujerar falonsa, yanda yake abu cikin izza da isa ya sani yin zuru ina kallonsu.
       Wanda yake riƙe da takalmin ya kai tsuggunne gabansa ya fara zare masa takalman robar dake ƙafar tasa irin na masu kiwo ɗin nan duk sun fashe saboda wahala. Takalman ya shiga saka masa, shi kuma ya amshi hular kwanon ya ɗaura a kansa tare da sauran kayan. Miƙe yay cike da ƙwarewar ƙasaita ya ɗare bisa mashin ɗin.
Makaho da wanda ya kawo masa mashin ɗin suma duk suka haye sauran mashinan da ƴan uwansu suke..
       Kasancewar nashi mashin ɗinne a gaba ya sake daidaitashi. Cikin sallon ƙasaitarsa ya ɗaga hannunsa sama, ƙaramin yatsansa ya fara miƙarwa alamar (ɗaya), ya ɗaga na kusa da shi (biyu), yana ɗaga na ƙarshe alamar (uku) suka saki wata irin sautin ƙara data gigita kusan mafi yawan jama'ar layin. Tuni mata suka shiga gudun afkawa cikin ɗakuna, masu ƙarfin hali naɗan leƙowa suga mike faruwa?.
        Kasancewar layin da suke yana gab da bankin tuni saƙonsu ya isa kunnuwan jami'an tsaron dake zagaye da wajen. Har rige-rige jami'an tsaron keyi wajen hawa ababen hawansu, dan sunsan wannan singing ne na tabbatar da shiɗin na kusa da bankin.

        Daga ɓangarensu kuwa a wani irin mugun gudu suka harbo mashinan suka fito daga cikin layin, hakan yayi dai-dai da gabatowar motocin jami'an tsaron kwanar layin suma. Isowar jami'an tsaron ya sakasu danna wani abu a jikin mashinan nasu tuni hayaƙi ya gauraye titin baki ɗaya suka harba mashinansu tamkar walƙiya.

       ALLAH yaso a ƙaramin titi suke, da tabbas babu abinda zai hana haddasuwar gagarumin haɗari saboda yanda gaba ɗaya titin ya lulluɓe da hayaƙi, mai tahowa baya ganin mai tafiya.
Sai dai duk da wannan hayaƙi hakan bai hana mota ɗaya cikin motocin jami'an tsaron bin bayansu ba a guje suma. Kusan mintuna uku cikakku hayaƙin ya ɗauka kafin ya baje, zuwa lokacin tuni mashinan nan sun ɓace ɓat daga yankin ma baki ɗaya tamkar na aljanu.
       Rai a ɓace sauran jami'an tsaron ke yarfar da hannaye, kowa yanajin takaici da ƙunar rai cikin zuciyarsa. Masu ƙarfin hali ne ke ƙoƙarin tsintar ƙananun takardun dake yashe a ƙasa alamar masu power bike ne suka sakesu tare da hayaƙin. Abinda ke a jiki ya ƙara harzuƙasu, dan kamar yanda ya saba barin sunansa idan ya aikata laifi a wannan karonma hakane. Sunan nasa ne a jikin takardar tare da zanen fuskarsa ta tsoffi raɗam.
      A zabure ɗaya daga cikin jami'an yace, “Kai! Wannan ai yana cikin al'amajiran dake a ƙofar bankin suna bara”.
     “What!!?”
C.P ya faɗa a matuƙar zabure.
       Manager da shima ɗaya daga cikin takardar ke hannunsa muryarsa a hargitse ya ce, “Tabbas wannan al'amajirin sati biyu da suka wuce na fara ganinsa a wajen nan. Amma dai wannan ya cika matsiyaci”.
         Zafi da ƙunar da zukatansu suke musu ya hana kowa ƙara magana. A kuma dai-dai lokacin matar gwamna da yaronta suka iso wajen suma. Dan sun gaji da jiran tsammani a cikin banki. Jin cewar basu kamashiba yasa ɗanta ya fara masifa tamkar zai haɗiye harshensa. Hakama mataimakin gwamna ya tabbatar musu karsu wuce awanni ashirin da huɗu basu kamo hegen ba.
    Daga haka kowa yabar wajen rai ɓace. Jami'an tsaron ma kowa ya koma inda ya fito domin ƙulla mai yuwuwa.


Jami'an farin kaya harsun kama hanyar barin wajen suma suka dawo, sakamakon kiran wayar oga kwata-kwata na hukumar tasu da ɗaya daga ciki yayi domin sanar masa halin da ake ciki. Shine ya basu umarnin komawa su duba inda wannan gagarumin ɓarawo ya fito bayan barinsa banki.
      Sun shigo layin, inda suka iske mata da yara cike suna kallon kujera da kayayyakin da gurgu da makaho suka cire. Cikin mamaki suma suke duban kayayyakin, tare da ɗanyin tambayoyi ga mutanen wajen kowa na faɗin albarkacin bakinsa.
       Ɗaya daga cikin jami'an yakai duƙe yana ɗaga kayan dake bisa keken guragun. A mamakinsu sai ga facemask exactly da wadda ke jikin fuskar guy ɗin, kuma itace zane a jikin takardar da ya bar musu a titi.
       Komai basuce ba, saboda basusan da mutanen da suke tare a wajenba dan ya zama shu'umi kuma. Suka tattare kayan kaf har sandar makaho suka bar wajen..

      A lokacin da mashinan power bike ɗin can ke reren gudun tserewa wasu daga cikin ɗaliban babbar jami'ar jihar ke tururuwar fitowa domin neman ababen hawa da zasu maidasu gidajansu dan sun ƙare darasin karatu na wannan rana.
       Matasan ƴammata uku dake ƙoƙarin tsalla titi cikin matuƙar gajiya da yunwa suka daka uban tsale domin komawa baya sakamakon gabatowar waɗanan mashina dake gudu tamkar su kaɗai ne a titin.
       Ɗaya a cikinsu takai ƙasa sakamakon tuzguɗewa da takalmin ƙafarta yayi, ƙarar data ƙwalla ne ya maido mafi yawan hankalin mutane da idanunsu ke akan power bikes ɗin kansu. Ɗayar budurwar tai saurin kamo wadda ta faɗin tana ambaton kalmar “Subahanallahi Hafsat!”.
 ...


Read / Download TAKUN SAKA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On TAKUN SAKA
avatar
khadija-9-2-3

6 months ago

Reply

Please I need to read it

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to khadija-9-2-3

click Here or subscribe to download it

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album