Join Our WhatsApp Group

YAN GUDUN HIJIRA Complete Hausa Novel Document by YAN GUDUN HIJIRA


YAN GUDUN HIJIRA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 52470



YAN GUDUN HIJIRA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 13, Sep 2023

Author: Zainuddeen Zain ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : PEN WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 08034840276

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 285.12 kb

File Type: txt

Views: 602+

Download: 346+

Last download: 1 day ago

Description/Story: VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ɗauke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.


: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




🅾1⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```


_The price of success is hard work, dedication to the job at hand, and the determination that whether we win or lose, we have applied the best of ourselves to the task at hand._



*Shafin Masoya*


_ASEEYA ABUBAKAR IMAM_
_HAUWA AUWAL TSOHO_
_SAUDAT ABDULLAHI SAJ_
_HAFSAT IBRAHIM QUEEN HAFCY_
_NABEELA DIKKO_
_'YAR FATHER_
_AMEENA SANI MANI_
_FATIMA UMAR ABDULLAHI (MUMMY YUSUF)_
_FATIMA LAWAL UMAR ROGO_





```SHIMFIDA/TSOKACI```



Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin halittu, wanda bai Haifa ba kuma ba a haife shi ba, wanda yake da mulki cikakke kuma tabbatacce. Tsira tareda amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) dangaban goshin Allah, wanda duk wanda ya kaucewa tafarkinsa ya bata. Tareda iyalan gidansa da sahabbansa hadi da duk wanda ya bi tafarkinsu ya zuwa ranar tsayuwa.



Godiya fiye da a kirga zuwa ga mahaifiyata, wacce ba zan taba buda littafi ba face na sankamamata godiya kan dawainiya da wahala da take yi a kaina, tabbas ba domin mahaifiyata ba, da maikaratu ba za ka san waye _ZAINUDDEEN ZAIN_ ba, ina rokon ubangiji da ya yafe mata kurakuranta, ya kuma sa aljanna ce makomarta. Ubangiji ka kareta daga sharrin duk wani mai sharri. Amin.



Masoyana, kuma naku daban ne, banida baki da zan iya furta godiya zuwa gare ku kan gwarin guiwa da nake samu daga wurinku, ina mika godiya kan addu’o’I da fatan alkhairi da kuke yi zuwa gare ni. Inaso kuma kusan cewa, ina yin ku sosai da sosai. Irin ana tarennan, kun dai gane.



Wannan labarin kirkirarre ne, duk da cewa jigon labarin ya faru da gaske, duk abubuwan da za su fito a labarin kirkira na yi. Labari ne na wata baiwar Allah da ta shiga gararin rayuwa, tun kuruciyarta har ta kai shekaru 31, an aurar da ita ne ga wani mutum da ke zaune a garin Maiduguri mai suna QASIMU, ita matar mai suna SAJIDA, haifaffiyar garin Kalgo ce da ke jihar Kebbi. Tun tana da shekaru 16 aka aurar da ita, duk da a lokacin tanada wanda take so sosai, a haka aka tankwarata, ita kuwa ta yi biyayya ga mahaifanta duk da rayuwarta ba ta so ba. Bayan aurensu da malam QASIMU, wulaknci kala-kala, sai ya dinga biyowa baya, duk abinda ta yi, ba ta burge shi, har dukan ta yake yi, a haka har suka haifi ‘ya’ya guda biyu: BILKISU ita ce babba inda take da shekaru 14 sai ‘yar karamar mai suna AMISHA inda take da shekaru 4, kafin AMISHA SAJIDA ta haifi da namiji, wanda rashin kulawa da take samu daga mijinta ya zama ajalinsa, wanda shi ne dalili da ya sa, a lokacin da ta haifi AMISHA, dole ta jajirce wurin ganin ta kula da ita yadda ya dace.



Dalilin Qasimu na wulakanta matarsa kuwa, shi ne, saboda shi ma da wacce yake so, amma a gida aka tilasta sa kan lallai sai ya aureta, shi ne yake wulakanta ta da zimmar ko zai rage radadi da raunin da aka yi wa zuciyarsa.


SAJIDA kuwa, ba ta sarye ba wurin kokarta janyo hankalin maigidanta zuwa gareta ba duk da ba ta son sa, amma ina, abin sai gaba yake yi, duk da sun ajiye ‘ya’ya kuma ga shi sun fara manyanta.




Kwatsam suna a haka, ‘yan Boko Haram za su kawo hari a garin nasu, wanda zai yi sanadiyyar bazamarsu cikin jeji da basusan ina za su nufa ba, za su hadu da masifu da dama a cikin jejin, haka za su koyi darussa su kuma hadu da mutane da dama.



Ya wannan abin zai faru, ina kuma za su tafi? Duka amsoshinku suna cikin wannan littafin mai suna; *’YAN GUDUN HIJIRA* _labarin Sajida_




***FARKO***




Lokacin damina ne, ga shi da misalin karfe biyar na maaraice, kuma da alama akwai alamun hadari duba da yadda giragizai ke shawagi a sararin samaniya, da kuma yadda suka lullube rana har ma za ka yi zaton dare ne ya shigo, iska mai sanyi wanda ke kadawa a hankali kadai ya isa ya saka mutum nutsuwa. Abin ka da gari mai yawan jama’a sosai, garin MAIDUGURI. Duka wannan yanayi mai dadi tareda kwantar da zuciya bai hana hawaye zuba ba daga idanun SAJIDA, zaune take cikin gida da ke dauke da daki kwaya daya wanda suke zama ita da mijinta QASIMU da ‘ya’yansu guda biyu BILKISU da AMISHA. Sai zabgar hawaye take har da shessheka a kukan nata, sai kokarin sharbar majina take daga hancinta, amma ina abin ya fi karfinta, tana tsakiyar ratsa kuka, ta jiyo kukan Amisha daga dan karamin dakinsu wanda ko kyaure ba ya da, ga labulen dakin ya yi datti kamar wanda aka dauko daga juji, jin kukan diyarta mai shekaru hudu a duniya, ya kara jefa ta cikin wani sabon kuka wanda har sauti ya fara bayyana, ta tsinci kanta cikin halin rashin iya motsawa balle ta je ta rarrashi diyar tata, wacce rabonta da ta saka abinci a cikinta tun garin kwaki da ta sha da safe. Cikin shesshekar kuka ta tada kanta sama, a ranta tana cewa, ya ubangiji kana ganin halin da muke ciki ni da ‘ya’yana, ka kawo mana dauki…tun bata kammala addu’ar ba sai ta ji shigowar BILKISU daga sallamar da ta yi kafin ta shigo. Fuskarta cike da hawaye ta tada kai ta kalli ‘yarta BILKISU da take kira da MAMANNE kasancewar sunan mahaifiyarta take da, “me ke faruwa naga kin dawo cikin damuwa, MAMANNE?” ta fada muryarta na rawa cike da alamun kuka ga kuma tausayi cikin muryar. “Sani mai shago ne ya ce ba zai sake bamu bashin garin kwakin ba, wai saboda ba ma biya, ya ce yana biyar mu bashin sama da shekara, kuma wai bai ga alamun za mu iya biyanshi ba, shi ba zai yarda mu kashe mashi shago a banza ba” ta fada sai ta karasa cikin kuka. Cike da tausayi ta janyo ta a jikinta ta rungume sai rusar kuka suke. Ita tunaninta daya ne, yanzu yarannan nata a haka za su kwana cikin yunwa da wahala.




Suna a haka, sai suka jiwo ana, sallama, jin bakuwar murya, sai suka yi sauri suka share hawayen da suka cika fuskokinsu, suka amsa sallama tareda yi wa mai sallamar iso, sai ga wata mata ta shigo, daga ganinta kasan irin matannan ne masu wadata, duk da ba za ka kira ta mai kudi kai tsaye ba, malama AISHA sunanta kamar yadda ta sanar da su bayan da ta gabatar da kanta.




“dama ina tsaye ne lokacin da ‘yarki ta zo neman bashi wurin mai shago, shi ne na biyota bayan naji abubuwa da ya fada a kanku, nasan tabbas kuna bukatar taimako, ga wannan” ta mika musu, awara tareda dankali da aka soya, sun sha yaji da albasa ga kabeji a ciki, ta kuma ce da su; “ku kwantar da hankalinku, duk abinda ubangiji ya yi, mai kyau ne, wata rana duk wannan talaucin zai gushe. Idan kin aminta, zan dauki diyarki aiki a gidana, sai ta dinga kawo maku abinci daga wurina, kuma na dinga biyant duk karshen wata”



Sai da ta yi ajiyar zuciya na tsawon lokaci, kana ta aminta, ba tareda ta ko yi tunanin shaidawa mijinta ba, domin tasan ba zai taba goyon bayan haka ba. Duk da ba zai taba taimaka musu ba ta ko wacce hanya.




“kinada aure ne?” inji malama Aisha ta fada a dai dai lokacin da ta kai idanunta tana kallon farfajiyar gidan da ya sha shara sosai, ga tsafta, amma gidan ba tsari ba kuma kulawa daga maigidan. “eh inada miji” “Allah ya sawwaka”



Nan ta shida mata cewa za ta zo da safe domin ta kai su su ga gidan, daga baya sai su saka ranar fara aiki, ta kawo kudi ta basu, ta ce ga wannan ku sayi kayan abinci, domin ai mutum ba ya zama da yunwa.




Ta yi mata rakiya har kofar gida, ta dawo ta kira AMISHA suka zauna suka saka awarar da dankalin cikin kwano, wanda har ya fara lamba, suka zauna su uku suna ci, su dukansu fuskokinsu cike da tausayi sai da aka fara kiran magariba, suka samu suka karasa ci, bayn sun wanke hannuwansu, AMISHA ta fara zabga musu surutu. Murmushi kawai SAJIDA ta yi ta ce “lallai AMISHA ba ki da kunya, wato dazu yunwa ce ta sa sai rusamin kuka kike yi, yanzu kuma za ki zo ki dameni da wannan surutu naki?” suka share da dariya, nan ta umarce su da su dauki butoci domin su yi salla lura da lokaci ya rigaya ya yi.




SAJIDA mace ce baka ga ta doguwa mai kakkauran jiki, tanada alamaun kirar karfi, ga ta da zuciya mai kamar maza, tanada kirki sosai ga addini kuma ga tausayi, nan da nan hawaye sun fito daga idanuwanta, ba kyakkyawa ba ce, haka ba zaka kira ta da mummuna ba, haifaffiyar garin KALGO ce da ke jihar KEBBI, aure ne ya kawota garin MAIDUGURI hannun QASIMU.



Da suka idar da sallah, ta kira Bilkisu ta aiketa da kudin da malama AISHA ta basu, domin ta siyo musu kayan abinci. Fitar BILKISU da kamar minti biyar sai ga hadari dauke da iska ya taso, kan titi sai guduwa mutane ke yi, wadanda ke cikin gida kuwa sai ta kansu suke yi, domin irin iskannan ne mai masifar karfi wanda har itace yake kayar wa.




Wanne hali BILKISU take ciki?
SAJIDA fa wanne yanyi za ta shiga?
Ina QASIMU da har yanzu bai dawo gida ba tun fitar sa da safe?



Duk amsoshin suna cikin shafi na gaba, labarin har yanzu bai fara ba.




DR. ZAIN
[2/3, 4:40 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾


🅾2⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_A common mistake that people make when trying to design something completely foolproof is to underestimate the ingenuity of complete fools_




*Shafin Masoya*



_M. D. R. Arrigasiy_
_Fiddausi Sodangi_
_Ayush Iliyasu_
_Amra Auwal_
_Sayyada Maryam_
_Madara_
_Zeety_





***CI GABA***



Iska ake ta famar zabgawa mai dauke da masifar karfi tareda wani sanyi wanda ke saka mutum kakkarwa ba tareda ya nufa ba, haka kake jin iskan dauke da sauti mai firgitarwa, sai daukar bugun kwano yake daga kan dakuna yana yawo da su a sararin samniya da farfajiyar garin MAIDUGURi, itace kuwa haka suke faduwa kamar ma’askin dare ya hau kan mace mai gashi. Mutane kuwa sai kokarin ceton rayukansu suke yi ta hanyar neman hanyar wucewa gida, cikin gudu, garin gaba daya sai ya yi duhu, ko tafin hannunka ba ka iya gani, wutar PHCN kuwa tun kafin iskan ya kawo aka dade da daukewa, kasancewar masu hasashe sun tabbatar da yiwuwar iskan zai yi barna.



Hankalinta a tashe, ta rungume AMISHA sai zabgar kuka take yi, a ranta tana cewa wannan masifa har ina, yunwa da talauci ga shi sun janyo na yi asarar diyata, wayyo ni SAJIDA na shiga uku…kalaman ta take ta maimaitawa ke nan a zuciyarta, cen ta jiwo rufin dakinsu ya fara babbakewa, iska ya fara daukarsa, cen sai ji ta yi fuuu! Iska dauke da kasa na shigowa cikin dakin nasu ta sama, kasancewar rufin dakin iska ya dauke shi, ganin haka, ta kalli AMISHA da ke rungume a kirjinta, ta tada kanta ta kalli saman dakinsu, kawai ta sunkuyar da kai wani sabon kuka ya soma daga dan karamin bakinta, kasancewar wannan lokacin kukan ya kwaceta har sautinsa ya bayyana. Ba ta san lokacin da ta buda baki ba ta ce; “QASIMU! Wai kana ina ne, ya za ka tafi ka bar mu cikin wannan masifar? Oh! Ni ‘yasu, yanzu wanne hali BILKISU take ciki?” ta fada a daidai lokaci da take kokarin nemo malullubi da za ta rufe jikin AMISHA da shi, ganin yadda take kakkarwa ba ko tsayawa.




BILKISU kuwa, kasancewar inda aka aiketa ba nisa da gida, har ta rigaya ta siyo juyowa da za ta yi ne iskan ya taso, inda idanuwanta suka cika da kasa, ta rafka kuwwa, mutane da ke guduwa domin neman mafaka suka bangajeta ta fadi, ga ta a kasa ‘yan abubuwan da ta siyo sun watse sai lalube take kasncewar idanuwanta suna a cike da kasa, ga kuma matsanancin duhu da iska mai karfi bugu da kari ga sanyi, mafi muni kalar tufafin da ke jikinta, kan talauci wani hijabi ne da yanzu shekarunsa sha tara, na mahaifiyarta ne take sakawa, shi kadai suka mallaka, idan mahaifiyarta ta dawo daga lalurarta sai ita ma ta dauka ta fita, idan kuma fita ta kama su a tare, a haka take fita dole ba hijabi a jiki, har ‘yan unguwarsu na mata sharri, _mai hijabin da ya girmemata_ a jikinta kuwa zani ne, wanda ta yi daura gaba da shi, wannan ya bai wa sanyi damar ratsa jikinta yadda ya dace, musamman ma da hijabin ba kauri, saboda ya sha ruwa kuma ga huji wurare da dama a jikinsa.



Da laluben ta samu ta tattara wasu daga cikin kaya da aka aiketa ta siyo, ganin ta tattara sai ta nemi wata rumfa ta shiga ta tsaya, a lokacin tana gani idanuwanta sun fara budewa daga kasa da ta cika su. Iskan ya kwashi awanni hudu ana yin sa daga bisani aka sauko da ruwa masu matsanancin karfi, ganin iskan ya tsaya, kuma ga ruwa ana laftawa da har sun dauki awa daya da kusan rabi ana laftawa ba ko alamar tsaiko ko sassauci, Bilkisu ta ratsa ta cikin ruwan a guje ta nufi gida. Isar ta gida gaba daya jikinta a jike har kana ganin kwancin mamanta a kirjinta duk da daura gaba ne a kirjin nata kuma ga shi ko bra babu, cikin kakkarwar sanyi, ta yi tsaye, a lokaci daya ta sake kayan da mahaifiyarta ta aiketa ta siyo, ganin yadda mahaifiyarta da kanwarta ke shan kashin ruwa zaune cikin daki, kasancewar rufin dakin da iska ta dauke....


Read / Download YAN GUDUN HIJIRA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album